Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai tsammaci fitowar Meena a lkcin ba jiyayi
kawai sunyi karo da juna, dasauri Meena tace
"subahanallahi" wani irin takaicine Yakama Hafeez ganin
cewa ita kad'ai ta dafawa kanta indomen, duba jikinsa
Hafeez yashigayi ko allah zaisa yaga inda ta6ata masa jiki
yasauqe haushinsa akanta, amma sai dai anyi Sa'a babu
inda jikinsa ya6aci,dan haka dubanta ya shigayi kmr
wacce tayi wani abun.
Meena kam tsaye tayi tanabinsa da kallo, Chan Hafeez
yaqufula yace "ke yar qauye wannan wacce irin qaxamar
dahuwa ce kikayi jibi yadda kikawani zabga tarugu sai
kace wata maiyya.
Meena tazaro ido waje tace "nice mayya Kuma?"batare
da Hafeez ya kulata ba yace "common get out" Meena
taratsa ta gefenshi zata wuce tana gunguni Hafeez yace
"magana kike ne?" Meena ta manna masa ta wucewarta,
Hafeez yayi tsaki yace qyatt yar qauye kawai sai wani
faman big head kike xanyi maganinki very soon. Nan
yashiga kwalawa Daniel kira!
A bangaran Meena kuwa d'akinta ta wuce kaitsaye dukk
haushi ya isheta mgnr Hafeez ce kawai ke mata yawo a
kunnenya, kwafa tayi cike dajin haushi tace "tabb wato
ni Hafeez zaicewa Maiya? Wlh sai yagane kurensa sai na
mai dashi yazama mayen shima in yaso mahad'e
muzama mayun mu biyu,..Meena sai faman cin
indomien din ta takeyi wnda taji kayan had'i, tanaci tana
masifa ita kid'ai a d'aki.
•° •° •° •°
Washe gari.
Meena tunda safe bayan ta idar da sallah tanufi kitchn
dan tasamu abinda tad'aura, mgnr Balkisu ce tafad'o
aran Meena lkcin da aka kawota inda Balkisu ke sanar da
ita abunda Hafeez yafiso yayi brkfst dashi wato soyayyan
kwai da tea, dariyar mugunta Meena tayi, nan tashiga
farfasa kwai wnda xatayi amfani dashi ta jajjaga tarugu
mai yawa ta yanka albasanta tazuba maggi da kayan
kamshi ta zuba cikin kwan ta bubbugashi sosai yabi
jikinsa, nan tahau suyan kwan, daga gefe kuma tad'aura
ruwan zafin tea dinsa Wanda tazuba lipton da citta suga
da kalinfari da barkono sosai, ae fa nan qamshi ya
karad'e gdan.
Hafeez sai da ya tabbatar da cewa yayi wanka sannan ya
shirya tsaf abinsa cikin shaddarsa sky blue sai hularsa
wadda tayi matchn da kayansa, agogon hannunsa
yad'auka yasa sannan yafesa turare yanufi hanyar fita,
bud'e kofan nan da Hafeez zaiyi yaji kamshin ya doki
hancinsa da sauri yaqarasa cikin falon ko da yaduba
dinning area yaga anshirya komai tsaf tsaf kmr yadda
aka saba, cikin hanzari yanufi dinning table yaxauna tare
da duban agogon hannunsa qarfe takwas da rabi yana
ganin haka yayi saurin zaro wayanshi dake aljihunsa,
wata nmbr yayi dialing cikin natsuwa yake mgn yace
"yes mansur am on ma way just giv me 15 to 20 mint a
will b thr soon" yana gama wayar ya hau bud'e brkfst
din ruwan zafin tea din yafara zubawa kadan cikin cup
sannan yadibi kwan nashi cikin plat, wani irin kamshi
mai dad'i ne yake ta doke hancinsa.
Sai da ya tabbatar da ruwan xafin yad'an huce dai dai
yadda zai iya sha sannan yajawo kusa dashi, plat din
kwansa yasa agaba dasauri yadebo mai yawa yaddana a
bakinsa yafaraci a hnkli yad'an lumshe ido sai da kwan
yakai qarshe Hafeez yaji wani irin azababben zafin
barkono ya ziyarci harshensa dasauri yafurzar ya dauki
cup din tea dinsa ya kurba ko zaiji d'an ji dama, ae fa
nan Hafeez ya miqe tsaye idanunsa sukayi jajir
harshensa yadinga fiddowa waje sbd tsabar azaban da
yakeji ko mgn yakasa(kasancewar Hafeez bayason abuda
yaji SBD ulcer)
Meena dake la6e tana kallonsa sai kwasar dariya take
abunta, kara leqawa tayi don taga yadda yake daka tsalle
ae kuwa tana sa kai sukayi ido biyu da Hafeez.
NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:10AM, 8/4/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣3⃣
Hafeez nahad'a ido da Meena yatabbatarwa kansa cewa
itace tahad'a masa wannan muguntan, dan haka a
fusace yayi kanta sai dai Hafeez baisamu daman
qarasawa gareta ba sbd wani irin abu da yatsaya a
zuciyansa nan da nan yanemi hnklinsa yarasa jagwaaf
yafad'i qasa gamida riqe kirjinsa yanata mutsu-mutsu a
kasa. Abu dai kmr wasa wasa tun Meena na yar dariyarta
har dai talura cewa Hafeez da gaske yake, ae da gudu
Meena taqarasa inda yake kwnce nan tashiga jijjigasa
tana kiran sunansa.
Gabad'aya idanunsa suncanja kala Hafeez yajigata
sosai zuciyarsa wani irin suya take masa.
Meena ta lura abin nashi dagaske ne ba wasa dan haka
dagudu tashiga kiran Daniel, Daniel yazo da hanzari
ganin ogan nasa cikin wani hali hakan yasa yafahimci
cewa ulcer dinshi ne yatashi dagudu Daniel yashiga
d'akin Hafeez yad'auko maganinsa nan ya qoqarta
yasamu yabashi maganin yasha.
A hnkli Daniel yasamu yad'aga Hafeeez dakyar yataimaka
mishi ya kaisa d'akinshi. Hafeez jiyayi tsanar Meena
taqaru a xuciyarsa.
A bangaran Meena kuwa jitayi gabad'aya jikinta yayi
sanyi, sai ynxu takejin kwata kwata bata kyauta ba
nadama tashigayi marar iyaka.
Tunda wannan abu yafaru kuwa Hafeez bai qara bin
tankan Meena ba, yar kulatan ma dayakeyi suna rigima
kwata kwata ynxu ya daina.
Mgnr abincinsa kuwa Daniel kedafa mishi kmr
kullum.
• • • • • •
Meena abin duniya dukk ya isheta Hafeez ko kallon
indatake baya son yi jiyayi gabad'aya yatsaneta, shiyasa
da zarar gari yawaye yake Allah Allah yafice a gdan.
Yayin da ita kuma Meena ke tunanin hanyoyin da zatabi
dan taga cewa ta kyautata masa, Hanyar farko da Meena
tafarabi shine da zarar Hafeez yafita zuwa office dinshi a
wannan lkcin ne take shiga d'akinsa ta gyara ko ina ta
wanke toilet tattara under wears dinsa ta wanke masa,
haka kullum Hafeez idan yadawo sai yaga komai Na
d'akinsa very neat.
Ana cikin hakane Daniel ya samu Hafeez yasanar dashi
cewa yanaso zai zaije enugu can garinsu domin gudanar
da bikin kirisimeti, Hafeez yayi mishi izini sannan
yad'auki kudi mai tsoka yabawa Daniel.
Lkcin da Daniel zaitafi garinsu har qofan d'akin Meena
yaje yayi sallama da ita, nan itama tayi mishi fatan
adawo lafiya.
*DA YAMMACI*
A yammacin ranar ne Meena tashiga kitchen tad'aura
tuwon semo da miyan d'anya ku6ewa, Meena taxage
sosai tadafa abinci mai kyau da tsari dukk dan taburge
Hafeez.
Bayan Meena tagama girkinta ne takoma d'akinta
toilet tashiga ta silla wankanta sannan tafito tashirya tsaf
abunta cikin wata jar atamfarta mairatsin ash kala,
atamfar taimata kyau sosai, simple mark up tayi sannan
tanufi falo taxauna ta kunna Tv.
Horn din motar Hafeez Meena taji, dasauri tamiqe taleqa
window' Hafeez din ne kuwa ta hango yayinda yake
qoqarin fitowa a mota, dasauri takoma maxauninta.
Murd'a kofan falon yayi yashiga batare da ya lura cewa
akwai mutun a falon ba, dasauri Meena ta taso da
fara'arta tayi mishi sannu da zuwa batare da Hafeez ya
kulata ba tasa hannu tana qoqarin ansar briefcase dinsa,
wani irin takaici Hafeez yaji baisan lkcin daya tunkud'e ta
ba tafad'i. Hafeez ko ajikinsa haka yatsallaka Meena
yawuce.
Dinning area yamaida dubansa yaga cewa tahad'a masa
abincin dare tsaki yaja mtssssww stupid, Hafeez nafadin
Haka yanufi d'akinsa.
Jikin Meena yayi sanyi sosai a hnkli ta tashi a wurin
tashiga d'akinta, saman gadonta tahau tarafka wani uban
tagumi nan tashiga yin tunani kala kala akan yadda
zatabi da hafeez nan dai tayanke shawaran zata jure
komai dan ganin tacikawa Balkisu alqawarinta kmr
yadda tacikamata nata.
Magri nayi Hafeez ya d'aura alwalarsa yawucewarsa
masallaci, bayan sun idar da sallah restaurant yanufa kai
tsaye yacika tumbinsa, dukk da cewa yasan Meena tayi
girki amma Sam baijin iyacin girkinta koda wasa.
__•__•__•__°__°__°__•__•__•
A kullum Meena tana qoqari sosai wajan kula da Hafeez,
ta gyara mishi d'aki tasa roomfrshnr ta wanke toilet
dinsa tagyara mishi kayansa, sannan tayi mishi girki
kullum dukk da cewa Hafeez bayaci amma Meena dai dai
da rana d'aya bata fasa abubuwan da takeyi ba, tsawa da
gyara turi da masifar Hafeez baya hana Meena ta
kyautata masa.
Meena ce zaune a falo tanajiran shigowar Hafeez, sai jin
tayi telephone Na qara (wato landline wnda kowa xai iya
d'auka, kasancewar Meena batada waya) dasauri Meena
tamiqe ta isa wurin da telephn din ke ajiye tad'aga
wayan kmr yadda taga Hafeez nayi, sallama tafarayi
sannan suka gaisa
Take anan Meena tagane muryan Balkisu ne nidai
naga Meena sai murmushi takeyi daga bisani kuma naji
tace mekikace daqarfi!! ?? Gabadaya naga hankli Meena
yatashi dasauri tajefar da wayan tanufi d'akinta.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:47AM, 8/4/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣4⃣
A rikice naga Meena tafito daga d'akinta sanye da hijab
dasauri naga taja kofan d'akin ta rufe sannan tanufi
hanyar waje a hanzarce, bakin titi tanufa kai tsaye da
alamar tana jiran abin hawane.
Kmr wucewan minti biyar Meena na nan tsaye bata
samu abin hawa ba, sai ga Balkisu nan cikin motarta tun
kafinma taqarasa tagane cewa Meena ce tsaye bakin titi.
Dasauri Balkisu tayi parkn din motarta kusa da
Meena, zuge glass din motar tayi lkcin ne Meena
tafahimci cewa Balkisu ce, ae kuwa da hanzarinta
taqarasa cikin motar.
Bayan tashiga cikine Balkisu tafashe da yar dariya tace
"a'a Anty amarya inazaki haka badai kice mgnr da
mukayi bane dukk tafirgitaki haka ba?" Meena tayi wata
irin sassanyar ajiyar zuciya tace "haba Balkisu mai xai
hana hanklina baxai tashi ba karki manta fa cewa basan
garinsu mahaifiyata ba ynxu idan ta tafi tabarni batare
da nabita naga dangina ba mai kike tunanin xaifaru?
Gsky nidai xanbi Amma na xuwa garinsu, Balkisu tadubi
Meena da murmushin nan nata tadafa kafad'arta tace
"haba kekuwa Anty amarya ae baki bari naqarasa miki
abinda nake son cewa ba kawai naga kinkatse call din
shiyasa kikaga nafito a hanzarce".
Ynxu koh da ace bin Baba Rabin zakiyi hakanan zakitafi
batare da izinin yayana ba ko kuwa hakanan zakije
hannu siddan babu kayan sawa balle tsaraba?
Meena ta sadda kanta qasa tace "wlh dukk na rikice ne
sbd bana fatan abinda xaisa nasakeyin nisa da
mahaifiyata" Balkisu tace "hakane amma ae ba yau bane
tafiyan nata sai jibi ne fa Dan haka muje namaidaki gda
ki kwantar da hnklinki zanfad'awa Yaya mgnr tafiyan
naku amma inaso kema kisameshi dakanki kifad'a masa,
toh kawai Meena tace.
Hakanan Balkisu ta mai da Meena gda sai faman
zolayanta takeyi.
** ** **
Hafeez ne zaune awani tafkeken Restaurant yana cin
abincinsa hnkli kwance, daga gefe kuma inda ya ajiye
wayansa tashiga ruri! A hnkli Hafeez yajawo wayan 'luvly
Sister' sunan da Hafeez yayi saving nmbn Balkisu shine
ya baiyanna agaban screen din wayansa da sauri
yad'auka gamida sawa a kunnenshi, bayan sun gaisa ne
Balkisu ke sanar da Hafeez mgnr tafiyan Meena wnda
zasu ita da mahaifiyarta, Hafeez yace "olryt Allah
yakaimu lkcin" Balkisu tace ameen nan suka d'an ta6a
hiransu daga bisani kowannensu ya ajiye waya.
Abangaran Hafeez kam shiru yayi hakanan kuma sai
yakejin kmr babu dadi, can dai kuma ya hori xuciyarsa
tama daina damuwa da wannan yar qauyan ae ma inta
tafi kahuta, inba ma tsabar rainin wayo ba Balkisu nake
aure ko ita ae kamata yayi taxo da kanta taneme ixinina
wato tanaji ita watace tafi qarfin takawo kanta knan?,
hakanan Hafeez yayi tasaqawa da kuncewa a cikin
xuciyarsa. Har dai yagama cin abincinsa sannan yanufi
gda.
Yau ma kmr kullum Meena tayi masa abinci ta ajiye
dukk da tasan cewa baci xaiyi ba, haka nan bayan
shigowarsa cikin gda har bakin kofa tabisa dan ta
tarbeshi amma gayen nata ko kallon inda take baiyi ba,
balle yanxu dama cike yake da haushinta akan qin xuwa
da batayi da kanta tafara tambayarshi ba.
Inda sabo kam Meena tasaba da irin abubuwan da
Hafeez ke mata wanda zuwa ynxu kam har sun fara
daina damuwarta.
Misalin qarfe tara na dare Meena tashiga bayi tayi wnka
sannan tad'airo alwala, kayan bacci tasaka masu sauqin
nauyi hakanan tajawo xani tad'aura saman sleepn drss
din sannan tasanya hijabinta ta gabatar da nafilfilunta
kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne ta yankewa
xuciyarta shawaran cewa gwnda taje a daidai wannan
lkcin tasanar da Hafeez mgnr tafiyanta inba haka ba da
safe koh da zata tashi olrdy ya fita.
Hakanan ta gama yanke shawaran ta, ta amincewa
zuciyarta, Dan haka d'akin Hafeez tanufa kai tsaye a hnkli
tashiga knckn kofar,...sai da Hafeez yagama jan ajinsa
kasancewar yasan babu wnda xai kwankwasa mishi kofa
adaidai wannan lkcin sai Meena shiyasa sai dayagama
jan ajinsa sannan yace yes come in! A hnkli Meena ta
murd'a kofan d'akinta shiga.
Hafeez tagani zaune bakin gado dagashi sai farar vest
da boxsas yanata aiki da system inshi, da sallama tashiga
cikin d'akin, Hafeez ya amsa mata sallamarta batare da
yad'ago ya kalleta ba.
Meena taduqa har qasa ta gaida Hafeez,..Hafeez kuwa ko
kallo bata ishesa ba amaimakon ma ya amsa gaisuwansa
datayi sai cemata yayi yes inajinki fad'i abunda yakawoki
kinga aiki nakeyi.
Meena ta had'iye wani yawu dakyar yawuce sannan
ta sadda kanta qasa sbd jitayi gabad'aya Hafeez yayi
mata wani irin kwarjini, cikin nutsuwa Meena tace
"dama Amma nane xatayi tafiya xuwa gda shine nake so
na bita" Hafeez yace "dakyau yar qauye xa'aje qauye
kenan? Meena dai batace masa komai ba sai wasa kawai
take da d'an yatsanta.
Wani murmushin takaici Hafeez yayi sannan ya d'auko
wata waya LG yamiqa mata yace ga waya nan inkinje kiyi
amfani da ita, Meena ta amsa tayi godiya sannan Hafeez
yad'auko bandir din kudi yan dari biyar biyar ya
watsawa Meena cike da gadara yace gashinan wannan
akaiwa tsohuwa nasan zata buqata.
Mgnr Hafeez ta matuqar 6ataran Meena amma sai ta
danne xuciyarta miqewa tayi cike da d'acin rai takalli
Hafeez ta kalli kud'in har dai Meena tayi niyar sakar
mishi mgn sai kuma nan da nan ta taushi zuciyarta, ajiye
masa kudinsa tayi a qasa dai dai qarfarshi taficewarta a
d'akin.
Binta Hafeez yayi da kallo cike da mamakinta
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:27AM, 8/5/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣5⃣
Balkisu da kanta taje wani babban super market
tahad'owa Baba Rabi tsaraba masu kyau na amfani, su
sabulun wnka wanki turaren shafawa kwalayen biskuit
da dai sauransu, hakanan ta kwasa tayi gdan Baba Rabi
dasu ta kai mata. Baba Rabi tayi farinciki sosai da irin
yawan hidimar da Balkisu keyi da ita, nan tayi tasawa
Balkisu albarka gami da nuna farincikinta.
Washe Gari.
Tunda asuban fari bayan Meena ta idar da sallah
batasamu ta kwanta ba sai da ta tabbatar da cewa tayi
dukkan wani aikinta kmr yadda tasaba, agogon dake liqe
jikin bangon d'akinta ne yabuga qarfe 6:30 a gaggauce
Meena tafad'a toilet tayi wanka kasancewar tasa qarfe
7:00 Hafeez ke fita, gashi yau tanason tawuni gdnsu dan
tasan irin shirye shiryen da yakamata suyi ita da
Ammanta.
Wata dakakiyar shadda lemon green wadda akayiwa aiki
dazare orange, riga da siket ne su Meena tad'auko tasa
(woww ni kaina munay sai dana yaba wannan shiga)
dukk da ba wata kwalliya Meena tayi sosai ba amma tai
matuqar kyau, nan tad'auko takalmi orange gyale
orange.
Motsin Hafeez taji yana qoqarin fitowa daga d'akinsa
dasauri taduba agogo taga 6:57 a hanzarce ta zura wata
qatuwar Hijabi tanufi waje.
Ki6iss sukayi da juna Hafeez ke kokarin fita yayin da
Meena tafito a d'akinta dasauri tace Yaya!!
Mamakine qarara ya baiyanna a fuskar Hafeez jin cewa
Meena ke kiransa da Yaya dukk da cewa bata fiye kiran
sunansa ba, sannan a iyazatonsa yana tunanin tayi fushi
da shi sbd abinda yayi mata jiya daddare.
Tsayawa Hafeez yayi batare da ya juyo ba, a hnkli Meena
taqarasa kusa dashi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa a
takaice Lfy, Batare da nuna damuwa ba Meena tace "Dan
Allah sonake kamin izini xanje gdnmu nawuni acan
sannan inba damuwa inaso ka ajiyeni a gda.
Hafeez har yayi niyyar cewa wani abu sai kuma
yafasa, juyowa yayi yakalleta sama da wasa sannnan
yace olryt nabaki nan da minti d'aya inbaki shirya ba xan
wucewata.
Ae Hafeez nacewa haka dasauri Meena ta miqe kafinma
Hafeez yabar falon tuni tashige d'akinta hijabin dake
sanye jikinta tacire tasanya gyalenta sai takalminta da
tasa tad'auki wayarta a gaggauce tarufe d'akinta da kofar
falo, kasancewar ita da Hafeez kowa nada nashi
mukullin.
Hafeez ne zaune cikin motarsa yana jiran fitowan Meena,
hango ta yayi tafe sanye da gyale dasauri Hafeez yasake
kallonta dakyau wani irin abu yaji ya d'arsu a zuciyarsa
wanda shi kansa baisan miye ba wani irin kishi yaji
domin kuwa ko da ace maqiyin Meena ne yaganta to
tabbas dole ya yaba mata sbd tayi masifar kyau, cikin
zuciyar Hafeez yace "lallai yarinyan nan ta rainamin hnkli
ba ynxu naganta sanye da hijabi ba? Wato dan zata fita
shine hadda wani sa gyale.
Hafeez naganin Meena taqaraso ya watsa mata wata
uwar harara, wanda hakan yasa Meena tasha jinin
jikinta, a qufule Hafeez yace kee wato baki shirya fita
zuwa anguwan ba shine kikayi westin tym dina?
Meena tadubi kanta sama da qasa sannan tasake duban
Hafeez tace "wlh yaya na shirya" Hafeez yadaure fuska
yace kina nufin da gyalen nan zaki fita? Meena tafahimci
abinda Hafeez yakeson cewa wato bai da tsarin son
iyalinsa su sa gyale, dasauri Meena ta koma cikin gda
tasanyo hijabi dukk da cewa hijabin sam baiyi matchn
dakayan jikinta ba hakanan tasanya abinta domin ita dai
buqatarta kawai ta jita ajikin Ammanta.
Gdan baya Meena ke qoqarin bud'ewa dasauri Hafeez
yace ke yar qauye wakike ajiye drivanki look inbaki
shirya tafiyan ba nixan wucewata ko ancemiki banda
abubuwan yine, jiki a sanyaye Meena tabude gdan gaba
taxauna Hafeez yaja motan sukafice a gdan.
Sanin datayi Hafeez baisan gdnsu ba shiyasa tadubeshi
cikin sanyin muryanta tace "famfamari zamuje wurin
masallacin juma'a, ko uffan Hafeez bai ce mata ba
hakanan yaja motarsa yanufi anguwan da tafad'a mishi.
Sunxo dai dai kofan gdan ne Meena tace sun iso
tsayawa yayi a hnkli daga gefen hanya, Meena tasa
hannu zata bud'e kofan Hafeez yace "ke tsaya yar kauye
karki 6allamin murfin mota, zura hannunsa Hafeez yayi
yabud'e mata kofan sannan yace, nabaki nan da awa
biyar kikoma gda kinji abinda nace?"
Ran Meena ya6aci sosai amma talura Hafeex neman
rigima yakeyi shiyasa kawai ta gyada masa kanta tafice a
motar.
Meena taji dadin kasancewa da Ammanta sosai wnda
har hakan yasa tashagala tamance da umarnin Hafeez.
Qarfe 2 dai dai Hafeez yakoma gda amma still Meena
bata dawo ba, wani irin haushi Hafeez yaji ganin cewa
yadawo gda babu Wanda ta tarbeshi dukk da cewa baya
kulata amma yau din sai yaji babu dadi.
Wani irin tunani ne yazowa Hafeez lkci d'aya wanda
yad'imautashi, dasauri ya zari car key dinshi yafice a
gdan, gdansu Meena yanufa kai tsaye sbd tunawan
dayayi cewa matuqar Meena tace zata koma gda tofa
motan haya xata hau, tunanin Hakan ne yasa ya
gaggauta zuwa yad'auko ta da kansa.
Hafeez na danna kan motarsa cikin kwanar gdansu
Meena nan ya hango abinda yad'aga masa hankali.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:23AM, 8/5/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣6⃣
Hafeez Meena ya hango tsaye a kofar gdansu ta tsaida
mai adai-daita sai faman murmushi takeyi mishi yayin
da suke mgn ita da mai adaidaitan, wani irin kishi Hafeez
yaji, nan fa jikinsa yafara kyarma a guje yashiga cikin
layin ko gabansa ba ya iya gani mai kyau, Hafeez na pake
motanshi kafinma yakasheta a hanzarce yabude murfin
motan yafita batare da ya kashe motan ba.
Gadan gadan Hafeez ya nufi kan mai adai daita, mai adai
daita na cikin tsaka da ciniki da Meena sai ji kawai yayi
anshaqo wuyansa ta baya ana dukansa ta ko ina.
Dasauri Meena tafasa ihuu! Tana roqon Hafeez da
yabar abinda yake yi, Hafeez kam kojin ta bayayi
gabad'aya jiyake kmr ya kashe mai adai daitan sbd
haushi,. ihuun da Meena takeyi ne yajawo hnklin mazan
anguwar dakyar suka samu suka kwaci mai adai daita a
hannun Hafeez.
Idanun Hafeez gabad'aya sun rine sunkoma ja sbd
tsananin kishi, a tsorace Meena tafara ja dabaya sbd
gabad'aya Hafeez tsoro yabata sai wani irin huci yakeyi
tamkar zaki cikin dawa, gawata uwar harara dayake jeho
mata.
Da gudu tashiga gdansu dai dai lkcin ne Baba Rabi
takejiyo hayaniya daga waje dole tamiqe tanufi hnyar
waje don ganin mekefaruwa, Meena ce tashigo gdan da
gudunta sai faman waiwayen bayanta takeyi.
Hafeez kam mutanen cikin anguwar sai tambayanshi
sukeyi mai wannan bawan Allah yamasa? Kota Kansu
Hafeez bai biba yanufi motarshi ya kasheta yarufe
sannan yanufi cikin gdansu Meena din.
Meena rungume Amma tayi dukk tsoro yacikata sai
wani faman haki takeyi kmr wacce tayi gudun 3kilomita,
Baba Rabi sai faman tambayarta takeyi Aminatu lpy
kuwa meyaparu waye ya biyoki? Meena kasa mgn tayi sai
faman kallon hanyar shigowa gdan takeyi a tsorace
"domin atunani Meena hadda ita Hafeez zai hada"
Hafeez ne yashigo gdan sallamarsa, Baba Rabi ta amsa
mishi sallaman yayin da ta kura mishi ido tanajiran
yafad'i da wacce yazo domin atunanin Baba Rabi shine
Wanda ya biyo Meena,(domin kuwa Baba Rabi ko a hoto
bata ta6a ganin Hafeez ba) Hafeez har qasa yaduqa ya
gaishe da Baba Rabi, Baba Rabi ta amsa "lafiya kalaw"
Lkcin ne Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar xuciya
sannan tace "Amma wannan shine Hafeez yayan Balkisu"
Baba Rabi ta fad'ad'a murmushinta sosai tace "Allah
sarki kayi Hkri Sam ban shaida ka ba, nan tayi mishi iso
ixuwa cikin gdan, A falo Hafeez yazauna Baba Rabi da
kanta takawo mishi abinci tuwon semo da miyar
allayahu zallah, drinks takawo mishi da ruwan sanyi.
Baba Rabi da Meena kitchn suka koma suka fara had'awa
Hafeez juice din kwakwa, Hafeez kam yunwa yakeji sosai
dan haka bude kulan yashigayi tuwon semo yagani anyi
malmalanshi ansa leda tsaf sai kuma miyan allayahu
wnda taji manja, malmala d'aya Hafeez yad'iba yasa a
plat bayan yazuba miyan allayahun nan fa yahauci, kafin
Hafeez ya ankare tuni yagama da malmala guda"woww
vry nyc Hafeez kawai ke fad'i yana lasan baki😋"
Meena ce tashigo Hannunta d'auke da jug din juice din
kwakwan, duqawa tayi tad'auki glass cup a kusa dashi
batare da ta kalleshi ba tashiga zuba mishi.
Kura mata idanu Hafeez yashigayi kmr yajawota
kusa dashi haka yakeji, Meena nagama zuba mishi juice
din ta tashi tabar falon a hanzarce.
Hafeez jiyayi kmr baxai iya tashi awajan ba sbd wani irin
qoshi dayayi, rabonsa da cin abinci kmr haka har
yamanta, murmushi kawai Hafeez keyi shi kad'ai yasan
abinda yasashi murmushin.
Meena ce tashigo cikin falon wannan karon ba Hijabi,
filas din da Hafeez yagamacin abinci dasu shine Meena
tashigo danta kwashesu, Hafeez kam sai binta yake da
kallo tamkar wata baquwa, Hafeez kam sai mamakin
knsa yakeyi yadda ya lura cewa Meena naqoqarin zautar
dashi lkci d'aya mamakin kansa yashigayi sosai wnda
har Hafeez yakama tantamar anya kuwa shine? (LOL)
sai da Meena ta gama kintsa falon sannan Baba Rabi
tashiga falon suka sake gaisawa da Hafeez, Baba Rabi
tasake da Hafeez sosai sai jansa take da fira, wanda
shikuma Hafeez gabad'aya kunya tagama cikasa kasa
sakewa yayi da Baba Rabi, bayan sund'anta6a hira sama
sama ne Hafeez yaciro kudi Wanda shi Kansa baisan
iyakarsa ba yace wa Baba Rabi gashinan tayi tsaraba,
dafarko Baba Rabi qin kar6a tayi tace a'a ae Balkisu tayi
musu hidima sosai dan haka baxata kar6i kudinsa ba,
gabad'aya Hafeez jiyayi daraja da kimar tsohuwar taqaru
a idonsa, dakyar dai Hafeez ya samu ya lallama Baba
Rabi ta Amshi kudin,....daga bisani Hafeez yace da ita shi
xai wuce gda dama yaxo ne dan yayi mata Allah yakiyaye
hanya, Baba rabi nan tayi tasa mishi albarka tana mai
nuna jindadinta sosai.
Hafeez nafitowa Meena tasa Hijabinta tad'auki wayarta
sukayi sallama da Amma, a hanzarce tarufawa Hafeez
baya a tare suka fice a gdan.
Gaban Meena sai dukan uku uku yakeyi gabad'aya
taqisakewa sai faman takure kanta takeyi.
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:50AM, 8/6/2016]
MUNAY✍🏽: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
✨BURIN HAFEEZ✨
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
By
©MUNAY
®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.
Episode3⃣7⃣
Daga Hafeez har Meena ba Wanda yace da wani uffan
haka har suka isa gda, Hafeez nayi parkn Meena tayi
sauri tafice a motan, tsuki Hafeez yayi cike da haushinta,
a filin gdan Hafeez yayi parkn din motanshi baiko sami
damar sakata ma ajiyarta ba, a hanzarce yarufawa
Meena baya.
Meena da sauri tabud'e kofan falon sannan tanufi
d'akinta, isar take nan takama kofan da niyyar tabud'e
sai jitayi Hafeez yace "kee! Tsaya anan Meena ko waigawa
takasa tsaye tayi bakin kofar kmr wadda aka shuka.
Hafeez nazuwa a fusace ya manna Meena ajikin Bango,
take mata babban yatsanta yayi naqafa da qarfi Meena
tasaki Yar qara, Hafeez yace "aikin banxa ashe kina mgn?,
Meena ganin Hafeez ya kura mata ido ko kiftawa baiyi
yasa tasadda kanta qasa, Hafeez gyad'a kai yayi yace
"dakyau hakan Yatabbatar min da cewa baki da gaskiya
sannan inaso kifad'a min uban waye yabaki izinin tare
mai adai daita har kitsaya dashi kina masa dariya? Meena
wacce sai mutsu mutsu takeyi tanason kwace kanta daga
riqon da Hafeez yayi ma hannayenta gashi ya taka mata
babban d'anyatsa yaqi sakewa, Meena kamar xatayi kuka
tace nifa badariya nake mishi ba, kawai tambayarsa nayi
anawa xaikain.....kafin Meena taqarasa abinda take son
cewa Hafeez yadaka mata tsawa yace ni ba wannan
natambayeki ba cewa nayi meyasa kike masa dariya?
Meena tayi rau rau da idonu tace Dan Allah yaya kayi
hkri baxan sake ba.
Hafeez yace no ba laifinki bane laifina ne sbd kin raina ni
ko? Meena ta girgixa kanta tace "a'a
Hafeez yace okay toh yayane? Wato hakan ma yananufin
cewa idan kukaje garin naku haka xakiyi behaving? Kina
tare

Please Login or Register in order to submit comment