Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gane abin da ke cikin ransa ba, ya ci gaba da tambayar ta. "In ce dai babu nisa ko?" "Babu nisa sosai...wata gaisuwa na ke son zuwa." "Gaisuwa?" A wannan karon ya dawo da dubansa gare ta. Ta gyada kai, "Wallahi kuwa." "Allah sarki." Ya ce ya na sosa kai, "Wane ne ya rasu?" "Wallahi dan gidan wata aminiyata ce ya rasu daren jiya, da sassafen nan aka sanar da ni." Ita da kanta sai da ta ji wani iri abu banbarakwai a bakinta saboda mamakin karyar da ta shirga cikin kankanin lokaci. Ya nisa cikin tausayawa ya ce, "Allah ya ji kan rai, ya gafarta masa...mu kuma ya kayuta namu zuwan." "Amin-amin" Ta amsa kai tsaye kamar gaske. "Wannan ai babu damuwa Hajiya." Ya ci gaba, "Idan kin gama shiryawa kawai direba ya kai ki..." "A'a Alhaji". Ta katse shi, "Babu bukatar mu tafi da direba a wannan tafiyar don kuwa ni da kawata da mu ka jima ba mu hadu ba za mu je, kuma tuntuni ma na riga na yi mata bayanin ni zan ja motar." Ta dan yi shiru ta natunanin yadda za ta dire karyar da ta shiryo. Ta ci gaba a wannan karon da rawar baki, "Har gardama fa mu ka yi, ta naban iya ba, ina cewa na iya! Ka na so ta yi mini...dariya ne ko kuwa ya ya?" "A'a Hajiya ba na kaunar haka. Abin da ki ka riga ki ka sani ne Tunda Allah ya zurta ni na ji ba na kaunar iyalina su ja mota, don ni na dauki hakan abin kunya a gare ni. Kuma koya mu ku mota ma da na sa aka yi, ai ba don ku dinga ja ba ne, saboda kawai bacin rana." ya tsagaita ya na daidaita numfashinsa, a halin yanzu kuma ya hade fuskarsa sabanin baya. Hajiya Rukayya ta dukar da kai jin dogon jawabin da ya yi na kin amincewa, wanda da ma ta yi zaton samun sa. "Da alama idan ki ka saki za ki yi wa kanki sakiyar da babu ruwa, Muddin ki ka bari Alhaji ya ce lallai direba ne zai kai ki babu yadda za a yi asirinki ya rufu. Ki san duk yadda za ki yi a matsayinki na ya mace ki shawo kansa. "wani sashe a zuciyarta ya rada mata. Ta cira kanta a hankali ta dube shi. Da raunin murya ta ce, "Haba Alhaji." A hankali sai ta matsa kusa da shi sosai, wanda har ya na iya jin hucin numfashinta a gefen fuskarsa, "Mene ne abin jin kunya don mun ja mota da kanmu? Ai ni kuwa ina ganin babu kasawa ga hakan. Kuma ma idan ka na tunanin kasawa ne, wa zai kula har ya gane cewa ni ce ke jan mota?" Ya girgiza kai, "Gaskiya Hajiya ni ba na son abin..." "Kai don Allah Alhaji". Ta katse shi bayan ta kara matsawa kamar za ta shige jikinsa. Ta kara sauke muryarta kasa sosai kamar mai rada, "Alhaji don Allah ka amince...yau daya dai." Ta dan hade fuska, da shagwaba ta ci gaba, "Gaskiya idan ba ka amince ba raina zai iya baci, kuma za mu bata." Duk da ta yi wata yar malalaciyar dariya a karshen maganar tata wadda ke nuna da wasa ta ke abin da ta fada, hakan bai hana shi shiga fargaba ba. Haka kawai sai ya ji gabansa na faduwa, a sannu kuma sai ya ji zuciyarsa ta soma amincewa da bukatar ta. Fahimtar ta da hakan ne ya sa ta furta a hankali, "Alhaji ka amince?" gyada kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba. "To, ai kai kawai ka gyada mini ba ka ce komai ba." Ta jefa shagwaba cikin muryarta, "Ka yarda na je?" Ya kuma gyada kai, kana a hankali ya ce, "Na yarda ki je." Ta mayar da kanta ta jingina jikin majiginar kujerar saboda dadin da ya mamaye zuciyarta. A hankali ta shiga furta, "Na gode, Alhaji, Allah ya kara dankon soyayya tsakaninmu." Wannan kalma ta kara tsunduma Alhaji Basiru cikin tsananin mamaki. *** Tun sa'ar da su ka kama hanyar zuwa gidan malamin tsibbun Hajiya Rukayya ke jin dadi ta nata washe hakora kamar wadda akawa wani babban Albishir, saboda tunaninta na ganin cewa yau ne za ta kawo karshen abin da ya tsokane mata idanu. Kuma ya ke damunta wato kishiyarta da danta mujahid. Koda yake a yanzu hankalinta ya fi karkata ga mujahid din, ta fi so ta ga babu shi kafin mahaifiyarsa musamman mada Baraka ta haska ma ta illarsa, na cewa ya na da gadon mace biyu. Ta dubi Baraka da ke zaune gefenta na dama gaban motar, daidai lokacin da ta fada wani kwazazzabo, "Baraka ni fa na fara ji a jiki na bukata ta biya, Ba ki ji yadda zuciyata ke tumbatse da farin ciki ba." "Ahaf! Wannan ma kadan kika ji, sai ma bukata ta biya tukunna." Baraka ta ce ta natabe baki, "Don ma kin ce dan kawai ki ke so a kawar, da da uwar ai da farin ciki naki ya fi haka." "ke dai yi shiru tawa". Hajiya Rukayya ta ce gami da dora yatsanta a baki "Ina so mu yi a hankali ne idan yanzu mu ka ce za mu yi mai gaba daya, ba makawa sai na shiga zargi da tuhuma kuma zai yi wuya na kubuta, amma idan mu ka dauke su daya bayan daya, sai ki ji shiru kamar an shuka dusa, babu wani dan iska da zai kalle ni, balle har ya zarge ni." "E to, ke ma kin yi tunani. "Baraka ta ce sannan ta daga yatsanta manuni, ta yi wa Hajiya Rukayya nuni da wata yar karkatacciyar bishiya da ke gabansu kadan, "Idan kin isa ga bishiyar can sai ki tsaya, mun iso gidan." Hajiya Rukayya ta gyada kai ba tare da ta ce komai ba, sannan ta ce, "Da ma yanzu na ke shirin tambayar ki ganin cewa muna nisa cikin wannan uban daji." Ta daka mata harara, "Ke kuwa akwai ki da tsoro Rukayya. Ina wani daji a nan? Ai yanzu babu dajin, ba ki ga har gidaje sun fara yawaita a cikin sa ba. Tab! Da a ce yan shekarun baya ne ki ka zo, da ba za ki kira wajen da daji ba yanzu." "Allah kawar?" Hajiya Rukayya ta ce da mamaki lokaci guda kuma ta na kara nazarin dajin. Dajin ya na da fadi da tsawo, sannan akwai yar duhuwa duk da cewa dai akwai yan gidaje tsilla- tsilla. "Ina, ai yanzu ina dajin ya ke." Baraka ta ce cikin murmushi bayan sun mayar da murafen motar sun rufe. Ta dubi Hajiya Rukayya ta yi kasa-kasa da murya, cikin rada-rada ta ce, "Sai ki yi shiri, kuma ki iya bakinki, ki san abin da za ki ce don nan mun zo wurin da ba a shiririta." "To, an gama...kar ki ji komai." Hajiya Rukayya ta amsa a tsorace, ita ma cikin rada bayan ta dafe kirjinta, alamun tsoro karara a fuskarta. A lokaci guda kuma ga rashin mamakinta sai ta ji zuciyarta ta soma harbawa, domin ita tun da ta ke ba ta taba ganin daji irin wannan ba a fili, sai dai ko a akwatin talabijin. Cikin fargabar da matsananciyar bugun zuciya ta dafawa Baraka baya su ka nufi dan durkushasshen gidan. Kadan ya rage fitsari ya kufce ma ta sa'ar da ta taka wasu busassun ganyaryaki su ka bada wani amo. Turus su ka ja su ka tsaya cak kamar dawakan da aka ja wa linzami. Da sauri su ka fara waige- waige kamar barayi sakamakon tsawar da su ka ji an yi mu su kamar daga sama yayin da su ka shiga gidan. "Ku tsaya nan, kar ku kuskura ku kuma takawa, idan ba haka ba fuskokinku za su koma keya, mutanen banza!" muryar da har yanzu su ka kasa ganin mai ita ta ci gaba da gargadin su. Tsananin tsoro da fargaba ya sa su ka soma tsuma kamar wadanda ake kada wa gangi. Nan da nan dakakkiyar zuciyar da Baraka ke tunkaho da ita ta bi ruwa. Karar sukuwar dokin da su ka ji daga bayansu ya sa su juyawa lokaci guda, kana da gagawa su ka tsuguna sakamakon ziyarar da wani kakkarfan haske ya yi w idanunsu. Sannu a hankali sai su ka fara ganin wata irin halitta a gabansu, wadda ba za su iya tantance wa zuciyarsu fasalinta ba. Abu guda da su ka fi lura da shi sosai ga halittar shi ne, ta fi kama da dodon da su ka sha ji a tatsuniya fiye da komai. Halittar ta fashe da wata irin shaidaniyar dariya, a hankali-a hankali kuma sai ta soma sauya kama, babu jimawa sai ta dawo siffar mutum sosai. Mutumin da ya maye gurbin halittar baki ne kato, sanye a jikinsa wasu bakaken kaya ne masu ratsin ja. Ya kuma fashewa da dariya tsawon lokaci, sannan ya soma da duban su ya na hura hancinsa mai kama da begila. Kusan minti guda ya yi ya na duban su, daga bisani ya ce da wata budaddiyar murya, "Kai mutanen banza. Shagalallu, bukatar da ku ka zo mini da ita mai sauki ce, ba kuma na bukatar ku sanar da ni komai game da al'amarin domin tuni dan marayan aljanu ya kawo min labarinku." Ya yi shiru ya na wani gurnani mai ban tsoro. Su ka yi ajiyar zuciya lokaci guda kamar wadanda aka watsa wa sassanyan ruwa, cikin mamaki su ka fara satar kallon junan su. "Lallai matsalar ki." Ya nuna Hajiya Rukayya, "Bai wuce ta kishiyarki da danta ba, me ki ke so a yi mu su?" Da tsawa ya bukata. Tsawon lokaci su ka dauka ba su amsa ba saboda tsananin tsoro. Sai daga bisani Baraka ta zura hannu a sace ta zunguri Hajiya Rukayya, cikin rada ta ce, "Ki fada masa abin da ya kawo mu." Ba ta yi gardama ba. Take ta sanar da shi bukatarta ta son a fara kawar ma ta da mujahid. Bokan ya tuntsure da dariya, kana ya yi wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, "Tabbas kin zo da al'amari mafi sauki a gare ni, kuma karamin abu wanda ba ni ya kamata na yi shi ba saboda saukin sa, duk da cewa dai ke mai wahala ne a gare ki matukar ki ka kuskure wa abin da zan umarce ki." ya saurara ya na zare idanu. Hajiya Rukayya ta dafe kirji jin abin da ya ce. "Hajiya". Ya dawo da hankalinta gare shi cikin murya mai tsoratarwa. "Dole ki yi taka-tsan-tsan da abin da zan gaya miki tun kafin na sanar da ke, domin ko ya ya ki ka kurkure na hango miki nadama a rayuwarki." Ya yi shiru kana ya ci gaba da dariya. Su kuwa babu abin da su ke yi sai kyarma. "Hajiya" ya kuma kiran sunanta, wannan karon muryar ta fi ta baya tsoratar wa, "Matso nan na sanar da ke." Ya miko ma ta hannunsa. Ta juya da sauri ta dubi Baraka a tsorace. Kafin ta ce wani abu Baraka ta ce, "Ki matsa mana, kar ki fa bata ma sa lokaci." Ita ma a tsorace ta yi maganar. Take ta ji wani abu mai kama da kwallon kafa ya taso daga cikinta zuwa wuyanta. Ba don ta yarda Baraka na kaunar ta ba, da sai ta ce ba ta da babbar makiyiya irin ta, don a iya tunaninta babu wanda zai ce ta matsa kusa da wannan Boka sai makiyinta. Babu yadda ta iya, haka ta matsa kusa da Bokan a hankali kamar wadda ke rabar wuta. Wani wari ne ya fara dukan hancinta daidai lokacin da ya miko dogon bakinsa fa kunnenta. Duk da cewa abin da ya ke fada wani abu ne da ta jima ta na neman sa, hakan bai hana ta jin kamar za ta amayar da kayan cikinta ba, saboda tsananin warin bakinsa "Rike wannan!" Ya ce da kaushin muryarsa bayan ya gama yi mata radar. *** Da alama tafkeken ruwan saman da aka kusan kwana ana tafkawa a daren na jiya, kamar da bakin kwarya, shi ya haifar da wadatacciyar iska, iskar da ke kadawa fil-fil-fil babu alamar tsagaitawa. Iskar za ta fi gamsar da mutum idan har aka yi sa'a ya yi wanka, kamar yadda wasu su ke hasashe. To amma kuma ga mamakin wasu tsiraru daga cikin mutanen da ke mantawa da kudurar Ubangiji Madaukaki, korafi da mamakin ruwan su ka rika yi su na cewa, wai kasa ta tsotse makekan ruwan da aka maka. Hakan ya haifar da rabuwa a tsakanin su, yayin da wasun su ke cewa, meyiwa kasar ta tsotse ruwan ne saboda jimawa da aka yi ba a samu ruwan ba. To, ko ma dai mene ne, Allah shi ne ya saukar da ruwan, kuma shi ya kaddara kasar ta tsotse shi kasancewar sa Mai yin yadda ya so. A daidai wannan lokaci da iskar ke ci gaba da filfilwa, direba Lukman, direban gidan Alhaji Basiru na daya daga cikin mutanen da ke jin dadin ta, duk kuwa da cewa kwance ya ke a daki abinsa ya na ta sake-saken abin da ka je ya zo. Sannu a hankali ya yi mika akan figaggiyar katifarsa mai kama da takkaken silifas, sannan ya yi salati ta cikin iskar hammar da ke fita daga bakinsa. Daga kwance ya langwabar da kansa gefe guda, ya kai dubansa ga fuskar agogon da ke makalr a jikin bango. Ya yi tsaki ganin har zuwa lokacin takwas ba ta yi ba. Ya kuma dauke kansa a hankali daga duban agogon zuwa ga rufin dakin kamar mai kidayar hudojin da ke jikin kwanon, lokaci guda kuma tunani da mamakin kiran da Hajiya Rukayya ta yi masa a yammacin jiya su ka lullube masa zuciya. "Lukman na kira ka ne saboda na shaida maka cewa gobe ba na so ka zo kai yara makaranta..ni zan kai su. Sai dai ina so ya zama kai za ka dawo da su. Amma fa ka sani hakan ba ya na nufin kullum ba ne, daga gobe shi kenan" Maganar da Hajiya Rukayya ta fada masa a jiyan ta ci gaba da kewaya zuciyarsa. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 2 Posted by ANaM Dorayi on 08:18 AM, 29-May-15 "To, mene ne dalilin Hajiya na yin haka?" Tambayar da ya ke yi wa kansa kenan a duk sa'ar da ya tuno da maganar, to amma har zuwa yanzu ya rasa samun amsa. A hankali ya dogara hannunsa biyu ya tashi zaune a karo na farko tun lokacin da ya kwanta bayan ya dawo daga sallar Asuba. Abu guda da ya fi amincewa da shi a zuciyarsa shi ne, ba banza Hajiya Rukayya ta shirya hakan ba. To idan kuwa hakan ne babu shakka ya kwadaita da ya san dalili. "To, a ina zan san dalilin?" Wannan karon da sauri ya furta kuma a fili. Nan da nan sai ya fara zargin kansa da yin Allah wadai, da ya kasa tambayar ta dalili a jiyan. "Gaskiya na yi sakaci, tun a jiya ya kamata na tambaye ta dalilin ta na..." Tunaninsa ya katse da ya tuno da abin arzikin da ta yi masa a jiyan. Ya laluba aljihun gaban rigarsa da sauri kamar mai yin rige-rige da wani. Har yanzu kudin na nan. "Ga wannan ka karya kumallo da safe a maimakon wanda ka ke yi anan." ya tuna abin da ta ce da shi lokacin da ta miko masa kudin. "Har dubu daya Hajiya?" Ya tuna abin da ya ce da ita lokacin da ya karba ya kirga. Abin da ya riga ya sani ne tun farkon daukarsa aiki a gidan, kyautar Hajiya Rukayya ba ta wuce Naira Hamsin, a ta yi yawa dari. "Kai gaskiya da walakin." ya kara furtawa a fili ya na duban kudin. Bayan tsawon lokaci ya na duban su ya mayar aljihu, sannan ya kuma komawa ya kwanta ya na fadin, "Bari na jira lokacin da ta ba ni ya cika na ga abin da ya samu a gidan." Ya ja tsohon mayafinsa mai kama da matacin koko ya rufa. A can cikin zuciyarsa ya na Allah-Allah karfe daya ta yi. Da kyar da curewa guri guda kamar kunkuru mayafin ya ishe shi. *** Karfe takwas daidai agogon da ke makale jikin bango cikin makeken falon ya saki wani daddadan kara, karan da ya ja hankalin Zainab da yaran guda uku da ke cikin falon zuwa fare shi. Yaran ba wasu ba ne, Mujahid ne danta da Hauwa'u da Sailuba, 'yayan Hajiya Rukayya. Yanzu kasan sa'a guda kenan su ka share su na zaman jiran zuwan direba Lukman, don ya kai su makaranta, amma shiru ka ke ji kamar an aika bawa garinsu. Wannan al'amarin ya fi cusa zainab cikin damuwa. Al'adarta idan ta yi wa Mujahid wanka, ba ta iya yin komai sai ta ga Lukman ya zo ya tafi da su makaranta, wasu ranakun ma kafin ta gama shirya shi ya ke zuwa, amma sabanin kullum yau ga shi ta gama kammala masa komai, sama da sa'a guda bai zo ba. "To, mene ne ya hana shi zuwa?" Abin da ta ke yawan tambayar kanta kenan, amma ta kasa gane dalilin. Abu guda dai da ta fi yarda da shi shi ne, koma dai mene ne ya hana direban zuwa to ya na da karfi. Cikin wannan hali na damuwa da Zainab ke ciki Hajiya Rukayya ta shigo falon da sauri kamar wadda aka biyo a guje. "Me ya faru har yanzu ba ku tafi makaranta ba?" Wannan ita ce maganar da ta fara fita daga bakinta a maimakon sallama. "Wallahi har yanzu direban ne bai zo ba, ga shi kuma har sun yi latti." Zainab ta amsa ma ta cikin girmamawa, duk da cewa ba ita ta tambaya ba. "To, ina ruwanki? Ke na tambaya ko kuwa ya ya, Zakakura?" Zainab ta kada kai, "Allah ya huci zuciyarki, da ma gani na yi kin yi tambaya kuma duk cikin su babu wanda ya amsa, shi ya sa." Hajiya Rukayya ta kuma doka ma ta harara, "Sannu mai baki, su kuma 'yayan nawa ina ki ka kai min bakin nasu? Ko ki na so ki danganta min da wannan dolon yaron naki, wawa marar baki?" Ta juya ta naduban Mujahid a wulakance. Zainab ta cira kai ta dube ta, makale a fatar bakinta wani dan murmushi ne da Hausawa ke yiwa lakabi da yake, "To, don Allah ki yi hakuri, na ji na yi miki laifi, amma surutun ya isa haka..." "Bai isa ba!" Ta katse ta, "Na ce bai isa ba!" Ta tattara hankalinta gare ta, kana ta dora hannu a kirju, "Ni ki ke cewa surutun ya isa haka? Ni ce ma mai surutu?" Shiru ba amsa daga Zainab. Hajiya ta kwashe wata irin dariya da ta tuno da shirinta da ke a kasa, "Babu komai, kin susa dainawa." Ta ce a ranta. A fili kuma sai ta ce, "Na ga alama wuyanki ya yi kauri yarinyar nan." Ta tsagaita da dariya ta shiga gyada kai, "Amma ba komai, ci gaba za ki kwashi kashinki a hannu nan ba da jimawa ba." Ta juya ga yaran, "Ku tashi mu tafi ni na kai ku. Shi kuma Lukman idan ya zo ya fada mini dalilin kin zuwan nasa." Hauwa'u da Sailuba su ka mike kamar ba sa so, fuskokinsu cike da damuwa. Duk da cewa kananan yara ne da ba su haura shekaru tara- tara ba kasancewarsu an haife su yan biyu, su na matukar nuna damuwa da abin da mahaifiyarsu ke yi wa Zainba din, wasu lokutan ma har hakuri su ke bawa Zainab din idan mahaifiyarsu rufe ta da fada. Su ka rufa ma ta baya. Daf da za su fice daga falon ne ta juyo ta dubi Mujahid da har yanzu ke zaune kusa da mahaifiyarsa, "Kai kuma algungumi ba za taso mu tafi ba, ka makale a jikin uwarka ka na duban mutane dai-dai?" lokacin da suka shiga makarantar tuni dalibai sun jima da shiga azuzuwa, wasu ma har sun fara kara tu, amma duk da haka bai hana Hajiya Rukayya tsayawa wani dan madaidaicin shagon sayar da kayan tsotse-tsotse da lashe-lashen dake cikin makarantar ba. "Hajiya Na manta ban tambaye ki guda nawa ba". A wannan karon kafin ya dafa motar ya fada. Ta yi murmushi, "Ba mu biskit din guda uku, alewar kuma guda biyu." Ya so ya ce ma ta ta yi kuskuren fadar alewa biyu a maimakon uku ganin yaran su uku ne, amma sai ya kyale, sai da ya je ya kawo, sannan ya yi ma ta abin da ya kira wo da tuni, "Hajiya kin manta kin ce alewa biyu na ga yaran su uku..." "Ka ga saurara." Ta katse shi, "Ban ce ma na manta ba, kai dai nawa ne kudinka?" Bai ji haushi sosai ba don ya san shi ne ya yi shisshigi. "Naira dari da hamshin." ya amsa daidai lokacin da ya mika ma ta. "Ungo." ta miko masa sabuwar Naira dari biyu ko kari babu bayan ta karba. Sannan ta juya ga yaran da ke zaune bayan motar ta fara raba mu su. Duk da cewa saurayin ya sa hannu a aljihu ya na kokarin dauko ma ta canji, hakan bai hana shi jifan tsuntsu biyu da dutse guda ba, don kuwa da wutsiyar idonsa ya na kallon yadda ta ke rabon, ya san dai dole daya zai rasa, kuma za a bukaci ya kawo. A kan Mujahid alewar ta kare bayan ta gama raba mu su biskit din. Mujahid ya dube ta, ya dubi yan uwansa ganin alewar da ta kare shi bai samu ba, alamun damuwa gauraye da na kuka su ka bayyana a fuskarsa. "Yi hakuri Mujahid, kai bari na ba ka taka alewar mai dadi, ka ji." Ta ce ta nayin wani irin murmushi, sannan ta bude. 'yar karamar jakarta da ke ajiye gaban mota, ta dauko alewar, "Rike, da kyau, kar ka kuskura ka ba kowa. Kowa ya sha tasa. Kun ji ko?" Ta gargade su. Su ka gyada kawunansu cikin gamsuwa kuma hakan ne ya sa saurayin ya dauke kansa cikin fitar da rai cewa zai sake samun ciniki. "Ga canjinki Hajiya." Ya ce bayan ya gama kirgawa. "jeka ka rike" Ta ce da shi cikin kosawa, kana ta ja motar ta yi gaba. Saurayin ya bi motar da kallo sannan ya kece da dariya a fili ya ce "Kai kudi ma dai ba su da kama...dubi wannan mummunar mata haka kamar an sassako cikin wannan zundumemiyar mota. *** Sau daya kawai ya latsa hon din motar babbar kofar gidan ta bude. Cikin hanzari direba Lukman ya shige da motar cikin yalwatacciyar farfajiyar. Ba yanzu ya soma hanzarin ba, tun lokacin da ya bar gida ya nufi makaranta da zummar dauko yaran ya ke ta hanzari shi ya sa yanzu da ya danna hon din sau daya ya ga kofar ta bude ya ji dadi a ransa, har ma zuci ya shiga yabawa kulawar Malam Bukar akan aikinsa, duk kuwa da cewa wani lokacin sai ya yi hon sau fiye da goma bai bude ba ya na cen ya na ta gyangyadinsa. Kamar yadda ya saba, cikin sauri ya karbi jakunkunan da ke hannun su Hauwa'u bayan ya mayar da murafen motar ya rufe. Kai tsaye ya wuce cikin gidan, yaran su ka rufa masa baya. Duk wannan sauri da ya ke yi, ya na yin sa ne don kyautata zatonsa na samun bakon abu, musamman saboda hana shi zuwa gidan da Hajiyya Rukayya ta yi a safiyar yau. Hanzarinsa ne ya ragu lokacin da su ka yi daf da falon ya ji ana hira da shewa a ciki. Sallama ya fara kafin ya daga labulen. "Wa'alaikas salam." Muryar matan biyu ta amsa sallamar daga cikin falon. Zainab ce da wata kawarta da ta kawo ma ta ziyara, mai suna Barista Hannatu Muhmud. Barista Hannatu kawar Zainab ce tun su na makaratar sakandire. Sun shaku da juna matuka, har ya zamto duk inda su ka nufa za ka ji ana ce mu

Please Login or Register in order to submit comment