Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in daya dubata ya fara musu bayanin zuciyarta na barazanar kamuwa da heart attack, saboda tension d'in data samu kanta a ciki. Dadyn Husna na share zufar daya gangaro masa," to yanzu doctor ya zamuyi,"Abba ya tambaya? Abin yi shine kuyi kokarin sanin abinda ke damunta sai kuyi kokarin maganta mata shi, shine kwanciyar hankalin ta da kuma samun lpy ta.


Yah Ibrahim durkushe a kasan wajen, tunda yaji abinda ke damun Husna ya rasa sukuni yasan za'ai haka, dan baiyi treating Husna a yarda zata so shi ba, yasan akwai tsantsar k'iyayya da take masa, kuma a tunanin ta shima ya tsane ta, sai dai akwai akasin hakan a zuciyarsa. "Kiyi hakuri Husna, nakasance mai son kaina, banyi la'akari dahalin da zaki shiga ba, sai dai naki mai sauki ne akan ace na rabu dake Husna, nasan tarwatsewa zuciya ta zatayi.


Hajia maamaa ta rafka uban tagumi, bata da burin daya wuce ganin halin da Husna take ciki, gashi mazan gidan duk basa nan sun bi su hospital.


After few hours

A hankali idon Husna ya fara bud'ewa, bata jin komai a jikinta sai kanta da aka d'aure da bandage, cux ta samu taimakon gaggawa, idonta na bud'ewa ta k'are ma yan d'akin kallo, abinda ya fara d'axu ya dawo mata sabo, sallama su Ilham sukayi a room d'in, ganin su yasa Husna ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, da gudu suka nufeta suna kukan suma. Iyayen maza sunyi mutuwar tsaye, dan duk cikin su bbu wanda baiga rashin adalcin da hajia maamaa kema y'ayan su ba, sai dai mahaifiyarsu ce bbu yanda xasuyi da ita.


Hannun Ilham Husna ta rike gam a kirjinta, Ilham meyasa kuka kawo ni hospital, mai yasa ban mutu ba, bana son rayuwa Ilham, rayuwata bata da amfani, na rasa farin ciki har abada, nasan xan rayu cikin k'unci, Yah Ibrahim hajia maamaa ta aura mini, gaskia na yarda da zallar k'iyayyar da take mini,cigaba tayi da kuka.

Duk dauriya ta iyayen su sai da suka zubar da hawaye, Ibrahim kam kuka yake harda shesheka, yayi nadamar abinda yama Husna, gashi ya gefa rayuwarta a cikin tashin hankali .

Kokarin Mikewa Husna tayi Ilham ta taimaka mata ta tashi, "Ilham ina doctor?" Yana ciki Husna raudah ta bata amsa,ku ki rashi please inason ya mini allurar da xata kaini lahira kowa ya huta, sai a lokacin Abban Ibrahim ya matso kusa da Husna, cikin tattausar murya ya fara lallashin Husna akan ta yarda da kaddara,addu'oi ya bata ta ringa yi da yardar Allah xata ji sauki a ranta, sauran magana kuma sai sunje gida.


An sallame su an kuma bawa Husna treatment da magungunan da zata cigaba dasha, gaba d'aya suka rankaya sai gida.


Jigum jigum a kayi gidan biki ana jiran feed back na lapiar Husna, ganin motoci na shigowa gidan a jere yasa mamen Husna ta zauna dab'as a k'asa, dan tasan Husna ta rasu ganin fuskar Iyayen d'auke da damuwa. Hajia maamaa har tun tube take ta nufi tsakar gidan. Ganin fitowar Ilham tana rike da Husna a kafad'ar ta yasa jama'ar wajen hamdala, farin ciki ya bayyana a zuciyarsu, cikin sauri hajia maamaa ta nufi Husna tana murna da idanunta jajir. Husna na ganin haka tayi saurin barin jikin Ilham dan kar hajia maamma ta tab'ata, hakan ne yyi sanadiyayyar ta tafi luuuuuu zata fad'i, ji tayi an tareta ta fad'a kirjin mutun, jin kamshin turaren Yah Ibrahim yasa Husna ta saki wata razanan niyar k'ara ...............





Kuyi hakuri da wannan zakuji mu gobe insha Allah





Aishat A Muh'd


&


Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:57 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 51-52*




Cikin wani irin xafin nama Yah Abdullah da Yah ibraheem suka yi kan husna kowanne yana kok'arin d'aukan ta don bata agajin gaggawa, Yah Abdullah ya riga ibraheem xuwa inda husna take har ya kai hannun shi da niyyar d'aukan ta sai ji yayi Yah ibraheem yace

"stop it now Yah Abdullah "
Da sauri kuma cikin mamaki Yah Abdullah ya d'ago kanshi yana kallon k'anin shi kallo d'aya yayi wa ibraheem ya karanto tsantsar kishi a cikin idanun shi don hka sai ya matsa gefe ya fad'a tunanin daman ibraheem yana son husna kenan tun da gashi har ya nuna mishi kishi don xai d'auke ta kuma wannan kishin da ya karanto a fuskar ibraheem ya tabbatar sai ana yiwa mutum mugun so ake nuna kishin nan, daman ibraheem yana son husna to ina tsanar da yake mata, shi kad'ai dai Yah Abdullah yake wannan tunanin.

Yayin da ibraheem kuma ya tsugunna saitin kan husna ya sa hannun shi yana gyara mata gashin kanta da ya barbaxu har xuwa fuskar ta ya kura mata ido yana kallon ta kawai.

Ganin shi yak'i d'aukan ta ya d'ora ta kan bed don mamee ta duba ta kuma yak'i bari wani ya d'auke ta ya sata a gaba yana kallon ta kamar wanda bai ta6a ganin ta ba.

"Haba ibraheem d'ina me ka tsaya yi maxa ka d'ora ta kan gado Xahra ta dubata tun da ka k'i Abdullah ya d'auke ta "

Cikin nutsuwa yasa hannayen shi duk biyun ya d'auke ta sai da ya had'a ta da faffad'en kirjin shi sannan cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya k'arasa kan bed d'in hajia maamaa ya kwantar da ita a hankali ya sa pillow ya d'ora kanta sannan ya dad'a tattara gashin nata ya samu waje ya xauna kusa da ita a gefen gadon ya kamo hannun ta yana yana murxa tsakiyar tafin hannun nata.

Kowa ya xuba ido cikin matuk'ar mamaki ake kallon ibraheem yanda yake yiwa husna tsana da amman gashi har yana wani lalla6a ta (ni da sister sumy muka ce ae yanxu ma aka fara wannan so min ta6i ne).

Da hka kuma hajia maamaa tace kowa ya fita daga bedroom d'in nan en uwa suka fita gaba d'ayan su daga mamee sai ibraheem da hajia maamaa wadda take cikin tashin hankali lokaci xuwa lokaci tana share kwallar idon ta, cikin k'ware wa mamee ta duba husna sai Dr ibraheem ya xama d'an kallo kamar ba likita ba, nan mamee ta gama duba ta har tayi nasarar samun numfashin ta ya dawo dai dai sannan tayi mata allurar bacci daga K'arshe tayi mata dressing din ciwon da taji a goshin ta tana gama wa ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa tace

"zahra baki mana bayanin halin da take ciki ba xaki fita "
Dawowa cikin d'akin tayi cikin dauriya mamee tace "maamaa ba wani babban matsala ba ne suma tayi sai kuma ciwon da taji a goshin ta amman Insha Allah xuwa nan da yamma xata farka qlau "

"Alhamdullilah ngde wa Allah sai yanxu naji hankali na ya kwanta "

Cewar hajia maamaa ita kuwa mamee dafa kafad'ar ibraheem tayi tare da cewa " ibraheem ka ban kunya sai kace ba jarumin namiji ba kana ganin matar ka a wannan yanayin ka kasa duba ta duk ka wani firgice "

Murmishi yayi tare da sosa kai yace "ae ni mamee namance dani likita ne ma sai yanxu na tuna tsabar rud'ewa ni wlh har tsoron tashi nake tayi kada ta sake ji wa kanta ciwo mamee"

Ya K'arasa fad'i cikin yanayin sanyin murya cikin tausayin shi tace "kada ka damu ibraheem Idan ta farka xamu yi magana da ita kuma Insha Allah komai xai wuce amman sai kayi hak'uri"

"okay mamee Allah ya huce xuciyar ta Kafin ta tashi ma"

Er dariya mamee tayi kawai ta fice daga d'akin daman hajia maamaa ta shige toilet don rage cikin ta don ba k'aramin firgita da rud'ewar ciki ta samu ba sai yanxu tukunna ta samu nutsuwar rage cikin nata.


Ya kasa sakin hannun ta idanun shi ya xuba mata yana kallon ta cike da mamakin yanda husna ta koma wannan ba don yayi saurin fallasa abin da yake xuciyar shi ba da tuni dakon son da yake mata ya tashi a banxa ba lallai ya aure ta ba, don tun Kafin ya tafi England karatu ya sanar da hajia maamaa ta rik'e mishi husna ta kular mishi da ita don ita tashi ce shi yafi dace wa da ita fiye da kowanne namiji.

Yayi xurfi a tunani yaji muryar mumy akan shi da sauri ya dawo cikin hayyacin shi ya d'ago kai ya kalle ta harara ta watsa mishi tare da cewa "sai ka tashi ka bata waje tasha iska ka wani xo ka tsare ta da ido sai ka farkar da ita lokacin tashin ta bai yi ba "

"sorry mumy nah bari na tafi "
Ya fad'i hkan yana tashi tsaye bai gama mik'e wa ba sai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar husna ya sumbace ta a saman goshin ta kumatun ta da kuma saman tsakiyar le6en ta sannan a Hankali ya furta

"i luv u so much my dear husna Allah ya baki lafia "

Sannan ya K'arasa mik'e wa kallon mumy yayi yaga ta xuba mishi tana kallon shi d'an d'aga gira yayi yana cewa "mumy what wrong wannan kallon fah? "

"amman ibraheem baka da kunya a gaba na kake hka? "

Rungume ta yayi yana cewa "mumy idan banyi a gaban ki ba a ina xanyi "

"ina ruwan ki ba Matar shi ce ba ya biya sadaki an d'aura " Cewar hajja maamaa kenan bayan ta fito daga toilet d'in, girgixa kai kawai Mumy tayi Sam hajia maamaa bata ganin laifin ibraheem akan komai bayan shi ta ke bi wannan kaunace da kulawar da take bashi tun ran da aka haife shi.

"Ya kamata kaje ka yi wanka ka kwanta ka huta don nasan ka gaji"
Cewar hajia maamaa kenan tana xama kan bed d'in.

"Okay maamaa ki kular min da mata ta sosai "
Fad'in ibraheem yana kama hannun mumy "kada ka damu khaleelu na "fad'in hajia maamaa tana murmishi, daga hka suka fice daga d'akin.

Part d'in su suka tafi bayan ya shiga bedroom d'in shi wanka yayi tare da shirya wa cikin wani 3quater yellow da white d'in t-shirt mara hannu bayan ya fesa perfumes ne ya sha coffee d'in da mumy ta kawo mishi Sannan ya kure speed di'n AC ya kwanta kan katafaren gadon shi tuni ya lula tunanin husna yasan ba k'aramin fad'a xa'a sha da ita ba don shi kanshi yasan ta tsane shi kuma shine da kanshi yasa ta tsane shi din yasan yayi kuskure kuma xai gyara kuskuren da yayi Insha Allah, da hka bacci 6arawo ya d'auke shi daman kuma a gajiye yake sosai tun da ya diro nigeria bai huta ba sai yanxu.


Yamma nayi aka fara shirye shiryen kai amare gidajen su amman ban da husna wadda take kwance har yanxu tana bacci sakamakon allurar da akayi mata don hka Fadila da raudah basu samu damar yin sallama da husna ba aka mik'a su gidajen su sun sha kuka sosai abin gwanin ban tausayi, ana dawo wa daga kai su nan en uwa suka fara tafiya gidajen su na kusa kusa kenan xuwa mangarib gidan yayi shiru babu hayaniya sosai don an ragu da yawa sosai kuma part d'in saukar bak'in shi ne na K'arshe daga baya duk suna ciki suna huta gajiyar biki don an gaji kuwa.


Mumy ce a tsakiyar palo tana tsaye da wani madaidaicin cup a hannun ta tasa spoon tana juya wa sai ga ibraheem nan ya fito daga d'akin shi har ya sake wanka ya canja kaya xuwa black jeans nd T-shirt pink mai gajeran hannu kayan sun matuk'ar amsar jikin shi yana ta xuba k'amshi kan nan nashi yasha gyara da sajen nan sai kyalli yake yi murmishi ya saki wanda yake k'ara fito mishi da ainahin Kyan shi ya k'arasa wajen yana cewa

"mumy nah me xan samu I'm hungry wlh sai dai bana son abinci mae nauyi "

Ita ma mumy cikin murmishi ta ce "fad'i abin da kake so son, amman Kafin nan shanye wannan abin "

Ta k'arasa fad'i tana mik'a mishi cup d'in hannun ta kar6a yayi tare da kallon cikin cup d'in madara ce cike a cup d'in sai dai ta canja launi alamar an xuba wani abun bayan milk di'n kallon mumy yayi wadda daman can shi take kallo ya yatsina fuska tare da cewa
"Wannan mene mummy?"
"maganine son "
"me yasame ni kuma mumy ni lafia ta qlau Kinsan ban son irin wannan maganin gargajiyar"
D'an hararar shi mumy tayi tare da cewa "da yake xan baka abin da xai cutar da Kai ba "
"no mumy sorry xan sha "

Yana gama fad'in hka yasa cup d'in a baki ya fara sha maimakon yaji d'aci sai wani gardin madara ne da xak'in xuma ya baibaye cikin bakin shi sai d'an bauri Kad'an nan ya shanye shi tas sannan ya mik'a wa mumy cup d'in kar6a tayi tare da cewa "Yawwa ko kai fa son ga wani kuma"
Xaro ido yayi yana kallon hannun cup d'in mumy tare da dafa ciki yace "wash mumy ki bari sai anjima "
"A'a ibraheem yanxu xaka sha bashi da yawa ae kuma kankana ce da milk sai xuma"

Bashi da yanda xai yi hka ya kar6a ya fara sha yana mai jin kunyar mumy wato shi take gyara wa kenan kamar wata mace shi yasa yake alfahari da mumyn shi.

Yana cikin sha Abdullah ya shigo falon kallon ibraheem yayi tare da kallon cikin cup d'in hannun shi sai kuma ya kalli mumy yace "Mumy mene yake sha ni aka ware ni"

Murmishi mumy tayi tare da cewa "tambaye shi ga ka gashi magani ne yake sha "
Tana gama fad'in hka ta nufi kitchen, Yah Abdullah janyo ibraheem yayi kusa dashi a hankali yake cewa "kai malam me kake sha Hka babu ajiye wa d'an uwa?"

Murmishi ibraheem ya saki tare da cewa " hmm Yah Abdullah maganine mumy ta sani a gaba tana bani kamar wata mace "

Ya K'arasa fad'i yana Yatsina fuska dariya Yah Abdullah ya kwashe da ita Kafin kuma yace "kai malam mumy ta kyauta xaka yi mata godia sai nan gaba mybe ma ka dawo neman Kari tana gyara ka ne don kada mace ta rai na ka "

"koh? "
Cewar ibraheem yana ajiye cup d'in bayan ya gama sha.
"ofcourse yaro kuma xaka ce na fad'a maka, nima bari na bita kitchen na samu rabo na don gobe xan gudu abuja "

Har ya mik'e tsaye ibraheem ya janyo shi ya fad'a kan kujera yace "kai Yah Abdullah ka tausaya mata tana fama da tsohon ciki ka bari ta haihu mana "

Dariya suka tuntsire da ita lokaci d'aya tare da tafawa kamar wasu sa'annin juna cikin dariyar Yah Abdullah yace "ka kawo shawara kuwa ibraheem na hak'ura "

Xumbur kuma ibraheem ya mik'e tsaye tare da cewa "ohhh my god Yah Abdullah ka 6ata min time da surutun ka xanje duba jikin husna "

Yana gama fad'in hka bai jira abin da Yah Abdullah xai ce ba ya fita daga palon da sauri, girgixa kai Yah Abdullah kawai yayi sannan ya shige kitchen Inda mumy take had'a wa ibraheem abincin da xai ci.


Shi kuwa ibraheem yana fita ya nufi part d'in hajia maamaa, a dai dai time d'in husna ta farka firgigit da sauri ta dafe kanta jin yanda yake mata ciwo sosai kallon d'akin take cike da matuk'ar mamakin abin da ya kawo ta d'akin hajia maamaa a hankali kuma ta fara tunanin abin da yafaru ae kuwa tana gama tunanin ta dage ta k'walla wata uwar k'ara mai k'arfin gaske, nan fah aka fara riga rigan shiga d'akin tsakanin Yah ibraheem, hajia maamaa da ilham don su kad'ai ne a part d'in.
Ihu take tana cewa "abin da baxai ta6a yiwu ba kenan amman kuwa an cuce ni a rasa wa xa'a aura min sai Yah ibraheem wayyo Allah nah "

Tana gama fad'in hka kuma xumbur ta mik'e tsaye dai dai lokacin hajia maamaa, ilham da Yah ibraheem sun shigo cikin d'akin da sauri hajia maamaa ta nufi wajen ta tana kok'arin rik'e ta don ganin yanda take layi kamar wata er k'waya fincike jikin ta tayi da k'arfi tare da cewa
"kada ki k'ara rik'e ni na tsane ki kamar yanda kika tsane ni "

Sakin baki yah ibraheem yayi yana kallon husna bai yi wani yunkurin xuwa wajen ta ba, hajia maamaa ta kalla sannan ilham lokacin da ta kalli ilham sai da ilham taji d'an cikin ta ya juya cikin muryar tsiwa tace "Har da ke aka had'a baki wajen aura min mak'iyi na koh? "

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da Yah ibraheem ya furta a cikin xuciyar shi lokaci d'aya kan shi ya fara ciwo, ilham kuwa cikin sanyin murya tace "taya xa'a had'a baki da ni a cuce ki husna kuma maamaa da iyayen mu ba cutar ki suka yi ba gata suka yi miki kiyi hak'uri kiyi biyayya da xa6in su "

Wani harara ta watsa wa ilham tare da sakin wani murmishin takaici ta tafa hannayen ta sau uku tukunna tace " ke ma goyan bayan su kika yi ashe ke ma mak'iyiya tace lokacin da aka raba ni da Yah Abdullah na hak'ura na sake samun wani masoyin mai sona da gaskiya muna k'aunar junan mu aka raba mu to wannan auren shi ma hka xa'a raba shi "

Tana gama fad'in hka ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa tace "husna ina xaki je?"

Fad'in hka da tayi ta d'ago xata kalli hajia maamaa sai lokacin idanun ta suka sauka kan Dr ibraheem khaleel wanda sai had'a uban gumi yake najin furucin husna yasan yarinyar akwai ta da kafiyar tsiya Idan ta dage da abu.

Da har tayi niyyar taje ta rufe shi da duka ko ta samu sassauci cikin xuciyar ta sai kuma ta fice da gudu ta barsu kowanne jiki a sanyaye xuwa part d'in su tana shiga suka ci karo da mamee da sauri mamee ta rungume ta daman yanxu xata fito don ta duba ta sai gashi ta shigo ruwan wanka mai xafi ta had'a mata tayi wanka ta fito mata da Kayan bacci ta sanya sannan ta had'a mata tea tasha da d'an pepper soup din chicken tana gama sha kuma ta ba ta magungunan ta tasha bayan ta gama sha ta bud'e baki xatayi magana kenan mamee ta tsikara mata allurar bacci ae kuwa husna ta saki er k'ara ta jin xafi cikin en mintuna ta bacci yayi awon gaba da ita.

Tashi mamee tayi tsaye tana kallon husna cike da tausayin ta tana sani tayi mata allurar bacci don ta samu hutu a kanta Idan ba hka ba tashin hankali xa'a yi tayi a daren amman xuwa gobe da safe ta dan huce xata xauna su yi magana ta fahimta har ta samu damar lalla6a ta yarda da xa6in da aka yi mata.

Tana niyyar fita taga ibraheem jingine jikin kofar d'akin yana kallon husna idanun shi sunyi ja sosai, tuni tausayin shi ya kama mamee don tasan tabbas ibraheem yana son husna hannun shi ta kamo xuwa cikin palon cikin sanyin murya yace "mamee mene yasa kika yi mata allurar bacci da kin barta ta fad'i abin da take son fad'i an ta6a ta ne mamee da xan iya hak'ura da husna da na hak'ura da ita na rok'e ki mamee ki lalla6a min ita ina son ta bansan yawan son da nake yiwa husna ba mamee help me mamee please "

Cikin tsananin tausayin shi mamee tace "kada ka damu ibraheem ka cigaba da addu'a da kuma hak'uri "

"Insha Allah mamee ngde "
Da hka ta lalla6a shi ya tafi don dare yayi nan kan kujerar ta xauna tana tunanin abin da ya kamata tayi............





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:00 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*





*Page 53-54*




Cikin wannan daren mamee da ibraheem basu samu damar yin cikakken bacci ba shi ibraheem yana tunanin yanda husna xata farka xuwa gobe don yasan a gobe xa'a gama magana da yaga ya kasa bacci sai ya mik'e ya shiga toilet yayi alwala tare da yin nafilfilo yana addu'ar yasa husna ta amince da auren nashi.

Mamee kuwa tana tausayin husna tana kuma tausayin ibraheem ta rasa yanda xatayi wa xata goyi baya acikin su ta danne wa d'aya farincikin shi wad'annan tunanin shi ya hana ta samun cikakken bacci daga K'arshe ita ma alwala tayi ta fara kai kukan ta wajen mai dukka.



*WASHE GARI*


Husna bata farka ba sai wurin 9 na safe tana tashi wanka tayi agurguje tare da yin alwala ta fito bayan ta shirya cikin simple arabian gown milk colour bata yi wata k'walliya ba don bata da wannan time d'in bayan ta idar da sallah ne ta xauna tana addu'o'in ta tana neman xa6in Allah xuwa yanxu xuciyar ta ta fara d'an huce ma amman fah tana nan kan bakanta sai an warware wannan auren don baxa ta iya xama da mak'iyin ta ba.

Tana cikin hka mamee ta shigo d'akin hannun ta d'auke da cup d'in tea kallo d'aya husna tayi wa mamee ta d'auke kanta da sauri don ganin tarin damuwa a kan fuskar mamee gashi idanun ta sun yi ja sai jikin husna ya fara yin sanyi dak'yar ta iya gaida mamee saboda yanda bakin ta yayi mata nauyi.


Mik'a mata cup d'in tea d'in tayi cikin sanyin jiki husna tasa hannu ta kar6a ta fara sha sai da ta shanye sannan mamee ta juya xata tafi cikin sauri husna ta damk'e kafafun ta cikin muryar kuka tace

"mamee nah nasan nayi miki laifi kiyi hak'uri don Allah Idan kika juya min baya ke ma ina xan sanya raina naji dad'i "

Dawo wa mamee tayi ta xauna sannan ta rik'o hannun husna tace "baxan iya juya miki baya ba husna abin ne yafi K'arfi na kin bani mamaki sosai ace a matsayin ki na mace baxa ki yiwa iyayen ki biyayya ba xaki na ta surutai kamar wata mai ta6in hankali, Kinsan kuma ni xakisa cikin damuwa sai a ga kamar ni nake xiga ki "

Tun da mamee ta fara magana husna ta fara kuka cikin tausayin 'yar ta ta take kallon ta Idan ba hka tayi wa husna ba xata janyo matsala sosai shi yasa take mata hka.

"mamee ya kike so nayi don Allah ki fad'a min xa6in ki ni kuwa Insha Allah xanyi miki biyayya iyakar iyawa ta bana son ganin ki cikin damuwa "

Ajiyar xuciya mamee ta saki tare da yin hamdala bata ta6a xaton husna xata bata had'in kai ta farat d'aya ba don hka tace

"ni kawai ra'ayi na kiyi biyayya da abin da aka xa6a miki "

Share hawayen fuskar ta tayi tare da cewa "naji mamee kuma na amince "

Tana k'arasa fad'i kuma ta sake fashe wa da kuka cikin tsananin tausayin ta mamee ta rungume ta tana cewa "Alhmdllh Naji dad'in abin da kika ce husna Allah yayi miki albarka hak'ik'a yau kin faranta min fiye da koyaushe "

Nan ta cigaba da rarrashin ta da yi mata nasiha ana cikin hka aunty rufaidah da Yah yaseer suka shigo nan suma suka d'ora da rarrashin nata.

Husna kuwa ba don komai ta amince ba sai bata son ganin mameen ta cikin damuwa kuma har yanxu tana cike da hajia maamaa.

Amincewar husna shi ya kwantar da hankalin en gidan amman ibraheem kawai yaji hkan ne amman yasan ba xaman jin dad'i xasu yi ba amman duk da hka ya ji dad'in amincewar ta ta.

Aranar Yah Abdullah da Ilham suka wuce abuja bayan sun shirya da husna don kuwa share ta take yi tun maganar da tayi jiya da dare sai da ta lalla6a ta suka

Please Login or Register in order to submit comment