Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki kamar nasa, ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second Nihad sai Umma, gaba daya ta dau karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me Nihal dinta xata yi da shi, duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows almost everything that's happening in the world wato he is current, suna dadewa sosai suna hira.... Sai kuma Hajiya Inna da takanas sai ta aiki dreban gidansu Hamid ya zo ya kira mata khalil xata aikesa don hankalinta yafi kwanciya ta basa dukiyarta a kan yaran gidan, kuma aiken baya wuce na dari ko dari biyu. Tun da Nihad ta shiga bangaren Mumy bayan ta fito daga bangaren Umma Mumy ke kallonta, ita dai tana xaune tana ta danna waya, Mumy tace "Wani mai kike shafawa Nihad?" Nihad ta daga kai tace "Mumy cream din Aunty Kamila ne tace in dinga shafawa" Mumy bata ce komai ba, bayan few seconds tace "Ina sauran kayanki?" Nihad tace "Mumy Aunty Kamila tace in bar su a can gidanta" Mumy tace "To tashi driver ya kai ki ki kwaso yanxu" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni fa ba abinda nake bukata a cikin kayan" Tsawa Mumy tayi mata tace "Baxa ki tashi ba" Tashi Nihad tayi kamar xata yi kuka, sai kuma tace "Toh Ai Aunty Kamilan na nan ki bari idan ta koma gida Mumy" Mumy tace "Ba dai gobe za ku fara lectures ba?" Nihad ta gyada mata kai a hankali, Mumy tace "Toh dama ki tabbatar baki dawo gidan nan ba tare da akwatunan ki ba" Mumy na fadin haka ta wuce dakinta, Nihad ta turo baki ta mike ta fice daga parlon, ita har ta mance yaushe rabon a harareta balle a mata fada sai yau... Washegari bayan ta shirya xuwa makaranta sai da Mumy ta kara jaddada mata kwaso akwatunan ta, har da guntun hawayenta, bayan ta fito compound ta ji ranta ya kara baci da ta tuna cewar shegen mutumin nan ne har yanxu Driver din gidan, kuma ita wllh baxata wani je ta hau adaidaita Sahu ba, tana isa gate suka hada ido da shi don kallon sama har kasa yake mata, wani matsiyacin kallo tayi masa tace "Da bashi ne kake kallona haka?" Aminu dai sai gwaggwale ido yake, Ta wani ja tsaki ta ma gwammace taje ta hau adaidaitan sbda ganinsa kadai na kona mata rai, ficewarta tayi daga gate Aminu yace "Ohh fitina ta dawo ni Aminu, wllh har na manta da ita a duniyar nan" Khalil dai bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da komowar Nihad gida tana kwance bedroom din Umma tana bata labarin yanda suka yi da Aliyu jiya da daddare, Umma dake xaune gefen gadon ita ma ta mike da sauri tace "Kice wllh" Nihad na Murmushi tace "Wallahi Umma" Wani guda Umma ta saki tace "Alhamdulillah, Allah na gode maka... Yaushe yace xa su xo?" Nihad tace "Nan da sati biyu" Umma tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, amma in ji baki gaya ma kowa ba?" Nihad tace "Aa ke kadai da Husnah na fada ma" Umma tace "Kin ji ki, wacece kuma Husnah, meye na gaya mata xa a kawo kudin ki? Duniyar nan da ta lalace yanxu ai kowa boye kansa yake, kar ki sake gaya ma kowa" Nihad tace "Har Mumy?" Nihad tace "Aa ba dai kin gaya min ba ai shkkn, ni xan mata magana sannan inyi ma Abbanku magana, amma sai xuwa next week" Nihad tace "Toh Umma" Wani gudar Umma ta kuma saki tace "Allah nagode maka diyata xata xama surkar Janar jikamshi" Dariya kawai Nihad tayi, Umma tace "Toh sai ki kula ki kama kanki kar ki sake kula kowa tunda dai kina da tsayayye yanxu" Nihad tace "Toh, amma Umma yana wani ce min xai rabani da su Husnah" Umma tace "Ahhh!!! shi kuma ya haka??" Nihad tace "Wallahi, kuma ni banga abinda xai sa ya rabani da su ba" Umma tace "Toh ke dai kar ki musa masa ku samu matsala, kiyi ta bin sa duk abinda yace kice to, su kuma ko a hankali ai xa a rabu, ke da kasar waje xa ku xauna? Ko ba haka ba" Nihad tace "Haka yace min" Umma tace "Toh kinga, su Husnah da ba kasar wajen xa su bi ki ba" Nihad tace "Ai shine" Umma tace "Kai amma nayi farin ciki da wannan labarin Nihad, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka" Nihad tace "Ameen, Umma bari in dauko wayana" Umma tace "Toh je ki dauko" Daga haka ta fita daga dakin. Ko da wasa Nihad bata sanar ma Mumy ba, tana ta sabgar gabanta throughout the week, kuma har tambayarta Aliyun yayi ko ta gaya ma Mumy tace masa eh. Duk da warning din da Umma tayi ma Nihad na kan cewa kar ta sake gaya ma kowa Aliyu xai turo sai da ta gaya ma Farooq, kamar yanda take favourite din Abbanta haka take favourite din Farooq a gidan, a WhatsApp suke chatting ta gaya masa sai ga shi ya sauka ya kirata, tana dagawa yace "Are you serious?" Tace "Ehh ya farooq" Yace "Tohh maa sha Allah, Amma Abba bai sanar min ba" Nihad ta zaro ido tace "Yaya Umma tace xata gaya masa" Farooq yace "Ohk, toh Allah ya kai mu next week din, though xan shigo kano jibi" Tace "Toh Allah ya kai mu" Sallama yayi mata ya katse wayar, Tana komawa saman chatting taga message din Nihal tana congratulating dinta, wato har Umma ta gaya mata, murmushi Nihad tayi tace "Thanks twinny" Washegari da Nihad ta fito xata school khalil ya bi ta da kallo disgustingly as usual, sarai jiya Nihal ta gaya masa xa a kawo kudinta next week ta kuma gaya masa daga familyn da xa a kawo kudin, and he really pity the well reputable family, da shi kansa wanda xai aureta din, ganin irin kallon da yake mata ta tsaya tana kallonsa tace "Wai kai Allah ya tsine maka ne da xaka dinga min wani irin kallo idan kaga na fito? Ko da wani abu da muka hada ne ban sani ba? Toh wllh wllh wllh duk ranan da na sake fitowa ka min kallon walakanci Allah sai na gaura maka mari, kaji har na rantse" Khalil na kallonta yace "Ki mari wa?" Cike da rashin kunya tace "In mareka nace, ko uban waye kai da kake tunanin baxan iya marinka ba? Ni fa wallahi bayan na bar gidan nan na mance an halicce wani mutum me kama da kai a duniya? Toh akan me daga dawowa ta xaka dinga bi na da kallon raini?" Khalil bai ce mata komai ba cause the sight of her is making him feel feverish, ga wani tafarfasa da zuciyarsa yake, jin bai ce mata komai ba ta ja wani tsaki tace "Banza kawai" Daga haka ta fice daga gidan, Aminu dake lekosu ta dakinsa ya fito yace "kaii, Allah ya wadaran wannan yarinya"

Ana saura kwana hudu su Aliyu xa su kawo kudi, Nihad na bacci da rana Kasancewar ranan asabar ce babu lectures wayarta ya fara vibrate, bude ido tayi don Aliyu yace xai kirata tana jawo wayar taga wata Coursemate dinta Sajida da ba wani shiri suke ba ce ke kiranta, da kamar baxata daga ba sai kuma ta daga ta kai kunne, Sajidah tace "Nihad what is this i am seeing on social media?" Nihad ta bude ido tace "Kamar me?" Sajidah tace "Hau WhatsApp" Daga haka ta katse wayar, sai ga kiran wata secondary school mate dinta Hafsah, tana ta kallon kiran sai kuma ta daga, daga daya bangaren Hafsah tace "Nihad what's happening?" Nihad ta mike xaune tace "Ban gane ba?" Hafsah tace "Ki hau WhatsApp" Nihad na kokarin shiga WhatsApp sai ga kiran wata warce suka yi islamiyya tare, kawai haka nan taji gabanta ya fadi, ta dai daga kiran, Badiyya tace "Nihad garin yaya haka don girman Allah??" Hankali tashe Nihad tace "Wai me ke faruwa?" Badiyya tace "Ki kunna data" Nan Nihad taji jikinta ya fara rawa, wani kiran ne ya shigo taki dagawa tayi rejecting ta bude data ta hau WhatsApp din da sauri, messages ta gani rututu na shigo mata, kawai ta bude wanda hannunta ya kai, Wata school mate dinta ce ta turo mata video tana tambayar "what is this Nihad??" Hannun Nihad na rawa ta bude video din, kanta ta gani with just skimpy undies a saman gado ba kuma bacci take ba, sai kuma taga ta mike tsaye turning all over jefar da wayar tayi jikinta na rawa tana zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai kuma ta saki wani kara ta sauka daga kan gadon ta durkusa kasa, ringing kawai wayarta ke yi amma ta kasa motsawa daga inda take, bude kofar dakinta aka yi ta daga kai da sauri, Umma ta shigo tana zaro ido tace "Nihad me ke faruwa a social media yanxu Nihal ta kirani tana kuka, kuma wai ta kiraki bakya dagawa" Nihad ta kasa cewa komai, bata ta6a zama soo weak all her life ba kamar wannan moment din, ji take kamar komai na jikinta ma ya daina aiki, wayar Umma ne ya fara ring ta daga da sauri, Nihal na shessheka tace "Umma ki hau WhatsApp na tura maki" Umma tace "Tohh" Da sauri Umma ta hau WhatsApp ta shiga chat dinta da Nihal ta bude video din, salati ta saki bayan ta gama kallon video din har karshe ta jefar da wayarta kan gado tace "Nihaddd????" Dai dai da second daya wayar Nihad bai samu breathing space ba, kiran su Husnah ne, Naf, Zully, infact calls upon calls kawai amma ta kasa kwakkwaran motsi inda take a durkushe balle ta daga wani waya, sai rufe ido take tana budewa kamar dai warce ke mafarki tana son ta farka, Umma na tafe hannu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace ni Sumayya, Nihad wa ya maki haka? Garin yaya haka Nihad?" Bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo da tashin hankali kwance fuskarta, Umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah mun gode maka ni Sumayya, me xa mu gani haka Nihad" muryan Mumy na rawa tace "Nihad??" Kawai sai ga hawaye na xuba idonta tana girgiza kai, Wannan ne yasa Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace" Kwalban turare da Mumy ta gani gaban mirror din dakin ta figa tayi kanta amma tuni Nihad ta shige bandaki ta sa makulli, Umma kuma ta rirrike Mumy tana kuka tace "Aa Maryam ki kai zuciyarki nesa kiyi ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un, nima shi nake yi" A haka ta ja mumy dake kukan bakin ciki da takaici suka fita daga dakin.
kafin dare kai ka ce mutuwa aka yi a gidan, gaba daya iyalan gidan Alhaji Abubakar sun iso gidan Abba, makusantan Mumy duk sun xo gidan, Umma ma yan uwanta da kawayenta duk suna gidan, Aminu sai bin duk wanda ya shigo yake da kallo cike da mamaki don ba ace masu kowa ya mutu a cikin gidan ba gashi khalil da yake ma gulma baya nan tun rana ya fita, kowa kuma ya shigo babu walwala yake nufar entrance din parlor, all the way from Abuja haka Farooq ya biyo flight ya dawo, Usman ma daga kaduna haka ya taho... Tun faruwan abun nan Umma ke kuka non stop, handkici hudu duk sun yi jagab a hannunta, Mumy kuwa in ka ganta sai ka tausaya mata she is so heartbroken, banda kanninta mata biyu da Yaya farooq da suka jibgi Nihad son ransu babu wanda yayi attempting ta6a ta ko ce mata komai a gidan...... Tashin hankalin Nihad bai linku ba sai da taga alamar Aliyu yayi blocking dinta ta ko ina, WhatsApp, IG, Phone call, Twitter, infact all, kawai sai take fatan Allah ya dau ranta ta huta kawai, gashi har lkcn ta rasa a ina aka mata wannan video din idonta biyu ba bacci take ba.....


*Ci gaban labari*

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take yashe da kallo, tsakiyar parlor ne kuma a kasan Carpet, gashi babu kowa parlon, everywhere looks strange to her, da sauri ta mike xaune as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar wani daki ta juya suka yi ido hudu da shi, sai da numfashinta ya dauke na few seconds da kyar ta jawo numfashin, lkci daya komai ya dawo mata ta kurma wani uban ihu jikinta na rawa tana kallonsa, sai kuma ta mike a guje tayi hanyar kitchen kamar mahaukaciya....




Nan na kawo karshen free pages, sai mu hadu a payment group.

Domin samun ci gaban littafin *Nihaad* it is only 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

And u show ur evidence via👇🏻
07087865788
Thank you as u patronize and i am assuring u that Nihad will be counted among my best In sha Allahđź’–


At first tsayawa yayi kamar bazai bi ta ba amma ganin ta kulle kofar kitchen din yayi saurin bin bayanta, Tsaye ya ganta ta dau table knife tana kuka sosai facing the knife towards her stomach, ya kalleta daga sama har kasa, sae kuma ya shiga cikin kitchen din ya dau asalin wuka ya karasa har gabanta ya mika mata yace "In da gaske kike" runtse ido tayi tana kuka iya karfinta, ya kamo hannunta ya saka wukar a ciki sannan ya koma bakin kofa ya jingina da wall din wajen ya rungume hannunsa yana kallonta da wani scorned expression, ta bude ido a hankali ta jefar da wukar ta sulale kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wayyo na shiga uku na lalace" sai kuma ta daura hannu a ka ta kurma uban ihu tana kallonsa, juyawa yayi ya bata waje, Ko sanda aka yi leaking Video dinta bata tunanin tashin hankalinta ya kai wanda take ciki yanxu, she is still yet to believe who she is seeing, wani ihun tashin hankali ta kuma kurmawa lkci daya kuma tayi shiru, to ko dai aiko sa aka yi gidan, tunanin hakan ya sa ta hau share idonta gabanta na bugawa da sauri, lkci daya tayi assuring kanta kawai aikosa aka yi gidan shine ya shigo masu har ciki, da kyar ta mike tsaye kamar me tsoron taka kasa ta karasa kofar kitchen din ta leko parlon a hankali with throbbing heart, zaune ta gansa saman kujera, suna hada ido ta wani hade rai har sannan gabanta na faduwa tayi karfin halin cewa "Malam idan aikoka aka yi sai ka shigo ma mutane har cikin nan? Wannan wani irin samun waje ne? Duk tsakar gida bai isheka ba sai ka shigo har nan" Kallonta kawai yake da wani stern look a fuskarsa, ta wani kara shan kunu tace "ko shi mai gidan ne ya baka damar shigo mana har cikin nan?" Ba abinda yace mata still, kuma babu alamar xai ce mata komai sai ma dauke idonsa da yayi, ta dake ta fito daga kitchen din gaba daya, tace "Wai baka jin ina maka magana ne ko nan din ma rashin kunyan xaka min?" Yace "Ok" Yana fadin haka ya mike ya juya yayi hanyar kofar fita daga parlon, wani irin kwanciya hankalinta yayi, taji ta samu relieve da nutsuwa, sulalewa kan kujera tayi ta jinginar da kanta da kujerar tare da sauke wani dogon ajiyar xuciya, haba ita dama ta san aikosa gidan aka yi shine xai shigo ma mutane har parlor saboda samun waje, shi kam yana fita ya kulle kofar parlon, Nihad ta share hawayen idonta a hankali tana tunanin to ina wanda aka aura mata din, har yanxu fa bata gansa ba, mikewa tayi ta nufi hanyar dakuna ta bude wani daki a hankali ta leka ciki taga babu komai dakin banda katifa, ta kulle ta sake bude wani taga shi ma katifar ce kawai, toh where is the so called husband, a hankali ta juya ta koma dakin da ta kwana ta xauna gefen gado, she is just imagining ace abinda tayi tunani daxu a kitchen gaskiya ne ai da kawai da gaske kashe kan nata xata yi kowa ma ya huta, but why will she even think that way at the first place, it is something that is neva and neva going to happen, agogon dake dakin ta kalla taga karfe goma sha daya saura, har lokacin bata ji tana jin yunwa ba, ita ta ma mance rabonta da cin abinci a cikinta, tana ta xaune dakin with different thought and imagination a ranta, can kuma ta mike duk jiki ba kwari tana tafiya a hankali ta koma parlor, windown dake kusa da kofar parlon ta tafi tana leka compound din, karamin compound ne da xai iya cin mota uku, ga mamakinta sai ta gansa xaune kan wani dakali a tsakar gidan ya rike kansa, wani faduwar gaba taji ya dirar mata, but seriously what is this man doing in this house for God sake, me yake har yanxu bai tafi ba, to ko dai mai gidan ne yace ya jirasa, this time around ta ma rasa wani takamaiman tunanin xata yi, duk sai ta birkice taji jikinta na rawa.... amma taki barin ƙwaƙwalwarta ya fassara mata abinda xuciyarta ke raya mata a lokacin, noooo it can't and will never be, tasan aikosa gidan kawai aka yi wallahi...... _Har a lokacin da ya gama hada takalman idon Abba na kansa, ganin xai fita parlon Abba yace "Ibrahim" Juyowa yayi yana kallon Abba, Abba ya nuna masa waje alamar ya xauna, komawa yayi ya xauna a hankali yana kallon Abban, Abba ya nisa yace "Kana da mata ne Ibrahim?" Khalil ya ɗan yi jim, amma ganin yanda Abba ya kafe sa da ido yayi saurin girgiza kai yace "Aa" Abba yayi kasa da murya yace "Ohk! Kana da wani dalilin da yasa baka yi auren ba har ynxu ko kawai ra'ayinka ne?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Dama da kaka aka ce xan yi auren idan Allah ya yarda" Abba yace "Kana da yarinyar da xaka aura ne Ibrahim?" Khalil ya dago ya kalli Abba dake ta kallonsa, sai kuma ya sake sunkuyar da kai a hankali yace "Aa ban samu ba dai tukun" Abba yayi shiru yana kallonsa as if thinking of where to start from, kallonsa kawai Abba yake daga sama har kasa duk da a xaune yake, kamar jikinsa ya basa Abban na kallonsa, sai duk ya tsargu, upside down ya juya palm dinsa a hankali not wanting to disclose the ring he is putting on, muryar Abba yaji yace "Ina son xan maka aure, xan kuma yi maka komai na auren sannan in baka gida ku xauna don na ya6a da nutsuwa da hankalin ka, bana jin ina da fargaba a kanka Ibrahim.... amma baxan yi hakan ba tare da yardar ka ba, da kuma yardar iyayenka, ina rokan wannan alfarman a wajenka Ibrahim" Khalil ya ji komai ya tsaya masa na kusan 10 seconds, lkci daya ya ji he is feeling heat all over, ya dai yi karfin halin dago kai ya kalli Abba, ganin yanda Abba ke kallonsa wanda in dai ka san Abba to xaka fahimci yana cikin damuwa wanda baya iya boyuwa ko min pretence din mutum, Khalil ya kirkiri fara'a a fuskarsa yace "Amma nagode sosai Alhaji, Allah ya kara girma, Allah ya saka da alkhairi, Nagode Alhaji" Abba yaji dadin reaction dinsa sosai cause he neva expect that, ya xata xai ce Aa ko kuma ya kawo wani excuse din, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Ameen Ibrahim, sai mu je can gun iyayenka yau mu yi magana da su ko? Su ma kuma ina fatan Allah xai sa su amince" Khalil ya hadiye abu da kyar yace "To ba damuwa Alhaji" Abba yace "Ka shirya nan da awa biyu mu tafi" Yace "Toh Alhaji" Abba yace "Nagode, amma sai dai baka tambayeni da warce xan hada ka ba" Khalil kallon Abba kawai yake, Abba yace "Yar cikina ce ba wata ba, saboda na yaba da komai naka ya sa nake son hada zuri'a da kai, ni kadai na yanke shawarar nan, kuma idan Allah ya yarda ban yi abun da xai cutar da kai a gaba ba Ibrahim, xaka yi farin ciki da hadin nan wataran, kawai tun yanxu ina neman alfarman ka koyi hakuri da ita don yarinya ce, kuma ita ma nasan watarana xata yi alfahari da xabin da nayi mata, fatana kawai Allah ya dora ni kan iyayenka" Khalil kam yayi nisa tunanin da yake don bai ma assimilating maganganun Abba, thousands of thought ne suka yi crossing mind dinsa a moment din nan, why him of all people, this means disappointing every of his relative, ko Abba bai fada masa wacece cikin yaran nasa ba ya san wacece, no!!! they are not and will neva be compatible, how will that even be? Muryar Abba ya tsinta a tsakiyar kansa ya a ce masa "Xaka iya tafiya, Allah yayi maka albarka" Ko Ameen din khalil bai iya ya amsa ba ya mike ya kwashi takalman Abba ya fita daga parlon, lkci daya yanayinsa ya sauya, wasu xufa suka hau keto masa, Yana fita compound ya nufi mai gadi ya dire masa takalman, Aminu ya mike da sauri yace "Lafiya na ganka a birkice haka? Me ya faru?" Khalil bai basa amsa ba ya nufi chalet, har idanuwansa sun kada .... Muryar Nihad ne ya dawo da Khalil duniyar tunanin da ya fada a tsakar gidan, ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta, a fusace tace "Wai baka ji abinda nake ce maka bane? Ka gaya min uban me ya kawo ka gidan nan?" Mikewa yayi yace "Ki kira babanki ki tambayesa, don shi ya kamata ya baki wannan amsan" Kasake tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo, severely yace "Sannan ina me baki shawaran kada ki sake daga min murya, ko kuma ki sake min wasu tambayoyi a gidan nan" Daga haka ya bar ta wajen tsaye ya koma cikin gidan walking fast, shikenan abinda take ta hana ƙwaƙwalwarta fassara mata ya tabbata, shikenan tsoronta da fargabanta ya tabbata, ta fashe da wani matsanancin kuka me ban tausayi ta sulale kasa ta daura hannu a ka ta kurma wani uban ihu tace "Na shiga uku na lalace, na banu na lalace, Me nayi ma Abbana xai min haka, me yasa Abbana xai min haka, me nayi ma yan gidanmu suka min haka, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka take sosai kamar ranta xai fita, ta fi minti ashirin xaune kasan interlock ta kasa tashi, she is more than shock, why her?? Ganin abun ma take kamar a mafarki, Nihad ta ci kuka ta gode Allah a zaune wajen, daga karshe ta kalli gate din gidan sai kuma ta mike da sauri ta nufi gate din amma tana kokarin budewa taji key aka sa, sulalewa wajen tayi tana ci gaba da kuka tana girgiza kanta, nan ma tafi min sha biyar, bata ta66atar da gaske an tsaneta a gidansu ba sai yanxu, sosai kanta ya fara mata ciwo, jin strength dinta ya fara karewa saboda kukan

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

1 year ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

1 year ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

1 year ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

6 months ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment