Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ai. To ya zakiyi da Faisal? Zaki iya coping da rashin ganin sa harna 2 wks? A zuciyata nace wanan mutumin Dan renin hankali ne, kodai ya gane na kamu da sonshi, shiyasa yake min haka? Amma a fili sai nace face dinsa kawai nayi missing, Amma ruhin mu yanan manne da juna, da har nake jin kamar muna tare. Yanayin sa ne ya canja, cikin shan mur yace min gud nyt.

Yanayin yanda ya shiga damuwar nima sainaji banji dadi ba, jiki ba kwari na shiga gdn aunty Salma tace ya tafi nace eh, to zauna muyi wata magna dake nace to da gaske ne kin dauke ni a matsayin blood sister ki? Nace eh, zanyi miki tambaya Amma don Allah Aysha karki boye min komai ki fadamin gaskyr abinda yake cikin zuciyrki nace to, a zaman da nayi daku na sati daya nan, na fahimci akwai soyayya me zafi tsakanin ki da broda saidai kunki Ku gaskanta hakan a junanku, Sbd haka inaso ki fadamin kina sonsa? Kuka na fara eh ina sonsa Amma kuma nasan yafi karfina, nayi kokarin hana zuciyata ta kamu da sonshi, but I fell, ina tsananin sonshi Amma ba yanda zaayi kabeer ya auri marar asali Irina,,,,,sauri tayi ta rufemin baki karki damu shima yana sonki, naga zallar sonki a kwayar idonsa, nafi kowa sanin halinsa Aysha, kuma inaso ki Sani a sanina bayan ni, kece mace ta farko da kabeer yake zama yayi hira da ita cikin sakin fuska, kice mace ta farko da kabeer ya fita outing da ita, sanan kece mace ta farko da Ya nunawa caring, wanan shi ya tabbatar min da cewa he is in Luv wit you, kuma kema kinyi deserving a so ki, kinada wasu qualities da sai an Tara mata dubu baa sami guda goma irinki ba, matsalar ki guda daya rashin sanin iyayenki, wanan kuma bazai hada aure ba indai yana sonki, mun barwa Allah, yafi mu sanin dalilin da yasa yayi haka. Idan ba zaki damu ba inaso ki ringa amsa wayar Faisal a gabn broda kinji? Nace to, zaki iya tafiya saida safe nace Allah ya kaimu

Washe gari

Sai wajen 9am na tashi na shirya break fast, yau kunun gyda da kosai nayi Sbd aunty Salma tanaso sanan na soya Irish da plantain na dafa ruwan tea komawa daki nayi nai wanka, nasa wata English gown peech color nayi fakin din gashina ya kwanta luf a gadon bayana, idan ka ganni saika ce swara ce, Sbd muna kama sosai, saidai ni dimple dina ya fito sosai.

Sai wajen 9:30 ya shigo gdn a dinning ya samemu muna cin abinci, shima yazo yayi joining dinmu ba karamin murna yayi ba daya samu kunu da kosai Sbd yanaso sosai kallona yayi yace kinji dadin ki Aysha, gaskiya Faisal ya more bakida kiwa irin ta yan matan zamanin nan Aunty Salma tayi dariya tace gaji da shi, wanan santi kawai kake wa mutane, sai yau Kasan bata da kiwa daka kwashi koko da kosai? Phone dina ce ta fara kuka, INA dauka cikin sansanyar murya nace hlo swit heart gud morning, morning my dear I hope kin fara shirin tahowa dai ko? Wallahi an fasa tafiyar sai next WK, what? Ke bakya tausayina ne? Baki damu ma da halin da nake ciki ba ko? Aysha ko kin daina sona ne? Kinsan da yadda nayi 1 WK din nan kuwa? Wallahi ina sonka swit heart, I miss you beyond your expectations, ba yanda zanyi ne shiyasa don Allah ka kara hakuri, iam begging pliss! Naji Amma gobe zan taho abj idan yaso ma taho tare, Kayi hakuri don Allah, me gidan yayi tfy, may b bazai kai 1 WK din ba ma, kuma yana dawowa zan taho, bakya so nazo? Inaso mana, banaso kabar wajen aikinka ne to shikenan zan duba na gani, alright, bye take care I miss you, I miss you too.

Cikin nishadi adon gari yake cin kosan, Amma ina fara waya da Faisal yaji ya fita a ransa Amma haka yaci gaba da cusawa, wani irin kishi ne ya addabi zuciyarsa da kyar ya samu yayi controlling Kansa, Amma dayake he is very smart duk kallon da aunty Salma ta kafeshi dashi bata gano wani abu a fuskarsa ba. Muna gama wayar aunty Salma tace Faisal ne ko? Nace eh, ko cewa yayi zai biyoki? Nace eh, to ai da kin kyaleshi yazo, yanada gaskiya fa Aysha, Allah ya taimake shi ya sami finan discission irin ki ai bazai yi da wasa ba, ai komai yayi akan ki be fadi ba bcos you deserve it, wani irin shu'umin murmushi yayi yace sister iam going, nan take naji gabana ya yanke ya fadi, na rasa abinda yake min dadi aunty Salma ce tace tun yanzu? I have a lot to do ko kinsan Mutanen da Suleiman PA ya bawa appointment din ganina sunfi mutun Dari, kuma nayi missing mum sosai I need to see her. Shikenan Allah ya kaika lpy yace amin, kafeni yayi da sexy eyes dinsa yace Mrs Faisal me zance masa idan naje? Tell him dat I really miss him, OK I will, na tafi sai munyi waya nace to Allah ya kiyaye

Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/1, 10:44] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣6⃣0βƒ£βž–1⃣6⃣5⃣

Yana sauka a Kano ya tarar da jerin motocinsa sun zo daukar sa, direct gdn mum dinsa ya wuce a Nasarawa GRA yana shiga yaje yayi hugging dinta yace I miss you mum, I miss you too my son, ya sister ka da yaran? Lpy kalau tace na gaisheki ina amsawa, iam feeling Hungary me kk dafa min? Favorite dinka nayi kuma da kaina nayi maka, oh thank you mum may god bless you wit Aljannar firdaus murmushin jin dadi tayi tace amin son. Dakin sa na gdn ya shiga yayi wanka Yasa wata yellow shirt da black jeans Sanan ya zauna yaci abincin, saidai wani Abu daya tsaya masa a rai shine test din girkin Aysha kawai yake son ci, wani irin missing dinta yake, kadan yaci abincin yaji ya fita akansa jinsa yake kamar wani marar lpy, kallon da mum take binsa dashi ne yasa ya waske ya fara wata irin faraa Wato mum har yanzu kina nan da girkinki me dadi, abincin yayi dadi sosai wallahi murmushi tayi irin na manya sanan tace ai kuma bakaci da yawa ba, ah naci da yawa mana kinga fa kadan na rage, to idan ka gama inaso muyi magana dakai, gabanshi ne ya fadi Amma saiya daure yace na gama, dama so nake na tambaye ka lkcn da kaje Kaduna ka gaisa da neehal kuwa? Aa ai bamu hadu ba ma, me yasa? Ai na fada maka duk yanda zakayi ka nemeta Ku gaisa, Wallahi nima naso hakan tafiyar data tasomin zuwa abj ne tasa bamu hadu ba, Amma ita ta ganka ai, Kaine baka ganta ba. Inaso ka Sani har yanzu hanklina be kwanta da zubaida ba, dandai kace ita kk so ne, Amma idan har zakabi umarni na nafiso ka auri neehal Sbd kyakyawar yarinya ce da saika hada yan mata dari baka samu guda daya kamarta ba, kuma gata yar manyan mutane, na Dade inaso naga mun hada jini da familyn Alhaji Abdullahi Idris makarfi, don Allah son kayi hakuri ka cikamin burina. Duk da sanyin A/c dayake dakin saida gumi ya jike shi jagab, zuciyarshi yaji tana bugawa duk duniya ba wacce yakeso yaga farin cikin ta irin mum, yana tsananin gudun bacin ranta ya zama dole kenan ya auri neehal, kallon mum yayi yace to amma mun kun binciketa sosai? Kinsan fa bazata rasa Wanda yake sonta ba, na tabatta zatayi kotanason wani bazata ki auran ka ba, Sbd ba matar da zata Dora ido akan ka bataji ta kamu da sonka ba iam proud of you my son murmushin yake yayi yace Allah ya zabar mana abinda yafi alkairi, Amma don Allah mum karki ma iyayenta zancen tukun, ba komai ne yake burge wasu matan ba, ki bari mu dedeta kanmu tukun, shikenan my son Allah yayi maka albarka yace amin, a gdn ta yau yayi niyar kwana Amma sai ya fasa yayi mata sallama ya tafi gd.

Yana zuwa gd wanka yayi ya kwanta akan gado, Amma Sam bacci yaki zuwa, fuskar Aysha kawai yake gani a idonsa, tabbas yana son Aysha so me tsanani, bazai iya tuna lkcn daya fara sonta ba, shidai kawai abinda ya Sani shine sonta ya Riga ya gama yi masa illa a kowanne bangare na jikinsa, be taba sanin ya so yake ba sai akanta, kuma bazai taba iya rayuwa ba tare da ita ba Aysha ce rsyuwarsa itace farin cikin sa, itace komai nashi yanzu ya zaiyi da mum? Ta Yaya zai fuskanci mum yace bayason neehal Aysha yake so? Ta Yaya zai tunkari mum ya fada mata yarinyar da yake so baa San asalinta ba? Tabbas idan taji lbrn ta bazata taba amince maka aurenta ba wata zuciyar ta bashi amsa, ba abinda yake son gani yanzu kamar aysha, yayi missing cuty face dinta, smiling dinta, wani irin kuka ne me karfi ya kwace masa haka ya zauna saida yayi me isarsa, muryarta kawai yake son ji, kawai sai ya dauki phone dinsa ya fara dialing......

Tunda ya tafi naji gabadaya garin yayi min zafi nayi kokarin na boye damuwa ta Amma na kasa har aunty Salma ta gane halin da nake ciki, yau ko hirar da muka saba munayi na kasa da wuri na koma daki na kwanta tunanin sa ya addabi zuciyata, wasu zafafan hawaye ne suka fara zarya a fuskata, daidai nan phone dina ta fara kara ina dauka yace me kike baiiyi bacci ba Aysha? A zuciyata nace Dan renin sense, shi meya hanashi baccin? Kamar yasan tunanin da nake sainaji yace harna fara bacci saina tuna na taho na barki a wani gari da baki saba sosai ba, sai nake ji kamar na takura miki, kuma nayi wa Allah alkawari zan rike ki bisa amana, zan kula da farin cikin ki har zuwa ranar da zan aurar dake, wanan dalilin ne yasa nace bari na tabbatar da kina cikin farin ciki kafin na kwanta, kuma da alama you're not in d mood, nasan tunanin Faisal ne matsalar ki, so zanzo na tafi dake gobe Sbd bana so na karya alkawarin Dana daukar wa Allah akan zan baki farin ciki, be jira abinda zance ba ya kashe wayar. Wato badan yayi missing dina ya kirani ba? Meyasa baya sona? Meyasa har yanzu ya kasa ganewa iam in Luv wit him? Farin ciki ka Dade da rabani dashi Kabeer, tun ranar dana kamu da sonka na rasa farin cikina kuka ne me karfi yaci karfina dakyar na samu nayi bacci

Maman Aysha
[10/2, 12:53] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣6⃣5βƒ£βž–1⃣7⃣0⃣

Washe gari
Yau ya kama Saturday bamu tashi da wuri ba sai 9am da sauri na shiga kitchen na hada break fast muna gama ci naje na gyara dakina Dana aunty Salma, sanan nayiwa su khairat wanka nima wankan na shiga ina fitowa na shirya cikin wasu English wear's rigar pink ce tanada Dan tsayi, amma bata karasa gwiwa ba sai blue jeans kayan sun kamani sunyi min kyau sosai, kara taje kaina nayi na daure da band ya kwanta a gadon bayana, make up nayi sosai Sbd yau har janbaki nasa me karatu Baku ganni ba nayi kyau kamar a sace ni, idan ba magana nayi ba sai Ku rantse daga kasar India nakeπŸ˜€lol

Ina fitowa naga nabil da khairat sunata kokawa akan ball, rarrashinsu nayi nace suzo muje garden din gdn muyi ball, aikuwa suka biyoni da gudunsu iskace me dadi take kadawa dake lkcn damina ne, da gudu muka shiga garden din muka fara ball da muka gaji da ball din sai muka Fara wasan gudu duk Wanda ya kamani saina cillashi sama na cafe, saina kara zubawa a guje yaran iya karfinsu suke bina Amma sun kasa kamani Sbd gudu nake sosai.

Shigowarsa gdn kenan har yaje bakin kofar falo saiya jiyo hayaniyarsu a garden, kawai saiya nufi wajen rungume hannunsa kawai yayi ya zuba musu ido yana kallonsu fuskarsa dauke da wani smiling da shi kade ne yasan maanarshi zuciyarsa ce ta fara bugawa, ba abinda yakeso irin yajita ajikinsa, a hankali lebensa ya furta I Luv you Aysha.

Kafafuwa na naji sun gaji da gudun, na juya baya naga still suna bina sai kawai na fara Neman inda zan boye musu, ta bayan wasu dogayen Flowers na shiga, ina juyowa naci karo da wata bishiyar fulawa na tafi luuu zan fadi Sbd dama na gaji, lumshe idona nayi INA zuba ido na ganni a kasa, kawai sainaji ni a jikin Abu me taushi kamar auduga, kamshin turarensa ne ya farkar dani daga duniyar Dana shiga a hankali na bude idona muna hada ido ya sakar min wani lallausan smiling dinshi me tsada, bansan lkcn Dana mayar masa ba, kyakyawar fuskarsa na zubawa ido INA kallo, a zuciyata nace kana tambayar me yasa mata suke binka? Abinda suke bi ai ba boyayye bane kabeer, zallar kyaun da Allah yayi maka suke bi, tabbas kabeer kayi gaskiya da kace dakai mace ne da nikaf zaka ringa sawa bcos you are more than handsome kanada kyau kabeer, ya Allah ka mallakamin kabeer, Allah ka taimake ni kayimin wanan gatan, ADON GARI sunan ya dace dashi sosai tabass kabeer adon gari ne da kowacce mace zatayi burin ta mallake shi hawaye ne ya zubo a idona batare da nasan fitowarsa ba.....katse min tunani yayi da cewa ya salm aysha kuka kike? Ko kin bige ne? Nace aa to meyasaki kuka? Ohh sabd na rikeki ko? Iam sorry naga zaki fadi ne shiyasa, da sauri ya sake ni sanan ya zubamin sexy eyes dinsa yace kike fitowa ba dankwali ko? Kuma yanzu idan wani yazo ya ganki a haka fa? Cikin shagwaba dani kaina bansan na iyaba nace wallahi dankalin ne nauyinsa nake ji, yaushe ka shigo garin? Zuwana kenan ko cikin gdn ban shiga ba dariya nayi me karamin kyau sanan nace eyya to mu karasa cikin gdn muna fitowa naga su nabil sai nemana suke da gudu sukazo suka rungume shi suna cewa oyoyo uncle, lkc guda muka shiga cikin gdn aunty Salma tana zaune a falo da mamaki ta kalle shi tace broda yaushe a gari? Ina fata dai lpy? Relax sis every thing is normal, kawai dai nazo na tafi da Aysha ne, abinka da yan uwan da suka shaku da juna, tana jin voice dinsa ta gane acikin damuwa yake maganar. Mikewa tayi ta kama hannunsa suka nufi bed room dinta

For correction or contributions 08067063932

Maman Aysha
[10/2, 20:17] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣7⃣0βƒ£βž–1⃣7⃣5⃣

A bakin gado ta zaunar dashi sanan ta dubeshi tace nasan ko waye kanina, mutun ne me dauriya da zurfin ciki, sanan baka da sa Abu arai, komai da sauki kake daukar sa, kuma na Sani baka iya karya ba kuma baka son meyinta, kallo daya nayi maka na gane kana cikin matsaneciyar damuwa zama tayi a kusa dashi ta dafa kamanarsa sanan tace pliss my broda tell me the truth me yake damunka? Yar gdn senator Abdullahin Idris makarfi mum take son auramin, kinfi kowa sanin yanda mum ta dauka ki Mutanen nan, batason yan uwanta kamar yadda take son Haj Asiya, ba abinda bazata iya yimin ba idan naki bin umarninta. Ni kuma zuciyata Aysha takeso, INA son Aysha so me tsanani, mutuwa zanyi idan ban auri Aysha ba sister, kuma kinsan abin is very complicated iam very sure koba case din neehal mum bazata taba bari na auri Aysha ba indai taji lbrnta, wani irin kuka ya fara me ban tausayi iam confuse sister, iam totally comfuse pliss help me wallahi bansan ya zanyi ba nidai abinda na Sani kawai shine aysha ce rayuwata inhar ban auri Aysha ba to zaku rasani. Itama kukan take tabbas Aysha tafi dacewa dakai akan kowacce mace a duniya, kuma nima INA goyon bayanka, kuma daidai ta shigo da maganar auran neehal ne, da zamu samu a janye wanan maganar da sai indai karfin mu ya kare wajen ganin tayi accepting din Aysha. Sbd haka kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, ka mika alamuranka a wajen Allah idan har aysha matar kace duk duniya ba Wanda ya isa ya hana, kadai yanzu kayi tunanin yanda zaka soke maganar neehal, zanyi insha Allah, nifa rabona da neehal dinma tun bata fi 8 yrs ba, idan muka hadu a hanya ma bazan ganeta ba, gaskiya nima na manta kamanin yarinyar. Shikenan zamuje mu tafi INA matukar alfahari da samun yar Uwa kamarki, Allah ya raya miki zuria'arki. Kiyi hakuri da dauke Ayshan da zanyi, wallahi na kasa jure rashin ta a kusa dani, tunda na koma na kasa baccin kirki, dariya tayi tace ai na dade da ganoka amma sai kayi disguising dinmu, shima dariya yayi sanan suka fito a tare.

A kitchen ya same ni na Dora lunch ya watsa min wani shu'umin kallo yace zuwa nayi na tafi dake, Sbd Faisal ya matsamin dole saina dawo mishi da matarsa, dariya nayi nace kuma kaga be fadamin ba, dama ai bazai fada miki ba, kuma nima bance ki fada masa ba. Juyowa nayi muka hada ido nayi dariya nace bazan fada ba, me like dafa mana ne? Favourite dinka nake dariya yayi da har saida fararen hakoransa suka fito sanan yace kinsan favorite dina ne? Nace eh mana, to meye? Pounded yam wit egusi soup dariya yayi sosai yace baki canka ba dambu ne favorite food dina, ohhh sorry kuma wallahi baba mero ta taba fadamin, shagwabe fuska nayi nace Amma zakaci wanan dima ai ko? Kai kawai ya daga min ya fice yana dariya. Cikin kankanin lkc nagama komai na jera a dining, duk inda nayi idonsa a kaina yake har muka zo cin abinci, nan ma ya kafeni da ido, sainaji duk na kasa sakewa Dan kadan naci abincin na mike na koma daki, shi kuwa zama yayi yaci ya koshi bayan ya gama ya biyoni har daki yace nazo mutafi, sai alokacin naji hankalina ya tashi Sbd mun saba da aunty Salma sosai har waje ta rakoni ta hadamin shatara na arziki muna zuwa bakin mota naga yanda jikin su yayi sanyi itada su nabil sainaji kamar kar na tafi, kawai saina Dora kaina a jikin motar na fara kuka, dama itama kadan take jira kawai saita karaso ta rungume ni tana kuka, folding din hanunsa yayi ya zuba mana ido yana kallon mu dayaga abin bana kare bane sai kawai ya janye aunty Salma ya maida ita gida, harya dawo INA kuka kama hannuna yayi yasani a mota driver shi ya bude masa ya shiga ya zauna a kusa dani, driver ya ja muka nufi airport.

Muna sauka a kano escort dinsa suka zo suka dauke mu, direct gdna muka wuce muna shiga naga an gyara gdn banda kamshin turare ba abinda yake kallon sa nayi da niyar tambaya, kawai sainaga baba mero ta fito daga kitchen da gudu na tafi na rungume ta nace i miss you baba mero, sanan na durkusa na gaishe ta sanan nakai kayana daki na dawo kallona yayi yace nifa iam hungry ki taimaka ki dafamin light food zanje gd nayi wanka na dawo nace to, nima wankan nayi nasa wata English gown yellow sanan na shiga kitchen nayi masa potatos ball da lemon kankana da madara, na kara saka turaren wuta a gdn. Sanan na dauko wayata na kira aunty Salma mun Dade muna hira da ita sanan mukayi sallama.

Sai wajen 8 pm ya shigo gdn ni nayi serving dinsa yaci abincin banda santi ba abinda yake bayan ya gama muka fara hira, daidai nan Faisal ya kirani INA dauka yace yana waje, nan take gabana ya fadi sainaji bana son fita adon gari yana nan, Amma sai nace masa OK gani nan zuwa. Dagowa yayi yace INA zaki? Faisal ne yazo, dama kin fada mishi kin dawo ne? Eh ya kirani dazu, OK saiki tashi ki je ai, ya maida kallonsa kan phone dinsa, kasa tashi nayi saida ya kara cewa jiranki ake fa, sanan na tashi jiki ba kwari na fice, muna zaune da Faisal yazo ya shiga motarsa ya fice daga gdn, Faisal yace yau me yasami Mr kabeer? Nace me ka gani? Naga ko yayi min magna, kamar be taba sanina ba, murmushin yake nayi nace may b sauri yake

Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/3, 12:40] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣7⃣5βƒ£βž–1⃣8⃣0⃣

Yana barin gdna gdnshi ya wuce zuciyarsa banda bugawa ba abinda take yakamata nayi saurin daukar mataki akan soyayya ta da Aysha, idan ba haka ba I will loose her phone dinsa ya dauka ya fara dialing no kamal, duka biyu ya dauka hlo adon gari garin? Lpy kalau ango, tunda amarya ta tare najiga shiru, fushi nake dakai Sbd bakazo kaga dakin amarya ba, kayi hakuri zanzo insha Allah, to Allah ya kawo ka amin, ya lbrn Mutanen gdn? Suna nan kalau, ya neehal ita yaushe ne bikin nata? Ankusa da yanzu tare aka hada ma, mijin da zata aura ne yayi tfy, Amma yanzu ya dawo, Allah sarki shima Dan Kaduna ne mijin? Eh Dr haidar ba, Dan abokin dad dinmu ne alhaji Bashir bakori, shima likita ne yanada asibiti me suna bakori obstetrics $maternity private Hosp, acan neehal take aiki, eyya Allah ya taimaka, Bari na barka haka saida safe to Allah ya kaimu nagode sosai.

Dr marwan friend dinsa ya kira, suna gaisawa yace marwan Kasan Dr haidar Bashir bakori a Kaduna? Sosai ma, he is my friend, don Allah tromin no sa don Allah, me zakayi da ita? Don Allah tromin koma meye zakaji daga baya, OK to zan tromaka yanzu

No tana shigowa ya fara dialing, ana dauka suka gaisa, sanan ya fara masa bayani kamar haka" sunana kabeer M BAGAUDA, mu family friends din gdnsu neehal ne, mahaifiyata tana kokarin hada aurena da neehal, ba tare da saninta ba, kuma nasan kai take so Sbd haka na kira na fada maka kayi saurin yin wani Abu akai, domin kuwa akwai kyakyawar fahimta a tsakanin parents dina da nata, idan har mum dina tayi magana to ba abinda zai hana a auramin ita, Sbd haka Sbd haka kayi kokarin yin wani Abu daga yanzu zuwa next WK, banaso na zama sanadin raba masoya masu tsananin son junansu irinku. Wata sansanyar ajiyar zuciya yayi sanan yace nagode Mr kabeer tabbas neehal ce rayuwata, kuma rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne, insha Allah tun daga yau zan fara daukar mataki, nagode Allah ya saka da alkairi

3days later
Suna zaune da mum dinsa suna hira aka kirata a waya, tana dubawa taga Haj Asiya da sauri ta dauka bayan sun gaisa Haj Asiya tace dama kira nayi na fada miki gobe zaa kawo lefen yarki, kiyi hakuri don Allah na fada miki late, Wallahi abin ne ya taso urgent, muma be fada mana ba sai jiya. Jiki a mace mum tace oh ikon Allah dama kun mata miji ne? Eh anyi mata HAJIYA, ai Dan abokin abbansu ne ma, to Allah ya tabbatar da alkairi tace amin, amma sai kinzo ba HAJIYA tunda abin yazo a kurarren lkci, bikin nan da wata daya zaa saka, so in Allah ya kaimu bikin kyazo, to shikenan Allah ya kaimu.

Kallon shi tayi rai a bace kaji wai lefan neehal zaakai gobe, a zaune yake Amma saida ya mike, neehal din da kike so na aura? Eh wallahi, kai Amma wanan Abu be yimin dadi ba mum, naso na cika miki burinki, naso na auri neehal Sbd na faranta miki mum, Amma Allah yasa haka shi yafi alkairi tace amin son, kaima Allah yayi maka sauyi da mafi alkairi yace amin, bari naje gd amma zandawo da daddare insha Allah, to shikenan saika dawo.

Yana fita ya kira aunty Salma a waya ya fada mata duk abinda ya faru, tayi murna sosai sanan tace zan shigo kano gobe insha Allah, Sbd haka kafin nazo kayi kokari ka sanar da mom maganar Aysha, to shikenan sis nagode.

7:30pm
Ya shiga gdn mum cikin sa sanye da farar jallabiya saida ya durkusa ya gaisheta sanan ya

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment