Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita nakeson kasancewa har k'arshen rayuwata,
wani irin abune ya soki zuciyar Suhailat a fusace tace toh
shikenan naji yanxu inaso kasanar dani tsakanin
RAFEE'AT da SUHAILAT wa kake so??
Wani murmushin takaici Hafeez yayi yanuna Suhailat da
d'an yatsa yace what do u mean kina nufin zand'auke
kine inbar Rafee'at to bari kiji indai wannan shine
tunaninki toh gwnda tunda wuri kicanja shi domin kuwa
Rafee'at wani b'angarece ta rayuwata bazantaba iya
rabuwa da ita ba koh da kuwa sama da k'asa zata had'e,
cike da masifa Suhailat tace ohhh haka ma zakace toh
wlh inhar baka zab'eni amatsayin wacce zaka aura ba
toh wlh inatabbatar maka dacewa sai ka tafka babbar
hasara arayuwarka domin bakasan koh ni wacece ba
indai matuqar ina raye wlh babu kai babu auran waccan
k'idahumar.
Hafeez murmushi yayi ya dakatar da Suhailat yace
dakata mallama inamai gargadinki kadaki k'ara cewa
matar aure na k'idahuma, maikike zato dama haka kawai
zan aureki banda tabbas din koke wacece Rafee'at kuwa
tunbata mallaki hankalin kanta ba Allah yard'auramin
sonta so ni inaganin bbu yadda za'ayi Na zab'eki nabar ta
kingane ae dan haka ki kwntar da hnklinki ayi taron nan
lpy kikoma hannun mahaifanki.
Hafeez nafadin haka yasa kai yafice zuciyarsa gaba daya
ajagule.
Yana fita falo yanufa, mommy naganinsa tadubesa da
murmushi tace yauwa Hafeez ynxu kuwa nake k'okarin
nemanka, kaga tun mutane basu fara taruwa ba inaso
kaje oasis bakery ka ansoma Balkisu birthday cake dinta.
Hafeez yace toh Momy bari inyi sauri inje indawo, karaff
Balkisu tace yaya Hafeez plsss nima zanbika da sauri ma
Aysha (ummi) autar Momy tace yaya nima zanbika, a
hnkli Hafeez yaduk'a wajan autan Momy yace swry
ummi bazan iya zuwa dake ba sauri nakeyi zanje nadawo
kinji karki damu zanzo miki da ice-cream, gyada masa
kai tayi takoma gurin momynta tahau saman kujera taci
gabada wasanta. Balkisu kam binshi tayi abaya cike da
zumud'i ta marairaice fuska plsss Yaya znbika wlh baxan
dameka da surutu ba. Okay kawai yace da ita har yanufi
hanyar fita kuma chan sai yajuyo ya kalli Rafee'at wacce
kanta ke k'asa tak'i yarda suhada ido sbd fushi takeyi
dashi, a hnkli Hafeez ya kira sunanta Rafee'at d'ago knta
tayi a hnkli tadubesa shikuwa Hafeez naganin tadubesa
yahada hannayensa alamar neman afuwa sannan yayi
mata nuni da inyadawo zaimata bayanin komai,
murmushi tayi maisauti sannan ta gyada masa kanta.
Da sauri yabar falon yana murmushi, sunafita yanufi
parkn spc yadauki mota suka nufi oasis.z
Abangaran Suhailat kuwa waya tadingayi tana fad'awa
frnds dinta cewa Hafeez yaci amanarta ya yaudareta
ashe yana da mata baifada mata ba, dukk wnda tak'ira
sai dai yabata hkri, ganin haka yasa takira daddynta
tafada masa maganganun da sukayi matuk'ar girgiza shi
hnlkinsa gabadaya yagama tashi, Suhailat kam nagama
fadin sak'onta takashe wayarta, gabadaya lkci daya
tazama zautacciya hnklinta yagama fita akanta sbd zafin
kishi, hakanan tacire d'an kwalin kanta tanata faman
sambatu da neman mafita domin kuwa acewarta da taga
auran Hafeez da wata gwnda taga mutuwarta dan haka
da sauri tabud'e k'ofa tanufi hnyar kitchn koh da
shigarta tadauki sabuwar wuqa sai shek'itakeyi cikin
zuciyarta tace koh inbisu falo inkashe kowa da kowa
sannan nima inkashe Kaina, har tafara fita a kitchen din
kome ta tuna kawai saita koma kitchen din nan tafara
mgn cikin sambatu wlh sai dai mumutu gabadayanmu
bazai yuwu namutu nikadai ba, surutan da takeyine
yajawo hnklin Iya ladi mai aiki wacce take k'okarin
wanke babbar tukunya awaje kasancewar tana bakin
window din tawaje hakan yabata damar lek'awa
bak'uwan nance tagani tana k'okarin bude silinda na gas,
ga kuma surutan da wannan baquwar takeyi hakan ya
bama iya ladi tsoro dan haka tafara ihun Neman
taimako tafadin Hajiya! Alhaji! jama'a yar k'unan bak'in
wakece wannan bakuwa da gudu tanufi cikin gda don
tasanar dasu ta'addancin da ake shirin aekatawa
kasancewar da dan taxara shiyasa take gudu tananeman
agaji.
Mommy ce tafara jiyo ihuun neman taimako kmr iya
ladi ce a kitchen ae da gudu suna Kalmar salati suka nufi
kitchen din gabadayansu, mommy na bud'e k'ofa
Suhailat na cinnawa gas din ashana ae kuwa take anan
gdan yayi wata irin girgiza tamkar antada bomb take
gdn Yakama da wuta ta ko'ina.
Kafin iya ladi tak'arasa ciki tuni Gas din yatashi take
itama tasamu nata domin kuwa girgizan nan yasa tayi
wata mummunan faduwa Wanda yayi sanadin sumanta..
Inallilahi wa'inna ilaihiraji'un.......
®NWA
[11:52AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:08AM, 7/15/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣3⃣
Cikin tsananin tashin hankali gabad'aya jama'ar unguwar
kowa yafito, kowa sai mamakin faruwar wannan
al'amari yakeyi, Alhaji shehu makocin su shine yayi
tunanin kiran fire servirce(motar yan kwana-kwana)
bayan shud'ewar wasu yan mintina kuwa sai ga sunan da
gudu sunshigo cikin layin ba su tsaya jinkirin komai ba
suka zago babban tiyo dinsu sukafara zuba ruwa
tasaman gdan, Dakyar akasamu wutan nan ta mutu
bayan yan wasu mintuna kenan wasu maza guda uku
ma'aikatan fire service cikin shirinsu na aiki suka tunkari
hayakin suka afka cikin gdan.
Koh da shigarsu suntarar da gawawwaki tare waje guda
gabadaya sunk'one ta yadda koh fuskokinsu ba'a iya
ganewa, haka nan suka dibi gawawwakin bisa abin
daukar gawa suka fitar da su izuwa waje, sai da suka
gama kwashesu sannan sukashiga bincike acikin gdan.
Suna cikin lalubensu ne Allah yasa sukaci karo da iya
Ladi wacce ke kwance sumammiya da gudu suka k'arasa
wajenta ganin cewa tanada sauran numfashi yasa sukayi
saurin dauketa don bata taimakon gaggawa.
Hafeez ne tafe shida Balkisu sai surutu take zuba masa
Hafeez yadube Balkisu yace ohh Balkisu ke kam daban
kike ina yanxun nan da zamu fito kikamin alqawarin
cewa baxaki dameni da surutu ba sai gashi tunba'aje koh
inaba kin isheni da surutu ynxun nan sai in ajiyeki anan
ki hau mashin, dasauri Balkisu tasa tafin hannu tarufe
bakinta tana dariya. Chan kuma Balkisu tajuya bayan
mota tazura hannunta a sit din baya tadauko robar ice-
cream wanda suka siyoma autar Momy.
Balkisu tace amma gsky Yaya Hafeez nima zansha roba
daya, Hafeez girgiza kansa yayi yace ohh gsky babu
rabonki anan wannan dukk na aura ne. Balkisu ta turo
baki cike da shagwab'a wai ita tayi fushi.
Hafeez dai bai kulata ba domin hnklinsa gabadaya
yanaga Rafee'at BURINSA bai wuce ya Isa gda da wuri ba
don yasamu damar bawa Rafee'at hkri sannan dole ne
yasamar wa Suhailat ticket a yau din nan gobe takoma
garinsu da irin wannan tunanin Hafeez yashiga cikin
layinsu.
Dan dazon jama'a ne suka k'awanye ko ina na cikin
anguwar cike da mamaki Hafeez yadinga horn ana bude
masa hanya har ya samu ya isa k'ofar gdansu, inalillahi
wa'inna ilaihiraji'un shine kawai abinda Hafeez ya iya
furtawa dagudu suka fito atare shida Balkisu suka nufi
cikin gda, gawawwaki suka gani jere a kwance anrufe da
fararen kyalaye Hafeez ne ya nufi wajen da gudu
yanafadim meyafaru ne mekefaruwa haka? gabadaya
illahirin jijiyoyin wuyansa dukk sunfito bude gawarwaki
yafarayi daya bayan daya Hajiya Hauwa yafara gani
gabadaya illahirin kammanunta sunsauya gabadaya
tak'one nan Hafeez yashiga girgizata yana fadin plss
uwata kitashi dan Allah haka yashiga bude gawawwakin
yana sambatu, Balkisu kam Sam tak'i kuka tsayawa tayi
kyam waje guda chan kuma tafara tafiya a hnkli ta isa
kan gawar autan Momy tabude ta nan Balkisu tashiga
jijjigata tanafadin ummi! Autan Momy! Kitashi ga ice-
cream nakawo miki plsss kitashi qanwata kitashi!! wlh
wasa nake miki bazan sha ice-cream dinki ba. Dasauri ta
Isa kan gawan iyayen nata natafara fadin Abba kace
ummi ta tashi plss Momy ya kukayi shiru ne kunmanta
yau ne birthday na Dan Allah karkumin wannan wasan
kutashi mushiga cikin gdanmu Yaya Hafeez kace Umma
ta tashi anty Rafee'at ba ynxu kikamin alqawari zaki kaini
park ba plss kitashi anty Rafee'at nan tashiga ihuuu
tanafadin iyayenta sutashi.
Jama'ar anguwan kowa ya tausaya musu, a hnkli cikin
tausayawa Alhaji Shehu yakaraso garesu yana lallashinsu
Hafeez Balkisu kuyi hakuri iyayenku kam sun amsa kiran
mahaliccinsu
Hafeez da Balkisu atare suka fadi k'asa summanmu. Yan
cikin anguwansu kam wasu sai dasuka zubda kwalla sbd
tsananin tausayinsu domin kuwa dukk wani dake cikin
anguwar matuqar yasan family din Alhaji Abdullahi
Shariff toh tabbas yasan irin wannan family din ake kira
Happy family.
Da gaggawa motar ambulance ta kwashesu akayi asibiti
dasu don basu taimakon gaggawa, inda kuma Alhaji
shehu makocinsu yayi tsaye agaban wannan gawarwaki
har sai da ya tabbatar ankaisu makwancinsu, Allahu
Akbar.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 7/16/2016] MUNAY✍
🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣4⃣
La'illaha'ilallah muhammadur-rasulullah S.A.W, shine
abinda iya ladi tafara furtawa lkcin da tadawo cikin
hayyacinta da gudu nurse din dake kusa da ita taje ta
kirawo Dr, Dr da xuwansa kuwa nan yashiga yi mata
wasu yan gwaje-gwaje yana gamawa ya girgiza kansa
nan yajuya ga nurse din dake tsaye yabata umarnin
tamiqo masa allura da hanzarinta kuwa ta miqo masa
take anan yasakeyi ma iya ladi wata allurar kankace me
tuni bacci yadauketa..
Balkisu tunkafin su isa asibiti tasamu farfad'awo sa6anin
Hafeez wandake kwance cikin halin RAYUWA Ko
MUTUWA! da isarsu asibitin wasu maza majiya k'arfi
suka taimakawa nurses din nan aka daura Hafeez bisa
gadon daukar marasa lpy I.c.u suka nufa dashi kai tsaye.
Abangaran Balkisu kuwa wata nurse ce taxo ta tafi da
ita izuwa nurses station(wurin zaman nurses) gabadaya
nurses din dake gurin babu abinda sukeyi ma Balkisu
face nasiha da ban hkri na rashin da sukayi.
Yan'uwa da abokan arzik'i kuwa gaba d'aya sun sami
damar halartan jana'izar su Alhaji Abdullahi kowa sai
jimamin wannan rasuwa yakeyi mai cike da abun
al'ajabi, hakanan gdansu Rafee'at suma dukk sunjigata
da wannan al'amari.
Likitoci da kyar suka samu kan Hafeez domin zuwa
yanzu yanayin nasa ana iya cewa alhmdllh, Balkisu kam
gabad'aya tazama kurman dole tak'itace da kowa uffan
wasu irin hawaye masu k'unci da rad'ad'i kawai ke zuba
a kuncinta.
Misalin k'arfe uku da rabi na dare Hafeez ya farfado, a
hnkli ya fara bud'e idanunsa tun yanaji suna mishi nauyi
har dai yasamu ya bud'esu gabadaya cikin natsuwa yake
kiran sunan mahaifan nasa chan kmr wucewa wasu yan
sakwani Hafeez ya miqe zaune cikin tsananin firgici take
yaji kansa yafara Sara mishi drip din dake sanye a
hannunsa ya fisgeshi sannu a hnkli ya zaro k'afafunsa
qasa tamkar d'ankoyan tafiya haka yafara fita a cikin
d'akin. Balkisu Na zaune daga bakin k'ofa tarafka uban
tagumi sai zubda kwalla takeyi maganar bacci kam
babushi gabad'aya bacci ya k'auracewa idanunta.
Tana cikin wannan Halin ne taji andafa kanta tare da
kiran sunanta da sauri tad'ago ganin Ya Hafeez ne tsaye
akanta tamiqe da sauri ta rungumeshi wani irin sabon
kukane ya zo mata Wanda Hafeez shi Sam kukan yak'i
zuwar masa, a hnkli yake Shafa kan Balkisu Alaman
lallashi
Suna cikin hakane Dr din dake kula dashi yafito daga
office dinsa kenan ya hango patient dinsa tsaye, da sauri
yak'arasa gurin yana isa yariqe hannun Hafeez yana
k'okarin mai dashi cikin dakin, Dakatar dashi Hafeez yayi
cikin wata raunanniyar muryansa yace no Dr karka
damu am ok nagode da k'okarinka akaina.
"A ynxu banida wani BURI illah naga k'anwata cikin
walwala, nan ya cigaba da Shafa kan Balkisu yanafadin
k'anwata Sam kadaki damu domin natabbata mutuwar
mahaifanmu dasa hannu wasu aciki inkuwa har hakan
takasance nayi imani da maikowa mai komai saina
d'and'ana musu abinda suka aikatawa family na sannan
Balkisu.." Bai k'arasa fadin abinda yakeson cewa ba sai ga
wata nurse nan da gudunta tak'araso wajen Dr din
tanafadamishi cewa wannan tsohuwar tafarfado amma
jikinta ya Matsa sosai.
Cikin nuna tsananin damuwa Dr yadafe goshinsa yana
fadin ya salaam, nan ya mai da dubansa ga Hafeez yace I
thnk itama she ix part of ur family! Hafeez najin haka
yace da Dr din plss suje sugani kowaye ce, Dakyar Hafeez
yasamu suka k'arasa d'akin da iya Ladi ke ciki, iya Ladi na
nan kwance sai jujjuya kanta takeyi tanata furta Kalmar
shahada.
Hafeez naganin Iya Ladi baisan lkcin da ya kwala mata
kira da k'arfi ba, a hnkli ta waro idanunta ganin Hafeez
tsaye akanta yasa take ta k'ok'arin ganin ta tashi zaune
amma Sam hakan yafaskara sbd wata irin hajijiya dake
d'awainiya da ita, da sauri Hafeez ya duqa daf da ita. Iya
Ladi babu abinda tafara furtawa sai Hafeezu yar k'unan
bakin wake ce! Hafeez yayi sururu yana tambayar
wacece yar k'unan bakin wake? iya Ladi tace" wannan
bak'uwa taka da Kuka zo tare itace tayi sanadiyyar
gobarar da tashi dasu Alhaji da Hajiya domin naji
lokacin da yarinyar take fadin sai takashe Ku kai da
Rafee'atu atunaninta kana cikin gdan shine tabude
silindan gas yayi ta linking daga bisani ta kyasta ashana
nayi k'okarin gudun Na sanarwa Hajiya abunda ke
faruwa amma Allah bai bani iko ba har wannan yarinya
tasamu galabar kona gdan, take anan Hafeez yamiqe
tsaye yafara ja da baya yanafadin no! no!! no!!! Suhailat
karkimin haka kinsalwantar dani Suhailat kin ha'inceni
kin durqushemin rayuwa kin kassarani kin maidamu
marayu no Suhailat dama abunda kike shirin aikatawa
kenan? dana sani daban fita a gdan ba, yana fadin
maganar yana jada baya har ya isa jikin bango nan
yashiga gwara kansa yanafadin nayi nadamar saninki
arayuwata natafka babban kuskuren amincewa wata
diya macce bayan Rafee'a na,Suhailat kinci amanata
bazanyafe miki ba! Bazantaba yafemiki ba! Kincuceni
kincutar da Balkisu inallillahi wa'ina ilaihiraji'un, ganin
bashida niyyar daina gwara kansa a bango Balkisu tazo
da gudu ta rungume shi tanafadin yaya kadaina plss
kadainan dakyar da taimakon Dr suka samu Hafeez
yadaina amma sai wani irin numfashi yake fiddawa
yanata sambatu, Iya ladi dake kwance tace Dan Allah
Hafeezu karka kafadamin cewa su Hajiya da Alhaji
sunrasu?. Hafeez ya sadda k'asa yace iya Ladi sai dai mu
sami dangana domin kuwa Suhailat ta aikatamin abunda
har namutu da tabonshi zankoma ga mahallicina, nayi
kuskuren amincewa diya macce a ynxu bayan Balkisu
babu wata diya macce da zansake yarda da ita Suhailat
kin ha'inceni bazan taba yafemiki ba.
Iya Ladi najin kalaman Hafeez nan take tafahimci cewa
su Hajiya Allah yayi musu rasuwa, take anan tafirgice
jikinta yaqara tsanantawa babu abinda take furtawa sai
neman gafara.
Kafin wayewar gari kuwa iya ladi tace ga garinku(iya Ladi
ta amsa kira) Hafeez da Balkisu nasamun labarin
rasuwar iya Ladi take anan sukaje komai yadawo musu
sabo.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [9:00AM, 7/18/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣5⃣
Tashin hankali wanda ba'a samishi rana, a yaune Alhaji
Kabeer musa wato mahaifi ga suhailat yayi dirar mikiya
acikin garin borno bai wani sha wahala ba kasancewar
Alhaji Kabeer da abokin Hafeez yaxo dashi tundaga
taraba state kasancewar abokin Hafeez din yasan gdansu
shine musababbin dayasa Alhaji Kabeer ya tisa k'eyarsa
agaba.
Da isarsu barno kai tsaye gdansu Hafeez suka nufa, koh
da shigarsu Cikin anguwar Ahmed(abokin Hafez)ya nuna
masa gdnsu Hafeez kafin ma driva yasamu damar parkin
motar tuni Alhaji Kabeer yabude murfin motar yafito
yanufi hanyar gdan da aka nuna masa, mazan dake
zazzaune daga gefen gdan yan karban gaisuwa tuni
ma'aruf(qanin alhaji abdullahi) yataso daga cikinsu don
tsaida wannan mutumin dake k'okarin tunkarar gdan da
yakasance a kulle, gashi dai daganin mutumin kasan
cewa baicikin natsuwa. dan haka da sauri suka isa kofan
gdan atare, ma'aruf nazuwa yafara tambayar wannan
mutumin yace" mallan lafiya kuwa? Naga kataho a
hargitse kana qoqarin bude wannan gdan gashi dai
naganka amma babu alamar dangantaka ko sanayya
atattare da kai zan iya sanin ko kai waye"
Cikin zafin rai Alhaji kabeer ya dubesa yace"nikuwa
nahada dangantaka da wannan gdan tunda yakasance
ya'ta tana hannunku, uncle ma'aruf ya k'ufula sosai
ganin cewa wannan mutumin yazo masa da rainin hnkli
waye kuma yarsa? Da sauri uncle ma'aruf yasake jefa
masa wata tambayar akaro na biyu" waye yarka kuma?
amma dai ba'anan gdan ba? Alhaji kaber yace kwarai
kuwa a wannan gdan ne koh ba nan bane gdansu Hafeez
Abdullahi.
Kamar daga sama sukaji ance eh nan ne, da sauri
sukajuya a tare don ganin mai basu amsa.
Hafeez ne tsaye rungume da hannayensa a kirji,
fuskan nan tashi tayi fayauu tsakanin jiya da yau
gabadaya Hafeez ya rame ya chanja kammanu' a hnkli
yake tafiya kasancewar har ynxu bayajin qarfin jikinsa ,
qarasawa yayi wajan nasu yanuna daddyn Suhailat
yace"koba kafadamin ba nasan cewa kaine mahaifin
suhailat ko ba komai ga kammaninku nan yanuna, ka
kasance mahaifin mai kisan kai azzaluma..
Da sauri dadyn Suhailat yadakatar dashi tahanyar
nunashi da yatsa yace "kai Yaro dakata waya baka ryt din
ambatarwa yarinyata wadannan munanan alkaba'in?
"maza kaje kafito min da yarinyata" cikin tsananin fushI
Hafeez yace tirrr da hali irin na yarka.
Ko dayake dama hausawa sunce juma'ar da zatayi kyau
tundaga laraba ake iya ganeta,sannan dukk wata tarbiya
tana farawa daga gdane sai dai ga dukkan alamu daga kai
har yar'taka wacce kake tutiya da ita Sam babu wannan
alamun atattare da ku.
Tuni hawaye masu ciwon gaske sun wanke fuskar
Hafeez' Daddyn Suhailat ne yadakatar dashi tahanyar
cewa "nace kaje kafito min da diyata ko kai kurmane?"
Take anan ran Hafeez ya6aci gabadaya kamanninsa suka
sauya, jaa da baya yakamayi cike da masifa yakewa
Daddyn Suhailat bayanin dukkan abubuwan da sukafaru
ta sanadin yartasa' Daddyn Suhailat najin wannan bayani
tuni gume ya wankesa, sbd tabbas yasan yartasa zata iya
aikata abunda yafi haka, sannan bashida ryt din da zaixo
yatada husuma sbd Suhailat da kanta tafadamishi
dukkanin abinda tayi niyyar aikatawa, take anan yaji
wata irin nadama marar iyaka, cikin ransa kuwa fadi
kawai yakeyi inama lkcin baya xai iya dawowa domin ya
gyara kuskuren da ya tafka akan rashin bawa Suhailat
ingantaciyyar tarbiya.
Mgnr da Hafeez keyice tadawo da Daddyn Suhailat daga
dogon tunanin da yatafi" ae ina mai tabbata maka cewa
saina dauki fansar ta'addancin da dabbar diyarka ta
aikatamin domin tun sanda wannan al'amarin yafaru
nake tunanin tayaya za'ayi naga mahaifin Suhailat domin
nadauki tawa fansar dukk da cewa Suhailat tariga da ta
mutu toh amma ko ba komai idan nadauki fansar
abunda ta aikatamini zansamu sassauci.
Da sauri kuwa Daddyn Suhailat yad'ago kai gamida
cewa fansa Kuma? Wacce irin fansa? Hafeez yayi wani
murmushi mai ciwo "yace fansar abinda ta aikatamin
domin nayi alwashin sai na salwatar da rayuwar nata
iyayen, sai kuma alhmdllh gashinan ka kawomin kanka.
Daddyn Suhailat najin haka ae da sauri yakoma gefen
uncle ma'aruf yanafadin Subahanallahi Hafeez kasan
abinda kake cewa kuwa? Hafeez ya turbune fuska yace
tabbas nikuwa na san abinda nake cewa sai dai
natabbata bazaka amincewa hakan ba har sai kaga
nadauki mataki.
Uncle Ma'aruf ne ya dakatar da Hafeez daga munannan
alqawarinsa, Hafeez kam yayi nisa sai sambatu yake
yanafadin sai yakashe mahaifin Suhailat, mazan dake
zazzaune cikin rumfa masu amsar gaisuwa sune suka
taso Dan ganin abun yaqi qarewa.
Dakyar akasamu Hafeez ya dan sauqo sannan ya umarci
Daddyn Suhailat daya bacewa ganinsa tunkafin yakira
masa hukuma..sbd baya qaunar ganinsa balle jin sunan
diyarsa.
Tuni Alhaji Kabeer yabar cikin garin borno.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣6⃣Alhaji kabeer sbd tsananin rud'ewa bai samu daman
komawa da Ahmed ba, anan cikin garin borno ya barsa.
Hakan ne yabawa Ahmed din damar zuwa yayi ma
abokin nasa ta'azziya da jajen abunda yafaru, daga
bisani kuma ya jasa gefe nan ne yayi masa bayanin
dalilin zuwansa da yadda akayi yazo sannan Ahmed
yad'aura da yimasa bayanin ko wacece Suhailat, kwarai
da gaske Hafeez yayi matuqar mamakin jin lbri Suhailat
wata irin nadama ce tadinga addabar zuciyar Hafeez take
yaji gabadaya dukk yatsani kansa.
*Bayan Wata Daya*
Yan'uwa danginsu Hafeez babu yadda basuyi ba akan
suna son tafiya da Balkisu tazauna a hannunsu amma
Hafeez ya qeqasa qasa yanuna sam bai amicewa hakan
ba, dole suka rabu dashi kowa Yakama gabansa.
Bayan kwana 2 Hafeez yasa aka gyara masa gdansu dake
cikin federal lowcost chan suka koma shida Balkisu
domin a cewar Hafeez baxai iya sake rayuwa acikin gdan
da sukayi rayuwa da mahaifansa ba.
Dama ya lafiyar kura balle kuma anta6ota, wasu irin
sabbi halaye Hafeez ya qirqirowa kansa gabadaya
yakoma miskilin gaske. Gashi ynxu kwatakwata Hafeez
baya yadda da kowa sannan idan kaga fara'ar Hafeez ko
murmushinsa toh tabbas yana tare da Balkisu ne.
***
BURIN HAFEEZ a kullum shine yaga cewa ya bawa Balkisu
ingantacciyar rayuwa kamar sauran yara, sannan tuni
Hafeez ya qudurta a ransa cewa tunda yarasa Rafee'ansa
toh babu shi babu kula wata d'iya macce, wannan shine
yabama Hafeez damar nunawa dukk wata diya macce
k'iyayya 6aro-6aro matuqar bai had'a jini dake ba,
hakan yasa tsakanin macce da Hafeez kuwa babu komai
sai tsantsar hantara da nuna zafin rai domin acewarsa
"dukk halinsu d'aya"
Dukk irin yawan yan matan dake nuna tsantsar
soyayyarsu ga Hafeez amma Sam basu fuska balle ya
amince dasu, sai dai suyi ta nacinsu su gaji.
Abangaran Balkisu kuwa bata da wani Buri da yawuce
taga cewa yayan nata ya mance da komai yayi auransa
don fuskantar sabuwar rayuwa, amma hakan yafaskara.
Gashi Hafeez kullum yana cikin kad'aici da damuwa
Wanda hakan yayi sanadiyyar jawo masa hawan jini, tun
Balkisu na nuna damuwarta har tasaba da kafiya irin na
yayan nata.
Amma sai dai Zuwa ynxu Balkisu taqudurta a ranta cewa
sai ta rusa dukk wani BURI na yayanta akan qin son aure
wanda atunanin likitansu ya basu shawaran cewa lallai
Hafeez yana buqatar macce wadda zata kula da
rayuwarsa sosai.
Wannan shawara ta Dr muh'd ta matuqar tsayawa aran
Balkisu domin tasan abune mai wahalar yuwuwa
kasancewar Hafeez yatsani macce arayuwarsa, shiyasa
dukkanin wani tunaninta yatsaya akan taya za'ayi auran
Hafeez yasamu yuwuwa?
Balkisu da kanta tasan cewa Hafeez baida wani BURI da
yawuce yabata kyakyawar kulawa, ita kanta tasan hakan
nafaranta mata rai dahakan kuma take alfahari dashi
domin ya zama tamkar uwa uba a gareta sbd babu
abinda tanema tarasa, toh amma sai dai ganin walwala
da farincikin yayan nata yafi mata komai arayuwa.
"Dan haka kema Balkisu tunda ynxu kingirma kin mallaki
hnklin kanki kinfahimci minene rayuwa yakamata
kikawo sauyi da farinciki arayuwar tilon Dan' uwanki"
Balkisu tayi nisa sosai cikin tunanin ta, jitayi anata buga
mata k'ofa da sauri tamiqe tanufi k'ofan ta bud'e.
Hafeez ne tsaye yasakar mata murmushi itama
murmushintayi masa tace" yayana jiki yayi sauqi
kenan?" Kyad'a mata kai yayi yace sosaima naji sauqi,
ynxun nan ma Nadawo daga masallaci najiki shiru ne
yasa nace bari inzo indubaki.
Balkisu tad'an waro idanu waje tace "Yaya anyi kiran
sallah ne? Hafeez yadubeta da mamaki yace "kina nufin
bakiji kiran sallah ba? Gashi kuma ga dukkan alamu
idanuwanki basuyi kama dana mai bacci ba, aikin me
kikeyi haka Wanda ya d'aukemiki hnkli?
Ganin Hafeez yatsureta da tambaya yasa tayi saurin
cewa Yaya bakomai kawai Allah baisa naji kiran sallah
bane, kafin Hafeez yace wani Abu tuni Balkisu ta tajuya
cikin d'aki da sauri tafad'a toilet.
Kasancewar lkci yaqura alwala kawai tayi tafara gabatar
da sallah.
Balkisu tajima zaune bisa sallayah sai jero aduo'i takeyi
tanamai roqon Allah yashige mata gaba Ya kuma bata
ikon cika alqawarin da tadauka nakawo farinciki a
rayuwar d'an uwan nata.
"Cigaban lbrin"
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [2:40AM, 7/21/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣7⃣
Haka rayuwa taciga da kasancewa, a kullum Balkisu bata
da wani tunanin da yawuce tayadda za'ayi auren yayan
nata yakasance? Wacce hanya zatabi? wazata tunkara da
matsalarta? Gashi dai Hafeez baya bari takula qawayenta
balle tasamu wacce zatayi shawara da ita don nemawa
kanta mafita.
Shiyasa a kowanne dare yakasance Balkisu bata iya
runtsawa, kullum tana mai miqa wuya da neman
taimakon ubanji dan haka takai kukanta ga mai kowa
mai komai.
** ** **
Yau tsawan sati d'aya kenan Balkisu na ziryan zuwa
gdansu Meena amma kullum bata samunta,(Burin
Balkisu shine taga cewa ta taimaki Meena, amma ga
dukkan alamu Meenah a tsorace take da Balkisu shiyasa
take gudun dukk wata hnya daxata hadasu.)
Yau yakasance ranar Asbar, Wanda hakan yayi dai dai da
Balkisu bata da lectures dan haka tun qarfe bakwai na
safe tashirya tsaf kafin Hafeez yafito kasancewar tasan
qa'idar sa dukk weekend sai 11 yake fitowa dan haka tayi
amfani da wannan damar tafice tanufi gdansu Meena.
Balkisu na isa qofar gdansu Meena hakan yayi dai-dai da
fitowar ta daga cikin gdnsu fuskar nan ta ta sha6e-sha6e
da hawaye ga hannunta d'auke da bokatin alala, Balkisu
naganin haka tayi saurin fitowa daga cikin motarta gami
da kiran Meena! Meena da sauri tawaiwayo don ganin
mai kiranta, wacce tayi tsammanin kuwa ita tagani dan
haka ta tsaya kmr wacce aka shukata.
Dasauri Balkisu ta rufe motanta ta isa ga Meena cikin
muryan jajenta Balkisu tace" haba Meena mai yayi zafi
haka a kullum nazo bana tarar dake sai kace wacce
keqoqarin cutar dake look Meena yakamata kiyarda dani
wlh Burina shine kawai inga cewa nataimaka miki sbd
nariga nadauki alqawarin hakan"! Sadda kai qasa Meena
tayi sannan ta d'ago takalli Balkisu da wani irin
murmushinta mai ciwo, a hnkli Meena taja wani gauran
numfashi sannan tace" tabbas baiwar Allah nagode da
dukk wani qoqarinki akaina sai dai inaso kisani cewa
bana buqatar taimakon kowa, plss naroqeki ki janye
qudurinki akaina sbd dukk yadda kikaso haKan baxai
faruba sbd wasu dalilai dasu ka kasance sirriina Dan
haka na roqeki plss kiyi nisa daga cikin rayuwata gashi
ina matuqar ganin girmanki" dasauri Balkisu ta tari
numfashinta tace" plss Meena yakamata ki yarda dani
inaso kisanar dani dukkan lbrinki sbd hakan ne kad'a
xaibani damar sanin koke wacece da kuma yadda
zansamu sauqin taimakawa rayuwarki domin jikina
yajima yanabani wani abu daban..
Meena tagoge d'an guntun hawayen dake qoqarin zubo
mata batare da takoma kallon Balkisu ba tajuya bayanta
gami da cewa"na fad'amiki tun a lkcin baya cewa sanin
lbrin rayuwata babu abinda zai qareki dashi nidai
shawarata agareki kijanye dukk wani burinki nason
taimakawa rayuwata nagode" Meena nafad'in haka
tad'aura bokatin alalarta a kai taratsa gefen Balkisu
tawuce.
Balkisu tsayawa tayi sororo tana tunanin kafiya da taurin
kai irin na Meena, "gashi bansan dalili ba a kullum
zuciyata naqara azalzalata akan lallai na taimaki Meena,
sai dai kash ga dukkan alamu

Please Login or Register in order to submit comment