Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaayi ace kamar yata tana yawon Neman inda zata zauna, Allah yasa haka shine mafi alkairi a rayuwarki nace amin. Sanan na kalli su Abba nace Abba kuma kunji lbrn wacce ta sace ni, kuma me yasa ta saceni? Yace kwarai kuwa, me aikinmu ce ta sace ki wato abinda ya faru shine

Some yrs back
Ni Dan asalin garin makarfi ne, mahaifina shine sarkin garin, kuma tsohon attajiri ne, bayan na gama karatun sec sai maihaifina ya turani Cairo nayi university, kuma anan na hadu da mahaifiyarku ita balarabiyar misra ce so familyn mum dinki gabadaya suna misra kanwarta jalila ce kawai anan 9ja ita Hutu tazo suka hadu da mijin. Bayan na auri amminku har an haifi kamal saina fada harkar siyasa na tsaya takarar chairman din garinmu, da temakon Allah da temakon ubangidana alhaji Mohd BAGAUDA na samu nayi nasara, Sbd kirki da kuma kyautatawa jamaa da muke, bayan munciye shekarunmu sai yan garin suka kara tsaidani, a lkcn kuma akwai abokin takarata alhaji tasi'u hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, lkcn da ake rungutsumin siyasa zaayi zabe, daidai lkcn aka haifeku bazan iya fadin irin farin cikin da nayi ba a wanan ranar domin kuwa nurse din data yimin albishir din haihuwarku ma kyautar mota na bata. Alhaji tasi'u shine yasa a saceki Sbd bokansa ya fada masa cewa duk duniya ba abinda nakeso kamar Ku, kuma dole sai anyi sacrificing daya daga cikin Ku asirin zai yuyu, wanan dalilin ne yasa ya hada baki da Uwani me aikin mu ya bata 1million ta saci daya daga cikin ku. A gdn gonarsa na kura sukayi da ita zasu hadu, Dake Allah ba azzalimin bawansa bane akan hanyarsa ta zuwa kura daga zariya yayi accident, kuma yasa aka nemoni yayi min bayani da bakinsa ya nemi gafarata, washe gari Allah yayi mishi rasuwa. Tun daga lkcn muke Neman Uwani amma ba lbrnta har se yanzu da kikazo mana da lbrn ta rasu. Mun shiga tashin hankali marar misaltuwa a game da batan ki, kullum acikin addua muke Allah ya bayyana mana ke indai kina Raye, Sbd haka ba abinda zamu cewa Allah sai godiya. Jibi insha Allah zamu koma duba kabeer, idan munje zaki rakamu gdn mutumin daya rekeki muyi misu gdy nace to Allah ya kaimu yace amin, naga dare ya fara ya kamata muje mu kwanta ko? Mukace to, kowa ya mike Yaya kamal ma yayi sallama ya tafi gdnsa.

Dake angyaramin dakina INA zuwa na haye gado na kwanta saidai fur bacci yaki dauka na so da tausayi n adon gari ne a zuciyata, phone dina na dauko na fara dialing no Amma akashe, wani irin xugi da zafi zuciyata ta fara in har banji voice dinsa to confirm bazan iya bacci ba, to wa zankira ya hadani dashi? Aunty Salma zuciyata taban amsa, da sauri na fara dialing no ta bayan mun gaisa nace mata ya me jiki tace da sauki, Amma ni na dawo gd Dr marwan ne zai kwana a wajensa nace ayya to Allah ya sauwake saida safe. Yanzu ya zanyi kenan? Neehal ce ta shigo dakin da sauri tace my sis ga hydar zaku gaisa INA karba yace kanwarmu ya kk? Nace lpya kalau, haka dai yayi tamin surutu, daga karshe mukayi sallama na bata wayar yanayin yanda suke ta soyayyarsu a wayar sainaji hnkl ya kara tashi, kawai saina fashe da kuka da sauri neehal tayi sallama da haidar tazo ta rungume ni meya same ki kk kuka sis? Na rasa yanda zanyi nayi mgn da kabeer, kuma gashi bani da no Dr marwan, hydar yanada ita bari nasa ya tro mana, ba mata lkc ya tru ai kuwa da sauri na fara dialing yana dauka nace ya hadamu, cikin unique voice dinsa yace aysha bakiyi bacci ba? Ta Yaya kake tunanin zan iya bacci bayan phone dinka akashe take? Tunanin ka ya hanani bacci kabeer, tausayin halin da kake ciki ya hanani sakat, ji nake kamar na cire ciwon ya dawo jikina, inasonka kabeer, INA maka son da ko kuda banaso ya tabaka, kuma gashi na jawo maka ciwo kana zamanka, duk ni na saka a halin da kake ciki yanzu don Allah kayi hakuri kuka ya kwacemin, da wata irin cool voice yake magna stop crying Aysha, don't blame your self bake kika jamin ba haka Allah ya rubuta, kinga iam not feeling fine, kuma kukan ki yana kara tayar min da hankali so don Allah kiyi shiru, yanzu lkcn farin ciki ne, kinga yanzu ba abinda zai hana muyi aure ko? Nace eh, so dariya da godewa Allah ya kamata kiyi ba kuka ba kinji? Nace to, nayi missing dinki sosai yaushe zaki dawo ki ganni? Abba yace jibi zamu zo, Amma idan nazo bazan tafi ba, ni zanci gaba da kula dakai har saika warke, wata sansanyar dariya yayi yace are you sure? Nace yes, still dariyar yake da gaske zaki iya rikeni, ki feeding dina, kimin every thing da nake bukata, nima dariya nayi nace emana, yace to shikenan we shall see, I love you Aysha, nace I Luv you too, gud night OK night

Maman Aysha


[10/14, 10:22 PM] Chopy: [10/8, 18:50] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
2⃣0⃣0βƒ£βž–2⃣0⃣5⃣

Washe gari a makarfi muka wuni aka zaga dani gidajen yan Uwa alhaji kakanmu kamar ya cinye ni sabd murna kowa sai Jana yake ajiki a hanya nake cewa dad dama haka muke da dangi? Yace su yanzu yan Uwana kawai kk gani, zamu sa rana muje misra kiga familyn amminku nace to Allah kaimu yace amin.

Sai wajen 6pm muka shiga kd, muna zuwa muka watsa ruwa mukayi sallar magrib, sanan nabi lfyr gado na kwanta bansan lkcn da bacci ya dauke ni ba, sai can naji neehal tana cemin na tashi muje muci abinci, nace nifa ba kullum nake cin dinner ba kuje kuci kawai ni zansha cooker Oates da snacks, wato bakya son cin abinci ko? Zan hadaki da ammi ai, da gudu ta fita dining tana zuwa ta tarar su kadai ake jira, ammi tace INA Ayshan kuma? Wai bazataci ba, cooker Oates zata sha Abba yace kirata, a waya ta kirani nazo Abba yace dole sainaci abinci nace Allah Abba nakoshi, Abba yace to je ki hada Oates din kisha nace to.

Ina daki INA duba abu acikin laptop dina saiga neehal ta shigo cikin shirin ta tace my sis hydar ne yazo, Amma ke zaki fara fita a matsayin nice, so nake na gwadashi na gani ko zai ganeki, amma fa sai kin cire kunyar nan taki, nasan zaki iya tashi ki shirya nace to, pyjamas ne ajikina Riga da wando kawai saina Dora bakar after dress akai ta bani turenta nasa, sanan tace swit man nake ce masa, kuma INA Dan durkusa wa idan zan gaisheshi nace to. Wit confidence na tafi INA zuwa bakin kofar naji gabana ya fadi, Amma kawai saina basar na shiga nayi mishi sallama ya amsa sanan na durkusa na gaisheshi na samu waje na zauna juyowa yayi ya kalleni yace nayi missing dinki sosai my baby, tunda sis dinmu ta dawo kin manta dani cikin shagwaba nace to ba muna waya ba, eh munayi, amma ba kamar eye contact ba, to ai yanzu gashi ka ganni ko? Murmushi yayi yace eh, kinsan INA sonki da yawa shiyasa, nafiso kullum na saki a gabana INA kallon ki, neehal ce ta shigo da tray ta durkusa ta gaisheshi nan take ya zama comfuse, zuba mana ido yayi yana so ya gane wani Abu kawai saina katse shi da cewa to ga kanwar tamu nan saidai ka manta baka tambayeta me jiki ba, Kasan fiancΓ©e dinta mukaje dubawa a kn jiya, may b zakasanshi ma Mr kabeer M BAGAUDA, yes nasan shi very nice guy, bansan shine patient din ba ai da naje na dubashi, wallahi baby guy din yanada kirki sosai wani farin ciki naji ya kamani, shaf na manta plan din da muka hada nace saika zauna dashi ma zakaji ya kara burgeka, shiyasa nake kara sonshi wallahi....... Cikin kidima da tashin hankali hydar yace kaddai maganar daya kirani kwanakin baya ya fadamin ta tabbata? Neehal a gabana kk cewa kina son wani?mikewa nayi nace relax Mr hydar, iam aysha tunda ka kasa ganemu ga neehal din can, sis iam sorry kinsan indai zaayi maganar kabeer dole sainayi magana, amma wacce magna kabeer ya fada maka hydar? Da mum dinshi taso hada auran shi da neehal, shine ya kirani ya fadamin Sbd na dauki mataki, juyawa yayi ya kalli neehal yace baby abinda yasa nace zan kawo lefe urgent kenan, turo baki tayi tace ni nayi fushi dakai tunda ka kasa gane ni, ta juya ta fara tafiya mikewa yayi da sauri yayi hugging dinta yace iam sorry my dear kamar taku ce tayi yawa sanan ya kalleni yace kanwarmu nice to met you, dariya nayi nace nice to meet you too, na fita na basu waje.

Da kyar ya samu ta hakura sukaci gaba da hirar su ta soyayya bayan ya tafi ta shigo dakina aikuwa na fara tsokanar ta hydar ya kasa ganeta a tsakanin mu, tace kaddai ki cika baki gb zamu je kanon ai ki bari idan kabeer ya ganeki saiki ji dadin tsokana ta, nace to shikenan Allah ya kaimu gben tace amin, hugging dina tayi tace gud night sis

Maman Aysha
[10/8, 21:33] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
2⃣0⃣5βƒ£βž–2⃣1⃣0⃣

Washe gari muna gama break fast muka fara shirin tafiya kano har dakin Ammi naje nace don Allah ammi ki rokar min Abba ya barni na zauna idan munje na karasa mgnr a kunyace dariya mum tayi tace to Mrs kabeer zan fada mishi Amma kinsan zamuyi missing dinki ko? Saidai muyi hakuri kawai Sbd mu faranta miki, nace thank you mum, you're well come my dota.

Wani hadaddan material muka sa me combination din yellow and red, dinkin Riga da siket ne kayan sun mana kyau sosai red rose silk muka daura, komai iri daya mukasa tunda muka fito falo ammi da Abba suka fara wani irin smiling na farin ciki, Abba ne yace you looks so beautiful my twins Allah ya raya min Ku mukace amin Abba, sanan yace Aysha kince zaki zauna acan ko nace eh yace to shikenan ba matsala muje ko, a tare muka fita a Lexus din Abba muka tafi da motocin escort dinsa guda uku daya a gaba, biyu a baya.

Asibitin muka fara zuwa, muna fitowa daga mota su mum dinshi suna shigowa sai su abba suka tsaya su shiga tare, kuma mukayi gaba, neehal tace ni zan fara shiga, kuma ni zanje a matsayin ki nace to, a zaune yake yayi daidai akan Gado da laptop a gabanshi, sanye yake cikin wata red shirt armless sbd hannunsa, da blue jeans ya kara kyau yayi fresh kamar ba jinya yake ba, shida sulaiman PA ne kawai a dakin, muna shiga neehal ta wuce bakin gadon direct, taja kujera ta zauna a kusa dashi sanan ta gaisheshi ya amsa yana wani Dan iskan smiling, tace honey ya jikin yace da sauki daidai nan ya jiyo muka hada ido nace kanina INA wuni? Yana wata yar iskar dariya yace don't take me as a fool Aysha, kina ganin zaki iya bace min? Tun shigowarku na gane ki, wata sansanyar dariyar farin ciki nayi nace shiyasa nake kara sonka you're very smart, karasawa bakin gadon nayi nace Mrs hydar saiki tashi ki bani kujerar na zauna tunda ya ganeki INA wata yar iskar dariya, tana tru baki ta mike ni kuma sai tsokanar ta nake, na kalli kabeer nace Yaya hydar kasa ganemu yayi, neehal tayi caraf tace ai sabd dare ne shiyasa, nace ba wani nan kareshi kawai kike muka yi dariya gabadaya, Abba ne suka shigo a tare sukace dariyar me kuke tayi ne haka? Na basu lbrn abinda ya faru suma sukayi ta dariya sukace ya kamata kiyiwa hydar abinda zai ringa ganeki da sauri neehal. Bayan sungaida kabeer Abba yace muje gdn naku Aysha nace to, gabadaya muka tafi har mum dinsu kabeer dama tun jiya na fadawa mum zuwanmu.

Muna shiga compound din rayuwar gdn gabadaya ta dawo min, INA gaba suna bina a baya muka shiga har part din mum, INA shiga su junior suka taho da gudu zasu rungumeni, da suka ga neehal kuma sai suka tsaya suna kallonmu, suka rasa wajen wa zasu acikinmu cikin tsananin farin ciki mum ta tare mu saidai itama tsayawa tayi tana kallonmu, ta kasa gane ni aciki ina ganin haka naje na rungumeta kawai saina fashe da kuka, sanan tace su ammi su zauna taje ta kira dad ya fita shigo dasu Abba da Yaya kamal, sanan yaje ya kira mama dasu Yaya zee duk aka hadu, bayan angama gaisawa abbanmu yayi bayani cikin nutsuwa, sanan yayi wa dad godiya sosai kuma yayi mishi addua domin acewarsa bashida abin da zai saka mishi, shima dad ya rokeni gafara yace wallahi besan ya akayi yaji tsanata da rashin tausayi na a zuciyarsa ba, Amma wallahi yayi nadama daga baya, mamace tayi caraf tace nima don Allah ku yafe min, nice silar komai Sbd ni nayi asiri na rabaku Amma wallahi nayi nadama Sbd tun yanzu ga sakamako Nagani da muna gani kamar mu kadai ne gatanki, Ashe babanki babban mutun ne a 9ja, don Allah ki yafemin kinji nace bakomai Allah ya yafe mana gabadaya. A gdn mukaci abinci sanan muka kuma asibiti harsu mum da dad, daganan su Abba sukayi sallama suka dau hanya

Maman Aysha
[10/14, 10:22 PM] Chopy: [10/9, 12:39] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

2⃣1⃣0βƒ£βž–2⃣1⃣5⃣

Su Abba suna tfy mum da dad ma sukace zasu tafi sun bar min su junior dake a gdn zan kwana tace idan na gama zata tro azo a daukemu nace to, suna tfy saiga elbash da murna na tareshi muka shiga ciki ya dubashi ya kara yimin murnar ganin iyayena, sanan yace motata tana nan zai mayar da batir din yakai a wanketa ya kawo min gobe nace to nagode, saida na rakashi har bakin mota sanan na koma. Haka muka zauna da aunty Salma da mum wadda yanzu take nunamin tsananin so, munata hira Sbd yanzu jikin nashi da sauki any time zaa iya sallamar shi ana kiran idar da sallar magrib su mum da aunty Salma sukace zasu tafi, kuma nasan Sbd sunaso subarmu musake ne, amma wani lkcn suna kaiwa 11pm basu tafi ba. Saida na rakasu har bakin mota sanan mukayi sallama na juya na fara tfy kenan kamar daga sama naji muryar Faisal yana kirana, tsayawa nayi har ya karaso ya kalleni yace kin kyauta Aysha, kin samu parents dinki Amma ko ki fadamin, yau kusan 1 WK kenan ba lbrnki yanzu ma Dr marwan ne yake fadamin adon gari yayi accident, kuma yace kema kina nan. Ashe dama soyayya kuke da adon gari? Kunya ce ta kamani gabadaya na kasa bashi amsa, any way ba matsala INA sonki, ban taba son wata ya mace a duniya kmr yadda nake sonki ba Amma inhar zanyi miki adalci, ya zama dole nayi hakuri ki auri abinda zuyarki take so, Allah yasa haka shi yafi alkairi a hankali nace amin nagode Faisal Allah yayi maka sauyi da wacce tafini, wani smiling yayi yace samun irinki da wahala Aysha, na Riga nayi loosing mu karasa ciki na dubashi ko? Nace to a tare muka shiga har cikin dakin muna hada ido dashi yasha kunu, Faisal ne ya karasa har bakin gadon yayi masa sannu ya amsa da fara'arsa har saida suka taba hira ma sanan na rakashi ya tafi. Kabeer yaji haushin rakashi Faisal din da nayi, Amma sai ya basar mukaci gaba da hira ban bar asibitin ba sai wajen 10pm dakyar na tafi sabda banaso nayi missing din shi su junior har sunyi bacci sai daukar su akayi, lkcn da muka karasa gd mum da dad suna zaune suna hira nima na zauna mukaci gaba da hirar sai wajen 11 muka kwanta.

Washe gari da wuri na tashi nai break fast nayi wanka, sanan nayiwa kabeer kunun gyada da kosai Sbd yace shi yake so, sai kuma nayi masa paper soup din kifi ragon ruwa soyayyen irish da kuma plaintai, nayiwa mum sallama dad ya bani key din motarsa camry 2015 na tafi da ita asibiti INA zuwa na samu har yayi wanka ya shirya an gyare dakin banda kamshi ba abinda yake akusa dashi na zauna nace gud morning my soul, yace morning beauty ya gajiya? Murmushi kawai nayi nace me zanyi serving dinka? Yace kunu da kosai INA budewa kamshin ya doki hancinsa, ni nake bashi a baki harya koshi sanan na zuba masa kifin ma na bashi saida na tabbata ya koshi sanan na debe kayan na sasu a gefe naje na wanke hannuna sanan na dawo mukaci gaba da hira, daidai nan Dr Abdul da marwan suka shigo Dr Abdul yace ai sallamarka ma zamuyi sai kawai aci gaba da treating dinka a gd yace to shikenan nagode sosai doctor yace a ba wani Abu, Husna tana tambayar ka idan ka warke ya kamata ka kawo mana madan su gaisa yace ba matsala zan kawota insha Allah awaya na kira su mum nace karsu zo an sallame shi zamu taho yanzu. Ni na rikeshi mukaje har mota, bayan ya zauna na zagaya na shiga su Sulaiman suna binmu a baya muka nufi gdn mum dinsu, a part dinsa na gdn zai zauna an tanadar masa duk wani abu na jin dadi daka sani munyi waya dasu Abba na fada musu ansallameshi, Abba yace neehal da hydar zasu zo gobe sauki shirya ki biyosu nace don Allah Abba kayi hakuri ko sati daya nayi, be gama warkewa ba fa dariya Abba yayi yace kai aysha na fuskanci kinfi son kabeer damu, wai ke bakisan munyi missing dinki bane? Dauriya kawai fa muke nanda lkc kadan nasan Kabeer zaice zai turo, so kinga bamu wani zauna dake sosai ba zaayi auren ki, nace to shikenan Abba Allah ya kaimu goben yace amin. Yauma sai dare na koma gd.

Maman Aysha
[10/9, 14:55] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

2⃣1⃣5βƒ£βž–2⃣2⃣0⃣

Yauma da wuri naje gdn, dasu basma mukaje ga yayyan aunty Salma khairat da nabil suka hadu sunata wasa, wajen 12pm su neehal suka karaso ita da hydar muka zauna ake ta chapter a dakin, saika manta ma zaman jinya muke sabd hanun yayi sauki sosai nida aunty Salma muka shiga kitchen muka shirya abinci me rai da motsi kowa yaci ya koshi, sanan mukaje gdn elbash nida neehal matarsa ta haihu mukayi musu barka ta you and your babys dream muka bi nasayi kayan baby na 20k, ita kuma aunty rahama na sai mata turmin Hilton da murna sosai ta tare mu, itama tayi mamakin kamar da muke da neehal mun Dade muna hira ta rokeni gafara nace na yafe mata, elbash ba karamin murna yayi ba, mukayi musu sallama muka koma gdn su kabeer Bayan munyi sallar laasar su neehal sukace zasu tafi nan take gabana ya fadi Sbd Abba yace na bisu, kirnta gefe nayi nace Abba fa yace na biku dariya tayi tace Mr Luv ammi tace a kyaleki, idan sunzo saiku tafi wato son kabeer ya rufe miki ido ko missing dina ma bakya yi ko? Wallahi ba haka bane sis...dadai nan mukazo bakin kofar falon waje, wata pritty girl muka gani tana ta hada su sulaiman da allah akan su barta ta shiga ta duba adon gari amma sunki, neehal ta kalleni tace my sis akwai aiki a gabanki don gaskiya wanan kabeer din naki saikin kara daura belt, kinsan he is more than handsome, dole yan mata su bishi, ammafa bance kije kiyita damun kanki ba sbd yana sonki sosai. Mu muntafi sai munyi waya, nace to Allah ya kiyaye INA daga mata hanu muna dariya har suka bace, sanan na koma ciki.

5pm yahuza suya

Yan mata da samari ne zaune anata shakatawa kowa yana harkar gabansa, a gefe grp din yanmata ne masu ji da Kansu da yawan su zai kai su goma suna shan ice cream suna hira kawai saiga wata kyakyawar yarinya tazo wajen tace hii friends sukace hlo ralma ya gari tace gari ba dadi, kamar ya ba dadi? Baku da labrn ADON GARIN yan mata da samari yayi accident a tare sukace what! Yaushe kenan? Cikin damuwa tace yau kwana hudu har an sallameshi ya koma gd, tab aini banji lbrnsa ba kwana biyu I tot yayi tafiya ne, ya salam ya zama dole naje Dubiya koda bazai amsamin ba, kinsan ganin fuskar guy din nan kadai farin ciki yake sani koda kuwa hararata yayi, ramla tace aikuwa dakyar idan zaa bari ki ganshi, domin kuwa PA da body guards dinsa ne a gdn sai sunga dama ake shiga nima yanzu daga can nake da renin hankali littafi da Biro suka bani sukace na rubuta sunana. Zuby dake gefe tana sauraransu tun lkcn da akace yayi accident tayi mutuwar zaune a zuciyatta tace yanzu adon gari yayi accident har ya kwanta a asibiti Amma ban sani ba, cikin tashin hankali tacewa body guards dinta kuzo mutafi, tana tafiya suna take mata baya suka nufi gdn mum.

Su neehal suna tfy na bude motar da nazo da ita na dauko wata rigata aciki, na shiga dakin aunty Salma na gdn nayi wanka na dauki rigar ta Dana dauko a mota English gown orange me spagetti hand ta Dan tsuke daga sama rigar tayimin kyau sosai na yane kaina da karamin orange gyale sanan na fesa turare a falo na sami mum da aunty Salma suna hira nayi musu sannu na wuce dakinsa, a zaune yake da friends dinsa harda Dr Abdul sunata hira, INA shiga na juyu da baya da sauri mikewa yayi ya biyo bayana, a corridor muka hadu yace ya kk koma? Kafin nayi mgn yace inason shan fruit salad nace to, saida na fadawa mum a kunyace sanan na nufi kitchen na fara hada mishi in few minutes na gama lkcn Dana kaimasa shida sadik ne kawai a dakin, INA shiga sadik ya fita a kusa dashi na zauna na fara bashi kamar wani karamin yaro yana sha muna hirar mu ta soyayya

Kamar an jefota daga sama ta shigo dakin suna hada ido ta fashe da kuka haba kabeer don Allah, wacce irin kiyayya kake nunamin? Ina matsayin matar da zaka aura, Amma kayi accident harka kwanta a asibiti ban sani ba. Kiyi hakuri zuby, wallahi hnklna ne baya jikina, komawa tayi ta daya gefenshi ta zauna sanan cikin kissa tace ya jikin? Yace da sauki dauke fruit salad bowl din tayi tace bari nima na samu ladan kawai ta fisge spoon din hannuna ta fara bashi abin mamaki sainaga ya bude baki yana karba, na kafeshi da ido amma ko ajikinsa nan take naji zuciyata ta fara zugi mikewa nayi zan fice daga dakin sainaji ya ruko hannuna yace INA zaki? Murmushin karfin hali nayi nace zan Dan Baku waje ne Ku Diskanta kaida madan dinka na zare hannuna na fice daga dakin

Maman Aysha




[10/14, 18:45] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“

2⃣2⃣0βƒ£βž–2⃣2⃣5⃣

Ina fita daga dakin yace ta daina bashi fruit salad din haka ya ishe shi, bayan ta ajiye bowl din tace honey dama inason mgn dakai, ba tare daya kalleta ba yace inajin ki, yauwa Kasan a yadda muka yanke date din bikin mu nida kai, yau saura sati uku kenan bikin, kuma Kasan har yanzu a family Ku ba Wanda yaje gdnmu akayi mgn, ni kuma gsky banaso na rasaka, shine nace me zai hana tunda baka da lpy idan time din yayi a daura auran idan yaso daga baya sai a daura auranku da Aysha kuma a hada bikin lkc daya ayi, murmushi yayi sanan yace duk yanda kk ce haka zaayi Allah ya kaimu lkcn cikin kissa da farin cikin samun nasara tace amin

Ni kuwa INA fita daga dakin wasu hawaye suka cika min ido, saida na tsaya a corridor na goge sanan na fita falon, aunty Salma da mom suna zaune na musu sannu na wuce daki, aunty Salma ce ta biyoni tace aysha me yake faruwa naga kmr ranki a bace yace? Kakaro murmushi nayi nace kaina

1 Comments On KABEER
avatar
abubakar-adam

11 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment