Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai bayan da mujahid ya ce ya na da ita a aljihun wandonsa na makaranta." "Wto ya tabbata ke ki ka je da hannunki ki ka dauko Alewar ki ka kawo ko?" "E, ni na dauko." "Ya gyada kai," To, wane ne Mujahid." "Ga shi." Ta dafa kan Mujahid da ke zune kusa da ita shi ne dan naki?" "shi ne." Ta tabbatar. "Zo Mujahid." Sifeto ya ce ya na dubansa gami da mika masa hannu. "Tashi ka je". Zainab ta ce da shi ganuin ya na dubanta. Mujahid ya mike idanunsa fal da kwalla ya nufi Sifeto, tun kafin ya kai gare shi ya mika hannu ya rike shi. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 3 Posted by ANaM Dorayi on 08:22 AM, 29-May-15 "Yaro kai ne Mujahid?" "Uhm!" ya amsa a ciki gami da gyada kai, a lokaci guda kuma ya na waiwayen mahaifiyarsa. "Wace ce mamanka?" ya nuna Zainab. "Ka na makaranta?" "E, ina yi." A wannan karon ya bude baki. "A wacce makaranta ka ke?" "Sasif Model School". "Ajinka nawa?" "A Naziru tu (Nursery 2) na ke." Mujahid ya amsa. Lallai yanzu ya tabbatar mujahid ya na da wayo. To amma ya na so ya tabbatar saboda tambayar da ya ke son yi masa sai mai wayo sosai ne zai iya amsawa. "Ka iya turanci?" Ya bukata bayan ya saki murmushi. Ya gyada kai, "E, na iya". "Idan na yi maka tambaya za ka iya mayar min?" ya gayda kai ba tare da ya yi magana ba. "How old are you?" (Shekarunka nawa). "I am five years old." (Shekaruna biyar). Kusan ba wanda bai ba sha'awa ba, saboda yadda ya amsa turanci ba tare da rawar baki ba. Yanzu Sifeto Habibu ya samu tabbacin Mujahid na da wayo sosai, hakan ne ya ba shi damar shiga yi wa Mujahid tambayoyi kai tsaye, "Mujahid wane ne ya saya maka Alewa?" "Momi babba ce." "Wace ce Momi babba...wannan?" ya nuna Zainab. "A'a." Mujahid ya ce da girgiza kai, "Daya Momin." "Waccekenan?" "Momin yan biyu." Sifeto ya gyada kai, ya gane wadda Mujahid ya ke nufi, "To, a ina ta saya ma?" "A makaranta." "Yaushe?" "Un...un, gobe da safe." "Gobe da safe? Ko dai yau da safe?" Sifeto Habibu ya gyara masa. Ya san shirme ne na yaro. Kuma ya kwana da sanin cewa ba kowane yaro ne ke iya rike lissafin raneku ba. "Eh, yau da safe ne." Mujahid ya gyara. "A wajen Habu mai shago, na makarantarmu." "Ka tabbatar?" ya gyada kai. Sifeto Habibu ya juya ga su Alhaji Sambo, "Alhaji ina ita uwargidan ta ke, ko ta na asibitin?" "A'a, ta na cikin daki, ba ta jin dadi ne." "Assha! Allah ya sawake. A wane daki ta ke?" "Ta na dakinta, zo mu je." Alhaji Sambo ya gayya ce su bayan ya mike tsaye. Yan sandan su ka mike su ka dafa masa baya, su ka bar Alhaji Gali da Zainab da Mujahid a falon. Sa'ar da su ka isa dakin Hajiya Rukayya kwance su ka same ta kan gado ta na ta faman barci, amma na karya. Kafin shigowarsu idanunta biyu, amma jin motsinsu na nufo wa dakin ya sa ta rufe idanun nata kamar mai barci. A nata tunanin wannan
wata hikima ce da za ta kubutar da ita daga tuhumar yansandan, don gudun kar a gane ita ce sanadin afkuwar aika- aikar. Su ka dan tsaya a kanta, tsayuwa ta yan dakiku. Bayan kiran da Alhaji Sambo ya yi mata a kalla sau biyar, shiru babu ko motsi, sai Sifeto Habibu ya ce, "Kyale ta Alhaji mu koma falon." Babu wanda ya yi magana su ka juya su ka fice daga dakin. Su na shigowa su ka iske Doctor Nasir zaune ya na jiran su. "Ya ya Doctor, me ka gano?" Cewar Sifeto Habibu. Doctor Nasir ya mike tsaye, "Yallabai binciken da na yi na samu akwai guba mai hadarin gaske a jikin Alewar da su ka sha, wanda gubar na iya kashe mutum nan take. Idan kuma wasu halittu ne ba mutum ba, ba sai sun kai ga sha ba, ko shakar ta su ka yi za su iya mutuwa." Sifeto Habibu ya jinjina kai, "Yanzu dai ka gama kenan?" "E, na gama." Sifeto ya juya ga su Alhaji Sambo, "To, Alhaji a yanzu mun kammala wannan a matsayin rukuni na farko kafin mu dawo na biyu. Kuma kamar yadda doka ta tanada, za mu tafi da ita amaryar har zuwa lokacin da za mu kammala bincikenmu mu mika abin kotu." Zainab ta cira kai da sauri ta dube shi, "Yallabai me na yi?" "Ana zargin ke ce da hannunki ki ka dauko alewar da ta kashe wadannan yara." Kasa magana ta yi, kawai ta kifa kai ta shiga yin wani kuka na takaici, kukan da ka iya sa mai dakakkiyar zuciya taya ta. Amma duk wannan bai hana jami'an tsaron tafiya da ita ba, har da Mujahid ganin ya ki yarda a tafi da ita a bar shi. *** Kamar yadda ya zame masa sabo zuwa gidan karfe bakwai na safe domin kai yara makaranta, yau ma haka ne. To amma sabanin lokutan baya, yau ya riski mummunan labari da bai taba tsammani ba koda a mafarke-mafarken da ya sha yi a daren jiya. Tun da dai ya iso gidan ya ke zaune wajen maigadi Bukar wanda ya labarta masa faruwar mummunan abin, sai ya ji duk jikinsa ya mutu. Ya cire tagumin da ya zabga hannu bibbiyu bayan ya nisa, ya dubi maigadin, "Wato yanzu kenan kana so ka ce yan sandan sun gane cewa Zainab ce ta aikata laifin?" "Ba ni ne na ke son na ce ba, hakan ne. To idan ma ba haka ba, me ya sa su ka tafi da ita?" Lukman ya jinjina kai, yayin da shi kuma Bukar ya ci gaba da cewa. "Kai lallai mugu ba shi da kama. Kaga dai matar nan idan bangaren sakin fuska ne, kyauta da alheri ba kamar ita, ashe ashe... Shi ya sa fa wasu suke cewa mai shiru-shiru mugu ne, ko ni yanzu da na auri ami shiru-shiru gwanda mai suru..." "Ba haka ba ne!" Lukman ya katse shi "Ni ina da jan akan wannan al'amari, domin tabbas na san Zainab ba zata aikata wannan danyen aikin ba." "Uhm, uhm, Lukman.. Ka ga! Ka kiyayi kanka da shisshigi cikin wannan magana domin kuwa abin ya dangana da hukuma, idan aka ji kana fadar haka kai ma za ta iya shafarka." (Ayimin afuwa narasa kusan phragrap daya) Ta yi shiru na dan lokaci, kana ta ce "Lukman- Lukman na ji ka ce ka yi laifi da ka zo yau ko?" "Cewa na yi, na yi ko ban yi ba?" ya gyara ma ta. "To ba ka yi ba, ai dama kwana daya mu ka yi ko?" "Eh." Ya gyada kai. Falon ya yi shiru na dan lokaci. "Lukman ina bukatar wani taimakone gare ka kamar yadda ka yi min na baya..." A bazata ya ji maganar, har sai da ya dan zabura. Ya kalle ta a bukace da son jin taimakon, "Hajiya kamar na me fa?" Maimakon ta fada masa, sai ta ce, "Lukman a wancan karon nawa na ba ka?" "Du...bu daya." Ya amsa cikin rawar baki a tunaninsa cewa za ta yi ya biya ta. "Yau na shigangada, ina zan samu dubu daya." Ya ce a ransa. "To, a wannan karon aikin da zan sa ka ya rubanya na baya a kudi sau goma, kuma mafi sauki wajen aiwatarwa akan na baya. Ka ga kudin zai kai dubu goma kenan." "Dubu goma Hajiya?" Bai san sa'ar da ya ambaci hakan ba. A iya rayuwarsa yau shekaru arba'in da daya kenan bai taba rike naira dubu goma tasa ba. Koda ya ke ba anan ya fara aikin tuki ba, ya fara ne a gidan wani attajiri A.A. Boza. A wancan lokacin ya dai sha ganin makudan kudi, ya ma sha raka Alhajin banki karbo miliyoyi, amma duk wannan ba ta sa ya taba rike dubu goma a matsayin mallakar sa ba, har zuwa sa'ar da ya bar gidan ya dawo nan. "Eh, dubu goma Lukman, ka na ja ne?" Ta tabbatar ma sa gami da bukata. Ta ci gaba jin ya yi shiru "Me ka gani? Kawai idan za ka iya ka amsa min, sai na baka rabin kudinka tun yanzu ka ga zarar ka kammala sai ka karbi rabin." "To..to Haji..ya ya wanne irin aiki ne wan...nan? Ke ba ki fada...min ba har yan...zu." Ya ce bakinsa na rawa. "Ba wani aiki ba ne magana ce kawai ta fatar baki." "Idanunsa suka kara girma (alamar mamaki). Ya za a ce daga maganar baki mutum ya sami dubu goma? "Shekara nawa dubunnai daga cikin al'umma ke dauka su na aikin karfin musamman a wannan kasa tamu da mutum ke dama da talauci amma su ke gaza mallakar dubu goma?" a zuciyarsa ya fada. "Ya ka ce?" Ta dawo da hankalinsa gare ta. "Hajiya ina tunanin wacce irin magana ce mutum zai fada da baki kawai ya sami Naira dubu goma? Ta kyalkyale da dariyar karfin hali har da kyakya cewa. "Ka ga kuma magana ce mai sauki wajen fada, kwatankwacin gyada kai ko girgizawa ga mutum yayin da ya ke amsa tambayoyi, abin bukata kawai, za ka iya?" "Ka ce za ka iya dubu goma ba wasa ba ce." Wani sashe a zuciyarsa ya rada masa. Kai tsaye kuma ya ci gaba da lissafa ma sa abin da zai yi da dubu gomar, ciki har da auren dalleliyar bazawara sauta ga wawa. "Eh..zan iya." Ya amsa kai tsaye. Ta dan kau da murmushin da ke kan lebbanta. "Ka san duk abin da ya faru a gidan nan ko?" Ya jinjina kai. "Na sani Hajiya." "To a takaice dai yan sanda jiya sun zo sun yi bincike amma ni ba su bincike ni ba saboda ba ni da lafiya amma kowane lokaci daga yanzu su na iya zuwa kuma dama wanda su ka rage ba a yiwa tambayoyin ba mu biyu ne, ni da kai." Ya yi zumbur ya mike tsaye cikin firgici, "To ni me na yi?" Ya bukata cikin saurin baki. A rayuwarsa duk barikin da ya yi ya na karami ba abin da ya fi tsoro irin yansanda, duk da kasancewarsa gwani kuma shugaban zuke-zuke da caca a kauyensu wancan lokacin. Ta bi shi da kallo cikin mamaki, kana ta bushe da dariyar karfin hali ganin har ya fara hada gumi duk da na'uarar sanyaya daki da ke iya bakin kokarinta a karamin falon. "Zauna mana to, sarkin tsoro ina za ka?" Ya yi ajiyar zuciya "Ai Hajiya abin ne na ji ya na kokarin fin karfi..." "To zauna ka fada mana!" Ta ce da daga murya. Ya zauna a hankali. "To mene ne ke kokarin fin karfinka?" Ta bukata. Ya share gumin da ya soma taruwa a goshinsa. "Hajiya ni kin san duk wani abu in dai da yan sanda a ciki tsoronsa na ke." "Ka na namijin?" Ta rike baki. "To shi namiji karfe ne bai san wuya ba?" ya ce ya na zaro idanu. "Ai idan ki ka lura ma ko karfe idan ya sha wuya ya na sarrafuwa." Hajiya Rukayya ta yakune fuska, "To ka ga kwantar da hankalinka, in dai ina raye ba kai ba wahala, ka na ji ko?" Ya dube ta ya dan yi dariya "Allah Hajiya?!" "Af, ka dauki abin wasa, kawai ka yarda ka karbi wanan garabasar kar ka zama mai gudun rabo." ta dan kwantar masa da hankali. "To na ji Hajiya, wacce irin magana ce?" Ta mike tsaye, "Ina zuwa" Ta fice daga falon, ta bar shi zaune a nan ya na ta sake-saken zuci. Jim kadan ta dawo, kudi rike a hannunta yan naira hamsin-hamsin bandir guda. Ta na zuwa daidai shi ta jefa masa a kan cinyarsa. "Ga su nan naira dubu biyar ne, kafin ka kammala na cika ma sauran" numfashinsa ne ya ji kamar zai dauke da ya dubi kudin. Nan da nan ya dauka ya fara jujjuyasu. Sababbi ne kal-kal. Ya nayin kallon da ya ke musu na maita sun isa su tabbatar da a shirye ya ke ya aikata duk abin da aka umurce shi, tuni ya manta da cewa ya zo ne ya ji dalilin da ya sa Hajiyar ta hana shi zuwa gidan shekaran jiya da kuma kyautar dubu dayan da ta yi masa. "Hajiya yanzu ke na ke jira.. Wacce magana ce?" Ta yi murmushi ganin cikin dan kankanin lokaci ta gama shawo kan Lukman da maasu gidan rana (kudi). san kalmar a'a?" Ta bukata bayan ta tsayar da dubanta gare shi. Tambayar ta ba shi dariya, "Haba Hajiya ai ko yaron da aka yaye yanzu ya san wannan kalma. Ita wannan kalma ai ta na amfani ne yawanci don nuna ba haka abu ya ke ba, na ki ko rashin sani ga wani abu, kai har..." "Yauwa dan gari da kai ake zance". Ta katse shi, "To abin da na ke so ka yi kenan a duk sa'ar da yansandan su ka riske ka don yi ma tambayoyi, ma'ana duk abin da ka sani sai ka nuna ba ka sani ba, abin da ba ka sani ba shi ma daman ba ka sani ba." "Af, lallai aikin mai sauki ne" ya ce a ransa kana ya bushe da dariya "Wannan ne kawai aikin Hajiya?" "Eh mana" Ta amsa ta na tabe baki. "Yanzu daga wannan na ci dubu goma?" "Kwarai kuwa." Ta tabbatar masa. Ya kuma duban dubu biyar din da ke hannunsa, sannan ya mike tsaye ya sa a aljihun wandonsa, ya koma ya zauna. "To sha kuruminki Hajiya an gama, yaushe za su zo?" "Kowanne lokaci daga yanzu, kai dai ka kasance cikin shiri" ya kuma mikewa "To ina iya zuwa gida na adana kudin nan na dawo?" Ta kalle shi "Ka na iya zuwa amma ka dawo da wuri" Har bakin kofar ta rako shi da amon muryarta ta na jaddada masa bukatarta, shi kuma ya na dafe da kudin ya na tabbatar ma ta da kada ta ji komai. *** Kamar yadda abin ya ke a zukatan wadanda ya shafa, ita ma Barista Hannatu haka ya ke a zuciyarta domin tun a jiyan da abin ya faru bayan ta koma gida ta kasa runtsawa, babu komai cunkushe a zuciyarta sai mamaki da tunanin faruwar al'amarin. Har kawo yanzu karfe bakwai da rabi da ta shirya ta ke kokarin tafiya asibitin, tunanin ya gaza yankewa. To amma fa har zuwa yanzu zuciyarta ta ki ta amince da cewa kawarta ce ta aikata laifin. Shi ya sa yanzu ma da take tsaye gaban dogon mudubin bayan fitowa daga wanka take gaggawar ta tafi asibitin domin bin diddigin abin don sanin gaskiya, a matsayinta na mai bayar da kariya (Lawyer) Bayan fitowarta da nufin tafiya asibitin sai ta yi tunanin tafiya gidan su Zainab domin sanar da mahaifanta. Shakka babu ta san rikicewar da kawar tata tayi zai yi wuya ta sanar da mahaifan nata. Sa'ar da ta isa gidan ba ta iske mahaifin Zainab ba don tuni ya tafi kasuwa. Ko da ta sanar da Mahaifiyar Zainab da wani yayan Zainab din da ta samu a gidan sai su ka rikice, su ka rasa yadda za su yi. Daga karshe da kyar Barista Hannatu ta rarrashe su ta nuna musu idan Allah ya so komai zai daidaita. Bayan ta bar gidan kai tsaye ta wuce asibitin. Ko da ta isa sai ta iske labarin cewa ai tun jiya kawarta ta ke hannun hukumar binciken laifuffuka (Yansanda) sai ta ga ba ta ga ta zama ba. Nan da nan ta bar asibitin ta tunkari hedikwatar yansandan. Ba a wannan karon ne ta taba zuwa hedikwatar ba, wannan shi ne karo na uku, domin a baya ta zo kusan karo biyu don yin wasu bincike game da wasu kesa-kesai (Cases), da ta kare, don haka ba bakuwa ba ce a wajen. Kai tsaye bayan ta isa ta wuce ofishin ASP Haladu domin saninta na cewa shi ne ofishin da ke da alhakin wannan matsalar. Ta kuwa yi sa'a ba ta samu cunkuson jama'a ba kamar yadda ta sha samu a baya. Bayan dan jira na abin da ba a rasaba aka yi ma ta umarni da ta shiga. A nutse cikin dankareriyar kujerarsa ta same shi, shi ne dai da ta sani. Shi ma bai manta ta ba. Bayan sun ida gaisuwa, ya ce, "Barista-Barista, yau ke ce da kanki?" Ta yi yar dariya "Ni ce Wallahi yallabai" "Ina ce dai kes (Case) ki ka biyo?" Ta gyada kai kawai ba tare da ta yi magana ba. "Yauwa ni na san dai ganin ku ba banza ba, akwai magana" ya ce shima ya na dariya "Wane kes ki ka biyo?" "Yallabai na biyo kes din wata kawata ce Zainab wadda aka kawo ta nan jiya" Alamun dariyar da ke kan fuskarsa su ka sauya zuwa na mamaki. "wacce Zainab ce kawarki? Wadda ake zargin ta aikata kisan kai? Menene hadin ki da ita?" Barista Hannatu ta yi dan murmushin karfin hali "Yallabai ina da ja ne game da zargin da ake mata, domin kuwa na san zai yi wuya ta aikata, tun da kuwa na san halayenta ciki da waje, tun muna firamare (Primary) muke tare" ASP Haladu ya nisa "Wato yanzu dai ki na so ki nuna min cewar sanin da ki ka yi ma ta tun daga firamare zai iya hana ta aikata laifin da ake zarginta ko? Ko mutum idan ya na karami idan ya girma halayensa ba sa sauyawa?" Ta girgiza kai "Ba haka nake nufi ba" "To ya kike nufi?" A wannan karon ya na dariya ya bukata. "Ina nufin a yadda abin ya faru akwai dimbin mamaki ace wadda ake zargi ce ta aikata" "Wato yanzu dai ki na da ta cewa kenan?" ya bukata har yanzu ya na dariya. "Shi ne ma dalilin da ya sa na zo?" "Ki na nufin za ki iya ba ta kariya ne?" A yanzu ya tattara hankalinsa gare ta kamar mai kokarin gane wani abu a tare da ita. "Eh, kariya na ke so na ba ta da kuma bi ma ta kadin sharrin da a ka yi ma ta na bata suna, yanzu ina so a mika batun kotu ne?" ASP Haladu ya fashe da dariya, kana ya ce bayan ya sassauta. "Na san ki na da kokari sosai wajen tsayawa a kotu don ganin kin baiwa wanda ki tsayawa kariya. Amma wannan karon na san ko da ni mu ka tsaya a kotu sai na kada ke, duk da ba aikina bane. Barista Hannatu ta dan biyewa dariyar da ya ke yi ciki karfin hali. "Ba ka fahimci abin da nake nufi ba shi ya sa, saboda haka kawai ka kyale ni. Ina kan bakata ta ba ta kariya kuma yallabai yanzu ina son ganinta." Ta sauya hirar. Ya yi jim na dan lokaci sannan ya ce "Barista da dai kin jinkirta zuwa lokacin da za mu karasa bincike tun da yanzu mun yi nisa, domin yanzu ma akwai wadanda na tura can gidan don su kuma samo mana wani abu." Ta nisa "Yanzu ba za a bar nu na ganta ba kenan?" Ya yi shiru ya na tunani, ya san idan ya hana ta ganin Zainab din a matsayin wadda zata ba kariya bai kyauta ba, dadin dadawa ba shi da zabi don haka sai ya ce. "To yanzu ki ke son ganin ta ko kuwa ya ya?" Ta yi yar dariyar karfin hali (domin duk abin da ta ke hankalinta ya na ga tunanin Zainab din, da halin da take ciki). "Eh! Yallabai yanzu mana." Barista Hannatu ta ce. *** Idan ka kwatanta fitar Lukman da shigowar yan sanda gidan du-du-du bai dara rabin sa'a ba. Su ma a zaune a falon su ka iske Hajiya Rukayyar tare da yan zaman makokin, sa'ar da maigadi Bukar ya yi musu jagora. Bayan sun gaisa tare da yi ma ta gaisuwa, sai Sifeto Habibu ya shiga yin abin da shi ne ya kawo su, ba kama kafar yaro. "Hajiya zan so dayan biyu cikin wadannan abubuwan." ya dan yi shiru sannan ya ci gaba, "Ko dai mu kebe a wani waje ba wannan ba, ko kuma a dan ba mu waje." (Ya na nufin yan zaman makokin su fita daga falon. "A'a,mu ne dai ya kamata mu ba ku waje..." Wata mata da ta yi matukar kama da Hajiya Rukayya ta fada da saurin baki. Kana ta mike ta ce da sauran matan, "Ku taso mu koma ciki kafin su gama." Babu wadda ta musa, sauran matan su ka mike jiki a sanyaye su ka rufa ma ta baya, kai tsayae su ka fice daga falon. Sifeto Habibu ya numfasa, "Hajiya tun a jiya mu ka so mu ji ta bakinki game da wannan al'amari, amma sai ya kasance ba ki ji dadi ba shi ya sa mu ka jinkirta zuwa yau. To amma a binciken da mu ka yi mun samu labarin cewa ke ce ki ka sayawa yaran ita waccan alewa da ta zama silar rayuwar yayanki... Ya ya abin ya ke?" Ta zunkuda kafada gami da girgiza kai." Yallabai ni ba ni na saya musu irin wannan alewar ba. Ni alewar da na saya musu ma... Ai ba jiya ba ne yau fa kusan mako guda kenan, kuma ace ba a sha ba sai a jiya?" Sifeto Habibu ya girgiza kai "Hajiya Wannan fa an ce a jiya ne sa'ar da ki ka kai su makaranta..." "A'a ni jiya da na kai su makaranta ban saya musu komai ba. Ni dana kai su a makare, yaushe zan tsaya na saya musu alewa?" Ta fada ta nadaga hannu. "Yanzu dai ke alewar da ki ka saya musu an kai mako guda kenan?" "Sosai kuwa, domin jiya mako guda daidai." Ya jinjina kai "To Hajiya na ji kin ce jiya kin kai su makaranta da kanki. Me ya sa? Ko dama ke ce ki ke kai su? Ba ku da direba ne?" Tambayoyin sun yi ma ta yawa don har taso ta rikice sai da ta dau dakiku a kalla goma kafin ta ce "Direba ne ke kai su, amma ai ranar makara ya yi..." "Bai zo akan lokaci ba kenan?" Ta gyada kai "Kwarai domin har na dawo bai zo ba. "To bayan ya dawo ya sanar da ke dalilin makararsa? Ta gyada kai "Eh, bai tashi da koshin lafiya ba ne." Sifeto ya gyada kai a lokaci guda da nisawa. "To bari na koma da ke baya Hajiya, a wancan lokacin da ki ka saya musu alewar tsawon sati da ya shude, a ina ki ka saya musu? Itama a hanyar makarantar ne?" Ta girgiza kai "A'a. Shi lokacin mun fita unguwa ne kawai". "To wacce iri ki ka saya musu?" "Ah!" Ta bude baki cikin mamakin karya "Alewa da ka sani Alewa ai Alewa ce." "Haka ne amma ai kowacce da sunanta ko?" "Eh, tabbas amma ni yanzu ba zan iya rike sunan ba domin ban kula ba." Ya nisa da karfi "To yanzu Hajiya, ina za mu ga matukin gidan nan, ma'ana direba." Da ta yi niyar ta ce musu yanzu ya fita sai ta yi tunanin kar su gano abin da su ka shirya. Sai ta sauya da cewa Bai zo ba amma kuna nan za ku gan shi." Ta na rufe baki su ka ji sallama a bakin kofar shigowa falon. "Yauwa ka ga dan halak ma, ga shi nan". Hajiya Rukayya ta ce ta naduban Lukman da ya daga labulen falon ya shigo. Gabansa ya fara faduwa ganin yan sanda uku zaune kowanne da gishin baki kamar jelar tsuntsu, habarsu aske tas kamar bayan kasko. "Kai sakarai kar ka nuna tsoronka tun yanzu mana, aikin naira dubu goma fa za ka yi kuma har an ba ka dubu biyar." Wani sashe a zuciyarsa ya tunatar da shi. Ya nufi daya daga cikin kujerun ya zauna. "Sannun ku da zuwa." "Yauwa sannu." Sifeto Habibu ya juya ga Hajiya Rukayya. "Hajiya don

Please Login or Register in order to submit comment