Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana buga kafafu tace"Ni wallahi sai nace ma ba zan bishi ba ai wallahi kun bani haushi." Baba Ladi ta rike 'kugu tana kallonta tace"To ko dukana zakiyi ne."!? Ni ba dukanki zanyi ba ni dai nace kawai ki daina min haka." Tace"Auwo! ai na dauka zaki gaura min mari ne saboda nace mijinki ya neme ki dama ai nasan duk laifin daga gurinki ne." Sayyada tace"Eh naji laifina ne ni dai ki daina yi min haka." Baba Ladi tace"Ai na daina uwata ki harhad'a kayanki ki fito ko tafi." Sayyada ta zumbura baki tana 'kunkuni Baba Ladi tace"Kyaji dashi kina so kina kaiwa kasuwa humm."!

Baba Ladi na fita Sayyada ta nemi guri ta kwanta tana tunanin abinda ya faru tsakaninta dashi jiya da daddare lumshe ido tayi ta takure jikinta guri guda ajiyar zuciya take saukewa jin wani irin shau'ki na fizgarta.

A hankali ya shigo dakin hannunsa duk a cikin aljuhu kallonta yake tana ta mutsu mutsu ga idonta a lumshe!! gyaran murya yayi tayi saurin bude idonta suka kalli juna lokaci guda ya fahimci halin da take ciki yarinyar fitinanniya ce kamarshi, Had'e fuska yayi kamar bashi ne mutumin da yake mata sambatu jiya ba yace."Ke! kina kwance baki shirya ba ko Baba bata fad'a miki bane."?

Mikewa tayi zaune tana daura dankwalinta tace"Ni bata fada min komai ba yace."Okey ni na fada miki ki shirya zamu wuce Kaduna yanzu."

Shiru tayi yace."Ko bakya ji ne?"!? "Ina ji." okey shine kikayi min shiru ni ne mahaukaci kenan."!? tayi kasa da kanta yace."Minti goma na baki ki fito ki same ni." Fita yayi bai saurari amsar da zata bashi ba.....Ta jima kafin ta mike ta dauko jakar data zo da ita ta gyara kayanta hijab ta zura ta fito tana zum'bure-zum'bure! Baba marka tace"Ai tuni ya fita yana can kofar su Amina kije ki same shi." Cikin zuciyarta tace'cm''Ni ba zanje kofar su Amina ba idan ya gama ya fito ya same ni." Hanyar fita ta nufa Baba Ladidi tace"To Allah ya jishshemu alkairi.'' Allah ya kiyaye hanya." Ciki-ciki ta amsa tana fita ta ganshi tsaye da Amina suna magana kici-kici tayi da fuskarta ta wuce su.... Amina tace"Sayyada a sauka lafiya a gaishe min da aunty Luba da mutan gida." Ko kallonta ba tayi ba ta fita ranta in yayi dubu ya 'baci tilas ta nuna masa 'bacin ranta dangane da tsayuwarsa da Amina.
7/21/20, 5:38 PM - Ummi Tandama: 27
Can inda yayi parking din motarshi ta nufa ta tsaya jikin motar tana jiran fitowarsa, ranta na masifar 'baci a duk lokacin da taga ya tsaya da Amina suna magana ta 'bangaranshi tasan babu wata matsala ta 'bangaran Aminar ne take zargin wani abu babu shakka har yanzu Amina bata daina son Yaya Sadam ba."

Cikin sassarfa ya 'karaso gurin ta dauke kanta tana kumburi yace."Ke! a maimakon ki bude motar ki shiga sai kiyi tsaye anan gurin saboda tallata kai."!

Ba tace masa komai ba ta bude motar ta shiga ta zauna...Ya bude boot ya saka akwatin kayanta kana ya zagayo ya bude motar ya shiga.....Bisilimillahi yayi ya kunna motar suka gangara kan hanya........Sai da suka hau kwalta sannan ta juyo ta kalleshi tayi bala'in had'e rai tace"Wai don Allah Yaya Sadam! meye had'inka da Amina ne."?

Ya san za'a rina dama wannan kumburin da take yi ya gane kona menene kishi ne da yarinyar ba na wasa ba 'bata fuska yayi yace."Ke! wannan wace iriyar magana ce kikeyi."?

Jikinta a d'an sanyaye tace"Naga kamar akwai wata ala'ka a tsakaninku shine nake son sani."

Yace."Wato ke kina kokwanto ne ko."!? Ta daga kai tana kallonsa.....Murmushi yayi yace."Kin manta da cewar Amina 'yar uwata ce kamar yanda kike 'yar uwata." Shiru tayi shaf ta manta da hakan tace"Ni fa ba wannan ala'kar nake nufi ba." Yace." Wace ala'ka kike nufi bayan wannan." Cikin rashin dubara tace"Sai naga kamar kuna soyayya ne." Dariya ta bashi yace."To idan ma soyayya muke akwai aibu a ciki ne ai ba laifi ba ne."

Gabanta ya fad'i tace"Yanzu kai zaka iya auran Amina." Yace."Me zai hana idan Allah ya kaddara hakan." Shiru tayi ranta yayi 'bakikirin.....Shi kuwa tukinsa yake hankali kwamce in banda abun Sayyada ina shi ina wani aure yanzu ita d'in ma bai samu nutsuwa da ita ba.


Tunda ya fad'i haka sai ta ci kunu ta dauke kanta tana kallon hanya shi kuma yana dan satar kallonta ta gefan ido mamakin yarinyar yake wai kishi takeyi ko da yake dole tayi kishinsa tunda tana sonsa.....cikin zuciyarsa yace"Idan miskilanci kike ji dashi na fiki yarinya....Bai kara tanka mata ba har suka isa kaduna Sayyada na nukufurci shi kuwa idan ba kiranshi akayi a wayarshi ba kajin muryarshi ya daina kallon inda take kwata kwata.


Lokacin da suka isa gidan aunty Luba na asibiti zata haihu babu kowa a gidan Sadam ya kira Mammah a waya ya sanar mata gasu sun sauka tace"Suma gasu nan zuwa yanzu aunty Luba ta haihu amma d'an babu rai! Sadam yaji wani iri a jikinsa sosai ya kwallafa rai kan dan da aunty Luba zata haifa yana da bala'in son yara Sayyada kuwa har kuka sai da tayi suka zauna jiki a sanyaye suna jiran dawowarsu.


Alhamdullahi Aunty Luba jikinta da sauki suka shigo gidan Mammah na taimaka mata Sulaiman na bayansu hannunsa rike da manyan ledoji fuskarsa babu wani alamun alhini da damuwa ya karaso palon kicin ya nufa ya aje ledojin hannunsa ya fito.

Sayyada ta rungume auny Luba tana mata ya jiki tausayinta takeji sosai tace"Wallahi aunty na tausaya miki Allah ya kawo mai albarka ke kuma Allah ya baki lafiya."

Aunty Luba ta share hawayen dake zubowa a fuskarta tace"Ameen sayyada nagode da addua....Shiru palon yayi kowa ranshi babu dad'i in ka cire Sulaiman da ya harde kafafunshi yana latsa waya tamkar bashi abun ya shafa ba.


Sadam! yasha jinin jikinsa ya dago kai yana kallon Mammah yace."Wai haihuwa tayi babu rai ko kuma bayan ta haihu d'an ya koma."!?

Mammah tace"A'a ai bata haifeshi da rai ba likitocin sunce ta dad'e tana nakud'a ne har d'an ya galabaita basu tafi asibiti ba shine yasha ruwan haihuwa ya mutu." Yanda take fadin maganar zaka tabbatar da cewar ranta babu dad'i!

Sadam! ya girgiza kai yana kallon Aunty Luba yace."Aunty Luba ya akayi kika bari haka ta faru haba tamkar ba wayayyiya ba kina ciwo ki kasa tafiya asibiti har sai da kika galabaita sannan gaskiya banji dadin wannan abu ba."

Aunty Luba tayi shiru kanta a 'kasa sai zubar da hawaye take....Tabbas Sulaiman ya cuce ta ta rasa d'anta dama tunda taga yana nuna halin ko in kula akan cikin tasan baya so itace take kid'anta tayi rawarta kan cikin banda shi.....Tun farkon dare take nakuda tayi tayi dashi ya tashi ya kaita asibiti yace shi bacci zaiyi haka tayi ta fama da ciwo har garin Allah ya waye koda gari ya waye Sulaiman baiyi yunkurin kaita asibiti ba sai da ya gama komai na rayuwarsa sannan ya dauketa ya kaita asibiti lokacin tayi masifar galabaita haka likitoci suka dinga fad'a.....Kuma saboda tsabar mugunta irin nashi Yace."Ba zata fad'awa kowa ba har sai da tashi wannan mugun yanayin da yasa ta rasa dan da tasha mutukar wahala a kansa Tabbas inda tasan Sulaiman bashi da kyawun hali babu abunda zai sanya ta aureshi.


Sadam! ma ya dan fuskanci wani a dangane da al'amarin tun farko Dan uwanshi ba mutum ne me son yara ba duka d'abi'unshi na nasara ne yanzu ya fahimci da saka hannunsa komai ya faru.....Ganin Aunty Luba na kuka ya sanya ya dinga rarrashinta shi kuwa Sulaiman din hankalinsa na kan waya charting yake da 'yan matansa....Sai da ya gama sannan yasa baki kamar gaske yake fad'in"Kiyi hakuri mana wanda ya baki ya amshi abinsa idan kin kwantar da hankalinki sai kiga kin samu wani."

Aunty Luba ta kalleshi da mamaki! wai shine yake wannan maganar shida farkon samun cikinta yace a zubar da ta'ki yarda shine ya sakar mata wahala wulakacin yau daban na gobe dabam gashinan sai da yayi sanadiyar da yasa d'an yazo babu rai amma saboda tsabar munafurci yake wannan maganar.........Sallamar 'yan uwanta ne ya katse musu hirar Sadam! ya nufi sashensa Sulaiman kuwa zama yayi suka gaggaisa da yan uwan aunty luba kamar gaske sai wasa da dariya ake dashi.


Daki guda Mammah! tasa aka gyarawa aunty luba tace ta zauna a gabanta tayi jego zata kula da ita yanda ya kamata Yan uwan aunty Luba sunji dadi sosai suka dinga fad'in"Lubabatu kinyi sa'ar Uwar miji.

Sayyada kam a gurinsu ta tare ta saki jikinta sosai da 'kannan aunty Luba suna ta hira kanwar aunty Luba mai suna Asiya jininsu ya had'u da Sayyada sai da ta girmi Sayyada da kusan shekaru biyar amma sai ka lura zaka fahinta saboda ita Asiya tana da karamin jiki......Suna kicin suna aikin abinci Asiya tace"Sayyada na lura fa tun dazu baki le'ka mijinki ba alhalin kin san yana gida bai fita gaskiya yana da kyau kije ki duba shi koda akwai abunda yake bukata."!

Sayyada tace"Asiya kenan baki san halin wannan ba mybe ma ina zuwa zai koro ni shi ba ayi masa gwaninta."

Asiya tace"Duk da haka dai kije ki gani sai ki dawo mu karasa aikin abincin." Sayyada tace"To ban'ki taki ba bari na 'karasa murza fulawar nan sai naje." Asiya tace."Yawwa ko kefa su maza ba'a sanya a kansu ballanta irin naki da mata suke rubibi yanzu sai kiga wata ta kwace miki shi wallahi."

Sayyada tasa dariya tana fad'in"Kai Asiya nifa wallahi ina ganin beken matan dake rubibin namiji ni duk kyau da haduwarka baka isa nayi rububi a kanka ba." Asiya tace"Humm Sayyada kenan baki san abinda ke faruwa bane a wannan duniyar ni dai shawarar da zan baki tunda kin samu to ki rike hannushi bibbiyu."
Sayyada Dariya kawai tayi ta wanke hannunta tace"Bari naje na dawo." Asiya tace"To shikkenan."



Waya sukeyi da Captain Habu Yace."Habu bana jin zan iya fita aikin dare wallahi jikina duk a mace yake ni kaina na rasa abinda ke damuna kwana biyu wata iriyar kasala da mutuwar jiki ke damuna."

Captain Habu yace."Hakanan zaka daure ka fito domin tun safe su Saleh ke bunkice a gurin kuma dazu munyi waya dashi yace akwai tabbacin mutanan nan a gurin saboda haka kaga zuwanka nada amfani domin kafi mu dabaru masu kyau."

Yace."Allah ya nufe da zuwa yanzu na idar da Sallah isha'i zan shigo bracck din." Captain Habu yace."To shikenan a huta gajiya da kyau komai xakayi kayi kafin ka fito domin kar kasala ta sanya ka kasa aiki."Cikin sha'kiyanci yake masa magana Sadam! yace."Okey wato ka fassara magana ta da wata manufa ko."? Habu yace."No kawai dai na fadi hakane." Dariya sukayi dukaninsu kafin su kashe wayar a tare.


A hankali ta turo kofar ta shigo dakin bakinta dauke da sallama.

Ya d'aga kai a nutse yana kallonta zum'bura baki tayi ta wuce zukud'um!zukud'um! zata shige masa d'aki.

Yace."Ke! meye haka zaki wuce mutane ki shiga d'aki wani abu kika ajiye a ciki kome."?

Ja tayi ta tsaya tayi kici kici da fuska har yanzu haushinsa takeji kan maganar da yayi zai auri Amina.

Ya 'bata rai sosai yace."Wai shin wannan fizge fizgen da kikeyi na meye? na lura dake tun muna hanya kike wani cin kunu wa zaki nunawa miskilanci."

Shiru tayi kanta a 'kasa Tsaki! yaja ya dauke kansa.....Dakin ta shiga ta zauna gefan gado kwallah ta cika mata ido.....Haka kawai da ta kalleshi sai taji haushinsa idan ta tuno da maganarsa.

Ya shigo dakin yana tattare hannun riga toilet ya nufa domin daura alwala ya fito a nutse ya wuce ta masjid ya nufa domin yin sallah......Sayyada da kyar ta mike taje ta daura alwala ta fito sallah ta tayar ta zauna kan daddumar tana lazimi tana jin kiran sallah isha'i sai ta mike ta gabatar da tata zama tayi kan daddumar bayan ta idar da sallahr tana jiran shigowarshi.


Koda ya shigo ya ganta a zaune bai ce komai ba ya nufi wardrobe dinshi kayanshi ya soma cirowa yana kimtsa jikinsa.....Sayyada ganin yana sanya kayan aiki sai gabanta ya fad'i! da alama aiki zai fita kallon bayansa takeyi babu kiftawa jikinsa ya bashi ana kallonsa yana juyowa suka hada ido tayo saurin sunkuyar da kanta kasa.

Girgiza kai yayi ya cigaba da shirinsa Ta mike jikinta a sanyaye zata fita yace."Ke! ina zakije da daddaran nan."!? A hankali tace"Zan koma sashen Mammah ne." Yace."A'a kiyi zamanki a naki gurin ni zan fita idan ma nine bakya son gani."

Tace."A'a ni dai gwara ka barni naje can na zauna abunda ma aiki zaka tafi."

Yace."Eh aiki zan tafi yanzu idan ban dawo ba kar ki damu da safe ma had'u."

Tace"Shine kuma kake cewa na zauna ni kad'ai."

Yace."Ina da dalili ai yanzu kika tafi sashen Mammah kika zauna shikkenan Sulaiman zai zo ya saki a gaba kuyi ta shirme."!

Da mamaki! take kallonsa sam! bata ji dadin wannan maganar tasa ba duk da take yarinya mai karanci shekaru ta fahimci tamkar Sadam din na zarginsu ne sai ranta ya baci tace"Wai Ya Sadam! me kake nufi ne."? kar fa ka manta Sulaiman dai d'an uwana ne kusancin dake tsakaninka dashi yafi wanda muke dashi me zai sanya ka dinga zargin wani abu zai shiga tsakanina dashi gaskiya ni na gaji."!!

Yace."Ke! ni zaki kawowa maganar banza da wofi! ni zaki nunawa cewar Sulaiman dan uwana ne? Nace ba zaki koma sashen ba sai me ? idan Sule ke auranki sai ki koma nagani 'Yar kauye kawai wacce bata da wayo.''

Sayyada ta fashe da kuka ta tsani ya kirata da 'yar kauye shin wai me takeyi ne na 'kauyanci da kullum yake kiranta da wannan sunan......Cikin kuka tace"Wallahi ba zan zauna a daki ni d'aya ba sai kace mayya idan ka fita sai na fita kuma maganar 'yar kauye da kake kirana dashi ai duk tushen mu d'aya da ka.........Mari! ya kai mata a fusace!!! Ta matsa gefe tana muzurai! hannunta akan kumatunta kallonsa takeyi cike da tsoro da mamaki!

Yana huci! yace."Ba'a nuna ni da ya tsa Sayyada duk rashin kunyar da kike min kawai ina saurara miki ne! yanzu ma kina so ki zageni a kan Sulaiman ko."? Girgiza kai tayi tana zubar da hawaye. Yace."To in kuma cewa ga yanda za'ayi ki nuna ba haka ba ranki zai "baci! da banyi niyyar rufe ki ba amma yanzu furucin da kikayi ya sanya naji gwara kawai na rufe ki na huta a yanda kike kidahuma! zaki iya janyo min Sulaiman din nan ki cuci mutane."!!! Kuka takeyi tana bashi hakuri yayi mata banza ya cigaba da shirinsa.
Ransa duk ya 'baci da halin Sayyada kullum yana so ya nuna mata cewar ta kiyaye da Sulaiman ba sa'anta bane yana so ya nuna mata illolin Sule a tare da ita tana kaucewa shi ba zai fito fili ya fad'a mata waye Sulaiman ba saboda dan uwansa ne tilas ya rufa asirinsa amma ita saboda tsabar ta raina shi taki daukar maganarshi sai ya fara hukuntata sannan zata kiyaye.


'Kafafunsa ta rike tana kuka " Don girman Allah Ya Sadam! kar ka rufe ni a d'aki don Allah kayi hakuri kaji ko."!?

Yace."Sayyada taurin kanki yayi wa ban isa in fad'a miki magana d'aya ki dauka ba komai nayi miki kece kika jawo kina nuna min da cewar ni ban isa in fadi magana ki dauka ba sai ta sule shin wai Sulaiman ke auranki ko Sadam."!?? Cikin tsawa ya fad'i maganar! Tana kuka tace"Kaine ke aure na ba Sulaiman ba." Yace."Amma shine kike fifitashi a kaina."! " Bana fifita Yaya Sulaiman a kanka Ya Sadam ina yi maka kara ne kasancewarsa a matsayin dan uwanka na jini ni ma d'an uwana." Yace."To bana son wannan karar daga yau na soke ta babu ruwanki da Sulaiman." Tace"To insha Allahu." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Cika min kafafu Malama." Da sauri ta cikashi ta mike tsaye tana goge hawayenta a gogo ya daura fuska a murtuke ya dauko hularsa ya kwafa a kanshi ya dauki wani farin gilashi ya sanya kana ya kama hanyar fita .....Bayansa tabi ta ru'kunkume! tana kuka ya juyo da ita suna fuskantar juna.....Fuskarta ya tsurawa ido yana kallo ta dinga hawaye tana kallonsa....A hankali yace."Goge hawayen." Ta sanya bayan hannunta ta goge idanunta duk sunyi ja!!! Sai da ya tabbatar da ta samu nutswa sannan ya d'ora bakinsa saman goshinta ya manna mata kiss ajiyar zuciya ta sauke ya kalleta cikin mazewa yace."Ni zan fita aiki domin kar in tafi da hakkin ki nake so ki fad'a min shin kina bu'kata ko kuwa."!? Sam! ta manta wannan cptar tasu tace"Yaya Sadam! ban gane me kake nufi ba ni bani da hakki a kanka ai." Hararata yayi yace."Kin manta abun nan me dad'i da mukayi a *Dabi* har kika dinga ihu! kina ya kushina."! Sayyada taji tamkar 'kasa ta tsage ta fad'a ciki haka taji bala'in kunya ya kamata ta rintse ido tana jin kunyar had'a ido dashi tace"Ni bana bukatar komai wallahi." Yace."Ai ba wani abu bane dama don dai kar in tafi da hakkinki ne yasa nayi magana ok nima bana bu'kata ai."! Yafad'a yana me tsurawa karamin bakinta ido so yake ya tsotsi bakin gashi yayi su'butar baki yace baya bukata.........Tace."Ni wallahi kunya nake ji muje kawai."! Girgigiza kansa yaya yana me risinar da kwayar idonsa cikin nata kallon juna sukeyi Sayyada ta soma jin kasala na kamata kafin ta ankara taji ya tallafo fuskarta le'bunanta ya fara tsotsa kafin ya samu damar shigar da bakinsa cikin nata ya fara tsotsa tamkar wani mahaukaci haka yakeyi zafi-zafi! ya dinga tsotsar harshenta da le'bunanta sai da yaga tana neman fad'uwa sannan ya saketa nan ma sai da ya rike mata hannu domin taga taga tayi zata fad'i! ajiyar zuciya kawai suke saukewa ita dashi......Sai da suka samu nutsuwa sannan ya kama hannunta suka fita har bakin motarshi yaje da ita tana tsaye ya bude ya shiga zaune ya kalleta a nutse yace."Idan kin shiga ki fadawa Mammah na tafi aikin dare saboda jama'ar dake sashen yasa ban shigo ba." Kai kurrum ta iya d'agawa.....Ya kunna motar ya sake kallonta a karo na biyu yace."Ya dai."? girgiza kai tayi alamun babu komai yace."To ni na tafi idan kuma an kasheni zaki min takaba ko."? Ihu!! ta kurma! ta zura hannu cikin motar key din motar ta ciro tana haki!! sam bata san ma sanda ta akaita hakaba....Kallonsa take tamkar yau ta fara ganinsa bakinta sai rawa yake ta ma rasa me zatace masa.

Dariya kawai yake mata ya mi'ko hannunsa ta tagar motar yana fad'in"Malama bani key d'ina." 'Ki tayi yace."Saboda nace zaki min takaba shine kika cire min key." Sai hawaye shaaaaa! ya soma zuba a fuskarta tana kuka take fad'in "Allah na rantse ba zakaje ba tunda ka fad'i wannan maganar jikina yayi sanyi." Kuka take tana bubbuga kafafu wai ba zai tafi ba......Shan kunu yayi yace."Wai ke ina wasa dake ne? ki bani key dina ko kuma yanzu ranki ya 'baci."! Ta goge hawayen dake zuba tana makale kafad'a tace"Allah na rantse ba zakaje ba." Yace."Ashe kuwa xakiyi kaffara yarinya." Motar ya bud'e ya fito ita kuma ta ruga a guje zata shiga sashen Mammah taku biyar ba tayi ba ya cafko ta......Yayi dai-dai da shigowar motar Sulaiman cikin gidan wanda duk abunda ya faru akan idonsa..........







_*Kika fitar min da book Allah ya isa kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa Whasap numbar......07084653262 _08089965176*_





*BINTA UMAR ABBALE*
: 28
Ganin motar Sulaiman ta shigo gidan ya sanya Sadam! 'kara rungume ta a jikinsa yana kokarin kwatar key din daga hannunta ita kuma sai zillewa takeyi tana 'boye hannunta a bayanta........Sulaiman da kyar yayi parking din motarshi ganin abinda ke faruwa yayi mugun daga masa hankali Sayyada ce suke wasan soyayya da Sadam! wani irin gumi ya shiga zubo masa ya bude mota ya fito tamkar zai kifa saboda sauri da zafin nama yazo ya wuce su fuuuuuu!! Sadam! ya bishi da kallo wanda lokaci guda ya karanto abunda ke fuskanrshi kishi da bakin ciki ne muraran yake nunawa, nan ya sake tabbatar wa da kansa cewar abunda yake zargi gaskiya ne Sulaiman dan uwanshi na son matar aurashi.....Sayyada kuwa ganin wuce war Sulaiman din ya sanya kunya ta rife ta tasan yaga duk abunda ke faruwa jikinta ne yayi sanyi ta inda har yayi nasarar kwatar key din a hannunta bata sani ba.

Ya kalleta fuska a murtuke yace."Kina jina ko."? daga kai tayi tana kuka yace."Na fada miki babu ruwanki da Sule ko."? Ta daga kai yace."To kiyi min addua Allah ya dawo ni dani lafiya." Tace."Yaya Sadam! Allah ya dawo da kai lafiya ya tsareka daga sharrin masu sharri." Yaji dadin wannan adduar da tayi masa yace." Ameen ameen sai na dawo." Juyawa yayi ya nufi inda motarshi take tana tsaye ya tada motar ya fice daga gidan......Jikinta bab kwari ta bar gurin.

Sulaiman na zaune a parlor yana cika yana batsewa ta shiga ko sallamarta bai amsa ba yace."Sayyada zonan." Taje ta zauna kujerar dake fuskantarsa tana takurewa yace."Ina maganar da nayi miki kwanakin baya."!? Tace.",Wace iriyar magana ce Yaya Sulaiman." Yace."Kin manta kenan saboda ba maganar ce a gabanki ba ko."!? Tayi shiru yace."Naga kin soma sakin jikinki da Sadam! kin manta abunda nace miki ko? Sayyada tayi shiru tana sauraransa yace."Sadam! cutar ki zaiyi nayi miki rantsuwa da Allah ba sonki yake ba saboda haka nake baki shawarar ki kiyaye kar ki kuskura ki bashi kanki ma'ana kar ki kuskura ya sanki a matsayin 'ya mace na tabbatar da cewar idan ya riga ya sanki a mace shikkenan kin gama aiki a gurinsa sakin ki zaiyi ya cuce ki."

Sayyada ta shiga tunanin Maganar Sulaiman sai ta soma gazgatawa domin kusan kullum idan sa'bani ya shiga tsakaninsu da Sadam! din ya dinga maganar rabuwa kenan, anya kuwa maganar Sulaiman ba abar dubawa bace yana da kyau ta tabbatar da ingancin sonta a gurin Sadam din.

Yace."Idan kin nutsu kinyi tunani zaki ga sadam bai damu da kowa ba sai kansa sai kuma aikinsa ya dauki aikinsa da mahimanci sosai so ina ganin zai iya sakinki saboda aikinsa saboda haka kiyiwa kanki fada ki rage shigewa jikinsa kiyi nesa nesa dashi hakan shine zai fi miki alkairi."

Sayyada tace"To Yaya Sulaiman nagode da shawara insha Allahu zanyi yanda kace nagode kwarai da gaske." Sulaiman ya saki fuska sosai yaji dadi da ta dauki maganarsa da alama kuma zatayi amfani da ita yace."Naga wata waya sabuwar yayi irin ta mata zan siyo muku ke da Lubabatu." Sayyada ta washe bakinta tace"To Ya sulaiman mungode kwarai." Yace."Yauwa babyna bari ma na tashi naje na siyo muku yanzu."


Sayyada taji wani iri yanda yace."babyna ko Sadam! baya kiranta da irin wannan sunan ko da yake tun tana yarinya yake kiranta da baby amma dai ya kamata ya daina tunda yanzu ita matar kaninsa ce.


Yana shirin fita Mammah ta fito daga dakin da Luba take tace"Ina zakaje kuma Lubabatu nasan magana da kai." Yace."Yanzu zan dawo mammah." Tace''A'a zo ka shiga kaji ko menene ina lure dakai tun safe baka shiga dakin ba."

Yace."Mammah baki ne sukayi yawa amma bari na shiga yanzu." Ba dan ransa yaso ba ya nufi dakin da Luba take yana wani ya mutsa fuska sam! ya tsani karnin jini shifa gabakidaya idan mace ta haihu tsanarta yake shiyasa kwata kwata baya son zuwa inda Luba take.......Lubabatu na zaune gefan gado tayi wanka ta shirya tsaf sai kamshin turare takeyi amma kuma kana kallon fuskarta zaka san tana cikin bakin ciki.....Ya shiga da karamar sallama sai ya tsine fuska yake kan drowar ya zauna yace."Mammah tace kina nema na meye."!? Ta dago kanta tana kallonsa idanunta ya kawo ruwa tace"Sulaiman ashe so ya na zama 'kiyayya me yasa tun kafin na aureka baka fad'a min a'kidunka ba me yasa baka sanar dani tsarinka ba? zaka barni ina ta wahala ni kadai kayi min ciki ka dinga azabtar dan......."Ke! saurara min haka."Sulaiman ya katseta yana shan kunu yace."Idan kina ganin takura miki nake hanya a bude take babu wanda ya rike miki kafafu ki tafiyar ki idan kuma kina ganin zaki cigaba da zama shikkenan ni bana son surutai da maganar banza haihuwace bana so don ban shirya yin ta ba a yanzu saboda haka shawara ya rage naki."Rigarshi ya buge ya

Please Login or Register in order to submit comment