Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Meena bazata ta6a bani
had'in kai ba.
Nan Balkisu tashiga tunanin taya za'ayi tasan lbrin
Meena, gashi dai tasan cewa dukk yadda taso taji lbrin
Meena baxata ta6a fara tunkarar Yagana ba.
Cikin mota Balkisu tashi tazauna d'aukara kanta tayi
bisa sitiyarin motan gabad'aya tunaninta ya kwance
babu abinda take tunani face mafitar wanda zata
tunkara.
Kmr wucewan wasu yan'mintina Balkisu tad'ago da
kanta da sauri wani irin murmushin farinciki tasakar wa
kanta da sauri tace yess! Wannan shine kad'ai mafita,
wuta tabawa motarta da sauri tafice a layin ta hau titi.
Baifi tafiyar minti 2 ba tayi parkn motarta gefen
hanya da sauri tafito ta tsallaka titin tanufi daya site din.
Wurin Baba mai shayi tanufa, ko da isarta bata iske shi
ba wasu yan samari guda hud'u ta iske sunata firar
kwallo(ball) da sallama Balkisu ta isa garesu, gabad'aya
suka amsa mata, cikin natsuwa Balkisu ta gaishesu bayan
sun amsa sannan tace Dan Allah ina Baba maishayi wnda
ke sai da shayi wurin nan? Daya daga cikinsu yace Allah
sarki baba zakiru mai shayi kike nufi? Ae yau tsawon sati
d'aya kenan bai fito gurin sana'a ba sbd ciwon qafa
yasashi agaba.
Balkisu tayi jimm! Tana jinjina al'amarin cikin ranta,
chan tace Allah sarki Dan Allah koh zan iya sanin gdnshi?
Wanda keyi mata bayanin yace eh ae bbu nisa. Nan yyi
mata kwatance.
Balkisu tayi musu godiya sannan tanufi motarta tajuya
zuwa inda akayimata kwatancen, Balkisu batayi mamaki
dan ganin cewa layi daya suke da su Meena ba, sai dai
Mallan Zakirun gdnsa nafarkon shiga cikin kwanar,
wanda sukuma Meena gdnsu nad'anda nisa tsakaninsu.
Gdan da wadannan samarin suka kwantanta mata nan
tanufa, shigatayi kaitsaye da sallamarta. Wata mata ta
tarar tsakar gdn tana sassaqa wani itace dagani kasan
magani ne, da sauri matar tadubi Balkisu cikin nuna
rashin sani ta amsa sallamarta sannan tasaki fuskarta
gami da cewa "sannu da zuwa baquwa iso daga ciki",
Balkisu tayi farinciki da hakan ganin yadda yar
dattijuwar matar ta tarbeta.
Shimfid'amata tarbuma tayi sannan ta umarceta da
tazauna, Balkisu nazama tagaida dattijuwar matar cike
da ladabi.
Cikin fara'a kuwa ta amsa sannan tace "sai dai bangane
fuskar ba?" Balkisu tayi murmushi tace hakane Inna
dama nasamu lbrin Baba zakiru bashida lafiya shine
nazo naduba jikin nashi, murmushi tayi tace Allah sarki
sannunki kinji angode sai dai mallan din baya gda yatafi
ganin likitan gargajiya anan wani qauye sai zuwa anjima
da yamma zai dawo, Balkisu tagyad'a knta tace toh
shknan badamuwa Allah ya bashi Lpy ni zanwuce gobe
in Allah yakaimu zandawo. Hakanan tafice a gdn tanufi
gda tana mai addu'ar Allah yasa tasamu abinda take
nema agarshi.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [7:04AM, 7/21/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣8⃣
Washe gari da sassafe Balkisu tafito tsaf cikin shirinta Na
baqar doguwar jallabiya da d'an guntun hijabinta pink
colour, dukk da cewa batayi wata doguwar kwalliya ba
amma tayi matuqar kyau. Falo ta nufa sannan takira
Daniel tasanar dashi irin brkfst din da xai had'a wa
Hafeez, sannan takoma ta sanar dashi cewa bada ita zai
had'a brkfst din ba. Hakanan Balkisu tafice batare da taci
komai ba, domin a daren jiya da zarar Balkisu ta rufe
idanunta Meena kawai take gani dan haka dakyar taga
gari ya waye mata.
Da fitarta kuwa bata nufi ko ina ba sai Bolori anguwansu
Meena, "wannan karon Balkisu bata nufi gdnsu Meena
ba k'ofar gdan Mallan Zakiru ta tsaya,
A hnkli tafito daga cikin motarta ta nufi gdn Mallan
zakiru, cikin zaurensa ta tarar dashi zaune yanata
karatun al-qur'ani, jiki a sanyaye tayi masa sallama.
Mallan zakiru na kaiwa qarshen ayaa! Ya tsaida karatunsa
gami da amsawa Balkisu sallamarta cikin sakin fuska
Fuskan nan d'auke da fara'a yace baiwar Allah shigo
daga ciki, Cike da qarfin gwiwa Balkisu tashiga cikin
zauren, tana qoqarin zama a qasa kenan mallan Zakiru
yace haba ke kuwa yazaki zauna a qasa da wayonki?
Balkisu tayi murmushi tace laaah! Baba wlh bakomai,
Mallam Zakiru yace a'a ba'ayi haka ba d'an dakata, nan
yashiga kwalama uwar d'akin nasa kira bayan ta amsa
yyi mata umarnin takawo tabarma, cikin qanqanin lkci
kuwa sai gata tafe da tarbama. Da zuwanta ta
shimfid'awa Balkisu tabarma sannan suka gaisa
amutunce Wanda bayan sungaisane daga bisani takawo
mata ruwa sannan ta tashi takoma daga ciki.
Balkisu taji dadin karamci irin na gdn Mallan Zakiru
hakan kuwa yaqara bata qarfin gwiwar tinkararsa da
tambayoyin da take qunshe dasu, Dan haka byn ta
jajanta mishi ciwon qafansa, yace da sauqi, taqara
daurawa dacewa Allah yabashi Lpy yasa kaffarane.
ameeeeeeeen yace yanamai yin murmushi
zauren yayi shiru na wasu yan mintoci can Mallan Zakiru
yace "ae jiya mai d'akina take sanar dani cewa nayi
baquwa tayi tayi mini misalinki amma Sam nakasa
ganewa sbd Sam bantaba tsammanin kece ba amma
ynxu dana ganki natabbar lkci daya cewa kece kika zo
nemana jiya, Balkisu tayi murmushi tace Allah sarki, eh
wlh haka ne nice
Mallan Zakiru yadubi Balkisu da kyau yace Baiwar
Allah lafiya kuwa?Balkisu ta gyara zamanta tafuskanceshi
dakyau tace tabbas lfy dama naxo inyimaka wata yar
tambayane, Mallan Zakiru yajinjina kansa yamaimaita
abunda tafada "tambaya"?
Balkisu tagyad'a kai alamar eh, Mallan zakiru yace toh
Allah yasa nasani.
Balkisu tad'an ja numfashi a hnkli sannan tace
dafarko dai sunana Balkisu Abdullahi Shariff nazone
inaso inyimaka wata yar tambaya akan rayuwar Meena
inhar kasani.
Sbd tun ranar da muka hadu da yarinyan nan Allah
yasamin tausayinta araina naji zuciyata na azalzalata a ko
da yaushe akan nataimaka mata, toh amma sai dai
yarinyar kwata kwata taqi amincewa dani balle ta yarda
dani na taimaka wa rayuwarta, da ita nake kwana nake
wuni araina Dan Allah idan kasan wani abu dangane da
rayuwar yarinyan nan toh ina roqonka da kasanar dani,
wlhy bani da niyyar cutar da ita hasalima inason taimaka
matane.
Mallan zakiru yayi murmushinsa cike da dattijantaka,
sannan yace" tabbas yarinya bakiyi kama da miyagun
mutune masu cutarwa ba hasalima nasan waye
mahaifinki marigayi Alhaji Abdullahi, Balkisu najin haka
tayi murmushi farinciki tace eh hakane.
Mallan Zakiru yace tabbas zanfadamiki ko wacece
Aminatu, amma da sharad'i guda daya" Balkisu ta dan
muskuta kadan tace Baba kafadi kowanne sharad'i ne
insha allahu zanbi sharud'anka. Mallan zakiru yace
madallah, dama sharadin nawa shine inaso kimin
alqawarin cewa dukk wani abu dakikaji dangane da
lbrinta hakan bazaisa kijuya mata baya ba??
Balkisu tace insha allahu nayimaka alqawari, Mallan
Zakiru ya jinjina kansa sannan yadubi Balkisu......
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:13PM, 7/22/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode1⃣9⃣
Mallan Zakiru yaja dogon numfashi mai cike da alhenin
tuna abinda yajima yana damun zuciyarsa, a hnkli ya
sake kallon Balkisu sannan yace "Wato mahaifin Aminatu
Mallan suleman Wanda akafi sani da Sule, abokina ne shi
tun tsawon shekara ashirin da suka gabata. Asalinsu yan
Gwaza ne nan cikin jahar borno, Sule yakasance aminina
tun awajen sana'armu ta gyaran kekuna da mashin anan
babban get na Monday market, Sule nada mata daya
Rabi wacce itama yar garinsu ce da aurensu atare muka
gansu. Mallan Sule yakasance mutun mai son mutane
gashi Allah yadaura masa son yara, sai dai kuma babban
abunda ke damunsa shine yadda suka dauki tsawon
shekaru goma sha biyu amma Sam Rabi ko 6atan wata
bata ta6ayi ba.
Hakan yasa Sule yayi tunanin qara aure, Rabi kuwa Sam
bata tashi hnklinta ba kasancewarta macce mai sanin
yakamata Sam batada yawan hayaniya, ana cikin hakane
Sule ya auro Yagana, Allah cikin ikonsa Yagana nashiga
cikin gdan baifi da wata uku ba sai ga d'an qaramin
cikinta ya baiyanna.
Ana cikin wannan hali sai ga Rabi itama cikin hikima
da kyauta ta ubangiji sai gashi itama tasamu nata rabon,
wai karkaso kaga farinciki awajan Sule.
Abangaran Yagana kam abun ba haka yake ba, domin
babu irin masifar da batayi ba wai Rabi munafukace
dama tana haihuwa shine dantaga tasamu ciki wato
itama shine takwaso nata sbd gasa.
Haka nan kwanaki sukayi ta shud'ewa yayin da Yagana ke
azabtar da Rabi batare da sanin shi abokin nawa ba,
Gashi a kullum Yagana nayimata barazanar zata
kasheta a dukk lkcin da ta kuskura tasanar da mijinsu
irin abubuwan da take mata.
**
Bayan wata tara Yagana ce tafara haihuwa tasamu d'anta
namiji aka sha biki, bayan wata biyu itama Rabi Allah
yasauqeta lafia inda itama tasamu diyarta macce wato
Ameenatu.
Haka nan sukaci gabada zama na rashin jindadi
mussaman ma ita Rabi wacce take hak'uri da hallayar
Yagana.
Dukk wani hali na qunci da azabar da Rabi ke sha
abokina Sule sam bashi da masaniya akai".
Ana cikin hakane watarana muna cikin tsaka da aikin
kanikan cinmu wani bawan Allah yakawo mana gyaran
mota, Wanda mukuma bamu fiye son gyaran motociba
sbd bamu kware da gyaranta ba, amma awannan ranar
cikin ikon Allah sai wani bawan Allah yakawo mana
gyaran motarshi Sule ne yakarba yadan soma gwada
gyaranta.
Dakyar Sule ya gano inda matsalar motar take, wato
lagireto din motan ne yasamu mtsl dole Sule yaje
yanemo "jak" wato abin dake d'aga mota, hakanan
yasamu nadan taimaka masa yasa jak din motar
tadantashi daga bisani kuma yasamu yashiga karkashin
motan, Suleimanu na cikin tsaka da aikinsa wannan
motan tayi kuskuran fadamishi a kirji,. 'Mallan zakiru
yadan goge hawayen da yaxubo masa sannan ya cigaba
da cewa" dasauri ma'aikatan da muke wajan muka kawo
mishi taimakon gaggawa nan da nan muka samu muka
d'aga motar daga kirjinshi, nan fa muka tari texi domin
mukaishi asibiti amma kankace wani Abu rai yayi halinsa
Allah yakar6i ran abinsa.
Awannan lkcin Ameena naqarama bata mallaki hanklin
kanta ba, ayayin da d'an yagana wato bakura shima yana
qarami ga Yagana da tsohon ciki. Haka wannan
mummanan al'amari yafaru da mu, domin a gsky a
wannan lkcin na jima banji irin mutuwar da tashigeni ba
kamar ta Sule Wanda hakan yasa tundaga wannan ranar
banqara jin sha'awar wannan sana'a ba wannan shine
musabbabin dayasa nakoma sana'ar sai da shayi.
Mallan Zakiru yadan yi shiru cike da jimami yadubi
Balkisu yace " Balkisu nayi rashin babban amini. Balkisu
ta jinjina kai gabadaya tausayi yacikata.
Mallan Zakiru yacigaba da mgn, " wato bayan sati biyu
da rasuwar Sule sai ga wani sabon tashin hnkli Yagana
taxo dashi wai ita a dole sai anraba gado tunda tanada
d'a namiji ga kuma wani cikin ae tasan dukiyarta sai tafi
yawa, awannan lkcin kuwa Sai da yayan Sule yashiga
cikin mgnr.
Nan ne yake tambayar Rabi ko ta amince araba
gadon ynxu ko kuwa sai yaransu sundantaso, nan Rabi ta
nuna ita dai abarshi zuwa lkcin da yaran suka mallaki
hanklinkansu inyaso a wannan lkcin abawa kowa nasa.
Ae fa nan Yagana tayi taya6awa Rabi maganganu
marassa dadinji.
Ranar wata alhamis ne muka sami wani mummunan lbri
Wanda ya girgiza al'umar dake cikin wannan anguwa
tamu.
Domin kuwa Yagana cikin dare ta tashi takashe d'anta da
hannunta sannan ta yayyaga rigar jikinta tayiwa kanta
wasu tambari naciwuwuka tamkar ansameta an
yayyageta da wuqa. Ganin tasamu nasara yasa tanufi
d'akin Rabi ta ajiye gawar yaron sannan tafara ihuun
neman agaji dasauri mutanen anguwa suka farka, kowa
yyi shiru yana sauraren inda wannan ihun kefitowa.
Bayan kowa ya fahimci cewa a gdansu Yagana ne ake
wannan ihun hakan yasa jama'ar anguwa kowa yanufi
chan dan ganewa idonsa.
Koh da shigarsu cikin
Gdan gabadaya jikin Yagana a yayyanke da wuqa ga
kuma yaro kwance cikin jini, ae dasauri suka shiga don
axaton jama'a barayine suka shigar musu. Amma da
shigar jama'a cikin d'akin sai ga Rabi da wuqa a hannu
dukk tarikice yayinda ita kuma Yanaga ke ta neman
ceton jama'a.
Ganin mutane suntaru yasa Yagana tacigaba da kuka
tanafadin "shikenan Rabi kincika burinki naganin kin
hallaka d'ana sbd kina baqin cikin gadon da wannan
yaron zai samu, Hakanan Yagana takawo lbrin qarya
tasanar da jama'a cewa Rabi ce takashe mata d'a sannan
itama tayi qoqarin kasheta wai sbd gado.
Rabi kam mamakine ya baiyyana qarara a fuskarta, wasu
irin hawaye masu ciwo ne suka dinga bin kuncin Rabi
tunfaruwar wannan al'amarin kuwa Rabi ko uffan takasa
Cewa sai hawayen kawai datake ta xubarwa.... Kafin
wayewar gari kuwa yan sanda suka zo sukatafi da Rabi
police station Wanda daga baya kuma aka kaita koto bisa
hujojin qarya aka kai Rabi gdan yari amatsayin daurin
rai da rai.
Haka wannan mgnr takarade cikin anguwa da sauran
kewaye, wasu sun yarda jin cewa Rabi tayi kisan kai
yayin da wasu kam basu yarda ba, sai dai Wanda sukafi
yarda sune sukafi rinjaye. Hakan kuwa yasa mutunen
anguwa suke nuna halin kyama da gujewa Aminatu
hakan yayima Yagana dadi tasamu yadda take so.
Bayan wasu yan kwanaki da faruwar wannan rikitaccen
al'amarin Yagana tahaihu tasami diya macce, dukk da
cewa ba haka taso ba.
Dukk wata tsangwama da kyarar da Yagana keyima
mahaifiyar Amina shine tadawo dasu kan Amina, inda
take gana mata azaba kala kala tun Amina batayi wayo
ba har ta girma ta fahimci duniyar datake ciki, sbd
mutanen anguwan nan tamu gabadaya suntsaneta suna
ganin cewa itama inta girma halin uwarta zatabi na kisan
kai
Mallan Zakiru ya fyace majina sannan yashare
hawayensa yadubi Balkisu yace " kinsan wani abun
mamaki kuwa"? Balkisu ta girgiza kanta tace a'a baba sai
kafada.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣0⃣
Mallan zakiru yacigaba dacewa "wato yadda naga
Aminatu nashan wahala tun tana yar qarama hakan yasa
nayi tunanin cewa bari ind'aukota tadawo hannuna da
zama, kasancewar nima har wannan tsufan yariskeni
mai d'akina bata ta6a haihuwa ba.hakan yasa na
shawarci mai d'akina akan mgnr d'auko Aminatu,
hakanan itama ta nunajinddinta akan shawaran dana
yanke. Shiyasa da wani yammaci nashirya naje gdan,
inazuwa gdan natarar da Yagana nadukan Aminatu kmr
wadda Allah ya aiko, da sauri na k'waceta daga hannunta
bayan haka ban tsaya sauraren komai daga gareta ba
nanuna mata cewa inason zantafi gdana da Aminatu
takoma chan da zama.
Kafin ma naqarasa abinda nakeson cewa Yagana
tabuga wani uban salati nan tashiga kurma ihuu
tanafadin "yau nashiga ukuuu ni Yagana wato Zakiru irin
cin amanar da zakayiwa babban amininka kenan? Ana
cikin haka sai ga jama'ar cikin unguwa suntaru danjin
bahasin ihuun da takeyi, nan fa Yagana tashiga basu lbrin
qarya wai zuwa tayi ta iskeni tsakar gda ina qoqarin yiwa
Aminatu fyade wa'iyaxubillah" wato Balkisu tunda nake
arayuwata ba'ta6ayimin sharri Wanda ya girgizani ba
kmr Wanda Yagana tayimin.
Jama'ar cikin unguwarmu kowa sai alawadai da irin
halina yakeyi Wanda yagana ce taqaqaba minshi, wani
irin tashin hnkli nashiga marar misaltuwa Dan haka cikin
sanyin jiki najuya da nufin natafi gda amma Yagana ta
ziga samarin anguwan nan tamu dasu rakani gda da
ihuuu! Haka kuwa akayi yara da yan samari suka bini
sunatayimin ihuuu wnda hakan yyi sanadiyar nafarajin
wani irin hajijiya na yawo dani cikin rashin Sa'a inatafiya
qafata ta kufce tafada cikin wani rami dakyar nasamu
nacireta gabadaya qafartawa takumbura sbd ramin
qarami ne, toh fa tundaga nan ne nahadu da ciwon qafa.
Daga rana irin ta wannan lkcin ko gaisuwa bata shiga
tsakanina da Aminatu bawai Dan inatsoran Yagana ba a'a
sai dai inatsoran sharrin da Yagana zatakoma qaqabamin
ko kuma Aminatu.
Tabbas wasu sunfara fahimtar hali irin na Yagana shiyasa
dukk rintsi dukk wuyan da Amina Zatasha babu mai kai
mata d'auki gudun kar tayiwa mutun sharri domin
Yagana tadaurawa mutum sharri ba komai bane
agurinta. Shiyasa kowa ke gudun taimakawa Amina.
Ana cikin hakane Yagana tatsiro da sabon iskaci na
azabtar da Aminatu, da farko idan ta daura mata talla
dukk abinda Aminatu tayo ciniki sai yagana tace bazata
sammata kudi ladan guminta ba ko tasiyamata wani Abu
sbd Amina hayatakeyi acikin gdanta, hakan yasa dukk
randa Amina batayi ciniki ba toh ranar awaje zata kwana
sbd batayi ciniki sosai ba balle aciri kudin hayarta.
Dukk irin sanyin da akeyi akan Aminatu yake qarewa,
sannan dukk wani aikin gdan itakeyin shi kama daga
wanke-wanke shara wankin Yagana da na yarta girki
zuwa wasu aike kuma komai nisan waje Aminatu da qafa
zataje babu Wanda ya isa yataimaka mata, idan Amina
tasamu tayi wad'annan ayyukan shine takesamu taci
abinci a dukk lkcin kuma da Aminatu bata samu damar
yin d'aya daga cikin ayyukan gdan ba toh awannan ranar
batada abincin rana ko nadare koda kuwa rashin lafiya
tayi.
Mallan Zakiru nafadin Haka yafashe da kuka, Balkisu ce
ma tayi qarfin Halin bashi hkri. Mallan Zakiru yadubi
Balkisu yace "wlh Balkisu tunda nake arayuwata bantaba
ganin mata marar imani kmr wannan matar ba, yarinya
ace ita da gdan ubanta sannan ace wai tana haya sannan
abincin da zataci sai tayi aikatau a gdansu, wannan
al'amari na matuqar damun zuciyata.
Gashi Aminatu tun da girma yarisketa yan samari
sukafara zuwarmata manema auranta amma Yagana sai
tayi tsaye tace musu ae yarinyar babu abinda ta iya sai
kisa da yawace yawace, hakan yasa dukk samari suka
fara gudunta sbd ko ba komai tarihi yanuna cewa
mahaifiyar Aminatu na gdan Yari.
Mallan Zakiru yyi murmushi yace kinji wannan shine
d'an taqaitaccen tarihin Aminatu iya Wanda nasani,
sannnan abinda yasa kikaji dazu na kafa miki sharad'in
kada kigujeta shine kar labarin Yagana ya wargazamiki
lissafi kema kigujeta kamar saura.
Balkisu ta share hawayen da yagama wanke mata
fuska tace " baba ko kadan babu haka acikin raina dukk
da kasancewata yarinya mai qarancin shekaru hakan
bazaisa na Gaza tunkarar Yagana ba, domin a ynxu
danaji lbrin Meena sai naji gabadaya wutar son taimaka
mata nadad'a ruruwa acikin raina.
Baba Sam kada kadamu nayi alqawari insha allahu sai na
ku6utar da Meena daga cikin wannan qangin rayuwan
sbd a ynxu wani irin Tausayinta ne yaqara tasiri acikin
zuciyata. Mallan zakiru yace "nikuwa insha allahu
zantsayamiki zankasance dake a dukk lkcin da kika
buqaci taimakona sannan zandage dayimiki addu'an
samun nasara ba dare ba rana. Balkisu tayi murmushi
mai sauti gabadaya farinciki ya lullumeta dajin kalaman
mallan zakiru.
Bayan sungama tattaunawarsu Balkisu tamiqe sannan
tadubi Mallan Zakiru tace "toh baba ni zan tafi gda dukk
yadda ake ciki insha allahu zanke sanar da kai" nan fa
mallan Zakiru yayi tasawa Balkisu albarka.
Hakanan Balkisu tanufi gda zuciyarta acinkushe babu
abinda take sai tunanin yadda al'amarin zai kasance
mussaman abangaran Yayan nata, dan haka a ynzu a
shiryetake da ta tunkaresa da dukkanin buqatunta Dan
ganin ta tarwatsa dukk wani BURI Na yayanta Dan kawo
canji acikin rayuwarsa.
® NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣1⃣
Balkisu na isa gda qarfe sha biyu na rana na bugawa dai-
dai. dan haka sashenta kawai tanufa kai tsaye, koh da
shigarta saman gadonta tahau sharaff! Takwanta
gabad'aya dukk ji takeyi tagaji. Chan tayi nisa cikin
tunani sai jitayi cikin ta na mataguqi alamar yunwa na
nuqurgusarta da sauri ta tashi tafice daga d'akin dinning
area tanufa tea tahadawa kanta mai kaur sai soyayyan
kwan da tad'iba da plan10 falo takoma taxauna sannan
tafara bawa cikinta hakkinsa.
Balkisu Na daf da kammala brkfst dinta sai ga Hafeez
yafito daga cikin d'akinsa sanye da farar jallabiya d'akin
Balkisu yayi niyyar zuwa har yanufi hanya kmr ance
yajuyo sai hango Balkisu yayi zaune cikin falo, wata irin
sassanyar ajiyar zuciya yayi wanda hakan yajawo hnkli
Balkisu tajuyo, Hafeez tagani tsaye sakar masa
murmushi tayi tana fadin Yaya har kafito?
A hnkli Hafeez yaqarasa cikin falon tsare Balkisu yayi da
idanunsa sannan yace Balkisu inakikaje ne tundazu dana
farka nanufi d'akinki amma bakya ciki? Kuma nalura
dake acikin kwanakin nan kina yawan fita ina kike zuwa??
Balkisu shiru tayi gabadaya tarasa amsar da zata bashi.
Ganin bata da niyyar cewa komai yasa Hafeez
yanemi waje yazauna qara kallon Balkisu yayi fuskan nan
ba alamar wasa yace "ke badake nake mgn bane kinmin
shiru?
Balkisu gabanta ne ya shiga dukan tara tara bama uku
uku ba sbd kalaman da bakinta ke qoqarin furtawa
batasan yadda yayan nata Hafeez zai d'aukesu ba, a hnkli
tad'ago kanta tadubi Hafeez da raunatattun idanuwanta
cike da faduwar gaba Balkisu tafara mgn cikin sanyin
murya
"Yaya kagafarceni amma yazama dole ne intunkareka
da wannan mgnr dukk da bnsan da wacce irin siga zaka
kalli batuna ba, Hafeez yayi murmushi gabad'aya jiyayi
Kansa yakulle domin kuwa yasan cewa qanwar tasa da
wani abu mai muhimmanci take tafe, tunanin haka ne
yasa Hafeez yadubi Balkisu cikin sigar lallashi yace oyaa
qanwata go on ke nake saurare kifadamin dukkanin
damuwarki namiki alqawarin zan magance miki ita
matuqar bata fi qarfina ba.
Da sauri Balkisu tace yaya insha allahu baifi qarfinka ba,
sannan zanfadamaka damuwata amma matuqar zaka
biyamin buqatartawa nikuma nayimaka alqawarin
zanyimaka dukkanin wani Abu dakake so matsawar bai
keta addini ba, Hafeez ya jinjina kansa ganin cewa
qanwar tasa seriou take mgn yasa yayi saurin cewa OK
jst tell namiki alqawarin biyamiki dukk wata buqatarki
matuqar bai keta addini ba. Balkisu tayi murmushi tace
yayana bai sa6a addini ba asalima addini ya horemu da
aikatashi kuma bayan haka idan har ka aikata hakan
nikuma xankasance cikin farinciki har abada.
Jin Balkisu tace haka yasa Hafeez yace "okay sanar
dani inajinki matuqar zaisaki farinciki.
Balkisu tace "tunda kamin alqawari zanfadamaka sannan
karkayi tunanin in nafadamaka zaka bijirewa
buqatartawa, cike da qaguwa Hafeez yace "go on kenake
saurare.
Miqewa tsaye Balkisu tayi gamida tad'auke dubanta ga
Hafeez a hnkli tace yayana inasone Dan Allah ka janye
BURINKA nacewa bazaka tabayin aure ba, sbd ina
buqatar ganin wata diya macce a cikin gdan nan
matsayin matarka hakan zaisani farinciki matuqa
Kuma.....! Kafin Balkisu taqarasa abinda take son fadi tuni
Hafeez yataka mata burki ta hanyar daka mata tsawa
keeee!! Balkisu rufemin bakinki awajan kinsan mekike
fada kuwa? Ina mai gargad'inki dakiyi saurin janye
wannan buqatartaki kicanja wata domin ina tabbata
miki cewa wannan din bata samu shiga ba.
Da qarfi Balkisu ta fashe da kuka kmr wacce aka
aikowa mutuwa, Hafeez kam gabad'aya jiyayi hanklinsa
yatashi domin azahirin gaskiya bayajin zai iya biyama
qanwartasa wannan buqatar domin kuwa tsakani na da
macce sai idanuwa "cewa Hafeeez" wannan kuka da
Balkisu keyi gabadaya yatada hnklin Hafeeez da sauri ya
qarasa gareta yace "kiyi shiru plsss bnson kisawa kanki
ciwon kai, Balkisu tajanye hannunta daga riqon da
Hafeez yayi mata
Shiru Hafeez yayi ganin qanwartasa fushi take dashi
yasa ya sassauto murya a hnkli yace "plsss Balkisu u have
to understand cewa bana son aure bana buqatar
kasancewa da kowa, nan gaba kad'an aurenki zakiyi
hakan ma kawai ya isheni da zarar kinfara hayayyafa
yaranki sun isheni sani farinciki sannan idan kinduba
Bal....dasauri Balkisu tadakatar dashi cikin muryan kuka
tace yaya wannan ba reason bane sbd kaikanka kasan
cewa bani da saurayi hasalima baka bari Na kula kowa
toh wakake tunanin zai aure ni har wadannan BURi naka
sucika Wanda ka lissafo ynxu?
Da sauri Hafeez yace nima sanin kanki ne cewa banida
wacce nakeso waxan aura waxan so? Dasauri Balkisu
tace wlh yaya believe me idan nacemaka nasamo maka
mata nagartacciya Na yarda da tarbiyyan yarinyar akwai
nutsuwa da hnkli attare da ita, dasauri Hafeez yakauda
knsa hace "a ina kikasanta?" Balkisu murmushi tayi
gamida cewa tabbas Yaya zaka Santa amma baxan
fadama ko ita wacece ba har sai ka amincewa buqatata,
Yaya Hafeex karkamanta cewa kaine uwata Kaine ubana
Ashe kenan dama akwai watarana da uba zai kasance
yabar yarsa cikin maraici da quncin rayuwa?
Jin Balkisu tace haka gabadaya hankli Hafeez yatashi,
dasauri ya 6ullo mata ta wata hanya yace "naji I will
accept ur condition sai dai Inaso kisani cewa hakan
zaifarune idan har yaxamto cewa kema kinsami mijin
aure sannan xan amincewa buqatarki"
Dasauri Balkisu tajuyo a firgice tace "Yaya wakake
tunanin zai soni har ya aureni?"
Jisukayi anbud'e labulen falo a hnkli yaqarasa ciki
hannayensa sanye cikin aljihunsa cikin sassanyar
muryansa yace gani.
Muje zuwa donji wanene yashigo musu gda kai tsaye
gamida amsa cewa shine zai auri Balkisu.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode2⃣2⃣
A tare suka juya gabad'aya, Dr Muh'd suka gani tsaye
murmushi ya sakar musu da sauri ya k'arasa ciki yace
"am swry ban muku sallama ba afuwan Assalamu
alaikum" miqawa Hafeez hannu yayi sukayi musabaha,
can kuma falon yayi shiru nad'an wasu daqiqa
gabad'ayansu kowa da abunda yake tunani cikin
zuciyarsa' Dr Muh'd ne ya katse shiru ta hanyar cewa
"tabbas Hafeez najima inason Balkisu a zuciyata sai dai
na 6oye ne sbd ganin cewa baka bawa kowanne d'a
namiji damar tunkarar taba, a haqiqanin gsky soyayyar
da nakeyima Balkisu tawuce dukk inda kake tunani
domin soyayyar Balkisu tayi tasiri acikin xuciyata Wanda
hakan yasa nakasa ganin kowacce irin macce da daraja a
idanuna, sannan a kullum sai nayi niyyar tunkarar ka da
zancen amma sai zuciyata ta haneni.
Shiru Hafeez yayi gami da dafe kansa gabad'aya jiyayi
hnklinsa ya tashi domin kuwa a ynxu shi Kansa yasan bai
da tacewa kasancewar Dr Muh'd abokine ga gareshi
yasan koshi shi waye yakuma san halinsa Sannan yasan
waye zuri'arsa.
Balkisu kam dukk kunya ta isheta gabad'a jitayi kmr
qasa tabud'e tashiga.
Dr Muh'd ne yace "abokina idan ka amince min inaso
kabani auran Balkisu, Hafeez kam jiyayi kmr ya d'aura
hannu aka, da sauri ya qirqiro murmushin dole ya dubi
Dr Muh'd cikin sigar zolaya Hafeez yace ashee kai ragon
likita ne maitsoran macce? Dr Muh'd yace la! la!! la!! Ae
ni ba Balkisu nake tsoro ba yayan Balkisun nake tsoro,
gabad'aya dariya sukayi Hafeez yad'an bugi kafad'ar Dr
Muh'd yace kai dai bawani.
Dr Muh'd yakoma cewa "nidai babban yaya kai nake
saurare kabani Balkisu? Hafeez yad'anyi murmushin
yaqe sannan yadubi gefen da Balkisu ke zaune tayi shiru
ta duqar da knta tana wasa da yatsun hannunta, sannan
yasake maida dubansa ga Dr Muh'd yace "of cox y not
da bazan baka ita ba amma nifa karkayi tunanin zanma
qanwata dole" bari ynxu intashi inbaKu waje kud'an
tattauna idan kunfahimci juna ta amince toh falillahil
hamdu inkuwa har bata amince ba toh

Please Login or Register in order to submit comment