Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amman saboda ke mamee a matsayin ki na mahaifiya ta kin amince da hkan "

Cikin murmishin jin dad'i mamee ta rungume husna tare da fad'in "ngde husna Allah yayi miki albarka Allah ya baki yara masu yi miki biyayya fiye da yanda kike mana "

"Ameeen mamee nah Allah ya bar min ke hak'ik'a ke uwa ce ta gari nagode wa Allah da ya bani ke matsayin uwa "

"Ameeen 'yar albarka, amman fah har yanxu ba mu san wanda ta xa6a miki ba don ko su daddyn ku bata fad'a wa, kiyi hak'uri da duk wanda kika gani matsayin mijin ki "

D'an ta6e baki husna tayi bata sake cewa komae ba tana tunani a cikin xuciyar ta ta yarda da ta xa6a mata miji acikin en uwan ta maxa amman ban da mutum d'aya idan kuwa shine to wlh xa'a ga tashin hankalin da ba'a ta6a yi ba a gidan nan, Hmm bana fatan shi ne xama da mak'iyin ka ae akwai matsala.

Nan cikin d'akin mamee tayi kwanciyar ta a jikin ta Bata k'ara bi ta kan wayar ta ba don ta fidda rai da samun safwan har abada sai dai wani ikon Allahn ne amman ta rufe babin soyayya daga yau tun da ta rasa gwaraxan maxaje guda biyu, wanda xata auran sai dai ya auri gangar jikin ta amman ba xuciyar ta ba, to fah tunanin husna kenan.

Shi kuwa safwan da yaji k'arar fad'uwar wayar shi ma tashi ya saki tare da had'a kai da gwiwa yana wani irin kuka mai matuk'ar ban tausayi, yasan ya rasa husna har abada yana cikin hka umman shi ta shigo ta same shi hankalin ta ne ya tashi sosai ganin yanda yake rera kuka tasan tabbas safwan ba k'aramin so yake yiwa husna ba nan ta d'ago kan shi yana ganin umman shi ce ya fad'a jikin ta cikin kuka yake cewa

"Shikenan umma na rasa husna har abada? "
Cikin tsananin tausayin d'anta tace "safwan kayi hak'uri daman can Allah ya rubuta husna ba matar ka ba ce ka rage sa damuwa acikin xuciyar ka kada wani ciwon ya shige ka "

Jin yayi shiru ya dai na kukan yasa ta cigaba da cewa "a matsayi na na mahaifiyar ka ina son ka cire husna daga cikin xuciyar ka don Allah Kuma ina son kaje ka nemi auren sumayya d'iyar k'anwa ta ka rabo da husna "

Kama hannun umma yayi tare da cewa "Nayi miki alk'awari umma Insha Allah na hak'ura da husna daga yau sai dai son ta sai a hankali xan rabu dashi duk da nasan har na mutu baxan iya dai na son husna ba "

Ajiyar xuciya ya saki sannan ya cigaba da cewa "kuma xan nemi soyayyar sumayya tun da tun farko ita kika so na aura xan aure ta don na faranta miki rai umma Insha Allah "

Cikin tsananin farinciki umma ta rungume d'anta tare da cewa "nagode safwan Allah yayi maka albarka ya k'are min kai a duk inda kake hak'ik'a nagode wa Allah da yaban yaro mai biyayya "

Cikin murmishin yak'e safwan yace "Ameeen umma na "

Daga hka ta kama hannun shi suka fito xuwa cikin falon don yin lunch nan ta dunga lalla6a shi yana cin abincin har ya koshi don shi kanshi ya ji dad'in jikin shi yaushe rabon da yaci abinci kamar hka har ya mance yana gama ci bedroom d'in shi ya koma wanka yayi ya shirya cikin wasu mara nauyi ya fita xuwa garden akan wata kujerar huta wa ya kwanta hannun shi yasa ya dauko wayar shi tare da kamo pictures d'in husnar shi yana kallo yana xubar da hawaye nasan har abada baxan dai na son ki ba husna nan yayi ta sumbatu shi kad'ai yana fitar da hawayen tausayin kansu.



Hka abubuwa suka cigaba da tafiya sam husna bata nuna wa hajia maamaa tasan maganar ba sai dai idan suka had'u a hanya ta gaida ita ta wuce, yanxu hankalin ta ya dad'a kwanciya da ta ga safwan ya dai na xuwa skul don ta riga da ta fidda rai akan shi.

Ashe safwan rashin lafia yasha sosai kamar baxai tashi ba kuma duk akan son husna daga K'arshe iyayen shi suka aura mishi Sumayya tare da cewa tura shi k'asar london don duba lafiar shi, bayan ya warware kuma aka fara xuba amarci duk da son husna na nan mak'ale a cikin xuciyar shi amman sumayya yarinya ce mai hankali da nutsuwa kuma tana da kyau ba laifi gashi wayayyiya ce tuni ta samu zama acikin xuciyar safwan don tasan labarin shi Kaf akan rabuwar su da husna, anan kuma ya samu aiki a university di'n london yana koyar wa hankalin su kwance su ma iyayen nashi hankalin su ya kwanta duk da ba'a son ransu d'an nasu yayi nisa da su ba xuwa nigeria sai da xiyara.


A ranar da husna ta labarin safwan a ranar yini tayi kuka sosai har dare bata samu ta runtsa ba sai da tasha xaxxa6i na tsawon k'wanaki uku xuwa hud'u ko skul bata xuwa ta rame sosai, mamee tayi tsaye a kanta har ta samu lafia tana tsananin tausayin husna, hka ma rufaida yayar ta da Yah yaseer ba suna bata kulawa sosai, haka daddy ma ba'a bar shi a baya ba wajen bata tashi kulawar da sauran en uwanta.


Yanxu xumuncin su husna da Yah Abdullah ya dawo kamar da sosai yake kiran ta su sha hira har ya bawa ilham su gaisa, har rashin lafiyar nan da tayi sai da yaxo dubiyar ta shi kad'ai ban da ilham amman a ranar ya koma abuja.


Bayan ta warke garau ta koma skul, yayin da fadila ake ta xumud'in dawowar Yah ibraheem ita da gaske fah son shi take har tana tunanin ita ma yana son nata gashi har su hajia maamaa tace ta xa6a wa miji rana d'aya xata aurar dasu amman ba wanda yasan wa da wa ta had'a daga ita sai Allah suka sa ni tace sai ranar d'aurin auren kowa yaji wanda ta had'a shi da juna, fadila bata damu ba saboda sau nawa suke waya da Yah ibraheem a gaban hajia maamaa ko kuma wani lokacin ma Idan suka gama hira da hajia maamaa yace a bawa fadila don hka tana tunanin shi xa'a bata, toh masu karatu kun ji tunanin Fadila ko hkan mai yiwuwa ne....................




Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:47 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 47-48*



A cikin Wannan lokacin ne hajia maamaa ta yanke nan da sati biyu ne xa'a yi auren su husna,kuma sauran sati biyun Yah ibraheem ya dawo don hka nan iyaye da uwar gayyar wato hajia maamaa aka fara shirye shiryen biki da kuma dawowar Yah ibraheem, saboda tsananin murna hajia maamaa ta rasa inda xata sa kanta d'an lelen ta xai dawo gida nigeria kusa da ita ko dayaushe bakin ta cikin ambatar sunan Yah ibraheem take, hka ma fadila cikin tsananin farinciki take da ganin abin son nata don ta matsu taga yanda ya sake koma wa don rabon da ta ganshi an dad'e shi yasa take murna da xumud'in xuwan wannan ranar.


Duk wani had'a kayan lefe iyaye ne suka had'a sai dai abin wani mamakin hajia maamaa takanas ta tura mamee da mumy xuwa k'asar dubai had'a kayan lefen Yah ibraheem nan kuwa kowa ya sake jinjina irin k'aunar da hajia maamaa take yiwa wannan jikan nata, satin su mamee d'aya suka dawo da k'ayataccen lefe na gani na fad'a baxan iya kwatanta muku irin dukiyar da aka kashe a ciki ba tun daga kan akwatu nan xaka san an kashe naira a ciki kowanne lefe an jingine shi a part d'in hajia maamaa, Fadila sai rawar kai ake ganin lefen da aka kashe kud'i wajen had'a su duk na masoyin ta ne Yah ibraheem.


A yau sauran
k'wanaki uku Yah ibraheem ya dawo gida nigeria kuma a yau ne ranar Thursday aka yi kamu da walimah, husna idan ka kalle ta baxa ka tantance yanayin da take ciki ba ita dai gata nan sai yanda akace tayi take yi kawai jira take a fad'a mata wanda xata aura kuma an k'i sanar da ita.

Gaf da xa'a tashi daga kamun ne 'yan abuja suka k'araso wato yah Abdullah da Ilham yana gama parking suka fito (xaro ido nayi ni da sister sumy, kunsan abin da ya ba mu mamaki), ba komai ne ba sai ganin ilham da k'aton ciki a gaba tana ja da kyar ta dad'a xama wata babbar mace ta dad'a kyau alamun hutu da kwanciya hankali take ciki, shi kuma Yah Abdullah yana rik'e da bag d'in ta su nufo wajen kamun ae kuwa ana ganin su tuni 'yan uwa sun fara yi musu Oyoyo masu tsokana nayi, umman fadila kanwar su daddy cikin tsokana tace

"uhm su Abdullah ba kunya sai muka ga ilham da ciki da har da kukan ta baka so ka dunga cuta kamar xaka mutu, hala shi cikin duk a rashin so akayi yi shi? "

Nan kuwa aka kwashe da dariya ilham kuwa kunya ce ta lullu6e ta sunkuyar da kanta tayi tana murmishi, kamar ance ya d'ago kanshi karaf suka had'a ido da husna wanda tuni fuskar ta ta rikid'e xuwa tsantsar damuwa amman tana had'a ido da Yah Abdullah sai ta kakaro murmishin yak'e shi kuwa Yah Abdullah wata irin kunyar husna ce ta kama shi ya hau sosa k'eya daga K'arshe xame wa yayi ya gudu daga wurin.

Da sauri ilham ta rungume husna tana cewa "husna amarya nayi missing di'n ki sosai wlh "

Cikin murmishi ita ma husna tace "nima nayi kewar ki da har nayi fushi amman tun da naga babyn mu ne ya hana ki xuwa na hak'ura "

Cikin kunyar husna ilham tace " ni ae ba hka na so Yah Abdullah ne ya hanani xuwa "

Murmushi husna tayi tare da canja wani xancen har aka kammala kamu husna da Ilham sun manne da junan su duk inda husna tayi sai ilham ta bi ta nan mamee ta dunga yi wa ilham fad'a da da yanxu ba d'aya ba ne dole ilham ta samu waje d'aya ta xauna ba don ta so ba.

Da dare kuwa yah Abdullah ya dunga kiran ilham a waya amman saboda kunyar husna ta kasa d'aga wayar har ilham ta fahimta tayi mata magana ta d'auka wayar nan dai ta daure ta d'aga yake sanar da ita taxo bedroom d'in shi na da yana jiran ta su kwanta tun da tace toh tana xuwa ta kashe wayar gaba d'aya karshe sai ta kwanta kusa da husna don ita baxa ta iya tashi ta tafi wajen shi ba kunya take ji, nan dai bacci ya d'auke ta husna na xaune tana al'adar ta ta na tunani don abin ya xamar mata jiki dak'yar bacci ya iya d'aukan ta.

Shima nashi 6angaren Yah Abdullah da yaji shiru tak'i xuwa sai yayi kwanciyar shi don yasan kunya take ji amman yasan yau xai yi missing di'n ta don tun lokacin da suka shirya basu k'ara raba makwanci ba sai yau shi ma da hka bacci ya d'auke shi xuciyar shi cike da tunanin ilham din shi.


Washe gari juma'a kuma suka gabatar da Mother's Day wanda mamee , mumy da umman ilham suka had'a wani katon hall suka kama Anyi komai cikin tsari wajen ya k'ayatar sosai, amare sun yi kyau ba irin husna don ta had'u iya had'u ba k'arya mamee ta tsaya ta gyara d'iyar ta ta fatar nan sai shek'i take gwanin sha'awa.

Can naga en kungiyar marubatan da aka ji dasu a duniyar online en exclusive writers forum da kuma pure moment writers gasu a waje d'aya sun had'a Kai ba kyashi suna ta xuba surutu don kuwa akwai su da surutu lol, masu cin abinci da drinks suna yi nan kuma bayan mun cika cikin mu da abinci muka yi sallama da en exclusive da pure moment muka k'ara gaba don cigaba da bibiyar su husna don mu samu na rubuta wa bayan mun yi musu godiya tare da addu'ar Allah ya mayar da kowa gida lafiya.


Bayan an tashi daga mothers day ne kuma kowa ya koma gida muna jiran ganin gobe ko ya xata kasance dawowar Yah ibraheem da kuma d'aurin aure.




Washe gari asabar da misalin karfe 10 am jirgin da Yah ibraheem ya shiga yayi landing a airport, Yah Abdullah da Ilham sai fadila sune suka tafi d'auko shi, can na hango wani kyakykyawan had'ad'd'an guy cikin shigar shi ta suit bak'a amman ya cire coat din tana mak'ale a damtsen hannun shi yayi masifar kyau kamar wani balaraben k'asar turkey yana tafiyar shi cikin kasaita fuskar nan tashi wasai da ita *DR IBRAHEEM MUKTAR IBRAHEEM* kenan da sauri Yah Abdullah ya k'araso inda yake suna xuwa gaf da juna suka rungume junan su cikin tsananin murna da farin ciki sun d'auki tsawon mintuna 5 a hka sannan suka rabu da juna wajen motar suka K'arasa wanda fadila duk ta k'agu ta gan shi kamar ta tayi tsintsuwa ta dire a gaban shi.

Ilham kuwa kallon tausayi take bin ta dashi don tasan hajia maamaa baxa ta had'a ta aure da Yah ibraheem ba don shi sai ya za6a, kuma ba don wai fadila tana da muni ko wani hali na daban ba amman xuciyar ta ta fara hasaso mata wadda xata xama mallakin Yah ibraheem xuwa nan da en mintunan da basu gaxa talatin ba.


Suna k'arasa wa wajen nan ilham ta gaida shi tare da yi mishi sannu da dawo wa hka ma fadila tayi sai dai ita cikin yanga da iyayi tare da wani fari da ido cikin sakin fuska ya amsa sannan ya shiga gaban motar Yah Abdullah ya shiga su ma Ilham da fadila suka shiga sannan suka nufi gida ana ta hira a motar cikin nishad'i.

Suna k'arasa wa gida ba wanda ya ga Yah ibraheem saboda saurin da ake ya shirya don bai fi sauran mintuna 6 a d'aura auren ba don hka cikin sauri yayi wanka tare da shiryawa cikin wata lafiyayyar lallausar farar shadda k'al da ita sabuwa anyi mata aiki da farin xare yayi kyau iya had'uwa ya fito ango sak dashi takalmi da hula xuwa agogo duk farare ne sol ba k'aramin kyau yayi ba daga nan kuma sai masallacin da xa'a d'aura auren.

Karfe 11 dai dai aka sanar da d'aura auren Yah ibraheem da Asma'ul husna, sai fadila da yaseer yayan husna sannan raudah da mus'ab yayan ilham, d'aurin auren da ya tara dumbin jama'a na ban mamaki kuwa, daga nan kuma suka xarce da yin walimah tasu ta maxa bayan d'aurin auren, idan ka kalli Yah ibraheem maimakon ka karanto tsantsar 6acin rai a fuskar shi sai akasin hka don kuwa Yah ibraheem wata kyakkyawar fara'a ce shimfid'e a fuskar shi har Yah Abdullah yana mamakin shi kuma Yah Abdullah ba k'aramin mamaki yayi ba da yaji da ibraheem aka d'aura auren Idan yayi la'akari da tsantsar k'iyayyar da suke yiwa junan su toh me yasa ibraheem yake fara'a kamar ita ce xa6in shi Hka dai Yah Abdullah ya cigaba da tunanin shi.


A cikin gida kuwa husna tana xaune a bedroom d'in ta ta shirya cikin wani lace purple tayi matuk'ar yin kyau ta fito a amarya sak tana cikin d'aura d'ankwali taji ana maganar an d'aura auren taxo fita kenan daga d'akin don taji da wa aka d'aura auren................



Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:50 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 49-50*




Ana maganar an d'aura auren taxo fita kenan daga d'akin don ta ji da wa aka d'aura auren wane ya xama mijin ta a yanxu, bedroom d'in mamee ta nufa don ta tambaye ta da yake ilham dasu fadila, raudah basa nan inda take tun Kafin d'aurin auren suka fita xuwa part d'in hajia maamaa kunsan kuma husna ta dai na shiga part d'in.


Ta d'ora hannun ta kan handle di'n kofar shiga bedroom d'in mamee taji muryar mameen ta tana cewa "su wane kuma maxajen nasu daddyn husna ?"
Jin hka yasa husna dakata wa da barin bud'e kofar can ta tsinkayi muryar dady yana cewa "raudah da mus'ab, Fadila da yaseer sai husna da d'an lelen hajia maamaa "

Cikin jinjina maganar mamee tace "kana nufin husna da ibraheem aka had'a? "

Cikin tabbatar wa daddy yace "k'warai kuwa mameen yara haka......... "

Kafin ya K'arasa fad'i suka ji bummm an bugo kofar da karfi an shigo da sauri su mamee da daddy suka juya sai suka ga husna ce ta shigo idanun ta na xubar hawaye cikin rawar murya da tashin hankali matuk'a da k'arfi tace

"mamee daddy Kuna nufin Yah ibraheem ne miji na? "
"tabbas kuwa Hkne husna" Cewar daddy kenan
Mamee kuwa shiru tayi tana tunanin rigimar da xa'a tafka ta yanxu Kuwa.

Cikin kid'ime ma husna ta fara surutai tana cewa " toh Allah daddy abin da baxai ta6a yiwuwa ba ku rasa wa xaku aura min duk cikin en uwana sai mak'iyi na, na rantse da Allah duk wanda ma yayi wannan tunanin har ya had'a auren nan toh yanxu yaje ya warware shi tun Kafin na..............."

Kauuu taji an dalla mata mari Kafin ta dawo daga rad'ad'in marin taji an sake marin ta a d'aya kumatun wani wawan ihu husna ta saki wanda ya janyo hankalin mutanen dake palon mamee xuwa cikin d'akin, tuni husna ta rushe da wani kuka saboda tun da take da daddy bai ta6a dukan ta ba sai yau lallai ta 6ata mishi rai ba k'arami ba kuma har yanxu tana kan bakanta.

Cikin kakkausar murya daddy yace "ashe hka kike husna ina miki kallon mai hankali don uban ki hajiar tawa kike gayawa magana toh wlh ko xaki mutu baxa'a ta6a warware auren ba, kuma da kike cewa mak'iyin ki ne don Allah Idan an Kai ki gidan shi ki kashe shi don ki nuna wa mutane tsabar tsananin k'iyayyar da kike yiwa ibraheem "

Yana gama fad'in hka fuuuu ya fice daga d'akin, nan mutane en uwa suka fara rarrashin husna amman ina tuni ta fara xuba ihu tana birgima a k'asa tana surutai

"tun wuri ku je kusa wadda ta had'a auren ta warware shi don baxan ta6a amince wa da auren mak'iyi na ba wayyo Allah lallai na yarda yau hajia maamaa ta nuna min K'arshen k'iyayya daman tasan abin da ta shirya shi yasa take raba ni da masoya na"

Hannu mamee ta d'aga xata mari husna taji caraf an rik'e hannun tana d'aga kai ta ga ashe hajia maamaa ce ta shigo d'akin cikin sauri tace
"Zahra kada ki ta6a ta ku bar ni da ita kuma wlh kada wanda yasa hannu yace xai doke ta xan sa6a wa wanda yayi hkan ".

Hannun ta ta mik'a ta kamo hannun husna xata janyo ta jikin ta cikin wani xafin nama husna ta wufce hannun ta tare da dank'arawa hajia maamaa wata muguwar harara da idanun ta da suka yi jawur da su saboda kuka.

Cikin rarrashi hajia maamaa tace "Haba er husna ta takwara ta xo mu je ki fad'a min damuwar ki? "

Cikin d'aga murya husna tace " kada ki k'ara ambatar sunana ko kixo Inda nake bana son ganin ki tunda kin tsanane bakya son farinciki da"

Duk wurin aka yi tsit ana mamakin yanda husna take fad'awa hajia maamaa magana son ran ta amman bata d'auki mataki akan ta ba lallai husna ta dabance cikin xuciyar hajia maamaa.

Dak'yar hajia maamaa ta iya jan husna xuwa part d'in ta don ma hajia maamaa irin karkarfar nan ce duk husna ta fita a hayyacin ta sai surutai take kamar mahaukaciya sabon kamu tana kuka wiwi da majina tuni kwalliyar da aka tsara mata ta bi ruwan hawaye .

Nan fah husna ta dunga hauka a part d'in hajia maamaa gaba d'aya ta hargitsa hankalin mutane sosai wasu a xaton su haukace wa tayi ganin ana kok'arin rik'e ta mamee ta danna mata allurar bacci yasa da gudu ta shige bedroom d'in hajia maamaa ta rufe har da sa key a jikin kofar, ta dunga buga kofar da karfi da dukka hannun ta tana buga kanta jikin kofar tana cewa

"hajia maamaa ta tsaneni bata k'aunar farin ciki na ni ma na tsane ta bana k'aunar ta "
Wannan maganar da tayi tace ta tsani hajia maamaa aka tabbatar husna ta haukace su ilham, raudah, aunty rufaidah da fadila kuka suke wiwi ita Fadila abu Biyu ne ya had'e mata ga rashin Yah ibraheem ga kuma halin da husna take ciki dama ita ce husna da tafi kowa sa'a, nan fah kowa yayi tsuru tsuru can na hango hajia maamaa tana goge hawaye da ha6ar xanin ta tuni ta fara nadama akan biye wa ibraheem akan kudurin shi yanxu Idan husna ta haukace duk ita ce sila.

Ilham ce ta d'auki wayar ta ta kirawo Yah Abdullah cikin kuka take sanar dashi husna ta haukace cikin tsawa yace "what! "

Yanda ya fad'a ne yasa Ilham cire wayar ta a kunnen ta don kada ya kashe mata dodan kunne ta cigaba da kukan tausayin husna don ita shaida ce akan yanda husna ta tsani Yah ibraheem.

Cikin kid'ima Yah Abdullah ya janyo Yah ibraheem gefe yace " Kaiii yanxu ilham ta kirawo ni wai husna ta haukace "
Cikin rud'e wa Yah ibraheem yace "nooo abin da baxai ta6a yiwu ba mu tafi gidan "

Don hka cikin mugun tashin hankali suka tafi gida baxan iya kwatanta muku tsakanin Yah ibraheem da Yah Abdullah wayafi wani shiga tashin hankali ba.

Suna isa gidan part d'in hajia maamaa suka nufa kai tsaye ae kuwa dakyar suka kutsa xuwa cikin palon saboda mutane har suka K'arasa bakin kofar bedroom d'in da husna take ciki nan Yah Abdullah ya dunga kiran sunan ta amman shiru bata amsa ba ko motsin ta sun dai na ji ganin hka yasa Yah ibraheem ya kalli Yah Abdullah yace

"mu 6alla kofar "
Yana gama fad'in hka suka fara dukan kofar da karfi har suka yi nasarar 6allata sai dai kuma suna shiga suka ga wani abin da ya dad'a dugunxuma hankalin su yashe suka ga husna a k'asa tana xube ko numfashi bata yi ga kanta ya fashe jini yana xuba sosai ko alamar numfashi babu a tattare da ita cikin wani irin xafin nama Yah Abdullah da Yah ibraheem suka yi kan husna kowanne yana kok'arin d'aukan ta...................





_Kuyi hak'uri da wannan sai gobe Insha Allah xaku ji mu_



Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:54 AM] ‪+234 806 410 5193‬: 🍃DANGANTAKAR ZUCI 🍃


Written by
Aishat A Muh'd
♻E. W. F
&


Sumayya salees sadeeq
©P. M. L



page 51&52





Yah Ibrahim ne yyi nasarar d'aukarta, cikin kid'ima suka kutsa ta cikin mutanen suka nufi mota da ita, gaba d'aya gida ya d'auki kuka, banda innalillahi wa'inna ilaihi raji'un bbu abinda ke fita daga bakun nan mutane, tausayin Husna ya hana hajia maamaa sakat ita kanta kuka take, Iyayen su maza tsaye a wajen gidan suna gaisawa da yan Allah yasan alkhairi, ganin Ibrahim sukayi da Husna a hannu bbu alamun numfashi a tare da ita, da gudu suka nufi wajen suna tambayar lpy, daga Ibrahim har Abdullah bbu wanda ya iya sanar dasu abinda ke faruwa, cikin sauri Ibrahim ya shiga motar ba tare daya ajiye Husna ba ya riketa a kirjinsa yana kwalla. Abdullah ya shiga gaba ya ja suka nufi hospital.

Iyayen nasu suma suka shiga mota suka bi bayansu, gaba d'aya gidan biki ya zama na makoki.


Cikin gaggawa aka nufi emergency da Husna, anyi nasarar ceto ranta inda doctor

Please Login or Register in order to submit comment