Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyi hankali ki daina abunda kikeyi."


Sayyada haushi ya sanya ta soma zagin Amina kafin kice kwabo sun kaure da fad'a har da kokawa Sayyada tayiwa Amina lilis ta zaneta tace"Idan kinje kice yazo ya rama miki shi wanda kike tarewa fad'an."


Amina na kuka ta nufi 'kofar su....Ita kuwa Sayyada sai ta kama hanya ta fice daga cikin kofar gabad'aya gidajan amare ta fara bi tana musu wanke wanke da shara yayi al'kawarin ba zata dawo gidan ba sai dare sai ta tabbatar ya bar garin sannan zata dawo.



Baba Ladidi ta nufi kofar su Kawu Tanko saboda tayi ya'kinin yana can aikuwa samunsa tayi zaune kusa da Baba iyatu da Marka suna hira ga 'kwaryar fura a gabansa yana sha.


Tana shiga ta sauke mayafin dake saman kanta ta rataye kan igiya.....Tace."Kai ja'iri gurinka nazo yanzu zan tona maka asiri ehe! wato dama abunda kaje ka karanto kenan iskanci."!


Sadam! Ya aje ludayin dake hannunsa ya had'e fuskarsa sosai yasan hargitsi irin na Baba Ladidi shiyasa yaci mur yana kallonta.


Ita kuma ta kalli Marka tana numfarfashi tace"Yanzu Marka dai-dai kenan abunda Sadam! yayi iye!? Haka kawai saboda son zuciya yarinya na irgar dangi ya kama mata nono ya murd'e wannan ai iskanci ne da yahudanci yarinya kamar Sayyada me ta sani."!?


Marka da Iya suka sanya salati suna tafa hannu." Sai su mayar da hankalinsu kansa......Dake mutum ne mai mutukar 'kwarjini da iya waskewa ko alama basu fuskanci razana a tare dashi ba sai ma wani kwarjini da yayi musu wanda suke ganin kamar ba zai iya aikata wannan d'an yan aikin ba.


Baba Marka tace"Haba Ladi! Wai kin manta halin Sayyada ne? hummm! gaskiya banji dadin jin wannan maganar ba haba jama'a! ai a fad'i abunda zai faru amma wannan dai karya ce Har guda nawa Sayyadar take haba jama'a!!!!


Baba Iya tace"To nima dai abinda na gani kenan Sadam! ba zaiyi wannan al'amarin ba.


Yace."Baba Marka ku kyalesu don Allah ni nasan saboda me yasa ta fad'i haka saboda d'azu ta tisa ni a gaba wai dole sai na auri sayyadar nace bana so a kai kasuwa shine suka 'bullo da wannan zancan to ni me zanyi da wannan mahaukaciyar yarinyar 'kazamiya."


Baba Ladi ta maka masa da'kuwa tana fad'in"Ubanka ni ce nake maka 'karya ko? Wad'annan kafiran idanun naka menene ba za ka iya ba Ai ni na yarda da abinda Sayyada ta fad'a su dai da kayi musu kwarjini sai su 'karata maganar auran Sayyada kuma ni na yanke hukunci."


Murmushi yayi kawai ya sadda kai 'kasa yana me cigaba da 'kur'bar furar sa.

Baba Marka ta kalleshi a nutse tace"Haba Sadam! ashe kana so ka bamu kunya kenan."!?

Ya kalleta a nutse yace."Wace iriyar kunya kuma."? Tace."Naji kana maganar kai ba zaka auri Sayyada ba karka manta da cewar Kaine kayiwa mahaifiyarta al'kawari zaka aureta kafin rasuwarta kayi 'kokari ka cika wannan al'kawari."


Yace."Baba lokacin da nayi alkawarin zan auri yarinyar Baba Indo na cikin halin ciwo lokacin inaso taji sau'ki ta dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa kuma a lokacin da 'kuruciya a tare dani amma ni har ga Allah ba wai na amince bane zan auri yarinyar ina me baku hakuri kuma ina mata fatan kan Allah ya bata miji nagari wanda ya fini nutsuwa da komai da komai.

Baba Ladidi ta saka kuka tana fad'in"Wallahi kai ba d'an halak bane Sadam! yanzu meye laifin Sayyada umm? yarinya san kowa 'kin wanda ya rasa yarinyar ma tafi 'karfin ka matar manyar mutane ce amma saboda muna so mu cika al'kawari muna ta binka kana mana wulakanci kar Allah yasa ka aure ta d'in." Ta dauki mayafinta dake rataye a kan igiya ta nufi hanyar fita tana share hawaye.

Amina ce ta shigo tana kuka.

Baba Marka tace"Ke kuma meye kike kuka.
Ba tace komai ba ta shige daki tana share hawaye duk sanda zasuyi fad'a da Sayyada ita take cin galaba akanta ta rasa menene dalili.


Baba Marka ta dinga rarrashin sa kan ya daure ya auri Sayyada kamar yanda yayi alkawari a can baya....Domin ya kwantar mata da hankali yace."Zai yi tunani kan al'amarin.








24/5/2020




*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*




*_Littafin Ni da Yaya Sadam! na kud'i ne 1 _ 2 ga mai bukatar karanta littafin zai tura #400 kacal ta wannan accont d'in.......0542382124......Binta Umar Gtbank.....Idan kuma katin waya zaka tura to sai ka tuntu'beni ta wannan numbars din nawa zan fad'i yanda zaka/ki biya kudin......08089965176 _07084653262.....Mutanan Nijar idan kuna bukatar karanta wannan littafi to zaku tura katin airtal ko orange na dala dari a wannan numbars......90899076 _88137740.....Dala d'ari itace a madadin d'ari uku kud'in Najeria_*




Free pege 4





Sayyada tunda ta fita daga gidan bata dawo ba sai gab da magariba tazo shigowa sukayi kici'bus dashi ya fito daure da alwala da nufi zuwa massalaci ya kalleta ta kalleshi babu tsoro a tare da ita ta zabga masa tsaki tare da fad'in "Dan iska kawai."


Sadam! ya bita da wani irin kallo na mamaki yanzu shi Sayyada ta kira da d'an iska? Zuciyarsa tace masa ka ta'ba mata nono dole kira ka da wannan sunan.....Tabbas hakane daya sashen na zuciyarsa ya fad'a masa haka.

Girgiza kansa kurrum yayi yayi gaba yana tunani kan al'amarin sam bai ta'ba jikin yarinyar da wata manufa kawai sai dan hukunci yanda ya fahimta yarinyar da kakarta sunyi masa wata fassara ta daban tabbas zai nunawa yarinyar shi d'in 'dan iska ne kamar yanda ta kira shi zai dinga murd'e nono da take ta'kama dashi.


Da 'kyar Baba Ladidi ta tirsasata tayi sallahr magariba sannan ta d'auki kayan tallanta ta fita can bakin wata katuwar bishiyar darbejiya ta nufa ta aje farantin gyadar marau da tibis Baba Ladi ce take soyawa duk daran duniya Sayyada na dauka ta fita dashi cikin ikon Allah sai kiga anyi cini dari dari biyu a cewar Baba Ladi ta siyi kalanzir da sukari na koko sana'a ko yaya take dad'i gare ta.


Tare da Kawu Tanko suka fito daga massalacin suna tafe suna hirar yaushe gamo Kawu Tanko na tambayar d'an uwansa Sadam! yace."Yayi tafiya zuwa Abuja wata uku zaiyi ya dawo insha Allah......Sai da suka zo dab da bishiyar da Sayyada take ya hangota matasan maza 'yan bana bakwai sun kewaye ta sai wasan banza suke d'aya har yana cire mata d'an kwali.


Gabansa ya fad'i sosai! sai yaja ya tsaya yana kallon Kawu Fuskarsa a d'aure yace."Kawu waccan yarinyar ba Sayyada bace."?


Kawu Tanko ya kalli inda yake nuna masa ya hango Sayya tsakiyar maza.

Yace."Itace ai nan ne gurin da take zama siyar da gyada Baba ke kasa mata tallah da daddare."


Sadam! Yaji kamar ya gaura masa mari! wannan ai cin amana ne yarinya marainiya suka zuba ido suna gani ta dauki hanyar lalacewa.


Yace."Haba Kawu! Haba duba fa ka gani Kawu kuna raye wannan al'amari yake faruwa! kar fa ka manta da cewar yarinyar nan amana ce a gurinmu Baba Indo bata cancanci wannan abu ba."


Kawu Tanko jikinsa yayi Sanyi kalau yace."Sadam! wallahi tallahi nayi dukanin iya bakin kokarina kan hana faruwar wannan al'amari Baba ta'ki fahimta akwai ranar dana zubar da gyadar a cikin kwata a ranar Baba sai da ta kusa tsine min kuma tafi sati bata amsa gaisuwa ta wallahi shiyasa nake jin tsoron shiga lamarin saboda gudun bakin uwa amma dukaninmu munyi iya bakin kokarinmu kan al'amarin."


Girgiza kai kurrum yayi ya nufi bakin bishiyar ba tare da yace komai ba.

Kawu Tanko ya bishi da kallo ya riga yasan halin Sadam! da ba'kar zuciya da gudun magana da zai dauki shawara sai yace kawai ya amince a daura musu aure shine zai kawo karshen matsalar.


Matasan samarin na ganinsa ya doso gurin sai suka watse kowa yayi nasa guri ita kuma tana fad'in" Kai Talle mai abin dariya kar'bi canjin ka wallahi ko kuma in had'a dashi cikin lissafina."

Talle yace."Kije na bar miki budurwata ai kin fi karfin komai a gurina."

Kyalkyalewa tayi da dariya tana gyara daurin dankwalinta tace"Talle kenan waye ya fad'a maka ni zan auri d'an 'kauye humm! mijina d'an birni ne kyakkyawa Soja mai aj.........Kafin ta 'karisa tagan shi a tsaye a kanta.

Mi'kewa tayi da sauri! tana mutsika ido ta fara zumbura baki jelar d'ankwalinta ta kamo tasa a baki tana taunawa tamkar wata shshasha! nan kuwa tsabar iskanci ne yayi mata yawa.


Sadam! Ya kalli talle dake tsaye tirmin danya shi ya'ki tafiya yana sanye da wani yadi fari yayi masifar daud'a duk yayi jirwaye mussamam hamtar sa da bakin aljihunsa sai wata shegiyar hula da ya kwafa a kansa sai kace kwano sa wani tabarau wanda yayi masa yawa.Shi nan bai yarda ba yayi gayu.


Sadam! mutum ne mai 'kyamkyami sosai shiyasa kallo guda yayi wa Talle da yaga bakinsa dagaje-dagaje yayi saurin kauda kansa yana ya mutsa fuska......Yace."Kai wuce ka bawa mutane guri dallah."! Talle ya ya hau ya'ke yana sosa 'keya yace."Ya asalin na wuce muna hira da masoyiyata."


Sadam! yaji wani bala'in takaici ya kamashi jin abinda Talle ke fad'a ba wai yana kishi bane kawai tsabar kauyancin da sukeyi shine yake bashi haushi.....Bai iya ce masa komai ba ya kalleta tana tsaye sai tauna gefan dankwalinta take yace."Dauki kayan tallan ki wuce gida."! Shiru tayi tana kallonsa tare sa zu'baro baki.

Kwata kwata baya son dukanta shiyasa ma kafin ya isa gurin ya saisaita tunaninsa domun a yanda zuciyarsa ke masa zafi da yarinyar yana gani zai iya yi mata mugun rauni saboda duka shiyasa taushi zuciyarsa akanta bayan haka kuma yanajin tausayinta saboda maraicinta gaba da baya.


Talle yayi wani 'kas! da hannu irin na gayu na 'kauye yayi wani juyi da kafafunsa da suke sanye da wani fatattakaken kambos yace."Baby sai gobe zamu had'e naga wannan gayen shima kamar yana sonki to karki damu da komai baby tunda ni kike so nima ina sonki."

Talle Ya fad'i wannan maganar ne domin ya cuzgunawa Sadam!! saboda a tunaninsa son Sayyadar yakeyi......Sadam! kam kallo ya bishi dashi cike da tsabar takaici ya ma rasa bakin magana ya dawo da kansa kanta "Dauki kayan tallan muje gida."

"To ai gyadar bata 'kare b......." Wani bahagon mari ya kai mata! Allah yasa bai same ta ba don da ta sake marin nan ya same ta to sai tayi jini da majina! da sauri ta dauki farantin gyadar ta kama hanya tana waiwayen sa.

Ya biyo bayanta cikin yanayi tafiyarsu ta sojoji.


"Allah ya isa ban yafe ba mugu azzalimi d'an iska." ! Ire iren surutan da takeyi kenan tana waiwayensa Sadam! na gani tana motsa bakinta amma baya jin abinda take cewa saboda kasa kasa take maganar.

Tana shiga kofar ta sa kuka a guje ta shiga ciki tana fad'in "Allah ya isa."!! Baba Ladidi! Kinga Ya Sadam! ya koroni ya hanani na siyar miki da gyadar ki kuma sai cini ki akeyi ya kori mutane."

Baba Ladidi dake kishingid'e kan tabarma ta mike zaune tana gyara daurin dankwalinta tana kokarin magana ya shigo gidan.


Kai tsaye inda suke zaune ya nufa ba tare da ya zauna ba yace."Baba ashe dama tallah kike d'orawa Sayyada yanzu don Allah me kika nema kika rasa da zaki dinga dora mata tallanta gyada da daddare tana shiga tsakiyar maza ke kin san sayyada ba nutsuwa ce da ita ba kike dora mata tallah."


Tace."Haka kawai sai na zauna 'kuda yabi bakina ba zan nemi na kaina ba kenan? meye laifi don na dora mata tallah ai ko babu komai kudin cinikin yana toshe mana wata kafar saboda haka daukar tallah yanzu Sayyada ta fara idan kaga ta daina to tana dakin mijinta."

Yace."A haka kike cewa in aureta kenan."!? Tace"Kwarai kuwa wai me kuke nufi ne? duk wanda zai ga Sayyada na zama gindi bishiya tana saida gyada sai ya fassara da wata manufar ni nasan halin sayyada baza ta aikata abinda kuke nufi ba ku kyale mu kawai mu nemi na kanmu."


Cike da tsabar takaici yace."Babu rashin ci babu rashin sha babu rashin gurin kwanciya kike wata maganar, A gaskiya to kan wannan al'amari muna iya 'batawa dake domin wannan ba tarbiya bace da daddare kawai ki kasa mata tallah ta shiga cikin maza ke kina kwance a gida ba fata nake ba idan wata matsalar ta faru me zaki ce mana saboda haka kome zakiyi daga yau Sayyada ta daina daukar tallah."


Baba tace"Sayyada ba zata daina daukar min tallah ba sai dai idan aure nayi mata wai ina ruwanku ne? kai kake wata magana idan kaji haushi yau ka turo sadakin auranta sai a daura muku aure ka dauke kayar ka amma matukar muna tare da ita baza ta daina tallah ba."


Yace."Ai ni na gama magana ba zan aureta ba kuma tallah sai ta bari domin yanzu idan na fitar daga wannan kofar zan nufi gurin Sarkin 'kofa in shigar da 'korafina akanki."


Ai sai Baba tasa kuka tana fad'in"Ni za ka kai 'kara gurin Sarkin 'kofa saboda baka da mutunci."

Yace."To kece ai kin'ki ki zauna ki fahimci mutane kawai kina bin son zuciyarki."


Tace."To naji zauna sai mu fahimci juna."

Ya samu gefanta ya zauna tace"Maganar dai ta kare idan kana so sayyada ta daina tallah to ka yarda a daura muku aure kafin ka koma amma kar ka sake ka kai maganar gurin Sarkin 'kofa to kaji."!

Yace."Shikkenan zanyi tunani kan maganar ki amma don Allah ko bayan na tafi karki 'kara dora mata tallah." tace"Haba ai magana ta 'kare bari na kawo maka abinci."

Yace."Bari dai naje can kofar Kawu Tanko naci a can."

"To babu laifi ai duk d'aya ne."

Yana fita Sayyada tace"Baba yanzu da gaske kike kin daina soya gyada kuma na daina daukar tallah? kinga fa yau dari da ashirin nayi sannan Talle ya bar min sanjin talatin d'insa kinga d'ari da hamsin kenan."

Baba ta kar'bi kudin tana lissafawa tace"Rabu dashi zai tafi ai sai mu cigaba da abinmu a kan wane dalili zasu hanani neman kudi."

Sayyada tace"Nima dai abinda na gani kenan." Mikewa tayi taje ta zubo abinci ta zauna tana ci tana tunanin abinda ya faru tsakaninta dashi da safe duk sanda ta tuno da lokacin da ya dora hannunsa a kan nononta sai tsigar jikinta ta tashi wanda tunda suka fara fitowa bata taba jin wani yanayi a jikinta ba sai a wannan karon da sukayi ita dashi.

****

Washe gari da safe dake tana riga kowa tashi a gidan Baba Ladi da Baba Marka na cikin dakin suna bacci ta share gidan ta had'e kwanuka ta wanke ta nufi bandaki domin ta wanke tana tura kofar bandakin lokacin shi kuma yana daure igiyar wandonshi karf suka had'a ido a razane! ta sauke idonta 'kasa ta saki kofar jiki na 'bari ta bar gurin....."Wayyo Allah wannan meye a mararshi kamar gashin jinjiri a kwance bakikirin a jiki dama haka jikin maza yake da gashi to me ya kawo gashi a marar sa.

Jiki a sanyaye taje bayan Baba Ladi ta kwanta ta rintse ido tsigar jikinta sai tashi takeyi.


Sadam! kam yaji takaicin ganin da tayi masa yana daure tazuge wato Allah ne ma yaso shi ya riga ya gama uzirinsa da yarinyar nan ta cuce shi.......Ya fito ya dauki brush dinsa inda ya aje ya goge bakinsa tsaf ya koma masaukinsa cike da takaicin yarinyar.







27/5/2020




*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________




Free Pege 5





Sayyada shiru tayi a bayan Baba Ladi tana zare ido rintse ido tayi sai kuma ta bud'e da sauri ta mike zaune ta hau sosa kai a hankali ta mike taje ta d'aga labule tana le'kensa yana goge bakinsa ta jima a tsaye a bakin kofa sai da taga ya mike tayi saurin sakin labulen ta dawo ta zauna tare da zabga tagumi tana tunanin abinda ta gani.

Can ta saki ajiyar zuciya da taji tafiyarsa da alamu ya koma masaukinsa sai ta fito ta d'ibi ruwa cikin bokiti taje ta wanke bandakin.....Tana fitowa shima ya fito daga dakin da yake suka had'a ido tayi saurin dauke kanta tana gumtse baki dariya take so tayi amma tana jin tsoro.

Sadam! ya girgiza kansa ya wuce dakin Baba bacci take sosai ya hau tashinta bude idonta tayi tana salati tare da hamma da alama tana jin dadin baccin yace."Baba ruwa nake so me zafi nayi wanka zan fita da wuri domin in zaga 'yan uwa kwana biyu kacal zanyi na koma."


Baba Ladidi na d'aura d'ankwalinta tace"aikuwa babu ruwan zafi sai dai na dora maka idan na dama kunu."


Yace."A'a ki fara d'umamin ruwan zafin kafin ki d'ora kunun." Tace"To haka za'ayi." Sai ta hau kiran Sayyada.

Ta shigo tamkar wata mai hankali tace"Gani Baba."

"Ki d'orawa Mijinki ruwan wanka."

Jin abinda tace yasa ta zum'bura baki tare da fad'in"Kai Baba."! Mikewa tayi ta bar gurin.

Duk suka bita da kallo yace."Wallahi baba ladi kina bani haushi wannan wace iriyar magana ce salon kawai ta raina ni yaushe na zama mijinta."


Baba Tace."Yo kwana nawa ne kuma ai gwara in dinga kiranta da sunan matarka yafi armashi."

Takaici yasa ya mike ya fito tsakar gida.....Tana tsugune can wani ke'bantaccen guri da suke girki tana kunna wuta a (kurfoti) ya tsirawa bayanta ido yana ayyana abubuwa da dama kanta shi yanzu ya auri wannan yarinyar ya auri me? yarinya babu fasali babu gaba babu baya sai uban tsayi kamar lisha shi yafi son mace mai brest da hips sosai duk da dai yarinyar bata gama girma ba amma yana ganin anya kuwa sai dai ya lura tana da shafaffen ciki da alama kuma zata yi hips masu kyau.


Duk hannuwansa ya zura a cikin aljihu yana kallonta ta mike da wata butar 'karfe da suke d'umama ruwa taje ta ciko da ruwa ta d'ora kan wuta tana juyowa suka had'a ido.


'Kasa tayi da kanta tana kauda kai tazo zata wuce shi....Sai da tazo daf dashi sannan dariyar da take 'boyewa ta su'bce sai ta rife bakinta da tafin hannunta tana kyakyatawa, idanunta tsaye a kansa tamkar taga mahaukaci.


Shan kunu! yayi sosai saboda ya fahimci abinda takewa dariya yace."Don Ubanki dariyar me kike? wa kika mayar mahaukaci anan gurin."

Baba Ladi ta fito da sauri tana fad'in"A'a ya naji ana zagi kuma."!?


Sayyada tayi bayanta ta 'boya tana ti'kar dariya Baba tace"Ke bana son ja'irci da shashanci dariyar me kikeyi haka."?


Tana dai dariyar tace"Baba gashinan a tsaye shine ya bani dariya wai da girmansa yake tusa hahahaha! Allah baba ba kiji tusar tasa ba mai warin tsiya da 'kyar na wanke band'akin."

Baba Ladi ta kama dariya tana tafa hannu ''Oh! ke kiji ja'irce na Sayyada a ina kikaga yana tusar."?
Shiru tayi tana kallonsa tana dariya.

Sadam! yayi tsai a tsaye yana kallonsu daga ita har Baban haushi suke bashi yana tunanin abinda zaiyi musu ya huce yarinyar nan Sayyada ta raina shi wai shi yake tusa mai wari amma dai yaji dad'i da bata fad'awa Baban cewa ta ganshi yana d'aure tazuge ba.


Baba tace"Sadam! kaji d'an bukin da Sayyada take maka ko hummm ni nasan barkwanci ne kawai irin nata humm Sayyada kenan."!!!!

Takaici bai barshi yace musu komai ba sai yayi shiru da bakinsa shiru ma magana ce dauke kansa yayi tare da kauda kansa ya murtuke fuskarsa.


Yana kallon yanda ruwan ke turiri yasa ya mi'ke aikuwa ta zabura! da gudu tayi hanyar fita wai ta d'auka dukanta zaiyi......Karo suka buga da Amina tana dauke da wani dogon kofi mai murfi cike da 'kunu mai zafin gaske aikuwa duk kunan ya kware a jikinta inda ta fasa wani irin ihu! tana tsalle radad'i da zafi ya isheta.


Amina ta jefar da kofin tayi kanta da gudu tana goge mata ita kuma sai kwara ruwa take a jikinta


Baba Ladidi ta karaso gurin tana salati tare da fad'in"Garin Yaya haka ta faru!? maza-maza ki cire rigar kai!!! abu baiyi dadi ba.


Yana tsaye daga inda yake yana kallonta tana kuka duk tayi wurjanjan da ita.

Baba Marka ta fito daga d'akinta tana fad'in"Jama'a wai meke faruwa ne? nake tajin kuka da hayaniya? Taga Sadam a tsaye bai ce mata komai ba sai ta karasa inda suke tana tambayar ba'asi Baba Kadi ta fad'a mata abunda ya faru....Tace"Sayyada wannan guje gujen naki bashi da amfani kinga abinda ya jawo miki ko."?

''Ni fa Baba ki 'kyaleni kar kiyi min wannan mitar taki kawai ki kyaleni naji da abunda nake ji." Tafad'a tana 'kokarin zare rigar jikinta wanda ko 'yar shimi babu Ita kuwa Baba Ladidi sai taya ta take.


Omar na ganin sun sa'bule rigar ya d'auke kansa da sauri sunkuyawa yayi ya d'auki ruwan zafinsa dake kan wuta ya kama hanyar bandaki.....Yana kauda kai ya isa inda suke tsautsayi yasa ya d'aga kansa aikuwa karaf! kan 'kananun brest d'in Sayyada da suke a tsaye kamar agwalima tas tas dasu shatin nipples din yayi baki abinka da farar fata....Tsigar jikinsa ta mi'ke yarrrr! cikin rashin hayyaci ya isa bakin rijiya ya ja ruwa ya sirka da sauri ya dauka ya shiga bandaki yana jin yanda gabansa ke harbawa alamun lafiya da kuma alamun sha'awar shi ta motsa.



Cikin dauriya yayi wankan ya fito da fuska a daure ko da ya fito sam! bai kalli inda suke ba ya nufi dakinsa domin kintsawa.

Baba Marka tace"Wannan dai sashanci ne Sayyada ki dauki rigarki ki mayar haba ai be dace ba ki cire riga alhalin kin san kin soma girma sai kace wata yarinya karama."


Baba Ladidi tace"A'a Marka 'konewa fa tayi kike cewa tasa riga mu bari dai gurin ya sha iska tukkuna idan rigar zata sai ta sa amma ba yanzu ba."


Marka tace"aishikkenan." Wucewa tayi dakinta ita kuma Amina ta dauko jug din ta fita Sayyada da Baba Ladi suka nufi daki Baba Ladidi na cewa "Zuwa anjima idan ba ta daina yi miki rad'adi ba sai muje gurin tofi."

Sayyada ta samu guri tayi rashe-rashe a tsakar da'ki kirji a bud'e saboda tsabar sangarta wai ita ta 'kone.

Baba Ladi ta fito ta d'ora musu kunu tana fad'in"Yau dai babu halin siyo mana kosai kenan dole in dauki mayafi inje da kaina bari dai na d'ora ruwan kunun."


Kullum daga 'bangaran Baba Tanko ana kawo musu kunu da yawa amma saboda rigima irin tasu ta tsofaffi sai suce sai sun dama da kansu Kawu Tanko da kansa yake siyo musu kosai iya inda zai ishe su amma sai sun kara siya idan yara sun shigo suyi ta raba musu, ganin yana wahalar da kansa yasa ya daina siya musu kosan shine suke bawa Sayyada na siyo musu kullm da safe.


Baba Marka ta fito da lullu'bi a kanta tace"To tunda kin d'aurewa 'yar aiken tamu gindi sai muje siyo kosan da kanmu." Tace."Marka kenan ba daure mata gindi nayi ba ni nasan sharrin 'konuwa shiyasa nace ta zauna babu riga yanzu tana iya saka rigar 'kunar tazo ta tashi kinga yanzu wa gari ya waya gwara a bari tasha iska tukkuna."

Baba Marka tace",To ashikkenan ni da ina ganin hakan bai dace ba tunda Sadam na gidan kinsan fa shi Namiji baya raina abu."

Ladi tayi dariya irin tasu ta tsaffi tace"Haba Marka kamar ba shi zai aure ta ba ai ba laifi bane kuma ba da gangan ta cire rigar ba, tsautsayi a ka samu."

Marka tace"Hakane kuma." Tace."Bari in dauko mayafi na muje gurin Tabawa me kosan."

Ladi ta yafa mayafi suka kama hanya suka fice daga gidan wai sun tafi siyo kosai.


Tsaf ya fito cikin kufta na yadin Kashmir yayi kyau sosai bai sanya hula ba saboda ba ma'abocin ta bane sai dai ya gyara sumarsa sosai sai kamshi yake mai dadi, jin gidan shiru yasa ya nufi dakin Baba Ladidi.


Al'marin yazo masa a bazata! yana d'aga labule ya ganta tayi wata iriyar kwanciya bacci ma takeyi.

Tsira mata ido yayi yana kallonta tas ya kare mata kallo sama da 'kasa ba kirjinta dake waje ba har dan pant dinta sai da ya hango sakamakon kwanciyar da tayi.

Rai a 'bace ya bude baki yana kiran "Baba Ladi.'! Shiru yaji ya saki labulan da sauri ya bude dakin Baba Marka bata nan da alama tare suka fita.


Tsakiyar tsakar gidan ya tsaya yana tunani, tsaki yaja ya sake daga labulan dakin Baba Ladidi tananan inda take sai

Please Login or Register in order to submit comment