Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aljanu tace dawowa ta kenan naji kai nake son fara gani, kuma nazo wanan so called sakatariyar taka ta hanani shiga. Yi hakuri mu karasa daga ciki yacewa guards dinta su koma office na biyu su jirata, sanan yace min ke kuma ki kawo mata drinks nace to. Lkcn dana shiga yana zaune kusa da ita suna hira cikin nishadi yanata sakar mata murmushin sa me tsada nan take naji zuciyata tayi zafi, naji gabadaya ba hargitse da kyar na Iya saita kaina naje na ajiye mata tray din a gabanta harna juya zan tafi tace me kk nufi, dawo ki zubamin, da facin rai nace ke baki da hannu ne? Kb ne ya kalleni yace obey her instruction she is my wife to be rasss naji gbna ya fadi, na nemi yawon bakina na rasa da kyar na samu energy n zuba mata, nace gashi hannun ta kawai ta miko ba tare da ta kalli cup din ba Sbd hankalin ta akan waya yake, nayi zaton ta rike na saki cup din aikuwa lemon ya zube ajikin mayafinta. A hanzarce ta mike ta kaimin mari, nayi saurin rike hannun ta me nayi miki da zaki mareni? Inaso ki Sani kowanne mutun yanada daraja, kasancewa ta ina aiki a karkashin mijinki bazai baki damar ki wulakantani ba. Aikuwa wallahi baki isaba saukin wanke min zanyi magana yace karbi ki wanke mata, ba musu na karba na wanke a sink din toilet dinsa saida na kade sanan na bazashi akan table din shi raina a bace na nufi kofa zan fita kawai sainaji tace banza marar asali.......Bata karasa ba ya wanke ta da mari cikin kuka tace akan wanan bastard din ka mareni? Inajin haka na fita da gudu ina kuka, Don't ever call her bastard and walk out from my office ta tsaya tana binsa da kallon mamaki cikin bacin rai yace I say out!! Tana rawar jiki ta dauki mayafinta ta fice tana kuka

Maman Aysha
[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/23, 13:16] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣1⃣0βƒ£βž–1⃣1⃣5⃣
Tana fita ya zauna ya dafe Kansa Sbd be saba hayaniya ba, ya dade ahaka daga baya kuma ya dauki laptop dinsa da key ya fice ya tafi gd.

Zuby kuwa tana fita gdn wata friend dinta rumana ta nufa tana zuwa ta zube a falo tana kuka da sauri tace zuby me yake faruwa kk wanan kukan? Nida adon gari ne rumana, inayin hakuri da miskilancinsa da duk wani wulakanci da yake min Sbd INA masifar sonsa Amma yau har marina yayi Sbd wanan yar iskar yarinyar da aka gano Bata da asali, wacece yarinya kenan? Aysha A TURAKI, meye hadinshi da ita? Wai yanzu itace sakatariyarsa, kuma wallahi na tsani yarinyar kinsan tana da wani irin shu'umin kyau zata Iya kwacemin shi, kuma kinsan irin wahalar Dana sha kafin ya amince zai aureni, gaskiya kam Amma tunda hakane da makirci zaki koreta bada isa ba, yanzu ki kirashi ki bashi hakuri kinsan ance me nema baya fushi kiyita lallabashi har ki samu ya hakura, a hankali sai musan yanda zamu fillowa al amarin. Shiyasa nake sonki my friend har naji zuciyata tayi sanyi bari naje na tafi kinsan da body guards naje company nasa Amma Sbd bacin rai basu San na fito bama , bari nace musu su tafi kawai ni na wuce sai munyi waya to shikenan.

Zaune yake yana ta tunani, Allah sarki aysha rayuwarta akwai abin tausayi a ciki, ace mutun bashi da kowa ita kuma irin destiny dinta kenan, insha Allah zan rike amanarki har zuwa lkcn da zakiyi aure daidai nan phone dinsa ta fara kuka yana dubawa yaga zuby is calling... Kawai sai ya mayar ya ajiye, haka tayi ta kira har wajen 10 missed call, ko tunanin me yayi kuma? Data kara Kira sai ya dauka, ta naji yayi picking saita fara kuka don Allah sweet heart kayi hakuri, bazan Iya rayuwa bakai ba don Allah ka tausayawa rayuwata ka yafe min. Naji zanyi hakuri Amma sai kin gyara halinki, kuma kin bawa Aysha hakuri Sbd kinyi mata cin fuska, to to na amince insha Allah zanzo na bata hakuri gb, is alright Allah ya kaimu goben, bye.

Ni kuwa tunda na koma gd INA daki saida nayi kuka me isata kallama dayace take min yawo a zuciyata "she is my wife to be" dama adon gari yana soyayya? Dama yayi dating matar dazai aura? Amma na tafka babban kuskure dana bari zuciyata ta kamu da sonshi, ya Allah ka cire min sonshi a zuciyata da wanan tunanin wani wahallalan bacci ya dauke ni ban farka ba sai after 4, INA tashi na shiga toilet nayi wanka nayi alwala nayi sallar laasar wata English gown na saka na fita wajen baba mero tace yanzu nake tunanin naje na duba naga ko lpy, Sbd tunda kk shigo banji motsinki ba dariya nayi nace bacci ne ya kwashe ni shiyasa, me kika dafa mana? Abinda kk so nayi miki, kina nufin danwake? Eh kai Amma nagode shiyasa nake kara sonki baba mero, itama dariya take kitchen na shiga na zubo Iya yanda zan Iya ci, sanan na dawo falo inaci muna hira muna dariya, wayata ce ta fara kuka INA dubawa naga Barr Faisal ne, da sallama ta na dauka bayan mun gaisa yace kira nayi naji amsata, Aysha kinyi tunanin? Eh nayi kuma na amince da soyayyarka, alhamdulilla yace, saida, saidai me Aysha? Akwai maganar da nake so na fada maka, amma nafiso muyi faceβž–face, is OK zanzo in d night, yau kaina yana ciwo ka bari sai gobe, ayya iam sorry my dear Amma kinsha magani? Eh to Allah ya sauwake, bari na barki ki huta sai na kara kira bye. Ina kashe wayar baba mero tace waye wanan din? Sabon saurayi nayi sunansa Faisal, kuma kina sonsa? Sosai ma, ni kuwa sainaga duk duniya ba mutumin da kika dace dashi kamar kabiru, wallahi duk lkcn da nayi sallah sainayi addua akan Allah yasa kabiru ne mijinki Sbd halinku na tausayi da rashin kyamar mutun iri daya ne, Aysha kina da kyakkyawan halin da har yasa nake jinki kamar yata, kullum burina shine na ganki acikin farin ciki, don Allah ki amince ki auri kabiru kinji Aisha. Baba mero kenan, ke kike kidanki kike rawarki, shifa har yanzu be taba cewa yana sona ba, kuma fa yanada wacece yake so har ansa masa rana ma, maganar so kam na Dade da ganewa yana sonki, saidai da kikace ansaka masa rana shine matsalar, Allah yasa haka shi yafi alkairi nace amin

Washe gari
As usual INA office saiga Suleiman PA ya shigo, bayan yaje sun gama da adon gari ya fito sai ya zauna a wajena muna hira saiga ta ta shigo ta dau wanka tayi kyau sosai, INA ganin ta naji gabana ya fadi Suleiman ne yace miss zubaida barka da zuwa, yauwa Suleiman ya aiki alhamdulilla da gadara ta bude office din ta shiga wai wanan zuby din a ina take ne Sulaiman? Yar gdn minister of foreign affairs ce, kuma ita yallabai zai aura in Allah ya yarda, to nazle da tazo jiya fa? Ita kuma yar gdn commissioner of police ce, lbri yake ta bani, Amma gabadaya hankalina baya tare dashi, har saida ya fahinta, sai yayi min sallama ya tafi Mr kabeer ne ya kirani a waya yace nazo yana don ganina inda suka zauna jiya yauma anan suke, dama my Queen ce take so ta baki hakuri akan abinda ya faru jiya, eh hakane, kamar yadda swit heart ya fada miki zuwa nayi na baki hakuri Sbd wallahi nayi regretting sosai don Allah ki yafemin, nace ba komai Allah ya yafe mana baki daya zuciyata tana yimin wani irin zugi da radadi na kishi ban taba sanin son adon gari yayimin mummunar illa ba sai daga jiya zuwa yau, da kyar na Iya cewa zan Iya tafiya? Yace eh, ina juyawa wasu zafafan hawaye suka fara zuba a idona zama nayi na dora kaina akan table na fara kuka sallama naji anyi INA dagowa naga Faisal ne cikin rudani yace wat's wrong Aysha nayi sauri nace ba komai bacci nayi, lpy na ganka anan? Nazo naga Mr kabeer ne akwai wani aiki da zamuyi dashi, to bari na sanar masa, ina fada mishi yace ya shiga Ashe friend dinsa ne

Maman Aysha
[9/24, 12:12] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣1⃣5βƒ£βž–1⃣2⃣0⃣

Yana shiga ya sami waje ya zauna yace Ashe kaida amarya ne? Yace wallahi kuwa, yau ta kawomin visit bayan sun gaisa suka tattana akan abinda ya kawo shi, sanan suka fito a tare har zuby. Ina cikin hada kayana Sbd lkcn tashi dama yayi naga fitowarsu Faisal ne ya karaso inda nake tsaye yana wani lallausan murmushi yace baby tafiya zakiyi? Cikin faduwar gaba nace eh, to muje nayi dropping dinki, thanks yau nazo da mota zubamana ido adon gari yayi yanamin kallon tuhuma, shi kuwa Faisal idonsa ya rufe yama manta da mutane a wajen, haka kawai adon gari ya tsinci Kansa da shiga damuwa, a INA Barr Faisal ya Santa? Yaushe suka fara soyayya? To ko shine yayi dropping dinta rana nan? Zuby ce ta katse masa tunani da cewa mu tafi swit heart cikin shan mur yace OK muje, A tare muka fita dasu saida ya rakani har bakin mota ya bude min na shiga sanan yamin sallama da sharadin zai zaizo bayan sallar magrib.

Tsaye suke ajikin motar sa suna sallama da zuby, amma gabadaya hankalinsa a wajen mu yake zuby ce tace amma na fuskanci Barr Faisal yana tsananin son yarinyar nan, kallo daya zaikai masa Kasan yayi falling da yawa saidai INA tausaya masa duk ranar daya gane bata da asali....enough me yasa bakinki baya shiru? Me yasa kk da taurin kai? So nawa kk so na fada miki maganar nan ta fita daga bakin ki, Karki bari na nuna miki bacin raina Sbd zaki sha wahala be jira driver shi ya bude masa motar ba ya bude da Kansa, kafin kace me body guards dinsa ma suka shiga motocinsu yau da motoci shida ya fito, cikin few seconds sukayi arranging din moticin suka fice daga wajen, itama jiki ba kwari ta bude motarta ta fita da tunanin wulakanci irin na adon gari.

Direct gdn mum dinsa ya wuce yana zuwa ya zube akan ciyarta banda shagwaba ba abinda yake, wash Allah wallahi mum na gaji sannu my son, ai duk lefinka ne da kaki yin aure, da kanada mata da yanzu saita yi maka tausa, sauri yayi ya canja topic din zancen da me aka dafa mana yau mum? Jallop din taliya ce, ya tsani taliya Amma Sbd karya fada ta kara cigaba da zancen yayi aure sai kawai ya basar yace bari naje gd nayi wanka, dama zuwa nayi naga lafiyarki, kuma abincin fa? A koshe nake, to dama inaso na fada maka gobe zan tafi Kaduna, Kasan next WK bikin abokinka kamal Sbd haka zanje mu fara shirye2 idan na tafi gobe sai angama bikin zan dawo, gaskiya mum kinaji da Haj Asiyan nan Ku kunata zumuncnku, mu kuwa haduwa tayi wahala saidai kusan kullum sai munyi waya dashi, kuma time to time INA zuwa nagaida dad dinsu a office, kuma duk lkcn naje Kaduna sainaje gdn kanwarsa ce dai neehal rabon da na ganta tun bata fi 8yrs ba, tab ai yanzu ta zama budurwa, yanzu haka ma likita ce kwanan ta kammala karatun ta, ah dakyau, ni zan wuce idan yaso goben sai sadiq ya kaiki a helicopter dina to shikenan son sainaji ka OK bye mum. Gida ya shiga yayi wanka ya kwanta bacci

Ina shiga gd nayi sallah na shiga kitchen dama yau dambu nake sha'awa sbd azumi nake, ina azumin litinin da alhamis. Tun safe nasa baba mero ta tanadarmin komai kafin na dawo, cikin 1hour nagama danbun, sanan na hada lafiyyayen zobo da yaji kankana, nayi potatoes bols, da paper soup din ostel dake ina sonshi sosai, kara share gdn nayi na gyara kitchen din kamar ma banyi girki ba, na kunna turaren wuta a falon sbd ya kawar da kanshin abincin, sanan na shiga wanka nasa wata orang English gown anyi shaping dinta, tayi min kyau sosai, gashina kuma anyi min twisting dake yanada tsaho ta kwanta min a gadon bayana nayi wanka da turare sanan na fito na karasa hada fruit salad
nasa a fridge

7:15pm
Nasha ruwa na gaji, kuma gashi Faisal yace zaizo kawai saina dauki phone dina nace don Allah yayi hakuri da zuwan Sbd kaina nasha ruwa na gaji gashi kaina yana min ciwo. Duk da ba haka yaso ba Amma Sbd gudun bacin raina saiyace ba matsala.

A kwance nake akan 3seater INA kallon series film din da ake Bollywood me suna Geet, baba mero kuma tana zaune a kasa tana cin dambu Sbd karar TV bamuji shigowar motarsa ba, kawai sai sallamarsa mukaji saida ya Dan jira for some seconds sanan ya shigo purple shirt da white jeans me digon purple ajiki yasa, ina kallonsa nace masha allah, allah yayi hallita anan. waje ya samu ya zauna saida na durkusa na gaisheshi, shi kuma ya gaida baba mero, kallon ta yayi da faraa yace baba mero yau kuma danbu kika yi? Aisha ce tayi wallahi, dake tayi azumi aikuwa akwai Aisha kawo masa, don naga kaima kana sonsa Sbd da kana sawa nayi maka, kallon fuskarsa nayi Sbd inaso na tabbatar da abinda take fada, sainaga yayi murmushi kawai, Amma fa ita yayiwa bani baπŸ˜€. A nutse na mike nace nan zan kawo maka ko dining? Cikin wata murya ta kasaita yace kawo min nan, a nutse na dauko flaks din abincin, sanan na dauko plate da spoon na bude fridge na dauko guntun zobon dazu da kuma fruit salad duk na Jere a gabansa kum duk lkcn Dana sunkuya zan ajiye kayan saiyaji kamshin turarena ya daki hancinsa, wani irin mayyataccen kallo yake bina dashi, har baba mero ta gane ta mike ta koma dakin ta. Da murya can kasa yacemin ba zakiyi serving dina ba? Da sauri nazo na zuba mishi I tot zaice yayi yawa, Amma sainaga ya fara ci na zuba mishi zobon a cup, yanaci yana kora zoban kana kallonsa Kasan yana enjoying cin abincin, INA satar kallonsa saida ya share dambun Tass, da Kansa ya kara zobon ya shanye, fruit salad din ne yace zai tafi dashi yasha a gd nace to mikewa yayi tare da cewa kya fadawa baba mero na tafi nace to, Bari na rike maka fruit salad bowl din. Saida na rakashi har bakin mota nasa aciki nayi mishi sallama, harna juya na fara tfy saiya tuno da abinda ya kawo shi gdn, cikin unique voice dinsa yace Aysha zo nan INA zuwa yace meye hadiki da Faisal? Da rawar murya nace sona yake, kuma kema kina sonsa? Kai kawai na daga masa, are you sure? Nace yes a hankali, to kuma Elbash fa? Aishi ba soyayya muke ba, kawaidai yana jinane kamar blood sister shi, nima kuma haka nake jinsa. Is alright saida safe, kawai ya shiga motarsa ya tafi.


Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [9/25, 12:10] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣2⃣5βƒ£βž–1⃣3⃣0⃣

Yana zuwa gd wanka yayi ya dauko fruit salad dinsa yasha, sanan ya shiga toilet yayi brush ya hau gado ya kwanta, kyakyawar fuskarta yake hangowa a yanayin daya ganta dazu ya rasa me yasa a yan kwanakin nan yake yawan tunanin ta, dandanon girki dazu ya tunu, meyasa yake jin kishinta sosai? Karfa ace na fara sonta? Wata zuciyar tace kul karma ka soma, Sbd mum dinka bazata taba amince maka ka aureta ba, da wanan tunanin bacci ya dauke shi

Washe gari
Wajen 12 pm mum din adon gari suka tafi kd da sadiq, ina zaune ina aiki Faisal yazo ya sami kujera a kusa dani ya zauna da mamaki nace lpy ka baro wajen aikin ka ka taho nan? Wallahi tunanin ki ne ya addabe ni, na kasa jurewa shiyasa nazo na ganki, wani murmushi ya sakar min yace yau tare zamuyi aikin. Haka ya zauna muna ta hira Sbd caring din da yake nunamin nima yanzu na fara sonsa sosai dagowa yayi yace Aysha nifa har yanzu ban taba ji kince kina sona ba, anya da gaske ana sona kuwa? Hawaye ne ya fara zuba a idona subahanalla me ya faru? Ko mgnr dana fada ta bata miki rai ne? Ko daya, ina sonka Faisal saida inaji ajikina aurena dakai ba me yiyuwa bane, Sbd duk ranar da parents dinka suka San ko ni wacece bazasu taba yarda ka aureni ba. Ban gane ba Aysha, yimin bayani yanda zan fahimta. Kaga yadda ka ganni to haka nake banida kowa, bansan kowa nawa ba, ba wani mutumin da zan nuna maka nace Dan uwana ne kuka sosai yaci karfina.....is OK Aysha ki dena kuka, koma ya kk INA sonki a haka zan samo miki iyayen karya a daura aurenmu, idan yaso koda su dad dina sun gane daga baya kinga kin riga kin zama matata, so duk yanda zasu yi dani bazan sakeki ba. Kallonsa nayi da jajayen idanuwa na nace kana ganin hakan zai yiyu? Yes me zai hana, kuma so nake muyi auren nanda 1 month, Allah ya zaba mana abinda yafi alkairi yace amin, bari na tafi zanzo in d night, nace to Allah ya kaimu tare muka fita nayi masa rakiya muna cikin tfy call ya shigo wayata, ina dubawa naga adon gari hlo sir, shigo ina son mgn dake, nace to Faisal bari na koma daga nan boss yana nemana, is OK saina zo. Da sauri na shiga office din kamshin turaren sa ne ya bugi hancin na sanan sanyin A/C ya biyo baya. Zaune yake akan 3 seater da sallama na shiga bayan ya amsa yayi min nuni da na zauna a kusa dashi, a darare na zauna sanan yace mum dina tayi tfy zuwa kd sai next WK zata dawo, ni kuma bana Iya cin abincin restaurant idan ba ya zama dole ba, so shine nake so daga yau ki ringa zama a gd kinayi mana girki, kafin mum ta dawo kallon kwayar idona yayi Wanda har saida tsikar jikina ta tashi inafat ban takura miki ba ko? Murmushin da nasan yana karamin kyau nayi sanan nace ba matsala to yanzu ki koma gd kawai ki Dora mana abinci Sbd harna fara jin yunwa nace to a tashi lpy.

Ponded yam nayi da egusi soup, sai paper chiken, da kuma kunun aya me kwakwa da madara zuwa 3pm na gama hada komai, sai kawai na shiga wanka na shirya cikin wani boyel sky blue Riga da siket ne, sanan nayi simple make up nayi na fito baba mero sai tsiya take min wai bata gane tsakanina da adon gari ba kodai mun daidaita kanmu ne nace aa wallahi har yanzu be ce yana sona ba, tace amma ya dauko hanya ai, a zuciyata nace Allah ya amsa bakin ki.

Saida ya koma gd yayi wanka ya canja dressing as usual kanan kaya yasa, black jeans da red shirt me tsada, sai flat cover shoe red, tun kafin ya shigo gdn muka jiyo kamshin turaren sa, da fara'arsa ya shigo saida ya Dan rusuna ya gaida baba mero, sanan nima na durkusa na gaisheshi sanan nace bismilla INA gaba yana bina a baya saida mukaje har kan dining nayi serving dinsa sanan na kawo masa ruwa a bowl ya wanke hanunsa yace ni ban Iya wanan katsantar ba, sink din dining area ya nufa ya wanke anan, sanan ya dawo ya fara cin abincin saida yaci yayi dagas sanan na kwashe kayan na dawo muka fara hira, yanzu abin nasa mamaki yake bani Sbd ya daina shareni yana sakar min fuska sosai, saidai saida har yanzu mulki da kasaita suna nan, kuma idan yana magana sai ya ringa wani basarwa phone dinshi ya dauka ya kira mum bayan sun gaisa yace masa ga neehal ma Ku gaisa ta karba Yaya kabeer ina yini yana jin voice dinta yaji gabansa ya fadi, lpy kalau neehal ya gd kuma ya shirye2 alhamdulilla ai zakazo daurin aure ko? Insha Allah, to Allah ya kawo ka lpy amin nagode. Tunda ya fara wayar na shiga tunanin wacece neehal? Me yasa mum dinshi ta matsu da saiya gaisa da ita? Shi ya katse min tunani da cewa Mrs Faisal ya akayi ne? Ko tunanin Faisal din ne? Waima na tambayeki, kin bawa Faisal lbrn ki nace eh, OK to me yace? Nan na kwashe duk abinda yace min na fada masa, wata yar iskar dariya yayi sanan yace shege Faisal, kuma kin yarda da discission din da ya yanke? Nace eh, har yanzu ke yarinya ce Aysha, kuma he is a barrister you can't understand his true color zai kara magana kenan call ya shigo wayarsa hlo OK your Excellency gani nan zuwa. Aysha bari na tafi zamu shiga meeting ne da Excellency, wani shu'umin kallo yayi min yace ina ganin daga can zan wuce gd, gobe da safe ki hadamin break fast da wuri don Allah, zanzo naci kinji beauty nima yau a Dana sunan wata sansanyar dariya nayi da har saida kumatuna ya lotsa nace Allah ya kaimu gbn.

Maman Aysha
[9/25, 22:53] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

1⃣3⃣0βƒ£βž–1⃣3⃣5⃣

Tun ranar da mum ta tafi kd kullum adon gari a gdn yake cin abinci, dalilin haka yasa wata shakuwa ta shiga tsakanina dashi da kyar yake tafiya idan yazo.

Yau Friday, ana saukowa daga sallah direct gdn mu ya taho wata farar gezna ce ajikinsa da kudin ta zai kai 150k da bleu zare akayi masa dinkin, ya Dora wata dakyakkiyar hula me tsadar gaske anyi mata Zane da blue and white zare, abinka da farin mutun ba karamin kyau yayi ba, white rice and stew da cose low nayi mishi bayan yagama ya kalleni yayi min lallausan murmushin sa me tsada yace zan tafi Kaduna gobe daurin auran kamal ina ganin sai Sunday zan dawo akwai wani Abu da kuke bukat? Jikina a sanyaye nace ba komai Allah ya kaika lpy ya dawo dakai lpy, yace amin beauty, neehal ce ta fado min rai a zuciyata nace shikenan zaije su hadu da ita, idan kyakyawa ce ma may b ya aureta tunda mum dinsa ba sosai take son ya auri zuby ba, hawaye naji ya fara zuba a idona muna hada ido yace haba my lovely sis, ya kk kuka kuma, ko bakya so kiyi missing din brodanki? Kai na daga masa ohh sorry karki damu Faisal yana nan zan fada mishi ya kula min dake sosai kinji. A zuciyata nace Dan renin hankali ni kai nayi missing ba Faisal ba, kuma ko baka fada ba Faisal kam ai muna tare......katseni yayi da cewa ko zaki bini mu tafi tare? 😳 aa Allah ya kiyaye yace amin, lekawa yayi sukayi sallama da baba mero ya bata kyautar kudin da nima bansan nawa bane sanan muka fito na rakoshi har bakin mota.

Da helicopter dinsa ya tafi, gdn su kamal ya fara zuwa dake unguwar rimi bayan ya gaisa da mum dinsa da kuma uwar ango sanan ya wuce hotel din daya kama musu shida body guards dinsa guda biyar da kuma sadi, kowa dakin sa daban sanan sanan dukkansu saida ya bawa kowa 50k. Karfe 8 suka tafi wajen dinner wacece fadar zaruwatta ma bata lkc ne, wani lafiyyayyen boyel yasa maroon da kudinsa zai kai 250k banda daukar ido ba abinda yake hammm me karatu just imaging wato zallar kyau ne ya hadu da daukar wanka, matasan kano sunyi gaskiya da suka sa masa suna adon gari domin kuwa ya yaki yam matan Kaduna wasu harda fada, amma shi besan ma sunayi ba πŸ˜€lol.

Washe gari bayan an daura aure wajen 4pm suka fara shirin tfy wajen mother's eve da Maman ango ta shirya, daidai nan FCT minister ya kira adon gari yace masa yayi winning contract din daya nema, Sbd haka duk yanda zaayi ya tabbatar ya isa abuja b4 8pm Sbd President zai zauna dasu 8:30, aikuwa ba shiri yayiwa ango da mum dinsa sallama ya suka wuce abj, 1 hour a abj tayi musu direct gdnsa nacan ya wuce yayi wanka ya canja kaya yayi shiga

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment