Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko bai dace ba, wai shin kai ka haifeni ko ni na haifeka? Laifi ne don nayi bincike insan inda xa mu tura er mu? Meye aibun tambayoyina? Ba neman aure ya xo ba? To kuwa ai dole ayi masa tambayoyi, Ko dama ance maza ne kadai xa su yi bincike banda mata? To wllh ka shiga hankalinka, ba ruwanka da harkana ko lamarina a gidan nan ina sake ja maka kunne" Farooq dai sai kallonta yake, can ya juya a fusace ya bar wajen, Umma ta bi sa da harara, Hafsah ce ta shigo parlon da leda a hannunta, Umma tace "Makira sai yanxu kika ga dama kenan, to kin kyauta kin ji ko? Ki tafi can parlona a sama ki jirani in xo in sameki ki gaya min gidan uban da kika je" Hafsah tace "Zan kai ledar kitchen" Umma tace "Aa wuce da shi sama, xa mu hade da ke a can" Hafsah bata ce komai ba ta wuce sama xuwa bangaren Umma, Nihad ta kai masu abincin da Mumy ta gama hadawa, wani tray kuma ga meat pie, samosa, spring rolls da doughnuts da Aunty Jamila ta kawo bayan Mumy tayi mata waya ta gaya mata tayi ta kawo, da yake tana da ma'aikata cikin kankanin lokaci suka yi suka gama, wani bowl me dauke da apples kusan goma ta kai masu a karshe ta ajiye, sannan tayi serving dinsu abincin. Bayan sun gama cin abincin, Nihad ta shigo parlon tare da Ya farooq, bayan ya gaisa da su ya fita, Mujahid ya mike yana kallon Aliyu yace "Bani makulli in dauko wayata a mota, they might be plenty of calls i missed" Aliyu ya mika masa makullin ya amsa ya fita, Nihad dai kallonsa kawai take, wayarsa ya ciro a aljihu ya shiga gallery bayan few seconds ya mika mata, ta amsa tana kallon screen din wayar, sosai gabanta ya fadi, ta dai yi shiru bata ce komai ba, yace "You promised kin daina dukka ire iren outing din nan, so where did this come from?" Nihad ta marairaice tana kara kallon hoton, 4 weeks ago ne suka je wani babban restaurant da su Naf da Husnah da samarin su, shine aka yi hoton a can, wando ne a jikinta sai crop top me shegen kyau da tsadadden sneakers a kafarta, sannan ta daura baƙin dankwali a kai ta xubo dogon gashinta, su Husnah ma duk ire iren shigar suka yi a hoton... jin tayi shiru Aliyu yace "Why are u quiet?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "Hoton nan ai ya dade" Yace "Karya kike, this is a recent pix, jiya da daddare Naf ta daura a status na gani nayi saving" Nihad tace "Am serious ba kwanan nan muka yi ba, kuma ai kafin in maka alkawarin daina fita tare da su ne muka yi hoton nan, ka tambayi Naf din ma" Yace "Nihad!!" Shiru tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, yace "Saboda ina sonki da aure ya sa ki ka ga har nake hanaki abubuwan nan da kike, banda haka i have no business with ur life style, quite alright kinsan i have other babes wa enda muke tare da su har yanxu, but ban ta6a daga kai na hana yarinya yin abinda tayi niyya ma rayuwarta ba, ban ta6a hanasu holewarsu yanda suke so ba, but ke saboda intention dina a kanki daban shi yasa nake hanaki duk wannan shiriritar da kike, Upon how wealthy my parents are, baxa su ta6a yarda in kawo masu mace mara kamun kai ince xan aura ba, baxa su ta6a amincewa, kuma ya kamata ki kara yarda yanxu tunda har na tako tun daga Abuja na xo gidanku to da gaske aurenki nake son yi, i will neva do that for any lady, sai sai idan dama ina da wata sabgar da xanyi a kano.... Nihad this should be ur last warning!!!" A hankali tace "Toh kayi hakuri, in sha Allah hakan baxai kara faruwa ba, i am promising u this" Yayi shiru yana kallonta, tace "Wllh da gaske nake baxan kara ba" Yace "Toh Allah ya sa..." A hankali tace "Ameen" Yace "Kince min driver din a nan yake zama" Nihad ta gyara xama tace "Ehh wllh, yanxu haka ma yana nan, ai yana kofar gida sanda ku ka shigo layin shi ne ya shiga cikin gidan" Aliyu dake ta kallonta yace "Da muka shigo layin ne ya shiga ciki?" Tace "Aa ai sannan baku karaso ba" Yace "Ohk where is he now?" Nihad tace "What will happen now, kawai mu fita sai ka xauna a compound ni kuma xan je in samesa a can boys quarters da yake zama, ince xan je karbo sako ya xo ya kai ni, daga nan idan ya fito compound xaka gan shi" Aliyu yace "Kamar wasan yara... But i urgently wants to see him" Nihad tace "Noo, ta haka kadai xai fito compound har ka gansa, so now let's go outside" Tashi tayi ta dau bowl din apples tace "Bari in kai maka wannan ka dinga ci" Daga haka ta fita, ya mike ya bi bayanta suka fito compound din, can karkashin thatch dake dauke da kujeru ta kai masa apples din ta ajiye saman table, ya xauna yana kallonta yace "Kin yi kyau" Tayi wani blush tace "Thank you, bari in je in samesa yanxu" Yace "Ohk" Hanyar Chalet ta nufa ya bi ta da ido har ta bace, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna hudu saura, Nihad na isa chalet din ta hade rai tana lekan parlor, isiya ta hango yayi dai dai kan kujera yana ganinta ya mike da sauri ya fito yace "Kaya xa a amsa Hajiya?" Tace "Ina wannan yaron?" Yace "Wani yaro?" Tace "Halilu" Isiya ya ɗan gwale ido a ransa yana kara nanata yaro da tace, can yayi saurin cewa "Yana can daki" Tace "Toh kaje ka kirasa Mumy ta bada sako a basa" Juyawa yayi yace "Toh Hajiya" Ya fi minti daya yana kwankwasa kofar dakin da Khalil yake ciki amma bai bude ba, shi dai yasan baya baccin rana balle yace, to ko kila yana bandaki, bai yi gigin bude kofar ba tun ranan da Saminu yayi masa haka yayi cutting din masa warning me lafiya, Bude kofar aka yi khalil na kallonsa yace "Ya aka yi?" Isiya yace "Aa dama mamarsu Sudais ce ta bada sako wai xa a gaya maka a waje" Khalil yace "Ohk" Fita yayi tun daga cikin parlor ya hangota, yana fitowa ya tsaya bakin kofa yana kallonta, Tana yatsine yatsine tace "Yauwa xaka yi dropping dina in amso sako yanxu, kaje ka dauko makulli ina jira" Juyawa yayi ya koma ciki ba a dau lkci ba ya fito rike da makullin motar, yana kallonta ya mika mata, ta hade rai tace "Meye kake mika min makulli cewa nayi ajiye ni xaka je kayi in amso sako ko kai kurma ne" Ya ajiye makullin saman matakalan chalet din yace "Toh baxan je ba, wanda ya daukeni aikin ma ya daga min kafan aiki yau...." Ya juya xai koma cikin parlon yace "Shi saurayin naki ya kai ki ki amso sakon...." Kasa cewa komai Nihad tayi ta bi sa da kallo, ta fi minti daya tsaye a wajen kafin ta juya ta koma gun Aliyu rai a bace.... Murmushi Aliyu yayi bayan ta sanar masa yanda suka yi da Drivern yace "Ohk, there is next time, xan kuma sauke masa girman kan da ke yaudaransa" Nihad tace "Toh wai dama talaka na irin wannan girman kan? Wllh sai ka xata fa gidan Ubansa ne nan din yanda yake abubuwansa" Aliyu dai bai ce komai ba, but all his thought is with the driver, he seriously want them to meet. Sai kusan karfe biyar Aliyu ya bar gidan tare da Mujahid bayan sun shiga sun ma Mumy da Umma sallama, Dollar dari biyu ya ba Nihad, yana tafiya dakin Umma ta fara shiga ta nuna mata kudin, Umma ta ja tsaki tace "Meye haka, ko dubu dari da hamsin bai kai ba, amma ya bani kunya duk wannan girke girken da ya kwasa?" Nihad tace "Umma fa a ko da yaushe cikin yi min kyauta yake, wannan ma cewa yayi inje saloon inyi gyaran gashi da shi fa" Umma tace "Toh Allah na tuba ina laifin ya baki dubu dari biyu da hamsin ma, duk kudin ubansa sannan kuma shi ma yace min yana business nasan baxai wuce exportation and Importation yake ba" Nihad bata kuma cewa komai ba, ta bude karamin jakarta dake hannunta ta saka kudin. Bayan magrib Khalil da Aminu na xaune kofar gida Aminu sai basa labarin samarin Nihad yake da irin shigar da suka yi, Khalil dai yana ta sauraronsa amma ba kallonsa yake ba, Aminu yace "Ina gaya maka wllh turarensu har bakin titi, kai kaga wani rantsattsen takalman da suka saka kuwa, kana ganin yanda suke tafiya kasan 'ya yan wasu shegu ne a kasar nan, wato barayin kasar nan" sai a nan Khalil ya daga kai da sauri yana kallonsa, Aminu ya kwashe da dariya yace "Allah kuwa, barayin gwamnati kenan" Motar da ke tahowa yasa Aminu yayi shiru suna kallon motar gaba daya don ta hasko su, Khalil ya mike kamar xai shiga gate, sai kuma aka yi kasa da fitilar motar....


07087865788✍🏻

Mu hadu after EID in sha Allah, sannan duk ku bi gidan yan uwa da abokan arziki aje yawon sallah a samo kudin littafin Nihad, don kuwa bayan EID sae dai in baku last free page inyi mursisi in koma gefe inyi shiru abu na, idan kuma an tattala kudin yawon sallah an xo an biya littafin Nihad ba wani xancen yin shiru daurawa kawai xa mu yi abun mu, idan Allah ya ta6a xuciyata ma har page biyu sae mu dinga yi...... 😁😜 Amma fa sai na ga kudi kaca kaca🙄


Allah Allah nake in gano wanda Abba ya aura ma Nihad da ja'irar ta suma amma abun ya ci tura jama'a, to ko dai Aminu ne don shi dama yace zai iya maneji da ita idan aka hadasa da kudi😯


*Shin kina buqatar kayan gyara Wanda zai yi amfani dasu Dan samu nutsuwar ki ke da oga??*

*To maza Garzaya wurin @Kayanmatan_zuru domin samun mini package me kunshe da maganin sanyi, maganin niima, maganin Karin dandano, maganin matsi, maganin Kara kuzari Akan farashi kalilan.....*

_Bugu da Kari akwai kyauta a cikin ko wani package..... Ku tuntube ta a Instagram_ @Kayanmatan_zuru
Ko whatsapp👇🏻

Wa.me/+2348033308307


💖💖 *NIHAAD* 💖💖





By _Khaleesat Haiydar_✍🏻





Aminu ya kalli Khalil yace "Ni wallahi ca nake saurayin nata ne ya dawo da daddaren nan kuma, kasan fa sai ya iya xuwa ya dauketa su tafi babu wanda xai sani banda ni da nake bakin gate din nan" Khalil yace "Saurayin wa?" Aminu bai kai ga basa amsa ba aka bude Driver seat, Hamid ne ya sauko tare da abokinsa Mujahid, a tare suka nufo gate din, tuni Aminu ya dinga jera ma Hamid gaisuwa uwa maroki, Hamid ya amsa yana kallon Khalil, sai kuma ya mika masa hannu, Khalil ya kai nasa hannun suka gaisa, Mujahid dai sai kallon Khalil yake, kauda kai khalil yayi ya fara tafiya xuwa gun mai gadin daya gidan dake kusa da su, Bayan sun shiga gate Mujahid na kallon Hamid yace "Waye wannan gayen?" Hamid yace "I don't know, ni ma yau na fara ganinsa, probably gidansu na nan layin" Mujahid yace "No, he looks a bit familiar, amma gaba daya na mance inda na san shi..." Hamid yace "Wait" Juyawa yayi ya koma bakin gate, Mujahid ya bi bayansa, Hamid na kallon Aminu yace "Aminu" Da sauri Aminu ya nufi gate din yace "Na'am ranka shi dade" Hamid yace "Wanene mutumin nan da ku ke tsaye da shi?" Aminu yace "Au.. ai sabon dreba ne, kasan Habibu ya bar gidan nan, Alhaji ya bude masa tafkeken shago ya koma can, shine ya kawo wannan, ai ya kwana biyu da fara aikin ma" Hamid dai sai kallon Aminu yake, Mujahid yace "Driver????" Aminu yace "Ehh dreban gidan ne" Mujahid ya kalli Hamid, Hamid ya juya ya koma cikin gidan, Mujahid ya bi bayansa yace "Seriously kamar na san shi a UK" Hamid yayi dariya yace "Kai dai kasan me kama da shi a UK" Mujahid yace "Toh amma kaman is very obvious, kawai dai i can't recall..." Parlon gidan suka shiga, Nihad na kwance parlor tana danna wayarta, tana ganinsu ta mike tayi wucewarta sama, Hamid ya bi ta da wani irin kallo, Mujahid ya saki baki shi ma yana kallonta, can yace "Yarinyar nan fa na feeling kanta da yawa" Hamid yace "A very spoilt Brat, right from when she is little bata da manners dama, unlike her half-sister Nihal..." Hamid ya xauna ya dau wayarsa ya hau kiran Farooq don dama wajensa suka zo. Washegari Monday Nihad ta gama shiryawa misalin karfe tara da rabi ta fito parlor, gaida Farooq da ya bi ta da kallo tayi, yace "Amma ba da wannan ɗan iskan mayafin xa ki fita ba Nihad?" Ta juyo tana kallonsa ta marairaice tace "Yanxu yaya me ya samu wannan mayafin? Dubi fa ya sauka har bayana fa" Yace "Wuce ki canxa" Muryar Umma suka ji tace "Ta canxa a saboda kai ke siya mata mayafan? Ko kuma sabida a jikinka ta yafa?" Ya juya ya kalli Umma, Umma tace "Sharesa kije kiyi breakfast din ki, ki kama gabanki" Dinning area ta nufa, Umma ta shigo parlon ta zauna, Farooq bai sake cewa komai ba, Nihad ta gama shan shayin da ta hada sannan ta mike, ta gefen ido farooq ke hararanta taki yarda ta kallesa ta nufi bangaren Mumy, a handle din kofar parlonta ta rataye mayafin sannan ta shiga parlon, zaunawa tayi saman kujera tana kallon Mumy tace "Ina kwana Mumy" Mumy tace "Wato sai kin gama duk abinda kike sannan xaki shigo ki gaisheni ko Nihad? Nihal bata ta6a kai wa karfe bakwai bata shigo nan ta gaisheni ba, amma ke sai sanda kika ga dama" Nihad tace "Toh Mumy ai saboda Nihal a nan bangaren take kwana shi yasa, ni kuma ai ba nan nake ba" Mumy tace "Toh yayi kyau ki ci gaba, nan gaba ma ki daina shigowa gaisheni kawai xai fi maki alkhairi" Nihad tayi shiru sai kuma tace "Kiyi hakuri" Mumy na kallon kayan jikinta tace "Wannan ɗan iskan dinkin kika yi da tsadadden atamfar nan kenan?" Nihad tace "Mumy gown ne fa" Sai kuma ta mike tace "Mumy na makara, yau muna da test" Mumy tace "Ki tabbatar Hijab xa ki sa Nihad" Tace "Toh, sai na dawo" Daga haka ta fita daga parlon, zare mayafinta tayi ta bar wajen da sauri sai da ta tafi dakinta ta dau jakarta sannan ta dawo parlor, lekan parlon ta dinga yi ta ga har lokacin Farooq na xaune, Umma ma na parlon, tana kallon Umma tace "Umma sai na dawo" Umma na Murmushi tace "Toh Allah ya tsare daughter" Ta saci kallon farooq tace "Yaya sai na dawo" Banza yayi da ita, bata ko kallesa ba ta fita, tana isa gate ko kallon Mai gadi da Khalil dake wajen bata yi ba tayi ficewarta daga gate din tana tafiya cike da isa, ta riga ta dau vow daga yanxu, da dai Khalil ya sake jan ta a mota gwara taje ta hau adaidaita, tayi canceling ta hau mota yayi driving dinta. Mai gadi na mata Allah ya tsare ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa masa, kamar yanda bata kalli Khalil ba shi ma haka ba kalli inda ta bi ba, Mai gadi yace "Ikon Allah, yau kuma da kafa xa a makarantar" Khalil yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Nihad na isa makaranta har wajen karfe sha daya basu da niyyar shiga lectures da su Husnah suna xauna Cafeteria suna ta hira abunsu, kaf Clique din sun canxa xuwa latest iphone da ya fito ko wata daya ba ayi ba amma banda Nihad, kuma kaf dinsu babu warce iyayenta suka siya ma, sun dai yi kame kamensu sun samu waya, Naf tace "Amma nayi mamaki kice ke baki da just 250k da xaki cika ki canxa waya, to shi wannan saurayin naki Aliyu meye amfaninsa?" Nihad tace "Aa ni dai baxan tambayesa ba, kuma dama ni bana tambayarsa komai" Sai kuma ta dau wayarta tayi dialing number Abba ta saka handsfree tayi masu alama su yi shiru, yana fara ring Abba ya daga yace "Hello dear" Shessheka ta fara yi tace "Abbaa" Daga daya bangaren Abba yace "What happened?? Me ya sameki?" A hankali tace "Abba ina shigowa makaranta xan sauka daga mota wayata ta fadi screen din ya fashe gaba daya" Abba yace "Subhanallah" Nihad tace "Yanxu ga shi wayar ya dauke" Abba yace "Hasbunallah, baya yi yanxu wayar kenan?" Tace "Ehh baya yi" Abba yace "Toh abinda xai faru idan kin koma gida ki ba wannan driver din ya je inda ake gyaran waya a gyara ko nawa ne ma sai ya kirani ya sanar min" A hankali Nihad tace "Toh" Abba yace "Shikenan, Allah ya tsare gaba" Nihad tace "Ameen, Nagode Abba, sai anjima" Daga haka ta katse wayar tana kallonsu Naf dake sauraron Abba gaba dayansu, suka kyalkyale da dariya suka ce "Gaskiya ne er daddy" Nihad tace "Toh amma me yasa xai hadani da wannan fitsararren yaron, this plan isn't going to work idan da shi fa" Husnah ta cije yatsa tace "Kashh, yau ga ranan Habibu, to wai shi wannan din dama har yanxu ba a koresa bane?" Nihad ta tabe baki tace "Toh mayen xai tafi ne? Wallahi duk abubuwan da nake masa ya ki tafiya sai ma gyara xama da yake yi a gidan yanda ku ka san gidan ubansa, yau ma fa wani gaye ne ya kawo ni schl don nace baxan sake shiga mota daya da drivern nan ba, ina tsaye busstop din anguwanmu sai ga benz din gayen, shine ya rage min hanya har cikin makarantar nan, amma da da adaidaita Sahu xa ku gan ni ae" Zully tace "Aa to baki yi masa yanda xai bar gidan bane, da nice tuni xan masa check out wllh, wannan ai karamin kwari ne" Nihad tace "Kai Zully wasu fa mayu ne, shi wannan a maitan ma yayi nisa, gaba daya na lura bai son barin gidan ne, tunda yana cin me kyau ya sha me kyau" Husnah tace "Kawai shiryawa xa mu yi mu je har gidan mu ci maki ubansa mu masa tijara" Nihad ta kyalkyale da dariya tace "Yauwa don Allah ku shirya ku zo dama 24/7 yana xaune bakin gate da mai gadi, amma fa you girls should dress decently kun san halin Mumy" Husnah tace "Wannan ba matsala bane duk xa mu sa Hijab a jaka, xuwa Thursday xa mu zo don ranan ne muke da time, gobe akwai club da xa mu je, Wednesday kuma xa mu je wani picnic, yauwa ki shirya mu je na ranan Wednesday din nan ba da daddare bane da yamma za ayi" Nihad tace "Ohk drop location" Throughout ranan babu wanda ya je kusa da dept balle ya shiga lectures, daga karshe ma fita suka yi xuwa wani babban eatry saurayin Zully xae siya masu abinci. Da yamma bayan la'asar Khalil na tsaye bakin gate yana sauraron Aminu dake basa labarin wani abokinsa da suka taso tare, lkci daya yayi mahaukacin kudi ya guji kowa daga karshe aka gano ashe kidnapping yake, Aminu dake ta kumfar baki yace "Har yau xancen da nake maka Inusa na dogon gida, yau kuma shekara uku kenan...." Bude gate aka yi duk suka juya, Inna ce ta shigo gidan da sallama tana rike da jakarta me kyau, Aminu ya mike da sauri yana washe hakora yace "Barka da zuwa Hajjaju" Inna ta ɗan kalli Khalil ta tsaya daga bakin gate din tace "Yauwa Aminu, yan gidan basa nan ne, naji ko ina shiru?" Khalil ya karasa ya gaisheta da ladabi ta kallesa tace "Auu, ni ai ban ganka ba Aminu kadai na hango, sannu ya kake" Khalil yace "Lafiya lau, Ya gida Hajiya?" Tace "Toh Alhamdulillah, yanxu Hamid ya ajiye ni a mota ko gama sauka ban yi ba ya juya yayi wucewarsa, gashi a can bakin titi in gaya maka naga wani apple me kyau ana siyarwa amma ya ki tsayawa in taya balle in siya, mun baro wajen can farkon shigowa anguwar nan wallahi" Khalil yace "Toh bari a dubo maki" Inna tace "Yauwa maza kaje kaji nawa nawa ne ka dawo ka gaya min" Fita gate din yayi, Inna ta bi sa da kallo, sai kuma tayi kasa da murya tace "Wai dama har yanzu basamuden nan na gidan nan Aminu?" Aminu na danne dariyarsa yace "Yana nan Hajiya" Inna tace "Toh saboda me? Shi Ibrahim din ne ya bar sa ya ci gaba da zama a gidan ko ko? Yau naga fitina" Aminu yace "Ae ba shi da matsala fa Hajiya, kowa a gidan ya shaida, kullum nan muke yini tare da shi" Inna tace "Aa rufe min baki Aminu, wllh in nice a gidan nan da ido daya zan dinga bacci" Tayi kasa da murya tace "Irinsu ne fa ke aikata mugayen abubuwa a duniya yanxu Aminu, ko kai baka ga siffarsa ba, wannan idan cacan baki ya hadaka da shi sai dai ya daga ka ya nana shege da kasa, to bai cuceka ba? Da nayi niyyar kwana amma gaskiya baxan iya ba da wannan mutumi a gidan nan, ina dalili" Dariya kawai Aminu yake, Inna tace "Bari in shiga mu gaisa da su kawai inyi fitowata in wuce" Daga haka ta wuce cikin gidan, tana zaune parlor da Mumy dake ta sauraronta Khalil yayi sallama bakin kofar, Inna tayi kasa da murya tace "Kaddai shi ne? Har nan ku ke bari ya xo maku??" Mikewa Mumy tayi ta nufi kofa, Khalil ya gaisheta da ladabi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhamdulillah" ledan hannunsa ya mika mata yace "Sakon Hajiya ne" Mumy ta amsa ta juya ta koma cikin parlon, inna ta hangame baki ganin leda shake da manyan apples tace "Meye wanan din? a ina naga kudin biyan wannan apple cike a leda, amma dai wawa ne wannan yaron, maza ciro kwara biyu ga dari biyu ki basa, sauran kuma ya mayar yace ance baxa a siya ba" Mumy na kallon Inna tace "Wai da na nawa kika ce ya siyo inna?" Inna tace "Aa ni ban aikesa ya siyo ba, kawai cewa nayi yaje ya tambayo nawa nawa ne, ni ban aikesa ya kwaso min ba wallahi" Mumy tace "Atoh ina amfanin mayar da abinda aka riga aka karbo Inna" ko rufe baki Inna bata jira Mumy tayi ba ta mike ta fixge ledan tace "Ai ba sata nake yi ba da xan siye duk apple din nan, kuma 'ya yana ba kudin banxa suke samu ba" Tana gama fadin haka ta fita waje da sauri, can bakin gate ta hango khalil a zaune tace "Yau naga gantalallen mutumi, wa ya bamu kudin siyan wannan uban apple din, ko don ya ga makeken gida ya zata sata ake yi" Tana isa kusa da su tayi kasa da murya tace "Ɗan nan cewa nayi ka tambayo nawa nawa ne, bar ganina haka, wllh rufin asirin Allah kawai nake takama da shi, bani da komai, maza ka maida masu kace biyu aka aiko ka kaji" Khalil yace "Aa Hajiya na siya maki ne kawai ki ci" Inna tace "Ka siya min? Ko dai lemo ka kwaso min?" Tana fadin haka ta kara bude ledan da sauri tana lekan ciki, ai ko taga apple ne ya fi goma, Inna ta gwalo ido tace "Albashin naka ka kwashe ka siyo min apple din?" Khalil yayi murmushi kawai, Inna ta rike ha6a tace "Kaii amma wallahi nagode, Allah yayi maka albarka, ko jikokina babu wanda ya ta6a min haka cikinsu, dari uku uku fa ake siyar da duk guda daya" Shi dai khalil murmushi kawai yake, Tace "Amshi ledan mu shiga Maryam ta maka godiya" Da sauri yace "Aa Hajiya" Inna tace "Amsa kawai

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment