Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta alfarma sanan ya wuce villa. Bai fito daga villa ba sai wajen 11pm direct gdnsa kawai ya wuce yayi wanka ya kwanta, saidai me? Tunanin aysha ya hanashi bacci kwana dayan da yayi beji daddadar muryarta, haddadan abincin ta da kuma kyakyawar fuskarta da be gani ba da kyar ya samu yayi bacci zuciyarsa fall tunanin ta

Washe gari

Tun wajen 9am ya nufi gdn Aunty Salma, lkcn daya shiga gdn shiru duk yaranta sun tafi makaranta sai yan aikin gdn da suke ta kaiwa da komowa. Wata daga cikin su yayi wa magana tace tun safe bata fito ba, yace me gidan fa tace ya fita, bed room dinta ya nufa direct ya tsaya a bakin kofar yayi knocking tana kwance tace waye? Yace ki bude mana, tana jin voice dinsa ta mike da sauri ta fito Sbd suna tsananin son junan su, what a surprise broda baka fadamin zaka zo ba a tare suka dawo falo nifa yunwa nake ji, kuma naga kamar yau ko break fast dinma bakiyi ba wallahi banida lpy ne, shima me gdn be karya ba ya fita, to ni ya zakiyi dani kenan? Bari nasa marwa ta soya maka Irish, yarinyar tana da tsafta sosai, to don Allah tayi sauri. Meyasa baka fadamin zaka zo ba? Wallahi nima un expected abin yazo min baki tayani murna ba nayi winning contract din nan ta gina estate a maitama, gidajen ministers ne, shine President ya nemi ni mu tattauna yanda abin zai kasance, to Allah ya taimaka yace amin. To ni yanzu wa zaka samomin ta tayani girki kafin na samu sauki, Kasan na shagwaba megida na baya Iya cin abincin restaurant. Inada wacce zansa tazo, idan tayi miki girki mijin naki ma bazai gane bake kikayi ba Sbd itama expert ce, zanyi waya Sulaiman ya sakota a jirgi gb, Amma fa Iya sati daya kawai zan ara miki ita, idan zan tafi tare zamu wuce. Ba matsala ai hakan maka taimaka min Allah ya kaimu goben yace amin

Maman Aysha
[9/26, 22:20] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣3⃣5βƒ£βž–1⃣4⃣0⃣

To Amma yar gidan waye yarinyar da zaka kawomin? Iam her father, mother, broda every thing. Ban gane ba? Nan take ya kwashe lbrna from AtoZ ya fadamata, kai Amma na tausayawa mata, har naji ina sonta tun kafin na Santa. Tunda hakane ka fadamata ta taho yau mana, idan naki fa? Pliss my broda taimaka min, kaga abbansu nana ya samu yayi break gobe kafin ya fita, aike kullum damuwarki kenan abbansu Nana, shikenan bari na kirata

Muna zaune a falo nida baba mero muna break fast, Sbd muma yau bamu tashi da wuri ba, kiransa ya shigo wayata, da sauri na dauka Sbd nayi missing unique voice dinsa yau 2 days bamuyi waya ba, bayan mun gaisa yace na bawa baba mero, suna gaisawa ha hadata aunty Salma suka gaisa dake sun saba sosai don tasha yi mata zaman biki ma idan ta haihu. Saida suka gaisa sosai har suka taba hira sanan yace ta bani wayar, INA karba yace don Allah alfarma nakeso kimin aysha, sister Salma ce bata da lpy shine nakeso kizo ki Dan taimaka mata da girki for 1 wk, idan zan taho saimu taho tare kinji, nace to yaushe kenan zan taho? Yau, nasa Sulaiman yayi miki booking din jirgi, idan kin shirya zaizo ya kaiki airport, ki fadawa baba mero ta tafi gd idan kin dawo saimu dakkota Sulaiman zai baki kudi ki bata nace to, Allah ya kawo ki lpy nace amin.

Jirgin 7pm na shga, Sbd haka 8:15 a Abj tayimin, INA sauka na tarar da driver aunty Salma yazo dauka ta muka tafi. Black Arabian gown ce ajikina, na yane kaina da mayafin rigar. Fadar kyau da haduwar gdn aunty Salma bata lkc ne me karatu kayi imagining kawai. Jiki ba kwari nayi sallama na shiga gdn, akan dining na same su suna cin abinci muna hada ido da aunty Salma kawai saita kware ta fara tari saida ya dauko mata ruwa sanan ya tsirga, wani irin kallo ta Bini dashi da har INA gaisheta amma batasan INA yi ba har saida adon gari yace sis gaisheki fa take, sanan ta dawo hayyacinta ah lpy kalau ya hanya nace alhamdulilla, marwa zo ki rakata daki, INA barin wajen ta kalli adon gari tace da ace ba uwa daya uba daya nake dakai ba da sai nace kawo yarinyar nan gdn nan set up ne,taya zaayi ka kawomin wanan kyakyawar yarinyar kamar ba mutun ba? Wata yar iskar dariya yayi sanan yace wallahi ki rage kishi, Dan nasan duk akan mijinki kike wanan abin, to tanada mijin da zata aura, kuma ita kudi ko kyau baya gabanta ballatana tayi tunanin aurar mijinki, kuma in banda abinki sister ai kema kyakkyawa ce. Ki kwantar da hankalin ki da Allah ki zauna da ita a bisa amana insha Allah ba abinda zai faru kinji my sis, tace to shikenan.

wacece aka kira da marwa ita ta rakani wani daki INA ajiye kayana na fada toilet nayi wanka, sanan nayi sallah, har dakin aka kawo min abinci, Amma saina kasa cin komai tunanin yanda zanyi zaman gdn...sallamarsa ce ta katseni, kamshin sa ya bugi hanci na kan gadon yazo ya zauna yace min ya hanya? Banyi magana ba sai dagowa nayi muka hada ido sanan muka sakarwa juna wani lallausan murmushi a hankali ya furta I miss you my lovely sis, can kasa nace I miss you too, yace da gaske? Faisal bezo ya tayaki hira bane? Basarwa nayi kamar banji abinda yace ba, abincin da aka kawomin ya kalla yace me yasa baki ci ba? Nace na koshi, ohh sorry ashefa bakya Iya cin abinci da daddare ko? Bari na dauko miki ice cream, yana kawomin yayi min sallama ya tafi

Maman Aysha
[9/27, 10:45] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣4⃣0βƒ£βž–1⃣4⃣5⃣

Yana fita da few minutes aunty Salma ta shigo tace aysha bakiyi bacci ba nace eh, don Allah fa kiyi hakuri idan mun takura miki, wallahi mijina ne ba kowanne abinci yake Iya ciba, ni kuma kwana nan ba kowanne abinci nake son jin kamshinsa ba, karki damu aunty Salma ba wani Abu wallahi, to ngd sosai, naji lbrnki a wajen broda I pity you Allah ya bayyana miki iyayanki nace amin. Tun kafin kizo da naji lbrnki naji INA sonki, so don Allah ki saki jikinki ki dauke a matsayin elder sis dinki kinji? Murmushi nayi nace to nagode, to me zaki dafa mana da safe? Duk abinda kk ce, OK akwai komai da zaki bukata a kitchen din, na baki choice kiyi mana duk abinda ya samu, murmushi nayi da har saida kumatuna ya lotsa nace to. Bari na barki ki kwanta saida safe nace Allah ya kaimu. Tabbas aunty Salma tafi adon gari kirki da saukin kai, kyakyawar mata ce Sbd suna tsanin kama da Broz sosai, yau daya na fara ganinta amma sainaji ta shiga raina. Addua nayi na kwanta Sbd tashib wuri zanyi

Ina idar da sallar asuba na shiga kitchen, paper soup din kaji na farayi, sanan na soya doya da kwai da plaintain na dama kunun gyada na kwaba fulawa nayi shawrma, sanan na tafasa ruwa a kettle na zuba a flaks ko wani zaisha tea zuwa 7am na kammala komai, INA fitowa daga kitchen naga yaranta nabil da khairat sun fito cikin shirin su na makrant, marwa ce take kula dasu. Da gudu suka zo suka rungumeni nabil yace ya sunanki? Nace aunty Aysha yace zaki zauna a gdnmu? Nace eh, yace INA sonki aunty Aysha, dariya nayi nace nima INA sonku nabil da khaitat murna suka hau yi, sanan na kama hannun su mukaje na zuba musu abinci sukaci, sanan na wanke musu hannu mu kaje na zuba musu shawarma a lunch box dinsu banda surutu ba abinda sukemin, gabadaya sai tunanin su basma da junior ya dawomin sabo bansan lkcn da hawaye ya cikamin ido ba, daidai nan mum dinsu ta fito da gudu sukaje sukayi hugging nata gud morning mum tace morning my kids, kunci abincin? Eh Aunty Aysha ta bamu, kuma yau da Aunty Aysha tayi mana shawarma da ita zamu tafi sch. Dariya tayi tace dats very gud, Aysha dama kin Iya shawarma nima dariya nayi nace eh, dakyau ko catering kk karanta ne? Aa, OK to kuje Ku tafi karku makara kharat ce tace ni awajen aunty Aysha zan zauna, nace yi hakuri kije khairat idan kin dawo zan kaiki wonder land ki hau mota, nabil yace nima zaki kaini? Nace eh da gudu suka fita suna murna INA dagowa muka hada ido da Maman su ta sakar min murmushin jin dadi tace sannu da kokari aysha. Daki na koma na gyara, itama na shiga na gyara mata room dinta da toilet ita kuma ta gyara part din megidanta sanan nayi wanka nasa wata fitted gown ta wani material green, dinkin yayi min kyau sosai, simple make up nayi na murza dauri me kyau, sanan nasa sarka da Dan kunne nayi wanka da turare na dauko laptop dina na fara kallon wani film da nayi down loading wa men hubbi maqatal. Sai wajen 8 me gidan ya fito ya zauna a dinning ya kwashi abinci, da zai fita aunty Salma tazo tace naje mu gaisa dama ta bashi lbrina tun dare, har kasa na durkusa na gaisheshi shi ya amsa da fara'arsa kuma yayimin godiya. Yana fita tace nazo muyi break, kunun gyada da plantain kawai na Iya ce, aunty Salma tace Aysha akwai abinda yake damunki, ko vakyason zama damu ne? Sbd dazu dana fito naga hawaye a idonki, nace wallahi ina son zama daku akwai kannena wanda ada nayi zaton uwarmu daya ubanmu daya, junior da basma kusan age mate din su nabil ne mu shaku sosai da yaran ni nake musu komai, duk lkcn dana tunasu sainayi kuka nakejin dadi. Eyya allah sarki kici gaba da hakuri insha Allah wata rana sai lbri, nace hakane kam. To me yasa kuma bakya son cin abinci? Nace ba kin ci nake ba, is my nature, dariya tayi tace aiko gashi nan bakya kiba,nima dariyar nayi daidai nan handsome ya shigo, yau kuma danyen boyel ne ajikinsa cream color gashin nan ya kwanta yayi luf muna hada idon na nemi nutsuwa ta na rasa sabd balain kyaun da yayi, karasowa yayi yace gud morning sis tace morning broz, nace masa INA kwana saida ya Dan lumshe ido ya bude sanan yayi murmushin da yake tafiya da imanin yan mata yace lpy kalau ya kwanan bakunta? Nima murmushin na mayar masa har saida kumatuna ya lotsa nace lpy kalau, duk abinda muke aunty Salma na kula damu, Amma saita yi kamar bamu take kallo ba. Ni nayi serving dinsa ya fara cin abincin saidai duk dagowar da mukayi sai mun hada ido, wani irin kallo yake min Wanda yasa wani mugun sonsa yake yawo acikin jinin jikina, har naji bazan Iya jurewa ba, mikewa nayi na koma daki na kwanta na fara tunani saura 2 month ayi bikinsa wasu zafafan hawaye suka fara zuba a idona, ina sonka kabeer, don Allah ka furta kace kana sona, at least ko baka aureni ba zanji sanyi a raina kuka nake sosai banji shigowarsa ba sai kamshin turaren sa daya daki hancina ya salm Aysha meya faru kuma? Don Allah ki fadamin Aysha, ko zaman gdn nan ne bakya so? Nace aa to fadamin don Allah meye matsalar ya karasa maganar cikin tsananin damuwa. A zuciyata nace ciwon sonka ne matsalata, Amma a fili sai nace ba komai iyayena na tuna bansani ba ko sunada rai ko sun mutu, daugoni yayi ya rungumeni a ajikinsa kiyi hakuri beauty kinji, asan is painful Amma addua zakici gaba dayi indai suna raye Allah yayi gaggawar bayyana su nace amin, hankii ya dauko a aljihunsa ya gogemin hawaye sanan ya kuramin ido da sexy eyes dinsa yayi magana da wata irin voice din da ban taba sanin yanada ita ba yace kayimin alkawari bazaki kara kuka ba, dakyar na Iya cewa na daina, sanan yace zanje mu karasa meeting da muke da Mr President ina ganin sai dare zan dawo idan da wani matsalar kiyimin text kinji? Nace to, kuma don Allah ki ware kuci gaba da hirarku da aunty Salma, kada kai kawai nayi. Harya fara tyfy ya jiyo yace ko Dan smiling bazaki yimin ba? Wani lallausan murmushi nayi masa da har saida kumatuna ya lotsa, sanan yace thank you my sis ya fice ya barni da kewarsa da kuma kamshin turarensa

Maman Aysha
[9/27, 14:55] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣4⃣5βƒ£βž–1⃣5⃣0⃣

Shakuwa ce me tsanani ta shiga tsakanina da aunty Salma, wadda har jinta nake kamar blood sister na, na sake da ita sosai har tsokanar juna muke, shima mijinta dake Dan harka ne harshi ake zama ayita hira.

Yauma kamar kullum bayan mun kammala dinner muna zaune anata hira har megdn khairat tayi bacci akan cinyata, nabl kuma INA koya masa h/work saiga adon gari ya shigo, bayan an gaisa yace kwantar da yarinyar nan ki zobomin abinci yunwa nakeji nace to, daki na kaita Sbd tunda nazo gdn tare muke kwana da ita, cusccus akayi wit vegetable soup Dana zuba yace kawomin nan, cin abinci akan carpet yafi dadi nace to yanaci anata hira, nabil yazo ya dameshi sai tsalle yake ajikinsa duk ya hanashi cin abincin ma, yace kai tashi kaje ka kwanta kona Zane ka, banda kiriniya ba abinda ka iya. Dariya aunty Salma tayi tace ai kai ya gado, Sbd ka bani wahala kana yaro, nan ta shiga bamu lbri tace bana mantawa lkcn da muka zauna a London a makotanmu akwai wani yaro, sunanshi selvesta duk ya girmemu, gashi Dan lukuti idan ya kama mutun baya yi masa da wasa Sbd karfinshi super master ake ce masa ga brodana da tsokana kuma idan yayi tsokanar aka dakeshi sai mum tace dole saina fita na rama masa, duk lkcn daka tsokano shi gbn har faduwa yake,Dariya mukasa gabadaya, mijinta yace kai Ashe matsoraciya ce ke, tace wallahi Dan bakaga yaron bane. Adon gari ne yace au ni na manta ma Ashe wayoyina a kashe suke bari na kunna, aikuwa kamar jira suke yana kunnawa calls ya fara shigowa, kuma duk rabi yan matane wasu ya amsa, wasu yayi rejecting kuma don jaraba yana gama amsa wani kiran, wani yake shigowa. Mijin Aunty Salma ne yayi dariya yace ka zama business cenre duk suka kwashe da dariya banda ni da kishi ya cikamin zuciya, wani kiran ne ya kara shigowa da hanzari na dago na kalle shi sainaga yayi wani smiling ya furta zuby can Kasan makogaransa cikin wata sansanyar unique voice dinsa yake mata magana kanajin hirar tasu ta soyayya ce nan take naji kirjina ya cushe, kaina ya fara sarawa tsananin sonsa ya fara yawo acikin jinina, kawai sainaji bazan iya cigaba da zama a wajen ba mikewa nayi nace musu saida safe aunty Salma da tun lkcn da yanayina ya canja tana kula dani tace tun yanzu zaki kwanta? nace eh bacci nake ji to shikenan Allah ya tashemu lpy nace amin

Gani yayi hirar tata bazata kare ba, yace kinga zuby I will call you back later, Ina wani important Abu ne, be jira abinda zatace ba kawai yayi switching off. Dariya babansu khairat yayi yace wato hirar da kuke is not an important issue ko? Anya karbuwar data samu guarantee ce kuwa? Murmushi kawai yayi, aunty Salma tace ai wanan brodan nawa sai a hankali, Amma inaji ajikina akwai yarinyar da zata karya alkadarinka kwanan, kuma you can't denied it. Wata shegiyar dariya yayi yace haba sis kin manta halina, ADON GARI ne fa, aini bana bari son wata ya shiga zuciyata ballatana har ya dameni, nidai zasu soni kuma har zuciyarsu ta nemi bugawa akaina, Amma ni ba wata wadda yarinya data isa na shiga wani hali akanta. Haka kace ko broz? Eh, to shikenan we shall see, mikewa yayi nizan tafi saida safe. Suka amsa da To Allah ya kaimu yace amin

Ni kuwa tunda na shiga daki nake kuka, wani irin son shine yake addabata wanan wane irin rayuwane? Na kamu da son mutumin da besan inayi ba tabbas ko shakka banyi, ciwon son adon gari shi zai zama ajalina, ita kam zuby Allah ya taimaketa tazo duniya a SAA, Sbd ko be aureta ba, zata iya bada tarihin yayi soyayya da ita, ya Allah ka ciremin son mutumin nan a zuciyata don na fuskanci mayaudari ne, yayi amfani da bewar da Allah yayi mishi ya koyamin sonshi, kuma yayi ignoring dina koda wasa yaki ya nuna yana sona, why me kabeer? Me yasa baka tausayi na, me yasa baka barni da bakin cikin rashin iyayena ba, kake kokarin kara jefa rayuwata acikin matsala, wata zuciyar ce tacemin karki zargi kabeer Aysha ki zargi kanki, Sbd shi besan ma kina sonshi ba, kinyi mistake da kika bari sonshi ya shigeki sabda ba yanda zaayi mutun me kudi, kyakkyawa Dan asali me tulin yan mata buhu buhu ya amince ya aureki, dole yar asali zai aura. Saida nayi kuka me isata, daga baya kuma wani wahalallen bacci ya daukeni.

Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [9/28, 11:59] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣5⃣0βƒ£βž–1⃣5⃣5⃣

Gobe ne ranar da kabeer yace zamu koma kano muna zaune muna hira da aunty Salma wajen 5pm, kawai saiga kabir ya shigo, da gudu yara sukayi hugging dinsa dake yana nuna musu so sosai, waje ya samu ya zauna yace kuje a shiryaku mu tafi yawo aunty Salma tace bazakaci abincin ba? Eh yau bana sha'awa, zan sami abinda zanci a rose flower sweet and bakery, nayi karaf nace ka bude a garin nan ne? Aunty Salma tace ai baki Sani ba? Aikuwa ya kamata kije, sabda idan kika shiga na garin nan saiki raina na kano, iya kudin shiga kawai 5000 ne, Ki shirya kuje mana, idan kin dawo zaki bani lbr nace to bari na canja dressing.

Wani hadadden filtex lace nasaka, zanen lemon green da orange color ne ajiki, amma orange din bashi da yawa, rose silk na daura orange nasa sarka da Dan kunne na stones suma orange color, 20k na sayesu, mayafi da shoe&bag ma orange zama nayi nai make up sosai a fuskata sanan na fita, takalmin danasa me tsini ne kos kos din takuna ne ya janyo hankalin su zuwa wajena nan take adon gari yayi mutuwar tsaye, bina yayi da wani irin mayattacen kallo da har naji kafata tana hardewa, da kyar na karasa wajen cikin sanyin murya nace na gama yace OK muje, sis sai mun dawo tace to. Shima saida ya biya kudi muka shiga, haka dokar wajen take, gaskiya kabeer ba karamin me kudi bane, domin kuwa rose flower sweet and bakery dinsa na abuja kadai ya isa ya rikeshi, wato fadar girman wajen ma bata lkc ne, ba abinda babu a wajen, akwai swimming pool, wajen wasan yara ya zuba haddadun motoci irin na wonder land, sai wajen lilo na yara daban, na manya ma daban, akwai wajen game din table tennis, basketball, suluka, volleyball dadai sauran su, akwai lafiyayyen garden da aka kawatashi da hadaddadun shuke shuke irin Wanda ko ranka ne a bace idan kaje wajen saika nemeshi ka rasa, sanan akwai restaurant duk wani kalar abinci ko snacks da abinsha akwai shi awajen, in fact idan kana cikin wajen saika manta a 9ja kake.

Tunda muka shiga wajen muke cin karo da hadaddun yan mata da samari, kai har matan aure baa barsu ba duk Wanda ya kallemu saiyaji mun burgeshi Sbd kyau da kuma dacewar da mukayi, direct wajen wasan yara muka je aka sasu mota suna ta murna mota tana zagayawa dasu, wasu kujeru muka samu muka zauna, kawai saiga wasu yan mata guda biyu sunsha kyau sukayi mana sallama, sanan daya daga cikinsu ta dubi adon gari tace don Allah ka temakeni ka bani koda 1 minut ne na ganka, basarwa yayi kamar beji me tace ba, Mr kabeer don Allah ka taimaka min, cikin fushi yace wai bakiga tare nake da wife dina bane, ban yarda ba, ba matarka bace ai daurin auren babban mutun Wanda yayi suna har a kasar waje irinka bazai boyu ba, da yanzu duniya ta Sani Kai musulmi ne kuma da Allah na hadaka, don Allah ka taimaka ka saurareni. Mikewa yayi suka koma gefe sanan ta fara masa bayani ni sunana juwaira Yusuf, dad dina ne minister of education, ranar da akayi bikin bude wajen nan na fara ganinka, kuma tun ranar na kamu da sonka saidai na rasa yanda zan hadu dakai sai yau. Kneel down tayi don Allah Mr kabeer ka taimaka ka aureni koda ata biyu ne Sbd wallahi INA tsananin sonka, naji Amma ki tashi, Sbd gbdaya idon mutane akanki yake ban damu ba kallona da mutane suke ba shine matsalata ba, ka amince da soyayya ta shine matsala ta, to naji tashi muyi magana, mikewa tayi ta zuba masa ido, kiyi hakuri don Allah idan nace zan aureki nayi miki karya, ban taba sha'awar mata biyu ba kuma insha Allah har abda bazanyi ba, kuma na Riga nayi dating matar da zan aura so INA yimiki fatan alkairi Allah ya baki Wanda ya fini, Tahowa yayi ya barta a wajen tana kuka yana zuwa yacemin taso mu tafi garden nace yaran fa? Daya daga cikin staff dinsa na wajen ya kira yace ya kula dasu khairat idan sun gaji ya rakosu guarding yace to

Wajen sabd shakatwarsa kadai ya tanade shi, sai yazo ake budewa ya gyara wajen sosai muna zuwa ya kwanta akan grass carpet ya lumshe ido, ya Dade a haka sanan ya ya bude a hankali ya kira sunana cikin damuwa yace Aysha me yasa yan mata suke bina? me yasa suke cewa suna sona? Akwai kyawawan samari masu kudi, masu class, wasu dunfini kudi ma Amma me yasa yan mata basa binsu Sani? Why me? Banaso nayi hurting din mutun, amma yan matan da suke sona sunsa dole inayi, what am I going to do? Aysha fadamin meye solution? Me zanyi su dena bina ba tare da na wulakantasu ba? Wallahi dani mace ne, da nikaf zan ringa sawa, cikin wata cool voice yayi magana Aysha fadamin me yakamata nayi? Nace kayi aure, idan sukaga kayi aure zasu Dan rege binka. To wa zan aura? Zuciyata har yanzu batasan zuby, na kasa son zuby Aysha, akwai mutumin daya da zuciyata takeso, saidai abune me wahala aurena da ita ya yuyu. Me yasa? Is a secret, tashi yayi ya zauna ya rike hannuna sanan ya kafeni da wani irin kallon daya saukar min da kasala yace ki tayani da addua Allah ya warware min matsala ta acikin ruwan sanyi, will you? Kai na daga masa Sbd gabadaya jikina ya mutu. Wani lallausan smiling yayi yace mrs Faisal, kuna waya kuwa? Nace eh ai na fada masa ma gobe zamu tafi, kai sorry wallahi na manta na fada miki an fasa tafyar gobe, Sbd me? Kinsan dad dinsu khairat yayi tfy ko? Eh, shine tace na taimaka na bar mata ke zuwa next WK saiki tafi, kai gobe zaka tafi kenan? Nan take naji gabana ya fadi, duk da nasaba da aunty Salma, Sbd shi nake jin dadin zaman garin, Ciwon sonsa zai wahalar dani kenan,,,,,,,,Tunanin Faisal kike ko? Kiyi hakuri ai kuna waya, sati dayan kamar yaune a wajen Allah, muje mu tafi naga magarba ta kawo kai

Maman Aysha
[9/29, 17:37] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣5⃣5βƒ£βž–1⃣6⃣0⃣

Ana kiran sallar magrib muka shiga gd KB yayi alwala ya tafi masallaci nima daki na shiga nayi alwala bayan mun idar da sallah muka fito falo aka debo take away din da mukayi a rose flower sweet and bakery muka baje gabadayanmu mukaci, sanan aka fara hira, sai wajen 10pm Mr kabeer ya mike yayi mana sallama har yakai bakin kofa ya juyo yace lovely sis ba rakiya? Murmushi nayi nace muje na rakaka har bakin mota na rakashi saida yace bude motar ya shiga sanan yace ina fata sati dayan da aunty Salma ta kara miki be bata miki rai ba? Wata yar sansanyar dariya nayi ace ba damuwa 1 WK din kamar yau

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment