Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan gado gabanta na fad'uwa! gayyar 'kawayenta ne da suka zo suka sanya ta saki jikinta duk sunci kwalliya dai-dai gwargwado amma kuma kana ganinsu zaka gane akwai banbaci da 'yan cikin gari......Itama amaryar tana sanye da Swiss les purple anyi mata dinki stone work dake duk Hjy Fatsima ta bayar an dinka mata rabin kayan lefan dinki irin na 'yan birni Sayyada tayi kyau sosai ta gyara gashinta ya sauka gadon bayanta ta yafa dankwalin les din kana sanya takalmi plete da pose irin ta amare tayi kyau sosai sai dai kana kallonta zaka gane bambamci da ita da amaryar cikin gari sannan kuma akwai yarinta a tare da ita tunda yanzu ba tafi shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar ba........Jama'ar da suka cika gidan suka dinga janta da wasa tana dai daurewa tana gaishesu da abun yayi yawa kawai sai ta fashe da kuka ta rungume Baba Ladidi to itama Baban ashe 'boye kukan take ganin Sayyada nayi sai itama ta fara nata aka rasa me basu hakuri su hakura....Cikin wannan hali suka shigo gidan....Sadam! da Sulaiman kaya iri daya ne a jikinsu shadda ce galila dinkin babbar riga, Sulaiman fuskarsa a sake ya dinga gaisawa da jama'a shi kuwa gogan bai wani tsaya sosai ba a gurin tunda yaga abinda yake faruwa takaici yasa ya bude dakin da suke sauka ya shige har da turo kofa....Sulaiman kam wayarsa ya fito da ita ya dinga musu hoto yana dariya sai da yaga abun nasu yana nema yayi yawa sannan ya soma rarrashinsu da kyar suka daina kukan Jama'a kuwa sai dariya ake musu.

Yana daga kwance cikin dakin yana jiyo abinda yake faruwa juyi kawai yake yana mamakin zubar da girma irin na Sulaiman yana jiyo muryarsa yana tsokanar Sayyada ji yake kamar ya tashi yaje ya kwad'e shi don takaici......."Yaya Sulaiman bamu wayarka muyi selfie." muryarta ya jiyo cikin taratsi tana wannan maganar.....Kafin ya ankara yaji sulaiman din na cewa"Muje inyi muku keda 'kawayen naki." Firgigt! ya mi'ke zaune rigarsa da ya cire ya dauka ya sanya ko botiran bai mayar ba ya fito fit!!! ai tuni sun fice daga gidan.....Kai tsaye hanyar fita ya nufa, yana jin yan biki na fad'in"Ango kasha kamshi Allah ya sanya alkairi." bai ce komai ba yayi gaba........Can baban soro ya riskesu suna ta hauka shi kuma Sulaiman din sai biye musu yake yana dariya harda Mariya da take matar aure ta cire mayafi tana gantsare-gantsare wai ita dole hoto takeyi tana so tayi kyau........."Wannan wane irin hauka ne."!!!! muryarsa ta sanya suka juyo da sauri....yana tsaye da fuska a daure ya hard'e hannunwa a kirji yana watsa musu dan iskan kallo....Ya kalli Sulaiman cikin takaici yace."Wannan dai ba girman ka bane wallahi karfa ka manta da cewar wa d'an nan yaran ba irin 'yan matan cikin gari bane babu abinda suka sani bayan haka kuma akwai matata a cikinsu dai-dai kenan kazo kana daukarsu a hoto kana dariya."

Sulaiman yayi shiru ransa ya 'baci Sadam bashi da mutumci kuma baya jin kunyar ya tozarta shi a gaban ko waye.....Ba tare da yace masa komai ba ya wuce ya barsu a gurin.....Cikin tsawa! yace."Dallah! malamai ku wuce ku bawa mutane guri in banda hauka kawai kun tsaya gaban gardi irin wannan yana muku hoto wai ku kyawawa! mtsssw!!!! Su Mariya suka shige cikin gidan jikinsu duk a sanyaye Sayyada taji haushin wulakancin da yayiwa kawayenta sai ta dinga zumbura baki tana hararasa! tazo zata wuce yace."Dube ta sam bata dace da amarya ba."! "To ai kai ma baka dace da ango ba." Yace."Ke waye ya fad'a miki dama ni ango ne."!? Hararsa tayi yace."Ni kike harara mara kunya." Ta juya tare da fad'in"Duk inda ango yake yana farin ciki amma banda kai kowa yace ka sanja hali ka'ki ji! Ni ba zaka takura min da kawayena ba tunda ai ba da wayarka muke hotonba." Yace "Zo nan ki 'karbi wayar tawa kuje kuyi hoton." Cikin rashin wayo ta dawo shi kuma ya zura hannu kamar zai dauko wayar caraf! ya rike damtsenta! suka kalli juna ita dashi saurin dauke kansa yayi jin wani irin maganad'isu na fizgarsa zuwa gareta....Cikin kasalalliyar murya tace"Sakar min damtse."!
"Idan na'ki fa."? yafad'a cikin wani irin voice hucin numfashinsu ne yake had'uwa sai jikinta ya soma kyarma! shi kuma ya kurawa bakinta ido yana kallo a hankali yace." Su Sayyada amarya." Dauke kanta tayi tana shan kunu. Ya saki murmushi tare da cizan lipls dinsa na kasa yace."Ina fatan kin shirya kar'bar angon naki." Zumbura baki tayi tana dauke kai! murmushi yayi ya sakar mata hannu yace."Ki shirya da kyau! ni ba ragon namiji bane kuma bazan d'aga miki 'kafa ba."
Murguda baki tayi tace"Ai a shirye nake kuma waye ya fad'a maka nima raguwa ce."!? ido ya zare ya bude baki yana kallonta cike da mamaki! fari tayi masa da gadar-gadar din idanunta wanda yasa ya kusa faduwa a gurin ta juya ta shige cikin gidan......''Iyeee! ashe dai 'yan matan 'kauye suna da abun mamaki yanzu ya tabbatar da cewar Sayyada tasan aure tasan abinda akeyi a zaman aure, lallai akwai badakala kenan.....Shifa baya jin zai taki yarinyar a yanzu sai ta zama cikakkiyar mace a ganinsa a sannan ne zata iya d'auke masa dukanin bukatarsa a yanzu yana ganin idan ya kusanci yarinyar zai iya sanyawa ta had'u da yoyon fitsari tunda yawanci masu irin shekarunta ke haduwa da lalurar ya girmi Sayyada da kusan shekaru ashirin kuma karfinsu ba daya bane jarabarsu ba daya bace shiyasa kawai ya yanke shawarar bari ta kara shekuru sai suyi zaman aure mai tsafta


Sayyada na shiga cikin gidan suka ke'be da Mariya tace"Mariya kinji abinda yake cewa kuwa."? Mariya tace"Sai kin fad'a." "Humm! wai cewa yake yi dafatan na shirya masa kaina ni wallahi tsoro nake ji fa." Mariya ta dinga dariya tace"Ke mijikin wayayye ne don Allah ki saki jiki kusha soyayya." Sayyada tace"Mariya kenan baki ga abinda na gani bane shiyasa kike cewa in kwantar da hankalina." Sayyada duk sanda ta tuno da sandar girman Sadam! sai gabanta ya fad'i! domin ba zata ta'ba mance ranar bankadashi a bandaki ba."


To haka aka cigaba da gudanar da sha'anin biki da al'adar garin....Kwana uku bayan daurin aure suka shirya tafiya Sayyada ta cika gidan da kuka tana kukan rabuwa da Baba Ladi baba marka suma kukan suke da kyar dai aka taushe ta tayi shiru aka kaita can gidan iyayenta nan ma sai da tayi kuka sun jima da mahaifinta nayi mata nasiha hakanan maigari ma yayi mata nasiha da fatan zaman lafiya sannan sukayi sallama da juna.


*****

Biyu shaura na rana sun isa garin Kaduna garin gwamna Nan ma jama'a ce cike da gidan 'yan uwan hajiya Fatsima da makota da abokanan arziki sai hidima sukeyi Ango da Amarya na shigowa suka cika gidan da bud'a suna tsokanar Sadam! sai sannan taji muryarsa yana ramawa harda dariya....'yar autar su Hjy Fatsima ce mai suna Zuhura ita ta ja hannun Sayyada suka shige can bedroom dinta ta bude mata lullubin sayyada ta dinga jin kunya tana kauda kai sai da taga zuhuran ba wata babba bace sai ta saki jikinta suna hira haka 'yan uwan hjy fatsima suka dinga shigowa d'aya bayan d'aya suna ganinta tare da sanya albarka Sadam! na kowa ne shiyasa suke kaunar matarsa.

Aunty Luba ce ta shigo tana cire 'kafa d'akyar kana kallonta kasan ta kusa haihuwa tazo ta rungume Sayyada tana fad'in"Sannu da zuwa amaryamu." Sayyada na jin muryar aunt Luba ta bude mayafi rungumeta tayi tace"ashe baki haihu ba." Luba tace"Ina kan hanya Sayyada ku tayamu addua." Tace."Insha Allahu aunty.....Tare suka ci abinci suna hirar yaushe gamo sayyada ta sake da ita sosai dama tuntuni sun saba tunda Sulaiman na kaita *Dabi* tun kafin auransu sannan duk sanda yaje *Dabi* yana bata waya su gaisa shiyasa sukayi sabo da juna.
Anan ne take jin labarin tafiyar Sulaiman din bayan daurin aure tafiya ta kamashi 'kasar larabawa *Qatar* sati biyu zaiyi ya dawo....Sayyada tayi masa fatan alkairi da dawowa lafiya.

***

Sai misalin karfe takwas na dare sannan gidan ya samu sau'ki masu aiki sun gyara ko ina na gidan kowa kuma ya kama gabanshi sai aunty Luba wacce dama tun bayan tafiyar mijin nata ta dawo gidan sai ya dawo tukkuna Hajiya Fatsima tace"Da zuhura ta zauna ta d'ebe mata kewa tunda anyi hutu......Hajiya Fatsima ta shigo dakin ta tarar dasu suna hira ta kalli Luba tace"Ya kamata Sayyada ta shirya sai ku rakata dakin mijinta ko."? aunt luba tace"To Mamah! tana fita Luba tasa Sayyada tayi wanka tas ta gyara mata jikinta kana ta feshe mata jiki da turare masu sanyin kamshi ta bata wani material mai kyau da tsada tasa ta yafa mata mayafi kalar material din takalmi sabo ta sanya suka fito a tare Hajiya Fatsima tayi mata nasiha sosai dangane da zaman aure.........Kai tsaye bangaran Sadam! din suka nufa lokacin yana daf da fitowa sai sukayi kici'bus! fuska ya saki sosai suka gaisa da Luba duk fad'an da sukeyi da Sulaiman bai shafeta ba saboda yana ganin mutuncinta sosai matace mai hankali da aiki da iliminta yace."Da kin bari ma nazo na dauki amaryarta da kaina ai ba wani abun bane." Tace"Oho dai naji ai komai zaka fada sai dai ka fad'a ni bana kishi tunda dai nasan nice uwar gida." Yace."Ai kuwa yanzu na daina yayinki tunda na samu amarya." Dariya tayi tace"Ai dama wannan halinku ne." hanya ya basu suka shige yace."To ni dama fita zanyi amma ba zan dade ba." Hararasa tayi tace"Kana da amaryar zaka fita yawo ko aiki ne da kai ya kamata ka dauki Uziri." Yace."Karki damu yanzu zan dawo insha Allah....Gurin aiki zan nufa yanzu amma bazan wani dade ba tunda nasan akwai amarya ke dai kawai ki zauna kiyi min gadinta." Tace."Baka isa ba nima ka barni da kishin dake damuna." Dariya ya dinga 'kyakyatawa ya kama hanya ya fita....Sayyada ta dinga mamakinsa dama haka yake sai dariya yake har da kyakyawata lallai ma Yaya Sadam! ita sai yayi ta sha mata kunu yana mata tsaawa.
Aunty Luba ta d'an zauna mata amma da taga dare yayi sosai sai tayi mata sallama ta koma can sashen su Hajiya......Sayyada tayi tsuru kamar mayya motsi kadan ta duba agogo karfe goma sha biyu da rabi tayi bai shigo ba sai ta kwanta kan gadonsa tana kuka haka bacci ya dauketa bata tashi ba sai asubah!!! tana kokarin sauka daga gadon ne taji motsin shigowa cikin palon ta koma ta kwanta nan taji ya turo kofar dakin ya shigo ya jima tsaye a kanta yana kallo duk a tunaninsa bacci take yaje yana jan kafafunta" Taki bude ido mugun haushinsa takeji ta dauka zaiyi ta rawar kai a kanta kamar yanda angwaye keyi shi sai yayi wanka ma yayi ficewarsa saboda bata da matsayi a gurinsa.....Da ta gaji da jan kafar ta da yake sai ta fuzge da karfi ta jiyo muryarsa yana fadin"Tashi kiyi sallah." Toilet ya nufa ta bishi da harara! Taji ciwon abinda yayi mata ya nuna bai damu da ita ba shiyasa yaje ya kwana a waje....jin motsin bude kofa yasa ta dauke kanta da sauri ya fito ya sauya jallabiya duk tana kallonsa ya dauki carbi ya fita....Nan ta mike ta nufi bandakin domin daura alwala.







10/6/2020



*BINTA UMAR ABBALE*




_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a madadin dari uku na najeria.*_
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________
_*Na kusa gama free pegea duk me bukata sai ya turo kudin karatu*_
*Free Pege18*
Da sauri Captain Habu ya bar gurin, Captain Saleh yazo yazo ya tsaya kawai a kansa yana masa wani irin kallo yaso ace ha'kansa ya cimma ruwa yaso ace bukatarsa ta biya a kansa amma babu komai watarana ya tabbatar da cewar bukatarsa sai ta biya a kansa ya dauki alwashin sai ya salwantar da ransa mutukar suna aiki a guri guda.
Mota Captain Habu ya shigo da ita da sauri Captain Saleh ya sunkuya domin taimaka masa sai ya d'aga masa hannu goshinsa duk ya tsatstsafo da gumi hannunsa a kafadarsa ya rike gurin harbin jini kam duk ya jika masa jiki.....Captain Saleh ya matsa gefe guda yana kallo Captain Habu ya rirrikeshi ya kaishi mota, sannan suka tasa 'keyar d'an boko haram! din wanda suka rufe masa fuska da wani ba'kin abu suka daure duk hannayensa da ankwa....Gurin cika yayi da mutane 'yan jarida har sun hallara a gurin mutane sai dauka suke a wayoyinsu da kyar motar ta fita daga gurin.....Cikin brecck din akwai asibiti dake kula da sojoji da iyalinsu kai tsaye can aka nufa da Sadam! wanda tsabar dauriya tasa idanunsa ya kada yayi jawur jijiyar kansa duk ta tashi kana kallonsa a lokacin zaka fahimci yana jin jiki sosai....Lokaci guda likitoci suka rufu a kansa har sai da suka samu nasarar cire bulet! din sukayi aikin gurin yanda ya kamata kana sukayi masa allurar bacci domin ya samu hutu.

Rundinar sojoji ta Najeria tayi mutukar jin dadi da faruwar wannan al'amari tabbas sun dad'e suna so su kama koda d'aya ne daga cikin wad'anan mutane domin su kafa hojjoji kana kuma su tsaurara bunkice akansa domin ya sanar musu inda sauran 'yan uwansa suke.....Saboda haka hatta da mataimakin shugaban 'kasa sai da yazo ya duba Sadam! kuma ya jinjina masa a bisa namjin kokarin da yayi....Sannan ya sanar dashi sakon mai girma President yace."Yana gaishe shi da kyau kuma yana jinjina masa hakika ya cika gwarzon maza.......Wannan al'amari yayi masifar 'batawa 'yan adawa rai mussaman Captain Saleh wanda shine mutumin da ya rufe kwatar da silaf din duk dan kar ya samu hanyar fitowa, Sadam! na da ma'kiya a gurin aiki sosai da sosai don wasu ma basu zo duba shi ba sai kananun maganganu ne ke tashi.......A can 'bangaran gida kuma tun misalin karfe takwas na dare suke kiran wayar shi sai dai Captain Habu ya dauka yace."Baya kusa Hjy Fatsima data gaji sai tace Ya fada mata gaskiya idan wani abun ne ya faru Captain Habu ya boye mata....Tun sannan suka sha jinjin jikinsu Sayyada kuka ta hau yi! Hajiya Fatsima ke rarrashinta da ta kwantar da hankalinta babu abinda ya faru.....Alhaji Auwal na kasuwa labai ya riske shi cewar sojoji sunyi nasarar kama dan boko haram! cikin kasuwar bacci amma kuma daya daga cikinsu ya jikkata domin dan boko haram din yayi nasarar harbinsa a kafada.....Ba tsaya wasa ba ya nemi numbar d'an sa to shima dai captain habu ne ya dauka nan yake tambayarshi ya ake ciki Captain Habu yace babu wata matsala insha Allah ya nemi da ya bashi Sadam! din sai ya hau kame kame! kashe wayar kawai yayi ya nufi gida....Yana isa ya tarar dasu cikin tashin hankali da damuwa domin suna zaune suna kallon labarai tashar Bbc news suka nuna Sadam! din akwance kirjinsa daure da bandeji yana jawabi da yanda abun ya faru.........Duk suka tashi hankalinsu Sayyada sai kuka takeyi sai an kaita gurinsa, Sulaiman ne ke rarrashinsa idan ka ganshi sai ka dauka ya damu da al'amarin amma a cikin ransa dad'i yake ji sosai yaso Sadam din ya she'ke barzahu sai ya samu damar auran matarshi Sayyada.

Hajiya Fatsima ta sako hijab suka nufi barikin sojojin domin duba halin da d'ansu yake ciki.....Ganinsa zaune yana shan yoght sai hankalinsa ya kwanta Captain Habu ya gaisa dasu Hajiya Fatsima tace"Ka kyauta wato shine ka'ki yi min bayani abinda ya faru sai a tv na gani."

Yace."Mamah ai abun alkairi ake fad'a shiyasa ban sanar daku komai nasan da na fada miki a lokacin zakice zaku zo to ganinsa a wannan lokacin zai d'aga muku hankali shiyasa muka bari sai da aka gama komai tukkuna."

Alhaji Auwal yace."Alhamdullahi ai da sauki ma al'amarin Allah ya kare ku ya kare ya kuma baku nasara a duk inda zaku shiga." Captain Habu ya amsa da ameen kana ya fita ya barsu domin su gana.

Sayyada gefansa ta zauna tana ta kallon kirjinsa inda aka harbe shi tsigar jikinta sai tashi takeyi hawaye kuwa wannan na bin wannan...Sulaiman ya gyada kai ba tare da yace wa dan uwan nasa komai ba ya fice daga dakin ya tsani yaga Sayyada na kusantar inda Sadam! yake. Motarsa ya shiga ya bar barikin sojojin.....A nutse ya gaisa da iyayen nasa yana musu 'karin bayanin kan yanda al'amarin ya faru...Hajiya Fatsima sai da tayi kuka tace"Ni kuwa Da zaka bi shawara ta to da ka ajiye aikin nan Sadam! akwai had'ari a cikinsa." A take ya 'bata fuska yace."Mammah bana son kina irin wannan magana wallahi! tunda na fara wannan aiki bana fata in aje kuma wallahi wallahi wallahi bana yi domin kudi ko wata daukaka ko mukami inayi ne kawai saboda 'kasata Nejaria sannan inayi ne domin taimakon al'umma addua kawai nake bukata a gurunku." Tace"Shikkenan Sadam! Ubangiji Allah ya shige maka gaba Allah ya kare ku a duk inda kuke ya tsare gabanku da bayanku." Suka amsa da "ameen." dukaninsu.......To koda suka tashi tafiya Sayyada ta'ki binsu akayi akayi ta'ki sai ma ta haye kan gadon ta 'buya a bayansa .Alhji Awal yace."A kyaleta ta zauna Sadam! bai so haka saboda abokanan aikinsa na shigowa duba shi to dan ba yanda zaiyi yasa ya hakura suka tafi suka barta.


To a cikin mota iyayen maganar suke inda Hajiya Fatsima take cewa''Ni kuwa rashin jituwar Sadam da Sulaiman na bani tsoro Alhaji yara kamar ba 'yan uwa ba ka duba ka gani Sulaiman ne ya dace ya zauna yayi jinyar dan uwansa amma ka lura ko minti biyar baiyi ba ya fita kuma bai ce masa sannu ba wannan al'amari ya 'bata min rai kuma babu babban mai laifi sai Sulaiman din tunda dai shine babba."

Alhaji Auwal yana draving yace."Kin san Sulaiman akwai sabga mybe kiransa akayi a waya shiyasa kika ga ya fita bai zauna ba amma na tabbatar zai koma ya duba shi bana so ki sanya wani abu a cikin ranki."

Tace."Wallahi al'amarin ke bani mamaki shiyasa nake magana Allah ya dai-dai ta tsakaninsu." Ya amsa da ''ameeen ya rabbi."!

***

Kallonta yake itama tana kallonsa idanunta yayi fululu saboda kuka babu yabo babu fallasa yace."Ya kamata ki daina wannan kukan ya isa haka."

Ta goge hawayen fuska mirya a dashe tace."Tausayinka nakeji don girman Allah ka daina wannan aikin kaji."

Shan kunu yayi yace."Ke! bana son shirme! Wannan aikin idan kinga na bari to bana nuffashi."

Hawaye ya sake kwaryo mata, tausayi ta bashi ya sanya hannu yana goge mata hawayen fuska a daure yace."Idan baki daina min wannan kukan ba yanzu zansa Captain Habu ya mai dake gida."
Zum'bura baki tayi....Yace."Ni dai na fad'a miki." fuskarta ta hau gogewa da hannunta tana kallonsa shima yana kallonta zuwa yanzu ya gama fahimtar yana da babban matsayi a zuciyar yarinyar yana ganin tsananin sonsa da kaunarsa a cikin kwayar idonta.....Suna cikin wannan hali Captain habu ya shigo da take away a hannunsa, Sai yasa dariya yana fad'in"Kaga laila majnun ko."!! Sadam yayi saurin dauke kansa yana dan harararsa, Yana dariya ya zauna a wata kujera yace"Sayyada lallai kina son abokina da yawa nifa yau na dauka hawayenki ne zai kare." murmushi tayi ta sunkuyar da kanta kasa.

Yace."Ga abinci na kawo miki kici." Girgiza kai tayi alamun bata ci. Yace."Me yasa."? A hankali tace"Bana jin yunwa." Kai tsaye yace."Ban yarda ba dole kici wani abu idan kuma kin fiso angon naki ya baki a baki to." Tayi saurin kallonsa yana kwance idanunsa a rufe ya bude yana harar Captain habu din da jin abinda yace.....Captain habu ya mike yana fad'in"Bari in baku guri tun kafin in sha naushi." Dariya tayi tana kallon mutumin nata....Bayan fitar captain habu da minti biyar likita ya shigo da sauri ya kalle ta domin yaga yanayin da take ciki har yanzu hijab dinta na jikinta.....Ta gaishe da dector din shi kuma ya tambaye ta mai jiki tace da sauki....Ya hau duba jikin Sadam! suna hira sama-sama bayan ya bashi magani ya fita ya juyo yana kallonta da d'aurarriyar fuska yace."Kar wanda ya 'kara shigowa kika gaishe shi ranki sai ya 'baci!." Da mamaki ta kalleshi yace."Kinji abinda nace miki ko."? d'aga kanta tayi....Ya mai da idanunsa ya rufe yana jin wani irin kishi a cikin ransa ai dole ne ma ta bar asibitin nan,

Muryarta ya jiyo tana fad'in"Ka tashi kasha maganin to."! banza yayi mata tace"Kaji." ya bude idonsa yana kallonta sai ta sunkuyar da kanta...."Sayyada."! ya ambaci sunanta cikin wata iriyar murya.Ta kalleshi yace."Bana bukatar damuwa yanzu kuci abinci ki kwanta ok."

"Nifa bana ci."! Tafada duk ranta a 'bace! yace." Kanki kikayiwa ai." Dakin yayi shiru na tsawon minti goma ta mike ta shiga bandakin dake cikin dakin minti uku ta fito tazo ta ra'ba kusa dashi zata kwanta....."Ke! meye haka tashi ki koma kan kujerar can ki kwanta." Abinda ya fada yasa ta maka masa harara! ya kuma ganta ta gyara kwanciyarta a gefansa....."Wai kina so ki dauje min ciwo na ne? idan takura min Zakiyi zan fita in bar miki da'kin." Kuka tasa tana shashshake takaici ya isheshi ya mike zaune da kyar yana kallonta kudundune a cikin hijab tana kuka yace."Kiyi min shiru malama dukanki ko zaginki nayi da zaki cika min kunne da kuka mtswww!.

Rage sautin kukan tayi tana goge hawaye yace."Ki kwanta inda kike tunda kin nace! kar ki matso kusa dani balle ki sanya ni a wani hali." Ita dai bata ce masa komai ba ta kwanta......Cikin karfin hali ya mike yaje ya kulle dakin ya dawo ya kwanta minti goma bacci ya daukeshi.....Ta bude idonta tana kallonsa kauna da sonsa da tausayinsa na 'kara nunkuwa a cikin ranta.



Itace ra riga tashi taga gari har ya soma haske tana kallon agogo ya nuna mata lokaci karfe shida da kwata na safe da sauri ta sauka taje ta dauro alwala ta fito motsinta shine ya farkar dashi ya mike zaune alhamdullahi jikin da sauki ya mike ya nufi toilet din Alwala yayi ya fito ya tada sallah, kusa da ita........A hankali ta juya tace."Ina kwana ya jiki"? Ya amsa mata babu yabo babu fallasa, mikewa tayi ta zauna gefan gadon hijab din ta cire ya kalleta da d'aurarriyar fuska "Ki shirya idan anjima za'a mayar dake gida ko kuma idan su Mamah sunzo ki bisu."

"Saboda me."?tafad'a tana kallonsa....." Ke! ni nake magana kina tambayata." ! ya fada yana kwalalo mata manyan idanunsa....Ba taji tsoro ba sai ma zumbura baki da tayi...."Ko ba kyaji ne."!? banza tayi masa. Duk tausayin kanta ya cikata Yaya Sadam! baya sonta sai wulakantata yake sai idanunta suka soma kawo ruwa, Idanunsa a tsaye a kanta ya gani da sauri yace."Karki kuskura hawayen nan ya zubo." Ai ya 'bata bakinsa don tuntuni hawayen ya tsinke sai kawai ya saki baki yana kallonta Dr ne ya shigo tayi sauri ta 'boye fuskarta cikin hijab, Ganinsa kan dadduma yasa dr fad'in"Alhamdullahi Yalla'bai da alama ba zaka dade a kwance madam ta iya jinya." Hannu ya bashi suka gaisa dr ya duba jikin nasa kana ya bashi magani yana fad'in''Ni zan dinga baka magani da safe Madam kuma ta kula da kai da rana da dare ." Yace."Kai ma na huttashe ka ai ba yaro bane ni zan sha magani da kaina." Dr na dariya yace."A'a Madam ya fi kamata ta baka zakafi samun sauki da wuri." Murmushi kawai yayi dr yayi masa sallama ya fita.
Mi'kewa yayi ya isa gadon ya zauna yana kallon bayanta shiru babu wanda yayi magana ya sanya hannu yaja hijab din ta baya

Please Login or Register in order to submit comment