Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirya sannan suka tafi, Sam batason ganin husna cikin damuwa itama sai taji hankalin ta ya tashi duk cikin family d'in su sun fi shiri da husna duk da kowa halin shi daban.

Iyayen su maxa sun yanke hukunci nan da sati d'aya husna xata tare a gidan ibraheem saboda uxirin da ibraheem ya bayar akan son ya k'ara gyara gidan shi duk kuwa da gidan sabo ne kuma komai sababbi da iyayen nashi basu yarda ba amman da hajia maamaa taji tuni ta amince da hkan, cikin tsayin satin nan mumy ta dage sosai da gyara d'an ta, hka ma tana aikawa da mamee a bawa husna shi yasa mamee take son mumy kuma tasu taxo d'aya.

Ita ma mameen sosai ta tsaya tana gyaran d'iyar ta ta cikin ta da wajen ta tuni husna ta k'ara wani kyau sosai fatar ta ta kara laushi da santsi kamar tana rayuwa a cikin k'ank'ara sai dai ramewar da tayi saboda damuwa har xuwa yanxu bata k'ara sa ibraheem cikin idanun ta ba kuma bata fatan sake sanya shi a idanun ta.


Suna waya da su Fadila, raudah da Ilham kullum sai sun kirawo ta su dad'e suna hira sosai, Fadila ta kwantar da hankalin ta suna ta cin amarcin su da Yah yaseer yayan husna ta hak'ura da Yah ibraheem ta ma fitar da son shi a xuciyar ta lafia suke xaune kamar irin auren soyayyar nan suka yi ba had'a su akayi ba.


Yammaci ne lik'is an yi ruwa an d'auke ko'ina yayi dad'i shukoki sunyi kore shar dasu gwanin sha'awa, husna ce xaune a cikin garden tana sanye da wani white jeans and T-shirt red colour mai k'aramin hannu ta gyara gashin kanta tasa mishi ribbom red colour ta d'aure shi tare da sakin shi baya dan kunnen ta red shi ma tayi kyau sosai takalmin kafarta plate shoe ne shima red colour amman irin mai igiyar nan sai k'amshin perfumes masu matuk'ar k'amshi take waya ce a hannun ta suna charting a group d'in su na family duk yawancin su suna online su Fadila, raudah, ilham, yah Abdullah, yah yaseer, yah mus'ab, aunty rufaidah, yah kabeer dukkan su dai sai hira ake sosai ba ta fiye magana ba kamar da har Yah Abdullah yana tsokanar ta ta xama silent ashe Yah ibraheem shima lokacin yana online yana sauraren hirar tasu amman tun da Yah Abdullah yasa shi bai ta6a magana ba.

Kamar ance ya d'ago kanshi ya hango husna xaune cikin garden shigar da tayi ba k'aramin kyau tayi mishi ba da yake yana barandar saman bene yana kallon duk wani motsin ta ya samu kanshi da sakin murmishi shi kad'ai kasa jure wa yayi ya sakko daga stairs ya taho garden din.

Jikin ta ne ya bata ana kallon ta don hka ta d'ago kanta da sauri ae kuwa suka had'a ido da ibraheem yana tsaye ya hartse hannayen shi a kirji wani irin ihu ta saki kamar wadda ta ga dodo ihu take ba kakkauta wa gashi ta runtse idanun ta gaba d'aya dai dai lokacin mamee ta taho garden din da k'aramin veil din husna don kanta ba d'ankwali ta fita shine ta biyo bayanta jin ihun husna yasa mamee ta fara sauri ta K'arasa wajen tare da kamo ta tace
"ke husna lafia kike wannan ihun? "
Jin maganar mamee yasa ta rungume mamee tana sauke ajiyar xuciya cikin tsoro mamee ta ce "me ya saki ihu ne wani abin kika gani?"
Gid'a kai tayi alamar ehh sannan ta nuna mata saitin da Yah ibraheem yake tsaye kuma har a lokacin idanun ta a rufe tukunna tace "Wannan nagani na tsorata "
Da sauri mamee ta juya ta d'auka ko gamo d'iyar ta ta tayi sai kuma suka had'a ido da ibraheem, takaici kunya su suka rufe mamee lokaci d'aya na abin da husna tayi shi kuwa ibraheem wanda Tsananin mamakin abin da husna tayi mishi yasa shi suman tsaye a wurin ya kasa motsawa dak'yar ya janye jikin shi ya tafi amman gaba d'aya jikin shi yayi sanyi.


Hannun husna mamee ta kama suka fara tafiya tana yi mata fad'a sosai akan abin da tayi bai kamata ba me take nufi da yi mishi ihu shi dodo ne sosai mamee tayi mata fad'a ae kuwa husna ta cika ta sake yin fam da ita................






Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:03 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




*Page 55-56*




Tun daga lokacin husna da Yah ibraheem basu k'ara had'u ba har ya xama a yau xa'a kai husna gidan yah ibraheem en uwa na kusa sun xaxxo har wata er k'warya k'waryar walima akayi, Kafin kuma da yamma wajen 5 aka mik'a husna gidan ta bayan tasha nasiha sosae a wajen mamee da daddyn ta ga sauran en uwanta su ma sunyi mata nasiha sosae hajia maamaa kuwa addu'a tayi mata tare da sanya mata albarka tun da yanxu ta hak'ura xata xauna da d'an gaban goshin nata, har da ita aka kai husna don daman tayi alk'awarin ita da kanta xata shigar da matar ibraheem cikin d'akin ta ae kuwa hannun ta rik'e da hannun husna har ta xaunar da ita kan katafaren gadon ta, husna kuwa har tayi kuka ta gaji hawayen ma sun daina fito wa daga idanun ta sai faman ajiyar xuciya take saki lokaci xuwa lokaci.

Ana sallahr mangarib en uwa suka yiwa husna sallama suka tafi ya rage gidan sai husna, aunty rufaidah da aunty aimana sai da suka gyara mata ko'ina na gidan suka kunna turaren wuta mae k'amshi tuni ko'ina ya d'auki k'amshi mai dad'in shak'a bayan sun gama su ma suka k'ara yiwa husna nasiha tare da bata shawarwari masu kyau tukunna suka tafi aka bar husna ita kad'ai bata ji wani tsoro sosai ba tun da ko'ina akwai haske kamar da rana.

Kayan jikin ta ta cire ta d'aura towel ta shige toilet wanka tayi tare da alwala bayan ta fito ta shirya cikin wata blue sky din sleeping dress doguwa ce har k'asa mai siririn hannu ta gyara gashin kanta sannan ta fesa different perfumes nd body spray masu matuk'ar k'amshi.

Abin sallah ta shimfid'a bayan tasa dogon hijab mai hannu har k'asa ta gabatar da sallahr isha'e bayan tayi addu'o'in ta kamar yanda ta sa ba sannan ta mik'e tsaye tare da cire hijab d'in nata jiyowar da xata yi suka had'a ido da Yah ibraheem tsaye a jikin kofar d'akin yana kallon ta hannun shi rik'e da wasu manyan leda wani wawan tsaki taja kamar xata tsinke harshen ta.

Duk da Yah ibraheem a duniyar nan ya tsani tsaki kuma ranshi ya 6aci amman bai nuna ba tunda sulhu yake nema, ajiye ledar hannun shi yayi kafin dakyar yace

" ga wannan ko xaki buk'aci abinci "
Yana gama fad'in hka ya juya da niyyar fita har ya fitar da kafafun shi daga cikin bedroom d'in husna kamar abin arxiki ya bud'e baki tace
"Yah ibraheem "

Cak Yayi ya tsaya jin ta ambaci sunan shi juyowar da xai yi sai gani yayi ta cillo mishi wannan ledar da ya ajiye a fuskar shi tuni kayan ciki suka tarwatse gaba d'ayan su a k'asa cikin tsanar shi tace
"an gaya maka ni mayunwaciya ce, bana son duk abin da ya fito daga hannun ta i hate u"
Tana gama fad'in hka ta rufe kofar ta tare da sa mata key kan bed ta koma hankali kwance ta kwanta tare da yin addu'ar bacci bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Yah ibraheem kallon kayan da ya tarwatse a k'asa yake duk da ranshi ya 6aci sosai akan abin da husna tayi mishi ya riga da ya yiwa kanshi alk'awarin baxai ta6a tanka mata ba har xuwa lokacin da xata huce ya bata hak'uri tare da neman soyayyar ta don kuwa duk abin da xata yi mishi xai danne xuciyar shi.

Yana gama wannan tunanin ya nufi inda ake ajiye Parker da abin yin mopping ya d'auko share wajen yayi tare da goge wa tukunna ya shige bedroom d'in shi wanka yayi tare da yin alwala sannan ya fito ya shirya cikin wasu sleeping dress farare sol dasu kan abin sallah ya hau ya fara jera nafila na godia ga Allah tare da addu'ar Allah ya karkato mishi da hankalin husna kanshi yasa ta so shi ko da rabin son da yake mata ne hka ya raya daren cikin bautar ubangiji har xuwa asuba bayan ya yi sallahr asuba ne bacci ya d'auke shi mai dad'in gaske xuciyar shi cike da tunanin abar son shi husna.


Washe gari da safe bayan husna ta tashi daga bacci wajen karfe 9:30 na safe brush tayi tare da shan ruwa cikin glass cup d'aya don yana taimaka wa jiki sosai yin hka kuma wannan shan ruwan safen Kafin taci komai horan mameen ta ne.

Gyaran bedroom d'in nata tayi sannan ta gyara falon ta da kuma babban palon gidan tasa turaren wuta ta turare gidan da k'amshi sannan ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata tsadaddiyar atampha kalar blue d'inkin riga da siket ne sun amshe ta kayan ta d'aurin dankawalin ta mai kyau bata yi wata k'walliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple amman duk da hka ba k'aramin kyau tayi ba tana cikin fesa turare taji an danna door bell don hka tana gama fesa wa ta fito xuwa falon ta bud'e kofar er aikin mumy ce shige wa tayi ta xauna er aikin ta gaida husna tare da cewa
"gashi inji mumy tace na kawo miki "
Ta fad'a tana ajiye basket d'in xuba kayan abinci ga hadaddun food flaks a ciki
"Okay je ki ajiye min kan dinning table "
"toh aunty "
Da sauri taje ta ajiye bayan ta dawo tace " aunty Ko da wani aiki da xan yi miki?"
Girgixa kai husna tayi tare da cewa "nooo babu komai wa ya kawo ki? "
"driver ne"
"Okay Shikenan "

Daga hka ta yi mata sallama ta tafi, kitchen husna ta shiga taga yanda aka tsara mata kitchen d'in ya had'u sosai kalar green ne plate ta dauko da cup d'in had'a tea tare da spoon and fork dinning table ta nufa ta ajiye nan ta tarar da kayan tea milk, bournvita, cornflakes da dai sauran su nan ta had'a tea tasha tare da cin chips and egg sai er source tare da plantain,sai da ta koshi sannan ta tashi ta dawo falo ta xauna wayar ta ta d'auko nan ta fad'a duniyar charting sai hira suke a grp d'in su wanda suka bud'e mai suna 4 sister's for life husna, ilham, Fadila da raudah suna ba wa junan su shawarari masu amfani sosai sai tsokanar husna ita kuwa tana bawa kowa amsar da ta dace.

Wani k'amshin turare ne ya bige hancin ta saboda dad'in k'amshin sai da ta lumshe idanun ta Kafin ta d'ago kanta suka had'a ido da Yah ibraheem yana sanye cikin wani blue d'in jeans da t-shirt black mai dogon hannu yayi kyau sosai kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya nufo inda husna take xaune wadda ta danna mishi harara Kafin ta mayar da hankalin ta kan wayar, k'arasa wa yayi ya xauna kusa da ita har kafad'ar shi na gogar ta ta da sauri husna ta matsa gefe cikin murmishi yace
"Gud mrng sweetheart, i hope kin tashi lafia? "

Bata yi mishi magana ba hka kuma bata sake kallon Inda yake ba K'arshe ma sai ta shige cikin bedroom d'in ta da kallo ya bita yana murmishi tare da shafa gashin kan shi xuciyar shi cike da tsantsar k'aunar ta da sha'awar ta da hka ya tashi ya nufi dinning table yayi breakfast sannan ya fita daga gidan gaba d'aya.

To Hka abubuwa suke tafiya tsakanin husna da Yah ibraheem bata kula shi k'wata k'wata ko magana bata yi mishi ko da yayi mata kullum shine xai gaida ita Idan suka had'u a palo but husna bata amsa wa amman hkan bai sa ya fasa yi ,ga wata axababbiyar sha'awar husnah da ta dame shi saboda irin shigar da take yi wani lokacin ba k'aramin tayar mishi da hankali take ba kusan k'wana yake murkususu akan bed da yana da ra'ayin kula mata waje da tuni yayi saboda sha'awar da take damun shi sosai abin ya fara ramar dashi ya rasa ta yanda xai rarrashi husna ta amince dashi don ya kawar da abin da yake damun shi.

Idan abin ya dame shi sai dai yasha maganin da xai dan samu sauk'in abin, ana cikin hka daddy ya kammala gina mishi hospital d'in shi an gama komai an xuba kayan aiki sannan ya nemi kwararrun likitoci an xuba a asibitin ranar da akayi bikin bud'e asibitin ko da ya sanar da husna ko tanka mishi Bata yi ba.

Ana cikin hka suka kwashe tsawon wata 3 da aure husna tana xuwa skul d'in ta don ya kyaleta ta cigaba su ma suna gaf da kammala wa drive guda ya ajiye mata wanda xai dunga kai ta skul yana dawo da ita, kuma har a yanxu husna bata je gida ba tun da aka kawo ta gidan Yah ibraheem rabon ta da gida, su fadila da raudah sun xo mata yini rana d'aya suka xo sun sha hira sosai kamar kada a rabu kowacce da tsarabar amarci don Sun samu ciki husna sai tsiya take musu suna rama wa ranar sunyi yinin farinciki sosai sai da yamma Yah mus'ab da Yah yaseer suka xo d'aukan matan su bayan sun taso daga aiki ae kuwa husna ta rik'e su sai da suka yi dinner agidan tukunna su ka tafi, hakurin Yah ibraheem ya fara karewa don hka ya fara tunanin neman mafita.

Kamar yau ranar sunday weekend kenan yah ibraheem yana xaune a palo sanye yake da wani 3quater fari da wata riga mai Shara Shara don ana iya hango kwantaccen gashin kirjin shi bak'i wuluk dashi yana amfani da laptop d'in shi amman kusan hankalin shi yana kan husna wadda take xirga xirga tsakanin kitchen da wurin dinning table tana shirya wa kanta abincin rana don bata yi da Yah ibraheem sai dai idan ta rage takai kitchen Kafin taxo wanke wanke sai ya d'ebo yaci hkan ba k'aramin kular da ita yake ba bayan ta gama had'a abincin ta gyara Inda ya kamata sai ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin wata gown red colour ce mai k'aramin hannu doguwa ce har k'asa sai dai tana da tsaga daga saitin gefen ta tsagar tun daga cinyar ta har kafar ta ana gani ga wuyan rigar babba ne mai irin V din nan ta sanya ribbom red da dankunne red shima ga hannun ta kan 'yan yatsun ta sun sha jan lalle tayi masifar yin kyau kowanne namiji mai lafiya yaga husna a hka sai hankalin shi yayi masifar tashi falo ta fito tana tafiya duk wata ga6a ta jikin ta sai fitar da sanyayen k'amshi take k'amshin da take shi kad'ai ya isa ya tada hankalin mutum gashi fuskar nan ta ta a daure take babu alamar fara'a sam.

Yah ibraheem wanda k'amshin turaren husna ya sashi d'ago kanshi ya Kalle ta sai kawai ya saki baki da hanci da ido yana kallon ta cikin wata masifaffiyar sha'awa tuni idanun shi sun fara canja launi xuwa ja har taxo ta shige ta gaban shi ya bita da kallo gaba d'aya jikin shi ya fara rawa xumbur ya mik'e ya nufi inda husna take xaune tana cin abincin ta hankali kwance batasan ma da tahowar shi ba...............


_Koya xata kasance tsakanin had'uwar husna da Yah ibraheem_?





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 7:09 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




*Page 57-58*





Husna abincin ta take ci hankali kwance batasan ma da tahowar Yah ibraheem xuwa inda take ba gashi tayi wani xama ta d'ora kafar ta d'aya kan d'aya wurin tsagar rigar ya bayyana kyakkyawar cinyar ta bata ankara ba sai ji tayi ana shafa mata cinyar ta a fusace ta sa hannu ta ture hannun shi daga jikin ta tare da cewa
"lafia xaka xo kana ta6a ni? "
Cikin tsananin buk'atar ta muryar shi a sark'e yace "Haba husna don Allah ke bakya yafiya be kiyi hak'uri da abin da nayi miki ina son ki so ba na wasa ba ki taimaka ki ban hakk'i na please "

Wata shegiyar harara ta watsa mishi tare da jan tsaki ta bar wajen tana karkad'a jikin ta wanda ya k'ara rikita shi d'akin ta ta shige don idan ta tsaya kula shi 6ata lokaci ne .

Wata irin muguwar sha'awa ce ta lullu6e ibraheem ya rasa ina xai sanya kan shi da yaga xuciyar shi tana ayyana mishi ya fita yaje ya nemi matan waje nan shed'an ya k'ara ingixa shi da sauri ya shige bedroom d'in shi ya fara kok'arin canja kayan jikin shi, ya bud'e drower din jikin dressing mirror ya had'a ido da wani kyakkyawan qur'an tuni jikin shi yayi sanyi da ya tuna abin da xai je ya aikata yanxu nan yayi fatali da shawarar da xuciyar shi ta bashi ya d'auko qur'an din ya fara karatu cikin kankanin lokaci yaji duk abin da yake damun shi ya ragu sosai bai bar karatun nan ba sai da akayi kiran sallahr la'asar sannan yayi alwala ya tafi masallaci daga can kuma ya shige gidan su.


Husna kuwa tana shiga bedroom ta bi lafiar gado ta kwanta tana faman charting a waya hankalin ta a kwance sam bata jin tausayin Yah ibraheem don ita ta sawa xuciyar ta da mak'iyin ta take xaune ba masoyi ba har yanxu bata yarda da son da yake furta mata kullum yana yi mata abin da tafi d'auka jikin ta yake so kawai ko ba wannan ba husna bata son Yah ibraheem ko Kad'an xaman hak'uri take kuma don kwanciyar hankalin mameen ta.

Kamar yau da safe husna ta gama had'a breakfast d'in ta ta gyara ko'ina na gidan sai k'amshin sanyayan turaren wuta da air freshener yake yi, wanka ta shiga bayan ta fito ta shirya cikin wata tsadaddiyar shadda purple tasha d'inkin stone's tayi kyau sosae a yau da niyyar tafiya gida ta tashi ko ya yarda ko bai yarda ba kuwa don ta dad'e bata ga mameen ta ba sai dai su yi waya da ita a kullum mamee cikin yi wa husna nasiha take kan tayi hak'uri su xauna lafia sai dai ta amsa wa mamee da toh kawai.

Tana fito wa ta hango Yah ibraheem xaune a 6angaren dinning table yana breakfast d'in da ta girka ita d'aya cikin jin haushin shi ta k'arasa wajen ae kuwa ta tarar gaba d'aya ya cinye chips da wainar Kwan da tayi har da tea d'in da ta had'a kuwa wannan shine karo na uku da xata yi mishi magana tun da taxo gidan cikin fusata tace
"malam kai ka ajiye da xaka xo ka cinye? "
Cikin murmishi har yana shafa sajen shi yace " Don naci abincin mata ta da ta ajiye laifi ne da xa'a tuhume ni akan naci?"

Harara ta xabga mishi sannan tace " da yake da sunan ka na dafa abincin ba ni kawai ka biya ni abinci na"

Ta k'arasa fad'i tana wani jijjiga jiki irin na masifar nan shi kuwa Yah ibraheem kallon ta yake xuciyar shi tana k'ara k'aunar ta komai tayi kyau yake mata bata ankara ba taji ya fisgo ta jikin shi kan kafafun shi ya xaunar da ita ya d'ora kanshi a gefen kafad'ar ta yace
"fad'i abin da kike so yanxu na nemo miki shi, Kiyi hak'uri don Allah jiya ban ci abinci na kwanta ba shi yasa na tashi da yunwa gashi baxan iya fita neman abinci ba kuma ban iya girki ba shi yasa na"

Kwace jikin ta tayi tana hararar shi tare da cewa "ni kada ka k'ara ta6a ni na fad'a maka "
Shi dai kallon ta kawai yake har ta juya xata tafi sai kuma ta dawo ta tsaya a gaban shi hannun ta rik'e da kugu tana wani d'aure fuska tace

"ina son xan je gida yau? "
Ga mamakin ta ko xai k'i yarda sai ta ga ya saki wani kyakkyawan murmishi yace "Okay ba matsala shirya sai na sauke ki na wuce hospital "

Bata K'arasa jin abin da yace ba tayi gaba yabi bayan ta da kallo yana lashe busassun le6en shi dafe goshi yayi tare da furta "husna rigima kenan amman ina addu'a Insha Allah sai nayi nasarar shawo kan ki "

Yana gama fad'in hka ya shiga bedroom d'in ya shirya sannan ya fito hannun shi rik'e da briefcase, a falo ya tarar da husna ta gama shirya wa tana tsaye tana jiran shi Murmushi yayi mata tare da cewa "madam na fito dafatan ban 6ata miki lokaci ba? "
bata kula shi ba tayi gaba ya bi bayanta shi ya bud'e mata motar ta shiga ta xauna ya rufe sannan ya shiga yayi wa motar key suka fice daga gidan.

Babu mai kula wani har suka K'arasa wani had'ad'd'an mall ya tsaya yayi shopping sosai na abubuwan buk'ata sannan suka K'arasa gida yana gama parking ta fice daga motar da gudu ta nufi part d'in su shi kuwa Yah ibraheem ya bita da kallo yana murmishi kafin ya fito daga motar ya bi bayanta bayan ya bawa mai gadi umarnin kwaso kayan ya kai kowanne 6angare ace inji husna sannan ya wuce.

Mamee tana xaune taji an fad'o jikin ta an rungume ta tana d'ago kanta ta ga husna ce ae kuwa nan ta fad'ad'a fara'ar ta sosai tana mai farincikin ganin d'iyar ta ta cikin koshin lafia alamar ta kwantar da hankalin ta
"d'aga min mamee na kada ki 6alla min ita "
Cewar Yah ibraheem da ya shigo harara husna ta watsa mishi tare da yin k'unk'uni mamee kuwa dariya kawai tayi nan suka gaisa sannan ya kalli husna yace"ki xama cikin shiri nan da 5 xan biyo mu tafi "
Ko kallon Inda yake husna bata yi ba sai da mamee ta ta6a ta Sannan dak'yar ta iya cewa "naji ae "
Sallama yayi wa mamee ya tafi yana fita mamee ta fara yi wa husna fad'a sosai tana cewa
"Ashe har yanxu husna baki kwantar da hankalin ba ina nan ina murna kin hak'ura kin xauna ashe ba hka bane to wlh Idan baki gyara ba xan xame hannuna daga lamarin ki tunda bakya jin magana "
""mamee! "
Cewar husna a firgice Kafin tayi magana sai ga mai gadi yana shigo da kayayyaki bayan ya gama shigo dashi yace " gashi nan inji yalla6ai ibraheem yace na kawo inji husna "
Cikin fara'a mamee tace "toh sannun ka "
Fita yayi mamee ta daure fuska kamar ba itace mai fara'a yanxu ba tace "Kalli abin da yayi daganin fuskar ki yanda kika nuna nasan baki xaci inji ki xai ce ba Allah husna kin bani mamaki ban ta6a xaton Hka kike da rik'o ba"


Nan fah mamee tayi wa husna tas kuka sosai husna take tana bawa mamee hak'uri amman fah har yanxu tana nan akan bakanta da xasu yarda da an raba auren ita fah ta tsani Yah ibraheem k'wata k'wata batason ganin shi sai dole.

Dak'yar mamee ta hak'ura sannan ta gyara fuskar ta ta tafi sauran part's din suka gaisa sai godia suke mata ita kuwa husna sai dai ta ta6e baki don ita tasan don ya birgeta yayi ita kuwa baisan ma haushin shi ta kara ji ba duk tafi dad'e wa a wajen mumyn ibraheem kamar ta had'iye ta don murnar ganin ta dakyar ta iya shiga sashen hajia maamaa sai da mamee tayi mata fad'a sosai sannan ta shiga fuska a d'aure

Please Login or Register in order to submit comment