Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itace a
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________



Free pege 8





*Asalinsu*
Jauro mai shanu shine mahaifin Alhaji Inuwa da Kawu Tanko sai baba Indo wacce Allah yayi wa rasuwa shekaru goma da suka wuce lokacin Sayyada nada shekaru hudu a duniya yanzu in an hada duk tana da shekaru goma sha hudu a duniya.

Malam Jauro mai shanu yana da mata biyu Baba Ladidi da Baba Marka wanda rana d'aya aka d'aura masa auransu suka tare a rana daya....Shekara nayi Baba Ladidi ta haihu inda ta haifi da namiji aka sanya masa sunu Auwalu sai da Auwalu ya shekara bakwai sannan baba marka ta haihu itama namiji ta haifa Aka sanya masa suna Haruna dake sunan mahaifin Malam Jauro ne sai suke ce masa Tanko.....Bayan shekaru uku Baba Ladidi ta haifi mace Aka sanya mata Aisha suke kiranta da Indo Tsakanin Marka da Ladidi suna zaman lafiya sosai da sosai ta inda yaransu basa gane cewar wacece mahaifiyarsu a ciki zaman lafiya da kwanciyar hankali suke inda har jama'ar garin suke sha'awarsu suke kuma kwatance dasu.

Dai-dai gwargwado Auwalu da Tanko sun samu ilimin addini dana boko sai suka soma har kokin noma da kiwon shanu da sauransu dake Auwalu mutum ne mai kuzari da zafin nama sai ya yanke shawarar fita daga garin nasu neman shekarar da sukayi aikin shinkafa ya cika mota guda ta a kori kura ya nufu kasuwar kano kasuwar (dawanau) ya sauka jama'a suka rufe shi kafin kice kwabo shinkafar da ya sauka da ita ta kare kimanin buhu talatin 'yan sari duk sun siye a take ya had'o kan kudinsa ya nufo gida suka sake aikin wata shinkafar ya sake dauka ya nufi garin kaduna anan ma dai shinkafar ba tayi wani tasiri ba suka siye tas....Kafin kice kwabo likkafa ta cigaba harkoki suka budewa Auwalu ya dinga bin gari gari yana sauke musu shinkafa mai kyau suna siya.......Cikin garin kaduna ya hadu da matarsa wacce ta kasance itace uwar 'yayansa Fatsima sunanta, ko da ya sanar da iyayensa cewar ya samu matar amma ba 'yar dangi ba bace can garin Kaduna take sai suka nuna amincewarsu sukayi masa fatan alkairi ba'aja wani dogon lokaci ba aka daura aure tare da amincewar su.



Allah ya albarkaci auran kawarai da gaske Arziki da wadata suka sake suke 'karuwa shekara na zuwa duk ya biya musu kudi sukaje suka sauke farali Dashi da Mahaifinsa Jauro da kuma baba ladidi da baba marka da Indo sai da dan uwansa Tanko da matarsa, addua ta ko wane fanni Alhaji Auwal ya samu ya gina gida mai kyau da kayatuwa sannan ya dawo garinsa na gado *Dabi* ya gyara musu dai-dai gwargwado ya zube musu abubuwan more rayuwa.....Tanko shike kula da harkokinsu na noma na garin.....Shekara daya da zuwansu aikin hajji Hjy Fatsima ta haihu inda ta haifi d'a Namiji aka sanya masa suna Sulaiman.....Malam Jauro da iyalinsa suka zo suka ga jinjiri suka sanya masa albarka.


****


Auran Kawu Tanko da Baba Indo a rana daya aka daurashi Kawu Tanko auran zumunci yayi inda ya auri 'yar gidan Dantani wanda ya kasance 'kani na jini da Malam Jauro Baba Iya itace matar Kawu Tanko asalin sunanta Hamara'u

Baba Indo kuma ta auri d'an gidan Maigarin garin *Dabi* mai suna Qasimu, ta zauna a cikin gidan mai gari dake gidan mai girma ne sosai bangare guda aka ware mata a cikin gidan.


***

Sulaiman nada shekaru hudu Hjy Fatsima ta sake haihuwa inda ta sake haihuwar Da namiji lokacin ne aka rigima tsakanin turawa da salihin mutumin nan da ya baiwa addinin musulunci guduma wato *Sadam! Hussain* a ranar da aka haifeshi aranar aka kashe Sadam! don haka sati na zagayowa Alhaji Auwal ya sanya masa suna Sadam! Saboda duk wani musulimi a wancan lokacin yaji ciwon abinda kafirai suka aikata kan mutumin nan duk mai kishin musulunci dole sai ya jajanta al'amarin.


*******


Sadam! tunda ya taso yake da wani irin hali mutum ne mai gudun zuciya da tsantseni yana da tsafta sosai kuma miskili ne sam baya son wasa idan kagan shi tare da d'an uwansa sai ka dauka shine babba saboda Allah yayi masa kwarjini da haiba dukanin family dinsu babu ba'ki sai shi dukaninsu farare ne kyawawa daga mazan har matan hanci har baka ga uban gashi shi kadai ne 'baki a cikinsu amma kuma a zahirance yafi su kyau sai wanda ya zauna dashi zai fahimci hakan kyakykyawa ne mutuka yana da manya idanu wanda suka dan risina kadan kewayayyiyar fuskar ta kawatu da wani saje mai kyau da tsari kasan ha'bar sa da saman bakinsa yana yawan yin gyaran fuska saman goshinsa akwai wani abu da yayi duhu tabon sallah kenan Sadam! yana da ibadah da kula da addini tun yana dan shekara goma sha hudu ya sauke al'kur'ani mai girma kwataa-kwata ba tsarinsu d'aya da yayansa Sulaiman ba wanda shi ya kasance mutum mai a'kidun turawa kaf karatunsa akasar waje yayi yanzu haka yana aiki 'karkashin hukumar tsare birni da kewaye na jahar Kaduna Sulaiman yana ta'ba siyasa sa'i da lokaci don har takarar dan majalisa ya tsaya Allah bai bashi ba.

***
Sadam! kam tunda ya kawo 'karfi yaji yana sha"awar aikin soja don haka kawai sai ya sanja shawara ya shiga makarantar horar da sojoji dake Kaduna ba, General Abdul Salamu shine ya tsaya kai da fata kan Al'amarin Sadam! a cewar sa a wannan zamanin idan Najeria ta samu jajurtaccen mutum irin Sadam! zata samu cigaba irin wanda ake bukata.

To tun Alhaji Auwal da Hjy Fatsima basa son abun suka dawo suna so domin General Abdu salam da kansa yazo ya sake wayar musu da kai kan yanda al'amarin suke sai suma daga baya suka gane abinda yake nufi.


A da Sadam! yana karantar aikin likita ne wato bangaran mata to sauyawar ra'ayi yasa ya aje karatun likitanci ya shiga aikin soja gadan! gadan! A yanzu Sadam! nada mu'kamin Captain a brecck din nasu kuma suna masifar ji dashi saboda babu wani abu da zai tun karo su na tashin hankali bai magance musu ba,


****

*Waiwaye adon tafiya*


Wannan magana da Baba Ladidi da Baba Marka suke ta samo asali ne daga gurin marigayiya Baba Indo wato mahaifiyar sayyada kenan Baba Indo in dai baku manta ba 'yace ga Baba Ladidi ta kasance 'kanwar Alhaji Auwal da Kuma Kawu Tanko....To a tun lokacin da aka kaita dakin mijinta ta had'u da lalura wani ciwo ya fito mata a kafarta guda inda ya dinga cin jikinta a lokacin har ta haifi Sayyada tayi wayo kusan shekararta hudu a duniya saboda yanayin jinyar da Indo take ne yasa Baba Ladi ta dauketa ta koma gurinta da zama. To duk a wannan lokacin Ciwon ajali ya kwantar da Malam Jauro inda baiyi wata doguwar jinya ba Allah ya amshi ransa......Wata uku a tsakani Baba Indo ta bishi a ranar da zata rasu a ranar Sadam! yazo garin hutu.....Lokacin Sayyada tayi bud'ud'u da jar 'kasa hancinta dagaje! dagaje! da majina gashi lokacin kunnenta babu yari ga aski baba ladidi tayi mata saboda kuraje da suka dame ta Sayyada dai kwandala ba zaka siye ta ba, aikuwa rankwashinta yayi ta yayi mata tsawa! ya korata gida tana ihu! ta shiga gidan bayan baba ladi ta boya tana nuna shi shi kuma sai hararata yake....Baba Ladidi tace"Daga zuwanka zaka dinga dukanta wannan ai cin zaline da mugunta.


Yana ya mutsa fuska yace."Baba wannan yarinyar sadaka aka bawa mutum ba zai kar'ba ba yarinya kamar ba mutum ba dubi jikinta ka'zama babu kyan gani."


Tace."Ai wasa take kuma yanzu dama nake cewa bari nazo nayi mata wanka."

Yace."Babu wani kawai don nayi magana ne amma da banzo ba haka zata kwana." Mikewa yayi yace."Zanje na duba Baba Indo kafin na dawo kiyi mata wanka." Cikin jin haushi Baba Tace"Ba zanyi ba d'in! kai kaji yaro da iyayi da kaine kake sani nayi mata wankan? sai dai idan ka dawo kayi mata ehee."!

Fita yayi bai ce mata komai ba....Halin da ya iske Baba Indo a lokacin da ya isa gidan ya bashi tsoro


Matan gidan sun kewaye ta suna mata fifita masu kuka nayi da salati baba indo kuwa bata san inda kanta yake ba sai nishi takeyi kamar ance ta bude ido sai ta ganshi a tsaye a kanta ta mika masa hannu matan gidan duk suka cika da mamaki hannunsa ta rike da kyau tana so tayi magana bakinta yayi mata nauyi da kyar tace"A kawo min Sayyada." Matar kanin mijinta ta fita daga dakin da sauri ta sanya yaro ya nufi can gidan ya fada musu halin da ake ciki......Minti ashirin ya kawo su Baba Marka ta fashe da kuka ganin halin da Indo ke ciki Ita kuwa Sayyada kin zuwa gurin mahaifiyar tata tayi ta 'buya a bayan Baba Ladi dake kukan zucci tana addua Allah ya saukakawa indo wannan larurar

Mahaifin Sayyada ne ya shigo dakin tare da wani likita Ba tare da wani tunani ba likitan nan ya hada ruwan allura ya zurkuda mata a cewarsa allurar zata sanya ta samu saukin ciwon.....Ai ko minti biyar ba'ayi ba jiki ya rikice Indo ta dinga wata iriyar girgiza kumfa na fitowa daga bakinta sai a sannan kuma Bakinta ya bude ta dinga salati ta bude idanunta da suka jirkice tana kallonsu tana kiran sunansu tace"Sadam! ko bayan raina ina so ka auri Sayyada wannan shine burina Baba ku xama shaida na bawa Sadam! Sayyada Mahafin sayyada yace."Allah zai cika miki burinki Indo zaki samu sauki mu cigaba da rayuwa." Sadam! yace."Insha Allah baba kina raye zaki ga aurena da Sayyada nayi miki alkawai." tace"Mutuwa zanyi ku yafe min." Sai ta fara sha'kuwa tana salati a wannan lokaci Rai yayi halinsa.
Wannan mutuwa tayi masifar girgiza zukatan mutane domin indo mutum ce mai shiga rai da barkwanci kowa sai da ya girgiza da jin mutuwar Indo Mussaman mutanan da suke rayuwa da ita a cikin gidan a wannan lokacin akayi mata suttura aka kaita gidanta na gaskiya, Sai bayan an dawo ne mutanan kaduna suka sauka a garin Alhaji Auwal yayi kuka sosai da mutuwar kanwarsa yana kaunar Indo shiyasa duk wani abun data bukata a lokacin tana raye a duniya yake mata......Sulaiman shima yaji mutuwar sosai tare suka dinga jajantawa junansu.


Sulaiman na ganin Sayyada yaji wani tausayi da sonta a zuciyarsa duk girmanta haka yake daukar ta su fita yayi mata siyayyar cizi biskit alawa iri-iri Sayyada ta zauna tana shan abunta bata da wata damuwa saboda da kuruciya a tare da ita a lokacin.

Sadam! kam ido ne nasa sam baya tanka musu watarana dai idan yaga abin yayi yawa sai ya daka mata tsawa idan tana wani shirman ita kuma sai ta fashe da kuka da ruga gurin Sulaiman tana fad'a masa shi kuma a lokacin ne zaka ga 'bacin ransa....Sadam! haushi da takaici ya sanya ya bar gurin sam a ganinsa abunda Sulaiman din yake wa yarinyar bai dace ba zata sangarce ta lalace duk girmanta sai ya dorata a cinya ko ya sa'bata a kafad'a ya fita da ita yana mata kiss a kumatu takaici kamar ya kashe shi.....Sai da sukayi fad'a kaca-kaca da Sulaiman din amma bai daina ba da karshe kawai sai ya daina kulashi gabad'aya to da yake Sulaiman din yafi shi saukin kai shine yake masa magana wani sa'in.


Bayan sadakar bakwai suka shirya tafiya.....Sayyada ta dinga gursheken kuka kamar ranta zai fita Alhaji Auwal yace." A had'a kayanta xai tafi da ita Baba Ladidi tayi tsalle ta dire tace"Bata yarda ba....Sulaiman ya dinga lallabata har da yi mata alkawari zai kaita umara tace"In dai sai ta basu Sayyada zai kaita Umara to bata so.


Sadam!!! 'bacin rai bai barshi yace komai ba shi dai ya zuba musu ido kawai sai da yaga iskancin Sayyadar yayi yawa sannan ya zare blet ya nufe ta yana zare ido......Ta ruga bayan Sulaiman tana kuka shi kuwa Sulaiman hararasa kawai yake yana fad'in"Wallahi ka dake ta da wannan blet din sai na rama mata mutum sai 'bakar zuciya kawai kai koma naka babu imani ka tausaya mata mana."!

Tsaki! Yaja ya maida blet dinsa ya daura a gu'kunsa ya koma ya tsaya shaye da toka sai wani cin magani yake duk suna kallo Sulaiman din ya sa'bata a kafad'a ya fita da ita sunfi 'karfin rabin awa basu dawo ba Sadam!!! sai tsaki yake yana kallon agogo an kira wayarshi ya kai sau biyar ana jiransu a bracck dinsu akwai sabbin sojojin da zasu horar dasu.

Mahaukaciyar siyayya Sulaiman yayi mata ta kayan zako iri iri Ya jibge baba ladidi ta cika da mamaki shi kuma yace."Ko idan sun kare ayi masa waya a sanar masa zai turo kudi." Baba Marka tace"Wannan ai ka siyo mata kayan ciwo haba ai abun yayi yawa za'ki ai ba abun sha bane."
Yace."Baba komai Sayyada take so zanyi mata tausayi take bani." Tace."To dai banda irin wannan siyayyar ta cutarwa kasan halinta yanzu sai ta'ki cin abinci ta dimanci shan alawa da madara.

Alhaji Auwal yace."Sai a kwashe kayan a dinga bata da kad'an-kad'an! Sadam!! yace."Nima dai abinda na gani kenan idan kun tara mata kayan za'ki taci ta sha to ku shirya da sanin cewar zata dame ku da kukan ciwon ciki."!

*To wannan shine tushen labari*

Page na gaba zamu dawo ainihin labari





30/5/2020


*BINTA UMAR ABBALE*



_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________



Free Pege 9



*Cigaban Labari*
To haka Sayyada ta cigaba da rayuwa a hannun Baba Ladidi tare da kulawar 'bangarori daban daban mahaifinta ma yana iya bakin kokarinsa akanta sai da da yayi aure ne matar da ya aura ta janye masa hankali daga kan Sayyada ya daina kulawa da ita sosai Sayyada sam! bata sha'ku da bangaran mahaifinta ba tafi shakuwa da bangaran mahaifiyar ta shiyasa ba sosai take zuwa can gidan maigarin ba sai Baba Ladidi ta takura mata sannan take zuwa Juma'a Juma'a, shima idan taje bata wani zaman arziki take dawowa gida a cewarta baza ta zauna Hansatu tana yi mata kallon banza ba domin sun sha fad'a sosai da ita da matar baban nata mai suna Hansatu.


Sayyada yanzu haka tana aji shida a karamar makaranta suna dab da jarrabawa makarantar isilamiyya kuwa sun hada izifi ashirin to babu laifi tana gane karatu amma Amina ta fita kokari, kun san dai kowa da irin baiwar da Allah yayi masa.


*****

Karfe uku shaura na rana tana zaune da kwanon abinci a gabanta hijab ne a jikinta kalar ruwan toka gefanta jakar makarantar isilamiyya ce Amina ce tayi sallama ta shigo


Ta gaishe da baba Ladi dake bakin rijiya tana wanke kwanoni kai tsaye ciki ta shige itama ta shirya tsaf da shirin tafiya makaranta.


"Sayyada baki gama cin abincin ba kenan? duba lokaci ya kure da yawa kin san dai yau malam Bashir ne zai shigo ajinmu ko."?

" Yi tafiyar ki malama kar ki dame ni! sai me idan malam Bashir ne zai shigo sai a ka fad'a miki tsoronsa nake."!

Amina jikinta yayi sanyi tace"Kin san dai ko zai barki ki kishiga aji sai ya doke ki da wannan bulalar mai zafi shine abinda nake guje mana."


"To me ya dame ki? kinga nifa bance dole sai na tafi dake ba tafiyar ki daban tawa daban mtwss!

Baba Marka ta daga labule ta fito tana fad'in" Surutun me nake ji Amina."!?

Amina data sha'ka da yawa tace"Baba Wai daga nace mata tazo mu tafi makaranta kar mu makara shine take fad'a min magana."

Baba Marka tace"To bakya ganin abinci take ci ne."

Amina tace"Ai dama cewa nayi tayi sauri baba."

Marka tace"Ke Sayyada maxa ki gama ku tafi karku makara." Sayyada tayi musu shiru tana cin abincinta haushin Amina takeji sosai kuma tayi al'kawarin sai ta kunyata a gaban 'kawayensu na makaranta.


Tana gama cin abincin ta mike ta wanke hannunta jakarta ta dauka ba tare tace Amina komai ba ta kama hanyar fita....Amina tabi bayanta tana fadin"Sai mu dawo." Baba Ladidi tace"To Allah ya bada sa'a."


Ko a hanya ma Sayyada 'kin kula Amina tayi har suka isa makaranta Sayyada ta tsallake can gurin 'kawayenta itama Amina ta zauna gurin 'kawayenta dama gurin zaman Amina a gaba yake ita kuma Sayyada can baya take zama tare da manyan 'yan matan da suka girme ta nesa ba kusa ba suyi ta zancan aure sam basa gane karatu sai maganar aure da hirar samari Sai lokacin jarrabawa yayi idonsu ya raina fata Sayyada ce kawai mai 'kokarin cikinsu ita ke basu amsa ko kuma idan ta rubuta ta basu su kwafa shiyasa suke tsoronta komai tace dai-dai ne."


Sai bayan malam bashir ya fita ne kafin wani malamin ya shigo Sayyada ta kallesu tace "Kun san menene."!? Suka ce sai ki fad'a." Tace"Wallahi na tsani Amina muguwar munafuka ce." Sadiya tace"Ke Sayyada ke da 'yar uwarki kuma me tayi miki."?

Tace"Humm! wai saurayina ko kuma nace mijin da zan aura shi take so har da wani shishshige masa shi kuma har da sa mata zobe bayan fa tasan da al'kawari a tsakaninmu dashi."

Ummi tace"Lallai Amina bata da kunya wallahi to ke wane mataki kika dauka."!?

Sayyada tace"Ku taso muje inda take." babu musu suka mike suka isa inda Amina ke zaune da kawayenta suna bitar karatu.

Aminta taji magana a kanta "Ke Amina ciro wannan zoben dake hannunki."! Sayyada ce me wannan maganar tasha kunu.

Amina ta dago kai tana kallonsu tace" Kamar Yaya na ciro zobe me ya shafeki dashi."

Ummi tace"Lallai Amina baki da kunya au! tambayar ta ma kike meye ruwanta bayan kinsan zoben hannun Saurayinta ne ai tana da iko dashi."


Amina ta mayar da kai kasa tana karatu Sadiya tace"Wallahi tun muna shaida juna dake ki ciro mata zobenta ai itace tafi dacewa dashi tunda ita zai aura amma saboda tsabar shishshigi kin wani shigewa saurayinta wai don ya aure ki mun gane abinda kike nufi."


Daya daga cikin kawayen Amina tace"A gaskiya wannan abinda kukeyi bai dace ba ina ruwanku da Amina ni dai tunda na shigo banga ta shiga sabgarku ba."

"Dallah malama rufe mana baki banza 'kazama wacce bata waye ba ke idan ke akaiwa haka zakiji dadi? Mijina fa taje tana cusa kanta a gurinsa har sai da ya sa mata zoben da yayi niyar saka min wallahi sai ta cire zoben nan ko kuma ta raina kanta."!Sayyada ce ke wannan maganar tana girgixa jiki....Ai kafin kice komai 'yan ajin sun lullu'be su suna son jin 'karin bayani ita kuwa Ummi 'kawar Sayyada sai fad'a musu take Amina munafukace me 'kwacen saurayi don haka kowa yayi taka tsantsar da saurayinsa.......Aikuwa sai aka fara surutai kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Amina 'bakin ciki ya sanya ta fashe da kuka idanu jage-jage da hawaye take kallon Sayyada tace" Yanzu ni kika tozarta a bainar jama'a Sayyada nifa 'yar uwarki ce."!

"Oho! wannan ke ya shafa ni dai nace a ciro min zobe ko kuma yanzu jiki yayi tsami wallahi."!

Amina tace" Wallahi bazan cire zoben nan ba tunda ai bake kika saka min ba sai ki bari idan wanda ya saka min zoben yazo sai ki saka shi ya cire min da kansa."


Sayyada tayi wani juyi had'e da buga tsalle! sai ta cafki wuyan Amina ta sha'ke cikin hijab tana fad'in"Wallahi sai kin cire min zobe banza shashasha me 'kawacen saurayi."

Amina da Sayyada kokawa suke sosai da sosai Sayyada duk ta ya kushe mata fuska sai 'kwa'kule mata hannu take tana murd'ewa wai dole sai ta cire zoben ita kuma Amina ta dunkule hannunta.


'Yan aji kuwa sai Ihu! suke suna dariya da fad'in"Wallahi babu wanda zai rabaku ku casu ai 'yan gida d'aya ne."


Mariya 'kawar Amina ita ce ta nufi ofis d'in malamai domin ta fad'a musu halin da ake ciki sai suka ci karo da Malam Bashir ya fito daga ofis yana kokarin shiga wani aji tace"Malam Bashir ana fad'a a ajinmu.'' Yace."Waye da waye."!? Tace"Amina ne da Sayyada. Kai tsaye a jin ya nufa da zabgegiyar bulalar sa.


Har yanzu kokawar suke Sayyada ta kusa ciro zoben Taji saukar bulala a bayanta ko a jikinta sai da ta ciro zoben sannan hankalinta ya kwanta ta saki wuyan Amina tana nishi! Amina ta mike zaune sai kuka take ga Sayyada duk ta ji mata ciwo da yakushi.....Malam Bashir yace."Ku same ni a ofis."

Yana fita Sayyada ta mi'kawa Ummi zoben tace"Ri'ke min wallahi komai za'ayi ba zan bayar ba."

Ta kama hanyar fita Amina ta mike da jiki a sanyaye tabi bayanta duk 'yan ajin suka bita da kallo Amina ta tsargi kanta sai rufe fuska takeyi kamar wacce tayi abun kunya.



Suna isa ofis din suka tarar da Malam Bashiri na zaune kan kujera da wayarsa a hannunsa yace."Ku tsuguna ko wacce ta d'aga hannu sama."

Babu musu sukayi abinda ya saka su sai da sukayi minti goma shabiyar a haka sannan yace."Ku sauke hannunku." Suka sauke Sayyada ya kalla yace."Daka gani kece mara gaskiya bari na fara jin ta bakin ki me ya had'aku fad'a."!?

Sayyada ta soma inda inda" Malam nifa d dama ita k.....A gida bama shiri da juna kuma munafuka ce ita."

Malm Bashir yace."Ni ba wannan na tambaye ki ba ina so ki fad'a min ma'kasudin fad'anku." Shiru tayi ya girgiza kai yace."Ko anan ma alamu sun nuna kece mara gaskiya Sayyada nagaji da halin ki yanzu yanzu zan kira Sadam! a waya in sanar masa da abinda kikeyi a makarantar nan."
Sayyada gabanta ya yanke ya fad'i jin abinda yace sai tace"Nifa malam wallahi ba laifina bane itace ta shiga gona ta."


Malam Bashir ya kalli Amina yace."Amina ke fada min abinda ya hadaku fada kafin na yanke hukunci."

Amina ta warwarewa Malam Bashir duk abinda ya faru tsakaninta da Sadam! da yanda akayi yasa sanya mata zoben hannunsa.


Malam Bashir yace."Sayyada kece mara gaskiya don haka a kanki zan dauki mataki ina ruwanki da zoben hannunta tunda dai ba ke kika saka mata ba ko kuma ance miki shi Sadam! din idan ya aure ki dake kad'ai zai zauna to ki shiga hankalin ki wallahi."Sayyada ta kama 'kunkuni hawaye na kokarin zubo mata....Malam Bashir ya fara neman numbar wayar Sadam sai da ya kira sau uku sannan ya dauka hands free ya bude duk suna jin muryarsa suka gaisa da malam bashir din wanda dama tun asali sun san juna abokan juna ne saboda duk lokacin da Sadam! din ya shigo garin a majalisarsu yake zama.


Mlm Bashir ya fad'a masa dukanin abinda ke faruwa tare da fad'a masa hukumcin da ya yanke a kan Sayyada zai korata gida ta zauna sai bayan sati biyu ta dawo."

Sadam! Yace."Yanzu ina Sayyadar take."? Malam bashir yace."Duk gasunan a kusa dani." Yace."okey bata wayar zanyi magana da ita." Sayyada najin haka sai gabanta ya fad'i! da sauri ta aro dauriya da jarumta ta kar'bi wayar da malam Bashir din ke mi'ka mata.




_Afuwa bani da change sosai kuyi manege_




31/5/2020



*BINTA UMAR ABBALE*



_*Littafin Ni da Yaya Sadam! na kudi ne 1_2 #400 ga duk mai bukatar karantawa sai ya tura kudinsa ta wannan accont din......0542382124.......Binta Umar gtbank idan kuma katin waya mutun zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din zan fad'a masa yanda zai biya kud'in....08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar littafin to sai ku tura dala dari ta wannan numbars.....90899076 _88137740 katin airtal ko orange.....Dala dari itace a

Please Login or Register in order to submit comment