Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama hanya ya fita daga dakin Lubabatu ta kwanta kan bed din tana wani irin kuka na tsantsar bakin ciki da nadama sulaiman ya yaudareta ta'ki kowa saboda shi ta wulakanta samarinta saboda shi amma shine zai saka mata da sharri yanzu ya kamata ta yanke shawara abunda zai taimake ta.

Koda ya fito palo ya gansu zaune sai ya saki fuska cikin makirci yace."Mammah mun gama da ita zan fita in dawo yanzu." Tace"To shikkenan." yana fita Mammah tace"Ina Sadam! ne ko ya fita." Sayyada tace"Yace."A fada miki ya tafi aikin dare." Tace."To Ubangiji Allah ya tsare shi ya dawo dashi lafiya."Sayyada ta amsa da "ameen." Hira sukeyi Alhaji Auwal ya shigo hannunsa rike da karamar jakar kasuwa Sayyada ta mike da sauri ta isa inda yake jakar ta karba tana masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayar ta mutanan *Dabi* tace kowa lafiya. yace."Watakila nima week end dina nayi a can." Tace"Aikuwa dai dasu Baba sunji dadi." Yace."Insha Allah zanje." Daki ya nufa Mammah ta mike ta bi bayansa bayan ta karbi jakarsa dake hannun Sayyada.


Sayyada ta zauna a palo tana tunanin maganarsu da Sulaiman gaskiya ya kamata ta fara gwafa Sadam! tanan zata gane cewar yana sonta ko baya sonta ta zauna tayi tunanin da abunda zata fara......Dakin aunty Luba ta nufa ta tarar da ita kwance tana kuka Sayyada ta zauna kusa da ita tana rarrashinta ita duk ta dauka Luba na kukan kan mutuwar babynta ne tace"Aunty insha Allahu Allah zai baki wani don Allah ki daina kuka." Lubabatu ta mike zaune tare da rike hannun Sayyada tace"Sayyada na daina kuka ki tayani addua kan abinda ke damuna a zuciyata."


Sayyada tace."Insha Allah aunty zan taya ki addua." Hannu tasa ta goge mata hawayen fuskarta, Sayyada ta dinga janta da zance har sai da taga ta sake sannan hankalinta ya kwanta.


Sulaiman ya shigo dakin hannunsa rike da ledoji sakin fuska yayi tamkar bashi ba yace"Yawwa Sayyada gwara da kika shigo kika d'ebe mata kewa." Sayyada tayi dariya tace"Ai tare ma zamu kwana tunda Ya Sadam ya tafi aikin dare." Yace."Hakan na da kyau ga wayoyinku." Ya mikawa ko wacce kwalin waya guda daya.....Lubabatu kar'ba tayi kawai ta aje gefe ita ba waya ce a gabanta ba.....Sayyada kam jikinta na 'bari ta fara bud'e kwalin wayar dalleliyar waya Inpinx hot7pro da cazarta da komai nata sabon layi ta bude tana godiya yace ."Kawo in sa miki layin ko." Sayyada ta mika masa ya sanya mata layi ya kunna mata wayar ya mika mata murna takeyi tana godiya shi kuma sai dariya yake mata.....Ta dauki tsohuwar wayar aunty Luba tace"Aunty bari in dauki numbar Asiya." Luba tace."Okey zaki ga nayi serving dinta da sistarna." Tace."To aunty." Numbar Asiya ta dauka tana duba numbars taga numbar Sadam inda ta gane numbarsa ce aunty Luba tasa *Sadam!Soja* tayi saurin daukar numbar tayi serving dinta duba wayar take yi Sulaiman nayi mata hira ya rashe ya zauna yaki tafiya har aunty Luba ta shiga mamaki da kokwanto domin duk hankalinsa na kan Sayyadar ko kunyar ta baya ji ita kam ta rasa wane irin hali ne da sulaiman mugun son matansa yayi masa yawa matar dan uwansa ma bai bari ba.


Gaskiya d'a namiji bashi da kunya wallahi haka sulemain ya zauna har kusan goma da rabi na dare suna hira da Sayyada wanda ita Luba da ta gaji juya musu baya tayi bacci ya dauketa Itama Sayyadar duk ta kosa ya tashi ya tafi ya'ki sai da ya soma mata magana ta tsiri hammar 'karya sannan yayi mata sallama ya fita.

Bargo ta dauka da pillow ta kwanta kasan kafet tana cigaba da duba wayar tabbas taji dadin wayar sosai......Numbar Sadam! ta duba shi a whasap taga ya sauka tun tara na safe ta sauke ajiyar zuciya.

Tes message ta tura masa.

_Assalamu alaikum barka da war haka ya ma'abocin kyau da kyawun zuciya ina maka fatan alkairi daga mai kaunarka_

Sai da ta tabbatar da test din ya tafi sannan ta kashe wayar ta kwanta bacci ya dauketa mai cike da mafarkin masoyinta Sadam!.


***

Sadam! na can wani daji cikin wani karamin kauye dake zaria *Dutsan wai* suna zargin masu garkuwa da mutane na da gida a cikin dajin.....Don haka da shirinsu suka shiga gurin suka rarrabu cikin dare suna haska tochlight irin tasu.....Zuruf!!! 'kafafun Sadam! suka afka cikin wani tarko! kafin yayi wani yun'kuri yaji ana janyo kafafunsa ta ciki.......a guje! su Habu sukayo kansa suna jansa ana jansa daga ciki.....Cije bakinsa kawai yake domin duk gwiwoyinsa sun dauje!! da kyar! suka samu suka ciro shi ya fito dake jarumi! bai tsaya duba kafafunsa ba ya soma sakarwa ramin alburushi ji kake tas! tas! tas!tas! gudu! sukaji ratatata!!!! da sauri Captain Habu ya haska gurin da torchlight can suka hangosu suna fitowa ta wani rami! ba wannan da Sadam! ya afka ba wani ne daban gudu suke suna neman hanyar tsira.......A guje! Sadam! ya rufa musu baya yana sakin alburushi ta ko ina! Sauran suka rufa masa baya......Cikin ikon Allah suka samu nasarar harbin daya a kafarshi a take ya zube a gurin yana rike 'kafarshi kiran 'yan uwanshi yake "Lauje!!! ku tsaya sun harbe ni Mado!!! kar ku tafi ku barni Oga!!!! ku tsaya ku cuceni sun harbe ni."!! Inaaa babu wanda ya tsaya a cikinsu ballanta su cece shi kowa takansa yake.......Sadam! na isa inda Matashin yake ya sa'be shi a kafad'a! ya cigaba da gudu dashi yana sakin harbi! nan ma Allah ya sake bashi sa'a ya sakar wa d'aya harbi a kwauri! a take ya kurma ihu! ya zube a gurin jan jiki ya soma yi yana daga hannu da kiran 'yan uwansa kamar yanda na farko yayi suka ki tsayawa kokarin ceton ransu suke........Duk yanda suka zo su kama sauran Allah baiyi ba sun tsere amma alhamdullahi tunda sun samu nasarar kama guda biyu tilas zasu fad'i inda sauransu suke fakewa."

Captain Habu ya dauki dayan a kafadarshi sauran sojojin suke haska musu hanya har suka samu suka fita daga dajin titi suka fita inda sukayi parking din motocinsu suka shiga kai tsaye suka wuce bracck din nasu.


****


Da asuba Mammah ta shigo ta tashe su Sayyada tayi sallah mammah ta had'awa Luba ruwan wanka tafasasshe taje ta taimaka mata ta gasa jikinta ta shiga ruwan zafi ta gasa kasanta sosai ta fito Sayyada har ta fito mata da kyan sawarta ta shirya tsaf Sayyada ta shigo musu da break fast suna karyawa suna hira akwai shakuwa da fahintar juna a tsakanin Sayyada da Aunty Luba Sulaiman ne yayi sallama ya shigo yayi shirin fita suka gaisa da Sayyada Luba ta gaisheshi ya amsa a sake kamar bashi ba yace."Zan fita me kuke so a siyo muku." Luba tace."Ni kam babu komai." ba tare da ya wani damu ba yace."Baby fa."? tace"Ya Sulaiman bana bukatar komai wallahi.'' Yace."To shikkenan sai na dawo ko." sukace"A dawo lafiya." Fita yayi yana jin wani nishadi a ranshi gani yake tamkar Sayyada ta zama tashi domin yana da labarin had'arin da Sadam! din ya jefa kansa a ciki ya tafi matattara ta 'yan kidnapping yasan sai abunda Allah yayi a kansa, komai Sadam yake ciki kan aikinsa idanunsa akai yana mamaki mutuka da suke jefa rayuwarsu a garari shi kam ko giwar wake yasha ba zai ta'ba yin aikin soja ba aikin siyar da rai a banza a wofi.

Bayan sun gama break fast Sayyada ta koma gefan gado ta zauna wayarta ta fara duba ko Allah zai sa ya mai do mata da amsar test din data tura masa tana so tasan bai san numbar ko ta wacece ba abunda yasa ta shirya wannan plan din tana so ta gazgata maganar sulaiman inda yake cewa baya sonta aikinsa ne a gabanshi da sauransu.

To ga dai test din yaje tun jiya amma babu amsa sai ta sake rubuta masa wani test din kamar haka.

_Da fatan ka tashi lafiya ma'abocin kyau da kyawun zuciya ina fatan ka yini cikin koshin lafiya_

Tura masa tayi dai-dai lokacin dasu Asiya suka shigo ita da aunts dinsu sai ta aje wayar tana musu barka da zuwa...........Su Sadam kuwa kai tsaye bracck dinsu suka wuce da 'barayin da suka kama a daran labari ya iske General AbdulSalam wato shugaban rindunar sojojin najeria mutumin da ya kasance mahaifi ga Halima kenan.....Cikin daran ya isa bracck din dakin da aka ajesu ya nufa kai tsaye........Sadam! na gurfane a gabansu yana tambayarsu ina 'yan suke da mafaka sannan iya a dadin mutane nawa suka salwantar wa da rayuwarsu......Dukaninsu sun kasa magana sai muzurai sukeyi Gen Abdulsalam na shiga gurin sadam ya mike yayi masa gaisuwa irin tasu General ya dafa kafadarshi yana yaba kokarinsa da bajintarsa domin yasan dabarunsa da kokarinsa ne ya sanya har akayi nasarar kama wad'annan azzaliman mutane babu shakka Sadam! ya cancanta a 'kara masa girma saboda jajurcewarsa kan aikinsa.


Sai da sukaci duka sannan suka fad'i sunayensu da garuruwan dasu dukaninsu suka ce basu san iya adadin mutane nawa suka salwantar ba mutukar sun nemi kudi gurin mutum bai basu ba suke kashe rai kuma su kira mutum inda suka san zai ga gawar dansa ko 'yarsa ko kuma d'an uwansa.

Gen. Abdulsalam har kuka yayi saboda tausayi wannan rayuwa da wad'annan mutane suka jefa kansu tayi tsauri da yawa kawai saboda zalinci su dunga garkuwa da mutum suce sai an basu makudan kudin da wani ma bai taba rike irinsu ba tunda yazo duniya idan kuma basu samu ba su kashe mutum tamkar kiyashi babu shakka suma daurin rai da rai ya cancanta ayi musu.......Da kyar suka fad'i inda suke da tabbacin idan sunje zasu ga sauran 'yan uwansu.....Washe gari da safe barikin sojojin ya cika da 'yan jarida kowa na bukatar karin bayani abun magana dai har sunyi yawa a bakin Sadam! masu rubutawa nayi masu daukar murya nayi kowane dan jarida yafi so yaji ta bakinsa......Su kuwa 'barayin suna d'aure daga su sai gajerun wanduna suna zaune cikin kwaleliyar rana sai daukarsu ake video domin haskasu a television........... Sadam! basu samu nutsuwa ba sai wajejan uku da rabi na rana sannan kowa ya nufi gurin iyalinsa....Mafi akasarin su a cikin bracck din suke da zama da iyalinsu Mutum uku ne basu zaune a barkin cikinsu harda Sadam! da ya nufi can family house dinsu.


A ranar Sayyada yini tayi tura masa test tayi ya kai sauk goma ko daya bai duba ba ballanta ya bata amsa, ganin labaran sha biyu na rana an nuno shi yana jawabi kan nasarar da suka samu ya sake kwantar mata da hankali ta 'kagu ya dawo gida ta ganshi ko taji sanyi cikin ranta.....Duk mai kaunar Sadam yaji dadin abunda ya same shi banda Sulaiman wanda lokacin da yaga Sadam! din a tv 'yan jarida sun kewaye shi suna daukar rahoto yaji wani bala'in kyashi da hassada ya kamashi yaso ace wannan fitar da yayi an kawo musu gawarsa mikewa ma yayi ya bar gurin ranshi idan yayi dubu to ya baci......


Ana kiran sallahr la'asar ya shigo gidan bai zame ko ina ba sai sashensa wanka yake so yayi saboda jikinsa yayi bala'in tsami duk ya daddauje gwiwoyinsa a lokacin da ya fad'a tarko......Zama yayi gefan bed yana kwance takalminsa a hankali ya zare ya cire safar sannan ya kwance blet din ya zare wandon a hankali ya zauna yana duba gurin sai yanzu yake jin zafin ciwon duk da a ido idan ka kalleshi zaka dauka ba wani gagarimun ciwo bane to shi kadai yasan yanda yake masa ciwo a jikinsa ....Hannu ya daga yana kokarin cire riga Ta shigo dakin gabanta ne ya fad'i ganinsa zaune! itama ta shigo ne tayi wanka ta sanja kaya.......Da sauri ta 'karaso inda yake "Yaya Sadam! yaushe ka dawo."!? tafada cike da kulawa Yace."Yanzu." Kallonsa take cikin nazari taga yana lallaba jikinsa ta kalli gwiwarsa taga ta kumbura kad'an da sauri ta tsuguna zata sanya a hannu akai ya rike yana girgiza mata kai."

Murya na rawa tace"Ciwo kaji." Girgiza kansa yayi alamun "A'a." tace"Ba gashinan na gani ba." Yace."Ke! ba wani ciwo ne na kuzo a gani ba daujewa ce."Tace"Sannu to." Shiru yayi yana yunkurun mikewa....Ta rike hannunsa wai zata taimaka masa kallonta kurrum yake yarinyar ta damu dashi sosai.....Toilet suka nufa tare ta had'a masa ruwan zafi tace"Yaya Sadam na ganka an nuno a tv kana magana." Yace."Eh." Tace."Gaskiya kayi kokari Allah ya tsareka daga sharrin masu sharri." Yace."Ameeen Sayyada." kama hanya tayi zata fita yace."Zo ki gasa min jikina." Ta juyo tana kallonsa sai ya mika mata towel kar'ba tayi a hankali shi kuma ya hau cire shart din jikinsa ya shiga kwamin wankan daga shi sai karamin wando....Tace"Ya za'ayi na gasa maka jikin....? Hararata yayi yace."Ba gashinan na kwanta ba ko ina da kika sani a jikina ki danna min da ruwan zafi ciwo yake min."

Tace."To." Ruwan ta shiga tsanowa da towel ta fara danna masa a kirji ya lumshe ido yana jin dadi yace."Ki dinga dannawa da kyau." Tace."To." Gwiwowinsa ta dinga matsawa ruwan zafi tana dannawa yana jin dadi.....Ta dauki kusan minti ashirin tana wannan aiki ya bude idonsa yana kallonta a hankali ya rike towel din yace."Ya isa haka nagode." Ji tayi kamar ta fashe masa da kuka tausayi yake bata.... "Hada min wani ruwan mai zafi." Yafada yana mikewa zaune....Ruwan ta hada masa yace."jeki zanyi wanka." Tace"Ko inyi maka." ? Da sauri ya kalleta yace."Ke! ni zakiyi wa wanka." Girgiza kai tayi da sauri! Yace."Oya fita ki bani guri.'' Simi- simi ta kama hanya ta fita tana kumshe baki Yaya Sadam kenan to wai wane dare ne jemage bai gani ba hummm!


Tana fita tayi ar'ba da wayarsa kan bed da sauri ta zauna tana dubawa test din da dinga tura masa ta shiga dubawa taga ko d'aya bai duba ba....Tayi mamaki sosai ko da yake ina yake da lokacin duba wani test yanzu amma dai tasan tunda ya shigo gida zai duba wayarshi ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ko wace iriyar amsa zai bayar idan yaga test din sa'konnin soyayya masu zafi ta tura masa wanda tasan duk wanda aka turawa irinsu tilas ya magantu kuma ya yabawa wacce ta tura..............................







_*Kika fitar min da book Allah ya isa! Kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa.....Whasap numbar....07084653262 _08089965176*_






*BINTA UMAR ABBALE*
: 29
Tana jin motsin fitowarsa tayi saurin ajiye wayar ta tsurawa kofar toilet din ido ya fito sanye da gajeran wando da towel rataye a wuyansa, kirjinsa data kalla shine ya bata sha'awa jikinta ya mutu murus! cikin kasala da mutuwar jiki ta dauke kanta....Mikewa tayi a hankali ta shiga toilet d'in, ruwan wanka ta had'a ta jima a tsugune kafin ta fara wanka haka kawai take jin sha'awar Sadam din na taso masa ganin faffad'an kirjinsa ya tafiyar da hankalinta sai ta dinga tunawa da zazzafar soyayyarsa da ya gwada mata a kwanaki biyu da suka wuce,

Da kyar tayi wankan ta fito daure da towel me kauri ta ta lullube jikinta da wani ma dai-dai ci yana tsaye gaban mirror yana gyara sumar shi tazo ta tsaya a bayanshi....ta mudubin yake kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace." Yace."Wannan kifta idanun da kikeyi ya nuna min cewar baki da gaskiya."

Tayi kasa da kanta duk bakinta yayi nauyi ganinsa a haka na bala'in tayar mata da hankali yace."Ke! wai meye kike ta sunkuyar da kai nifa bana son gulma." Dariya tayi tace"Ni tsoro kake bani wallahi duba jikinka a murd'e kamar irin 'yan dambe na tv." Yace."Ba wani nan ke dai kawai kice ina baki sha'awa ne shiyasa naga kina ta kallona."

Ta'be baki tayi tace."Wallahi ni baka bani sha'awa ba." Murmushi yayi kawai ya basar tun tana gasa masa jiki ya lura da irin kallon kurrular da take masa shine yanzu zata basar....Shi kansa yasan babu macan da zata kalli zatinsa tace bai mata ba yana mutukar alfahari da kyawun jikin da Allah ya bashi.

Yana matsawa daga gurin ta matsa mai ta shafa sama-sama ta gyara kwantaccan gashinta ta daureshi kana ta sanya wata duguwar riga mai hula duk da ba tayi wani make up tayi kyau sosai da sosai karamin hijab ta sanya a maimakon hular rigar......Shima cikin wata bud'ad'diyar t_shart da shout nickar ya shirya jikinsa ya zauna gefan gado tare da daukar wayarshi yana dubawa.....Sayyada ta samu turarashi masu karfi ta ambula a jikinta take dakin ya d'ume da kamshi Ya dago yana kallonta da 'baci rai! Yace."Saboda baki da hankali shine zaki yi min asarar turare ko dan baki san mahimancin sa bane." Kanta a kasa tace"Yi hakuri." Girgiza kai kurrum yayi ya cigaba da duba wayarshi....Gabanta ya fadi ganin wayar a hannunsa sai tazo ta zauna kusa dashi tana le'kawa....Bai hanata ba ya cigaba da duba test messages din da suka fi guda goma....Karantawa yake yana mamakin wace yarinya ce wannan ta turo masa da wannan haukan...."Ya Sadam! Wacece."!? Tafad'a fuskarta a murtuke."! Kallonta yayi ta gefan ido ganin tasha kunu yasa shima yace."Me ya dame ki budurwata ce." Tace"Bangane budurwarka ba." Yace."Eh ko zaki hanani kula 'yan mata ne buduwarta ce tayo min test gashinan tun jiya tana tambayar lafiya ta."

Tace."Wannan budurwar bata da hankali wallahi kace mata gwara ma ta hakura domin baka da gurin ajiye ta."

Maganarta ta bashi dariya amma baiyi ba yace."Ni nace miki bani da gurin ajiye ta."? shiru tayi tana kallonsa Yace."Ni ko yanzu na tashi aurena banda matsalar gurin zama koda kuwa mata hudu zan aura saboda haka ki daina fadar haka."

Sai idanunta ya cika da kwalla ta dake bata bar ta ta zubo ba tace."Ni kuma na rantse ba zan zauna da wata mace a gida ba kuma in dai kace aure zakayi to sai na fadawa su Baba dole ne kuma ka bari na koma makaranta."

Yace."Wannan ne kuma baku isa ai tun farko sai da nace su bari kiyi karatu suka 'ki sai yanzu kuma ki kawo min wata magana ai kin cuci kanki."

Kuka ta fashe masa dashi tana burgima kan bed din tace"Wallahi ba zakaje ka auro wacce ta fini ilimi da waye wa ba nima dole sai nayi karatu me zurfi kana so ka auro wacce tafi ilimi kuji dadin kirana da 'yar kauye ko."

Ya dinga kallonta yana mamakin iya shege da sangarta ta yace."To idan na tashi auran sai ki hanani makaranta kuma nace ba zakiyi ba."

Mikewa tayi tana kuka tace"Aikuwa sai na fadawa Abbah wallahi ba zan zauna ka auro wacce ta fini ilimi ba." Kallo kawai ya bita dashi har ya fita daga dakin....Girgiza kansa kawai yayi gaskiya a tsarinsa sam! baya son matarshi na yawon zuwa makaranta shiyasa tun farko yace su bari ko NCE su bari Sayyada tayi suka'ki Yanzu shaidar kammalar secondary shoocl ne kawai da ita yana ganin hakan ma ya isa ba sai ta koma wani karatun ba.


Sayyada kam a palo ta tsaya ta goge fuskarta ta dai-dai ta kanta kana ta fita tana mamakin Sadam! wato tun bai san wacece budurwar ba har ya dauka ya soma muzguna mata da bakar magana, aikuwa zata zuba ido taga ko zai bada amsa.


Bata dad'e da shiga sashen ba shima ya shigo da wannan shigar ta kananun kaya Sayyada taji kunya ta kamata sai ta lura shi ko a jikinsa haka ya shiga dakin jegon aunty Hauwa tana ji tamkar ta hanashi shiga saboda kishi tasan akwai baki a ciki kuma har da 'yan mata kai koda matan auran ma wata ba zata iya kauda kanta daga barin kallonsa ba, Mikewa tayi ta bi bayansa.....Sai taga ya dogare a bakin kofa wanda shima jama'ar dake dakin su suka hanashi shiga ciki da yasan zai riski mutane da yawa da shiryo jikinsa......Gaisawa sukayi da jama'ar dakin Sayyada ta ra'ba ta jikinsa ta wuce ta zauna kusa da Asiya....'Kawar Asiya mai suna Labibi ta dinga satar kallon Sadam! tana bala'in son cikakken namiji mai kwarjini da suffar mazantaka duk inda cikakkenan namiji yake to sadam ya kai inda ake so sosai taji ina ma mallakinta ne shi......Sayyada takaici duk ya cika ta tanaji tamkar ta mangare Labibi dake kalle mata miji tamkar zata cinye shi.

Shi kam! bai san sunayi ba yana can yana tsokanar aunt Luba itama tana tsokanar sa dama sun saba duk sanda suka had'u sai sunyi irin wannan wasan amma fa na mutunci sukeyi babu hauka a ciki.

Juyawa yayi zai fita sai kuma ya juyo yana kallon Sayyada yace."Ke! ki kawo min abinci ina palo." Tace."To.'' Yana fita Labibi ta kalli Sayyada tace"A gaskiya Sayyada kinyi sa'ar miji ba zan munafurce ki ba wallahi ki kamashi ki rike da kyau idan kikayi sake akwai 'yan mata a gari marasa imani zasuyi wuf dashi." Dariya suka sanya Asiya da Labiba ita kuwa Sayyada shan kunu tayi tana d'an hararar Labibin kamar tace Cikin wad'anda zasuyi wuf dashi d'in ai har dake mayya kawai! sai kawai ta share tace"Bari in kai masa abinci in dawo." Sukace "To shikkenan."

Tana Fita Labiba ta kalli Asiya tace"Kin san Allah Asiya da badan akwai sanayya a tsakani ba da tuni an wuce gurin dan wallahi guy nan yayi masifar kwanta min a rai."

Aunty Luba tace"Wallahi kar inji kar in gani Labiba ke Asiya Sayyada ba cancanci haka daga gurunmu ba."

Asiya tace"Haba Aunty Luba ni me kikaji nace? Nasan Sadam! yafi karfina ballantana ke! Labiba itama Sayyadar don dai za'bin iyayensa ce shine dalili amma 'yan matanshi duk 'yayan manya ne masu fad'a aji a najeria."

Labiba tace"Ke dai ayi sha'ani kawai yo ni ina ruwana da wasu 'yan matanshi kawai ni in ina san abu nasan duk yanda zanyi na same shi...........!



Mammah bata nan taje kasuwa had'o kayan barka a cewarta komai da akewa maijego to sai anyi wa Lubabatu........ yana zaune a palo da waya hannunsa yana jiran ta kawo masa abinci ta fito daga kicin hannunta dauke da tire kayan abinci ne a jere....."Na jera maka a daining ko na kawo maka nan."

Yace."Kawo min nan." Ta isa inda yake ya dauke kafafunshi daga kan tevur din dake gabanshi ta jera abincin a nutse ta had'a masa komai a plate Macoroni ce da miyar kifi da kayan lambu sai farfesun kan rago wanda Mammah! tayi wa Luba sai kamshi yake lemo mai sanyi ta dauko masa da ruwa duk ta aje.....Ya fara cin abincin ita kuma ta kama hanya zata bar gurin yace."Ke! dawo in gama ki kwashe kayanki ko sai naje na sake kiranki sannan.'' Dawowa tayi ta zauna kujerar dake gefansa......A wayance ta dauki wayarsa tana dubawa yana kallonta ya kyaleta.....Test ta turawa kanta da kanta na zagi da cin mutunci ga abinda ta rubuta.

_Ke! ki fita da harkar mijina domin ba sa'anki bane idan kuma kin'ki ji to wallahi ni Sayyada sai nayi maganinki banza karuwa mai bin maxan mutane ni kad'ai ce matarsa har mutuwa kuma nice uwar 'yayansa! nice za'binsa kina wahalar da kanki ne domin ba auranki zaiyi ba mahaukaciya kawai na barki lafiya_

Sai da ta tabbatar test din ya tafi sannan hankalinta ya kwanta ta cigaba da duba wayar numbars ta shiga tana dubawa numbar mace guda ta gani yayi serving da *Hali dubu* Halima ce baya ga ita ba taci karo da numbar ko wace mace ba duk maza ne abokansa dana aiki........."Ke! wai me kike dubawa ne a wayar bani wayata."! ya fada yana mika mata hannu.

Mika masa wayar tayi tana zumbura baki yana cin abinci yana dube-dube a wayar test din data tura ya karanta tsaf!!! ranshi ya 'baci ya juyo a fusace! yace."Don Ubanki! waye ya saki."!? Shiru tayi domin jikinta ya bata yaga test din....Ya aje cokalin a zafafe! Yace."Ba magana nake miki ba? waye ya saki zaginta."? "To itama waye yasa ta tace." Tana sonka."? Ya kawo mata wani bahagon mari!! a firgice! ta kauce! tana mamakinsa sai huci yake ya mi'ka mata wayar tare da fad'in"Maza rubuta mata ban hakuri ko kuma yanzu in ragargaza ki."!! 'Kin kar'bar wayar tayi ta buge rigar ta ta juya ta nufi dakin jegon aunty Luba.....Binta yayi da kallo cikin mamaki....Sayyada kam! tana sane tayi masa haka so take taga ni shi zai bata hakuri ko kuwa.

Tana shiga dakin ta nutsu suna ta hira ta tsalleke can inda ta aje wayarta ta dauko

Please Login or Register in order to submit comment