Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aysha wallahi ina tsananin sonki, yanzu zan baki lkc kije kiyi tunani akai, zan dawo jibi in Allah ya kaimu na barki lpy. Jiki ba kwari na shiga Palo su mum suna nan zaune yanda na barsu dad ne ya kalleni harya tafi? Nace eh, to zo ki zauna nace to, sanan ya fara magana "alhaji Lawan uban gidana ne, yayi min abubuwa na alkairi Wanda bazan Iya saka mishi ba saidai nayi masa addua kawai. Tunda name dashi ban taba Neman Abu a wajensa na rasa ba, kullum addua nake Allah ya kawo ranar da zai nemi wani Abu a wajena, nima na saka mishi da abinda yake min, kwatsam sai gashi yazomin da maganar yanaso na bashi auranki. kuma aduniya ba abinda alhaji Lawan zai nema a wajena banyi mishi ba, sbd haka inaso kisa aranki shi na zaba miki a matsayin miji, kuma nasa date din daurin aure nan da 2 wks. Sanan lawyer n Mr kabeer yazo ya sameni yace mu tabbatar mun wanke Mr kabeer akan kazafin da akayi masa idan ba haka zasu shigar damu kotu,kuma kinsan banida kudin da zan Iya ja dashi, sbd haka inaso ki wanke shi a shirinku na gobe da zakiyi. Mum ce tace Amma daddyn yara taya zaayi ka rasa Wanda zaka aura mata sai tsoho, mutumin daya fika a hafe ma. Ya isa ya dakawa mum tsawa (abinda be taba mata a gabanmuba) indai akan alhaji Lawan ne karki kara yimin magana, na Riga na gama yanke hukunci, Ya mike ya tafi daki. kuka nake me taba zuciya mum me yake shirin faruwa dani ne? Me yasa dad ya zabi farin cikin uban gidansa fiye da farin cikin yarsa daya Haifa? Wallahi mum bana sansa tsohone sosai don Allah kiyi wani Abu akai. Kiyi hakuri Aysha zan yi mishi magana insha Allah bazaki aureshi ba, muje ki kwanta bazan taba barin farin cikin ki ya rushe ba, saida ta rakani har daki na kwanta sanan ta tafi, murmushin jin dadi nayi nace mum ba karamin sona take ba Allah ya bamu ikon yimusu biyayya.

Mama ce zaune a tsakiyar yayanta inajinki samira kikace deputy governor ne yazo gdn nan eh wallahi mama wata yar iskar dariya tayi lkc yayi da zan tarwatsa rayuwar Haj Jidda, na tabbata bazata so yatta ta auri tsoho ba kunga akwai rigima kenan, sabd haka zanje na sami boka dankundalo yayi min aikin da zasuyi rigimar da zata zama sanadiyar barinta gdn.

Maman Aysha
[9/9, 11:33] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
3⃣0βƒ£βž–3⃣5⃣

Banyi wani baccin kirki ba inayin sallar asuba na zauna kart har saida rana ta fito, nayi addua na roki Allah ya fitar dani daga halin da nake ciki. Jiki ba kwari na tafi na hada break past, sanan nayi wanka, na tashi twins din mum ma na musu sukaci abinci sanan na kaisu sch. Gida na dawo na kwanta banda tunani ba abinda nake dad ya rasa Wanda zai auramin sai tsoho? Yaushe dad ya zarme da son kudi da har yake son kuntata rayuwa ta? Why dad don Allah kuka me karfi yaci karfina, saida nayi me isata sanan naje na wanke fuskata. Sai wajen 10 suka tashi ina jin motsinsu na fice naje na durkusa na gaishe su dad yace ummina lpy baki fita aiki ba yau? Murmushin karfin hali nayi nace yanzu zan fita, yau bamu da aiki da yawa ne shi yasa. Alright, ya zauna yayi break sanan ya fice. Mum ce ta kalleni ana ganin fiskarki ansan kinyi kuka Aysha, don Allah kiyi hakuri ki fitar da mgnr nan a zuciyar ki, insha Allah komai zai daidaita kinji dota na nace Allah yasa mum tace amin, ke kinci abincin ne? Nace aa, to zauna kici. Sai wajen 11am na shiga office, ina shiga elbash ya biyo bayana beauty meke faruwa ne yau? Na kiraki yakai sau goma bakiyi picking ba, dama wani mutun ne ya kawo kukanshi, wai wani alhaji yasa anyi nakiya irin wacece ake idan zaa fasa dutse a jikin gdnsa, as a result ginin yana Neman rushewa, kuma ya fadawa alhajin Amma yaki ya tausaya mishi, so shine nakeso muje mu dauko gdn, abi mishi hakkinsa, nace to muje. Beauty yau kalau kk kuwa? Duk da nasan you're calm, Amma yau shirun naki yayi yawa, is like akwai abinda yake damtafi? Ba abinda yake damuna muje kawai, ban yadda ba don Allah ki fada min, ya salam elbash banason mgn da yawa fa, dariya yayi yace oh I see ashefa yan jarida basa son mgna, nima dariya nayi muka fita a tare.

8:pm
Jama'a assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa acikin wanan shiri namu na Ya Take Ne? A yau shirin namu zai fara ne da bawa the youngest multi billionaire Mr kabeer wato adon gari hakuri akan akasin da aka samu a shirin mu daya gabata. Kamar yadda kuka Sani pyramid TV gdn television ne da yake yada abubuwa domin a kwatawa talakawa yancinsu, wanan shine dalilin da yasa muka haskawa jama'a abinda baba dattijo ya sanar mana saidai da muka tsananta bincike mungano cewa abinda ya fada mana ba gaskiya bane sbd haka don Allah pyramid TV na Neman afuwa a wajen adon gari da masoyansa. Shirin da muke tafe dashi acikin wanan sati shine.......
Jama'a anan muka kawo karshen shirin mu na wanan satin, ina me matukar godiya ga masoyana, kuma ina me bakin cikin sanarda masoyana cewa daga yau bazaku kara ganina ba, idan da Wanda na taba batawa rai daga lkcn Dana fara gabatar da wanan shiri zuwa yanzu don Allah su yafemin, amadadin hukumar gdn pyramid TV ni ayshat Ahamad TURAKI nake cewa bissalam.
Ina fita daga show room din office dina na shiga na kifa kaina a table ina kuka me taba zuciya shikenan rayuwata ta ruguje wanan wane irin kaddara ne kuka nake sosai. Elbash ne ya shigo office din aidama na fada yau ranki a bace yake kk musamin, kuma naji kin fadawa mutane cewa daga yau bazasu kara ganin ki ba, akwai abinda kk boye min beauty, don Allah ki fadamin me yake faruwa dake? Ko duk shakuwar da mukayi har yanzu bankai matsayin da zaki fadamin damuwarki ba? Ba haka bane elbash, to indai ba haka bane fadamin what is wrong with you? Auran dole dad yakeso yayimin da mutumin da ya girmeshi ma ahaife, wai deputy governor dad yake son aura min nan da 1 wk, kukane yaci karfina don Allah kababi shawara elbash yanzu ya zanyi? Kiyi hakuri kiyi biyyaya Aysha, kana nufin nayi biyayya na auri tsoho me mata biyu da yayya goma? Na Sani is unfortunate Aysha, Amma idan kk mishi biyayya Allah sai yayi miki zsbin abinda yafi alkairi. Shikenan zan duba na gani, ni zan tafi saida safe to Allah ya kaimu

Maman Aysha
[9/9, 21:58] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
3⃣5βƒ£βž–4⃣0⃣

Washe gari
Yau ko office na kasa fita haka na wuni jiki asanyaye saidai INA kokari boye rashin hankalin da nake ciki sbd kar mum ta damu.

5pm
Zuciyata tace take min zafi, abin duniya ya dameni kuka kawai nake sonyi gashi ba dama mun tana nan, kawai saina yanke hukuncin fita zaga gari ko naji sanyi a zuciyata. Shiryawa nayi cikin wata English gown yellow rigar ta hadu sosai wajen 25k aka sayeta nayi rolling da wani karamin yellow mayafi sanan NASA black shoe&bag na manna dark brown glass nayi kyau sosai, sanan na shirya su basma da junior muka fito nacewa mum zamu Dan fita zaga gari tace to sai kun dawo Amma karku Dade kinsa yau Excellency zai zo nace to, na kama hanunsu muka nufi motata. Direct rose flower sweet and bakery muka tafi, wani waje ne dayake tashe akano adon gari ne ya bude wajen, sbd shima time to time yana zuwa ya huta awajen, Amma fa wajen yayyan masu kudi ne domin kuwa idan kudin ka bekai 20k ba, baka isa ka shiga wajen ba. Wajen a zagaye yake da lafiyayyun flowers kala kala, shi yasa akasa masa suna rose flower sweet and bakery. Wajene daya tattara haddadun yan mata da samari, Amma fa yayyan masu kudi, kuma dama don yan mata da samari kawai adon gari ya bude wajen. Muna shiga naje nayi mana ordering ice cream, pizza da kuma shawarma wata kujera na samu muka zauna na budewa su junior ice cream din na basu suna sha suna wasan su. Shiru nayi inata kallon yan mata da samarinsu kowa yana harkar gabansa cikin farin ciki da annushuwa, Abin very interest, nan take na tuna irin mijin da zan aura tsoho me yayya goma, ina!! Bazai yiyyu ba wallahi ai idan kanaso ka mure rayuwar aure to ka auri yaro daidai dakai, Amma tsoho me zai Iya? Wasu zafafan hawaye ne suka fara yawo a kumatuna, kamar daga sama sainaji wasu yan mata sun hada baki wajen cewa waww!! ADON GARI, Kuma a lkc guda naga gabadaya hankalin yan matan wajen yayi gunsa harda wadanda suke tare da samarinsu, nima juyawa nayi domin na kashe kwarkwatar idona. Sanye yake cikin wasu shegun black jeans and shirt, a jikin shirt din an rubuta SMART GUY da red paint, sanan ya Dora red jacket akai gashin kansa ya kwanta yayi lub gwanin ban sha'awa, yasa red flat cover shoe me mugun tsada, idonsa a rufe yake da Dan karamin farin sun glass dauke yake da murmushi a fuskarsa da alama waya yake, kuma daga gani wacece yake wayar da ita tana da matukar muhimanci awajensa. Haka yazo ya wuce ta gabanmu da body guards dinsa guda 6 ya nufi wani special waje da akayi fencing da wasu shegun flowers kuma aka zuba lafiyayyun kujeru na hutawa aciki.dama sbd shi aka tanadi wajen. Daya daga cikin yan matan da suke gefena tace alhamdulilla yau kwana na biyar ina zuwa wajen nan sabd naga adon gari Amma ban ganshi ba sai yau, dayar tace ni kuma zuwa na uku kenan, dayar da aka kira da Rashida tace oh iska tana wahalar da me kayan kara Ku duba fa kuga duk kafe shi da idon da mukayi muna kallonsa shi besam ma munayi ba. Nima a zuciyata nace tabbas adon gari ya hadu ba karya, lkcn da mukayi fada dashi ganin tsoro nayi masa shi yasa ban kare masa kallo ba, inama yace yana sona, nan take na tuno da matsalar da take gabana ta auran tsoho bansan lkcn dana fara kuka ba, kifa kaina nayi akan table inata gurzar kuka.
Basma da junior kuwa suna ganin wucewar KB sai suka bi bayansa har cikin wajen suka farayi masa surutu, yaran sun burgeshi sosai besan lkcn daya beye musu ba sunata bashi dariya yace wa yazo daku nan sukace da auntynmu muka zo, yace OK, apple ya dauko ya basu sukai ta murna. Saida nayi kuka me isata harna gaji, na manta nazo da yara saida na duba inda suke wasa naga ban gansu ba, nan take na fara nemansu duk inda nake tunanin zasu na duba bangansu ba saida naje har bakin gate din shigowa Amma ba alamsrsu. A bangaren yaran kuma, KB zai tafi sai ya kamo hannunsu yace muje na rakaku wajen Aunty nku ni zan tafi gida, da suka nuna mishi inda na zauna sukaga bana nan ran KB ya baci kallon su yayi yace tuda auntynku ta gudu ta barku muje na kaiku gdna shikenan na sami yayya, zaku Bini sukace eh a tare, aikuwa yayi wajen motarsa dasu. Ni kuma a dawo daga bakin gate kenan cikin fargaba da tashin hankali kawai sainagano su suna shirin shiga motar, da sauri na tafi wajen Malam ya haka? Kawai daga ganin yara saika sasu a mota, Ashe suna wajenka, inata shan wahalar nemansu........Shut up marar tarbiya kawai, kin tafi yawon banza kin barsu, wa ya fada miki ana zuwa da yara nan wajen? Inaso ki Sani daga yau idan zaki fito yawon iskancin ki karki kara tahowa dasu, ki barsu agida. Kallonsa nayi da idona daya gama rinewa sanan nace ni ba yar iska bace, kuma idan har nasan yawon iskanci zanzo ai bazan tahoda yara ba, kuma idan da gaske iskanci ake awajen nan ai kafi kowa daukar zunubi tunda Kai ka bude wajen, nagode da kulawarka akan kannena. Wani irin kallo tsana ya bini dashi sanan yace stupid girl. Ban kara bi ta kansa ba na kama hannunsu muka tafi.

Maman Aysha
[9/10, 12:11] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
4⃣0βƒ£βž–4⃣5⃣

8:15pm
Na idar da sallar isha'i ina zaune ina lazimi na jiyo muryar dad yana kwalla min kira da sauri na fita, ina zuwa yace kiyi masa ki shirya Excellency yana jiranki cikin fargaba nace to, haka kawai naji gabana yana faduwa. Dake ban cire hijabin da nayi salla ba takalmina kawai nasa na fice. Saida nayi addua sanan nayi sallam na shiga ya amsa yana bina da wani mayyatacen kallo. Dukusawa nayi na gaisheshi, sanan yace kamar yadda mahaifinki ya Sanar dani kun riga kun gama magna, so bana bukatar jin ra'ayinki akaina. Abinda ya kawoni shine inaso kiyi list din abubuwan da kk bukata na hidimar biki. Cikin tashin hankali na dago muka hada ido dashi kawai saina fashe da kuka lalle ka tabbata marar adalci, sbd da kana da adalci danka yakamata ka nemawa aurena bakaida kanka ba, kuma kai mutun ne me tsananin sonkai sbd baka damu da yanda rayuwata zata Kasan ce ba idan na auri tsoho irin ka, kai kawai burinka ka mallake ni, to wallahi inaso kasani bana sonka, bana kaunarka, kuma wallahi saidai akai gawata gdnka domin kuwa dana aureka gara na kashe kaina da gudu na fice na barshi a wajen ina kuka me tsanani, mum tana zaune a falo(dake yau dad a part din mama yake) na wuceta da gudu na shiga dakina, cikin tashin hankalin ta biyoni me ya faru Dota? Me yasameki kk wanan kukan haka? Mum wallahi bana son shi, wallahi idan na aureshi mutuwa zanyi. Zatayi mgana kenan naga ambanko kofar dakin da sauri dad ne cikin bacin ran da bantaba gani a fuskarsa ba yace Ku fito falo inason ganin ku . mum ta kama hannuna muka fita, muna zuwa muka sami mama da Zainab da samira a zaune, cikin kakkausar murya dad ya fara magna Aysha naji rashin kunyar da kikayiwa Excellency, kin nunawa duniya cewa ni ban isa dake ba. Tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage, bata mage, wanan Karin magana haka yake. Yau zan fada muku abinda Baku taba Sani ba, kawai sainaga mum ta mike a zabure ta durkusa ta rike kafafunsa tana wani irin kuka me tsanani don Allah alhaji kayi hakuri da fadar maganar nan, kayimin alkawari ba Wanda zaiji mgnar nan meyasa zaka fada yanzu? Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata yimin shiru ko ban fada yanzu ba dama wataran dole maganar ta fito, cikin wata dakkyakiyar murya yace Aisha nace na'am inaso yau ki Sani bani na haifeki ba.....innalillahi was inna ilaihir rajuun juyawa nayi na kalli mum nace waye mahaifina? Kamar daga sama naji muryar dad yace itama ba ita ta haifeki ba nan take na fadi sumammiya da gudu aka sami ruwa aka yayyafamin sanan na farfado rungume mum nayi ina kuka me tsuma zuciya nace mum don Allah kice min ba gaskiya bane, don Allah kice ba gaskiya dad yake fada ba, batayi magana ba sai kuka da take me tsanani. Mutsitsika idona na farayi ya Allah kasa mafarki nake....muryar dad ce ta katseni da cewa ba mafarki kike ba dagaske ne bamu muka haifeki ba, wato abinda ya faru shine....

18yrs back
Nakai Jidda asibiti bada shirin haihuwa mukaje ba sbd cikin wata 7 ne, saidai muna zuwa da aka dubata sai akace haihuwa ce, haka na zauna inata addua har Allah ya sauketa lpy, da sauri nurse din tazo tace na kawo kayan baby, sai alokacun na tuna bamu dakko ba, sai nace Amma zanje na kawo yanzu tunda ba nisa sosai. Harna shiga mota zan tayar sai nurse din ta kara fitowa da sauri tacemin iam sorry to say babyn ta koma, saida ka debowa uwar kayanta jiki ba kwari nace to na tafi. Na wuce ta jkin wani gdn gona saina hango cincirindon mutane, sai nima na karasa wajen na tambayi me ya faru sukace wata mata ce ta sato jaririya, ta fada cewa wani Dan siyasa ne yasata ta sato masa yar, Amma bata karasa bayani ba ta mutun, nace INA yar aka miko min ke kinata shan hannu kina kuka, shine na roki yansanda da su barmin ke zan rikeki. Nan take mukaje police station aka bude miki file, suka bani takardu nayi signing aka kafa shedu, sanan na basu cikkaken address dina, na barki a hannun yan sandan na koma asibiti bayan ansallamo Jidda direct police station muka wuce, nayi mata bayanin komai sanan na damka amanarki a wajenta tare da alkawarin ba Wanda zaiji sai ranar auranki.

Wanan shine abinda ya faru kuma nayiwa Excellency bayanin komai yace ya yadda zai aureki a haka, Amma dake baki da mutunci, kuma ke ba gudar jinina bace kika ki bin umarni na, sbd haka inaso ki Sani daga yau bani bake, ki tattara komatsanki kibarmin gdna sbd ko yar Dana Haifa acikina bata isa ta kaucewa umarnina kuma naci gaba da zama da itaba, ballantana ke yar tsintuwa, sbd haka ki manta da kin taba sanin wani me kama dani arayuwarki, mun rabu dake har abada. Mum yace idan ka mata haka bakayi adalci ba, ina kake tunanin zata nufa yanzu? Ta tafi ko inama niba damuwata bace. Tabbas ba damuwarka bace sabda bakai ka haifeta ba, Amma inaso kasani ba ita kadai ka kora ba harni ka kora domin kuwa bazan taba zama agdn nan ba tare da Aysha ba.

Maman Aysha
[9/10, 15:15] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
4⃣5βƒ£βž–5⃣0⃣

Mama ce tayi wata shewa aidama ance sannu sannu bata had a zuwa, nidama nasan komai Daren dadewa asiri zai tonu, an Dade ana nunawa yayyana banbaci agdnan akan ki Ashe ma yar cin arziki ce, Allah ya raka taki gona. Haka na mike na fara Jan kafata da kyar na shiga daki da tattara kayan da nasan zasu min amfani, na janyo katuwar troly na hayen idona ya kafe, Ashe idan mutun yana kuka da hawaye ma rahamane? Falon na dawo na durkusa agaban Abba nace ga mukullin motarka nagode da kulawar da kuka bani, kuma harna mutu bazan taba taba mantawa da abinda kukayimin na alkairi, nagode Allah ya saka muku da alkairi Allah ya biyaku da gdn aljanna. A dakire yace ki rike motar ai taki ce, jiki ba kwari na mike nace mum don Allah ki yafemin, nasan kinyi dawainiya dani irin wadda kowacce Uwa takewa danta,kinyi fama dani tun ina jaririya nagode Allah ya saka miki da mafificin alkairi, kuma insha Allah zanci gaba dayi miki addua irinta da da mahaifi harna koma ga mahallicina, nagode Allah ya kaddara saduwarmu. Jan trolley nayi nafara tfy, da sauri mum ta rike hannuna jirani nazo mu tafi Aysha, ai nima na gama zama a gdnan sbd yau alhaji ya tabbatar min da ya daina sona, tunda ya koreki banga amfanin cigaba da zama dashi ba, alhaji rubutamin takarda ta mu taffadAi idan kinga mun rabu saidai idan mutuwace ta raba, kuma in banda ke da abinki kin manta cewa ni na baki amanar Aisha, kuma yanzu na karba sbd haka yanda na koreta kema dole kiyi hakuri da ita barima ki gani, wayarsa ya dauko ya kira abbanta bayan sun gaisa ya fada masa duk abinda ya faru, shi kuma yace a bata wayar yana bata abbanta yace mijinki ya fadamin abinda yake faruwa, sbd haka kibi umarnin sa idan kika sake kika fita daga gdn bada izninsa ba, ban yafe miki ba kina jina ko? Cikin tsananin kuka tace eh, sanan dad ya kalleni yace you can go. Harna je bakin kofa mum ta kara kirana daki ta koma ta debo wasu kaya ta miko min, wanan sune kayan da suke jikinki lkcn da muka karfeki, wanan kuma zanin goyen ne, wanan kuma sarka tace lkcn dana saya 500k ce Amma yanzu nasan tafi haka ki sayar kiyi amfani da kudin. Inayi miki addua Allah ya takaita miki wahala, yayi gaggawar hadaki da iyayenki cikin dauko, Allah yayi miki albarka kawai ta juya daki da sauri, nima da gudu na bude motata na fita daga gdn.

AmmaTafiya nake Amma bansan inda na nufa ba, saida nayi tafiya me nisa har na Dan wuce BUK new side sanan na tsaya a gefen titi na kifa kaina akan sitayari na fara kuka, ban farga ba naga 10:45pm na kalli wajen da nake ko motsin mutane babu, elbash ne ya fadomin a rai kawai saina kirashi hlo beauty ya akayi? Kazo kan titin gwarzo road gaba da new side kadan ina wajen. Tuki yake kamar zai tashi sama sbd shi a bompai yake, akwai nisa a tsakaninsu Amma sabd gudun da yake sharawa, kuma ba yawan motoci sbd dare ya fara a 30minute yaje wajen acikin mota ya sameni beauty meya faru kika zo bayan gari kika zauna? Cikin kuka nace komai ma ya faru elbash su dad basu suka haifeni ba, bansan iyayena ba, ba wani mutun da zan nuna nace Dan Uwana ne, bansani ba ko iyayena suna dare ko babu dad ya koreni a gdnsa yanzu banida kowa aduniya kuka yaci karfina. Ya salam Aysha zaki Iya driving? nace eh, to shiga mubar wajen nan ki shiga gaba zan ringa binki a baya zoo road zamu kinji nace to.

Maman Aysha
[9/15, 11:22] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
5⃣0βƒ£βž–5⃣5⃣

Tun a hanya ya sanar da Yaya bilal suna zuwa brodan Elbash ne Uwa daya uba daya. suna isa kofar gdn aka bude musu gate suka shiga da motocinsu matar Yaya bilal da faraarta ta karbe mu, sanan aka kaimin kayana guest room, elbash ya kira yayanshi gefe yayi masa bayanin komai sanan ya rokeshi alfarmar na zauna a gdnsa zuwa next WK idan amaryarsa ta tare sai na koma gdnsa. Ni kuwa tunda na shiga guest room din nake kuka Wanan wane irin rayuwa ce? Dad meyasa kayimin haka don Allah? Me yasa bakayi hakuri kaci gaba da zama dani ba why pliss? Kuka nake me tsanani kaina banda ciwo ba abinda yake elbash ne ya shigo dakin Aysha har yanzu baki dena kuka ba? Don Allah kiyi hakuri nasan kina cikin wani hali Amma ki sani akwai Allah, kuma shi yafi kowa sanin abinda yasa kika sami kanki acikin wanan halin, inaso ki mika al amuranki a wajen Allah, kuma kiyi tawwakali insha Allah zai zame miki alkairi, nima nabar aiki a pyramidTV, sbd ke dama na nemi aiki a wajen, so tunda yanzu bakyanan nima dole na tafi. Wato abinda ya faru kafin na fara aiki a pyramid TV ina daya daga cikin masoya kallon program dinki, kuma cikin lkc kadan naji na kamu da sonki kawai saina yiwa dad dina mgn inaso ya Samar min aiki a pyramid da yaki Amma dana matsa masa dole yaje ya sama min, ranar dana fara reporting na roki manaja daya hadani aiki dake sbd na sami saukin samun kanki, saidai Dan banzan kwarjininki ya hana nayi miki mgn, daga baya saina gane kinfi karfina sbd ke zubin matar manya ce irinsu adon gari, tun daga lkcn na canja son da nake miki da irin Wanda Yaya yakewa kawarsa, ina tsananin sonki beauty ina jinki tamkar ciki daya muka fito dake. Sbd haka don Allah ki dena cewa baki da kowa ni zan zame miki Uwa, uba, kuma broda in Allah ya yadda zan rikeki a bisa amana kuma zan temaka miki wajen nemo familynki. Na sami aiki a CBN kuma next WK ne daurin aurena Sbd haka zaki zauna anan gdn zuwa next WK idan amaryata ta

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment