Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so ba."
"Bana so yanzu."! ya fada murya a junkushe.! shiru tayi tana goge fuska......" Sayyada." ya ambaci sunanta ta amsa a hankali "Tashi ki bar gurin nan baki da amfani."
Kuka tasa tace"Kayi hakuri Yaya Sadam! naga baka da lafiya ne." "Babu ruwanki da rashin lafiya kawai ki bi umarnina amma tunda ba zakiyi shikeenan."

"Zanyi." tafad'a tana kallonshi....Girgiza kai yayi yace."Bana so kawai ka bar kusa dani malama." Gefan kirjinsa ta kwanta ya ture kanta tace"Kayi hakuri kaji." Shiru yayi mata.....Ya soma samun saukin abinda ke damunsa.....kawai sai yaji saukar hannunta kan joystick dinsa a zabure! ya tureta! tare da mikewa zaune yana hargagi!!!"Nace bana so malama! dole ne ki tashi ki bani guri me yasa lokacin da nake so baki ba sai yanzu."

Haushi yasa ta sauka daga gadon ta nufi bandaki wanka tayi ta fito ta bude jakar kayanta ta dauko duguwar riga ta bacci ta zura taje ta kwanta kan doguwar kujera tana kuka wannan wace iriyar rayuwa ce? mutum sai masifar tsiya! mutum babu uziri kullum cikin tashin hankali gaskiya halin Sadam ya soma damunta.

Yana jinta tana kuka yayi banza da ita yarinya kankanuwa ta jawo masa bala'i dole sai yayi wanka yanzu....bandaki ya nufa yayi wanka ya fito kirjinsa sai zafi yake haka dai ya daure ya kwanta yasan aiki ya riga ya 'baci kuma dole Dr sai ya gane wani abu ya faru........Kukan da takeyi ne ya soma damunsa"Sayyada." ya kira sunanta muryarsa a sama. Shiru tayi yace."Ko bakyaji ne." ? Banza tayi masa.....Ya dinga zanga tsaki yana juyi wai da me zaiji ne? ga sha'awa ga ciwo Allah kayi mana magani Ita dashi da kyar bacci ya dauke su.


Asubah ya tashi yana wani irin nishi! wanda shine ya tashe ta daga bacci ta mike da sauri ta isa bakin gadon.

"Yaya Sadam! sunansa take kira ya kasa amsawa sai kirjinsa ya rikewa.......Yana kiran sunan Allah Hawaye tuni sun soma tsere a fuskarta kofar fita ta nufa sam ba manta yanayin da take ciki.

" Sayyada." ya kira sunanta.....Da sauri ta dawo ta tsaya kansa jikinta sai kyarma yake yace."Karki fita da duhu a garin.''

"Yaya Sadam! dr zan kira." Ya girgiza yayi alamun kar ta kira dr din tace"To me yasa naga kana jin jiki dama naji tsoron kar ka fama ciwonka jiya."

"Nace miki ki koma ki zauna ko."! Ya fad'a a hasale! komawa tayi ta zauna tana kallonsa yana nishi! duk ta damu data kasa daurewa kawai sai ta zura dogon hijab dinta ta bude kofa ta fita da yake idanunsa a rufe yake sai rufe kofar ta kawai yaji..............Ya tsirawa kofar ido ransa ya baci wato dai sai da fita ya hanata taki jin magana idanunsa ya mayar ya rufe dama yasan dole ya tashi gurin mikin abun da yayi jiya ya wuce hankali wai nan ma don bai samu biyan bukata ba.

Tare Suka shigo da Dr ya isa bakin gadon yana dubashi gani yayi duk bandejin dake nannade da gurin ya warware duk ga alamun ruwa nan a jiki da jini da yake fita kadan kadan Dr ba yaro bane lokaci guda ya fahimci abunda ke da akwai Yace." Yallabai ya akayi haka ta faru."!? Sadam! ya dafe kansa bashi da tacewa shiru kawai yayi Dr yace"Yallabai mutukar zaka na motsa gurin nan to ba zaiyi yanda ake so ba kayi hakuri da komai ka warke tukkuna." Sadam! yace."Wai me kake nufi ne."? Dr yayi murmushi yace."Babu abinda nake nufi." Sadam yace "To kai dai kayi aikinka kawai." murmushi Dr yayi ya cigaba da akinsa......Shine ya taimaka masa ya mike tsaye har bandaki ya kaishi sannan ya fito yace."Madam ki cigaba da kula da Yallabai don Allah ko ya nemi wani abun kar ki biye masa." Sayyada dai kunyar duniya duk ta isheta......Sai bayan ya idar da sallah Dr ya hada masa tea mai kauri yasha da kanshi ya bashi magani ya kwanta sai da bacci ya daukeshi sannan ya bar dakin.....Sayyada ma sai sannan hankalinta ya kwanta taje tayi wanka ta fito ta shirya jikinta tsaf! ta zauna gefan gadon

Sulaiman ne ya turo kofa ya shigo yana sanye da suit kafafunsa sanye da rufaffen takalmi yayi kyau sosai dakin ya cika da kamshin turarensa mai tsada.

Koda idanunsa sukayi masa tozali da Sayyada kusa da Sadam! sai ranshi ya 'baci! ya had'e fuska kishi na damunsa da kyar yayi sallama ta amsa da sakakkiyar fuska.

"Yaya Sulaiman barka da zuwa." Ya amsa "Sannu Sayyada ya mai jiki." Tace"Da sauki ai bai jima da yin bacci ba."

Tsayuwa yayi a kansa yana jin wani irin kishinsa shifa yanzu bai'ki ace Sadam din ya mutu ba da zai fi kowa jin dadin hakan.

"Yaya Sulaiman ka zauna mana." Tafada cikin sanyin murya. Girgiza kai yayi yana ta'be baki yace."Sayyada kina ganin wannan rayuwa ta dace dake ko."? tace"Bangane ba Yaya Sulaiman." Sajansa ya shafa yace."Duk macan dake auran Soja to tana cikin hadari mai yawa da 'kananun shekarunki kike zaman jinya ina tausaya miki ke bakiyi cikakken karatu ba an cuceki anyi miki aure kin had'u da mugun mutum me son kansa."

Shiru tayi kanta a 'kasa yace."Ki zauna kiyiwa kanki Fad'a sam sadam! baya sonki tunda tuntuni ya nuna hakan a zahiri dole akayi masa." Sayyada dai ba tace komai ba addua takeyi Allah yasa kar Sadam! din ya tashi yaji abunda yake cewa tana gani kamar hakan bai dace ba dan uwansa ne amma yake aibata shi ashe dai ba Sadam! din ne kawai me mugun hali ba har Sulaiman din.



Kuyi hakuri da wannan 👏🏻



*Kika futar min da littafi Allah ya isa!/ Kika karanta baki biya kema Allah ya isa! Idan kina bukatar karanta littaffin zaki tura #400 ta wannan accont din......0542382124.....Binta Umar gtabnk*
My numbas 08089965176_07084653262


*BINTA UMAR ABBALE*

16/6/2020
22

"Sulaiman yace." Ni zan koma Sayyada amma ina so kiyiwa magana ta kyakkyawar fahinta ni tsakanina dake gaskiya ce da amana ina tausayawa rayuwarki ne." Tace."To Yaya Sulaiman zanyi tunani nagode." Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo fuska a sake yace."Mutuniyarki tace."A gaisheki da kyau." Sayyada tace"Ai nayi fushi da ita kowa yazo ya duba Yaya Sadam ban da ita."

'Bata fuska yayi yace."Shin bakya ganin lalurar dake tare da ita ne."? Da sauri tace"Eh kuma hakane fa amma dai duk da haka yanda suke da Sadam! ya dace tazo ta duba shi." Haushi da takaici suka rufe Sulaiman inda yasan amsar da zata bashi kenan da bai mata maganar ba.......Juyawa yayi ya fita tace"Ya Sulaiman Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da "ameen." yasa kai ya fice ranshi nayi masa suya dai-dai da 'kwayar zarra ya tsani yaga Sayyada na nunawa Sadam Kulawa, duk sai ransa ya 'baci.

Yana fita ya bude idonsa Sai da ta razana! ganin yanda 'kwayar idonsa ta sauya sai kace garwashin wuta da sauri ta sunkuyar da kanta 'kasa.

"Wane mataki kika d'auka dangane da shawarar da wancan banzan ya baki."!

Gabanta ya yanke ya fad'i da jin abinda yace kar dai duk irin maganganun da suke da Sulaiman yana jinsu. Allah yasa ba tace komai ba.

Tsawa! ya buga mata sam! ya manta gargadin da Dr yayi masa kan cewar ya dinga komai a hankali saboda lafiyarshi.

Jiki a sanyaye tace"To ai dai da kunnanka kana ji bance masa komai ba ko."

"So nake ki sanar dani matakin da kika dauka dangane da shawarar da ya baki." Ya sake maimaita mata tambayarsa ta farko.

Tana wasa da hannunwanta tace"Ni fa duk abunda ya fad'a jinsa kawai nakeyi ni babu wanda zai rabani da kai."

Ya watsa mata banzan kallo yana girgiza kai yace."Idan Sulaiman Sonki yake ni sai in sauwake miki ya aureki domin ni nasan ban d'ora miki iddah ba......! ni ba wawa bane na gane inda ya dosa dama kuma tuntuni naso na zargi wani abu dangane da kulawar da yake miki."

Tana kuka tace"Yaya Sadam! wannan wace iriyar magana ce kakeyi sai kace wani jahili irin wannan kalmomin da kake furtawa sai su kashe aure baka sani ba ka daina don Allah Ni nasan Yaya Sulaiman ba wai sona yake ba kawai kulawa c......"Rufe min baki dan Ubanki."! ya fad'a a harzu'ke! 'kokarin mikewa zaune yakeyi....Tayi saurin mikewa jikinta na 'bari tace"Ka tsaya kayi a hankali! da ciwonka."!!! "Ina ruwanki da ciwo na."? yafada yana gwalalo mata idanunsa masu dafi. Kasa tayi da kanta Yace" Har ina magana kina wani kareshi Nine zan fad'a miki wanene Sulamain ke baki san waye wannan ba to daga yau na fad'a miki duk sanda na sake ganin magana ta fatar baki ta had'aki dashi ranar sai na zaneki da blet wallahi suma tallahi jikinki sai ya fad'a miki."

"A gaskiya wannan bayi bane idan ka hanani magana da Sulaiman meye manufar hakan to ai sai kace kaima ka daina min magana tunda da kai dashi duk daya ne a gurina don haka ni ba zaka sanya ni nayi gaba da d'an uwana ba." Zuciyarsa ta dinga tafarfasa jin abunda ke futowa da bakinta lallai yarinyar tayi kawari ba tun yau ba yasan da cewa Sulaiman ya fishi matsayi a gurinta tunda gashi tana cewa dashi da sulaiman din daya suke a gurinta.
Zuba mata jajayen idanunsa yayi yana kallo ya rasa ma abunda zai ce mata....Ita kuma sai kwaranyar da ruwan hawaye take....."Ni na fad'a maka babu wanda zai zugani in rabu da kai saboda tun ban san kaina ba ban kai shekarun haka ba nake sonka kaunarka a cikin jinina take na tabbatar idan babu kai rayuwa ta ta lalac........"Get out."!! ya katseta a zafafe! da sauri ta kama hanyar fita daga dakin.....Wani irin nishi yake lokacin kankani ciwo ya dawo sabo wani irin haki! ya soma yi wai shin me yake damunsa ne yake ji tamkar an d'ora masa dotse mai nauyi a kirjinsa
*Kishi ne* Zuciyarsa ta bashi amsa tabbas idan hakane kuwa to zuciyarsa ta yaudareshi domin bai cancanci ya zauna yana kishin yarinyar da hankalinta ke kan wani ba, Yayi nadama matuka da zuciyarsa take kishin Sayyada...."Innalilahi wa'ina ilahi raji'un yake fad'a cikin zuciyarsa yana tunanin kuma wane irin mataki zai dauka kan Sulaiman wanda ya zame masa kad'an garan bakin tulu

Kanta a tsakankanin kafafunta tana kuka taji sautin tafiya takalmi 'kwas!'kwas! ta d'aga fuskarta idonta jage!-jage! da hawaye......"Halima ce cikin material mai sharara milk color anyi mata dinki rariya tayi rolling da mayafi mai totoci sai uban takalmi mai giya dake sanye a kafafunta hannunta pose dinta ce sa key na mota.....Ganin Sayyada na kuka sai taja tsaki ta tauna cingum din dake bakinta a ya tsine tace"Wahallaliyar banza da wofi kawai ni dama nasan *Man* babu abunda zaiyi dake 'yar 'kauye haka ruwan hawayenki zai 'kare a banza." Tana gama maganarta ta karka'da key din motar ta ta wuce ciki.

Sayyada ta bita da kallo zuciyarta na sake tafarfasa yunkurawa tayi zata bi bayanta sai kuma ta dakata tana nazari tasan halinsa tsaf! zai iya wulakanta ta a gaban Halima abunda ta tsana kenan wulakanci komawa tayi ta zauna jikinta sanyi kalau!!!! Wani irin kishi ne ke taso mata sai ta fara zargin wani abu ai babu tunanin komai ta mi'ke! murza kofar dakin tayi ta shiga.......Abunda ta gani yasa ta d'ora a hannu aka baki na rawa tace."Innalilahi wa'ina ilaihi raji'un! Duk suka juyi suna kallonta.......Halima na zaune dirshan kan gadon ta mike kafafunta shi kuma duk rabin jikinsa na jikinta sai shafa kwantaccan gashin kansa takeyi suna hira......Sadam! tayi bala'in shan kunu! a murtuke yace."Ke! dawowa kikeyi ashe dai baki da zuciya ko?ok kafin in irga biyar ki futa daga dakin nan ko kuma ranki ya 'baci."!! hawaye wani na bin wani tace"Yaya Sadam! duba fa da kyau kaga abunda kakeyi itafa ba muharramar ka bace ka yarda zata yaudareka! wallahi kaji tsoron Allah kema kiji tsoron Allah ki tashi ki fita."

"Ke! da tsoron Ubanki nakeji wa'azi zakiyi min? shin kin san yanda muke dashi ne ? da har kike wannan maganar! to bari kiji Wallahi duk sanda kika sake min magana makamanciyar wannan ranar sai na sanya an baki horo mai tsanani a bracck din nan, Sadam mijina ne nan da wani lokaci 'kankani sabida haka idan ma zaki kwantar da hankali ki kwantar ida ba zaki kwantar ba kece a wahale."!

Sayyada tace" Komai kikayi banyi mamaki! ba tsohowar guzuma an rasa miji ana bin mazajan mutane to ta Allah ba taki ba karuwar duniya."

A guje! Halima ta dirgo daga gadon tayi kan Sayyada mari ta dinga kwad'a mata a fuska har sai da hancinta ya fashe yana zaune yana kallonsu sai da yaga jini a hancin sayyadar sannan yayi magana" Ke Halima kyaleta ko yanzu kin nuna mata bambancin mutumin birni da 'kauye."!!!!!!!!! Wata iriyar nadama gami da dana sani suke kama Sayyada hawayen ma nemansa tayi ta rasa kawai ta 'kura masa ido tana kallo tabbas 'kiyayyar da yake mata ba 'karya bace tunda gashi ya iya fifita budurwarsa a kanta da take jininsa yana gani ta futar mata da jini amma bai ce komai ba sai ma bakar maganar da ya ya'ba mata hakane akwai banbanci tsakanin mutumin 'kauye da mutumin birni to Asalin kowa 'kauye da har yake wani tun'kaho shima daga kyauyen yake........"Murya a sar'ke tace"Yaya Sadam! nayi nadamar auranka!!! Yau na 'kara tabbarwa da kaina cewa baka sona! to kar ka manta da cewar Wawa! shike mance asalinsa Insha Allahu zan koma *Dabi* ni nan ce mahaifata data iyayena na barka lafiya." Tana gama maganar ta fita daga dakin.

Maganganunta sun ratsa shi sosai amma saboda ya tabbatar mata da cewar ita d'in ba a gabansa take ba yasa ya'ki yunkurin hanata tafiya yana kallo ta fice daga dakin ranshi idan yayi dubu ya 'baci wayarsa ya dauka zai kira Habu sai kuma ya fasa zuciyarsa tace masa ka kyaleta duk inda zata je taje! Halima kuwa domin ta dauke masa hankali sai ta shiga jansa da hira tana tarairayarsa da shafa sumar kansa jinta kawai yake amma kwata kwata hankalinsa da nutsuwarsa ba'a kanta suke ba.


Sam bata sha wani wahalar fita daga bracck din ba saboda masu tsaron gurin sun gane ta kuma sun san matsayinta a gidan shiyasa suka barta ta fita kai tsaye.


Tafiya tayi mai tsayi sannan ta tsaya ta samu abun hawa Unguwar dosa tacewa me babur din yace shiga muje kai tsaye ta shiga cikin babur din suka tafi har bakin gate ya kai ta ta fito tace"Bari na kar'bo maka kudin yi hakuri don Allah."
Yace."Babu damuwa." Tana shiga gate din Hajiya Fatsima da Baban gida na kokarin shiga mota sai ta dakata tana fad'in"Sayyada Allah yasa dai lafiya? yanzu muke shirin zuwa gurin ku.....Tace"Lafiya Mammah d'an bani d'ari biyu in sallami me babur din da ya kawo ni."! Mammah ta fito da kudi cikin jaka ta mika mata tana nazarinta.


"Ga canjin naki." mai babur din ya fad'a tace"Ka barshi kawai." dariya yayi yace."Ni idan ba zaki damu ba ma da kin rike kudin kin bani numbar ki ita nafi bukata." kallonsa tayi da mamaki kawai sai ta bar gurin....Mai babur ya girgiza kai yana lumshe ido gaskiya babyn ta had'u! babu dinsa yaja ya bar gurin yana santin Sayyada da yanda Allah yayi mata kyau.

Tana isa ta tadda Mamamh na tsaye na jiranta ganin irin kallon da takeyi mata ne yasa ta saki fuskarta tace"Mammah cewa nayi bari na dawo gida nayi wanka sai na koma sam bana sakewa a can wallahi."

Mammah ta saki ajiyar zuciya tace"Koda naji ai na dauka wata matsalar ce toko mu jiraki idan kin gama sai mu tafi tare...."Mammah kuje kawai kar na tsai dake insha Allahu yanzo yanzu." Tace"To babu laifi ."Dubu daya ta mika mata tace"Sai ki hau abun hawa ki tawo." ta karba tana godiya....Sai da motarsu ta fita daga gidan sannan ta nufi sashensu wato sashen Yaya Sadam! dake gidan......Wanka tayi a gurguje ta shirya cikin atamfa a gurguje take komai tsaf! ta shirya kayanta cikin akwati ta yafa mayafi akwatin ta ja ta fito ko dakin bata kulle masa ba ta nufi gate maigadi na kokorin bude kofa taja ta tsaya tana adduar Allah yasa Sulaiman aikuwa shine ya shigo cikin dan'kareriyar motarsa 'kirar zamani....parking yayi dai-dai inda take tsaye ya sauke glass din motar yace"Sayyada lafiya ko asibitin zaki koma."!? Fashewa tayi da kuka! da sauri ya bud'e motar yace."Shigo daga ciki ki fad'a min menene?

Ta shiga motar yace."Goge hawayenki ki fad"a min waye ya ta'baki!! Sayyada na jin dad'in yanda Sulaiman ke rarrashinta abinda Sadam! bai iya ba sai masifa da hantara da bakin hali.

Hawayen fuskarta ta goge a hankali tace"Yaya Sulaiman don girman Allah ka kaini *Dabi* yanzu."


Ya kalleta da mamaki! a fuskarsa yace"Saboda me? me akeyi da zaki dabi idan ina lissafi dai-dai ina cewa yau satinki daya da kwana daya barin ki garin to me zaki koma kiyi a can kuma.

"Yaya Sulaiman ni dai nace ka kaina *Dabi* nan ne asalina nan ne tushena bana kaunar zama a garinan." Ta karashe maganar tana kuka wiwi!!! Hankalinsa ta tashi mutuka idan akwai abunda ya tsana a duniya bai wuce ganin kukan Sayyada ba sai yaji kamar ya rungumeta ya rarrasheta jikinsa na rawa yace."Yi shiru daina kuka zan kaiki yanzu bana son ganin hawaye na zuba a fuskarki Sayyada." Shiru tayi tana goge fuskarsa.......Motar yaja ya fita daga gidan ba tare da tunanin komai ba ya dauki hanyar Jigawa zuwa garin *Dabi* sai da sukayi nisa sosai sannan ya soma bugun cikinta aikuwa ta fad'a masa yanda sukayi da Sadam! da yanda yake cewa ta daina kulashi tanayi masa magana da irin wulakancin da yayi mata gaban budurwarsa.......! Sulaiman yayi murumshi cikin sigar yaudara yace."Yanzu dai kin gane abinda nake so ki gane ko? dama na fad'a miki Sadam! ba sonki yake ba kinga ya nuna miki budurwarsa ta fiki daraja a gurinsa yanzu dai aiki ya rage naki kiyi kokarin ganin kin bar hannunsa kizo zan inganta miki rayuwa."
Shiru tayi tana nazarin maganarsa.

Yace." Sayyada ya kikayi shiru ne.",A hankali tace"Ya Sulaiman ina tunanin maganarka." Yace."Da kyau! babyna dama ina so nayi miki wata tambaya." Tace"To." Shiru yayi yana nazari....ka tsaham! taji yace."Ina fatan dai baki sallamawa Sadam! kanki ba ko."? duk da take yarinya ta fahimci abinda yake nufi amma sai ta bagarar da magana da fad'in"Ya Sulaiman ban gane maganarka ba." Yace."Ina nufin Sadam! baiyi wata mu'amula ta aure dake ba shine abinda nake nufi." Kai a kasa tace"Babu abunda ya shiga tsakaninmu.' Sanyi yaji na ratsa shi yace."To duk rintsi kar ki yarda yayi miki wani abu zai cuceki ne karshe ya sake ki tunda ya soma furtawa." Tace"To Yaya Sulaiman zan kiyaye. Yawwa ni ina so ne rayuwarki ta inganta." Yafada yana kallonta da wani munafikin murmushi. Wanda ita bata gane ko na meye ba....Tace"Nagode Yayana Allah ya kara zumunci." ya amsa da "ameen ya rabbi kanwata."


****
Sayyada bata dad'e da tafiya ba ya sallami Halima dalili! kawai yana so ya samun nutsuwar zuciya hakika Sayyada da Sulaiman suna so su tashe shi daga aiki duk sanda ya tuno da irin zugar da Sulaiman keyiwa Sayyada sai yaji kamar ya had'iyi zuciya ya mutu wai d'an ukanka shine ke cin dunduniyarka "Ke!! duniya!.......Sallamar Mammah ce ta dawo dashi hayyacinsa ya mike a hankali yana amsa sallamar Tana zama yace." Mamnah Sayyada taje gida ko."!? tace"Eh ina shirin fitowa sai gata ta shigo tace wanka zatayi nan bata sakewa sosai."

Ajiyar ya sauke dama duk abun ya dameshi yana tunanin kar tayi wani gurin Mahaifiyar tashi ya gaisar ita kuma ta tambayi lafiyar jikinsa......Da kanta ta bashi abinci suna hira kimanin awa guda Sayyada bata dawo ba Mammah tace"Allah dai yasa ba abun hawa ta rasa ba shiyasa nace ta bari mu tafi tare ta'ki, dole in koma gida tunda dai dravar daya ne baban gida zai kawo ta." Yace."Shikkenan Mammah a sauka lafiya." Tace."Ka kula da shan magani sadam! dan na lura baka kulawa da lafiyarka." murmushi yayi yace."Insha Allah Mammah."

****

Ganin Sayyada da jakar kaya tana ja sai Baba Ladidi da Baba Marka sukayi mamaki! kuma lokaci 'kankani suka fahimci akwai wata 'akasa domin dai su ba 'kananun yara bane....Sayyada ta shige da jakar kayanta dakin Baba Ladidi shi kuma Sulaiman ya zauna suna gaisawa da juna...........




_Mu tara a gaba nasan zakuyi mamaki ko? to gashinan dai babu yawa ayi hakuri dani don Allah!_





_*Kika futar min da book Allah ya isa! Kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa!.......account numbar 0542382124.......Binta Umar gtbank.......Whasap numbar 08089965176 _07084653262*_





17/6/2020





*BINTA UMAR ABBALE*
: 23
Tana cika da batsewa ta fito tsakar gidan ta samu gefe guda ta zauna tana gaishesu duk suka amsa suna me kallonta cike da mamaki!
Baba Marka tace"Jikina na bani wannan zuwan naku babu alkairi a cikinsa me yake faruwa."?

Sayyada ta fashe da kuka da shashsheka! Baba Ladidi itama sai ta fashe da kuka tana fad'in "Allah yasa dai wannan yaro ba sakin yarinyar nan yayi ba domin dama ni tuntuni jikina yake bani akwai matsala dangane da al'amarin." Sulaiman yace."Haba Baba ki daina kuka don Allah abun duk bai kai haka ba Sadam bai saki Sayyada ba har yanzu tana a matsayin matarsa."

Baba Marka tace"To alhamdullahi ku fad'a mana abunda ke faruwa." Ya kalli sayyada a nutse yace."To ke kina ji sai ki sanar musu dalilin ki na gudowa gida."

Hawayen fuskarta share tace"Baba na hakura da auran Yaya Sadam! baba marka tace"Kan wane dalili Sayyada ashe kina so ma'kiya suyi mana dariya ko."? idanunta yayi rau! rau! tace"Baba Ya Sadam! baya sona kullum sai ya zageni ya kyareni karuwarsa ma ta fini daraja a gurinsa kuma wai dole sai na daina kula Yaya Sulaiman! Baba Ladidi ba zan iya da halin Ya Sadam ba yana kwance bashi da lafiya amma ya'ki barin hankalin kowa ya kwanta kullum tashin hankali babu zaman lafiya." Tana hawaye take maganar.

Baba Marka tace"Ikon Allah me ya samu Sadam! din naji kince yana kwance babu lafiya.....Sulaimai yayi saurin cewa"'Yan boko haram! suka harbeshi a kafada kin san shi da shegen rawar kan tsiya wai dole ya isa haka zai je ya cuci kansa a banza a wofi."

Jin abunda ya samu Sadam! din yasa baba ladidi fashewa da kuka tana fad'in"Yanzu abunda ya samu Sadam! kenan amma a rasa wanda zai fad'a mana a cikinku wato idan ma mutuwa yayi shikkenan sai dai ku aiko mana ya mutu! ke Sayyada ban san baki da hankali ba sai yau! ace mijinki alburushi ya huda masa kirji ki iya tsallake shi ki tawo nan uwar me zakiyi mana a gida yarinya mara hakuri malam."!

Sulaiman yace."A'a Baba abi komai a sannu a hankali Sayyada ma tana da 'korafi ai gashi ta kawo muku 'korafinta kun juyawa magana ai idan daddawa da wari to 'bera dole yayi sata ya kamata ku duba maganar nan fa.

Baba Ladi na kuka tace"Habawa Sulaiman ai lalura ta wuce komai wallahi ban san da cewar kaima baka da hankali ba sai yau kai da ya dace ka dinga tausarta kaine zaka daukota ka dawo da ita gida yanzu meye amfanin abunda kayi."

Yace."A'a baba kar kiga laifina ni mutum ne me baiwa mutum 'yan cinsa bana so in ga ana muzgunawa mace ko wace irice ballanata sayyada da take jinina hakika Sadam! na zalintarta dan dai kawai kun ce dole sai kun aura masa ita ne ni dai ina me baku shawarar tun wuri ku warware auran nan don Wallahi Sadam! ba son Sayyada yake ba yana da budurwarsa Halima sunyi alkawarin auran juna."


Baba Ladidi tace"Wallahi mutukar ina raye a duniyar nan babu mahalukin da ya isa ya warware auran nan sai dai idan Sadam din ne yace ya saketa to wannan dole in hakura amma auran Sayyada da Sadam! mutuwa ce zata raba insha Allah." Sulaiman yaji d'acin maganarta sai kawai ya girgiza kai yace."Ai shikkenan baba wanda baiji bari ba....! Tace"Haba Sule ai dole Sadam! ya hana Sayyada shiga sabgar ka saboda da alama kaine kake zugata har yaushe akayi auran ma da za a fara yaji ba zai yiwu ba." Baba Ladidi fad'a take tamkar ta ari baki "Yau yau d'in nan zaki koma d'akinki kije ki cigaba da jinyar mijinki to kaji."""! Da jin abinda Baba ladi tace sai Sayyada ta fashe da kuka tana fad'i " Allah kuwa baba ba zan koma sai yazo da kansa sai ya gane ina da matsayi a gurinsa

Please Login or Register in order to submit comment