Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu abin hawa kina musu dariya? Toh bari kiji
inkikasa wasa a tafiyan nan wlh sai nace babu inda zaki,
sannan sbd tsaban kinrainani wato nabaki awa biyar
akanki dawo gda shine kikayi xamanki sbd tsabar
kinnrainani ma shine kike ganin kinfi qarfin kid'aga waya
ki kirani kice xaki koma gda.
Meena tace "wlh ba haka bane nadauka kana gurin aikin
kane shiyasa nayi tunanin komawa da kaina, a firgice
Hafeez yaqara matse ta da bango wnda gabad'ayansu
sunajin numfashin juna, Hafeez yamatso da kanshi daf
da fuskar Meena yace" an gaya miki cewa aiki na yafiki
muhimmanci ne ko kuwa bakisan cewaa..shiru Hafeez
yayi ya kasa qarasa abinda yake son cewa.
Sake mata hannu yayi sannan yanuna ta da yatsa yace
toh bari kiji ban amince ko da kinyi wannan tafiyan ki ke
yawaita hawan motan haya ba ko kice xakisawa mutane
gyale, can kuma Hafeez ya kufula yace ke daga yau ma
nayi canceln sa gyale a gareki, inkinga kinsa gyale toh
daga ke sai nine acikin gdan nan kinajina ko?
Da sauri Meena tace ehh!
Hafeez ya gyara tsayuwansa ya kalli Meena dakyau
sannan yace in kunne yaji jiki yatsara, d'akinshi ya wuce
yabar Meena tsaye.
Huuhh!! Shine abinda tace kawai tashiga d'akinta
A gajiye takwanta bisa gadonta tadafe goshinta, cikin
zuciyarta tace "hmmm Yaya kenan dama nakawo haka
araina sbd naga take takenka kwana biyun nan sokake ka
hanani wannan tafiyan shiyasa kake tsiro da rigima kala
kala nikuwa nasan halinka dan haka a ynxu dai baxan
biye maka muyi ta rikici ba, balle kasamu galaban hanani
yin wannan tafiyan.
Kiraye kirayen sallahn la'asar din da akeyine yasa Meena
tayi hanzarin tashi tanufi toilet tad'auro alwala.
Abangaran Hafeez kuwa wani irin abune yatsaya mishi
arai nan yafara jerowa kanshi tambayoyi wai mema yasa
nadamu da lamarin wannan yar qauyen ne mema zaisa
naji kishinta ohh my god kar fa najawa kaina raini agun
wannan bakauyiyar yarinyar (nidai Munay dariya nayi,
nace araina babu mai amsa maka wannan
tambayoyinaka sai munturo maka JUMAYMA Yar bincike
ta bincika mana kai LoL)
Hakanan Hafeez yayi ta faman sintiri cikin d'aki shi kad'ai
yarasa abunda ke mishi dad'i domin gabad'aya jiyayi
bayason abinda zaisa Meena tayi nisa dashi. Tunani
barkatai Hafeez yayi tayi har dai shima yajiyo kiran
sallahn yatashi yad'auro alwala yanufa masallaci.
** **
Bayan dawowar Hafeez a masallaci haka kawai ya tsinci
kansa da son xaman falo, kasancewar Meena nacikin
kitchen, shiyasa ya zauna yana kallon dukk wani shiga da
ficenta.
Haka nan Hafeez yayi xaune har Meena tagama
kirginta ta jerasu a dinning table ta wucewarta d'akinta
domin ta shirya kayan da zata tafiya dasu gobe.
*Washe Gari*
Tunda asubar fari Meena ta tashi kmr yadda tasaba
tad'aura abin brkfst ta jerawa Hafeez a dinning area,
sannan tashiga toilet ta silla wankanta, tana fitowa
tashafa versiline sai powdr Meena bata yarda tayi wata
doguwar kwalliya ba domin talura a yan kwanakin nan
Hafeez na matuqar nuna kishinsa akanta Wanda ita
kuma hakan yan burgeta yana kuma bata tsoro, wata
atamfarta tad'auko tasa sannan ta sanya hijabi har
gwiwa.
Travelling bag dinta tajawo ixuwa falo, sannan tanufi
sashen Hafeez ta kwan kwasa mishi kofa.
Hafeez nacikin d'akinsa yafito a wanka kenan yaji
kmr ana buga kofa, jallabiyansa ya jawo yasaka sannan
yaje ya bud'e kofan.
Meena yagani tsaye cikin shirinta na tafiya ga kuma nan
jakar kayanta a gefe, haka kawai Hafeez ya tsinci kansa
da fad'uwar gaba. Jiki a sanyaye hafeez yadubi Meena
yace "har kinfito? Meena tace eh! Ina kwana Hafeez yace
lpy Lou.
Mamakine Yakama Meena don yau ko ince ynxu taga
wani irin canji atattare da Hafeez komai yakeyi tamkar
Wanda bashi da lakka ajiki haka nan ya kama jakar
Meena yasa a booth din motarshi.
Har gdan Baba Rabi yakaita, Hafeez yashiga sungaisa da
Baba Rabin sannan yamusu Allah kiyaye hnya.
Bai wani jima ba a gdan yayi sallama da Baba Rabi,
Meena har tayi xamanta domin bata da niyyar mishi
Rakiya, sai da Baba Rabi ta doka mata harara sannan ta
tashi tabi bayansa.
Xakujini anjima don jin ci gaban lbrin, ynxu banda caji
ne. Tnxs oll😘
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:06PM, 8/6/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣8⃣
Wurin Motarsa kai tsaye Hafeez yanufa yayin da Meena
tarufa masa baya, bud'e motan yayi ya xauna batare da
ya rufe ba, hakan ne yabawa Meena dama bud'e daya
site din itama tazauna.
Wata irin nannauyar ajiyan zuciya Hafeez yayi sannan
yamaida dubansa ga Meena yace "idan kukayi tafiyan sai
yaushe zaku dawo? Meena wacce ke wasa da gefen
hijabinta kai duqe tace naji Amma nacewa sati d'aya
xamuyi mudawo, dammm! Gaban Hafeez yafad'i amma
sai yayi saurin dakewa yace olryt" shiru sukayi
gabad'ansu na d'an wani lkci, can dai Hafeez yace "amm
Balkisu takirani ta sanar dani cewa drivan Dr Muh'd ne
xaikiku can Gwazan ko? Meena tace eh shine..
Ciro kudi Hafeez yayi sannan yamiqawa Meena yace
gashinan susha mai a hanya, kar6a tayi sannan tayi mishi
godiya, Hafeez ya maida kallonsa ixuwa wani gefe batare
da yakalli Meena ba yace "i hope kinji gargad'in danayi
miki cewa banda sa gyale " Meena tace insha allahu
zankiyaye hakan.
Murmushin jindadi Hafeez yayi yace "vry gud of
u"Meena dai batace komai ba. A dan gaggauce Hafeez
yace ni xanwuce kada nayi latti Allah tsare hanya, Hafeez
sai tsintar knsa yayi dacewa "ki kula da kanki Meena"
Insha allahu shine abinda Meena tafad'a sannan tafice a
motan, sai da Hafeez ya 6acewa ganinta sannan tashiga
gda.
Hafeez na isa cikin falo gabad'aya sai yaji dukk gdan
yamasa fili babu Meena ba Balkisu, wata irin kewa ce
tadinga shigarsa Wanda hakan yasa Hafeez yanufi
dinning area yaxauna kawai sai tsintar kansa yayi
yanacin abinda Meena ta girka masa
Hakanan Hafeez yagama cin ferfesunsa sannan
yazuba kunun gyad'a yafara sha yana lumeshi idanu,
cikin ransa sai tunani yakeyi haka dama Meena ta iya
girki bansani ba Oh my God!! Hafeeez yabud'e cikinsa
sosai yakwashi girki.
Bayan ya kammalane yanufi d'akinsa domin ya shirya
zuwa office.
** ** **
Balkisu da kanta ta tura Habu driva yad'aukisu Meena,
hakanan suka kama hanya, cikin ikon Allah sun samu isa
garin gwaza lafiya.
Yan'uwa da abokan arziqi kowa yayi farin cikin ganin
Baba Rabi, haka nan su Baba Rabi sun sami tarbo mai
kyau awajan yan'uwansu (kasancewar iyayen Baba Rabi
sunjima da rasu, a hannun kawunta ta taso) Khadija yar
gdan kawu Usman tun zuwan Meena gdan nan Allah ya
had'a jininsu khadija tayi farin ciki sosai da xuwan
Meena(kawu Usman shine kawun Baba Rabi) yaransa
guda biyar mata hudu daga ciki dukk sunyi aure sai
khadija auta.
Meena ma tajidadin kasancewa da Khadija sosai, gashi
sunkasance sa'anin juna, khadija tabawa Meena wata
hud'u shiyasa inkagansu atare tamkar wasu twns,
Tun zuwansu gwaza Meena kullum tana tare da
khadija tana d'aukan lesson domin kuwa khadija akwai
wayo da son gayu shiyasa kullum Meena na tare da ita
tana koyan wasu abubuwan.
Abangaran Hafeez kuwa fushi yake da Meena wanda ita
batasan ma yanayi ba,..fushi yakeyi sbd Meena bata
kirashi tasanar dashi sun Isa lafiya ba, sai abakin Balkisu
yakeji. Kullum Hafeez wayanshi na kusa dashi yana jiran
call daga Meena amma shiru kakeji, da xarar Hafeez ji
kira yashigo wayansa da hanzari xai jawota yaduba a
tunaninsa Meena ce takira, Hafeez nason kiran Meena a
koda yaushe amma girman kai yahanashi aikata komai.
*Bayan Sati Daya*
Dakyar Hafeez yaga wucewan sati dayan nan domin
kuwa jinsu yake tamkar shekara d'aya wani irin farin ciki
Hafeez yake ji idan ya tuna cewa Meena yau zata dawo
kmr yadda tafad'a mishi, hakanan Hafeez yatsinci kansa
da fita waje yana sadaka sbd farinciki.
A gajiye Hafeez yakoma gda falo ya kwanta domin
yahuta, baifi wucewan minti biyu ba yafarajin bacci na
fisgarsa, kmr daga sama yaji wayansa Na ringing da
farko har ya share har ta tsinke baid'aga ba sai da aka
sake kira a karo na biyu sannan yasa hannunsa ya lalubo
wayar d'aukan kiran kawai yayi batare da yaduba
sunanan ba.
Cikin muryan bacci yace "hello" a bangaran Meena
tace Assalamu alaikum, lkci d'aya Hafeez ya fahimci mai
mgn firgigit ya miqe ya xauna dasauri Hafeez yace
Meena kece?
Meena tace eh Yaya nice dama nabugo insanar maka
cewa akwai wani biki da zamuyi anan bazan samu damar
zuwa yau ba inaso zanqara wani satin sbd in.....kafin
Meena taqarasa abinda take son fad'i tuni Hafeez ya
katse wayan.
Wani irin numfashi Hafeez keyi cike da tashin hnkli sbd
tsabar takaici baisan lkcin da yayi wurgi da wayansa ba
yace "ohhh no Meena baki Isa ba I cnt tollrt it any more
idan baxaki iya dawowa da kanki ba nizanje nadawo
dake, tsawan wannan satin dakikayi bakisan halin
damuwar dakikabar ni aciki ba, am vry eager to c ur
cute face Meena.
Hafeez nafad'in haka yanufi d'akinsa da sauri car keys
dinsa ya Zara yadawo yadauki wayansa afalo ya fice a
gdan.
Hafeez na kan hanya yakira Dr Muh'd yace yanaso Dan
Allah yabashi aron Habu driva zai rakashi izuwa wani
waje, Dr Muh'd yace okay Abokina ba damuwa.
Asibitinsu Dr Muh'd Hafeez yanufa yad'auki Habu driva
yace dashi yanaso yarakashi garin da yakaisu Meena a
yau din nan. Cike da bin umarninsa Habu driva ya harba
motansa izuwa garin gwaza.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:54AM, 8/7/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣9⃣
Kasancewar Habu driva yasan gdan kawu Usman hakan
yasa suka nufi gdan kai tsaye.
Meena ce zaune tsakar gda ita kadai ta rafka uban
tagumi tunani ne sosai aranta addua kawai takeyi kar
Allah yasa Yaya Hafeez yace baxa tasamu daman tsayawa
bikin nan ba,
Meena tayi nisa sosai cikin tunaninta sai jiyayi
andafata a hnkli tadago kanta, Khadija tagani tsaye, ae
kuwa bashiri tasakar mata murmushi, cike da kulawa
Khadija ta duqa daf da Meena tace sister anya lpy kuwa?
Wani murmushin yaqe Meena tasakeyi sannan tadubi
Khadija tace "sister lpy Lou mekika gani?" Khadija tace
a'a naga kinxauna ke kadai kin zuba uban tagumi ko dai
kina tunanin Shine? Dasauri Meena tace haba dai khadija
wlh ba haka bane kawai nadamune sbd inason natsaya
bikin Hamza (hamza qanin Kawu usman ne) Khadija tayi
murmushi sannan tadafa kafadan Meena tace "kema
bnda abinki banace ki kira mijin naki kisanar masa cewa
kina son yabaki damar qara wasu kwanakin ba?.
Meena tashare kwallar dake qoqarin zubo mata tace
"wlh sister na jarabba hakan hasalima dana fadamishi
bai ce dani qala ba kawai yakashe wayansa.
Khadija tace ohhh wlh kina damuwa da abinda
baikamata ace kindamu ba, kikasani ko ntwrk ne ko
rashin caji kibari anjima kisake tryn. Murmushin yaqe
Meena tayi tace oky.
Khadija tace yauwa kokefa, nan taja hannunta tace tashi
ma muje kasuwa daxu Baba yabamu kudin sayen anko
yakumacemin haddake dan haka kisaki ranki kitashi
mutafi.
Jiki ba kwari hakanan Meena ta tashi tashirya suka tafi
kasuwa.
Su Meena ko minti uku basuyi da tafiya kasuwan ba sai
gasu Hafeez sun kunno kai cikin anguwar.
Dai dai kofar gdan Habu yayi parkn, kafinma yace da
Hafeez wani Abu tuni Hafeez din yafahimci cewa nan ne
gdan.
Fitowa sukayi daga cikin motan sannan suka sami yaran
dake wasa kofan gdan suka aiki daya daga cikinsu akan
yaje yace wai ana sallama da Meena
Yaron kuwa dagudu yashiga cikin gdan kmr yadda aka
umarce shi, yana zuwa yace "wai inji wani mutumi
awaje yace ana sallama da Meena"
Amma nadaga cikin d'aki tajiyo muryan yaron da sauri
tafito waje tace da yaron "waye ke sallama da Meena?"
Yaro yace shima baisani ba, Baba Rabi tace da yaron
yatsaya nan tashiga ciki tad'auko hijabi tace da yaron
suje tagani.
Koda fitar Baba Rabi izuwa waje Hafeez tagani tsaye
jingine da mota, dasauri taqara wajansu tana musu
sannu da zuwa, Hafeez kam sai waige waige yakeyi inda
xai hango Meena.
Baba Rabi tace "sannunku da zuwa Hafeez kai ne tafe?
Hafeez yayi murmushin yake yace wlh kuwa Baba nine,
Baba Rabi tace toh sannunku da zuwa kushigo daga ciki.
Dakin Kawu Usman Baba Rabi tasauqe su Hafeez, bayan
sunqara gaisawane baba Rabi takawo musu ruwan sha.
Sannan tace da Hafeez yad'an jira kadan Meena
sunfita ita da yar'uwarta, shiru Hafeez kawai yayi,
tunanin inda Meena taje a wannan yammacin kawai
yakeyi.
Abangaran Meena kuwa suna can kasuwa wajen siyan
anko, bayan sungama ne Meena tace sister inaso kikaini
inda ake siyan gyale da hijabi, haka nan Khadija takaita
gurin da tabuqata, Meena tasaima kanta hijab kallan
ankon nasi sannan tasaima Khadija Gyale itama kallan
ankonsu.
Haka nan suka gama siyayyansu cike da farinciki suka
koma gda.
Mai taxi na ajiye su Meena fitowan nan da zatayi
idanuwanta sukayi tozali da motar Hafeez, rass!! Gabanta
yafad'i, amma sai tadake domin tana tantama kmr ba
motansa bace, hakanan suka kwashi kayansu suka nufi
cikin gda.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:57AM, 8/7/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode4⃣0⃣
Suna shiga cikin gdan da sallamarsu kafin sunemi waje
suzauna Baba Rabi tace "kee! Aminatu daga xuwa
kasuwa kuje kudawo shknan sai kumaida gari naku kuje
kuyi xamanku, Meena tace Amma wlh ba haka bane
mund'an tsaya siyan wasu abinne shiyasa mukadan
jima.
Baba Rabi tace toh ae kunkyauta sai kitashi kije d'ankin
Kawu Usman kinyi baqo, dasauri Meena takalli Baba Rabi
tace "Amma baqo kuma"? Baba Rabi eh kawai tacemata
tabar wajan.
Khadija tadubi Meena tace sister tashi kije natabbata
babu wani namijin daxaixo yanemiki har ayimishi izinin
zuwa d'akin Kawu face mijinki, plss tashi ki kintsa kijeki.
Kafin Meena tace wani Abu Khadija taja hannun Meena
izuwa d'akinsu, nan ta tsara mata kwalliya mai kyan
gaske Khadija da kanta tabud'e akwatin Meena taza6o
mata wasu riga da siket masu kyau tace tasasu. Batare da
Meena ta musawa Khadija ba hakanan tadauki kayan
tasa, sai da tashirya tsaf sannan tasanya hijab tanufi
d'akin kawu usman.
Qamshin turaren Meena ne yadoki hancin Hafeez,
dasauri yad'ago kansa Meena yagani tana qoqarin xama
bisa kujerar da yake zaune.
Meena wacce gabanta yatsananta Faduwa cikin siririyar
muryanta tace sannu da zuwa Yaya ina wuni? Hafeez ya
kura mata idanu ko qiftasu bayayi, shiru yayi tamkar
baxaice komai ba , can dai yace Meena ba wannan ne
yakawoni ba "Habu driba kam tun shigowar Meena
yabar d'akin" Meena tayi shiru tana sauraren Hafeez taji
da wacce yaxo.
Hafeez ya matso daf da Meena yace zuwa nayi domin
inaso kimai maitamin abinda kikace lkcin da kika kirani
awaya d'axu.
Shiru Meena tayi takasa cewa komai sai faman wasa
takeyi da d'an yatsanta,, Hafeez yaqufula sosai yace ko
bakyajina ne nace kimaimaita abinda kikafad'a daxu.
Cikin tsananin faduwar gaba tafara mgn tamkar ta mai
in'en "tace umh uhm dama cewa nayi inaso kabani
dama domin na samu halartan bikin Hamza.
Hafeez yace okey dukk satin da kikayi anan basu isheki
bane,? Meena tayi shiru! Hafeez yace kibani amsa mana
ko kuma baki san cewa kinbar mijinki shi kad'ai cikin
wani hali na kewa ba?
Kewa?? Shine abinda Meena tamai maita cikin
xuciyarta, Hafeez yace toh bari kiji nazo intafi da
mamata kuma ayau din nan komin dare xamu bar
Gwaza mukoma Maiduguri, Meena tad'ago kai fuska a
maraice tace "Dan Allah yaya kayi hkri kabarni ko kwana
biyu ne inqara.
Cike dajin haushinta Hafeez yace kinsan Allah bari kiji
wlh ko awa d'aya bazan bari kiqara ba, kuma kitashi
ynxun nan kije kihado kayanki inajiranki a mota.
Hafeez nafad'in haka yatashi yabar d'akin, a tsakar gda
ya tarar dasu Baba Rabi.. nan yaduqa har qasa yayi musu
sallama yace "Baba ni zan wuce ynxu" Baba Rabi tace
haba Hafeez baka tsoron kuyi dare a hanya, murmushi
yayi sannan yace Bakomai insha allahu, nan yayi musu
godiya yafice a gdan yakoma cikin motarsa yana zaman
jiran fitowan Meena.
Abangaran Meena kuwa dagudu ta tashi takoma d'akinsu
Khadija sai faman kuka takeyi, Baba Rabi nazaune cikin
d'aki taga wulgawar Meena dasauri ta tashi tabi bayanta.
Ko dashigarta ta tarar da Meena na kuka tana had'a
kayanta, Baba Rabi tadubi Meena tace "ke kuma miye
kikewa mutane kuka?" Meena wacce kuka yaci qarfinta
tafashe dawani sabon kukan tace " Amma Yayane yace
yaxo tafiya dani bayan Kuma nafadamishi cewa muna da
biki.
Baba Rabi wani uban tsaki taja tace "mtsww aekin wofi
kawai yoo dama inkika zauna bikin kawu Hamza uban
mexaki tsinana toh kisani dukk wani abu marar
muhimmanci dakike tunani yafi miki bin umarnin
mijinki domin kuwa bikin Kawu Hamza kodake ko bake
xa'a daurashi dan haka kirufewa mutane baki tun baki
tarawa kanki jama'a cikin d'akin nan ba.
Meena kam gabad'aya takawo iya wuya wani irin
takaicine ya sarqe ta, dasauri tashirya kayanta tsaf tayi
sallama da kowa kafin Khadija tadawo tayi saurin ficewa
tabar gdan (khadija na gurin Sa'idu tailor ta kaimusu
kayan ankonsu dinki)
Fushi Meena tayi sosai dan haka tana xuwa tasa
kayanta a booth tabud'e gdan baya tazauna.
Hafeez naganin haka yafito daga gaban mota yadawo
baya inda Meena ke zaune, kowa na gdan yafito yayi
musu Allah kiyaye hanya.
Batare da Bata lkci ba sukabar cikin garin gwaza, suka
kama hanyan Maiduguri.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [7:59AM, 8/7/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episod4⃣1⃣
Su Hafeez sunyi nisa sosai da tafiyarsu amma da gashi
har Meena ba wanda yace da wani uffan! Hafeez nema
tunfara tafiyansu yaketa satar kallon Meena sbd
kwalliyar dake fuskarta baqaramin kyau yamata ba.
Ajiyar zuciya Hafeez yayi a hankali ya maida bayansa ya
kwanta jikin mota sai fama tunani yakeyi a cikin
xuciyarsa, "Hafeez ke tambayar kanshi dama akwai
watarana da xataxo ni Hafeez zanso wata fiye da Rafee'a
ohh gosh! Nan yafara tunanin ya akayima yafara son
Meena badly haka"? Hafeez na cikin tunaninsa wayar
dake riqe a hannunsa yana jujjuyata nan tafara ringing.
Firgigitt! Hafeez yayi yadawo daga duniyar tunanin da
yatafi, cike da kasala Hafeez yadubi wayan don ganin
mai kiransa.
Sunan Dr Muh'd Hafeez yagani ya bayyana akan screen
din wayarsa hanxarce yad'uki wayan gamida karawa a
kunnesa "hello Abokina Allah yasa bakayi nisa ba wlh
Balkisu ce bata lpy tana fama da laulayi tundazu take
damuna akan nakiraka nace tabari zuwa an jima idan ta
huta amma Sam taqi, a hanzarce Hafeez yace ya salam
tana kusa plss bata wayan.
Hafeez na amsan wayan Balkisu tafashe da kuka
tanafadin Dan Allah Yaya Hafeez kayafemin mutuwa
xanyi wayyoo Allah na bayana xai fashe yaya, gabad'aya
Hafeez ya rikice kashe wayan kawai yayi sannan ya
umarci Habu driva da yaqara gudu.
Baifi tafiya 3Omint ba su Hafeez sukashiga cikin garin
Maiduguri, direct gdan Balkisu suka wuce kmr yadda
Hafeez yace. Suna isa cikin gdan da sauri Hafeez yanufi
ciki batare da yajira su Meena ba.
Meena kam batasan meke faruwa ba, amma a hanzarce
itama tabi bayan Hafeez.
Hafeez na isa cikin falon yafara kiran Balkisu! Billyn
mama!! Shiru yaji dasauri yanufi wani d'aki inda nan ne
yake tunani d'akin Balkisu yake.
Kafin Hafeez yaqarasa d'akin sai ga Dr Muh'd nan yafito
daga d'akinshi dasauri yakira sunan Hafeez yace "no
abokina gatanan kwance a d'akina nayimata allura ne
tayi bacci, fuska d'auke da damuwa Hafeez yace plss
mike damun Balkisu Dr Muh'd yana jin nauyin amsa
masa tmbyarsa amma babu yadda ya iya domin yaxama
dole ya amsa masan.
Jan Hafeez yayi izuwa wani corido sannan Dr Muh'd
yadubi Hafeez yace "abokina munsami qaruwa ne
Balkisu nad'auke da cikin wata biyu, sai dai da mtsl.
Dasauri Hafeez yace mtsl Kuma? Mtsl kmr tame
kenan, Dr Muh'd yace kasan dai nikadai iyayena suka
mallaka arayuwarsu shiyasa tunda girma ya riskeni suka
takura akan lallai sai nayi aure domin suma suga
jikokinsu suncika gdan nan.
Toh sai dai ba'anan gixo ke saqar ba, Balkisu tasamu ciki
sai dai yana masifar azabtar da ita kome taci baya xama
acikinta dukk tarame tafita hayyacinta kullum tana cikin
ciwo.
Nikuma tausayinta yajani nayi tunanin zubar da cikin,
sai dai kafin na kai ga aikata hakan iyayena sunce
muddin nabari cikin dake jikin Balkisu ya zube to basu
yafemin ba.
A gsky Hafeez ina cikin damuwa domin ni lfyr Balkisu
tafimin komai arayuwata.
Murmushi Hafeez yayi sannan yashiga kwntarwa Dr
Muh'd hankali dukk da kasancewar shima nasa hanklin a
tashe yake.
Sai qarfe Tara da rabi Na dare su Hafeez suka bar gdan,
suma suka nufi nasu gdan, Meena kam hadda hawayenta
ganin yadda Balkisu tarame lkci d'aya gashi har suka bar
gdan bata samu ta farfado ba.
Restaurant yafara wucewa dasu don sunci abinci, Amma
Hafeez gani yayi maza sunyi yawa agurin cin abincin Dan
haka take away kawai yayi musu suka nufi gda kai
tsaye....
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:52AM, 8/8/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode4⃣2⃣
Tun sanda Hafeez yaje gwaza yad'auko Meena suka dawo
yaga canji a tattare da ita sosai domin gabad'aya ta
kauracewa ganinsa dukk abinda tasan zai had'ata hnya
da Hafeez Meena tajanye , hakan kuwa baqaramin d'a
hanklin Hafeez yayi ba gad'aya yashiga damuwa ga uban
taurin kai ko ince girman kai da yahanasa kai kanshi
gareta balle yasan halin da take ciki.
Yau ya hakasance weekend, hakan yasa yau Hafeez na
gda bai je ko ina ba,..Wanda a bangaran Meena kam
hakan bai mata d'adi ba domin tanason fita zuwa d'aura
musu abin brkfst gashi kuma Hafeez yayi zamansa a falo.
Gabad'aya Meena taqagu Hafeez yabar falon Dan
tasamu damar wucewa a hankali Meena taske tabud'e
kofan d'akinta taleqa ko Allah zaisa taga Hafeez nan
amma sai taga wayam! baya cikin falon, hakan yasa
tafito a hanzarce tanufi kitchn.
Dai dai lkcin ne kuma Hafeez yafito daga waje hannunsa
d'auke da wasu takaddu daganin alama daga waje yafito
dasu, dasauri Meena tashiga kitch abinta. Hafeez kam
murmushi yayi gamida girgiza kansa domin yaga lkcin
datashige kitchen dasauri, falo yanufa ya ajiye tarin
takaddunsa sannan yanufi kitchen din.
Meena ce tsaye cikin kitchn ta tawani riqe qugu tana
tunanin abinda yakamata suyi brkfst dashi.
A hankali Hafeez yashiga kitchen din batare da sanin
Meena ba, Meena kam sai ji kawai tayi an rugumota
tabaya tsamm.
A tsorace tad'an juya Hafeez tagani take anan tasauya
kamaninta tawani turbune fuska kamar zatayi kuka, a
hnkli Hafeez yajuyo ta tafuskance shi sannan ya riqe
hannayenta cikin muryan rad'a yake mata mgn "haba
Meenata fushi kikeyi da d'an bawan Allah nan? plss kimin
afuwa wlh a lkcin jinayi bnda control inba d'aukoki nayi
ba u know i really miss u alot Meena ynxu yakama ki
juyo ixuwa ga mijinki kimanta da komai kimin afuwa
kinji matar da babu irinta."
Hafeez nagama surutunshi Meena tadungujeshi dasauri
tabar masa kitchen din, hnklin Hafeez gabad'aya yatashi
riqe goshinsa yayi sbd yadda yaji knsa nasara mishi cikin
sanyin jiki haka Yaja jiki yanufi hnyar falo.
Kmr daga sama Hafeez yajiyo muryan Balkisu tana kwala
mishi kira tunkamin tasamu taqarasa cikin falon.
Dasauri Hafeez yajuya Balkisu yagani da gudunta
tanufato shi, a hanzarce Hafeez yaqarasa wajenta yana
fad'in ke Billyn mama kanki d'aya kuwa? A cikin wannan
yanayin dakike ciki shine kike wa mutane gudu haka?
Balkisu ta turo baki cike da shagwa6a tace ni gaskiya
yaya cikin nan ya takuramin wlh shikenan ni baxanyi
abinda nakeso ba.
Hafeez yayi murmushi yaja hannunta suka nufi cikin
falo, bayan sun zauna ne Hafeez yadubi Balkisu yace "lpy
kuwa Balkisu naganki da sassafe?" Balkisu tace lpy law
wlh dama My precious ne yayi tafiya takama ynxun nan
izuwa wani qauye shine yacemin sai xuwa dare xai dawo
dan haka yace nashirya yayi dropn dina anan domin bai
yarda yabarni nikad'ai ba.sannan dama nazo ma da anty
amarya wani lbri mai dadi, Hafeez yace "minene yafaru"
dasauri Balkisu tamiqe tace yaya inaxuwa. Kafin Hafeez
yace wani abu ta tashi da sauri tanufi d'akin Meena
Koh da shigarta ta tarar da Meena kwance tayi rufda ciki,
dasauri Balkisu ta qarasa ta kwnta a hnkli cikin sand'a
yadda Meena baxataji ba,..Meena kam batamaji
shigowarta ba Dan tayi nisa sosai da tunani sai jitayi ana
huramata iska a kunne dasauri tarazana tace miye haka
ya.....shiru tayi takasa qarasa abinda takeson cewa sbd
wacce tagani a gabanta. Dasauri Meena ta tashi zaune
tadubi Balkisu cike da zolaya tace "a'a gawa taqi rami
kece yau a gdan namu"? Balkisu tahad'e fuska sosai
tadubi Meena sannan tace Anty Amarya koda baki cemin
komai ba tabbas akwai abinda yake faruwa a gdan nan
sbd daga ke har Yaya na lura bakwa cikin walwala, keda
mukayi alqawari dake amma sai nazo naga sa6anin haka
domin tunshigowata gdan nan idanuna suka ganemin
cewa Yayana nacikin matsanancin damuwa wanda cikin
alqawarinmu nafad' a miki cewa banaso kibarshi cikin
kewa ko damuwa sbd laluran dayake fama dashi.
Wata irin nannauyan ajiyan xuciya Meeena tayi sannan
tadubi Balkisu tace "wlh ba haka bane amma kimin
afuwa insha allahu zangyara kuskure na".
Murmushin yake Balkisu tayi sannan tace Allah yasa.
Cike da sanyin jiki Meena tace Ameeen!!
Lkci d'aya kuma Balkisu tasaki jikinta da Meena daga
bisani kuma taja hannun ta tace " yauwa Anty amarya
taso muje wurin Yaya domin naxo muku da kyakkyawan
labari. Meena tadubi Balkisu tace "kyakkyawan lbri
kuma?" Balkisu tace sosaima kuwa kedai taso muje.
Meena tace to Balkisu banqi takiba Amma kiyimin afuwa
Bari nasamu nad'aura mana abinda mukaci, dasauri
Balkisu tace plss kawai kidafa mana indomie muci kinsan
Yaya ma naso. toh kawai Meena tace sannan ta tashi
tanufi kitchen tad'aura

Please Login or Register in order to submit comment