Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatar hannun, sai da yaji hannun yana mishi rad'ad'i sannan ya barshi ya kunna shower ruwa na xubar mishi a jikin shi yana sauke ajiyar xuciya akai akai tare da fad'a cikin tunanin uban wanda yayi mishi haka, toh wane xai saka mishi kenkesu a cikin aljihun shi "husna, yes! itace don ba wanda xai min hka sai ita ae kuwa xata ci uban ta "

Sai da yayi wajen 40 mint yana wanka sannan ya fito daga toilet d'in yana d'aure da towel ajikin shi da wani k'aramin towel yana goge gashin kan shi agogo ya duba yaga lokaci ya wuce na Inda xashi kwafa ya saki ranshi a matuk'ar 6ace yana ayyana abin da xai yiwa husna ya huce akan abin da tayi mishi (Hmmm ni da sumy muka kalli juna tare da fad'in wannan shine ramuwar gayya kenan, ya mance duk muguntar da yake mata ne).

Wani black 3quater ya sanya tare da white d'in riga mara hannu mai irin mai bottom di'n nan ya 6alle botir guda biyu hakan ya lallausan gashin kirjin shi bak'i wuluk a kwance lub dasu daman rigar irin mae Shara Sharan nan ce ana iya hango fatar jikin shi da murd'ad'd'en damtsen hannun shi fuska a tur6une ya fito daga d'akin nashi ya tarar da hajia maamaa ta xuba uban tagumi tana ganin shi ta taso da sauri tana cewa

"ibraheem ya aman dafatan ya tsaya koh, ya kake jin jikin naka, na xuba maka abinci ka sake ci "

Da yake lokacin da ya shiga bedroom d'in shi key yasa ya rufe, yamutse fuska yayi yana dan kalle kallen k'asa, hajia maamaa ta fahimci abin da yake nema don hka tace
"ae tuni ankwashe su an xubar "
Sai lokacin ya saki ajiyar xuciyar kwanciyar hankali yana yamutsa fuska yace
"ni fah abinci bana bukatar shi maamaa "

"toh ni abin da ya bani mamaki ya akayi kenkeso acikin aljihun wandon ka taya suka shiga? "

Kwafa yayi tare da cewa "wanne ya saka xaki ce maamaa "
"auuu sama akayi kenan, to uban wane ya saka maka abin da baka so"
Nan ta fara fada an ta6a d'an gaban goshin ta, cikin takaici yace
"na tabbatar husna ce ta samin, tana ina? "
Dan shiru hajia maamaa tayi sannan tace "anya husna ce xata saka maka, abin da ita ma take matuk'ar tsoron, toh a ina xata same ta "

"yes! Ita ce wlh kuma sai na mata duka wannan ae ranin wayo ne ni sa'an tane da xata yi min wannan wasan "

Yana gama fad'in hka ya fice a fusace hajia maamaa taso tsaida shi don a yanda yake cikin 6acin ran nan xai iya ji mata mugun rauni, ta6e baki tayi tare da xama ko dan ita ta jawa kanta ba ruwa na Idan taji ajikin ta baxa ta k'ara yi mishi haka ba.


Suna xaune a parlour mumy husna, fadila, Ilham da raudah sai su aunty khadijah, aunty Amina, aunty marwa, aunty aimana, aunty rufaidah, gaba d'ayan su kallo suke a tashar mbc bollywood suna kallon wani series film madhubala suna d'an surutan su da dan musu akan wannan yafi son sultan don yafi birge shi yayi da wasu su ce sun fison RK sun raba kansu biyu kowanne da team d'in da ya xa6a.

A fusace ya bankad'e labulen falon ya shigo suna ganin kowanne ya nutsu aka dai na surutu kai tsaye inda husna take ya nufa damk'a d'aya yayi mata da hannun shi d'aya ya fara janta, tuni sauran en uwanta suka fara tausaya mata yaxo gaf da kofar barin falon yaji muryar mumy tana cewa

"lafia qlau kake kuwa, me tayi maka? "
"kamar ni wannan kaxamar yarinyar mumy ta samun kenkesu acikin aljihun trouser na "
Ya fad'i yana xuba huci tare da hararar husna wadda cikin ta ya d'uri ruwa kiris ya rage ta saki fitsari a wando, gaba en falon hankalin su ya dawo kan su girgixa kai mumy tayi tare da cewa
"toh kayi hak'uri mana kasan yarinta ce take damun ta "

"ba yarinta bace tsabar ta raina shi ne ibraheem maxa ka je kayi mata abin da kayi niyya yanda gaba baxata k'ara kwatanta hakan ba "
Gaba d'aya suka jiwo suna kallon mameen husna wadda take maganar hakan ba k'aramin dad'i yayi wa ibraheem ba kafin mumy ta ankara har ya kwashe ta sun bar falon tuni husna jiki ya fara 6ari tana kuka wiwi kallon ta yayi yace "yarinya yanxu kika fara kukan nan ma "

ita kuwa mumy ranta babu dad'i tace "Gaskia mameen husna baki kyauta ba Kinsan yanda ibraheem yake da bakar xuciya kada yaje ya ji mata ciwo "

D'an murmishi mamee tayi kafin tace "ae ita taja gwara ya koya mata hankali "

Shi kuwa ibraheem part d'in hajia maamaa suka nufa suna shiga ya fara kok'arin kwance belt d'in jikin shi husna tayi wik'i wik'i da ido mai cecanta Yah Abdullah baya nan ya tafi skul yana da lecture di'n yamma har yanxu bai dawo ba, Kafin ta ankara taji saukar belt a bayan ta gantsare wa tayi tare da cewa
"wayyo Allah nah don Allah kayi hak'uri wlh na tuba na dai na "

Ko kula ta bai yi ba ya fara dukan ta da belt ganin yak'i dai na dukan ta duk da uban hak'uri da take bashi kuwa don haka ta shige jikin shi tare da rukunkume shi ganin yana samun jikin shi Idan ya kawo mata dukan yasa shi sa hannun shi da niyyar 6an6arota daga jikin shi amman ina ya kasa ta mak'ale shi sosai.

Cikin tsawa yace "cika ni dan uban ki nace "
Cikin shashshak'ar kuka tace "ka daina duka na kayi hak'uri baxan k'ara ba"

"baxan hak'ura ba har yanxu ban miki rabin dukan da nayi niyyar yi miki ba"
Hannu yasa ya fisgo ta da karfi ya wurgar da ita k'asa ae kuwa ta had'o da rigar jikin shi har ta dan yakushe shi a damtsen hannun shi, haka ya xage ya dunga dukan ta tun tana kuka har ta koma Shashshak'a kawai.

Wayyo aranar husna taci dukan da tun da mamee ta haife ta ba'a ta6a yi mata ba, ana haka Yah Abdullah ya shigo da gudu part d'in hajia maamaa don aunty khadijah ce ta kirawo shi awaya tana fad'a mishi da sauri ya warce belt d'in hannun ibraheem tare da watsa mishi wani kallo ya nufi kan husna da tayi matuk'ar gala6aita ya d'ago ta xuwa jikin shi, wani irin abu Yah ibraheem yaji ya daki xuciyar shi a dai dai lokacin hajia maamaa ta shigo falon tare da su Ilham dukkan su kuka suke sosai.

Cikin wani irin 6acin rai tare da tsantsar tsanar Yah ibraheem husna tace
"Ko ni ba jinin ka bane bai kamata kayi min wannan dukan ba na sani tun da nayi wayo ka tsane ni kullum cikin duka na kake da cin xalina kasani na tsane ka i really hate you Yah ibraheem "

Tana gama fad'in hka ta fice daga part d'in hajia maamaa da gudu tana kuka gaba d'aya en wajen mamaki ne ya kama su na abin da husna ta ce yarinya amman ta fad'i wad'annan maganganun lallai ibraheem ya kai ta mak'ura, Yah Abdullah ne ya mike tsaye ranshi a 6ace yana kallon ibraheem wanda ya daskare a tsaye (anya garin gyaran gira baxai rasa ido ba), Yah Abdullah kuwa cewa yayi
"ka ga abin da nake gudu kenan ka riga da ka gama cusa tsanar ka a xuciyar husna har takai da ta furta maka da bakin ta "
Yana gama fad'in hka ya fice daga falon kallon su Ilham yayi ya daka musu tsawa tare da cewa "ku Kuma uban me kuke kallo "
Da gudu kowacce ta fuce kada ya huce akan su bedroom d'in shi ya shige ya xube kan bed tare da dafe kan shi wani abu ne yake mishi yawo a cikin xuciyar shi dakyar bacci ya dauke shi.

Husna kuwa tana fita part d'in su ta shige tana kuka sosai kan kujera ta fad'a tana kukan a haka Yah Abdullah ya shigo ya rarrashe ta wani mugun xaxxa6i ne ya rufe ta nan da nan sai da mamee tayi mata allura tare da bata magani sannan ta gasa mata jikin ta, sai da husna tayi k'wanaki uku sannan ta warware ta cigaba da sabgogin gabanta.

Tun da ga ranar bata k'ara kula Inda Yah ibraheem yake ba balle har ta tsokane shi ya jibgi banxa, ta fita harkar shi k'wata k'wata.

Ana cikin hka ne su husna, Ilham, raudah da fadila suka kammala primary school, lokacin da result ya fito Yah Abdullah ya xa6a musu wata privet school mai kyau da tsada amman don mugunta irin ta Yah ibraheem haka ya shiga ya fita sai dai akai su bording school kuma dukka iyayen maxa suka amince da hakan don hka dad'i ya ishi ibraheem don yanxu baya samun cin xalin husna don ta fita harkar shi, yayin da 6angaren su husna, Ilham, raudah da Fadila, Yah Abdullah bai yi musu dad'i kuma basu da yanda xasu yi don hajia maamaa ce ta tilas ta su Abba don idan abu ya faru toh Indai ya fad'a wa hajia maamaa Shikenan ya xaunu.

Ranar da xa'a kai su school d'in da sassafe suka shirya angama had'a musu komai husna ta fito da gudu daga part d'in su xata je d'akin Yah Abdullah su yi sallama suka hadu a hanya cikin dariya ta ce
"Wow Yah Abdullah kayi kyau wlh "
Kallon jikin shi yayi yana murmishi yana sanye da yadin kufta bak'i abin ka da farar fata ba k'aramin haska shi yayi ba cikin murmishi yace
"ngde my cwt sister "
Ya cigaba da cewa "yanxu sai ina? "
Tana yamutsa fuska tace "xuwa xanyi mu yi sallama da kai don har an xuba kayan mu a mota "
Har yanxu da murmishi kan fuskar shi yace "ae ni xan kai ku"
Tsallen murna ta fara yi yana kallon ta yana mata dariya, a lokacin Ilham da raudah da fadila suka fito tare da sauran en gida an rako su Yah Abdullah yana xaune a seat d'in driver yayin da husna take xaune a front seat sai Fadila Ilham da raudah suke xaune a bayan motar bayan angama yi musu nasihohi sosae kan suyi abin da kai su ban da shiririta sannan kuma suka yi musu addu'ar sauka lafia, Yah Abdullah yayi wa mota key suka fara tafiya a dai dai bakin gate husna ta had'a ido da ibraheem yana xaune kan bike d'in shi rik'e da key di'n mashin a hannun shi daman sometimes yafi amfani da mashin akan mota wani shegen murmishin mugunta ya bita dashi hararar shi tayi tare da kau dakan ta da sauri daga barin kallon shi a xuciyar ta tana cewa ba dole kayi mana murmishin mugunta ba tun da ka tura mu bording mugu axxalimi kawai ta fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yah Abdullah yayi yana cewa
"ke dawa kike Murgud'a baki? "
Dan murmishi kawai tayi tare da cewa "ni da Yah ibraheem ne da yake min murmishin mugunta "
Dariya kawai su Yah Abdullah suka yi mata, cikin nutsuwa yake driving ya dau hanyar da xata kai su school d'in.........





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 5:40 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*






*written by*

*Aishat A muh'd*



*&*


*sumayya salees sadeeq*















_Assalamu Alaikum readers xaku ga kamar munyi page 30, numbers d'in muka gyara dafatan kun fahimce mu_





*Page 29-30*






Tun da ya d'auki hanyar abuja yake xubar da hawayen tashin hankali raba shi da husna ba k'aramin tashin hankali xai shiga ba saboda tsabar tsananin son da yake mata sai da xuciyar shi ta ginu da sonta sannan rana d'aya hajia maamaa ta wargaxa komai, duk yanda ya dad'e yana tsara xaman da Xasu yi husna hkan baxai yiwu ba duk hasashe ne.


Wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun Yah Abdullah tare da buga steering motar da hannun shi d'aya hajia maamaa ta gama dashi wlh ta raba shi da husna batayi musu adalci ba ko Kad'an, da hka ya k'arasa abuja yana shiga gidan shi yayi hon mai gadi ya bud'e sannan ya shiga tare da yin parking ya tsaya dakyar ya iya amsar gaisuwar da mai gadi yake mishi sannan ya shige.


Kan bed ya fad'a tare da runtse idanun shi ya cusa hannun shi cikin gashin kanshi yana yamutsa shi Mtsww yaja tsaki tare da cewa a fili

"amman hajia maamaa bata yi ba wlh ni mai xanyi da ilham yarinya sai shegen sanyin jiki kamar mara jini a jiki (ni kuwa na kalli sumy muka yi murmishi tare da cewa ji Yah Abdullah da wani irin xance kamar shima ba irin yanayin Ilham d'in ne dashi ba 🤣) haka dai ya dunga surutu shi kad'ai gaba d'aya ya rasa yanda xai iya amsar k'addarar auren Ilham, yayi try d'in number husna but switch off cillar da wayar yayi tare da lumshe idon shi.



Husna kuwa tana shiga part d'in su da gudu ta wuce mamee tana kuka sosai cikin tsananin mamaki mamee ta bita da kallo tana tunanin mai ya samu husna take kuka haka tashi tayi ta bi bayanta xuwa bedroom d'in ta.


Kuka sosai ta tarar tana yi tare da bubbuga pillow tana fad'in "why! why!! Maamaa mai Nayi miki kika raba ni da masoyina kuma Kinsan irin tsananin shakuwar da muka yi da junan mu nasan baxan ta6a samun mai sona irin Yah Abdullah ba "

Kuka sosai husna take har dasu majina ba k'aramin tausayi ta bawa mamee ba har sai da taji idanun ta Sun cicciko da hawayen tausayin husna da Abdullah lallai ba k'aramin son junan su suke ba sai dai aikin gama ya gama tun da nan da en k'wanaki xai auri ilham.


K'arasa wa tayi Inda husna ta ke kuka ta dafa mata kafad'ar ta da sauri husna ta juyo tare da goge hawayen fuskar ta ganin mamee ce yasa ta k'ak'alo murmishin yak'e tare da cewa

"Laaa mamee nah yaushe kika shigo? "
"tun kina kuka da sumbatun son Abdullah "

Kunya ce ta lullu6e husna ta sunkuyar da kanta hannu mamee tasa ta d'ago da fuskar husna tana ganin yanda hawaye suke fita daga idonta girgixa kai tayi tare da cewa

"husna ni mahaifiyar Kice fad'a min damuwar ki kada ki 6oye min don duk duniya baki da kamata "
Rungume mamee husna tayi tare da sake fashe wa da kuka mamee bata hanata kukan ba don idan ta samu tayi kukan sai ta fi jin sanyi a cikin xuciyar ta bubbuga bayanta kawai mamee take cikin shesshak'ar kuka husna tace

"mamee bansan yanda xanyi na cire son Yah Abdullah acikin xuciya ta ba Ina sonshi ina sonshi sosai mamee don Allah ki ban shawara? "

Cirota mamee tayi daga jikin ta sannan tace "kalle ni nan husna Idan shawara kike son na baki share hawayen ki sannan ki saurare ni "

Hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta mamee ta Mik'o mata tissue ta fyace hancin ta sannan ta nutsu tana sauraren abin da mamee xata ce mata kuma tayi alk'awarin duk abin da mamee tace xata yi aiki dashi don baxata gurguwar shawara ba.

"da farko husna ina son ki yarda da kaddara mai kyau da mara kyau sannan kisa wa xuciyar ki Allah ya riga ya rubuta Abdullah ba mijin auren ki bane, don hka ina son kisawa xuciyar ki nutsu wa ki kwantar da hankalin ki ki cire wata damuwa saboda kiyaye lafiar ki, sannan ki dage da addu'a sosai kan Allah ya cire miki son Abdullah ya baki miji na gari wanda xai soki fiye da Abdullah ma, ki dunga danne duk wani abu akan shi kada ki bari mutane su fuskanci kishi kike da er uwar ki ilham ki dunga kau da kai akan Abdullah ko dan ilham ma Kinsan sharrin xuciya da hud'ubar shaitan kada wata matsala ta kunnu a tsakanin ku Kaf yaran gidan nan kun fi shakuwa da Ilham idan aka d'auke Abdullah, ki fad'a wa Allah damuwar ki Insha Allah xai miki maganin duk wata damuwa da kike ciki, nima a matsayi na na mahaifiyar ki xan taya ki da addu'a sosai, ko Kad'an bana son Kina sa damuwa acikin xuciyar ki shima Abdullah kada ki sauya mishi ku cigaba da xumuncin ku kamar da kin ji koh? "


Cikin dashashshiyar murya husna tace "Naji mamee kuma Insha Allah xan yi kok'ari wajen cire damuwa sannan xan mik'a al'amari na ga Allah "

Cikin murmishi mamee tace "Allah yayi miki albarka "
"Ameeen mamee nah ngde wa Allah da ya bani ke a matsayin uwa "

Jan karan hancin husna mamee tayi suka tuntsire da dariya kuwa sannan suka cigaba da hira irin ta tsakanin uwa da er tah.
Ilham wadda take jingine jikin kofar bedroom d'in husna tana nata kukan duk tattauna war da su mamee da husna suka yi taji don taxo xata shiga d'akin taji ta jinjina wa mamee sosai da ta bawa husna shawara ta gari wannan itace uwa ta gari wani son husna da mugun tausayin ta ya kama ilham sosai da gudu ta fice daga part d'in ta nufi part d'in hajia maamaa cikin kuka ta fad'a kan hajia maamaa tare da cewa
"na rok'e ki maamaa don girman Allah ki janye wannan auren da xaki had'a ni da Yah Abdullah ki mayar dashi kan husna suna matuk'ar kaunar junan su "
Ture ta hajia maamaa tayi daga jikin ta tare da cewa "kada ki k'ara xuwa inda nake da wannan maganar na riga da na gama yanke hukunci na don hka fitar min daga d'aki"
Ta K'arasa fad'i cikin tsawa don hka da gudu ilham ta fice daga d'akin hajia maamaa ta shige d'akin su tana kuka sosai tayi kuka har kanta ya fara ciwo wani bacci ne yayi awon gaba da ita sai faman sauke ajiyar xuciya take.

To cikin en k'wanakin nan abubuwa sun yiwa Yah Abdullah xafi sosai yabi ya rame ya fita hayyacin shi ko abinci baya iya ci sosai ya dage da kai kukan shi ga Allah, yayin da husna ma ta dage da addu'a sosai kuma tana jin dad'in yanda xuciyar ta ta fara sabawa da rashin Yah Abdullah, Hka ma a 6angaren ilham itama addu'ar neman xa6in Allah take, da hka har ya rage sauran k'wanaki 10 bikin Yah Abdullah da Ilham su hajia maamaa sai shirye shiryen biki ake don har lefe ita ta had'a (Sumy ta ta6e baki tare da cewa ba dole tayi shirye shirye ba tun da ta raba masoya 🤣)

Iyaye ma sai nasu shirye shiryen suke amman ta 6angaren ango Abdullah da amarya ilham babu wani shiri don dukkan nin su acikin damuwa suke............



```Kuyi hak'uri da wannan page d'in daga yau baxa mu k'ara typing ba sai xuwa bayan sallah Insha Allah, dafatan xamu dage da ibada kada mu 6ata lokacin mu wajen karance karancen novel's da kalle kalle ko xaman hira mara amfani adage da karatun alqur'an da addu'o'i dasu salatin Annabi da istigifari don neman dace wa,Allah yasa mu dace da ganin lailatur qadr , wanda nayi wa laifi wanda na sani da wanda bansani ba ku yafe min,Allah ya kar6i ibadun mu yasa kar6a66iya ce Ameeen thumma Ameeen```


_masu lafia Allah ya k'ara muku lafiya marasa lafia na gida dana asibiti Allah ka basu lafia don alfarmar wannan watan mai albarka, mu kuma writers Allah ya k'ara mana basirah da Kaifin tunani wajen rubuta novel's masu ma'ana_




*Aishat A muh'd*


```&```


```sumayya salees sadeeq```
[3/10, 5:45 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃






*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq






_Assalamu Alaikum readers dafatan anyi sallah lafia, Allah ya kar6i ibadun mu, Allah ya maimaita mana, ina muku barka da sallah_❤😍






*Page 31-32*





Iyaye ma sai nasu shirye shiryen suke amman ta 6angaren ango Abdullah da amarya ilham babu wani shiri don dukkan nin su acikin damuwa suke tsantsa musamman yah Abdullah ma, yayin da husna ta Duk'ufa da addu'a kan Allah ya yaye mata son Yah Abdullah a cikin xuciyar ta kuma Alhmdllh yanxu xuciyar ta ta fara sabawa da rashin Yah Abdullah ta mai da hankalin ta kan karatun ta.


Sam ta fita daga sabgar hajia maamaa ta daina shiga part d'in ta tun lokacin da ta raba ta da abin k'aunar ta Yah Abdullah sai dai idan sun had'u ta gaida da ita ko jiran amsawar ta Bata jira tayi gaba, hkan ba k'aramin damun hajia maamaa yake ba sosai amman hkan da take yi baxai hana ta canja ra'ayin ta ba Idan ta gama fushin nata ta sakko.



Kamar yau misalin karfe 9 na safe husna ta fito cikin shirin tafiya skul tana sanye da wata gown d'in atampha kalar white and pink d'inkin yayi kyau kuma rigar ta amshe ta sosai tayi light make up a face d'in ta fuskar nan tayi fiyau da ita sai ta sanya mayafi black Hka bag and shoe din ta black ne sai wayar ta a hannun ta sai sauri take don tana da lecture di'n 10 na safe gashi malamin irin mai xafin nan ne, tana fito wa palo ta tarar da daddyn ta da mamee suna break fast a saman dinning table k'arasa wa wajen tayi tare da sallama daddy ya d'ago kai ya kalle ta murmishi ya saki ganin yanda take xum6ura baki hannu ya mik'a ya kama nata tare da xaunar da ita kusa da kujerar da yake xaune yace

"sweet baby nah what happened with u?

Cikin shagwa6a tace "dad ina alk'awari na?

Da sauri dad ya dafe goshi tare fad'in "ohhh my god my mamanah (da yake some times hka yake kiran ta) ae na cika alk'awarin na ki "
Ya K'arasa fad'i yana miko mata keys d'in mota, da sauri husna ta damk'e keys d'in tare da rungume daddy cikin tsananin murna tana fad'in

"thank u so much my sweet dad, Allah ya k'are min kai "

Ta jiyo cikin murna tana kallon mamee tace "mamee nah ki taya ni godia wajen dad ya siya min sabuwar mota "

"Yayi er gidan dadyn ta toh my dear an gode Allah ya k'ara bud'i "

Cikin wani salon kallo daddy yayi wa mamee tare da cewa "Ameeen doctor nah! "

Murmishi suka sakar wa junan su irin na tsofaffin masoyan nan masu matuk'ar k'aunar junan su yayin da husna ta yi murmishi tana girgixa kai kawai ita dai salon soyayyar iyayen ta tana matuk'ar birge ta tea ta had'a tare da xuba chips and egg sai er source d'in da ake don cin chips d'in tayi bismillah tare da fara yin breakfast d'in ta.


Cikin en mintuna ta gama yin breakfast d'in sannan tayi ma daddy da mamee sallama ta fita da sauri saboda ganin time ya ja, tana fito wa farfajiyar gidan ta ga su fadila da raudah suna jiran ta cikin tsananin farinciki ta K'arasa wajen tare da cewa " my sister's ku taya ni murna my cwt dad ya siya min sabuwar mota "

Da sauri suka ce "da gaske kike ?"

"ehhh wlh kuxo ku gani tana parking space "

Lokaci d'aya suka rungume husna tare da fad'in "wow my sis congrats fah "

Nan suka K'arasa wajen wow suka had'a baki wajen fad'i ganin wata hadaddiyar mota green colour ce sai shek'i take nan fah suka fara shafa motar tare da santin ta ganin had'uwar motar duk anan suka shantake har goma ta kusan yi nan suka ankare Kafin husna ta shiga maxaunin driver raudah tana gefen ta sai fadila a baya don ilham hajia maamaa ta dakatar da ita da xuwa skul sai bayan bikin.

Da gudu husna take driven saboda time ya kure da hka har suka K'arasa skul ta samu waje tayi parking sannan suka fito kai tsaye department d'in su suka nufa, cikin nutsuwa suka shiga cikin hall di'n d'aukar lecture di'n sai dai wani uxirin ya tsayar da husna wajen wasu friends d'in ta amman

Please Login or Register in order to submit comment