Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana tunanin
nima zan amince ko nayimata dole".
Hafeez nafadin haka ya tashi yakoma daga cikin d'akinsa
dan basu waje sud'an tattauna
A hnkli Dr Muh'd yatashi daga inda yake yakoma gefen
Balkisu cikin tattausar muryansa yad'an duqa daf da ita
yace "toh Balkisu miye ra'ayinki agame da tayina ko ince
buqatata? Balkisu kam dukk kunya ta isheta qara duqar
da kanta qasa tayi,murya na rawa kmr wacce zatayi kuka
tace " a'a ni ina ganin baidace na amsa tayinka ba domin
kuwa wani 6angare na sashin zuciyata nasanar dani
cewa kawai tausayina ne aranka da kuma son
taimakamin ganin cewa Yaya Hafeez yayi aure matuqar
nima nayi.
Da sauri Dr Muh'd yace ko kusa Balkisu karki kawo
wannan gur6ataccen tunanin cikin zuciyarki, wlh
soyayyarki ta gsky ce acikin jini da 6argona yakamata
ace tuntunima kinfahimci hakan wlh Balkisu believe me
when I said banta6a son wata d'iya macce ba kmr ki ina
miki wani irin so Wanda ni kaina yana bani tsoro plss
kitaimakawa zuciyata nan yashiga yimata magiya
Ganin yadda ya marairaice fuska kmr zaiyi kuka yasa
Balkisu tace "to shikenan na amince ku gama mgn da
yaya Hafeeez tana fadin Haka ta tashi da sauri tashige
d'akinta gami da banko k'ofa direct gadonta tafad'a
tanajin wani irin nishad'i marar misaltuwa na shigarta.
Abangaran Dr Muh'd kuwa hannu yad'aga sama yana
jero adduo'i na farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga
ubangiji, yana gama addu'ansa d'akin Hafeez yanufa
yayi knckn Hafeez ya amsa yes shigo jiki narawa Dr
Muh'd yashiga cikin d'akin wani irin farinciki da nishad'i
yake ji nashigarsa da sauri ya rungumi Hafeez yace " yes
abokina adduar danajima inayi yau Allah ya amsamin
Balkisu ta amince ynxu amincewarka kawai nake jira.
Murmushi Hafeez yayi cikin zolaya yace congrat namaka
murna, ynxu kabari idan muka gama tattaunawa da ita
Balkisun zankiraka awaya muqarasar da mgnr, Dasauri
Dr Muh'd yace "wacce mgn za'a gama ae ynxu angama
komai tunda madam ta yarda ynxu kawai izininka nake
nema sbd ina so inturo magabata na, Hafeez kam jiyayi
gabansa yafad'i da sauri yace olryt karka damu I will giv
u a call let
Cike da zumud'i cikin fara'a Dr Muh'd yabar gdan.
Hafeez kam gabad'aya yashiga damuwa jiyayi wani irin
rashin sukuni ya ziyarcesa Dan haka da sauri yanufi
d'akin Balkisu dan yanuna mata cewa shikam bai amince
da wannan chakwakiyar ba.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [3:11AM, 7/27/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣3⃣
A hanzarce Hafeez yanufi d'akin Balkisu don ya nuna
mata rashin aminciwarsa akan wannan tsarin deal din da
takawo mai cike da rud'ani, a hnkli ya murza kofar
d'akin jin bud'e take yasa yashige d'akin kaitsaye turuss
ya tsaya cike da mamakin ganin Balkisu cikin wani
yanayin dabai ta6a ganinta ba.
Balkisu kwance take ta kife cikinta ta yayin da tad'an
d'aga kafafunta tana lilasu earpies ne a kunnenta tana
merming waqa cike da nishad'i" soyayyaa tayi mamaya
tayi charaf ta chafkemin zuciya nasamu saurayi
madubin duba inata murna" murmushi Hafeez yayi
gabad'aya ji yayi jikinsa yayi sanyi a hnkli yafice daga
cikin d'akin batare da tasani ba, falo yakoma yazauna
gabad'aya tunanin mafita Hafeez Yake nemawa kansa
amma dukk hnyar dayabi sai yaga cewa ya tauye dukk
wani farinciki na qanwartasa, kan Hafeez yagama
kulewa gabad'aya jiyayi bashida wata mafita ko dubara
domin kuwa BURIN HAFEEZ shine yaga tilon qanwar tasa
cikin farinciki dan haka komai xai iyayi dukk runtsi dan
ganin ya inganta farincikin Balkisu.
Take anan Hafeez yakira layin Dr M yasanar dashi cewa
yanason ganinshi zuwa gobe, Dr M yayi farinciki dajin
wannan kira dan haka addu'a kawai yyi yana maifatan
Allah yakaimu goben.
Abangaran Balkisu kam wani irin sabon yanayi taji
nashigarta kasancewar dukk wunin ranan nan suna
maqale da juna awaya ita da gwarzon likitan nata.
** ** **
Balkisu ce zaune cikin motarta tana zaman jiran
dawowar Meena daga talla kasancewar yau Monday ta je
skul shiyasa bata samu damar zuwa wajan Meena da
wuri ba sai ynxun.
Balkisu ta6ata kimanin awa biyu zaune cikin mota sai
zabga uwar hamma takeyi, agogon dake d'aure bisa
tsintsiyar hannunta take dubawa qarfe daya saura a
hnkli tasauqe wata irin ajiyar zuciya, kmr ance d'ago
kanki ae kuwa chan tahango Meena tafe da bokatin
alalarta.
Dasauri Balkisu taja motarta cikin sauri taqarasa wajan
Meena a hnkli tayi parkn motarta daf da Meena, zuge
glass din motar tayi a hnkli cikin rashin karfin gwiwa
takira sunan Meena, da sauri Meena tajuyo ganin Balkisu
ce mai kiran nata yasa tayi saurin niyyar barin wajan, da
sauri kuwa Balkisu tafito amotarta gamida shan gaban
Meena cikin raunatacciyar muryanta tace Meena plss ki
dakata kisaurareni koh da sau d'ayane daga wannan
baxan sake takuramiki ba namiki alqawari, zuwa ynxu
gabad'aya Meena tagama tsorata da Balkisu jiki na 6ari
Meena tace Dan Allah baiwar Allah ki kyaleni haka
naroqeki da sauri Meena ta ratsata gefenta da nufin ta
wucewarta, cikin sanyin jiki Balkisu tace "olryt Meena
kije karki saurareni amma na tabbata kinfi kowa
muradin son ganin mahaifiyarki tafito a gidan kaso, da
sauri Meena tajuyo fuskarta d'auke da mamaki qarara.
Murmushi Balkisu tayi tace " yes Meena nasan komai a
gameda lbrinki babu wani 6oye 6oye ynxu daya rage a
tsakaninmu, wlh kiyarda dani banida niyyar cutar dake
hasalima nidake nakeson muhad'a kai mutaimaki juna,
Meena tamaimaita abinda Balkisu tace mutaimaki juna??
Kmr ya mutaimaki juna? Balkisu tace "kwarai
kuwa,kuma hakan nidake gabad'aya zai amfanemu,
Murmushi Meena tayi tace " anya kuwa kinyi dogon
nazari akan wannan maganar taki? Balkisu tace ae ynxu
kece zanbaiwa damar yin tunani akan mgnr danaxo
muki da ita.
Meena ta gyara bokatin alalarta ta fuskanci Balkisu tace"
okay fadi mgnr naji Allah yasa zan iya" Dafa kafad'arta
Balkisu tayi cike da qarfin gwiwa tace no karki damu
insha allahu hakan bazai gagareki ba.
Balkisu tadubi Meena tace inba damuwa inason kizo
mushiga daga cikin mota ta hakan zaifi sirri, dasauri
Meena tad'ago tadubi Balkisu, Balkisu tamaqe kafad'a
tace yadai ko dai har ynxu baki gama yarda dani bane?
Meena ta girgiza kanta tace a'a ba haka bane mujee.
Cikin motar Balkisu suka shiga Meena jitayi wani irin
sanyi yaratsata a hnkli tadubi Balkisu tace inajinki kiyi
sauri kada namakara. Balkisu tadubi Meena sannan
tad'auke dubanta daga gareta tafuskanci gabanta,
Sannan takira sunan Meena bayan Meena ta amsa
sannan tasake cewa kinsan menake so dake? Meena ta
girgiza kanta tace a'a sannan Balkisu tajinjina kanta a
hnkli tasauke idanunta akan Meena tace "so nake ki auri
yayana, da sauri Meena ta gwalo idanu waje gamida dafe
kirji tace mekikace? murmushi Balkisu tayi domin
batayi mamakin ganin Meena tayi shock dajin buqatarta
ba, Balkisu tajinjina mata kai tace tabbas abinda kikaji
shinafad'a inaso ki auri yayana domin inason ganin sauyi
da farinciki a tattare dashi, da zaran kinyimin haka
nikuma nayi alqawari konawa ne zankashe domin na
d'aukaka qara ganin cewa Mahaifiyarki tafito daga gdan
yari, sannan inaso karki manta cewa nasan komai
agamedake basai kinyimin wani dogon bayani agameda
matar babanki ba namiki alqawarin zanji da komai kedai
kawai nabaki nan zuwa gobe kije kiyi tunani
Gobe da yamma zandawo domin naji shawaran dakika
yanke. Balkisu nafadin Haka tabudewa Meena qofa cikin
sanyin jiki Meena tafice daga motar yayin da Balkisu
kuma ta wuce tanufi gda nan tabar Meena tsaye cikin
tunani.
Note: akan masu complain cewa banason yin typn da
wuri inaja muku rai, wlh sam bahaka bane karku manta
fa cewa nabaku uzurina plss kumin afuwa insha allahu
zanqoqarta nagode.
®NWA
[11:54AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣4⃣
Cikin daren ranar Meena kasa runtsawa tayi, babu
abinda take tunawa sai ranar da tafara had'uwa da yayan
Balkisu irin yadda yanuna mata kyankyami da tsantsar
tsana qarara a fuskarsa, dan haka tasan tabbas a zaman
auransu xata cutu sai dai kome xainuna mata xa ta iya
shanyewa sbd lura da tayin da bashine da kansa yaxo
neman auranta ba hasalima qanwarsa yaturo to komiye
dalilinsa nayi haka? Nan fa tafara jeroma kanta
tambayoyi wnda ita kanta batada amsarsu.
A ynxu kam gabad'aya tunanin Meeena yatafi akan
yadda rayuwarta zata kasance a hannun wanda bai ko
kaunar ganinta gashi kuma a wani 6angare tana buqatar
mahaifiyarta kusa da ita, Dan haka ta gama yanke
shawaran amincewa auransa don tasamu damar
taku6utar da mahaifiyarta daga gdan kaso.
Da wannan shawaran aranta har bacci 6arawon yayi
awon gaba da ita.
** ** **
Washe gari
kafin kowa ya tashi a gdan Meena tariga kowa tashi kmr
yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne tafara ayyukanta
kafin qarfe 6 kuwa Meena tagama ayyukan ta tsaf, ruwan
sanyinta tad'iba tashiga bayi ta watso ruwa, bayan tafito
ne tadauki tallan kunun gyad'anta tanufi chan Bolori
primary skull inda chan ne Meena zata had'u da Balkisu.
A bangaran Balkisu kuwa ita ma sauri kawai take tayi sbd
bata son ta had'u da Hafeez kasancewar tasan sai yayi ta
jero mata tarin tambayoyi akan wacce take son had'ashi
aure da ita, gashi ita kuma basu gama mgn da Meena ba
Dan haka bata da kwakkwarar amsar da xata bashi,
hakan ne ma yasa tayi tunanin tad'aga appointmnt dinsu
wnda tace su haduwa da yamma tamai dashi zuwa da
safe.
Kafin Hafeez yafito kuwa tuni Balkisu tafice a gdan,
Bolori primary skul chan tanufa a niyyarta dama intaje
tasa yara sunemo mata Meena tunda dama nan ne
wurin sana'arta, Balkisu nashiga skul din ba tawani sha
wahalan neman Meena ba hangota tayi zaune ta rafka
uban tagumi.
Meena! Meena!! Kmr a mafarki taji ana kwala mata kira
dasauri tayi firgigit ta juya, Balkisu tahango zaune cikin
motarta dasauri Meena tamiqe tanufi wajanta.
Murmushi Balkisu ta sakar mata sannan suka gaisa da
junansu daga bisani tayi mata ixinin shiga cikin motar, a
hnkli Meena tabud'e murfin motar tashiga.
Jan motar tayi cikin nutsuwa suka bar gefen makarantar
chan wata anguwa suka nufa, sai da Balkisu ta tabbatar
sund'anyi nisa sannan tayi parkin, Da murmushi d'auke
a fuskar Balkisu ta dubi Meena tace "toh Meena kmr
yadda kikaji nace miki zanxo domin naji shawaran
dakika yanke toh gani nan na iso gareki don jin shawarar
da kika tsaida shin kin amince kuma kinshiryawa auran
yayana??
Meena ta sadda kanta qasa hawayene kawai keta
kwaranya cikin sanyin murya tace na amince da auransa
matuqar xankasance tare da mahaifiyata. Balkisu
tajinjina kai tace dakyau amma kinsan dalilina nason ki
auri yayana? Meena ta girgiza kai alamar a'a
Ajiyar zuciya Balkisu tayi sannan tamaida dubanta ga
Meena gabad'aya idanun Balkisu sunrine izuwa ja! Cikin
natsuwa takawo lbrin rayuwarsu tasanar da Meena, nan
Meena tashiga jinjina al'amarin cikin zuciyarta tana mai
tausaya musu sai dai kuma yadda taji lbrin Hafeez ta
tabbata cewa kawai tad'auko ma kanta dala ba gammo
ne amma kuma inta tuna mahaifiyarta sai taji wani irin
kwarin gwiwa na shigarta.
Balkisu tadubi Meena tace tabbas na yaba da kyawawan
d'abi'unki da yadda kika iya maida mgn ga masu hali irin
na yayana hakan yasa na tabbata cewa zaki iya dawo min
da Yayana normal kmr yadda yake a lkcin baya.
Murmushin yaqe Meena tayi sannan tadubi Balkisu tace
"Allah dai yabani ikon cikamin alqawarinki sbd naga
kinsa hope dinki akaina sosai, Balkisu tad'anyi yar dariya
tace "Meena kikwantar da hnklinki kedai kawai kisa
aranki daga gobe zuwa jibi muna iya xuwa a kowanne
lkci gdnku dan neman auranki sannan inaso kada
kifadawa kowa wannan mgnr har sai komai yakankama,
cike da jin kunya Meena tace insha allahu.
Meena har tabud'e kofar motan da niyyar tafita Balkisu
takira sunanta, cikin natsuwa Meena tajuyo.Balkisu tace
" aff namanta intambayeki yau mekike sai dawa ne?
Meena tace kunun gyad'a ne.
Balkisu tad'anyi murmushi kmr yadda hakan yaxama
jiki agareta sannan tace" gabad'aya kunun na nawane?
Meena tace na d'ari biyar ne zaro dubu biyu tayi
ajakarta tamiqawa Meena sannan tace gashinan kiyi
sadaka dashi haka har zuwa gobe kiyi manejin wannan
bnfito da kud'i bane.
Da farko Meena tanuna kin amincewarta sai da Balkisu
tad'an lallamota sannan tasamu ta ansa.
Direct gdan mallan Zakiru Balkisu tanufa don cika
alqawarinta kmr yadda tafada mishi cewa dukk halin da
ake ciki agame da Meena xataxo tasanar dashi (mgnr
lectures kam yau bbu ita)hakanan ta juya akalar motarta
izuwa gdan mallan Zakiru.
®NWA
[1:14PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:37AM, 7/29/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣5⃣
(Very sorry readers nayi mistake din numbr nasa 23 sau
biyu makin nasa 24 nayi mistk ynxu 25 xamu tashi)
Kamar kullum yau ma ya kasance mallan Zakiru na nan
cikin Zaurensa yana bitar karatu alqur'ani, da sallama
Balkisu tasa kai cikin zauren tare da neman izinin shiga,
cikin nutsuwa Mallan Zakiru yakai qarshen aya sannan ya
rufe qur'anin ya ajiye agefensa, cikin sakin fuska yayi
mata Iso
Mai d'akinsa mallan Zakiru yashiga yakira dan
takawo masa taburma, Inna takawo taburman tana
qoqarin shimfid'awa Balkisu tayi saurin amsa ta
shimfid'a tabarman, bayan ta xauna sannan suka gaisa
sannan Inna, ficewa Inna tayi tabasu waje kmr yadda
tasaba in mallan yayi baqi bata zama.
Balkisu tadubi Mallan Zakiru fuska d'auke da murmushi
kai dagani kasan tana cikin farinciki, "tace Baba kmr
yadda na sanar dakai cewa dukk yadda ake ciki a game
da Meena zansanar maka wato naafad'a mata inasone ta
auri yayana ynxun nan muka gama mgnr da ita sannan
ta amince zata aureshi nikuma nayi mata alqawarin
bayan bikinsu zanfito da mahaifiyarta a gdan yari.
Mallan Zakiru yyi murmushin jindadi yace "Masha
allahu' Allah sarki Aminatu allah ya sanya alkhairi,
Balkisu ta amsa da ameeen daga bisani Mallan Zakiru
yadubi Balkisu fuska d'auke da damuwa yace "amma
kmr yaushe ne kike xaton zaku turo magabatan ku don
neman auran Aminatu?
Balkisu tace "toh baba muna so mu tsaida ranan ne
tukun, mallan Zakiru yajinjina Kansa sannan yace toh
wacce shawara kika yanke agameda tunkarar Yagana
don niman auran Aminatu?
Balkisu tace Baba karka damu inaso ne in angama ajiye
mgn d'aya zamu turo qanin mafaifinmu sbd in.... kafin
Balkisu ta qarasa abinda take son cewa Mallan Zakiru
yace "Sam kada kiyi haka sbd dukk cikin garin nan bbu
wnda baisan waye mahaifinku ba nikuwa nafi kowa
sanin cewa muddin Yagana tagano cewa Aminatu gdan
masu hali zatayi aure toh fa baxata amince ba.Sbd dukk
wata hanya da tasan zatabi don ganin cewa ta lalata
wannan auran toh fa zatayi Kuma babu wnda ya isa
yadakatar da ita, Dan haka inaso kibar komai a hannuna
sannan kitabbatar da cewa cikin qanqanin lkci zakusa
lkcin auran don gujewa fitina.
Balkisu tad'anyi jimm! Sannan tadubi Mallan Zakiru
sannan tace amma Baba kana ganin ta wacce hanya
zamu bi? Mallan Zakiru yyi murmushi yace zansamo
wani daga cikin kauyanmu inyimata nuni da cewa shine
Wanda yakeson ya auri Aminatu amma fa dukk wani
wakili ko waliyi Na ango zaifito ne daga 6angaranku. Nan
Mallan Zakiru ya tsatssara ma Balkisu matakin da zasubi
don gujewa sharrin Yagana
Kwarai da gaske Balkisu taji dadin shawarwarinsa ae
kuwa nan tayi taxu bawa Mallan zakiru godiya, tana
mainuna jindadin taimakonsa gareta.
** *** ** ***
Qarfe hud'u Na yamma na bugawa Dr Muh'd na isa
gdnsu Balkisu don cika umarnin Hafeez kmr yadda
yabuqaci ganinsa.
Hafeez kam yau through out bai ko fita bakin get ba yana
nan cikin d'akinsa yana sana'ar tashi wato tunani, kwan
kwasa k'ofar dayaji anayine yadawo dashi daga duniyar
tunanin da yatafi, a hnkli yamiqe batare da yace komi ba
yanufi k'ofar bud'ewa yayi Dr Muh'd ne yagani tsaye
cikin dakakkiyar shaddarsa mai kyan gaske sai wani zuba
qamshi yakeyi, Hafeez yadubi Dr Muh'd har yaso yabashi
dariya sai kuma yabasar hannu yamiqa masa suka gaisa
sannan Hafeez yace dashi yaje Falo yad'an jira gashinan
zuwa
Dr Muh'd kam cike da zumud'i ya nufi falo yazauna dan
jiran Hafeez
Toilet Hafeez yashiga ya sakarwa kanshi ruwa yajima
a haka daga Bisani kuma ya silla wankansa, qananan
kaya Hafeez yasaka blue riga da baqin wando dukk da
cewa Hafeez baifiye son qananan kaya ba amma yau su
yaji yana muradin sawa turare mai dadin gaske ya fesa
sannan yafice a d'akin.
Falo ya nufa kaitsaye yana shiga kuwa ya tarar da Dr
Muh'd na nan zaune yana jinran fitowarshi, murmushi
Hafeez yayi ya girgixa kansa.
Bayan sund'an tattaba hira sama sama' Hafeez ya
dubi Dr Muh'd jiki a sa6ule yace "amm abokina wato
dalilin da yasa nace kazo ina neman ka yau shine inason
inji daga gareka shin kashirya auran Balkisu? In kashirya
wa auran inaso nan zuwa gobe kaje chan sabon fege gdn
uncle Ma'aruf kasanar dashi dukkan wani jawabi dakake
tafe dashi akan auran Balkisu.
Hafeez nafad'in haka ya sadda kanshi qasa cike da
damuwa da qunar zuci, dasauri Dr Muh'd yamatsa kusa
dashi a hnkli ya dafasa yace "tabbas abokina nasan kana
cikin damuwa da alhenin rabuwa da tilon qanwarka
amma kasani zaman Balkisu a gurina tamkar tana
hannunka ne insha allahu nayimaka alqawari baxan ta6a
cutar da qanwarka ba, zan riqeta amana tamkar kaine
awajan sbd inason Balkisu sosai inayimata so Wanda
baxan iyaganin abinda zai cutar da ita ba.
Da sauri Hafeez yarungume Dr Muh'd yana kukan
farinciki sannan yace "nagode maka abokina sannnan
inaso kasa aranka cewa Balkisu amanace a hannunka
sannan inaso idan zaiyuwu a d'aura auranku cikin wani
sati if possible"
Dasauri Balkisu taqaraso cikin falon fuskan nan sha6e
sha6e da hawaye cikin muryan kuka tace haba Yaya
Hafeez aure na nikad'ai nakeji kana mgn banji kana
mgnr naka auran ba, karka manta da alqawarinmu sbd
nariga nasamo ma nagartacciyar mata Wanda nake da
hope din cewa zata kularmin da yayana yadda yakamata.
Rasss! gaban Hafeez yafad'i, shidai bai San mieyasa Sam
baya qaunar yaji anyi mishi mgnr wata d'iya macce ba,
balle kuma harta kai ga mgnr aure.
Jiki a sanyaye Hafeeez ya maida dubansa ga Balkisu yace
"wai wacece wannan yarinyar dakike son Na aura
wacece ita a ina kika santa ya akayi kikasan tana da
nagartaccen hali meyasa kike son tilastani nayi aure?' a
jere Hafeez ya watsoma Balkisu tambayoyi?"
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:52AM, 7/30/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣6⃣
D'ago Jajayen idanunta tayi Wanda suka rine sbd kuka, a
hnkli ta sauk'esu akan Hafeez, wani irin kukane ya sake
kubce mata Wanda ita kanta batasan dalilin yinsa ba,
cikin dishashiyar muryanta tace "Yaya Hafeez karka ta6a
tunanin cewa auran wacce nakeson had'aku zai zama
cutarwa ko danasani a gareka wlh kayarda dani cewa
nafi amincewa auran Meena atattare da kai" Meena!!
Hafeez yamaimaita sunan da sauri k'urawa Balkisu idanu
yayi gabad'aya sai yaji tabashi tausayi, gashi akan
wannan Meenar da ta dage dole ne yaga cewa yadaure
ya aurenta mutuqar hakan zai sata farinciki da walwala.
Dasauri ya miqe tsaye daga zaunen da yake jawota yayi
jikinsa ya rugumeta nan yashiga bubbuga bayanta cikin
sigar lallashi, cikin murya qasa qasa Hafeez yace kwntar
da hanklinki Billyn mama na amince zan auri dukk
wacce kika kawomin ita matsayin matar aure, amma sai
dai I have one request 4 u, k'ura mishi idanu Balkisu tayi
alamar shi take saurare dasauri ya janye jikinsa daga
nata sannan yaci gaba da mgn "na amince zan auri
yarinyar da kikeson kawota cikin rayuwata sbd inada
yaqinin cewa bazaki ta6a had'ani da wacce bata dace da
rayuwata ba, sai dai kuma inaroqonki plss kada
kitilastamin zuwa d'aurin auren sbd hnkli da
kwakwalwata bazasu iya jurar ji ko ganin cewa wai yau
nike aure ba plss kisamu komawaye ya wakilceni sannan
dukk abinda kikaga yadace kawai kiyi nabar miki wuqa
da nama" Hafeez nafadin haka yayi sauri yabar falon cike
da d'acin rai.
Jikin Balkisu gabad'aya yayi wani irin sanyi, a hnkli Dr
Muh'd yaqaraso gareta cikin muryan lallashi mai nuna
tsantsan tausayi ga masoyiyar tashi, nan fa ya xage
damtse yayi ta tausar zuciyar cikin hikima da kwarewa,
sai gashi kuwa cikin qanqanin lkci ta manta da komai.
A Bangaran Hafeez kuwa d'aki yashiga ya kulle kansa ji
yayi gabad'aya duniyar tamasa xafi.
** ** ** ** **
Kmr yadda Mallan Zakiru yayi ma Balkisu alqawari haka
kuwa akayi yaje can qauyansu yasamo wani matashin
saurayi dake aikin faskare.
Abangaran Dr Muh'd shima yaje yasamu ya gana da
qanin mahaifinsu Hafeez, wato uncle Ma'aruf, uncle
Ma'aruf kam bayan binciken daya qarayi akan hallayan
Dr Muh'd yasamu kyakkyawan yabo hakan yasa ya
amince domin yafi kowa farinciki dajin lbrin. Dan haka
cikin qanqanin lkci aka sanya lkcin bikin Hafeez da
Balkisu
Mallan Zakiru da kansa yaje har wajen Yagana
yasanar da ita cewa d'an uwansa ne Wanda yaxo daga
qauyansu yaga Meena yakuma nuna cewa yana son
auranta, Yagana tayi farin ciki jin ancemata daga noma
sai faskare sune aekinsa koshi faskare da noman
aekatau dinsu yakeyi ana biyansa dan haka kenan su
Meena za'a sha noma wani irin farin ciki ne ya lullu6eta
datagama wannan tunanin, Dan haka batare da 6ata lkci
ba tanuna amincewarta.
Mallan Zakiru yyi matuqar farin ciki da hakan domin
kuwa hakarsu daf take da cimma ruwa.
Komai ya kankama yan'uwa da abokan arziqi anfara
hallara, gwaggwanin su Balkisu da mamaninta dukk
sunzo nan suka fara gyara diyar tasu Balkisu tafito fasss
da ita baqaramin kyau tayi ba.
Bangaran Yagana da yarta kuwa kullum basu da aiki
sai gori da kyarar Meena wai tarasa Wanda xata jaju6o
musu sai d'an kauye kauyan ma futuk nan fa zasu taru
suyita dan gware tama kai.Meena kam ko uffan bata
cewa dasu domin ita tunaninta a kullum bai wuce yadda
zata kasance a wani gda a matsayin matar wani
ba,sabuwar rayuwar da zata shiga kullum shike addabar
tunaninta.
Plan din Mallan Zakiru da Balkisu komai Na tafiya yadda
suke so da taimakon ubangiji.
RANAR DAURIN AURE
Ranar juma'a da misalin qarfe biyu na rana bayan
ansauqo a masallaci aka d'aura auran HAFEEZ
ABDULLAHI SHARIFF tare da AMINATU SULEIMAN akan
sadaki dubu hamsin, inda kuma suka sake garzayawa aka
sake d'aura auran BALKISU ABDULLAHI SHARIFF tareda
DR.MUHAMMAD SHU'AB GASHU'A an d'aura auransu
akan sadaki dubu d'ari.
***
Dubu uku Mallan Zakiru yacira daga cikin sadakin Meena
yakaiwa Yagana yace gashinan wannan shine sadakin
Aminatu, zokaga farinciki awajan Yagana nan fa ta
sokare kud'in a ha6ar zaninta
A cewar Yagana tunda Meena takala futuk ta aura to
miye zata siyamata tunda dai d'an kudin da Meena
kesamowa yaqare a kudin hayarta dan haka baxata
siyamata komai ba.
Da misalin qarfe hud'u na yamma Mallan Zakiru ya je
gurin Yagana wani tsadadden material da sarqa da yan
kunne da takalmi da kyale set komai yayi match kayan
sun matuqar haduwa, Balkisu ce ta aikomishi tace
yabawa Meena idan anzo d'aukar amarya tasanya
ajikinta. Hakan yasa Mallan Zakiru yakawo kayan dan ciki
alqawarinta.
Yagana naganin kayan dake hannun Mallan Zakiru dukk
tabi tawani rud'e, miqa mata kayan yayi yace "Yagana ga
wannan kayan daga hannun mijin Aminatu sukafito yace
dan Allah atabbatar da tasa wannan kayan zuwa an jima
sannan kisanar mata cewa kartabari kokadan kayan
sulalace sbd arosu yayi daxarar ta isa gdnshi ciresu
xatayi yamaidasu inda ya aro, wata irin dariyar k'eta
Yagana tafara dukk farinciki yabi ya lullu6eta.
Hakanan akayi shagalin biki a bangaran Balkisu da Dr
dinta, sa6anin Hafeez wnda ya kulle kansa cikin d'aki.
Misalin qarfe tara na dare wasu irin manya manyan
motoci tsadaddu ne sukayi fakin a k'ofar gdansu Meena,
da sauri wata gwaggonsu Hafeez tashiga gdan Cikin shiga
ta kece raini dukk da kasancewar dare ne amma shigar
da tayi kallo d'aya zakayimata kasancewa an narka daloli.
Yagana kam tabawa Aminatu kayan tasa baqaramin kyau
sukayi mata ba, ganin tayi kyau abinta yasa Yagana dukk
haushi ya isheta nan tashiga dangwarar kanta
tanayimata gori sai wani kusheta takeyi.
Ana cikin hakane Gwaggon Hafeez Hajiya Nana
tashiga domin tafiya da Meena.
Ae kuwa gabad'aya kan Yagana yad'aure shuru kawai tayi
tana kallon ikon Allah azatonta dukk wad'annan manyan
matan suma hayarsu akayi, al'amarin bai qara tsinkar da
Yagana ba sai da tabisu zuwa waje taga wasu irin dan
qara dan qaran motoci Wanda sune suka zo d'aukar
amarya Meena. Yagana tanaji tana gani aka sanya Meena
cikin mota sakeke tayi da baki cike da mamaki domin ita
takasa gane wannan Al'amarin jitayi andafata da sauri ta
juya Hajiya Nana ce cikin sigar lallashi take lallama
Yagana domin ita a tunaninta Yaganan tana cikin alhenin
rabuwa da diyarta ne, nan taciro dubu hamsin tamiqawa
Yagana. Cikin mota takoma sukaja take anan sukabar
cikin unguwar.
Yagana na ganin haka ko gyale babu a jikinta balle
takalmi haka tanufi gdan Mallan Zakiru cike da masifa
domin kuwa bakin nan nata taf yake da tambayoyi
Wanda babu mai amsamata su sai Mallan zakiru.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:47AM, 7/30/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣7⃣
Jiki Na 6ari haka Yagana ta shiga gdan Mallan Zakiru ko
sallama babu ta afka musu cikin gda, dai dai lkcin Mallan
Zakiru yafito daga bayi hannunsa riqe da buta yana kiran
mai d'akinsa ta kawo mishi abinci, Mallan Zakiru sai ji
yayi ance "toh algungumi munafiki azzalumi mai sai da
yaran mutane" da sauri Mallan Zakiru yajuyo danganin
mai mishi wannan alkaba'iran Yagana yagani tsaye ko
mayafi babu balle takalmi ta wani riqe qugu sai

Please Login or Register in order to submit comment