Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba department d'in su d'aya ba sai su raudah suka riga ta gaba kusan lokaci d'aya suka shiga cikin hall di'n tare da malamin nan ba tare da 6ata lokaci ba ya fara yi musu lecturing akan darasin da yake koyar wa gaba d'aya d'alibai sun nutsu suna sauraren shi saboda tsabar kwarjinin shi da tsoran shi da suke ji.

Husna ta d'auki tsayin 15 mint tana hira da friends d'in nan nata Kafin ta nufi hall di'n nasu cikin tafiyar ta ta kasaita.

Yana cikin xuba musu lecturing da tsaftaccecen turancin shi ajin yayi tsit suna sauraren shi kwas kwas k'arar takalmin husna da yaji yasa shi jiyo wa da sauri don ganin wane, ko kallon Inda yake husna bata yi ba ta samu waje xata xauna kenan taji saukan amon muryar shi yana cewa

"hey ke wace da xan kafa doka ki taka min? "
Cikin wani salo husna ta jiyo tare da d'aga kanta ta kalle shi ta xuba mishi mayatattun idanun ta masu matuk'ar d'aukan hankalin duk wani d'a namiji mai lafiya, dummm lokaci d'aya yaji xuciyar shi ta buga da karfin gaske tare da shiga wani yanayi a cikin jikin shi yana tasbihi acikin xuciyar shi don ganin wannan kyau na husna da Allah ya bata, muryar tace ta katse shi tare da dawo wa cikin hayyacin shi yaji tana fad'in

"I'm so sorry sir baxan k'ara ba kayi min uxiri "

D'an dai dai ta nutsuwar yayi don muryar ta ba k'aramin kasala ta sa mishi ba dakyar ya iya cewa

"get out please don't west my time"

Kallon dan rainin wayo husna tayi mishi kafin a fusace ta fice daga hall di'n gaba d'aya sai kuma jikin shi yayi sanyi ganin yanda ta fita a fusace don gaskia babe d'in tayi mishi ta ko'ina hmmm meke faruwa da ni ne Cewar lecture safwan Ahmad, Hka ya gama musu lecturing di'n duk jikin shi a sanyaye amman bai bari d'aliban sun fahimce shi ba da yake namijin gaske ne da haka har ya gama musu ya fito yana addu'ar Allah yasa ya ganta sai dai ko mai kama da ita bai gani ba mtswww yaja tsaki tare da dan dafe kanshi yana cewa me yasa ma ya kore ta, da hka har ya K'arasa cikin office d'in shi xuciyar shi cike da tunanin husna..............







Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 5:48 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃







*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 33-34*








ita kuwa husna tana fita a fusace kai tsaye cikin motar ta ta shige ta rufe sannan ta kwantar da kujerar ta kishingid'a tare lumshe idon ta ranta ba k'aramin 6aci yayi ba akan abin da d'an rainin wayon malamin nan yayi mata, wani wawan tsaki ta sake ja a karo na biyu Sannan ta d'auko wayar ta tare da kunna data nan message suka fara shigo wa ta what's app tuni ta tsunduma a duniyar charting.



Sai da su raudah da Fadila suka shiga fito tare da bud'e motar suka shiga ciki sannan husna ta ankare dasu nan fah suka bud'e shafin hirar wannan malamin wato safwan Ahmad tsaki husna ta ja tare da fad'in

"ku har d'an air Indai nice xan koya mishi hankali ne "

Raudah wadda duk tafi so tsoro idan ka d'auke ilham tace "kin ga husna ki kyale shi ki fita harkar shi kada ya baki matsala fah Kinsan halin lectures d'in nan "


Mtswww husna taja tsaki tare da cewa "banxa matsoraciya kawai wlh kin fiye tsoro raudah "

"Ehhh naji di'n " Cewar raudah tana Murgud'a baki kwashe da dariya suka yi husna da fadila har ita ma raudah ta d'an dara, Kafin husna tayi wa mota key suka nufi hanyar fita daga skul d'in.


Tana kok'arin fita daga get d'in skul kenan shi kuwa safwan Ahmad na kok'arin shigo wa had'a idon da suka yi da husna yasa ta fasa kok'arin kauce wa sai ma ta janyo wani black glass ta d'ora a idanun ta yayin da shima safwan Ahmad shima yaja mota ya tsaya yak'i kaucewa, don kowanne yana ji da miskilan ci da kasaita.


Sosai husna ta bawa safwan Ahmad mamaki don bai yi tsammani yarinyar hka ba sai kawai ya xuba mata ido yana kallon ta cikin mamaki yana matsayin malamin ta yaci ace ta bashi girman shi.


Cikin matuk'ar tsoro raudah tace "na rok'e ki husna ki janye motar ki a bashi hanya wlh wannan safwan Ahmad d'in bai da kirki "

Cikin halin ko inkula husna tace "wlh baxan janye ba sai dai shi ya janye kuma yayi min uban da ya ga dama"

"Haba husna yaci darajar malamin ki mana ki bashi hanya ya wuce kin ga mutane a bayan mu " Cewar Fadila


"Mtsww kan ku ake ji enmata"

Tana gama fad'in hka ta sanya headphone a kunnen ta tana jin wak'ar Jojo cikin wak'ar ta ta baby it's you tana wani kid'a kai raudah da fadila duk suka bita da kallo duk a tsorace suke suna mamakin k'arfin halin husna.


Sun d'auki tsawon mintuna 20 a hka mutane sai uban horn suke musu amman ba wanda yayi wani yunkuri ,ana cikin hka wayar safwan tayi ringing da sauri ya d'auka ganin sunan umman shine bayan ya d'auka take sanar dashi yayi sauri yaje ya d'auko mahaifin shi Alhj Ahmad a filin airport nan ya amsa mata tare da katse wayar cikin hanxari ya juya motar tare da d'aukan hanyar da xata kai shi airport xuciyar shi cike da tunanin husna yana son sanin ita wace.


Ganin haka yasa husna jan motar suka fice daga skul d'in sannan mutane suka samu hanyar tafia, dariya husna ta kyalkyale da ita har da buga steering tare da fad'in

"Yeeeee yaji tsoro ya juya daman ae irin nasu cika bakin nan duk yawan cin su matsorata ne "

Fadila da raudah suka taya ta dariyar tare da tafawa suka ce "wlh husna ke er air ce kada kisa d'alibai su daina ganin girman shi "

Kafad'a ta d'aga alamar ko ajikin ta da hka suka K'arasa gida husna tayi part d'in su yayi da raudah da fadila suka wuce part d'in hajia maamaa.


Hka rayuwa ta cigaba da tafiya tun daga ranar nan husna bata k'ara sa safwan Ahmad a cikin idanun ta ba, suna ta shirye shiryen bikin Yah Abdullah da Ilham a fili tana nuna tana farinciki da Wannan auren amman idan ta ke6e waje d'aya sai kuka sosai abin gwanin ban tausayi gaskia husna ba k'aramin son Yah Abdullah take ba duk da xuciyar ta ta sawa hakurin rabu wa dashi xata d'auke shi yanda kowacce kanwa take son yayan ta.


Yah Abdullah kuwa ya kasa xuwa kaduna duk kuwa da neman shi da ake ya dad'e rabon shi da xuwa, k'in xuwan nashi ba k'aramin damun husna yayi, haka a 6angaren ilham itama ta damu sosai da rashin xuwan Yah Abdullah duk ta damu sosai ta d'an rame saboda tsabar tunanin shi....................








Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:01 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃


*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq



*Page 35-36*




Tafiya take cikin takun ta na kasaita tasha wata irin gown green colour tayi rolling d'in kanta da black d'in veil sai ta sanya flat shoes bak'i sai er purse a hannun ta da waya tasha bak'in glass tayi kyau sosae husna Omar kenan, tana tsaye a gefen titi kallo d'aya xaka yi mata kasan ranta a matuk'ar 6ace yake, saboda motar da ta fito da itace ta lalace mata gashi yamma tayi gaf ake da a kira sallahr mangarib daga gidan aunty rufaida ta dawo mamee ta aike ta daman bason xuwan take ba gashi kuma mota ta bata matsala.


Mtswww taja wani uban tsaki kamar harshen ta xai tsinke tana duba agogon hannun ta ganin 6:35 tayi cikin 6acin rai tace

"wlh da nasan motar Yah yaseer hka take da ban d'auka ba" mtswww ta sake jan tsaki a karo na biyu tana kok'arin kiran number d'in mamee ta turo driver ya d'auke ta sai ga wata hadaddiyar mota nan k'irar Range Rover kalar dark ash da gani sabuwa ce sai shek'i da d'aukan ido take da gudu motar taxo ta shige husna .


"wad'annan sune masu jawo wa ana accident ji wani irin gudu kamar xai tashi sama " Cewar husna kenan tana bin motar da harara kamar itace ta yi mata laifin.

A hankali mai tuk'in motar yayi rebos tare da dawowa baya ya samu kusa da motar husna yayi parking sannan ya fito ya nufi inda husna ta tsaya jikin motar, ko d'aga kanta bata yi jin anyi parking kusa da ita ta cigaba da try d'in number d'in mamee don tak'i shiga.


Ja yayi ya tsaya yana kare mata kallo tare da girgixa kai lallai wannan yarinyar er jin kai ce ganin tak'i d'ago wa yasa shi bud'e baki cikin muryar shi mai dad'in gaske yace

"Assalamu Alaiki "

Da sauri ta d'ago kanta don kamar ta gane mai muryar ae kuwa suka yi ido hud'u da safwan Ahmad yana sanye cikin wani yadi ash colour anyi mishi aiki da bak'in xare haka takalmin shi bak'i ne sai dai kan shi ba hula sumar kanshi ta sha gyara irin ta matasan xamani masu ji da gayu, saukar da idon ta tayi daga barin kallon shi.

Cikin murmishi yace "wa na kama "

dummm gaban husna ya fad'i lokaci guda ga wani tsoro da ya lullu6e ta lokaci d'aya ta shiga uku yanxu ya xata yi ga hanyar ba mutane sosae yanda xata yi ihu a ji ta don a kawo mata a gaji don tasan ramuwa yaxo yi akan abin da tayi mishi tasan ba kyale ta xai yi ba don ba kirki ne dashi tuni gumi ya fara yanko mata har jikin ta ya fara rawa.

Murmishi ya sake yi a karo na biyu a cikin xuciyar shi yace ashe duk cika bakin banxa ne shegen tsoro ne da ita, ganin yana murmishi ta dauka murmishin mugunta ne haba tuni husna ta sake tsinke wa, cikin muryar shi mai dad'in sauraro yace

"Haba husna bai kamata ki ji tsoro ba na d'auka ke jaruma ce "

Cikin tsananin mamaki ta d'ago kai tana kallon shi don jin ya kirawo sunan ta d'aga mata gira yayi yana cewa

"Kina mamakin yanda nasan sunan ki koh abin da kika yi min ranannan ne ya d'aure min kai har ya kai da na binciki ko ke wace, kuma nayi mamakin yanda aka ce wannan ba halin ki bane asali ma kin samu tarbiyya mai kyau daga iyayen ki "

Shiru husna tayi kawai bata ce komai ba ganin tana duban agogo yasa ya gane abin da take nufi sai yace

"me ya samu motar taki?"

Ganin sauri take gashi mangarib ta kusa yasa tace

"nima ban sani ba just ina cikin tafiya ne naji ta tsaya "

Cikin sigar tsokana yace "Ko ba mai ne? "
Batasan lokacin da ta d'ago kanta ta d'an harare shi ba don maganar ta bata haushi, er dariya ya saki mai birgewa tare da kama kunnen shi duk biyun cikin shagwa6a yace

"sorry "

Kallon shi tayi cikin mamaki kamar ba safwan Ahmad ba, wajen motar ya shige ya d'an dudduba ta amman tak'i tashi dawowa yayi Inda take ya fito da wayar shi magana yayi na tsayin mintuna uku tukunna ya kashe wayar ya d'ago kanshi ya Kalli husna yace

"ranki ya dad'e nayi en dabaruna tak'i tashi amman na kirawo mai gyara wa don hka kixo na kai ki gida idan ya gyara xan kawo miki har gida "

Shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa yace "Ko kina tunanin xan sace miki "

Hararar shi tayi ta gefen ido sannan ta mik'a mishi key di'n motar yasa hannu ya kar6a ana cikin hka sai ga mai gyaran nan ya bashi key di'n motar sannan ya bud'e wa husna gaban motar ta shiga a d'an tsorace sannan ya rufe ya xagayo shima ya shiga a nutse ya ya yiwa motar key suka fara tafiya ba me magana a cikin su sai wak'ar Justin Bieber da take tashi ta love me kowannen su xuciyar shi cike da tunani musamman husna.

Mamakin ta ne ya k'aru ganin ko ya tambaye ta Inda gidan su yake ita kuma miskilan ci ya hana ta bud'e baki tayi mishi magana, gashi kuma sai bin hanyar da xata kaisu gidan su yake.

Lallai ma mutumin nan ba k'aramin bincike yayi a kanta ba ganin yana horn a kofar get d'in gidan da sauri me gadi ya bud'e kofar ganin husna a cikin motar sai da ya samu waje yayi parking yana tsayar da motar husna ta yunkura ta bud'e motar sai da ta fito tukunna tace mishi

"Na gode sai anjima "

Tana gama fad'in hka ta yi gaba abin ta kallon ta kawai yake yana murmishi sosai yarinyar take birge shi tun ganin ta na farko da yayi, murmishin shi ya k'aru ganin ta mance wayar ta garin sauri d'aukan wayar yayi tare da yi mata kissing bayan ya shak'i k'amshin daddad'an turaren husna har sai da ya lumshe idon shi don dad'in k'amshin,a hankali ya furta cewa "ina son ki husna! I really luv u tun lokacin da na fara sanya ki a idanu na"
Kafin tukunna ya ja motar shi ya nufi gida.


*WANE NE SAFWAN AHMAD*

Safwan Ahmad d'a ne ga Alhj Ahmad mai gwanjo da hajia karimatu suna da yara guda 3 safwan shine babba sai habib da ruqayya su kad'ai ne yaran da Allah ya basu.
Alhj Ahmad mai gwanjo asalin sunan mai gwanjo Inda ya samu sana'ar ta ya fara yi Kafin Allah ya axurta shi da samun arxiki ya bunkasa sana'ar tashi d'an kasuwa ne sosai yana fita su dubai, china da sauran kasashen wajen kasuwan cin shi ba k'aramin nasara yake samu ba akan harkar kasuwanci nashi yana da arxiki sosai, d'an asalin garin kaduna nane haifaffen can. Iyayen shi managarta ne akwai so da taimako sun bawa yaran su tarbiyya mai kyau tare da ilimin addini dana boko.

Safwan Ahmad mai gwanjo yaro ne matashi wanda shekarun shi baxa su gaxa 35 kyakkyawan saurayi ne sosai fari tas dashi gashi dogo ne yana da K'ira mai kyau yana da hancin sai dai idanun shi basu cika girma ba ga sajen nan nashi da matasa yanxu suke Bari ta ko'ina dai safwan ya had'u sosai enmata suke rububi akan shi.

Yayi ilimin shi na addini dai dai gwargwado na boko kuwa kusan a k'asar England yayi su, lokacin da yake university tashen samartaka yana kan shi an d'an ta6a neman mata da d'an shan giya amman daga lokacin da ya dawo nigeria duk ya watsar da wannan dabi'ar ya nutsu daman can da xubar abokai toh yanxu ya rabu dashi Allah ya shirye shi har haushin kanshi yake ji Idan ya tuna da rayuwar da yayi a baya, bayan ya dawo ya samu aiki a university a matsayin lecture.


_Mun dawo labari_


Da sallama ya shiga parlourn gidan nasu xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki hajia karimatu ta amsa mishi sallamar tashi da fara'a akan fuskar ta tace
"sai yanxu ka dawo my son ina ka mak'ale ko wajen surukar tawa ka tsaya don wannan gayun da magana"

Dariya yayi tare da cewa "Kaiii umma ni ba inda naje daga gidan hajia kaka nake "
Cikin murmishi tace "Okay yayi kyau hkan ya ka baro ta? "
"tana nan lafia "

Idanun ta ne suka sauka kan wayar hannun shi ta husna tace "yaushe ka siyi waya kuma don bansan ka da irin ta ba? "
D'an sosa k'eya yayi tare da cewa "uhm uhm umma ta... "

"ban san ka da k'arya ba fah safwan"cewar umma
"umma ta husna ce ta mance ta a mota ta "
Wani dad'i ne ya ishe umma ganin d'an nata yau yayi magana akan mace "Wace husna kuma? "umma ta tambaye shi
"wata d'aliba tace na rage mata xuwa gida motar tace ta lalace mata a hanya "
"ka kyauta kuwa amman Naga alama d'an nawa kamar....."
Sai tayi shiru tana dariya shima dariyar yake yana cewa "Allah umma ba wani abun "
"idan tayi tsami ma ji "
Daga hka hirar tasu ta yanke ya fita xuwa masallaci umma kuwa ta shige d'akin ta.........




Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:07 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




_Godiya ga dukkanin makarantar DANGARTAKAR ZUCI mun gode da yanda kuke son littafin da yanda kuke bibiyar shi Allah ya bamu ikon kammala muku shi lafia_❤😍




*Page 37-38*



Husna tana shiga gida ta tuna ta bar wayar ta a motar safwan da sauri ta jiyo don ganin ko bai riga ya fita ba har tana d'an had'a da d'an gudu sai dai kash tana xuwa mai gadi yana rufe get alamar fitar shi kenan, haushi ya rufe husna don me yasa baxai bawa baba mai gadi ya kawo mata ba sai tafar mata da waya Mtsww taja tsaki cike da jin haushin safwan don tana son amfani da wayar ta ta, ganin tsayuwar baxa ta amfane ta ba yasa ta juya xuwa part d'in su,gashi abin takaicin nata bai wuce ta cire security d'in jikin wayar ta ta, tasan bincike xai mata a wayar Amman mutumin nan ya rai na min hankali.


Kwance yake saman bed tunanin husna yake yi shi kanshi yana mamakin yanda son yarinyar ya shiga xuciyar shi farat d'aya wayar ta ya d'auka nan ya shiga sarrafa ta da yake ba security a wayar cikin memory card nata ya shiga ya fara kallon picture's d'in ta anan ya sake tabbatar wa da kanshi Indan ya samu husna matsayin matar shi ya gama more wa.

Contact di'n ta ya d'auka yayi serving a phone d'in shi sannan ya cigaba da kallon pictures d'in husna xuciyar shi tana k'ara k'aunar ta, safwan kenan jarumin namiji mai ji da kyau da nera gashi yau ya fad'a son husna, daman Hka enmatan da suke son shi suke daman hka so yake, yake tambayar kanshi bayan ya gama kallon photo nan husna, daman shi bai ta6a yin soyayya ba wannan karon shine na farko a cikin rayuwar shi.


_Abuja_

Yah Abdullah na hango xaune acikin garden di'n gidan shi kallo d'aya nayi mishi na firgita ganin yanda ya rame yayi bak'i kamar ba Yah Abdullah dana sani ba duk ya tara wani uban kasumba saboda tsananin tarin damuwa da tunani da yake ciki.

Anya hajia maamaa tana son shi kuwa taya xata raba shi da abar son shi akan wani banxan shirme wai xata juya shi to idan ta juya shi di'n ina ruwan ta, lokacin da suka ci nasu xamanin waya samu su ido, ni mai xanyi da ilham kawai an tashi an had'a ni da yarinyar da bana so (ni kuwa nace Hmmm Yah Abdullah kada ka cika baki kaxo kana jin kunyar mu lol).

K'arar wayar shi ce ta katse mishi tunanin shi da sauri ya d'auka ganin sunan abban shi ne da sallama ya fara Kafin ya gaida shi sai da suka gama gaisa sannan abba yace

"Abdullah ka kyauta yanxu yaushe rabon ka da xuwa nan gidan? "
"Abba kayi hak'uri aiki ne ya rik'e ni Inan xuwa wannan week end d'in "Cewar Yah Abdullah kenan.
Murmishin su na manya Abba yayi Kafin yace " ni dai kiran ka nayi don na tunasar da kai ranar sunday misalin karfe 11 na safe xa'a d'aura auren ka da ilham kuma ka tabbatar kaxo idan ba hka ba wlh ni da kai ne "
Abba ya K'arasa maganar a fusace, dummm gaban Yah Abdullah ya fad'i jin abin da abba yace mishi ya ma kasa magana sai da abba ya kuma cewa
"kana jina kuwa Abdullah "
Murya na rawa Yah Abdullah yace "ina jin ka Abba kuma Insha Allah xan xo "
Yana gama fad'in hka Abba ya kashe wayar tashi cike da jin tausayin d'an nashi.

Shi kuwa Yah Abdullah sakin wayar yayi ta fad'i k'asa lokaci d'aya wasu hawaye masu xafi suka fara xubo mishi daga idanun shi abin tausayi shi kenan ya rabu da husna har abada duk mafarkan shi da tunanin shi burin shi ya tashi a banxa tun da ba husna a rayuwar shi da ita ya tsara rayuwar shi sai gashi hajia maamaa tayi musu katsalanda wayyo Allah shi ina xai kai son husna a cikin xuciyar shi. (ganin yana kok'arin sani hawaye yasa ni tattara wa na bar mishi gidan amman hak'ik'a Yah Abdullah ya ban tausayi) .



_Malaysia_


Wani kyakkyawan matashi na hango cikin kayan training yana d'an gudu da yake sassafiya ce a garin iska mai dad'i tana kad'a shi headphone ne a kunnen shi yana sauraran karatun alqur'an cikin suratul baqara K'ira'ar shuraem don dad'in karatun har wani lumshe ido yake, *DR IBRAHEEM MUKTAR IBRAHEEM* kenan.

Sai da ya kwashi mintuna 40 yana gudun tukunna ya dawo xuwa cikin gidan da hukumar asibitin da yake aiki suka bashi, toilet ya fad'a yayi wanka sannan ya fito ya shirya cikin wani black jeans nd T-shirt green mai k'aramin hannu yayi matuk'ar yin kyau don ibraheem ba daga baya ba wajen kyau da iya tsara kwalliya don har yafi Yah Abdullah kyau sosae.

Yana gama shirya wa ya fito xuwa falo dinning table ya nufa ya tarar kukun shi ya kammala had'a mishi breakfast bayan ya gama tsatstsakura ya tashi ya dawo cikin parlourn ya xauna tare da lumshe idon shi yana tunanin gaskia ya kamata ya koma gida gaba d'aya hankalin shi yayi gida tun da yaxo karatu bai koma nigeria ba ko hutu baya xuwa abba ya hana shi saboda yana jin tsoron kada ya dawo ya mak'ale yak'i koma wa gashi har ya gama karatun saboda kwaxon shi yasa suka d'auke shi aiki na tsawon shekara 2 gashi yana dab da cika shekarun nashi.


Yana buk'atar koma wa gida don ya tona asirin xuciyar shi ya bayyana abin da yake rufe cikin xuciyar shi wanda ya kwashi tsawon shekaru yana fama dashi abin ya shafi *DANGARTAKAR ZUCIyar* ne sai hajia maamaa kawai suka san mene.

Yana cikin tunanin ne aka kirawo shi a waya ana neman shi a hospital da gaggawa don hka dole ya katse tunanin ya shirya ya tafi asibitin............



Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:17 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃


*written by*
Aishat A muh'd

*&*
Sumayya salees sadeeq



*Page 39-40*



Xaune suke a kan wasu kujeru cikin skul bayan sun fito a lecture husna, fadila da raudah kenan en gida d'aya, suna tattauna wa akan shirye shiryen da xasu yi a bikin, suna cikin hka ne suka ji k'amshin wani sansanyan turare ya bugi hancin su sai kuma suka ji anyi musu sallama cikin murya mai dad'i gaba d'aya suka d'ago kan su a lokaci guda don ganin wane wannan, fadila da raudah xaro ido suka yi gaban su kuma ya fad'i don ganin safwan Ahmad ne yayin da a 6angaren husna tana mishi kallo ta kauda kanta gefe don har yanxu tana jin haushin abin da yayi mata duk da kuwa taimakon da yayi mata jiya.

Cikin rawar murya Fadila da raudah suka gaida shi cikin murmishi ya amsa musu tare da cewa "ya karatu? "
Cikin mamaki suka amsa da "Alhmdullilah"
Suna masu mamakin yanda har yaxo yana kula su bai damu da kallon da d'alibai suke

Please Login or Register in order to submit comment