Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama na kirawo mace ta karshe wadda na ke son na yiwa yan tambayoyi, wato Baraka." Baraka ta hau mumbarin shaida ta tsaya. Kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar ce gaba daya a tsorace ta ke, kamar ace arr! Ta tsere. Sai rarraba idanu take. Wannan ya nayi na Baraka ya yi matukar yi wa Hannatu dadi, domin ta san dai ko ba Komai Barakar ba za ta wahalar ba. Hannatu ta dube ta, "Baraka mene ne tsakaninku da Hajiya Rukayya?" "Kawatace." Ta amsa a takaice. "Tsawon wane lokaci?" "Tun muna kanana" "Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu ku na tare?" "E, muna tare a zuciya, amma mun dade ba mu hadu ba." Kai tsaye kuma a takaice ta ke ba ta amsar. "Me ya sa?" "Saboda mun tashi mun kma jigawa, tsawon shekaru." "Kun jima ba ku ga juna ba sai a yan makonni biyu da su ka shude, haka ne?" "Eh, haka ne." "Mene ne ya kawo ki?" "Ziyara na kawo gurin irinsu kawayena, da kuma sauran yan uwa." "Wato daga can ki ka taho ma ta da alewar me guba da ta hallaka yayanta..." "Wannan tambayar ba ta dace ba." Garba ya katse ta bayan ya mike tsaye da hanzari. Sannan ya juya ga mai shari'a, "Ya mai shari'a, ya kamata fa a lura, Hannatu na amfani da wasu irin tambayoyi da ba sa kan la..." "Ya isa Garba." Mai shari' ya katse shi, "Tambayoyinta su na kan layi." Ya juya gare ta, "Ki na iya ci gaba Hannatu." Hannatu ta yi murmushi sannan ta kuma maimaita tambayar ga Baraka, "Wato daga can ki ka taho mata da alewar me guba da ta hallaka yayanta..." "Ni!" Ta katse Hannatu, "Wallahi bani ba ce." Ta dubi bigiren da Hajiya Rukayya ta ke "Hajiya ke ce ki ka ce ni na kawo miki wannan alewar?" A rikice ta kuma mayar da dubanta ga Hannatu "Wallahi tallahi ba ni na bata da hannuna ba. Ni dai na san na raka..." Ta yi shiru saboda wani abu da ya shiga zuciyarta. "Kin san kin raka ta ina?" Hannatu ta bukata da sauri. Idan ba ta fada ba ta san ita za ta kwana a ciki. Bakinta na rawa ta ce, "Na san ni na...ra...ka ta ta karbo...alewar..." Wani sabon ya nayi ne ya bayyana a fuskokin daukacin ma su zaman shaidar, ciki har da mai shari'ar. Yanzu idanunsu gaba daya ya na kan Barakar. "A ina ku ka karbo alewar?" Ta soma kuka, "A wajen wani babban boka." shi kenan ta bayyana. Hayaniya ta kuma kaurewa a wannan karon shi kansa mai shari'ar kasa tsawatarwa ya yi akan kari saboda mamaki. Sai da aka samu tsawon lokaci kana da kyar ya dakatar da hayaniyar. Hannatu ta dubi mai shari'a, "A yanzu babu bukatar na tsawaita jawabi domin gaskiya ta bayyana, sai dai kira biyu da zan yi ga shari'a shi ne, lallai ya wajaba ta hukunta Hajiya Rukayya da kawarta Baraka hukunci mai tsauri don gudun kada irin wannan ta kuma faruwa a gaba, donin zamansu cikin jama'a haka sakaka hadari ne. Haka nan kuma tilas ne shari'a ta hukunta duk wanda ya ke da sa hannu cikin wannan shiri don ya zama a gaba ya kiyaye don samun kyautuwar al'umma. Kira na biyu, ina neman shari'a da ta tirsasa Hajiya Rukayya ta biya Zainab diyar kudi Naira Miliyan daya, don yunkurin bata ma ta suna da ta yi ta hanyar makala ma ta abin da ba ita ta yi ba...bugu da kari da zaman da ta sa ta yi na tsawon kwanaki a gidan horo. Daga karshe ina addu'a ga duk matar da ta ke tare da kishiya, Allah ya kiyaye ta kar a kulla ma ta sharin da zai kai ta cikin wahalar da Zainab ta shiga, kwana goma sha daya a 'Women Detention Centre' ma'ana "Gidan horo na mata" Kusan gaba daya kotun aka tallafawa addu'ar Hannatu da "Amin". Ta yi godiya ta koma ta zauna. A yanzu dai Barista Garba ya yi shiru cikin tunani da jimami gami da nadamar tsayawar da ya yi wa Hajiya Rukayya kasancewar ta ba shi abin a rufe. Ya yi tagumi hannu bibbiyu ya na jiran jin hukuncin da mai shari'a zai yanke. Hajiya Rukayya da Baraka da duk yan uwanta kuwa babu abin da su ke yi sai kuka. Ba tare da tsawaitawa ba ya yi bayani game da duk hojjoji da shaidun da lauyoyin biyu su ka gabatar. Bayan ya kammala sai ya fara bayar da sakamako shari'ar kamar haka:- "...Bisa dogaro ga duk wadannan hojjoji da shaidu da aka gabatar, shari'a ta tankade tsaf, kuma daga karshe ta wanke wadda a ke zargi, wato Zainab, ta kuma sake ta, bisa dogaro da doka mai lamba 103, sashe na 119, sakin layi na biyu, cikin baka. Kana ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga Hajiya Rukayya bisa laifin da ta aikata na zama silar kashe yayanta biyu...Da kuma biyan Naira miliyan daya ga Zainab kamar yadda lauyarta ta bukata, bisa dogaro da doka ta 99, sashe na 121. Sakin layi na uku..." Ihun da Hajiya Rukayya ta kurma ne ya katse mai shari'ar, lokaci guda kuma ta sulale ta fadi kasa sumammiya. Bayan yan sanda sun yi waje da ita bisa umarnin alkali, sai ya ci gaba, "Haka kuma Shari'a ta yanke hukuncin daurin shekaru goma ga Baraka ba tare da tara ba, bisa laifin hada kai don yunkurin aikata kisan kai. Shi kuwa Lukman, kotu ya yanke ma sa hukuncin daurin shekara guda bisa karbar cin hanci, amma shi zai iya biyan tara ta Naira dubi hamsin...Wadannan kuma mun yi duba ne ga doka mai lamba 69, sashe na 173, sakin layi na farko, cikin baka." Da wannan mu ka kawo karshen wannan shari'a." Ya rufe littafinsa ya mike. Duk jama'a su ka mike. Ita ma Baraka da Lukman su na kurma uban kuka, har da kururuwa, yan sanda su ka yi awon gaba da su. BAYAN MAKO GUDA DA SHARI'A Karfe tara na safiya wannan rana ta Alhamis a ka sallamo Alhaji Basiru daga asibiti. Murna a wajen Zainab ba a cewa komai. Koda isowarsa gida jama'a su ka rika zuwa su na yi ma sa jaje gami da ta'aziyyar rashin yayansa. Bayan komai ya natsa, sahun jama'a ya dauke daga zuwa yin jaje da gaisuwa, da karfe hudu na yammacin wannan rana sai Alhaji Basiru ya gayyaci matarsa dakinsa saboda wani zama da za su yi, zaman da ya kira shi da zaman shawara. Da godiya ga Allah (S.W.T.) ya soma, bisa ketarar da shi da ya yi daga wannan mummunan hadari, kana ya ci gaba da cewa, "Zainab a farko, bayan godiya ga Mai duka, ina mika jinjina gare ki bisa namijin kokarin da ki ka yi wajen jure duk abin da Hajiya ta ke mi ki. Lallai kin isa jinjina, ya kuma dace da ma ga kowace mace ta rike abubuwa hudu wadanda su ne ki ka rike har ki ka kai wannan matsayi. Allah ya saka mi ki da alkhairi." "Amin." Ta amsa murya a sanyaye. Shiru na dan lokaci babu wanda ya yi magana. Zainab ta cira kai ta dubi Alhaji Basiru bayan ta nisa, "Alhaji." Ta kira sunan a nutse. Ya dago kai ya dube ta, "Na'am amarya." Ta dukar da kai cikin jin kunya ta ce, "Alhaji har yanzu ban fita daga amarci ba? Shekaru nawa..." "Har yanzu ba ki bar matsayin wannan suna ba tunda ban yi wani auren ba, bayan naki." Su ka yi dariya gaba daya. "Me ki ke so ki ce ne?" Ya tambaya bayan sun tsagaita da dariyar. Ta yi murmushi, "Alhaji ina son sanin abubuwa guda hudun nan da ka ce ya dace kowace mace ta rike." Shi ma ya yi murmushi, "Ai ke kin rike su shi ya sa har yanzu ki ke zaune daraf a mukamin da babu kamar ke a cikin zuciyata. Kuma duk macen ma da ta rike su to babu shakka za ta zama sarauniya a cikin zuciyar mijinta. Sai ta fi komai soyuwa a zuciyarsa. Kai! Har ya ji cewa ma zai iya bayar da ransa saboda ita." Zainab ta numfasa, "Maigida ai ka san kogi bai ki dadi ba. Ina so ka kara sanar da ni su don na kara kankame su, don Wallahi ba na son abin da zai bata ma ka rai ko kadan." Ta sunkuyar da kai kasa. Alhaji Basiru ya nisa, "Kina da gaskiya amaryata." ya daga yan yatsunsa hudu, "Wadannan abubuwa guda hudu su ne; Hakuri da Biyayya da juriya da kuma Gaskiya. Kin ga dai Hakuri shi ne, kawar da kai da sanya dangana ga abin da aka yi ma ko da ya bata ma ka rai. Juriya kuma ita ce, ci gaba da jajirce wa a kan abin da ka ke yi mai kyau komai tsangwama, Biyayya kuwa, bi da yarda da abin da aka san bai saba wa Allah ba, don farantawa miji rai. Gaskiya kuma, tsaya wa a kan abin da ka san an yi ba tare da kaucewa ba, da kuma yarda da abin da aka sanar da kai na game da kuskure don gyara, komai dacinsa. Don akwai Hadisi na Manzon Allah (S.A.W) da ke bayani game da, ba wani abu ne girman kai sai kin gaskiya" Zainab ta jinjina kai ganin ya dan tsahirta ya na duban ta. "Kin ga duk macen da tare wadannan abubuwa." Ya ci gaba, "To, babu shakka ta tsira." "Wannan gaskiya ne Alhaji. To amma ni ban ji ka tabo bangaren..." Ta yi shiru. "Bangaren me?" Ya bukata. "Bangaren su kwalliya, tsafta da kyale-kyale, kissa don jan hankalin maigida ba, wanda wannan ma na san su na daga cikin abin da ke kara dankon auratayya." "Ya gyada kai, "Kwarai kuwa Zainab, amma duk wadannan da ki ka lissafo su na karkashin abu na uku da na lissafo, wato 'Biyayya', don sai da ita ne za a yi duk wadannan abubuwa don faranta wa maigoda rai." Ita ma ta gyada kai, "Gaskiya ne wannan maigida." "Ki na da tambaya cikin wadannan abubuwa kafin na je ga shawarar da na ce mi ki za mu yi?" Ta girgiza kai, "Babu maigida. Na gane su sosai, kuma da izinin Allah zan dage don ganin na rike wadannan abubuwa da ya kamata a kira su da Garkuwar Aure." Ya yi murmushi, "Haka ne. Abu na gaba da na ke son na gaya mi ki wanda na ce shawara ne, shi ne ina so zan sauwake wa Hajiya." Ta dafe kirji, "Haba Alhaji, yanzu..." "Saurara!" Ya katse ta, "Idan ban sake ta ba ya ki ke so na yi da ita bayan ta na karkashin hukuncin daurin rai da rai? Ki na ganin aurena da ita zai yiwu ina nan ta na can? Kuma ko ba wannan ki na tunanin zan iya zama da ita?" Zainab ta sauke hannunta jiki a sanyaye, babu yadda za ta iya. "Ya na ji kin yi shiru?" Alhaji Basiru ya bukata ganin shirun nata na kokarin tsawaita. Ta nisa, "Babu koma Alhaji...tausaya ma ka kawai na ke yi da kuma ita Hajiyar". Ya yi murmushin karfin hali, "Ni mene ne dalilin tausaya min din?" Ta sunkuyar da kanta cikin kunya, "Saboda bukatarka ta zama da mata biyu." Ya girgiza kai kana ya yi wani dan guntun murmushi, "Babu komai amarya, kar ki damu, ke ma kin wadace ni." Ta dan harare shi cikin wasa, "Gaskiya kar ka kuma ce min amarya." Ya girgiza kai, "Ina! Ai ba zan iya daina wa ba." Ta gyada kai a takaice, da muryar wasa ta ce, "Lallai idan ba ka daina ba zan dau mataki." Ya fashe da dariya, "Ai ba za ki iya ba. Kuma ma wane mataki za ki dauka?" "Uhm! Ya wuce na cije ka?" "Cizo?" Ya bukata, "Ni kuma nawa hakoran fa? Ba sai na rama ba?" Ta daga kai su ka hada idanu. Abin da ta gani cikin idanunsa ya sa ta ce, "Bari na cije ka din ka rama." Ta yunkura ta kama hannunsa ta sa hakora. "Wayyo Allana!" Ya ce da yar daga murya. Ta sake shi da sauri, ta mike ta yi waje a guje. Bai tsaya wata-wata ba, ya mike ya bi ta da gudu. Dakinta ta nufa ta na dariya. Shi ma dariyar ya ke Da haka su ka shige dakin. KARSHE MUHAMMAD LAWAL BARISTA. Zaharaddeenn Shomar Whtapp

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment