Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huci take
kmr zakanya, murmushi Mallan Zakiru yayi domin kuwa
bai yi mamakin ganinta ba don yatsammaci haka.
Mallan Zakiru yadubi Yagana yace "toh ynxu kuma
Yagana wanne laifi nayi haka da har nacancanci ki biyoni
gda da masifa?
Yagana ta gyara tsayuwa cike da masifa tace "ae
kuwa kace dani haka tunda ka gama rainamin hankli
wato ashe sai da Meena kayi? Kafadamin suwa
kasayarwa da ita a nawa kasaidata? Mallan Zakiru yayi
murmushi cike da dattijantaka yace "akan naira dubu
uku kacal kuma suma kudin suna hannunki, kinga kenan
ashee bani kad'ai naci ribar sai da Aminatu ba.
Nan fa Yagana tabud'e murya tana tadajijiyoyin wuya ita
alafurr adawo mata da Meeena, Mallan Zakiru kam yau
dukk jiyayi lamarin Yagana ya kai mishi mak'ura wata
uwar tsawa yabuga mata wnda tayi sanadiyyar shiga
natsuwarta.
Sheqeqe Yagaña tayi tana bin mallan Zakiru da kallo cike
da mamaki, Mallan Zakiru yadubi Yagana cikin tsananin
fad'a yace "wlh kedai tirrr Allah wadai da hali irin naki
Yagana wlh ina mai tabbata miki cewa kiyi gaggawar
canja halinki kiji tsoran haduwa da mahallicinki domin
kuwa a kodayaushe lkci yana iya kuremiki.
"Dama mai kika d'auki kanki? Kind'auka cewa ke
kadaice kike da kwakwalwa da tunanin yadda zaki cutar
da wani toh kisani dama irin wannan lkcin nakejira,
najima inatunanin ta yadda za'ayi Na ku6utar da
Aminatu daga hannunki sai gashi Allah maji roqon
bawansa ya amsamin addu'ata da najima inayi akan
yabani ikon da zankubutar da Aminatu sai gashi
yakawomin hnya mafi sauqi, kuma bari kiji infad'amiki
Aminatu dai na gdanta ma'ana gdan mijinta bakuma
zanfadamiki inda take ba balle kije kitada musu
qayarbaya sbd jahilci irin naki.
Gwalo idanu waje tayi tadubi mallan Zakiru tace "Zakiru
nice jahilar"? Mallan Zakiru yajinjina kansa yace"kwarai
kuwa" Nan fa Yagana ranta yaqara 6aci cikin tsananin
fada tashiga nunashi da d'an yatsa tace "wlh kajira kaga
abinda xai biyo baya wlh dani kake mgn" Mallan Zakiru
yace "ae shi sharri kare ne kuma mai shiyake bi insha
allahu babu abinda xan gani sai alkhairi, kuma indai
aminatu ce tayi aure a babban gda gdan dasuka san
darajar mutum, gdan da inhar keda zuri'arki zasuyi
shekara goma kuna tara dukiya bafa zaku iya sayen koda
karen gdan ba, balle kiyi tunanin zuwansa" Mallan Zakiru
nafadin haka Yagana tayi kwaf ta kad'akai tafice a gdan
cikin tsananin fuskata.
"Mtsssw aikin banza kawai yarinya kin grma bakisan
kingirma ba, baki da wani aiki sai tunanin kanki da
ahalinki nawa rayuwar duniyar take da zaki d'auki son
duniya kid'aurawa kanki" Inna dai natsaye bata ce komai
ba, sai bayan da komai yalafa sannan suka zauna yake
bata lbrin dukk abin da yafaru.
Innah taji dad'i sosai da jin wannan lbrin.
** ** ** ** ** ** **
A bangaran Amarya Balkisu kuwa gabad'aya famlyn ango
sun hallara don d'aukar amarya, amma Balkisu tace sam
batasa Xancen ba, ita bbu inda zataje har sai ankawo
Meena cikin gdan ta sadata da yayanta sannan, babu irin
lallashin da basuyi ba amma furrr taqi amincewa a dole
suka hkra suka zauna zaman jiran isowar matar Hafeez.
Ba'awani jima ba kuwa sai ga yan d'aukan amarya sun
iso, hakanan Hajiya Nana ta lullu6e fuskar Meena
akashiga da ita cikin gdan, Bayan sun gama bud'arsu da
shewarsu ne Balkisu tazo da kanta taja hannun Meena
suka shiga d'akinta don suyi mgn.
Meena kam tun isarsu gdan babu abinda take sai kuka
daga ita har Balkisu babu mai ba wani hkri, dakyar
Balkisu tasamu tayi controlling din kanta sannan tashiga
roqon Meena da ta kular mata da yayanta nan Balkisu
tashiga fad'awa Meena abinda Hafeez yafiso da wanda
baya so.
Meeena kam sai kuka takeyi kmr ranta zai fita, hakanan
Balkisu tagama fad'amata dukk abinda yakamata sannan
takama hnya har zata fita sai tajuyo tace "Meena Dan
Allah kikasance mai juriya da hkri kmr yadda nasanki
sannan ynxu da zarar hidimar bikin nan taqare xancika
miki naki alqawarin" tanafadin haka tashare hawayenta
tafice a d'akin.
D'akin Hafeez Balkisu tanufa nan ma wani sabon kukan
tasha, wannan karon hadda Hafeeez shima yazama
tamkar wani qaramin Yaro sai kukan yakeyi, Balkisu ta
d'ago da jajayen idanunta tadubi Hafeez tace "plsss yaya
ka kula da Meena kmr yadda kake kula dani hakan
zaisani farinciki, girgiza mata kai kawai yakeyi batare da
yace komai ba.
Dakyar Anty munnawara matar uncle ma'aruf ta
6an6are Balkisu daga jikin Hafeeez, sai kuka sukeyi
gabad'ayansu.
Hakanan Hafeez yanaji yana gani akatafi da Balkisu
gdan auranta.
Wani irin k'unci yakamaji Wanda hakan yasa ciwon
xuciyarsa ya tashi dakyar yasamu yasha magani ya
kwanta.
Meena kuwa Hajiya Nana takaita asalin d'akinta Wanda
ya kasance mallakinta, d'akin kam ya matuqar had'uwa
da tsari komai tsaf tsaf nacikin d'akin.
Hakanan kuwa Meena tanemi gado ta kwnta wani irin
karkarwan d'ari tashigayi ga knta da yake tsananin sara
mata sbd ciwo, nan tadunqule waje d'aya ga wani irin
azababben tsoro daya dinga shigarta kmr ta shid'e.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [12:57AM, 8/1/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣8⃣
Dukk addu'ar da tazo bakin Meena ita kawai take
karantowa, runtse idanuwan tayi sosai bata ko k'auna
bud'esu sbd tsananin tsoro, yayin dashi kuma gogan
nata ke d'akinsa kwance yanata sharar bacci sakamakon
magungunan daya d'irkawa cikinsa.
A bangaran Meena kam dak'yar tasamu itama baccin
yayi awon gaba da ita daf da asuba, dan haka bata wani
samu ishashen bacci ba, hakanan ta daure ta nufi toilet
alwala tad'auro sannan tazo tagabatar da sallah.
Bayan ta idar da sallah ne tarafka wani uban tagumi cike
da damuwa,
Misalin qarfe takwas na safe Meena ta tashi tanufi
falo sbd wata irin yunwa da taji ta gallabeta har wani irin
duhu duhu take gani dakyar tasamu tafita koh Allah zaisa
ta samu abinda tasawa cikinta.
Koh da fitar Meena Daniel tagani yanata zirga zirga
tsakanin kitchn da dinning area, shiru tayi tana binsa da
kallo domin ita dai batasan ko waye shi ba.
Meeena na nan tsaye kmr wadda aka shuka, Daniel ne
yasake fitowa daga cikin kitchn a karo nabiyu hannunsa
dauke da flask din ruwan zafi kmr ance ya waiga sai
ganin Madam yayi a tsaye kmr wata marar gaskiya, ae da
sauri ya ajiye flask din ya qaraso gareta cike da
grmamawa yace gud murng madam, kintashi lpy? Cike
da mamaki Meena ta amsa lpy kalw, sannan Daniel yace
ni sunana Daniel nine ke kula da store room Na gdan
nan da kuma kitch, gyad'a kai kawai Meena tayi
hankalinta dukk yana wajen dinning area ita dai burinta
tasamu abinda taci.
Ganin hakane yasa Daniel yace am swry 4d disturbn u
madam, d food is ready da sauri yaqara kan dinning din
nan yafara bud'e mata abubuwan da ya girka kala kala,
Meena kam riqe baki tayi cike da mamaki tadubi Daniel
tace "Daniel dukk suwaye zasuci wannan abincin? Daniel
yace "madam boss ne yace ake girka enough abinci
yadda kowa zaici ya qoshi", Cikin zuciyar Meena tace
uhumm boss kodai runbu irin wannan almubazzaranshi
haka.
Sinasir da miyan allayahu shine kad'a Meena taga zata
iyaci Dan haka d'aukan plat kawai tayi Daniel ya taimaka
mata tazuba abincin, d'aukan plat dinta tayi ta koma falo
domin jitayi bazata iya zaman dinning table dinba,
zamatayi sosai tafara bawa cikinta haqqinsa.
Hafeez kam yau baqaramin makara yayi ba wurin tashin
sallah sai qarfe bakwai da rabi ya farka a gaggauce
yashiga toilet yadauro alwala, yana gama idar da sallah
yakoma toilet din yayi wanka yazo yasake shiryawa tsaf
abinsa, sai wani sauri yaketayi kmr wanda xaitashi sama
yau dai Hafeez ko za6en kayan sawanshi bai tsayayi ba
sbd yau bashida niyyar wuni acikin gda balle abokan
wasanshi suzo su sami damar takura mishi, Qarfe takwas
da rabi nayi Hafeez har yagama shirinsa.
Meena kam har tagama cinyye sinasir dinta, wani
qatoton qashi ta tsaya gwaigwaya sai faman ko kuwa
takeyi dashi, tana cikin wannan halin ne sai ga Hafeez
yafito daga d'akinshi cikin sauri sbd baya so ya hadu da
wannan Meenan da Balkisu ta d'aura mishi nauyin da
bazai iya cikawa ba.
Hafeez nafito wa cikin harban falo wata yarinya
yagani tayi zaman dirshan tanata faman ko kuwa da
qashi, wani irin abune ya tsaya awuyan Hafeez domin shi
arayuwansa yatsani yaga anacin abinci da hannu balle
kuma ita wannan ga dukkan alamu dambe takeyi da
qashi.
A fusace Hafeez yanufi falon yana xuwa yace "ke dabbar
ina ce miye hakan? Wacece ke ? Wannan wanne irin
qazanta ne?"
Meena kam batayi tsammanin da mutum tsaye kusa da
ita ba, tsawa kawai taji andoka mata Wanda ya mugun
razana ta har qashin hannunta ya su6uce ya fadi😂 da
sauri taduqa tad'auki qashinta tamiqe tsaye gamida
juyowa domin Meena kam tuni tagane mekiranta da
dabba sunan, shi din ne kuwa tagani tsaye fuskan nan a
turbune babu alamar wasa acikinta.
Wani irin shock Hafeez yashiga ganin wannan
fitsararriyar yarinyar agabanshi domin kuwa har abada
baxai manta wannan face din ba, da saurinshi kuwa ya
zaro idanu cike da mamaki yace "ke wat ar u doing here?
Meya kawo ki cikin gdana? Meena kam quramishi ido
tayi gabanta sai bugun tara-tara yake, nan fa Hafeez
yafara kiran Daniel! Daniel!! Daniel!!! da qarfi Hafeez ke
kiranshi kmr wanda yaga dodo agabansa. Dagudu Daniel
yaqaraso yace "yes boss am here" Hafeez yanuna Meena
da hannu yana kallon Daniel yace "Daniel who's dis girl?"
Daniel ya yadubi Meena wacce ke tsaye hannu riqe da
qaton qashinta wani yawu Daniel had'iye cike da tsoro
domin shi baisan wacce irin amsa xaibawa boss din
nashi ba, dominshi a tunaninsa koma wacece ai shi zai
fisa saninta... Daniel!!! Da qarfi Hafeez ya koma kiransa
cikin fushi yace "I'm not tlkn to u"? Who's dix girl?
Daniel ya sadda kai qasa yace boss I think she is ur wife,
amma nibensashi ba fa.
Meena kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Hafeez
yadubi Meena up and dwn yace cabb badai wannan abar
itace matata ba?
Meeena naganin Hafeez xai wuce gona da iri kawai ta
ratsa tagefenshi tawuce kitchn ta ajiye plat din sannan ta
wanko hannunta.
Dasauri tanufi d'akinta ta banko kofa, ganin tashiga cikin
d'akin nan ya tabbarwa kansa cewa lallai wannan
yarinyar itace wadda aka had'ashi da ita? Tabbb juyawa
Hafeez yayi izuwa d'akinshi take yaji yafasa fitar da yayi
niyyar yi.
Dakinsa shima ya shiga da sauri.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:53AM, 8/1/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣9⃣
Kai da kawowa Hafeez ya dingayi cikin d'akinsa
gabad'aya jiyayi Balkisu tagama 6ata mishi rai sbd tarasa
wacce zata hadasa dashi sai wannan fitsararriyar
yarinyar wata qazama da ita yar qauye.
Wani irin haushin Meena yadinga ji, jiyayi kmr yaje
yarufeta da duka.
Abangaran Meena ma haka abun yake d'akinta tashige
tana zuwa tafada kan gadonta,nan tafara kuka wani irin
haushin Hafeez da tsoransa ne suka tsayamata a cikin
xuciyarta lkci d'aya cikin ranta tace "wato dai shi
wannan uban masifan bashi da aiki sai cewa mutun
dabba qyaattt" Meena tayi kwafa cike da jin haushinsa
tace ae kuwa zan nunamaka halin dabbancin.
Tun daga wannan ranar Meena ta umarci Daniel da yake
kai mata abinci cikin d'akinta, dan haka yasa ynxu kwata
kwata Meena da Hafeez sunbar had'uwa dukk da cewa
suna gda daya.
** ** ** **
BAYAN SATI DAYA.
Tuni Balkisu tad'auka qarara izuwa babbar kotu dake
cikin jaharsu, da taimakon Dr Muh'd Balkisu ke gudanar
da komai batare da sanin Meena ba.
Sai da akayi sati guda currr ana abu d'aya shari'ace
aka gudanar inda Mallan Zakiru yazo takanas har kotu
shida wasu sauran mutanen cikin anguwarsu, suka bada
shaidan cewa lallai Yagana itace ta kashe d'anta.
Sbd irin kudin da Balkisu tanarkawa yan'sanda shiyasa
sukaje har gdan Yagana suka suka titsa qeyar ta izuwa
police station, nan fa suka shiga yimata horo na azaba
kala kala akan lallai ta amsa laifinta na kisa, dakyar
Yagana ta amsa laifinta ganin tana shirin shurawa zuwa
lahira.
Bayan Yagana ta amsa laifinta ne kotu tayanke mata
hukuncin d'aurin rai da rai a gdan yari tare da horo
maitsanani kasancewar yadda tayi wasa da hankli
hukuma.
Balkisu tayi farinciki da samun nasarar da sukayi,
hakanan akafito da baba Rabi dukk ta wani tsufa ta rame
ta d'an canja kammanu.
Sunanan tsaye mallan zakiru dasu Balkisu, yansanda
sukazo wucewa da Yagana hannuta saqale da ankwa ana
qoqarin wucewa da ita gdan yari. Dasauri Mallan zakiru
yatsaidasu nan fa yayi tayiwa Yagana tuni akan
abubuwan dasuka faru yace" ynxu dai gashinan kinga
qarshenki (Allah yashiryi masu halin sonkai irin Na
Yagana)
Baba Rabi kam sai godiya take ta jerowa Balkisu, daga
bisani ne Baba Rabi ta dubi Balkisu tace "baiwar Allah ko
zan iya sanin koke wacece"? Balkisu tayi murmushi cike
da farinciki tace "baba karki damu zanfad'a miki koni
wacece amma da farko inaso ki kwntar da hnklinki
kinatsu sbd nima yarkice kmr Meena"
Da sauri baba Rabi tadubi Balkisu tace yan nan kinsan
aminatu ne Dan Allah tana ina? Kiwa Allah kifadamin
koke wacece INA aminatu Na dan Allah kitaimaka ki
kaini gareta, Balkisu tace Baba kwantar da hanklinki
ynxuma wajan Meena zankai ki yanzu insha allahu zakiga
Meena, wani irin hawayen farinciki ne ya lullu6e Baba
Rabi.
Kofar wani katafaran gda Baba Rabi taga anyi parkn,
cikin girmamawa Balkisu tace "Baba fito mushiga daga
ciki", kurawa Balkisu idanu Baba Rabi tayi tana yimata
wani irin kallon tuhuma cikin ranta tace "anya kuwa
banyi kuskuren amincewa da wadannan mutanen ba,
bansani ba ko masu yanke kan mutane ne" tana cikin
wannan tunanin ne taji muryan Balkisu tace "Baba
karkiji komai wlh babu abinda zamu miki kizo muje
nakaiki wajan Meena" jiki a sanyaye haka nan baba Rabi
tarufawa Balkisu baya suka shiga cikin gdan.
"Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Anty amarya Meena"
cewar Balkisu dai dai lkcin da suke qoqarin shiga falon.
Meena kam nacikin d'akinta tana d'an wasu gyare-
gyaren ta juyo kmr ana sallama, kuma kmr muryan
Balkisu tajiyo domin dai ita tasan cewa bata kai
matsayin da Hafeez zai mata sallama ba. Dan haka da
sauri ta tashi tafice a d'akin da sauri tanufi falo.
Da gudu Meena ta isa falon don tarbon Balkisu, Tursuuu
Meena tayi ta tsaya cike da mamaki galala tayi da baki
domin abinda taganewa idonta (tsawan shekara tara da
suka shige Meena bazata taba mance wannan
nagartacciyar fuskar ba) fashewa tayi da wani irin kuka
mai tsanin ban tausayi.
Zaku jini anjima don jin cigaban lbrin, nagode.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:07AM, 8/2/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣0⃣
Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya lullu6e Meena
da gudu taqarasa wajan Baba Rabi, rungume junansu
sukayi a tare suna ta kuka, Balkisu da Dr Muh'd kam
suna daga gefe sai murmushi sukeyi.
Daga Meena har Baba Rabi anrasa mai lallashin wani,
kuka sukeyi gwanin ban tausayi, dakyar Baba Rabi ta
share hawayenta nan fa tashiga Shafa fuskar Meena ta ko
ina sai mamakin girmanta takeyi, yayin da itama Meena
sai kallon ta takeyi jiki take kmr ta manne a jikin Baba
Rabi.
Bayan sun natsu sun zauna Meena ta umarci Daniel da
yakawo musu drinks, cike da bin umarninta yakawo
drinks kala kala yadiresu musu shi. Sai da suka d'an
samu suka sharuwa sannan Meena tadubi Balkisu tayi ta
zabga mata adduo'i nafatan alkhairi tare da yimata
godiya, Balkisu sai murmushi takeyi.
Ana cikin hakane Dr Muh'd yatashi yace "shi zai koma
office" nan yayi sallama dasu yafice Balkisu har wurin
mota tarakashi daga bisani takoma cikin gdan.
Meena kam ana nan liqe da Baba Rabi dan jitake kmr
wani zai k'wace mata ita, Balkisu dai sai dariya take mata.
Meena tadubi Baba Rabi tace 'Amma' (sunan da
Balkisu ke kiran Baba Rabi dashi knan) Baba Rabi tadubi
Meena tace "Naam Aminatu" Meena ta shagwa6e fuska
tace Amma kintafi kinbarni cikin wahalalliyar rayuwa
naga rashin gata naga tozarta naga walaqanci
naga.....dasauri Baba Rabi ta toshe mata baki tace "haba
Aminatu minene kike fad'a haka yakamata ace kin yarda
da k'addara mai kyau ko marar kyau a matsayinki na
muslma, sbd wannan halin da muka tsinci kanmu
jarabawace ta ubangiji dukk abunda Allah yarubuto
cikin k'addararka to tabbas babu makawa sai tasameshi"
Dan haka karki wanisa damuwa aranki ko kice zaki dinga
tuna baya hakan bashi da kyau, ynxu ita wacce kike son
yin mgn akanta ae gashinan taga qarshen sakamakonta.
Balkisu ta jinjina kai tace tabbas Baba wannan haka yake,
Baba Rabi ta gyad'a kai tace toh kinga in hakane kuwa
bai kamata kidinga tuna abinda yariga yawuce ba, Na ma
gode Allah dayasa nasameki da ranki cikin k'oshin lafiya
gashi har kinyi aurenki a gdan mijinki kinga wannan ma
wata baiwace ta ubangiji Dan haka ki gode masa kiqara
gode masa a koda yaushe Allah yana tare da mai gaskiya
sannan yana bayan masu hakuri.
Da sauri Meena tafada jikin Baba Rabi taqanqameta tana
kuka, cikin zolaya Balkisu tace wlh anty amarya in baki
daina wannan kukan naki ba xand'auki Baba
mutafiyarmu, dasauri Meena ta dubi Balkisu ta d'an turo
baki cikin shagwa6a.
Baba Rabi tanumfasa tace "miye naga kina turo baki ae
da gaskiyar Balkisu sbd a yau insha allahu inaso naje
garinmu nasadu da dangina. Balkisu ta gyara zamanta ta
fuskanci Baba Rabi tace "Baba sai dai fa kiyi hkri koda
zakije garinku to ba yau ba sbd muma muna buqatarki
kusa da mu, sannan kada kidamu ba'anan zaki zauna ba
akwai gdan da muka ajiye miki na mussaman a
Famfamari, Riqe ha6a Baba Rabi tayi cikin nuna jindadi
da farinciki ta waro idanu tace dukk nikadai? Irin
wannan d'awainiyan anya kuwa baiyi yawa ba?
Balkisu tace haba dai Baba wanne irin yawa kuma kema
fa tamkar mahaifiya kike agaremu dukk abinda zamu iya
yiwa mahaifanmu to zamuyi miki dukk da cewan
Mahaifan namu basa raye" Baba Rabi ta goge hawayen
dake kwaranyo a mata a fuska, nan tashiga sawa Balkisu
albarka gamida yimata ta'azziyar rashin da sukayi.
Babban tashin hnkli Meena tashiga yayin da taga
Ammanta na qoqarin fita a cikin gdan, kuka takeyi sosai
ita fa lallai sai tabisu. Balkisu tace haba Meena miye
hakan? Sai kace wadda Baban guduwa zatayi, kiyi hkri
mana tunda Yaya Hafeez baya nan kibari idan yadawo
xai kaiki shi da kansa.
nan fa Meena tace batasan zancen ba.
Dole Balkisu takira Hafeez tasanar dashi cewa tanaso
zasu d'an fita wani waje tare da Meena, batare da 6ata
lkci ba Hafeez yace Allah kiyaye.
Cike da farinciki Balkisu tad'aukesu a mota suka nufi
Famfamari inda gdan Baba Rabi yake,
Wani d'an matsakacin plat house ne mai kyan gaske,
falo daya da d'akuna uku da toilet da kitchn sannan
kowanne bed room da toilet dinsa.
Masha allahu gda yayi kyau da tsari, Baba Rabi dai sai
godiya take tana sama Balkisu albarka.
Bayan sun gama gyara ko ina Na gdan Balkisu tace da
Meena ta shirya tayi dropn dinta a gda ita zata wuce
gdanta tad'aura abinci.
Nan ma dakyar Meena ta yarda suka tafi cike da kewan
Ammanta.
Akan hanyarsu takomawa gda Balkisu tadubi Meena
tace "toh anty amarya nacika miki dukkan wani alqawari
naki inaso nima kicikamin nawa kikular min da yayana
tamkar yadda uwa zata kula da d'anta. Dammm!! Gaban
Balkisu ya buga a hnkli ta kalli Balkisu jiki a sanyaye ta
gyad'a mata kai gamida cewa insha allahu.
Balkisu tayi murmushinta mai sanyi, dai dai nan suka iso
kofan gdan, Meena tayi sallama da Balkisu jiki a sanyaye
haka tabud'e get din tashiga, motar Hafeez tagani ajiye
wurin parkn motoci wato hakan nanufin yadawo?
damm! Taji gabanta yabuga sbd alqawarin da tayiwa
Balkisu ne yafad'omata.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:21AM, 8/2/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣1⃣
A hankali ta murd'a k'ofan falon tashiga ciki, Hafeez
tagani tsaye hannunsa d'aya sanye cikin aljihu d'aya
kuma yana amsa waya ya juya bayansa, cikin tafiyar
sand'a kmr wacce bata da gaskiya Meena ta nufi hanyar
d'akinta tana isa bakin k'ofa dai dai nan Hafeez na gama
waya.
Wani uban tsawa yadaka mata yace "keee!! Zonan nan"
Meena sai da tad'an figirta a hnkli ta juya akalarta izuwa
falo, Hafeez ya watsa mata wata uwar harara cike da jin
haushinta yace ke gdanku ba manya ne? Kina ganin
mutane baxaki gaishesu ba ko ba akoya miki bane?
Meena ta turo baki a hnkli tace INA wuni, mtssw Hafeez
yayi tsaki yace " bansani get out wuce kiban waje"
Meena ta juya da sauri tashige d'akinta tana gunguni.
A hnkli Hafeeez yace "Mtssw village girl gal kawai"cike
dajin haushin ganinta yanufi d'akinsa.
•° •° •° •°
Yau ya kasance weekend Hafeez na nan gda sai wasu
aikinsa yakeyi a system insa, zaune yake a falo sanye da
farar jallabiya gabad'aya ya maida hnklinsa akan
aikinshi.
A bangaran Meena kuwa a kullum bata da wani tunani
da yawuce taya zata fara jawo hnklin wannan uban yan
girman kan yakarka to izuwa gareta har tasamu tabashi
kulawan.
Cikin tunanin da takeyi ne wata dabara tafad'o mata
dasauri ta tashi tanufi falo, dama cikin shirinta take tsaff,
cikin natsuwa Meena ke tafiya har ta isa cikin falon
Hafeez tagani zaune yanata aiki a hnkli taqarasa gareshi
tace "assalamu alaikum" dasauri Hafeez ya d'ago kanshi
Dan ganin wacece keyimishi sallama.
Meena yagani tsaye gabansa sanye da wasu material
riga da siket sun matuqar amsar jikinta tayi kyau abunta
"koshi Hafeez cikin ransa sai da ya yaba wannan shiga"
amma a zahiri sai cewa yayi wa'alaikissalam, nan kuma
yatsaya sheqeqe yana kallonta cike da nuna isa yafara
kusheta yace ke kuma fa miye hakan zaki zo kitsaya akan
mutane?
Dasauri kuwa Meena ta zauna cike da sanyi tace "ina
kwana" Hafeez ya amsa ciki ciki yace "lpy" Meena taqara
da cewa sannu da aiki Hafeez yad'ago kanshi ya watsa
mata wata uwar harara batare da ya amsa mata ba ya
maida kanshi sannan yaci gaba da aikinsa, Meena na nan
tsugunne Chan tasake cewa "amm kayi brkfst kuwa"?
Hafeez yakawo iya wuya wani irin haushi yaji tabasa ina
ruwanta da cikinsa, kallonta yakomayi ya watsar da yinta
yacigaba da aikinsa.
Meena takawo iya wuya danne zuciyarta kawai takeyi
dan haka dasauri ta tashi tabar gurin, d'akin ta takoma
cike da jin haushin wannan izza da mulki na Hafeez.
Hafeez na nan zaune Daniel ya had'o kayan brkfst akan
tire yanufi d'akin Meena dashi, yana zuwa yafara
kwankwasa k'ofar d'akin a hnkli, da sauri Hafeez yajuyo
dan ganin mai k'wank'wasa kofan d'akin Meena, Daniel
yagani tsaye hannunsa d'auke da abinci da sauri Hafeez
ya taso dai dai lkcin Meena tabud'e kofa.
Wani irin takaici ne ya turnuqe Hafeez "cikin zuciyarsa
yace lallema yarinyan nan yaushe ma tawaye da har zata
fara bada umarni ana kawo mata abinci?sannan ma
tarasa Wanda zata sa ya kaimata abinci sai Daniel da irin
wannan shiga nata" Meena ce ta katse masa tunanin da
yakeyi, jiyayi tace sannu Daniel har ka kammala Daniel
yace "yes madam" hannu tasa zata amshi abincinta
Hafeez yadakawa Daniel tsawa yace "oyaa maida abincin
nan kitchn" jiki na rawa Daniel yajuya da abincin ixuwa
kitchn kmr yadda boss din nasa ya umarce shi.
Juyawa yayi gurin Meena fuskan nan a turbune ya nuna
tada hannu yace "ke yar qauye bari kiji kinyi kad'an
kidinga bada order a gdan nan wai dan akaimiki abinci
daga yau irin rana tayau bana so in qara ganin Daniel
kofar d'akinki danufin wai yakai miki abinci kinajina
koh? Kije da kanki kid'ibawa kanki inba haka ba kixauna
da yunwa" har Hafeez ya juya xai tafi sai kuma yadawo
ya dubi Meena duba na walaqanci yace "ke yar qauye
inaso daga yau kezakina shiga kitchn da kanki kidafa
abinci, take anan kuma yashiga kiran Daniel!
Jiki na rawa Daniel yaqaraso yace "yess oga" Hafeez
yadubi Daniel yace as 4rm today inaso karka qara bin
umarninta nacewa ka kawo mata abinci' Hafeez yariqe
kunnensa yana mainuna alamar warning ga Daniel
sannan yace "and then daga ynxu ita zata ke dafa
abincinta" Daniel yace okay oga.
Hafeez nafad'in haka yajuya yabar wajan, Meena
tsayawa tayi tana binsa da kallo cikin xuciyarta tace
"jibeshi da anyi magana yawani cewa mutum d'an kauye
qyaatt" juyawa tayi cikin d'akinta tad'auko hijabi tanufi
kitchn dan tasamu abinda tasawa cikinta domin kuwa
Meena intaji yunwa bata wasa da abinci.
Sumi sumi tanufi kitchn don tad'aura wani
abun,...Hafeez na nan zaune ta ratsa ta gefensa tawuce,
juyowa yayi yana kallonta tsaki yayi cikin xuciyarsa yace
"village gal"
Kitchen Meena tashiga nan tafara laluben abinda zata
dafa, tana cikin tsaka da dubawa ne taga hango kwalin
indomie da sauri ta janyo kwalin tad'auki indomie biyu
nan ta kunna rishow kasancewar bata iya amfani da gas
ba.
Take anan Meena tafara dahuwar indomie dinta wnda
taji albasa da attaruhu, ae fa nan gda ya kaure da qamshi
Hafeez kam mayen indomie take anan yajiyo qamshi na
dukan hancinsa wani irin yunwa yaqarajin tashigesa
kasancewar dama baiyi brkfst dinsa ba.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:00PM, 8/3/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣2⃣
Dasauri Hafeez yamiqe yanufi kitchen din, dai dai lokacin
ne kuma Meena ke qoqarin juye indomie dinta a plat,
yawun Hafeez ne yatsinke sai wani had'iyar yawu yake
(sbd Hafeez na mutuwar son indomie shiyasa ma kullum
gdan baya rabuwa da kwalayen indomie) Cikin natsuwa
Meena ta bud'e fridge din dake ajiye cikin kitchen
tabud'e tad'auki exotic mai sanyi sannan taduqa tad'auki
indomie dinta.
Hafeez

Please Login or Register in order to submit comment