Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah dan ba mu wuri mana." Ta yi murmushi "To". Ta mike tsaye ita ma ta fice daga falon, sashikan zuciyarta na ta fadar ra'ayoyinsu game da hakan. Wasu na cewa "Shi kenan asirinki ya tonu." yayin da wasu kuma ke cewa "Kar ki yi wata fargaba, Lukman ba zai bayar da kafa ba. Meyen kudi ne fa!" Ganin ta fice Sifeto Habibu ya tattara hankalinsa ga Lukman. Cikin duba na kwarewa ya ce. "Malam Lukman kai ne direban gidan nan ko?" ya gyada kai gami da cewa "Ni ne yallabai" "Kai kadai ne direban ko da wani?" "A'a, ni kadai ne yallabai, ba wani". "To me ya sa jiya ba ka zo ka kai su ba?" Tambayar ta yi ma sa bazata hakan ne ma ya sa ya amsa cikin rawar baki. "Eh, ba ni...da la...lafiya, yallabai...mura ce ke damu...na, shi ya sa ban...ban zo ba.." Sifeto Habibu ya jinjina kai, "Wannan shi ne kawai ya hana ka zuwa." "Yallabai shi ne." "To waye ya je ya dauko su, ma'ana bayan an tashe su?" "Ni ne?" Ya dafa kirjinsa. "Lokacin murar taka ta warke ne?" "A'a, na dai samu sauki." Sifeto Habibu ya shafi dumbujejen gashin bakinsa cikin kokarinsa na son sauya hirar. "Lukman sa'ar da ka dauko yaran nan ko ka ga wani abu a tare da su. Abin nufi a hannunsu wanda ya danganci na sha?" Ya girgiza kai "A'a gaskiya ban ga komai ba." Yanzu ya dan nutsu "Sai dai ko jukukkunansu." "Ban da wannan Lukman. Mun gode." "Yallabai ni ne da godiya." Cewar Lukman. Ya mike ya fice daga falon saboda umarnin Sifeto Habibu na sa shi ya kirawo ma sa Hajiyar. Ba a jima ba su ka dawo tare. Sifeto Habibu ya dube ta bayan ta zauna. "Hajiya yanzu za mu tafi domin mu tattara duk abin da mu ka samu, in ya so daga yanzu zuwa daren yau za ki ji daga gare mu. "Mun gode". "Mu ne da godiya."Hajiya Rukayya ta ce. Su ka mike su ka nufi kofar ficewa, har sun kai ga kofar Sifeto Habibu ya waigo. "Ko da ya ke Hajiya." Ya fara takowa zuwa ciki "Za mu iya cewa yanzu mun kammala bincikenmu. Abin da ya kamata ki sani shi ne, za mu kai ku kotu domin warware wannan matsala a can." Ya taya ya na duban ta sa'ar da ya kai ga tsakiyar falon "Zan so na ba ki shawara idan ki na da lauya ki sanar da shi domin za mu yi komai daga yau zuwa kwana shida mu ga an kira ku." Gabanta ne ya fara bugawa kafin ta yi fari da kwayar idanunta, cikin karfin hali ta ce. "To...to..yallabai..za a sanar da shi." Sifeto Habibu ya juya ya nufi kofar inda yan uwansa ke tsaye su na jiransa, su ka fice. Hajiya Rukayya da Lukman su ka numfasa, numfasawa me nauyi bayan fitar yan sandan. "Yau na shiga uku Lukman, wai ka ji kotu za a kai mu." Hajiya Rukayya ta fada hannunta a dafe da kirjinta. Lukman da ke zaune can gefe ya zuba tagumi ya cira kai ya dube ta. Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa ganin Hajiya Rukayya ta rikice, "Hajiya mene ne na damuwa cikin wannan al'amari? Ke da kike da gaskiya kuma aka cuceki. Me ye cuta? Aka kashe miki yaya har biyu. Haba! Wannan ai kamata ya yi ki fi kowa farin ciki kuma..." "Ba haka bane Lukman ka san fa kotu da bin diddigi." "Ammaai daga karshe gaskiya ce take nasara ko?" Das! Sai da gabanta ya fadi kafin ta ce. "Eh, ha...ka ne, amma ni da an yafe.." "Waye zai yafe Hajiya ai ko ke kin yafe yan sandan nan ba za su yafe ba. Saboda haka kawai ki saki jikinki a karbo miki hakkinki." Ta nisa kana ta sa hannu ta share gumin da ya soma jika ma ta goshi. A lokaci guda kuma sai ta fara tunanin zuwan Baraka kawarta sa'ar da ta isketa a daki zaune har kawo sa'ar da su ka dawo daga gidan boka. Ta na tafe har lokacin da Mujahid ya iske ta a dakin girki ya sanar da ita farkon faruwar mummunan ala'amarin, kawo lokacin da likita ya ce sun mutu zuwa yanzu da yan sandan su ka gama bincike su ka ce wai za su mika kotu daga nan zuwa kwana shida. Nan da nan zuciyarta ta shiga hadawa da tantance riba da rashinta a cikin al'amarin. Cikin kankanin lokaci sai ta gano cewa babu wata riba da aka samu ko alama, domin kuwa na farko Wanda fa su ka yi domin shi (Dan kishiyarta Mujahid) na nan da ransa yanzu haka. Na biyu yayan ta biyu duka sun mutu, su na da gado kuwa? Tun da an ce shi Alhaji Basiru da sauran numfashinsa. Abu na uku wanda kuma shi ne uwa uba wai za aje kotu, gurin da ta tabbatar idan ta shiga asirinta ya gama tonuwa, daga ya tonu kuma ba ita ba sauran rayuwa domin ta san zai yi wuya ta tsira. Nan da nan sai ta ji zuciyarta ta shiga kogin nadama da dana-sani, a fage daya kuma da zargi gami da la'antar matar da ta sa ta a wannan tafarki, Baraka. Ta kuma nisawa da karfi a karo na biyu, take sai ta ji kwalla ta soma kwararowa daga idanunta. Lukman da bai san me take tunani ba sai ya ji ya kagauta ta gama abin da ta ke yi shi ta cika masa sauran kudinsa ya yi tafiyarsa domin ya yi alkawari a zuciyarsa gari na wayewa zai yiwa kasuwar kantin kwari tsinke domin samo yan atamfofin da zai ganganda ya aika gidan yar bazawararsa Bintoto, shi fa aure ya ke so. Shi ya sa ya kasa bata dama ta ci gaba da tunanin ya ce. "Hajiya, ni ina ga kawai ki yi hakuri ki dake kotu za ta kwatar miki hakki. Yanzu abu guda da nake ganin ya dace ki yi kawai ki nemi lauya.." sai yanzu ta ji magana domin ko babu komai dai bata da wani zabi da ya wuce ta binciko lauya da zai tsaya ma ta, don haka da Lukman ya tabo wannan bangaren sai ta cira kai ta dube shi. Murya a shake ta ce "Lukman a ina kake ganin zan samu lauyan... Ka san fa ni ban san yadda zan yi ba." Ya ji dadi ya ji ta bude baki ta yi magana domin ya san in dai za ta ci gaba da magana da shi to sauran kudin sa ma za su fito. Ya sosa kansa "Hajiya ai wannan mai sauki ne, ko anan unguwarmu ma akwai wani da na sani..shi ma lauya ne." Ta ji dadin hakan da ya fada. Ta sa gefen gyalenta ta goge hawayen dake zuba daga idanunta. "Lukman! Kana nufin anan unguwar ku akwai lauya?" Ya gyda kai "Kwarai kuwa Hajiya makwabcinmu ne ma." "To yanzu ya za a yi mu gana?" Ya sunkuyar da kansa cikin yunkurinsa na son tuno lokacin da ya san Barista Garba Shehu ke zama a gida. Ya cira kai ya dube ya bayan ya tuno, "Hajiya na kan yawan ganinsa a gida da yamma...kai, ko yau ma idan aka yi sa'a za a iya samunsa bayan La'asar." Ta numfasa cikin gamsuwa "To yanzu nan zan ce ya zo ko ni ya kamata na neme..." "A'a Hajiya ai zai fi kyautatuwa ki neme shi." Ya katse ta. "Shi wanda ka ke nema a wajensa ai samunsa ya dace ka je ka yi." "Haka ne!" Ta ambata ta na gyada kai, "To yanzu yau din ya dace mu je mu gan shi ko?" "Kwarai kuwa ai da safiya ake kama fara." "To shi kenan". Ta mike tsaye "Idan anyi sallar la'asar ka zo ka kai ni wajensa, kuma ina zuwa". Ta nufi wata ko far dake manne cikin tafkeken falon. Ya so ya ce ma ta dubu biyar dinsa, amma ganin tana sauri kuma ta ce masa ta na zuwa sai ya kyaleta. Ba ta jima ba ta fito ta iso daidai kansa ta mika masa. "Ga cikon kudin ka Lukman. Dan Allah kar ka bata lokaci hudun na yi ka zo mu je." "An gama Hajiya." Ya ambata sa'ar da ya damki kudin, tamkar mai kamun fara. "Da zarar lokaci ya yi za ki ganni". Ya mike "Ko yanzu ma idan na koma gida da zarar kin gan ni na dawo to fa ya na nan sai kawai ki shirya mu je." "Yauwa Lukman don Allah ka kokarta". "To" Har ya je bakin kofa da kudin a hannu sai ya tuna take ya tsaya kamar an kira sunansa daga baya, ya cusa kudin a aljihunsa ya yin da zuciyarsa ke cewa. "Lallai komai taurin ruwa in an jefa dutse sai ya lume a ciki. Ka duba tsumulmula irin ta Hajiya amma da yake Allah ya kwata min. Gashi zan yi arziki ta dalilinta..." Da haka ya fice daga falon." *** SABANIN dazu da ta bar ofishin ASP ba kowa ta je ta ga kawarta, yanzu ofishin akwai mutane a ciki. Wannan ne ya sa ta samu waje ta zauna a falon ofishin ta najiran su fito ta shiga, zaman da ya ci gaba da tariyo ma ta faruwar dagulallan al'amarin garai-garai kamar a allon sinima. Shakka babu kallo daya za ka yi ma ta tabbatar cewa ta na cikin halin matsananciyar damuwar da ke bukatar tallafin gaggawa, jifa-jifa abin da kawarta ta ke yawan ambata ne yayin da ta je wajen ta yanzu, ke fadowa cikin zuciyarta. -Wallahi summa tallahi Hannatu ban san komai game da wannan alewa ba har sa'ar dana dauko ta na kawo...ba ni na samar da alewar ba...wallahi ba ni na samar da ita ba." Kuka ne ke biyo baya, kukan da ke sa zuciya kuka. Ta numfasa kamar dai yadda ta ke yi duk lokacin da ta tuno wannan kalami mai karya zuciya, wanda a wani sashen zuciyarta kuma shi ne ke sawa ta kara jin kwarin guiwa akan kudirinta na kare ta da kwato ta daga wannan kangi. To a daidai lokacin da ta numfasan ne mutanen da ke cikin ofishin (wanda su take jira su fito ta shiga ciki) su ka fito. Da gaggawa ta mike ta cusa kai cikin ofishin. "A'a...! Barista har kin dawo?" Tun kafin ta gama mayar da kofa ASP ya ce hakan, ya na duban ta cikin bayyanar da wani malalacin murmushi. Ita ma ta mayar masa da murmushin bayan ta rufe kofar, sai dai babu bambanci da irin wanda ya yi mata, "Eh, yallabai na dawo" Ta ce a sanyaye. "Sannu da zuwa...Bismillah.." Ya ba ta umarnin zama. "Yallabai na je na gan ta." Ta ce bayan ta zauna. "To amma ina neman wata alfarma." Ya tsayar da idanunsa ga kallon ta bayan ya dan tsuke fuskarsa. "Wace alfarma kuma ki ke nema bayan wadda ki ka nema ta, a kai ku kotu?" Ta nisa, "Ban da wannan yallabai don ita dama ba alfarma ba ce, tunda kuwa wajibi ne ku kai kotu ko da ban nema ba, sabo..." "To na ji yanzu wace alfarmar ki ke nema?" Ya katse ta, a kagauce gami da tambaya don kuwa ya san gaskiya ne abin da ta fada ko ba ta nema ba tilas a kai maganar kotu. Ta dan yi murmushi, "Haba yallabai mene ne na harzuka, sai ka ce wadda na ce ka sake ta?" Ya mayar da bayansa ga majinginar kujerar ya jingina, "To ai ke ce na ji ki na so ki yi min tsari kamar wadda aka hau kotu". "O.k, dama su lauyoyi tsari suke yi?" Ta ce bayan ta kada kai gefe. "Kin ga ni ban ce ba." ya daga hannu, "Kar ki kai ni gaba." Su ka yi dariya tare. "Don Allah wace bukata ce, fadi, don ina da aiki mai yawan gaske a gabana, kin ga bayan fitarki ma an kawo min rahoton wani bincike da aka yi dazu a can gidan, ina so a hada shi a shigar kotu. Idan so samu ne a ce Litinin kun hallara a kotun." Ta sunkuyar da kai, jim kadan ta dago ta dube shi, "Yallabai akwai halin a bayar da belinta kafin zuwa kotun?" Ya girgiza kai, "No! No!! No!! This is non bailable offence Hannatu (a!a!!a!!! Wannan ba laifin da ake ba da beli ba ne Hannatu) Abu guda kawai da zai sa a sake ta shi ne, a yi shari'a a tabbatar ba ta da laifi. Idan ta wanku daga abin da ake zargin ta, to sai kotu ta sake ta". Barista Hannatu ta kuma dukar da kai. Ba ta da ta cewa, domin ta san hukuncin kenan. Daga karshe haka ta hakura ta baro hedkwatar yan sandan da zummar zuwa ta fara bincike akan dan abin da ta tattara da wanda ta samu a bakin Mujahid kafin ranar Litinin, duk da cewa ta yi-ta yi ya bi ta ya ki yarda. *** Karfe hudu da kwata na yamma Lukman direba ya daidaita tsayuwar motar kirar "KIA" a kofar gidan lauya mai zaman kansa Barista Garba shehu, kwararre, gogagge kuma fitaccen lauyan da lauyoyi ke shayin karawa dashi. Cikin sauri ya fito bayan ya kashe motar, ya budewa Hajiya Rukayya kofa. Sannu a hankali kamar mai cikin wata tara ta fito. Ya mayar da murfin a hankali ya rufe. "Hajiya, nan ne gidan!" Ya yi ma ta nuni da dan madidaicin gidan mai dauke da farin fenti, da su ke tsaye gabansa. Gidan ba ya cikin sahun gidajen kece raini idan har za a tsunduma shi cikin jerin gidajen ma su hannu da shuni. To amma duk da haka shi ma ba laifi don ko ba komai dai shafe ya ke da sabon fentin farar kasa. "To yanzu ya za a yi mu tabbatar ya na ciki?" Hajiya Rukayya ce ta bukata. Lukman ya yi yan waige-waigenshi, "Kin ga wani lokaci fa, a nan kofar gida ma za ki gan shi, amma..." Wani yaro ya hango shi ya sa maganar tasa ta katse. "Kai! Zo mana!" Ya ce da yaron bayan ya yafito shi da hannu. Bai yi gardama ba ya tunkaro su. "Hajiya bari mu tura yaron nan ya kira shi." Ya ce bayan yaron ya iso gare su. Ba ta yi magana ba, gyada kai kawai ta yi. "Kai don Allah shiga nan gidan kace ana sallama da barista.." "Nan gidan?" yaron ya bukata ya na mai nuna gidan da yatsansa. "Eh, nan". Bai sake magana ba ya nufi gidan ya shiga, jim kadan ya fito. "Wai an ce ya na zuwa." Tun kafin ya iso wajen su ya fada. "Yauwa yaro, mun gode ka ji?" Lukman ya ce kana ya dubi Hajiya Rukayya, "Hajiya mu tsallaka daga kan dakalin ko?" Suka tsallaka. Daidai lokacin ne Barista Garba Shehu ya fito. Fari ne, ya na da yar kiba amma ba can ba, haka zalika shi ba dogo ba kuma shi ba gajere ba. Ya na da yawan fara'a daidai gwargwado. "A'a, Lukman kai ne kake sallama." Abin da ya fara fita daga bakinsa kenan. "Barista Garba Shehu!" Lukman ya ce gami da daga hannu cikin jinjina. Barista ya mika masa hannu su ka gaisa, kana ya duba Hajiya Rukayya da ke faman kallonsa tun sa'ar da ya fito, ya ce, Hajiya ina wuni?" Ta dan saki fuskarta kadan "Lafiya lau, ya gari, ya aiki?" "Lafiya Sumul Hajiya" ya amsa. "To madalla, sannu!" "yauwa sannu." Lukman ya dubi Barista bayan sun ida gaisuwar, "Barista wajen ka mu ka zo takanas ta kano." "Ni ko?" ya yi murmushi. "Kwarai kuwa." Ya gyada kai. "To ai ina ga zai fi kyautatuwa mu shiga daga ciki ko?" "Duk yadda ka ce." A wannan karon Hajiya Rukayya ce ta fada ta na murmushi. "Ina ga zai fi kyau...ku zo mu shiga daga ciki." Barista ya ce, sannan ya juya su ka dafa masa baya kamar jelar dawisu har cikin madaidaicin dakinsa. Dakin ba laifi kwarai da gaske. Daga kasa ya na shimfide da wani shudin kafet mai taushin gaske, ga wata tattausar katifa wadda a ka sa daga kusurwar yamma maso arewacin falon. Daga gabas maso kudancin falon kuwa wani dan teburi ne da ke daure da akwatin talabijin mai launi da bidiyo da kuma katuwar radiyo, rikoda. Daga samansu kadan an fasa bangon an zuro na'urar sanyaya ko dumama daki (Air Condition) duk ilahirin jikin bango kuwa zagaye ya ke da labule, hakan zai iya hana gane launin fentin da bangon ke dauke da shi. Sakale a sama wata kyakkyawar fanka ce ke ta faman aiki abin ta ba kakkautawa. Bayan sun zazzauna su ka kuma gaisawa. "Barista wasu yan matsaloli ne ke tafe damu." Lukman ya soma, "Shi ya sa ka ji na ce ma wajenka mu ka zo takanas." Barista ya gyada kai cikin saurare. "Ko da ya ke..." Lukman ya ci gaba bayan ya juya ga Hajiya Rukayya, "...wannan ita ce Hajiya Rukayya matar maigidana Alhaji Basiru, kuma ita ce ta kasance cikin wannan matsala. To da aka ce ana neman lauya, shi ne na shaida ma ta cewa akwai ka, saboda haka na yi ma ta jagora zuwa gare ka." Barista ya gyada kai cikin gamsuwa, "Wannan gaskiya ne. Hajiya wace irin matsala ce wannan?" Hajiya ta dube shi, cikin maraireta ta kwashe labarin abin da ya faru kaf na karya ta sheda masa. Barista ya jinjina kai bayan ta kawo karshe. Lallai ko shakka babu da alama shi ma abin ya ba shi mamaki. Domin sai da ya jima kansa a duke kana ya dago a hankali, "Hajiya sannu kin ji, Allah ya ji kansu ya kuma gafarta mu su." "Amin...!" Lukman ya amsa. Hajiya Rukayya kuwa tuni ta soma kuka. "Ki yi hakuri Hajiya, ki kwantar da hankalinki da yardar Allah zan tsaya tsayin daka akan wannan al'amari don ganin kin samu hakkinki." Ya dan tsahirta kana ya ci gaba, "Yanzu ina kanin mijin naki, da abokinsa?" Ta sa mayafi ta tsane hawayen dake zuba daga idanunta, cikin muryar kuka ta ce, "Suna can, asibi...ti, su na kula da Alhajin. "Wanne asibitin kenan?" Ya kuma bukata. "Asibitin lafiya jari." "Ok, a nan suke?" "Umn." ta gyada kai. "Shi kuma likitan da ya zo lokacin faruwara abin fa?" "Shi ma..acan ya ke". "Wato ita dai yanzu amaryar ta ki ta na tsare ko?" "Eh!" Ta amsa. "To mu na godiya Barista." Lukman ya ce sa'ar da su ka mike da zummar tafiya. Har bakin motar su ya raka su, su ka tashe ta su ka tafi. Hajiya na farin ciki ganin zata samu kariya a wani bangaren kuma ta na mamakin kankanta da karancin shekarun na lauyan da zai tsaya mata. *** A kokarin ta na ganin ta kubutar da kawarta daga cikin matsalar. Washe gari bayan ta gama kintsawa ta yi karin kumallo, ta fita ta nufi gidan Alhaji Basiru da zummar son ganawa da Lukman, a matsayin mutum na farko da ta ke son ta fara bincika. Lokacin da ta isa gidan, ta yi matukar sa'a da ta same shi zaune cikin harabar gidan, shi da maigadi Bukar. A gajarce su ka gaisa, kana Barista Hannatu ta bukata, "Don Allah ko Hajiya na ciki kuwa?" "A'a! Ba ta nan." Lukman ne ya amsa mata, "Ai ta na asibiti, tun dazu na kai ta." Hannatu ta gyada kai, "Ko kai ne Lukman?" Ta bukata ta na duban sa. "Eh, ba shakka ni ne." Ya tabbatar ya na jinjina kai. Ta yi ajiyar zuciya, "Ka ga kuwa ina son ganin ka." "Ni ko?" Ya dafa kirji. "Kwarai kuwa." Ta amsa masa. "Na taso kenan?" "Zan so hakan". Ta ce a takaice. Ya dubi Maigadi Bukar da ke taunar goro abinsa, "Malam Bukar ina zuwa" ya mike su ka dan kebe can gefe gindin wata kyakkyawar shukar fulawa mai yado. Ka sa jurewa ya yi bayan sun tsaya, kafin ta yi magana, yace, "Hajiya, na ce dai ko lafiya?" Ta tsaida kallon ta gare shi ta na murmushi, "Lukman ka gane ni ko?" "Sosai ma kuwa. Ba ke ce Hannatu Kawar amarya ba?" "Lallai kuwa, ko ka san abin da ya kawo ni?" "A'a, ina zan sani ba ki fada ba, ni da ba Allah- musuru ba?" Ya ce da wata irin tattausar murya. "Kana da gaskiya, na zo ne na yi ma ka wasu yan tambayoyi, a matsayinna na lauyar da za ta ba amaryar maigidanku kariya. Ka san za a kai su kotu ko?" Ya hadiyi yawu da kyar, "E...na..sani." Ya amsa cikin in-ina. Wannan ya biyo bayan kin jinin tambaya da ya yi a daidai wannan dan rukunin saboda ya san komai na iya faruwa tun da shi ma mai laifi ne. Kai! Idan ma ban da ya na tunanin idan aka je kotu Hajiya Rukayya ta yi nasara zai iya samun wani alkhairi daga gare ta, ai da tuni ya tsere kauyensy, (Gamadidi). Kafin ta kuma magana ya ce, "Me ki ke so ki tambaye ni?" Ta yi kasa-kasa da muryarta, "Dalilin rashin zuwanka kai yara makaranta shekaran jiya, na ke so na ji." Ya yi atishawa "Ai na jima ina amsa wannan tambayar. Ba ni da lafiya ne." "To ya a ka yi da rana kuma lokacin tashi ka je ka dauko su. Ka samu sauki ne?" "Na ji dama-dama lokacin." ya amsa da gyada kai. "Idan ka tashi daga aiki, abin nufi bayan ka dauko yara daga makaranta, kana tafiya da mota gida ne?" "A'a ya girgiza kai, "Ba na tafiya da ita duk a nan su ke kwana." "To a wannan rana ya aka yi ka tafi da mota gida. Ko ka san da ma za ka tashi da rashin lafiya? Kuma da rana za ka warke, shi ya sa ka tanade ta don kawai ka wuce daga can?" Tambayar ta kwarzanar masa zuciya don take launin fuskarsa ya sauya. Shiru ya yi cikin gaza amsawa. "Ya na ji ka yi shiru, ko ba amsa?" ya girgiza kai "Ba haka bane..." "To ya ya ne?" "Shi ne abin da nake so na tuno." Ta yi murmushi. "Ko na ba ka lokaci ka tuna?" "Da dai zai fi." Ba haka ya so ya ce ba, dole ce kawai ta sa shi fadar hakan da gudun tonawa Hajiya Rukayya asiri. Ta kuma yin murmushi, "To bari na baka dogon lokaci don ka tuna. Ni zan tafi." Ta motsa sahunta, ta yi taku biyu. Ya dube ta, "Sai yaushe kenan?" "Sai mun kuma haduwa." Ta bar shi nan tsaye ta nufi maigadi Bukar da tuni ya soma sana'ar tasa gyangyadi. "To Baba ni zan koma." Ta ce a tausashe. Ya cira kai firgit ya dube ta, "Uhum, yar Baba a sauka lafiya." Da a lokacin za a tambaye shi da wa ya yi magana, ba zai iya fada ba saboda gyangyadi da ya ci karfinsa. Bayan barinta gidan ba ta zame ko ina ba sai asibiti. Likita Idris shi ne na biyu cikin jerin mutanen da ta ke son ganawa da su, koda ya ke shi ba kamar sauran ba, wani taimako ta ke bukata daga gare shi. Ta taki sa'a kuwa, shi kadai ta iske a ofishin nasa ya na ta faman aikace-aikace. "Likita ya mai jikin?" Abin da ta fara fada kenan bayan sun gaisa. "Jiki da sauki Hannatu, ai koda yaushe ya na samun rangwame." "To, Allah ya kara sauki" "Ameen-ameen." Shiru ne ya dan gifta tsakaninsu. "Likita na zo ne don neman wani taimako gare ka, koda ya ke ya na da matukar fa'ida na sanar da kai matsayina cikin wannan al'amari bayan na amintaka ta da Zainab." Ta bude jakarta ta dauko wani kati na shaidar aiki (I.D Card) ta mika ma sa. Bai yi magana ba ya karba. Ya yi nazarinsa a hankali tun daga gaba har zuwa baya. Yanzu ya gane matsayin nata. Ya nisa, "Ga shi Hannatu." Ya mika ma ta. Ta sa hannu ta karba kana ta ci gaba da cewa, "Likita ina so na ba Zainab kariya a game da wannan badakala, shi ya sa na soma bibiyar al'amarin." "Wannan haka ya ke." Likita Idris ya ce ya

Please Login or Register in order to submit comment