Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan sai ya tabbatar muku da cewa *Dabi* nan ne tushensa."

Baba Marka ta ri'ke baki tana fad'in" Oh! kiji wata magana a gurin Sayyada shi Sadam! din ne da bakinsa yace miki *Dabi* ba nan ne asalinsa ba ko 'ka'ka."!?

"Eh mana yana nunawa budurwarsa haka sannan suna kirana da 'yar 'kauye to shima dai 'kauyen ne asalinsa."

Baba Ladi tace"Babu shakka kema kinyi magana Sayyada ni na tsani mutumin da zai dinga kushe asalinsa Sadam! zai zo ya same ni har gida ku rabu dashi tabbas ba zaki koma ba sai yazo da 'kafafunsa."

Ajiyar zuciya ta sauke taji dad'in yanda Baba Ladidi ta fahimce ta.....Shi kuwa Sulaiman haushi da takaici ne suka cika masa zuciyarsa yayi musu banza yana ji suna hira da maida magana ya sharesu tunanin yanda zata 'bulle masa kawai yake da yaga babu haza sai ya mi'ke......Baba Marka tace"Ina zakaje kuma yanzu nake shirin dora abinci." Yace."Idan kun girka kuci abinku ni na tafi." Duk suka bude baki suna kallonsa cike da mamaki!

Sai bayan fitarsa sannan suka dauke kansu daga hanyar da yabi suka cigaba da hira suna mamakin yanda ya sauya lokaci guda Sulaimn bai ta'ba zuwa *Dabi* ya tafi a ranar ba sai ya kwana biyu yake tafiya amma yau ko awa guda baiyi ba ya juya lallai akwai wata 'akasa.


****

Hankalinsa kaf na kan kofar shigowa daga yaji motsi sai ya dauka itace Hjy Fatsima tace"Anya Sayyada ta samu abun hawa kuwa? bari muje kawai yanzu Baban gida zai kawo ta." Kai kurrum ya iya d'agawa Har mahaifiyar tasa ta fita ya kasa cewa komai jikinsa ke bashi babu lafiya.....Koda Hajiya Fatsima ta koma gida duk ta duba ko ina bata ga Sayyada ba sai ta fito farfajiyar gidan tana tambayar mai gadi yace."Hajiya naga Alhaji Sulaiman ya dauketa a mota. sai ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki gidan tayi tunanin Sulaiman din yaje mai da ita gurin Sadam din ne shiyasa hankalinta ya kwanta.


Kusan awan Mammah biyu da tafiya ya rasa abinda ke damunsa shiru har yanzu bata dawo ba ya mike tsaye yana zagaye dakin hankalinsa duk ya tashi......wayarsa ya dauka ya kira numbar Mammah ta dauka kafin yace."Komai tace"Sulaiman ya kawo ta ko."!? Yace."Ban gane ba Mammah."! tace."Ina nufin Suleiman ya kawo Sayyada domin da na dawo mai gadi yake shaida min da cewar Sulaiman din ya dauketa a mota." Gabansa ya fad'i le'bansa na rawa yace."Bai kawo ta ba."! Tace"A'a bai kawo ta kamar yaya? ina ya kaita to? shiru yayi mata sai ta kashe wayar hankali a tashe ta fara kiran wayar Sulaiman d'in.....Lokacin yana kan hanyar dawowa gida tace"Sulaiman ina Sayyada."? kai tsaye yace."Tana *Dabi."* Hajiya Fatsima ta sanya salati tace"Me yake faruwa ne? me taje yi a *Dabi."?* yace."Mammah ki bari idan na dawo mayi maganar yanzu ina kan hanya. " Tace."To Allah ya saukeka lafiya."

Yana kashe wayar kiran Sadam! ya shigo sai da ta kusa katsewa ya dauka......."Ina Sayyada."!? yafad'a murya a sama! Kai tsaye yace."Tana can *Dabi."*
"What!." Yaf'ada jikinsa na kyarma! Sulaiman yace."abunda kunnanka ya jiye maka! Sayyada ba zata zauna a cikin irin wannan halin ba kana fifita yarinyarka kanta wannan cin zalina ne da shiga hakki duk sanda ka san muhimancinta kaje ka dawo da ita."

Wani irin jiri ne yake nema ya kayar dashi a gurin yace."Yanzu kana so ka sanar min da cewa kaina ka jagoranci tafiyar ta ko 'ka'ka."!? "Kwarai kuwa yanzu na kaita har na juyo ina kan hanya zuwa gida."

Murmushi yayi mai ciwo yace."Kasan wani abu Sulaiman."? Yace."Sai ka fad'a." Wani murmushin ya sakeyi kana yace."Komai nacin ka! komai binbininka! komai mayatarka! ko mai sharrinka! Sayyada tayi maka nisa! Wutsiyar ra'kumi! tayi nesa da 'kasa! duk abunda kake ciki na sani tuntuni kana son Sayyada kana min zagon 'kasa a matsayinka na d'an uwana da ya sha nono ya bani Duk maganganun da kazo ka shirya mata jiya a kunne na wanda kai duk a tunaninka ko bacci nake hummm! kayo shuka a idon makwarwa! Sule! Sayyada tafi 'karfinka mutukar ina raye a duniya duk inda za'aje za a dawo da gida ni Sadam! sai na nuna maka kai 'karamin d'an akuya ne."!!!! 'Kit! ya kashe wayar......Sulaiman ya gangara bakin titi yana sakin wani irin nuffashi kan motar ya buga da karfi yana fad'in"Wannan yaron matsiyaci ne! ni yake fad'awa wannan maganganun babu shakka zai gane cewar tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya amma sai yayi dubu bai fito ba zasu zuba dashi dashi sai ya kassara masa rayuwa.


Yana kashe wayar yayi jifa da ita gefe guda zama yayi gefan gadon ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa wai Sulaiman ne ke son matarsa shin wannan wace iriyar rayuwa ce ? uwa daya uba daya yana cin dunduniyarsa! Innalilahi wa'ina ilahi raji'un!


***

Hajiya Fatsima na zaune zaman jira shigowar Sulaiman ya shigo da sauri ta mike tsaye yace."Mammah ki zauna naga duk kin tashi hankalinki." Tace"Ya zanyi iya zama na kwantar da hankalina sulaiman ina yarinyar mutane."? Yace."Sayyada fa tana *Dabi* tace"Kan wane dalili ka kaita *Dabi* me akayi mata? Yace."Zauna nayi miki bayani." Zama tayi tana kallonsa yace."Mammah na shigo gidan nan ba tarar da Sayyada zata fita da jakar kayanta tana kuka da kyar na rarrasheta ta shiga mota na tambayeta abunda ke faruwa tace ba zata fada min ba sai na kaita *Dabi* nace ni kuma ba zan kaita ba sai ta sanar min da komai tace to idan ban kaita ba wallahi zamu nemeta mu rasa wannan magana data fada sai ta bani tsoro kawai sai na yanke shawarar kaita in yaso idan munje ta fad'i dalilinta sai mu dawo saboda nasan babu yanda za'ayi Baba Ladidi ta barta ta zauna......Sai da muka isa take shaida mana cewar Sadam! ke nunawa karuwansa ita bata da mahimanci a gurinsa ya sanya daya daga cikin karuwansa ta doketa har ta fitar mata da jini babban abunda ya tayar min da hankali shine wai ya hanata kulani ko gaisheni bai yarda tayi ba saboda yana zargin wai ina sonta Mammah raina ya 'baci! mutuka me zanyi da matar d'an uwana? da jin wannan maganar sai Baba Ladidi tace"Sayyada ba zata dawo ba sai yazo da kansa ya nuna musu mahimancita a gurinsa....Yanzu kafin shigowata Sadam ya kirani a waya ya 'kare min zagi Mammah na rasa abunda ke damun Sadam a rayuwa."

Hajiya Fatsima ranta yayi masifar 'baci! da jin abunda ya faru wai me yasa ko wace iriyar matsala ake samunta ta 'bangaran Sadam! ne? Wannan karon dole ne ta nuna masa kuransa babu shakka itama tana goyon bayan Sayyada ta zauna har sai Sadam din ya gane tana da mahimanci a gurinsa kuma dole ne ta nuna masa kuskuransa kan abinda yayi.

*****

Sayyada da 'kyar taci abinci ta kwanta kan gadon Baba ladi tana share hawaye a yanda take son Sadam! bata ta'ba tsammanin zai fifita budurwarsa a kanta ba ai babu komai duk da tana bala'in sonsa dole sai ta nuna masa kuransa sai ta nuna masa bambamci d'an kyauye da d'an birni zata nuna masa shima d'an kyauye yasan muhimancin kansa.


Sai kusa karfe uku na rana ta tashi daga bacci tayi wanka ta shirya ta fito baba Marka ta dauko mata dambun masara wanda yaji zogale da albasa da gyada gai man gyada zuryan sai kamshi yakeyi ta d'ebo mata ruwa randa mai sanyi sai lalla'bata sukeyi taci dambu sosai kana ta zauna suna hira daga zarar ta tuno dashi sai gabanta ya yanke ya fad'i!!! Yanzu ko wane irin hali yake ciki oho Allah dai ya dinga kula da kansa yana shan magani kan lokaci tasan halinsa sam bai damu da lafiyarsa ba, kaf tunaninsa ya dame ta sai ta mike salau!salau! taje ta kwanta had'e da rungume pillow tana kuka "Ya Sadam! ban so na barka ba ina sonka kai kuma kana nuna min tsana me nayi maka na damu da lafiyarka kai baka damu dani ba." Zancen zucci takeyi har ya fito fili baba ladi tana jinta sa'ilin da ta shigo dakin bata ce mata komai ba ta dauki abunda zata dauka ta fita daga dakin.


*****
To kamar yanda take ciki cikin damuwa shima haka yake cikin damuwa domin ko da Captain Habu ya shigo sai da ya fada masa halin da ake ciki Captain Habu ya nuna masa kuskuransa kan abinda yayi kana yace shi bai ga laifin Sayyada don ta tafi ba sai ya samu me jinyarsa.....Kaca!kaca sukayi dashi kan yace Sayyada bata da laifi shine yaji haushinsa.....Halima ma kasa gane kansa tayi ko tazo gurinsa korarta yakeyi ya gwammace ya zauna shi kadai a dakin yana tunanin mafita.......Sulaiman kam ko da wasa bai sake zuwa dubashi ba saboda yasan baxa su kwashe da dadi ba dalili duk laifi an taru an dorawa Sadam! din a maimakon ya kashe wutar a'a kullum 'kara ingiza iyayen nasa yake suna ganin laifin Sadam din abin duniya yayi masa yawa dan ma jarumin namiji ne baya sa damuwa a ransa......Mammah ta daina zuwa duba shi sau biya a rana yanzu sau daya take zuwa da safe shikkenan sai wata goben kuma hakan bai dameshi ba burinsa kawai yaji sauki ya koma bakin akinsa Sayyada kuma da suka kama suka rike suje su jikata su sha yayi rantsuwar sai dai su gaji su dawo da ita kuma har abada ba zai saketa ba kuma idan ya samu wacce hankalinsa ya kwanta da ita ya aura sai me.!?


****

Sayyada yau kwanata biyar da zuwa *Dabi* ta soma raina kanta domin har 'yar rama tayi sabida ta kwallafa ranta kan Sadam! kullum dashi take kwana a ranta duk ta rasa ya zatayi sai ta 'buya a daki taci kukanta ta koshi Baba ladidi ta gane duk halin da take ciki bata ta'ba tanka mata ba idone nata gaba idan ance ta sake yin yaji tayi tunda gashi tun ba'aje ko ina ba ta raina kanta shi kuma Sadam! din zai zo ya same ta ne."!


Cikin hijab ta fito Baba Marka na kad'in lagwani tace"Ina zaki je kuma."!? tace"Gidansu Ummi." Baba Ladidi na kicin tana kad'a miya tace"A'a Sayyada kin san dai kina da aure yanzu ko bana son shashanci kuma ni bana son ki fita saboda gudun surutun mutane ki koma ban yarda ki fita ba."

Tace."Bafa dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo." "Eh duk da haka dai ki koma kar ki fita idan kuma ban isa ba to shikkenan." Tace."To baba bari na shiga 'kofar su Amina na sami yaro sai ana aikashi gidansu Ummi din." Baba Marka tace"Haba Sayyada wa zaki fadawa halinki koma dai ki zauna ni bari na samo miki yaron." Baba marka ta mike ta dauki hijab ta zura Ta fita Sayyada ta koma ta zauna sai kumburi take.

Baba Marka suka shigo da 'kanin Amina baballe tace to ga yaro na samo miki ki aike shi.....'Daki ta shige ta 'kwalawa yaron kira ya daga labule ya shiga tace"Kai Baballe kayi maza kaje gidansu Ummi kace tazo yanzu nazo garin."

Baballe yace."To." ya fita kwanciya tayi tana tunanin shawarar data yanke.........Minti goma Ummi ta shigo suka gaisa dasu Baba tace"Ina Sayyada ko dai karyar Baballe ce." Baba marka tace"Tana cikin daki ki shiga." Ummi ta bankada labule ta shiga tana Sayyada kina ina."? Sayyada ta rungumeta suna dariya Ummi ta cikata tana kallonta Sayyada kinyi kyau sosai." Dariya Sayyada tayi tace"Ummi zauna muyi magana dake." Ummi ta zauna tana kallon Sayyada abun sha'awa.

Sayyada tace"Dallah wai kallon me kike min ne." ? Ummi tace"Gani nayi kinyi 'kiba Yau kwanaki goma sha biyar ko."? Sayyada tace"Eh Sayyada ta zayyane wa Ummi abinda Sadam! ke yi mata Ummi tace"Lallai ma Yaya Sadam! din nan dan wulakanci ne wallahi gwara da kika gudo gida idan ya damu dake sai yazo ya baki hakuri." Sayyada tace"Lallai Ummi baki san waye Ya sadam! ba miskiline wallahi ba zai bani hakuri ba ke nifa yanzu tunaninsa ne yayi min yawa na rasa yanda zanyi kullum da kyar nake bacci." Ummi tace"To me kike so ayi yanzu."

Sayyada tace"Gurin Malam Bashir zaki je ki kar'bo min numbar wayarshi sai muje inda ake kiran waya na kirashi Allah Ummi muryarsa kawai nake so naji gashi bashi da lafiya kin san 'yan boko haram! sun harbeshi a kafad'a."! Ummi ta dafe kirji tace"Da gaske kike Sayyada."!? Tace"Wallahi da gaske nake yana kwance a asibiti fa." Ummi tace"Amma shine kika tawo kika barshi kai Sayyada."

Sayyada tayi rau! rau! da idonta tace."Nima yanzu nake nadama tausayinsa nakeji kuma ina tausayin kaina ni nafi so ya gane mahimancina."

Ummi tace"To yanzu idan kin kirashi a waya kice masa me."?

Sayyada tayi shiru tana tunani tabbs bata da abunda zata ce masa....Tace."Ummi ke dai kiyi kokarin kar'bo min numbar ni nasan abunda zance masa."Ummi tace"To bari naje gidansu Malam Bashir din Allah yasa yana nan."

Ummi ta mike ta fita, Sayyada ta koma ta kwanta tana addaur Allah yasa a sami number a gurin Malam Bashir d'in.




18/6/2020




_*Kika fitar min da book Allah ya isa!/Kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa! Accont numbar......0542382124........Binta Umar gtabk.....Whasap numbar 08089965176 _07084653262*_
24

Ummi ba tayi minti ashirin da fita ba sai gata ta dawo kai tsaye dakin baba ladidi ta nufa sanin da tayi cewar Sayyada na ciki aikuwa Sayyada najin sallamarta ta mike zaune "Ummi Allah yasa kin samo numbar."
Ummi tace"Sayyada naje gidansu malam bashir ance bai dade da fita ba." Sayyada tayi rau! rau da ido" Wallahi Ummi nasa rai! ni kadai nasan abinda ke damuna a cikin zuciyata." Ummi tace"lallai Sayyada kina son Yaya Sadam! da yawa dama shine yake sonki da kinji dadi." Ummi shima yana sona wallahi kawai miskilancinsa ne yayi yawa yana ganin kamar idan ya nuna min so ya girmansa ya fad'i a gurina."

Ummi ta ciro hannunta dake cikin hijab tana dariya da sauri sayyada ta fizge takardar hannunta tace"Ummi amma kin shammace ni wallahi na dauka da gaske kikeyi." Ummi tace"Don inga yanda zakiyi ne gashi kuwa har kin soma kwalla zakiyi kukq sai kace wani ne yace ki gudo ki barshi." Sayyada ta kai mata duka tana dariya....Ummi tace"Kin san me zamuyi."? Sayyada ta girgiza kai tace"Shekaran jiya naje gidan Mariya naga mijinta ya siyo mara karamar waya sabuwa muje can sai kisa kati ko d'an hamsin ne ki kirashi." Sayyada tace"Alhamdullahi Ummi kin kawo shawara me kyau shiyasa nake sonki duk cikin kwayena."

Sayyada Ummi tare suka fita lokacin baba ladi na tuka towo baba marka na daura alwala a bakin rijiya Sayyada tace"Baba wai ashe Mariya ce tayi 'bari ban sani ba sai yanzu Ummi take fad'a min don Allah ki barni inje na dubata." Baba ladi tace"Sayyada bakya bari ayi sallah ba rana tayi sanyi sai kije." Tace"Haba baba nan da nan bafa dad'ewa zanyi ba." Tace"aishikenan sai kin dawo ace muna gaisheta kafin muzo."

Sayyada tace"Zan fada mata in Allah ya yarda." Suna fita suka ci karo da Amina ta fito daga 'kofarsu ta saki fuskarta sosai saboda taji labarin duk abunda ya faru da sayyadar shiyasa take farin ciki Nunawa tayi kamar bata san komai ba tace"Sayyada yaushe kika zo."? Itama Sayyadar bata nuna mata komai ba tace"Yau kwanana biyar da zuwa." Amina tace"amma shine baki shigo mun gaisa ba." Tace"Allah ne bai nufa ba." Gaba tayi Ummi tabi bayanta Amina ta ta'be baki tare da fad'in"A dai juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe insha Allahu yanda na rasa Yaya Sadam! kema sai kin rasa shi.


Mariya na kwance kan ledar tsakar dakinta tana malelekuwa laulayi takeyi amma saboda sharri irin na Sayyada ta 'kaga mata 'bari!

Mariya ta dinga ihu!! tana rukunkume Sayyada tace"Kawata yaushe kika zo iyee! kinga yanda kika girma kuwa don Allah cire min hijab dinki na gani sun fito." Sayyada tace"Mariya kyaleni don Allah." Mariya tace"Wallahi ba zan kyaleki ba sai kin sanar dani abinda ta wakana nima ai haka kike titsiye ni da tambaya.

Mariya sai da tasan yanda tayi ta cirewa Sayyada hijab ta kurawa kirjina ido sai ta kwashe da dariya tana kallon Ummi tace"Duba ki gani Ummi wallahi nonowan Sayyada sun 'kara kumari lallai sunji matsa da luguda." Ummi ta dinga sheka dariya tana kallon Sayyada ita kuwa shan kunu tayi tace"Bana son iskanci don Allah ku saurara haka." Duk suka saurara tace"Ke Ummi kamar baki san abinda yake damuna ba kina min dariya sai kace shashasha! Ummi tace"A"a kyaleni inyi dariya ta ai abun dariyar akayi." Kwafa tayi tace"Mariya ina wayarki take." Tace "gatacan kan mudubi menene? " Da kudi a ciki ko babu." Mariya tace"Da akwai dazu Saleh ya sanya min." Tace"Yawwa bani aro." Mariya ta mika mata wayar ta fara daukar numbar cikin wayar sai da taga daukar numbar kuma zata kira gabanta ya hau faduwa ta dago tana kallonsu "Me zan ce masa dan Allah."? wai tambayarsu takeyi....Mariya tace" Waye? dake bata san abunda ke faruwa ba Ummi tace"Au! dama baki shirya abinda zaki fada masa ba." 'Daga kai tayi kamar wata sokuwa Ummi tace"To kawai ki kirashi kice kece kiyi masa ya jiki." Sayyada ta fara kiran wayar hannunta na kyarma....Ringing takeyi bai dauka ba sai dab da zata katse ya dauki wayar tana jin sautin muryarsa ta sauke ajiyar zuciya wacce ta sanya jin wata iriyar kasala ya nemi gefan gado ya zauna tare da sassauta muryarshi yana fad'in "Salamu alaikum da wa nake magana."!? " Say.....Sayyada ce."! Ta fad'a a hard'e! wani irin yarrrr! yaji a jikinsa ya lumshe ido tare da kashingid'a gefan gadon yace."Sayyada dai ta *Dabi."*? Tace"Eh." "okey." kawai yace yayi shiru da bakinsa kudin wayar nata tafiya ta kasa cewa komai shi kuma sai sauraranta saukar numfashinta yake.....Mariya tace"Ke Sayyada karki 'karar min da kudin waya gaskiya nima da 'kyar na samu aka samun katin dari." Cikin inda-inda tace"Dallah! ba zasu 'kare b.....gyaran murya yayi ya sanya gabanta fad'uwa! Yace"Wayar wa kika ara."!? Ta 'kawata ce."! "okey to kin san baki da abinda zaki ce min kika kirani a waya kina 'karar mata da kudi a banza meye amfanin hakan." Shiru tayi yace."Yayi ni zan kwanta sai anjima ko." kafin ma tace wani abu ya kashe wayarsa.....Sakato tayi da waya a hannu idanunta yayi rau!rau! da ruwan hawaye sai ta juyo kan Mariya tana surfa mata masifa "Akin banza aikin wofi Mariyar nan kin bawa mutane kunya me akayi akayi katin naira dari da har kike surutu kai gashinan kinsa ya kashe wayarsa." Ummi tace"Gaskiya Mariya nima banji dadin abinda kikayi ba Yaya Sadam! fa ta bugawa waya." Mariya tace"To ai ba laifina bane kune baku fad'a min ba tun farko ke Sayyada Allah ya baki hakuri." Sayyada tace"Aikin banza ke Ummi tashi mu tafi ke kuma ki rike wayarki ba zan kara zuwa aro ba."

Mariya tace"Haba Sayyada meye abun daukar zafi kuma ai nima ban sani ba na fadi haka wallahi da nasan Mijiki kika kira bazan kunyata ki ba." Sayyada ko kallonta ba tayi ba ta kama hannun Ummi suka bar gidan....




Bayan ya kashe wayar sai ya kwanta rigingine yana me kallon rufin dakin Fuskarsa dauke da miskilin murmushi shi yasan yarinyar dama tana can a dame yasan ba zata ta ta'ba samun nutsuwa ba mutukar bata tare dashi ya tabbatar da cewar son da take masa a cikin jinin jikinta yake Sulaiman shine yake haukansa........Alhamudullhi jikinsa yayi sauki domin duk an kwance masa daurin dake kirjinsa babu abunda baya yi da kansa komai yana iyawa yanzu har riga yana sawa mara nauyi kuma yana fita gurin training horar da sojoji aikine kawai baya fita sai ya kara samun sauki sosai.....Tuntuni ya koma part dinshi dake bracck din sai dai kullum Dr ya kanzo safe da yamma ya bashi magani sannan ya duba yanayin gurin ciwon.

Can gida kuma Alhaji Auwal ya yanke shawarar tunkararsa da maganar Sayyada dan ganin da yayi yaja bakinsa yayi shiru ko zuwa sukayi dubashi idan basu ne sukayi masa maganar yarinyar ba baya yi musu kai ko maganar *Dabi* suke baya sanya musu baki haka zasu gaji suyi shiru yana jinsu ba zai tanka ba.


Yana can gorin horar da 'kananun sojoji masu sanin makamar aiki wani soja yazo ya sanar dashi zuwan mahaifin nasa..... Ba tare da 'bata lokaci ba ya bar aiki gurin abokin aikinsa ya nufi bangaran nasu Yana isa ya tadda Mahaifin nasa kofar shi ya bude kofar tare da fad'in"Abbah bisimlih shigo daga ciki." Alhaji Auwal ya shiga ya zauna kan kujera Sadam ya bude firji ya d'auko masa ruwa da lemo masu sanyi ya aje masa kan teble dake tsakiyar palon "Abbah ga ruwa nan." Yafada yana kokarin zama kan kujera. Alhaji Auwal yace."Ba shan lemo ne ya kawo ni ba nazo ne kan maganar Sayyada." Sai ya gyara zamansa a nutse yace."Ina sauraranka Abbah."

Alhaji Auwal yace."Yau satin Sayyada biyu a *Dabi* kayiwa mutane shiru kai bakace komai shin wai me ka maida mutane ne? kai baka isa ayi maka magana ba kaji baka isa a fada maka gaskiya ka dauka ba! abinda sulaiman yayi shine dai-dai ka raina sulaiman nima ka raina ni tunda har ka iya 'ketare maganata shin jiya ban turo sulaiman gurinka ba kan cewar ka fad'a masa a wace matsayar aka tsaya shin menene matsayin Sayyada a gurinka ka nuna masa shi bai isa kayi magana dashi ba sai dani zakayi to gani nazo sai kayi dani ina sauraranka."

Sulaiman ya dafe kansa yana mamakin ki tumurmurar da Sulaiman yake shirya masa gurin iyayensa yau sharabon sa da yaga sulaiman ai yafi sati uku tun ranar da sukayi waya wato ranar da ya kai Sayyada *Dabi* bai sake ganinsa ba sai yau azo masa da wata magana....Amma saboda baya so yaja maganar tayi tsayi yasa kawai ya soma bawa mahaifin nasa hakuri Alhaji Awal yace."Duk zancan hakuri bai taso ba shin yanzu meye matsayin Sayyada a gurinka." Yace."Abbah Sayyada nan a matsayin matata har yanzu." Alhaji Awal yace."To idan dai hakane maza maza ka shirya zuwa *Dabi* ka dawo da matarka domin baxa ka maida mu kananun mutane ba." Domin bin umarnin mahaifin nasa yace."Insha Allah zanje." Yace."Kamar yaushe ka shirya tafiyar domin in harhad'a musu kayayyaki." Yace."A cikin satin nan insha Allahu " Yace."Allah ya kaimu lafiya." Sallama sukayi da mahaifin nasa ya rakashi har inda yayi parking din motarsa sai da motar ta fita daga bracck din ya koma bakin aiki.


****
Kullum Baba Iya sai ta shigo kofar su Baba ladidi ta sassaki habaici ta kama hanya ta fita rannan dai da baba ladidi ta gaji sai da ta tanka mata tace"Ke Iya duk fa irin maganganun da kike fada kan zaman Sayyada a gidanan na gane inda kika dosa ki sani ba wai auran ne ya mutu ba sa'bani suka samu da har kikecewa auran yanzu ya zama na zamani daga anyi sai rabuwa to ki sani wannan dai mutuwa ce zata raba kuma da kike kira sayyada karamar bazawara to banaji Sadam! ya kauda budurcinta har yanzu a matsayin budurwa take." Baba Iya na ganin Baba ladidi ta harzuka sai ta wayance tana bada hakuri ita ba haka take nufi ba ai itama ta haifa ballantana tayiwa dan wani baki simi-simi ta fice daga kofar ta nufi kofarta tana dariyar 'keta.

Sayyada kuwa ranar yini tayi tana kuka wato har an soma kiranta da karamar bazawara lallai mutane 'yan gaza gani basa ganin abu suyi shiru sai sun magantu sai taji tana so ta koma dakinta ta zauna tayi ta hakuri da halin mijin nata.


*******
Babu zato babu tsammani sukaji sallamarsa a cikin gidan........Baba Marka tace"Lale maraba da soja ga wuta ga ya'ki soja marmari daga nesa lale maraba." Da sauri ta mike tana gyara masa gurin zama Sayyada ta dirgo daka gadon baba tana le'kensa ta tagar dakin Yana sanye da yadin kashmir brwon wanda ya kasance duk kusan rabin kayansa shine kansa babu hula sumarshi a gyare tare da sajensa yayi kyau sosai albarkacin jinyar da yayi ya kara haske da gogewar fata.....Baba Ladidi ta fito da ludayi a hannunta tana fad'in"Miskili kafi mahaukaci ban haushi an gama anzo biko kenan." Yace."Baba idan da ankashe ni gurin ya'ki me zakice ko baki san abinda ya same ni bane."? tace"Mun samu labari wallahi ai nayi kuka kamar babu gobe nace idan an kashe min angona ina zan sa kaina naji dadi

Please Login or Register in order to submit comment