Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mgnr da nake so dake, banyi musu ba naje na zauna, sanan ya dubeni yace baki mamaki ba dana taho dake gdn, instead of na wuce dake gdnku? Yaci gaba da magana washegarin ranar da abin ya faru na kira dad dinki nayi mishi bayanin cewa na bugeki da mota kina asibiti unconsciousness, me makon ya tausaya yanda kowanne uba yakewa dansa idan Abu ya faru, saiya jefeni da wasu maganganu da nake son jin amsarsu daga gareki, Aysha zan tambayeki bana son kimin karya, Sbd ba mutumin dana tsana irin munafiki, makaryaci da kuma me cin amana, so pliss I want you to tell me d truth. Tambayata ta farko wane irin umarni dad dinki ya baki kika ki yi? Yace rabonsa dake kusan wata hudu kenan, a gdn wa kike bayan kin bar gdnsa? Sanan daga ina kike lokcn dana kadeki? Cikin nutsuwa na fara bashi lbri tun daga ranar da deputy governor yace yana sona, korata da daddy yayi, zama agdn elbash aikin dana fara da kuma korata da matar elbash tayi Wanda shine sanadiyar fitowata harka kade ni. Saida ya zubda hawaye don tausayi sanan yace kin tabbata lbrn da kika fadamin gasky ne? Nace eh, yace to karki damu naji duk adduar da kikayi dazu bazan boye miki ba da natsaneki Sbd rashin kunyar da ki kayimin, da kuma tozartani da kikayi a media, Amma yanzu na hakura kuma zan temaka miki, zan baki daya daga cikin gdajena ki zauna, zan nemo miki wata tsohuwa data tafa aiki a gdnmu mutuniyar kirki ce Ku zauna tare, sanan zan daukeki aiki a matsayin sakatariya ta, Amma inaso ki tsare mutuncin kanki. Insha Allah zanyi nagode Allah ya saka da alkairi, amin, idan yaso Monday saiki fara fita

Maman Aysha
[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/20, 10:13] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
8⃣0βƒ£βž–8⃣5⃣

A ranar yaje gwamai ya dauko baba mero, ya direct gdn daya bamu mu zauna a lamido crecent ya wuce da ita ya sami almajirai suka tayata gyarn gdn, sanan yaje mall dinshi ya iyo mana provision, duk wani Abu da Kasan ana bukata a gd adon gari ya sayo mana, har detergents saida ya siyo, ya sayo mana gas cooker da cylinder saida ya tabbatar komai yayi normal sanan ya dawo gd. Ni kuwa tunda ya fita nake bacci ban farka ba sai after 3 toilet na shiga nayi wanka nayi alwala INA sallah naji motsin shigowarsa, bayan na idar nayi addua saina fita a dinning na same shi har yayi wanka yasa wasu shegun blue shirt da black jeans saida na Dan rusuna nace ina wuni? Ba tare daya kalleni ba yace lpy INA gajiya, ya jikin? Nace da sauki hankalinsa gabadaya akan phone dinsa yake, shiyasa na sami damar kare masa kallo wato bayan fitinanan kyaun da yake dashi, yana dauke da wani sirri da saika Tara maza dari baka sami guda daya me irinsa ba, in fact kyaun shi is very unique......ke meye kika zuba min ido kina kallona ina ta mgn ba responding? Kunya ce ta kamani na rasa me zance masa, bismilla zo kici abinci nace to a kujerar gefensa na zauna, tunda na zuba abinci bancin banci yakai 3 spoon ba sai wasa da spoon din kawai da nake Sbd tsananin kwarjini da kuma kunyarsa da nake ji, inajin ko ganewa yayi sainaji yace koma daki tunda ba zaki Iya ci a gabana ba, aikuwa da sauri na mike ina tafiya kmr wacce kwai ya fashewa a ciki na shiga daki naci, bayan na gama na shiga kitchen zan wanke plate din yace na bari me aikinsa zai wanke, dake duk masu aikin gdnsa mazane. Ina zaune ina kallo a laptop dina ya shigo dakin ni xan fita, sbd inada meeting yanzu. kamar yadda na fada miki na dauko baba meron tanacan a gdn so ki hada kayanki nayiwa bala driver mgn zai kaiki karbi wanan ya miko min wrappers din 1000 guda biyu, Ku biya ta boutique ki sayi kayan da zaki ringa zuwa office dasu, dakai food items gdn idan da akwai abinda babu kayimin magana, ina phone dinki nasa miki no na, phone dina a kashe take Sbd inaso na canja layi saidai na rubuta a paper. Be quick da Allah sauri nake da hanzari na dauko yana fadamin harna rubuta, sanan yace 9am nake fita office, so iam expecting you b4 nine kuma bana son late coming be jira abinda zance ba kawai ya fice daga dakin wata sansanyar ajiyar zuciya na saki dole kayi abinda yafi haka ma, Sbd Allah ya baka duk wani Abu da Dan Adam yake bukata a duniya, ba abinda ka nema karasa gabadaya voice dinsa ta tafi dani, Sbd gashi dai da harshen Hausa yake min magana, amma yanayin yanda yake pronouncing kowacce kalma saika rantse ba Hausa yake ba. Me karatu kar kuga kamar na zake da yawa, wallahi adon gari ya hadu ne sosai, is not my fault yanada fitenannan kyau ne, kuma ga class shiyasa

Maman Aysha
[9/20, 16:34] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
8⃣5βƒ£βž–9⃣0⃣

Ta wani B classic boutique nabi na sayi kaya masu kyau, Amma gown sunfi yawa aciki na debo haddadun shoe & bag sanan muka wuce lamido crescent inda sabon gdn yake. Muna zuwa me gadi ya bude mana gate muka shiga, gida flat house ne me kyau anyi interlocking gdn gabadaya, kuma yanada packing space da zaa Iya ajiye motoci 4, Dan madaidaicin falo ne dauke da arch guda biyu, na bangaran gabas dauke yake da corrido sai dakuna guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya, na bangaran yamma, kuma one bed room ne da toilet aciki da alama a matsayin master room akayi bangaren arewa kuma dinning area ne da kuma kofar ketchen gdn yayi kyau sosai, ga unguwar very silent ba hayaniya.

Wasu yan madaidaitan kujeru yasa lemon green, so komai na falon lemon green ne, sanan gabadaya 3 bed room din ya zuba furniture's aciki, da alama bakinsa da yake saukarwa da agdn. Malam bala da baba megadi ne suka shigamin da kayana ciki, dakin da yake a matsayin master room na zaba a matsayin dakina, kuma baba mero ta tareni da faraarta.

2 days later(7:45pm)
Zaune muke muna rangada hira nida baba mero sbda matar tanada tsananin kirki ga barkwanci duk lkcn da muka zauna saita bani dariya, yau kwana biyu kenan da fara zamanmu amma kamar mun shekara da ita. Tana bani wani lbri inata dariya ya shigo gdn yanata sallama bamuji ba, har saida ya shigo cikin falon wata night gown ce me laushi a jikina, doguwa ce har kasa kaina ba dankwali saida na raba gashin gida biyu na tuke su sun kwanta a gadon bayana. Fuskarsa ba yabo ba fallasa saida na rusuna na gaishe shi sanan yace kinsan gb zaki fara fita ko nace eh, to abinda ya kawoni na manta ban fada miki address din wajen ba, Sbd state government ta karfi hayar BAGAUDA house, na koma kamfanina na club road, nace to, kinsan wajen ne? Eh mun taba zuwa Neman ka wajen daga office din mu OK to nan zaki goben har yanzu baki sayi sim card din? Nace aa, ga wani saiki yi amfani dashi Sbd da kinada waya da bansha wahala nazo ba, juyawa yayi yace baba mero ya gdn ba matsala dai ko? Tace wallahi ba komai, don Allah dama inaso na fada miki karki bari mum dina tasan kuna nan, sanan don Allah ki kula da Aisha sosai kamar yadda zaki kula da yarki, ki dauke ta a matsayin ya kuma ki kula da tarbiyar ta don na fuskanci kanta yana rawa. Ke kuma Aysha inaso ki dauki baba mero a matsayin Uwa, kuma kiyi mata biyayya banason rashin kunya kinji ko don nasan baki da kunya. So ni zan tafi saida safe muka amsa da Allah ya kaimu. Baba mero ce tace ke Aisha haka ake bazaki tashi ki rakashi ba, dariya nayi nace ni awa zan rakashi? Tab kinaso ya wulakantani kenan, wane irin wulakanci? Ba saurayinki bane? Aa wallahi ba abinda yake tsakanina dashi tausayi na kawai yake , to ai saida so ake samun tausayi, aa baba mero kibar wanan maganar, yaga ina bukatar taimako ne kawai, saiya temaka min zanje nayi sallah na kwanta gobe tashin wuri zanyi
[9/20, 20:02] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
9⃣0βƒ£βž–9⃣5⃣

A bangaren elbash kuwa yana dawowa gd ya sami aunty rahama tana jiki duk a sanyaye, yace rahama me yake faruwa naga kamar baki da lpy, dariyar yake tayi sanan tace kalau nake, muje kayi wanka kaci abinci yace to, a daddafe yayi wankan Sbd gabadaya hankalinsa yana gun Aysha ya matsu yaje yaga halinda da take ciki, tunda ya isa abuja yake Neman ta a waya be sameta ba, kuma ya kasa tambayar rahama Sbd kar ranta ya baci. Harta jire masa abinci akan dining zai fara ci kenan saiyaga bazai Iya cin abinci ba tare daya ganta ba, kawai saiya mike rahama INA zuwa bari na duba Aysha don Allah, nan take ta saki kukan munafirci Aysha fa yau kwananta uku rabonta da gdn nan, nayi duk Iya kokarina naga na nemeta Amma na rasa, kuma ba Wanda yasan lokcn data fita da naga motarta tana nan nayi zaton itama tana ciki, saida na duba dakin naga wayam. Tunda ta fara mgn yake salati, daga karshe kawai saiya fashe da kuka idan ma guduwa Aysha tayi to kece sila, jikina yana bani abin kikayi mata ya bata mata rai harta bar gdn. Me yasa rahama? Meyasa kika fiye son kanki da yawa? Me yasa kika bar zuciyrki ta bushe kika zama marar imanin da kika kasa tallafawa rayurwarta? Bata da kowa fa, kuma ni kadai ta aminta dashi a garin nan yanzu wa yasan inda ta tafi? Why pliss itama kuka take sosai tabbas ni nayi silar tafiyarta, Amma wallahi nayi regretting don Allah kayi hakuri ina masifar sonka kishi ne yasa na aikata don Allah ka yafemin zama tayi tana rasgar kuka kana kallon ta zaka San tayi nadama, kamota yayi ya rungemeta ajikinsa yace shikenan daina kuka Allah yasa ta fada hannun nagari, kuma Allah yasa haka shine mafi alkairi a gareta rahama tace amin.

Yau kwana na biyu kenan da fara fita aiki, kuma ba wata matsala inayin aikina succefully, ya kafa matakan tsaro sosai, Sbd sai an tsallake office hudu sanan azo nawa, office na farko screening din mutun ake a tabbatar baya dauke da makami, harmu sttaf din wajen akewa, office na biyu kuma body guards dinsa ne suke zama physically suke checking din mutun, idan basu yadda da mutun ba tunda daga nan suke korarsa, sai office na uku kuma anan ake duba sunan mutun aga idan da sunansa acikin list din Wanda zai gani a ranar, office dina ne na karshe ni kuma duk Wanda yazo zan mishi waya na fada masa idan ya amince saiya shiga.

Zaune yake a office yana signing wasu files kawai sai wayrsa ta fara ruri yana dubawa yaga deputy governor ne yace yallabai ka wuni lpy? Lpy kalau, Aysha Ahamad TURAKI ta dawo company ka da aiki, Sbd haka inaso ka kureta yanzu nan, to yallabai tayi wani lefin ne? Umarni nake baka, baka da right din da zaka Sani na koreta yallabai Sbd kamfanina ba a karkashin gwamnati yake ba idan zan koreta ni zanyi raayi da kaina ba wani ne zai Sani ba, kuma yarinyar tana tsananin bukatar taimako banga abinda zaisa a koreta ba. Idan maganar da nayi ta bata maka rai kayi hakuri bissalam. Yana katse kiran ya fara dialing no me girma governor yayi na farko baa dauka ba, yana kara dialing aka dauka governor yana tsananin son adon gari Sbd aminin babansa ne, kuma yanada amana. Bayan sun gaisa ya bashi lbrn abinda ya faru tsakaninsa da duputy, yace to ba matsala kazo around 8pm sai muyi mgn, yace to Abba nagode

Maman Aysha



[10/14, 9:52 PM] Chopy: [9/21, 16:33] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
⃣9⃣5βƒ£βž–1⃣0⃣0⃣

Yaje ya sami governor yayi masa bayanin komai a tsunake, me girma governor ya tausayamin sosai, kuma yayi masa alkawari zai dauki kwakwaran mataki akan shi. Adon gari na fita daga government house me girma governor ya kira deputy da chairman din partynsu, da kuma wasu mutun biyu masu fada aji a party din sunyi mishi warning sosai akan ya fita harkata, kuma sun fada mishi duk abinda ya sameni y kuka da Kansa, ya bada hakuri kuma yayi alkawari bazai kara ba.

Yauma as usual ina office banda aikin tunanai ba abinda nake, maganar da mukayi da baba mero ce ta dawo min kodai da gaske adon gari sona yake? Sbd caring Da yake nunamin yayi yawa, kuma naga baya shiga harkar yan mata aikuwa idan da gaske adon gari yana sona nafi kowa saa wani lallausan murmushi nayi, sai wata zuciyar tace min kinga Aysha kar ki zake da yawa tausayin ki kawai yake mutumin daya hada duk wasu qualities da ake nema ajikin da namiji me zaiyi da marar asali irinki. Nan take na dawo hayyacina tabbas gaskiya zuciyata ta fadamin, elbash ne ya fadomin a rai Allah sarki ko ya yaji da yazo ya tarar bananan? Phone dina na dauko na fara dialing no dake sabuwar no ce harta katse be dauka ba, saida na sake dialing ya dauka yana jin muryata yace Aysha INA kika shiga INA ta nemanki? Kina Kano ne, ko kin tafi wani garin? Kuma a gdn wa kike yanzu ko kin sami parents dinki ne? Mikewa nayi na tafi ta wajen window na fara bashi lbrn abinda ya faru tunda ga ranar da nabar gdnsa har zuwa yanzu. Kina nufin kina kano? Eh OK to zanzo na sameki a office din gobe nace to shikenan, awaiting call ne ya shigo phone dina har three missed call INA dubawa naga Mr kabeer da sauri na dauka, shigo office dina yanzu nace to, INA shiga naga wasu mata guda biyu dayar sanye take da uniform din yansanda, dayar kuma kana ganin ta zakasan gayu ya ratsa ta, suna tsaye abakin kofa kafin nayi magana yace da wane Dan iskan kike waya har wadanan useless din suka shigo min office batare da naba da izini ba? Rasa amsar da zan bashi nayi Sbd bansan lkcn da suka zo suka wuce ba. Kallon su yayi yace ke nazlee Kike kowa, inaso kisani bana sonki, har abada bazan taba sonki ba, kuma wallahi na kara ganin kafarki a wajena saina saba miki, kuka ta fara haba adon gari don Allah, meyasa kake wulakantani Allah ne ya jarafceni da sonka ka tausaya min mana, cikin tsawa yace nace ki fice min daga office ko sai nasa anfitamin dake, da gudu tafice tana kuka woman police din da suka shigo tare ta bita da sauri. Ba tare da ya dago ya kalleni ba yace ke kuma baki amsa min tambayata ba? Voice dina tana rawa nace uhmm....elbash ne, aiki kika fito yi ko soyayya? Wallahi ba saurayi......dalla yimin shiru be shafeni ba idan ma sonki yake, nidai abinda nakeso ki gane shine karki ga na baki na baki gd, kuma INA nuna miki caring kiyi tunanin ko kinada wani matsayi ne a wajena, your nothing tausayin ki kawai nake, so duk abinda nake miki sadakatur jariya nake Sbd haka ki dauki kanki a matsayin ke ba kowa bace face staff dina, matsayin ki dayane da duk wani ma'aikaci dayake aiki a karkashina, kuma wallahi idan kika kara barin wani ya shigo bada izinina ba sainayi punishing dinki, idan zakiyi soyyayar ki bari idan kin koma gd kyayi, I hope you get me right? Tunda ya fara fadansa nake kuka, dakyar na Iya ce masa eh, sanan yace fita ki bani waje na juya na fice jiki ba kwari. Kujerata na koma na Dora kaina akan table inata aikin kuka saida nayi me isata sanan na shiga toilet na wanke fuskata INA fitowa naga wani had some saurayi a tsaye kana ganinsa kasan he is smart muna hada ido yace min kabeer yana nan kuwa? Nace eh wa zaa ce masa? Kice marwan ne, OK phone din da na saba kiransa da ita na dauka na fara dialing yana dauka na fada masa yace ya shiga, juyawa nayi nace yace ka shiga wani mayen kalau ya bini dashi, sanan ya wuce. Yana shiga yace adon gari kana sha'aninka, a ina ka sami wanan beautyn? kuma dan iskanci ka barta a matsayin sakatariyarka is she not a graduate? Graduate ce mana, mafioso tayi aiki a kusa dani ne, tayi aiki a kusa dakai kana sonta ne? Ba wani so inaso na kare mutuncinta ne, Sbd idan tana kusa dani zansan duk wani move dinta. To tunda baka sonta ni ina ciki sabd gaskiya she is beautiful kuma tanada class Kasan harna gama tsayuwa ta a wajen bata naga kai ta kalleni ba, saidai is lyk kamar tayi kuka naga Golden eyes dinta sun Dan kumbura, ko Kai ka bata mata rai? Bansan ba, Kasan bana son surutu da yawa don Allah ka fadi abinda ya kawo ka, OK zuwa nayi mu tafi gdn kaci abinci, nasa anyi maka favourite dinka, kamar Kasan yunwa nakeji kuwa, bari na fadawa mum karta aikomin da abinci yau. Tare suka fito suna hirarsu suna dariya ni zantafi ki rufe office din ki tafi, nace to, marwan ne yayi min wani lallausan murmushi yace bye Aysha, nace OK bye.

Maman Aysha
[9/22, 13:25] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣0⃣1βƒ£βž–1⃣0⃣5⃣

Ina fitowa naga hadari ya hadu a garin har an fara iska ina tsayi INA jiran me keke napep kawai saina ga wata shegiyar mota ta faka a gabana aminci Allah ya tabbata a gareki ranki ya Dade, sunana Barr Faisal, na Dade INA Neman ki Allah be hadamu sai yau idan bazaki damu ba don Allah ki shigo na baki lift sbd inaso nasan gdnku. Bana bukatar taimakonka don Allah mallam ka tafi, nima don Allah ki taimaka ki saurareni, ni masiyinki ne ba makiyi ba pliss, wallahi na Dade INA sonki, yayyafi naji anfara sai kawai na hakura na shiga muka tafi daidai lkcn kuma motar marwan ta fito, Mr kabeer yana gdn gaba, marwan ya kalli Mr KB yace kare mata mutuncin da kake ya tashi a banza indai a commercial car zata ringa yawo, yanzu haka wanan guy din yanzu ya fara ganin ta, amma kaga yayi convincing dinta ta shiga motarsa yarinyar nada shu'umin kyaun da duk haduwar namiji saiyaji yana sonta, so you have to be very careful, cikin bacin rai KB yace bisu abaya muga INA zai kaita. Haka sukayi ta binmu har kofar gd munyi exchanging no dashi sanan na shiga gd, saida suka tabbatar ya tafi sanan suka dau hanyar gdn marwan.

6:15pm
Kwance nake akan gado abin duniya yayi min zafi, tunanin mum dasu junior ya addabeni yanzu shikenan dad ya rabani dasu? Allah sarki mum, koda wasa bata taba nunamin ba ita tahaifeni ba duk so da kaunar da take nunamin tashi daya mun rabu, ko ya takeji a zuciyarta? Gashi na kira layinta baya shiga, daidai nan naji Kira ya shigo wayaata INA dubawa naga elbash ne, hlo ka wuni lpy? Lpy kalau na matsu na ganki bazan Iya jira harsai gobe ba, so yanzu haka INA kan titin lamido crescent yimin kwatancen gdn, nace to inayi masa sai gashi har kofar gdn, saida na fadawa baba mero sanan na fita, fararen kujeru na ajiye muka zauna a compound din gdn, yana kallon fuskata ya gane nayi kuka, wato har yanzu baki daina kuka ba ko beauty? Wallahi tunanin mum dasu basma ne yaki ya fita a zuciyata, kuma abinda yafi damuna shine idan na kira layinta baya shiga, aikuwa akwai yar matar babanta a office dinmu, Bari na kirata ta turomin sabuwar no ta. Aikuwa yana mata magana ta turo masa Sbd sonshi take, yana bani na fara dialing, bugu biyu ta dauka inayin magna ta fashe da kuka nima kukan nake saida mukayi me isarmu, sanan take fadamin dad ya maida ita abuja Sbd ni, kuma shi ya canja mata layi, nima na Bata labari tun daga ranar da nabar gdnsu har zuwa yanzu in brief ta tausayamin sosai na tambayata su basma da junior ta basu muka gaisa tace kullum sai sun tambayeni sai nace musu kina makarnta, mun Dade muna fita da ita kafin muyi sallama, na Bata hakuri akan ta kwantar da hankalin ta nima yanzu bana cikin matsala hankalina a kwance yake. Cikin farin ciki nacewa elbash nagode Allah ya saka da alkairi, wallahi bakaji yanda naji dadi ba, daidai nan me gadi ya bude gate adon gari ne ya shigo gdn sanye cikin orange shirt da black jeans gashinsa ya kwanta yayi lub, ga wata iska me dadi da take kadawa fuskarsa ba walwala ya karaso wajen ya mikawa elbash hannu sukayi musabaha, ko kallon inda nake beyi ba ya shiga ciki elbash ne yace Aysha ni zan tafi kici gaba da hakuri kinji nasan halinsa yana da miskilanci dariyar yake nayi nace la karka damu wallahi ka gaida aunty rahama yace to zataji insha Allah. Gabana yana dukan uku2 nayi sallama na shiga na same she suna ta hira shida baba mero, ita kadai ce ta amsa min sallama, Amma shi ko kallona beyi ba saida na rusuna na gaisheshi kamar yadda na saba, Amma da kyar ya amsa min ina ganin haka kawai saina tafi daki, INA shiga ya biyoni Ashe ke yar iska ce bansani ba? I don't think lbrn da kika bani gaskiya ne, Sbd na fuskanci kinada rawar kai, wato kin fara Tara maza ko? Cikin sanyin murya nace elbash ne fa, eh nagani elbash ne, Wanda yayi dropping dinki dazu kuma fa? Rasss naji gabana ya fadi.......ko aure kike so? Still banyi magana ba, bazan hanaki soyayya ba tunda bani zan aureki ba, Amma inaso kisani bana son shashanci da rashin kamun kai, ban yarda ki ringa Tara min baza agida ba Sbd haka ki fadawa elbash din ya turo iyayensa wajena muyi maganar aure tunda shi yasan ko ke wacece, zai yadda ya aureki ko besan asalinki ba. Wanan shine last warning dazan baki car key ya wurgomin kan gadon, ga keyn motar da nazo da ita yanzu nan, na barmiki ki ringa zuwa wajen aiki, gud bye. Tunda ya fara magana nake kuka harya fice ya Allah ka kawomin hanyar da zanga iyayena cikin ruwan sanyi ko a daina yimin gori, saida nayi me isata sanan na shiga toilet nayi alwalar sallar magrib.

Maman Aysha
[9/22, 18:32] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣0⃣5βƒ£βž–1⃣1⃣0⃣

Washe gari da wuri na tashi na shirya cikin pink lace nayi dauri me kyau, nasa costume masu kyau, da dauki pink shoe & bag na fice, a motar da KB ya kawo min Mercedes 4matic 240 na tafi, INA zuwa na sami waje na faka motar, tunda na fito Mutanen cikin gun suke bina da kallo har na wuce office dina, Sbd bana shiga harkar kowa acikin wajen. Na zauna befi da 15 mint ba saiga shi ya shigo cikin wasu lafiyayyun suit fuskarsa manne da karamin farin glass din da yake kara masa kyau mikewa nayi nace gud morning sir morning kawai yace ya shiga office, ni kuma na koma na zauna naci gaba da aikina.

12pm
Ina zaune saiga wata kyakyawar budurwa ta shigo da body guards dinta har guda uku at least zataban 6yrs direct kofar office din KB ta wuce da hanzari na sha gabanta bewar Allah baa shiga sai anfada masa, wani kallon wulakanci ta watsa min ke kuma wacece? Kodan naga alamar ke bakuwa ce shiyasa baki sanni ba, aini banida Katanga da shiga office din ina shiga ne duk lkcn danaga dama. Kiyi hakuri nafadamasa Sbd zaki Iya jamin matsala, tsawa ta daka min dalla yimin shiru bansan ya akayi ya kwasoki ba ma, I must talk to him ya zama dole ya koreki wallahi stupid kawai, hayaniyar da yaji ne tasa ya fito yaga abinda yake faruwa suna hada ido naga ya saki wani lallausan murmushi what a surprise? Yaushe kika shigo garin? Da muryarta kamar ta

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment