Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gaida ita sannan ta fice hajia maamaa ta bita da kallo jikin ta a sanyaye ganin har yanxu husna bata huce ba.

Yinin nan husna tayi shi cikin jin dad'i har xuwa lokacin da Yah ibraheem yaxo suka tafi gida mamee ta k'ara yi mata nasiha sosae, bayan sun isa gida husna kwanciyar ta tayi a cikin d'aki don baxa tayi girki ba Mumy ta basu sun taho da dinner d'in dare wai don duk kada husna ta wahala tana masifar son husna sosai ba k'aramin dad'i taji ba lokacin da hajia maamaa ta had'a auren.

Washe gari bayan husna ta dawo daga skul ta yi girki ta gama ta gyara ko'ina sai ta fito xuwa wurin garden, swimming pool ta hango a gefen ta sai taji tana sha'awar shiga ciki don hka ta K'arasa wajen ta fara cire kayan jikin ta sai ta bar half vest d'in jikin ta bak'a sai wani wando iyakar cinyar ta ya tsaya shima baki ta tattara gashin kanta ta d'aure sannan ta fad'a cikin swimming pool din.

Yah ibraheem yana xaune saman baranda yana amfani da system din shi yaji k'arar abu ya fad'a ruwa cikin sauri ya d'ago kanshi ya hango husna cikin swimming pool sai iyo take cikin nishad'i wani murmishi ya saki sai da ya kalle ta son ran shi sannan ya tuna wani abu wani murmishin mugunta ya saki ya shige cikin bedroom d'in shi cikin second 10 ya fito daga dakin hannun shi rik'e da wani remot xama yayi a kan kujera sannan ya danna remot din yana dariyar mugunta.

Husna wadda tayi nisa da yin iyo a cikin ruwan xuciyar ta cike da nishad'i sai ta hango wani abu daga nesa yana nufo inda take cikin tsoro ta k'ara kallon abun sai ta ga kamar irin kifin nan ne shark Wanda ake nuna wa a cikin film mai cinye mutum ta hango ya nufo ta gadan gadan tuni cikin husna ya kad'a tsabar tsorata batasan lokacin da ta saki fitsari ba tuni ta fara neman hanyar fita daga swimming pool din amman ina babu hanya wannan shark din ya tsare hanya................




Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:12 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




_sadaukar wa ne gare ku en group d'in *Aunty & sadeey novels grp and Sumynbash novels* mun gode da yanda kuke k'aunar littafin nan sosai Allah ya bar xumunci, Aishat & sumy suna muku fatan alkhairi_🤝😍



*Page 59-60*



Gaba d'aya husna ta kid'ime ta gigice ta rasa yanda xatayi gashi sai kallon ta yake yana bud'e baki kuma ya tsaya cak waje d'aya bai yi kanta ba, husna jikin ta sai rawa yake ta tsorata iya tsorata har wani gumi ne yake tsatstsafo mata na tashin hankali.
Yah ibraheem da yake xaune yana kallon Inda take dariyar mugunta sosai yake har da hawaye shark din nan na roba ne ya siyo shi saboda ra'ayin kan shi ya ajiye shi cikin swimming pool din,hannun shi yasa ya d'auko remot din da ya ajiye ya sake danna wani wajen tuni wannan shark din nan ya sake yin kan husna gadan gadan ganin hka yasa husna k'walla wata uwar k'ara tare da cewa
"wayyo Allah nah somebody help me "
"Yah ibraheem ka taimaka min wayyo Allah Yah ibraheem help me please "
Husna ta dunga kiran yah ibraheem da iyakacin k'arfin muryar ta, cak Yah ibraheem ya tsaya da dariyar da yake ganin yanda husna take kiran sunan shi tana neman taimako xumbur ya mik'e tsaye don ganin yanda ta fara fita hayyacin ta da wani irin xafin nama ya fara gudu ya sauka k'asa ya nufi wajen swimming pool d'in wani tsalle yayi tare da fad'awa cikin ruwan amman Kafin ya K'arasa wurin husna tuni tayi k'asan ruwan.

Cikin sauri ya nutse cikin ruwan ya d'auko ta tare da fito wa daga wurin ya ajiye ta a k'asa hannun shi yasa ya fara danna cikin ta a hankali ruwan da tasha ya fara fito wa sannan ya rufe mata hanci ya kai bakin shi dai dai nata da niyyar hura mata iska cikin bakin sai gashi ta farka tana tari sosai ruwa na fita ta bakin ta gaba d'aya har yanxu a firgice take.

Hannun shi yasa ya janyo ta jikin shi ya rungume tsam yana shafa mata baya a hankali kuma Yah ibraheem ya fara canja salo nan ya fara shafa gashin kan ta wanda ya jik'e da ruwa xuwa jikin ta yana wani lumshe ido jiyo da kanta yayi ya had'a bakin shi da nata ya fara yi tsotsa cikin buk'atu wa gaba d'aya ya fara fita a hayyacin shi jikin shi har wani rawa yake ya wani matse ta sosai a jikin shi kamar xai mayar da ita jikin shi yayi nisa sosai da abin da yake duk jikin shi ya saki.

Husna wadda ta dawo hayyacin ta ta jita a jikin Yah ibraheem yana kissing d'in ta son ran shi tuni ranta ya 6aci cikin fusata ta ture shi daga jikin ta da sauri ya k'ara sa hannu ya rik'o ta ganin hka yasa husna ta daddage iyakar k'arfin ta ta tunkud'a ibraheem xuwa cikin swimming pool din nan sannan ta juya ta tafi cikin gidan hankalin ta kwance bedroom d'in ta wuce ta cire kayan jikin ta toilet ta shige don yin wanka.


Lokacin da husna ta tura ibraheem cikin swimming pool din da ido ya bita har ta 6ace wa ganin shi fito wa yayi ya kwanta akan kujerar hutawa yana faman sauke ajiyar xuciya a yau gaskia ya kai matakin da baxai iya jure wa ba dole ya san abin yi tashi yayi shima ya shige xuwa bedroom d'in shi don ganin mangarib ta gabato gaba d'aya jikin shi a sanyaye yake ba k'arfi a hka ya wuce masallaci.

Bayan ta fito daga wanka tayi sallahr mangarib tana xaune tana addu'o'in ta har aka kirawo sallahr isha'e tayi sannan ta shirya cikin wata riga dark purple ce iyakar ta gwiwar ta hannun rigar d'an siriri ne ta saki gashin kanta bayan ta busar dashi da hand dryer tukunna ta gyara shi perfumes ta fesa masu sanyin k'amshi sannan ta fito falo wurin dinning table ta nufa abincin da ta dafa ta d'ebo tana ci a nutsu idanun ta kuma suna kan plasma TV tana kallon film d'in Harry Potter order of the Phoenix a mbc Max, hankalin yana kan kkallon gaba d'aya har Yah ibraheem ya dawo daga masallaci ya gama k'are mata kallo tsab sannan ya wuce d'akin shi wanka yayi sannan ya sanya wani 3quater fari sol da vest fara ya fesa perfumes tukunna ya fito xuwa falo kai tsaye wajen da husna take ya nufa don yau xuciyar a dake take hakk'in shi yake nema kawai ya gaji da halin da yake ciki, husna bata ankara ba taji an d'auke ta cak wata k'ara ta saki ta tsorata amman Yah ibraheem bai kula ta yayi bedroom d'in shi da ita husna sai bugun kirjin shi take da hannun ta tana cewa
"malam wai lafiar ka qlau ne xaka xo ka d'auke ni ina cin abinci bana ce kada ka k'ara ta6a ni ba "
sai da ya shiga d'akin sannan ya sauke ta cikin wani yanayi ibraheem yace
"husna na gaji da wannan abin da kike min ya kamata a yanxu ace mun shirya tsakanin junan mu "
tsugunna wa yayi a gaban ta ya sauke gwiwowin shi a k'asa cikin sanyin murya yace
"Don Allah husna kiyi hak'uri ki mance da abin da ya dad'e da wuce wa ki bani had'in kai mu gina sabuwar rayuwar da iyayen mu xasu yi alfahari damu "

Harara ta xabga mishi sannan tace " wannan kuma kai ya shafa ba ni ba "
Ta k'arasa fad'i tana jan tsaki tare da fita daga d'akin ta wuce nata sai faman jan tsaki take.

A wannan lokacin hakurin ibraheem ya gama k'are wa husna kawai yake da buk'ata wata muguwar sha'awa yake ji fiye da ko yaushe don hka kawai sai ya shige d'akin husna wadda fitowar ta daga wanka kenan tana d'aure da towel fari sol dashi iyakar shi cinyar ta, yana shiga ya mayar da kofar ya rufe ta har da sanya key ya nufi inda husna take tsaye ta saki baki tana kallon ikon Allah ganin ya shigo mata d'aki kai tsaye har da sanya key.

Nan husna ta fara ja da baya ganin yanda yake taho wa Xuwa inda take idanun shi sun yi ja sosai cikin tsiwa ta fara cewa "wai kai wanne irin mutum ne ka fa tak'ura min xan...... "
Bata K'arasa fad'i ba taji tayi baya ta fad'a kan gado ganin wurin ta yake taho wa har yanxu yasa ta fara tsorata da yanayin ibraheem yanda ta fad'a kan gadon hka ibraheem ya bita ya janyo ta jikin shi da k'arfi ya had'a ta da faffad'en kirjin shi gaba d'aya husna ta gama tsorata gashi sai mutsu mutsu take amman ta kasa Kwatar kanta.............


_kuyi hak'uri da wannan page d'in sai gobe Insha Allah_


Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:15 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




_muna matuk'ar alfahari daku *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM AND PURE MOMENT OF WRITER'S* hak'ik'a kune abin alfaharin mu wannan shafin sadaukarwa ce gare ku Allah ya k'ara mana basirah da kaifin tunani wajen rubuta novel's masu ma'ana, Muna muku fatan alkhairi_🤝😍




*PAGE 61-62*



Gaba d'aya husna ta gama tsorata dashi sai mutsu mutsu take amman ta kasa Kwatar kanta ya riga da ya had'e ta da faffad'en kirjin shi bud'e baki tayi xata yi ihu caraf ya cafke bakin nata da nashi ya fara kissing d'in ta cikin k'ware wa lokaci d'aya ya fita a hayyacin shi yayin da husna kuma take kuka wiwi na bak'in ciki da takaicin abin da Yah ibraheem yake yi mata.

Tana kuka tana bugun shi da hannayen ta amman ina ko a jikin shi don duk abin da xata yi mishi xai jure ko don ya cimma burin shi ya gaji da xuba mata ido, a cikin wannan daren mai dumbin tarihi da mahimmanci wajen Yah ibraheem ya mayar da husnar shi cikakkiyar Matar shi ya tsinci kanshi a wata sabuwar duniyar ta daban wadda bai ta6a tsammanin akwai irin ta ba sai yanxu, wani sabon son husna nane yake dad'a ratsa kowanne sassan jikin shi yayin da husna tasha kuka sosai duk idanun ta ya kumbura yayi ja saboda tsabar kukan axaba don ba k'aramin wahalar da ita ibraheem yayi wata irin sabon tsanar shi ta sake ji.

Wanka ya shiga yayi tare da yi alwalar sallahr asuba sai da yayi raka'atul fijir sannan ya nufi masallacin dake jikin gidan shi wanda had'e yake da gidan bayan sun idar da sallahr ne ya dawo gida d'akin husna ya shiga ya ga ko tayi sallah shashshak'ar kukan ta ne ya fara dukan kunnen shi cikin sauri ya K'arasa kusa da bed d'in ya kawo hannu xai ta6a ta da sauri tasa d'ayan hannun ta wadda dak'yar ta iya d'aga shi ta buge hannun nashi tare da watsa mishi harara da kumburarrun idanun ta.

Murmushi ya saki tare da cewa "kin min ixini na taimaka miki habibty ?"
Ko kallon Inda yake bata yi ba K'arshe ma juya kanta tayi ga wani irin axaba da take ji ajikin ta dan motsi tayi aikuwa ta saki k'ara saboda xafin da take ji ajikin ta.

Hankalin Yah ibraheem a tashe yace "baby nah me ya faru, ko sai na duba ki? "
Shiru tayi mishi tana cigaba da kukan ta ganin hka yasa shi sa hannu ya rik'o blanket din da ta rufe jikin ta da niyyar ya duba ta ko taji ciwo a jikin ta ae kuwa husna ta dunga yi mishi ihu don bata da k'arfin tashi sai ihu bakin ne bai mutu ba.

Sakin blanket din yayi tare da rufe kunnen shi dukka biyun da hannun shi saboda k'arar ihun da take mishi da sauri ya fice daga d'akin ya rasa yanda xai yi tunanin wanda xai kirawo ya duba ta yake don a yanayin da ya fahimce ta taji ciwo a jikin ta gashi tak'i yarda ya duba ta tunanin shine ya tsaya cak akan mamee ita kad'ai ce xata iya duba ta ba tare da anyi tashin hankali da husna ba don hka agogo ya kalla yaga 7:30 na safe da sauri ya janyo wayar shi ya lalubo number d'in mamee bugu biyu ana uku ta d'auki wayar a tsorace tace
"ibraheem lafia? "
D'an sosa k'eya yayi tare da cewa " am uhm mamee daman husna ce bata da lafia so tak'i tsaya wa na duba mamee kixo yanxu don Allah please "
"Haba ibraheem idan tak'i tsayawa ka duba ka kyale ta ciwon bai dame ta ba ne"
Marairaicewa yayi yana cewa "please mamee don Allah ki xo"
D'an shiru tayi tana tunani Kafin tace "Okay ina xuwa "
Cikin tsananin jin dad'in xata xo yace "mamee thank u so much Allah ya kawo ki lafia "
"Ameeen "

Ajiyar xuciya ya saki bayan ya kashe wayar sannan ya fito ya nufi d'akin husna a hankali ya lek'a yaga har yanxu tana kwance kuka take yi sosai wani irin tausayin ta ne ya kama shi.

Shi kanshi yasan bai saurara mata bai yi mata a hankali ba saboda bata bashi had'in kai ba, yana nan tsaye yaji an danna door bell da sauri ya nufi palo ya bud'e kofar had'a ido suka yi da mamee wata irin kunya ce ta lullu6e shi tun Kafin mameen tasan 6arnar da yayi bayan ta shigo falon tace
"tana ina ibraheem? "
"mamee tana bedroom d'in ta "
"Okay mu je toh"
Tana gaba yana bin ta a baya har suka shiga bedroom d'in husna kukan tane ya fara yiwa mamee sallama kallo d'aya tayi wa bedroom d'in tasan abin da ya faru don ko ina a hargitse ga sleeping dress din husna a k'asa da na ibraheem wata kunya ce ta kama mamee amman ta dake ta k'arasa kusa da bed d'in da husna take kwance ko hannun ta bata iya d'aga wa.

Da sauri ibraheem ya tsugunna yana kwashe kayan baccin don sai yanxu ya ankara da ya mance bai kwashe su ba, juyo wa mamee tayi xata yi mishi magana ta ga abin da yake kwashe wa da sauri yayi baya da kayan yana sunsunkuyar da kai irin na mai jin kunyar nan abin sai ya bawa mamee dariya har sai da ta d'an murmursa Kafin ta ankara har ya fita daga bedroom d'in da sauri hannun nashi na rik'e da kayan.

Dawo da hankalin ta mamee tayi kan husna sannan tace "sannu husna wannan kukan yayi yawa xai iya janyo miki wata matsala "
Cikin kukan axaba mai had'e da bak'in ciki da takaici tace "Haba mamee ya xan yi shiru kin ga muguntar da yayi min kuwa ji nake kamar xan mutu mamee ga kuma......... "

"shiiiii calm down husna kowacce mace daman hka yake kasance wa da ita don hka ni kam yau ina cikin farinciki kuma ina alfahari da ke husna Allah yayi miki albarka "

"Ameeen mamee amma...... "
"husna nace kiyi shiru Bari na duba ki "

Duba husna ta fara anan ta tabbatar da ba da had'in kanta ibraheem yayi mata ba don taji ciwo fita tayi ta kirawo ibraheem tana fad'a mishi sai tayi mata d'inki a wurin cikin xaro ido yace
"ohhh my god mamee don Allah ki bata hak'uri ba da sani nane ba"
"ni abin da na tambaye ka xaka ba ni sauri nake "
cikin sanyin jiki ya shige bedroom d'in en mintuna Kad'an ya dawo da kayan d'inki da allurar da xa'a yi mata bayan mamee ta kar6a sannan tace "kaje ka siyo magungunan da xata sha "
"Okay mamee thank u "
D'an hararar shi mamee tayi tukunna tace "mene na godia kuma "
D'an sosa kai yayi yana murmishi mamee ma murmishin tayi sannan ya fice ita kuma ta Koma d'akin husna dak'yar da sid'in goshi husna ta tsaya mamee ta yi mata d'inki ae kuwa tasha kukan axaba har wani shidewa take sosai mamee ta tausaya mata.

Bayan ta gama yi mata ta ne Yah ibraheem ya shigo d'akin da ledar magungunan a hannun shi kallon husna yake kamar shi ma xai yi kukan hka yake ji kar6ar ledar mamee tayi sannan tace "ibraheem had'o mata tea cikin cup "
"Okay mamee "
Ya fad'i yana yin gaba don ya gaji da kallon hararar da husna take yi mishi, nan mamee ta taimaka mata tayi wanka ta gasa jikin ta sai lokacin taji dad'in jikin ta sannan ta gabatar da sallahr asuba a lokacin mamee ce ta gyara mata d'akin tsab ta fesa air freshener masu k'amshi sosai.

Lokacin da ibraheem ya shiga kitchen ya rasa ta inda xai fara dafa tea don shi bai ta6a shiga kitchen da sunan girki ba kunna gas yayi ya d'ora butar dafa tea sannan ya xuba ruwa aciki shiru yayi yana dan tunanin sai me can kuma yace "yes na tuna sai sugar da lipton "
cikin tsananin murna ya xuba sugar mai uban yawa tare da xuba lipton guda biyar sannan ya rufe cikin en mintuna ta tafasa ya d'auko rariya da cup ya fara tacewa garin tacewar tafashshen ruwan xafin ya tsallo mishi tuni ya saki tukunyar k'asa ya fara dan tsalle yana rik'e hannun da ruwan xafin ya tsallo mishi tuni wajen yayi ja sosai abin ka da farar fata, Allah ya taimake shi ya cika cup d'in sannan ragowar ya xube bai bi takan tea d'in da ya xube a k'asan tiles di'n kitchen d'in ba ya d'auki cup d'in ya fita daga kitchen d'in.

A dinning table ya tsaya ya had'a tea d'in sannan ya nufi d'akin husna ko firfita wa bai tsaya yi ba saboda tsabar sauri, yana shiga ya tarar har husna tayi gayun ta cikin wata er riga mara nauyi doguwa ce amman bata K'arasa har k'asa ba mamee ta tubke mata gashin ta da kallaba d'aya jelar gashin har ta sakko kafad'ar ta ba k'aramin kyau tayi mishi ba kamar ya lashe ta haka yake ji ido ya xuba mata yana kallon ta sam ya mance da mamee a wajen sai da tayi mishi magana ya bata tea d'in sannan ya dawo hayyacin shi yana shafa kai cikin kunya.


Mamee ce ta mik'a wa husna cup d'in tea d'in da sauri husna ta kar6a saboda wata mahaukaciyar yunwa da take ji bata tsaya duba wa ba ko da xafi ta kafa kanta tare da sa bakin ta jikin cup d'in dan kur6a tayi da sauri ta feso shayin daga cikin bakin ta...........





Aishat A muh'd


*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:26 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*
*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*





*PAGE 63-64*




D'an kur6ar tea d'in tayi da sauri ta feso shayin daga cikin bakin ta saboda wani xafi ga wani uban xak'in sugar na fitar hankali da taji ya ratsa cikin bakin ta da sauri Yah ibraheem ya nufi wajen ta amman wata harara da ta aika mishi shi yasa shi tsayawa yayin da mamee ta k'arasa wajen ta tana cewa
" Ya akayi husna tea d'in da xafi?"
Cikin 6acin rai husna tace "mamee ba gwara xafi ba da wannan uban xak'in sugar kamar so ake a kashe mutum "
"ke bana son shirme bari na kawo miki wani"
Cewar mamee tana fita daga d'akin yayin da ta bar husna da Yah ibraheem sai kallon ta yake kamar ya lashe ta yayin da husna kuma bak'in cikin abin da ibraheem yayi mata fal cikin xuciyar ta lokaci xuwa lokaci tana share k'wallar takaici can kuma a fusace tace
"malam ka fitar min daga d'aki bana k'aunar ganin ka "

Wani murmishi mai ciwo ibraheem yayi Sam baya son yaji husna tana furta irin kalaman nan cikin sigar lallashi da lalla6a wa Yah ibraheem yace
"husna kiyi hak'uri da abin da nayi miki gaba d'aya ba'a cikin hayyaci na hkan ta faru ba amman next time xan........."

"next time d'in uban me tabbb kada ma ka k'ara gigin maimaita abin da kayi Idan ba hka ba uhm"
Husna ta katse Yah ibraheem cikin tsawa.

"but why husna da xaki ce hkan, Kinsan hakk'i nane koh? "

Cikin tsiwa ta bud'e baki xatayi magana kenan mamee ta shigo d'akin tsit tayi kamar ba ita ba shi kuwa Yah ibraheem fita yayi daga bedroom d'in yana tunanin wacce irin xuciya ce da husna da tak'i hak'ura akan abin da wuce.

Sai da mamee ta tabbatar tasha tea d'in sannan tasha maganin nata tukunna ta bata shawarwarin da xata kula da kanta yanda wurin xai yi saurin warke wa sannan ta tafi gida.


Lokacin da mamee ta k'arasa gida tana parking taga mumy ta fito daga part d'in hajia maamaa k'arasa wa tayi suka gaisa sannan tace
"mameen husna yau fitar sassafe kika yi hala daga asibiti aka kirawo ki? "

"uhm daga gidan ibraheem nake wlh "
Cewar mamee cikin sauri mumy tace "lafia me yafaru? "

D'an murmishi mamee tayi kafin tace "husna ce bata jin dad'i ne? "

"kaji shirme maimakon ya duba ta sai ya taso ki da sassafen nan "

"ae mumyn Abdullah d'an nawa 6arna yayi shi yasa gashi Kinsan halin 'yar taki da rigima take " fad'in mamee tana murmishi tuni ita ma mumy fuskar ta ta fad'ad'a da fara'a sosai kafin tace "hala bai wahalar min da d'iya ba ko dai Bari yanxu na shirya naje na duba ta don nasan bakin ku d'aya baxa ku fad'a min gasky ba "

Tana gama fad'in hka ta wuce da sauri Xuwa part d'in ta yayin da mamee tayi er dariya sannan ta wuce 6angaren ta ita ma.


Cikin sauri mumy ta shiga kitchen tare da taimakon er aikin ta suka shirya abinci mai rai da lafia har da yi wa husna ferfeso na musamman bayan ta gama komai an shirya cikin foodflaks an kai cikin mota ta shiga toilet tayi wanka ta shirya sannan ta fito xuwa part d'in hajia maamaa tana ce mata xata je duban husna bata da lafia.

Cikin tashin hankali hajia maamaa tace "me ya same ta? "
Cikin kunya mumy ta sanar da ita ae kuwa hajia maamaa cikin murmishi tace "bari na dauko hijab d'ina mu tafi ae wannan dubiyar tawa ce "

Bedroom ta shiga ta sanya hijab sannan suka fito xasu tafi a farfajiyar gidan suka had'u da mamee ta fito xata tafi hospital nan suka yi sallama kowanne ya kama gaban shi.

Husna kuwa bayan tafiyar mamee wani nauyayyen bacci ne yayi awon gaba da ita wanda bata samu damar yin shi ba daren jiya sai yanxu, ta 6angaren Yah ibraheem ma baccin ne yayi awon gaba da shi can cikin bacci yaji ana danna door bell dan tsaki yaja tare da cewa
"ko wane xai xo ya dame ni ina bacci na Mtsww "

Haka ya tashi ya fito xuwa falo daga shi sai 3quater da vest a jikin shi yasa hannun yana gyara gashin kanshi da ya hargitse bud'e kofar yayi suka had'a ido dasu mumy da hajia maamaa cikin mamaki da xaro ido yace

"Mumy hajia maamaa lafia? "
Harara mumy tayi mishi tare da cewa "kasan abin da ka aikata ae ni d'iya ta naxo duba wa "
Tana gama fad'in hka ta shige bedroom d'in husna yayin da hajia maamaa tace

"ka ta6o er lelen mumyn ka yau mu je na ga jikin nata ka had'u da mata uwar raki gashi kuma Allah ya bata jarumin namiji"

"Kaiii hajia maamaa ae husna jaruma ce ita ma "

Kama baki tayi kafin tace "au hka xaka ce "
Cikin dariya yace "ehhh mana "
Ita ma dariyar tayi da hka suka

Please Login or Register in order to submit comment