Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi ko ma a jikin shi idanun shi sun rufe husna kawai yake buk'atar gani.

Cikin wani Murmishi da yake k'ara mishi kyau yace "husna ba gaisuwa ne ko har yanxu ba'a huce ba ne? "
Fadila da raudah suka fara kallon kallon juna mamaki ya dad'a kama su, a hankali ta d'ago kanta tare da watsa mishi kyawawan idanun ta akanshi ae kuwa wannan kallon da tayi mishi ba k'aramin k'ara gigita safwan yayi ba yaje ya k'ara kamu wa da sonta, kamar mai ciwon baki ta fara cewa
"bani waya ta "
Ta fad'i tana mik'a mishi hannun ta, gaba d'aya su Fadila da raudah a tsorace suke da yanda husna tayi mishi amman ga mamakin su sai suka ga ya saki wani murmishin tare da cewa
"ohhh na manta da ita tana gida kiyi hak'uri xan kawo miki anjima "

Wani kallon ta watsa mishi tare da sauke hannun ta sannan ta mik'e tana cewa su fadila" ku tashi mu tafi kunsan muna da abin yi koh? "

Tana gama fad'in hka tayi gaba su ma su raudah xasu tafi suna cewa "malam sai anjima "
Suka yi gaba gid'a kai yayi yana murmishi ya gyara tsayuwar shi tare da hard'e hannuwan shi a kirjin shi yana bin husna da kallo sam ranshi bai 6aci da abin da husna tayi mishi ba kuma yana fatan xai shawo kanta ta kar6i soyayyar shi Insha Allah, yana gama wannan tunanin ya nufi inda motar shi take kai tsaye gida ya wuce.

A cikin mota kuwa Fadila ce ta fara magana tace "husna yaushe kuka shirya ke da safwan Ahmad ne?
Cikin murmishi ta basu labarin abin da ya faru tsakanin su jiya da yamma, cikin dariya raudah tace
"ah su malam safwan Ahmad an fad'a tarkon so ae kuwa na taya ki murna samun namiji kamar safwan a wannan xamanin sai an tona ga kyau, kud'i, wayewa da ilimi ae kawai ki ba da kai bori ya hau "
"ae idan baki sani ba raudah nima fah yana burgeni kawai Kinsan jan ajin nan na mata xan yi mishi "
Gaba d'aya suka tuntsire da dariya tare da tafawa fadila na cewa "husna baki da dama wlh naji yace xai xo anjima ma"
"ehhh hka naji yace "
Cewar husna yayin da raudah tace "aja ajin da kulawa kada a hargitsa mana malam yaxo aji yana kiran husna maimakon koyarwar da xai mana"

Dariya suka sake tuntsire wa da ita sannan husna tace "Haba dai sai kace wani mara kai "
"Hmmm ke dai ki bar irin wad'annan mutanen idan suka fad'a soyayya idanun su rufe wa suke kamar irin su Yah ibraheem d'ina "Cewar Fadila

Tuni fuskar husna ta rikid'a xuwa tsantsar 6acin rai don an ambato mata mak'iyin ta don hka Bata k'ara cewa komai ba, raudah ce ta xunguri Fadila tare da yi mata alamar tayi shiru sai alokacin Fadila tasan tayi kata6ora don husna tasha fad'a musu kada su k'ara ambatar sunan Yah ibraheem Indai suna tare Idan sun san hirar shi xasu yi to su bari ta bar wajen, ba wanda ya k'ara magana har husna tayi parking suka fito daga motar har tayi gaba ta jiyo tana cewa "ku fad'a wa ilham anjima mu had'u a part d'in mu sai mu k'arasa shirye shiryen namu "
Fuskar ta ba fara'a take maganar don an ta6o mata wani abu da ya shige a cikin rayuwar ta, nan suka amsa da toh sannan kowanne ya shige part d'in su ita kuwa fadila part d'in hajia maamaa ta wuce .


_5:00 na yammacin ranar alhamis_

Husna ce kwance kan kujera ta d'ora kanta a cinyar mamee driver yayi sallama a bakin kofar palon mai aikin mamee ta amsa sallamar tare da k'arasa wa ta bud'e kofar nan yake sanar mata wani na kiran husna a waje, nan ta dawo cikin falon tana fad'i wa husna sak'on yatsina fuska tayi tare da cewa "Kice bana nan kawai "
Har ta juya xata tafi ta fad'a wa driven da aka aiko taji mamee na cewa "larai ki ce tana xuwa a kice malam idi drive ya kai shi wajen da dadyn ta yake xama yana huta wa "
"toh hajia "
Cewar larai sannan taje ta fad'a wa driven, ita kuma mamee ta umarce ta da takai mishi abin motsa baki, sannan ta jiyo da kallon ta kan husna tace
"tashi maxa ki shirya ki je bana son wulakanta mutane "
"amman mamee Kinsan dai............. "
Kafin ta K'arasa fad'i mamee tace "ni dai nace ki je "
Hka husna ta mik'e tsaye ta nufi bedroom d'in ta wani hijab ash ta sanya mai hannu ta d'an fesa turare sannan ta fito ta xuwa wajen farfajiyar gidan kai tsaye inda wurin hutawar daddy yake ta nufa wuri ne mai kyau wanda aka k'awata shi da abubuwa masu Kyan gani a ido da yake ya juya baya bata ga fuskar shi sai da taje daf dashi tayi mishi sallama da sauri ya d'ago kai tare da amsa sallamar had'a ido suka yi sunyi kusan second talatin suna kallon junan Kafin husna ta fara janye idonta ta ja kujera ta xauna tare da cewa
"ina yini? "
Cikin murmishi yace "lafia qlau ,oh sai yanxu aka ga ra'ayin gaida ni"
Kauda kanta tayi bata ce komai ba nan ya mik'a mata wayar ta da key di'n motar ta sannan a cikin wannan lokacin safwan Ahmad ya samu damar amayar wa da husna abin da yake cikin xuciyar shi tare da rok'an ta kan ta soshi ko da rabin son da yake mata ne nan duk yabi ya rikita husna da xafafan maganganu har ta kai ta amince da shi a lokacin ta gane wane safwan Ahmad kuma taji xuciyar ta ta amince dashi duk da kuwa har yanxu son Yah Abdullah yana nan mak'ale cikin xuciyar ta nan dai basu rabu ba sai da ya yarda husna ta amince mishi kuma a hankali xai koyar da ita son shi da hka suka rabu cikin kaunar junan su.

Tana shiga part d'in su mamee ta kalle ta sannan tace "ke da bakya son fitar dad'e war me kika yi "
Kunya ce ta lullu6e husna ta ajiye key da wayar kan table ta gudu d'aki yayin da mamee tayi dariya kawai tana gode wa Allah da ya kawo wa erta chanji acikin rayuwar ta. Nan fah soyayya aka bud'e shafin ta tsakanin husna da safwan soyayya yake nuna mata ko acikin aji ne yana d'aukan darasi sai dai ka ga suna jifan juna da murmishi yana kashe mata ido tare da d'aga mata gira gaba d'aya bata iya sake wa wani lokacin sai ya matso kusa da Inda take xaune kamar xai shige sai ya d'an rankwafa saitin kunnen ta ya furta mata kalmar "i luv u baby nah kinyi matuk'ar yin kyau " da dai ire iren kalmomin soyayya ita kuma sai ta lumshe idon ta tana murmishi alamar taji dad'in abin da yace mata, su Fadila da raudah kuwa duk akan idon su hkan yake faruwa ba k'aramin burge su suke ba sai an fito suyi tayi musu tsiya sai dai su kalli juna suna dariya.

Gaba d'aya su husna yanxu ba xama sai shirye shiryen biki suke saboda an shiga satin bikin duk da ba wani programs da yawa xasu yi ba daga kamu, walimah sai dinner hka kawai suka shirya don xuciyar husna sam ba dad'i don ma safwan yana d'ebe mata kewa, ranar alhamis suka gabatar da kamu babu ango Yah Abdullah ba kamar shi kowa bai ji dad'in rashin xuwan Yah Abdullah ba, hka Washe gari Friday suka gabatar da walimah a farfajiyar gidan kuma ranar ma yah Abdullah bai xo ba, ran iyayen nashi Yayi matuk'ar 6aci musamman mai gayya mai aiki hajia maamaa.


_washe gari misalin karfe 11:00_

Aka d'aura auren Yah Abdullah da Ilham, husna tana jin sanarwar an d'aura auren ta kulle kanta a d'aki tana kukan rabuwa da Yah Abdullah har abada ta rasa shi kenan sai da taci kukanta ta more sannan ta fito kallo d'aya mamee tayi mata ta fuskanci abin dake damun erta ta girgixa kai tayi cike da tausayin husna.

Bayan d'aurin auren da mintuna 20 Yah Abdullah ya shigo garin kaduna yana sanye cikin shadda fara sol da ita yayi kyau sosae duk da uwar ramar da yayi kuwa, nan fah iyayen shi da hajia maamaa suka dunga yi mishi fad'a sosai kallo d'aya xaka mishi kasan baya cikin nutsuwar shi yana d'auke da tarin damuwa a kan fuskar shi don idanun shi sunyi jawur dasu kamar ba ango ba, yana son sa husna a idon shi amman ya rasa inda xai same ta saboda gaba d'aya gidan a cike yake da mutane, lokacin da xa'a tafi dinner kuwa dakyar ya shirya xai je sai da abban shi yayi mishi tatas sannan ya amince ba don yaso ba Allah sarki Yah Abdullah so masifa ne wani lokacin.

Wajen dinner d'in ya had'u sosai ango da amarya suna xaune sun yi matuk'ar yin kyau duk da kuwa kowannen su tarin damuwa akan fuskar shi, kamar ance ya d'ago kanshi idanun shi suka gano mishi abin da yayi matuk'ar girgixa shi ya kuma kid'ima shi ba nan take yaji wani kishi ya rufe shi ba komai ya gani sai husna tare da safwan akan table d'in daban su Biyu suna xaune daga ni hirar soyayya suke yanda suke jefan junan da wani irin kallo soyayya tuni kan Yah Abdullah
ya fara juya wa.................



Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:32 AM] β€ͺ+234 806 410 5193‬: πŸƒDANGANTAKAR ZUCI πŸƒ


Written by
Sumayya salees sadeeq
&

Aishat A Muh'd



Page 41&42




A hankali ya fara furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan waye suke tare da Husna, wato shi yana chan dauke da soyayyarta a xuci amma ita har ta samu wanda take so, daga ganin yarda suke xuba soyayya yasan a kwai shakuwa a ciki, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, xaman gurin ya gundiresa, A hankali Ilham ta fuskanci rashin nutsuwarsa, cikin nutsuwa ta d'ago ido ta kalle shi, gani tayi b'acin rai a fuskarsa idonsa yyi ja, duk da dama da jan idonsa yaxo kasancewar kukan daya sha bbu dare bbu rana.
Baisan tana kallonsa ba, dan ya bada nutsuwarsa ga duk wani movement na Husna da Safwan.
Zuciyar Ilham gaba d'aya bbu dad'i, ganin tsantsar kiyayyar da Yah Ibrahim ke nuna mata, a hankali ta juya idonta inda taga yana kallo, ganin Husna tayi da Safwan suna kashe selfie cikin annushuwa da jin dad'i, da gani basu da wata matsala, bbu kuma abinda suka sa a gaba sai soyayya.
Kwalla ce ta cika mata ido, ita dai ta shiga uku, wane irin aure xatayi? Duk da tana son Yah Ibrahim amma hajia maamaa bata kyauta mata, tasan xata rayu cikin kunci, data sani tabarshi ya auri wacce yake so.



Kasa jurar ganin Husna da Safwan yayi, cikin sauri ya dauke kansa yana juyowa suka had'a ido da Ilham, ganin idonta da Kwalla ya gane taga abinda yake kallo, tausayinta ne ya kamashi. Ilham bata da matsala, komai nata ya masa, kawai shi baya sonta ne Husna yake so, amma Ilham ko ba kanwarsa bace yanxu akwai aurenta ne a kansa,dole ya bata kulawa.

Basar wa yayi ya tambaye ta" mai yasa kike kuka? "

Murmushi tayi" ba kuka nake ba Yah Ibrahim, abune ya fad'a mini a ido"

Shiru yayi yana naxari, cikin sanyinta tasa gefen net d'in ta ta goge hawayen.

Duk abinda ke faruwa mom da mamee suna kallo, cux a waje d'aya suke kuma a kusa da ango da amarya, Ilham tafi basu tausayi, cux Mace xata iya auren wanda bata so taji dad'i, in har shi yana sonta,amma ace mijin ma bata tata yake ba ai akwai matsala.


Taro yayi taro anci ansha, anyi raye raye da bisa tsari, gurin ya tsaru 11pm aka tashi a wajen.

Safwan dakanshi yakai Husnarsa gida, ganin dare yayi yasa basu tsaya wani hira ba ya mata sallama sai da safe, dan gobe ne xa'a kai amarya gidan mijin ta dake Abuja.


Fitar ta a mota ta fara yima Safwan bye bye, duk a idon ya Ibrahim, Cikin sauri Husna ta nufi part d'in su dan chanja kaya dan taji alamun period dinta yaxo, tana shiga corridor d'in da xai billa da ita dakinta taji an rike hannunta, xatayi ihu taji an tushe bakinta, sosai ta tsorata ta fara kiciniyar kwatar kanta. Jin kamshin turaren Yah Ibrahim yasa hankalinta ya kwanta. Yah Ibrahim ka cikani please, cikata yayi ya xuba mata mayattatun idanunsa da suka rine, cikin sarkewar murya ya fara magana.

"Husna ashe dama akwai ranar da Allah xai nuna mini kina tarayya da wani bayan ni, duk soyayyar da muke wa juna ina chan ina fama da sonki amma Husna ashe kina nan kin mallakawa wani xuciya ki? Husna ina sanki, wallahi baxan iya rayuwa ba idan bbu ke........ "dakata Yah Ibrahim, kasan me kake cewa kuwa, aure ya riga ya haramta tsakanina dakai, Ilham itace matar ka, ita take bukatar kulawarka, ita take bukatar ka firta mata wadan nan dad'ad'an kalaman ba Husna ba, Yah Ibrahim ban taba son wani d'a namiji ba sai kai, ban taba mallakawa kowa zuciyarta ta ba sai kai, akanka na fara so, naso ace munyi aure dakai, sai dai kaddara ta riga fata, "hannu tasa ta share hawayen ta," Safwan malami nane, kuma yana debe min kewar rashin ka," please Yah Ibrahim, ka manta mun taba soyayya dakai, ka rungumi matarka ka bata kulawa please" fashewa tayi da kuka ta wuce ciki tabar Yah Ibrahim a tsaye, gaba d'aya jikinsa ya mutu, sosai ya hango zallar kaunarsa a idon Husna, sai dai yasuyi, hajia maamaa ta gama cutarsu, ta tarwatsa farin cikin su.


Husna na shiga daki ta baje akan bed dinta ta fara kuka mai cin rai, soyayyar Yah Ibrahim ce take nukurkusarta, shi yasa tunda ya dawo taki yarda su hadu, sai da tayi kuka mai isarta sannan ta nufi toilet.
Washe gari

An kai amarya Ilham dakin mijin ta bayan nasihohi da fad'a da itayenta sukayi mata, shima Ibrahim yasha nasiha akan ya rike Ilham bisa amana, ya manta duk abinda ya faru, hajia maamaa harda kukan farin ciki wai yau burinta ya cika,(ni da sister mukace kaji wannan tsohowar, suna kukan bakin ciki tana kukan murna) lol. Sosai nasihar ta ratsa Ibrahim ya kuma dauri aniyar kula da Ilham.

Husna da Safwan kam ana tare, dan har Abuja shi yakaita dasu rauda, sosai soyayyar da Safwan ke nuna wa Husna take basu mamaki, lallai Husna tayi sa'a, Allah yayi mata chanji na alkhairi, dan suna ganin indai ta auri Safwan to tagama mure jin dad'in dunia sai dai ta nemi lahira. Soyayya da shakuwa tayi malemale a xuciyar masoyan, har suna jin baxasu iya rayuwa ba batare da juna ba.




Kuyi hakuri da wannan mun san dama kuna hakurin to ku kara, ku kuma cigaba da binmu dan jin karshen labarin mu.



Sumayya salees sadeeq
&
Aishat A Muh'd
[3/10, 6:39 AM] β€ͺ+234 806 410 5193‬: πŸƒ *DANGARTAKAR ZUCI*πŸƒ



*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 43-44*



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har akayi wajen wata uku da bikin Yah Abdullah da Ilham, yanxu husna ta cire Yah Abdullah gaba d'aya a cikin xuciyar ta soyayyar su kawai suke xuba wa da safwan din ta, a yanxu kusan kowa na gidan yasan da soyayyar safwan da husna kuma sun amince dashi sosai saboda mutum ne na gari ga hankali da nutsuwa, mamee taji dad'in ganin shi a matsayin wanda xai auri erta.

Ana cikin hka safwan ya sanar da husna ta fad'a wa su dady xai turo iyayen su ayi magana, husna bata yi k'asa a gwiwa ba ta sanar da mamee maganar ita ma mamee ta fad'a wa daddy a lokacin da ta sanar dashi a lokacin yana kok'arin shiga part d'in hajia maamaa don hka bayan ya shiga part d'in ya tarar da yayun shi Abba 1 da Abba 2 bayan sun gaisa sai yake cewa

"maamaa daman yaron da yake son husna na ne yake son ya turo iyayen shi "

Cikin rashin fahimta hajia maamaa tace "wane yaro kuma daman husna ta tsayar da wanda xata aura ne? "

"Ehhh tabbas mun sha gaisawa dashi yaron yana da kirki malamin su ne ma" Cewar Abba 1 wato abban su Yah Abdullah.

"Humm ae kuwa abin baxai yiwu ba saboda husna na riga da na xa6a mata wanda xata aura kuma kada wanda ya fad'a mata, su dai iyayen yaron xaku fad'a wa Idan lokaci yayi kowa xai sa ni " Cewar hajia maamaa

Abba 2 wato abban su ilham yace "Haba maamaa taya xa'a yi mata hka da farko suna soyayya da Abdullah kika k'i aura musu juna kuma tayi hak'uri da hkan Har ta dad'a xa6ar Wanda xata aura a karo na biyu don Allah ki barta ta auri wanda take so"

"kaiiiii mustapha " hajia maamaa ta daka mishi tsawa sannan ta cigaba da cewa "sam kada na k'ara jin wad'annan maganganun a bakin ka ina da ikon da xan xartar da komai a kan ku don hka na riga da na yanke hukunci "

Cikin ladabi Abba 2 yace "Allah ya huci xuciyar ki yi hak'uri Allah ya sa hkan shi yafi alkhairi Allah ya bata hak'urin jure wa"

"Ameeen " suka amsa a tare sannan daddy yace " ibraheem ya fad'a muku last month d'in nan xai dawo "
Tuni fuskar hajia maamaa ta fad'ad'a da fara'a sosai tace "Masha Allah yau ba mu yi waya ba shi yasa Allah ya dawo mana dashi lafia"

"Ameeen maamaa "
Daga hka suka cigaba da hira wani xuwa wani lokacin sannan kuma suka tashi suka nufi 6angaren nasu da yake weekend ne, lokacin da daddy ya fad'a wa mamee abin da suka tattauna da hajia maamaa da en uwan shi sam mamee bata ji dad'in hkan ba ta so ace wannan Karon an bawa 'yar ta damar xa6an mijin aure,amman bata da abin cewa sai dai addu'a kawai.


Bayan k'wana 2 da hkan iyayen safwan suka xo sun samu tar6a sosai a wajen su Abba bayan an gaisa sun ci sun sha sannan suka bijiro da buk'atar su ta neman aure, nan su Abba suka fara da basu hak'uri sannan suka fad'a musu anyi mata miji amman ita yarinyar bata ma sa ni ba, hka suka baro gidan cikin sanyin jiki suna tunanin sanar da safwan wannan mummunan labarin.

Da murnar shi ya tari iyayen nashi da suka dawo amman ganin damuwa akan fuskar tasu ya sa jikin shi yin sanyi nan dai suka daure tare da fada mishi kafin su ankara sai ganin safwan suka yi ya dafe xuciyar shi tare da lumshe ido xai fad'i baban shi ya taro tare da fad'in
"SAFWAN!"

Da k'arfi ya furta hkan cikin wani irin yanayi safwan yace "na'am Abba na ina rok'an ka ka taimaka min kada na rasa husna ina son ta xuciya ta xafi take min sosai "

Sai ga hawaye yana xuba a idanun safwan wani mugun tausayin shi ne ya kama abban shi da mahaifiyar shi nan fah suka dunga rarrashin shi tare da bashi hak'uri dak'yar hawayen suka dai na xubo wa sai kukan xuci yake don shi kad'ai yasan abin da yake ji a cikin xuciyar shi yana son husna ba Kad'an ba ashe ba rabon shi ba ce an bawa wani ita, hka yayi ta sumbatu sai dak'yar bacci ya d'auke shi, iyayen nashi sunyi jugum jugum basa son damuwar d'an nasu ko Kad'an.


Cikin k'wanakin nan safwan ya rame sosai abin gwanin ban tausayi ko abincin kirki baya iya ci kullum cikin tunanin yanda xai rabu da husna yake, gashi ko kiranta yak'i yayi a waya.

Ganin k'wana 2 safwan shiru bai Kira ta ba yasa hankalin husna ya tashi sosai nan ta kirawo shi awaya yak'i ya d'auka tuni hankalin nata ya k'ara tashi sosai ta rasa yanda xatayi K'arshe tana kuka ta fad'a wa mamee safwan ko lafia baya d'aukan wayar ta, kallon tausayin 'yar ta tabi husna dashi baxa ta iya fad'a mata K'arshe rarrashin ta tayi.


Ko dayaushe cikin kiran safwan take shima nashi 6angaren kasa daure wa yayi ya d'auki wayar bai 6oye mata komai ba ya sanar da ita duk abin da yake faruwa husna batasan lokacin da ta yar da wayar ba da gudu ta fice daga d'akin nata.............





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[3/10, 6:42 AM] β€ͺ+234 806 410 5193‬: πŸƒ *DANGARTAKAR ZUCI*πŸƒ



*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 45-46*


Da gudu ta fice daga d'akin nata hankalin ta a matuk'ar tashe bata tsaya a ko'ina ba sai bedroom d'in mamee tana shiga ta tsaya tana xuba uban haki amman ta kasa magana, mamee wadda take xaune kan sofa tana waya ta d'ago kanta da sauri don ganin wane tana ganin husna ce idanun nata sai xubar hawaye suke yasa ta saurin yanke wayar tare da tashi da sauri ta kamo hannun husna ta xaunar da ita kan sofa tare da dauko ruwa ta tsiyaya a cup ta bawa husna bata yi musu ba ta kar6a tasha sannan mamee ta kar6i cup d'in ta ajiye lokacin ne husna ta samu hawaye masu xafin gaske suka xubo daga idonta tare da sakin wata ajiyar xuciya.

A nutse mamee ta kalli husna sannan tace "Ya akayi 'yata, me ya faru sanar da ni?"

Cikin shashshak'ar kuka husna tace "mamee da gaske ne hajia maamaa ta xa6a min mijin aure har an sanar da safwan? "

Toh fah abin da ake gudu ya xo Cewar mamee a cikin xuciyar ta Kafin kuma ta Kalli 'yar ta ta cikin tsananin tausayin ta tace "hak'uri xaki yi husna tabbas abin da safwan ya fad'a miki gaskia ne "
Hannu husna ta d'ora akai tare da furta "wayyo Allah na wai ni kad'ai ce ba'a so a gidan nan ne daman nasan hajia maamaa ta tsane ni duk cikin jikokinta " ta fad'a cikin kuka.

Kamo ta mamee tayi ta rungume ta tana bubbuga bayanta cikin sigar lallashi tace "ba son ki ne bata yi ba asali ma daga ibraheem sai ke Kune kuka fi soyiwa a cikin xuciyar ta a duk cikin jikokinta ina son don Allah kiyi hak'uri ki danne xuciyar ki husna"

Cikin sauri husna ta janye jikin ta daga na mamee sannan tace "mamee nah kina so ne na kar6i xa6in hajia maamaa na auri wanda bana so kuma bansan da wane xata had'a ni auren ba, haba mamee ta raba ni da Yah Abdullah na hak'ura yanxu kuma ta sake raba ni da masoyina a karo na biyu safwan anyi min adalci kenan? "

Cikin kuka sosai husna take wannan maganar, hannun ta mamee ta kama tare da cewa "Duk na sani husna amman hkan ba xai hana ayi wa hajia maamaa biyayya ba na rok'e ki husna da kiyi hak'uri, a matsayina na mahaifiyar ki ina rok'an ki wannan alfarmar da kiyi hak'uri ki kar6i xa6in ta ina nan ina miki addu'a kuma Insha Allah xaki ga dai dai a rayuwar ki "

Hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta cikin tausayin kanta da murya a shak'e saboda kukan da tasha ta Kalli mamee wadda ta xuba mata ido tana kallon ta don taji abin da xata ce sake rik'e hannun mamee tayi tare da cewa
"Shikenan mamee nah naji na yarda da xa6in ta mamee

Please Login or Register in order to submit comment