Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bukata. Amma don ganin ran Baraka ya soma baci sai ta yi ta maza ta saduda, ta mika wuya, "Yanzu ke ce abar ji, Akuyar daure, mara yanci." "Kin ci abinci Baraka." hajiya Rukayya ta ce ta nadariya, "kuma kar ki damu, ni ma na kusa samun yanci tunda yanzu na hau hanya, kin san kuwa sannu ba ta hana zuwa...saboda haka ki sa mana rana kawai, babu wani abu." Baraka ta cira kai ta naduban kyakkyawan rufin dakin da aka yi matukar kawata shi, alamun ta na tunani, "Me zai hana mu je gobe idan ki na da hali, tunda ni jibi zan koma." Ba ta yi tunanin komai ba ta amsa, "Allah ya kai mu goben lafiya. Amma fa kin san ba na son a fara ta kanta, na fi son a fara ta kan wannan shegen dan, musamman ma illar rayuwarsa da ki ka fito mini da ita." "Wannan kuma ya rage naki sabuwar amarya a dakin miji...gobe idan mun je kya ma sa bayani. Ni zan koma." Ta mike tsaye a hankali. "Tun yanzu?" Hajiya Rukayya ta ce da ita cikin daga murya. "Wallahi akwai gurare da dama da na ke so na kai ziyara kafin na koma jibin, sai dai goben kawai kya ganni." "To, Allah ya nuna mana" Hajiya Rukayya ta ce bayan ita ma ta mike tsaye, "Mu je na taka miki." To, a daidai lokacin ne Zainab ta daga labulen dakin ta shigo gami da sallama, shigowar da ta zamar mata da-na-sani. "Wa'alaikis sa..." Yunkurin amsawar da Baraka ta yi ya gaza kai gaci saboda zungurarta da Hajiya Rukayya ta yi gami da cewa, "Ke ita ce fa!" Baraka ta fahimci wadda ta ke nufi, don haka sai ta mayar da dubanta ga Zainab, a tsanake ta shiga yi mata duban Raini da wulakaci, kamar yadda ta ga Hajiya Rukayyar ta galla mata wata uwar harara. Ita kuwa a nata bangaren maimakon ta damu, sai ta saki wani matsakaicin murmushi, "Yaya bakuwa mu ka yi ne?" "Bakuwa? Ina ruwanki da bakuwa? Ta ki ko tawa? Haijaya Rukayya ta ce fuska a yatsine kamar yakuwar da ta sha matsa. Zainab ta yi kasake ta nakallon su cikin kunya. "Da ke na ke! Bakuwarki ce ko tawa?" Ta kuma fada da tsawa. Zainab ta nisa kana ta kuma yin murmushin karfin hali cikin son mayar da abin wasa ta ce, "Tawa ce mana tunda ta ki..." "Ke rufe mana baki sarkin iya magana, wa za ki yi wa wayo." hajiya Rukayya ta kuma katse ta, "Ki ji mu da yarinya?" Ta juya ga Baraka wadda tunda al'marin ya fara babu abin da ta ke yi sai hararar Zainab din, "A to! Ni ban ma san ta ba, amma kin ji saboda kalen dangi wani bakuwarta ce...ko ta ya ya na zama bakuwarta?" "Oho!" Cewar Hajiya Rukayya, "Wa ya san ma ta, kin gan ta nan kullum haka ta ke shisshige mini wai ita kanwa..." "Kanwarki? A gidan uban wa?" Baraka ta katse ta, "Dama an taba kanwa da abokiyar gaba?" "Ke ma dai kya fada". Hajiya Rukayya ta fada bayan ta mayar da dubanta ga Zainab wadda har yanzu ke tsaye, kai sunkuye, cikin tsananin jin kunya. "Ke!" Ta daka mata tsawa, "Wai mene ne ya kawo ki daki na?" Zainab ta cira kai a hankali ta dube ta, "Ba komai, dama abinci ne na kammala na zo don na sanar da ke". "Abinci?" Baraka ta cafe ta naduban Hajiya Rukayya, "Abinci fa ta ce? Har abinci ki ke yarda ku ci tare? Haba Gaskiya mana ki ka kasa fitar da ita daga gidan. Ai ta riga ta cinye ki...kai lallai ma Rukayya nan da wauta ki ke. Idan banda abinki, wa ke cin abinci da kishiya, wadda idan aka ba ta wuka aka ce ta yanka ki, a guje za ta aikata." Hajiya Rukayya ta girgiza kai, a lokaci guda kuma ta daga hannu, "Kin ga ni fa ba tare mu ke ci ba. Ina ni ina cin abinci da wannan." Ta nuna Zainab, "Ta dai gama ne, ta zo ta sanar da ni kawai. Yo da na ci abinci da wannan ba gara na mutu da yunwa ba." Zainab ta dago kanta da ke duke da nufin ta ce wani abu, sai baraka ta yi mata tsawa, "Ke malama! Ba ma bukatar maganarki, maza-maza ki fice ki ba mu waje tunda nan ba dakinki ba ne." Ba ta kuma wani yunkuri ba, ta juya jiki a sanyaye, zuciyarta cike da nadamar shigowarta dakin. Hajiya Rukayya da Baraka su ka fashe da dariya har da tafawa. "Shegiya kadan ma ta gani." Baraka ta ce, "Yadda na tilasta ma ta ta fita daga dakin nan, haka za ta fita daga gidan nan ko da ba ta so." Suka kuma kwashewa da dariya, kana su ka rungume juna. *** Wata dalleliyar mota kirar KIA picanto shudiya, ta cusa kai cikin tafkekiyar harabar makeken gidan bayan bude babbar kofar da maigadi ya yi. Kai tsaye direban motar ya wuce da ita cikin babbar rumfar kwanon da aka tanada musamman don ajiyar motoci, sannan cikin sauri ya fito ba tare da ya kashe motar ba, ya bude kofar motar ta baya. Alhaji Basiru, baki, kakkaura mai matsakaicin tsawo ya fito kallo daya za ka yi masa ka lakanci ya na da fara'a sosai duk da wadatattun kumatun da ya ke da su. "Sannu da zuwa Alhaji." Dattijo da ya bude mu su kofa ne ya fada bayan ya isa gare su. "Yauwa, sannu malam Bukar." Alhaji Basiru ya amsa, kana kai tsaye ya nufi kayatacciyar kofar da za ta sada shi da cikin gidan, zuciyarsa cike da zulumin abin da zai tarar a gidan, wanda ya zame masa sabo tun lokacin da ya kara aure. Ya daga labulen babban falon shakatawar gami da sallama. Zainab kyakkyawar fara da ke zaune kan daya daga cikin tausasan kujerun da ke kewaye da falon ta amsa sallamar da tuni ta gane muryar da ta yi ta. Cikin fara'a ta mike ta tare shi, ta karbi karamar jakar da ke rike a hannunsa. "Sannu da zuwa Alhaji." Ta ce. "Yauwa, sannu amarya. Yau ke kadai ce a falon? Ina yayar taki?" Ya amsa gami da tambaya. "Ta na ciki wallahi, dazun nan ta shiga." Ta ba shi amsa. Ya nufi daya daga cikin kujerun ya zauna. "Bari na kawo ma abin da za ka sanyaya makoshinka maigida." Ta ce da fara'a bayan ta ajiyr jakar a gefensa. Cikin nutsuwa ta mike ta nufi doguwar na'urar sanyaya ruwa da ke ajiye a can gefe guda, hakan shi ya yi daidai da lokacin da Hajiya Rukayya ta daga labulen falon ta shigo ba tare da sallama ba. "Sannu da zuwa." Ta ce da kyar kamar mai ciwon baki. "Yauwa. Sannu uwargida, kwanciya ki ka yi ne?" Alhaji Basiru ya amsa tare da yi ma ta tambaya cikin rashin damuwa da hade fuskar da ya ga ta yi. "Wane ne ya ce ma kwanciya na yi?" Tambayar kenan da ta fito daga bakinta. Alhaji Basiru ya yi murmushi, "Uwargida kenan...mene ne na zafi cikin wannan tambayar? Gani na yi idonki kamar da alamun barci." Ta yi wani takaitaccen tsaki, "Ni ba barci na ke yi ba, idan ma fada ma aka yi, wanda ya fada ya zama babban makaryaci." "To, ai shi kenan." Ya ce da ajiyar zuciya. Idan da sabo dai ya saba. Wannan wata al'ada ce da ya san ta dauka, ta mayar da karamar magana babba, duk don kar a zauna lafiya. Da yalwataccen murmushi ya dubi Zainab, wadda ke kokarin darkusawa gabansa, hannunta na dama rike da doguwar robar sassanyan tataccen lemon zaki, karamin kofi rike a hannunta na hagu. "Yauwa, a gaishe ki amarya. Na gode." ya fada bayan ya karba. Ta mike cikin jin kunyar abin da ya fada, ta koma kan kujerar da ke kusa da Hajiya Rukayya ta zauna, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Sannu Hajiya, har kin fi..." "Wane irin sannu...ciwo na ke yi?" ta katse Zainab da daga marya, sannan ta shiga jifan ta da wata uwar harara. Maganar ba ta yiwa Alhaji Basiru dadi ba, don haka yace, "Haba Uwargida, wai me ya sa ba..." "Ka ga malam, babu ruwanka a cikin wannan maganar." Shi ma ta katse shi, sannan ta ci gaba da cewa "Ai dama kai ka ke daure mata gindi, idan banda daurin gindin da ta ke samu a wajenka, ya ma za a yi wannan yar matsiyatan ta dora wa Hauwa'u sharri, wai ta yaga ma ta littafi, alhali wannan dan banzan yaron nata ne marar jin magana kamar barawo ya yaga kuma ma wani rainin hankali, na yi magana yarinyar nan ta rufe idanu ta yi min rashin mutunci a gidan nan, zagi ta uwa ta uba..kai in banda ruwa ya daki babban zakara, wannan yarinya ta isa ta ja da manyan mata, yarinyar da na tabbatar a haihuwar kaji na haife ta sau babu iyaka.." Ta dan sarara kadan, sannan ta ci gaba da cewa, "Ko da ya ke ba na mamaki don shi matsiyaci idan ya samu dama babu abin da ba zai iya.." "Ke saurara Hajiya! Zainab ta katse ta cikin fushi tuni fuskarta ta sauya. Da kaushin murya ta ci gaba da cewa "Ina so fa ki sani duk abin da ki ke mini kyale ki na ke yi saboda gudun ka ce-na ce da kuma darajar wanda mu ke aure, amma ba don tsoron ki ba. Kar ki ga ina kauda kaina akan wasu abubuwa ki yi tsammanin ban san abin da.." "Zainab" Alhaji Basiru ya katse ta ta hanyar kiran sunanta. Da girgiza kai ya ce, "kar na kara jin bakinki" Ranta ya yi mutukar baci, amma duk da haka sai ta shiga tausasar zuciyarta don bin umarnin mijin nata Ita kuwa Hajiya Rukayya sai ta mike tsaye ta natafa hannu ta nafadin "Ka kyale ta mana ta gani idan da yau sai na dandaka ki a gidan nan, don ina da tabbacin ko daga barci na tashi na fi karfin ki." Da wannan maganganu ta fice daga falon. Bayan fitar ta sun dauki tsawon lokaci babu wanda ya ce da wani komai. Alhaji Basiru mamaki ne ke damun sa da tunanin, yaushe za a kawo karshen wannan abin da ke faruwa a gidansa. Da ya ke ya san mai laifin sai ya numfasa a hankali, ya dubi Zainab, "Ki kara hakuri akan wanda ki ke yi da, komai na duniya watarana tarihi ne." Haka ya ci gaba da tausar ta saboda ko da yaushe dai kokarinsa ya daidaita tsakaninsu, don ba ya son rabuwa da kowaccen su, kamar yadda zuciyarsa ke ba shi shawara wasu lokutan ya kawo karshen matsalar ta hanyar saki. Amma idan ya tuna illar sa a addinance sai ya danne zuciyar tasa ya lallashe su. Lokacin da ya tabbatar ya gama tausar zuciyar zainab, sai ya mike ya bi bayan Hajiya Rukayya da nufin ita ma ya tausashe ta don a samu zaman lafiya. Amma ko da ya shiga dakin ya na yi mata magana sai ta yi kamar ba da ita ya ke ba. Don ya tabbatar ma ba za ta saurare shi ba sai ta shiga rera wasu wakoki na habaici gare shi. A daidai lokacin da wannan ke faruwa, acan bakin kofar gidan ma wani abu ne ke faruwa tsakanin malam Bukar maigadi da wasu bakin turawa da su ka zo wajen Alhaji Basiru. Turawan biyu yan asalin kasar Ingila ne, wanda a nan fiye da rabin harkokin Alhaji Basirun su ke. Kuma su ba sa jin Hausa, yayin da shi kuma Malam Bukar ba ya jin Turanci. Tsawon lokaci su ka kwashe suna musayar yawun da ba shi da amfani, don kuwa babu wanda ya fahimci dan uwansa, saboda rashin gane abin da kowa ke cewa. Baseer, shi ne abiin da turawan ke iya furtawa na daga sunan Alhaji Basiru. "Na ce mu ku a nan gidan kaf Babu Baseer, sai dai Alhaji Basiru kun ki yarda ko? To shi kenan sai ku yi ta yi, idan kun gaji da tsayuwa kwa tafi." Malam Bukar ya ce a kufule ganin suna kokarin cusgunawa daddadan gyangyadin da su ka zo su ka same shi ya na yi. Turawan biyu su ka kuma duban junan su cikin rashin fahimtar abin da ya ke nufi wanda kuma shi ne abin da su ke yi duk sa'ar da ya yi maganar. "Have you understand what he is saying?" Daya baturen ya ce da dayan. Wanda aka tambaya ya girgiza kai, alamun bai gane ba. Baturen da ya yi tambayar ya kuma duban malam Bukar fuska cike da alamun damuwa, ya kuma maimaita bukatarsu gare shi. "To, ai kuma sai ku yi tunda ni dai na yi mu ku bayanin babu wani Baseer a nan kun ki yarda. Yanzu kuma ga shi na ji ka tsiro da wani sabon abu kamar ka na ambatar Talle ko mene ne? Sai ku yi ta yi, dama ai mu na samun labarinku, ba ku da aikin yi sai shariri ta..mutanen da ke kula da lafiyar Beraye don sun tambayi abin da babu har wani abin mamaki ne? Ya na gama gadar haka ya rufe idanunsa kana ya langwabar da kansa a kan majinginar kwantacciyar kujerar mai kama da gado, wadda aka yi ta da icen makara ya ci gaba da gyangyadi abinsa. Turawan su ka kuma duban junansu cikin damuwa kana su ka kuma kallon malam Bukar wanda tuni ya fara layi irin na ma su gyangyadi. Wanda ke yi ma sa tambayar ne ya tuno wata dabara. A hankali ya mika hannu ya taba kafadar malam Bukar. Firgigit! Ya tashi sauran kiris ya hantsilo daga kan kujerar. Daga bisani ransa ya kara baci da ya ga cewa har yanzu turawan nan ne da ya tsana da gani su ka tashe shi. Ya mike cikin fushi da zummar kai duka gare su amma saboda labarin da ya taba samu a kauyensu tun ya na saurayi cewa, wai fararen fata jikinsu kamar nunanniyar Gwanda ya ke saboda rashin kwari, idan baki ya kuskura ya doke su mutuwa su ke yi domin wai jini ne zai fito daga jikin nasu, su kuma ba sa kaunar su ga jini a jikinsu, wai saboda haka sai yi fushi su mutu. Tunanin hakan ne ya sa shi sauya abin da ya yi nufi a farko na kai mu su duka, zuwa fadin, "Kai wai ku diyan gidan uban wane ne da za ku dame ni? Na ce mu ku ba mu da wanda ku ke fadi a gidan nan kun ki yarda. To, wai me ku ke nufi ne don buhun ubanku?" Turawan ba su damu da fadan nasa ba, don dama ba sa jin abin da ya ke fada. Don haka kawai sai dayan Baturen ya daga hannuwansa biyu kamar yadda ya yi nufi, ya fara yi wa malam Bukar zance irin na kurame da su. To, a sannan ne malam Bukar ya fara fahimtar su. Bayan dan lokaci da ya dauka ya na duban Baturen sai ya fahimce shi. Take shi ma ya sauya zuwa hakan. Cikin kankanin lokaci su ka fahimci juna duk da ba yarensu daya ba. A cikin tattaunawar tasu ne, Malam Bukar ya tambaye su, abin da ya sa ba su buga masa waya ba. Su ka sanar da shi sun nema ba su samu ba. Da fara'a ya sanar da su, su yi jiransa ya je ya sanar da Alhajin zuwan nasu. *** Tabbas Malam Bahaushe ya yi kyakyawan tunani da ya ce, " Sa kai ya fi bauta ciwo" Hakika haka abin ya ke, don wannan karin maganar ya yi tasiri akan Hajiya Rukayya wacce sau da yawa ta kan gagara tashi sallar Asuba ko da kuwa an tashe ta. Amma ga samun sauyi sai ga shi yau ta tashi tun kafin kiran sallar farko, saboda bukatar kanta. Bayan ta yi sallar Asuba, a gurguje ta shiga wanka, cikin mintinan da ba su fi a kirga da yatsun hannu ba ta fito, kana a gaggauce ta sanya kayanta ta fito fes da ita. Ta isa ga wani tafkeken madubi da ke kafe a jikin bango wanda a shi ne take yin kwalliya a duk sa'ar da ta yi wanka. Ta kare wa kanta kallo tsaf a cikin madubin kana ta yi murmushi. "To, yanzu me ya rage mini?" Ta tambayi kanta a fili ta cikin madubin, kamar mai neman shawarar siffarta da ta bayyana akan madubin. "Abu uku ne kawai ya rage miki." Zuciyarta ta kissima ma ta. Ta fadada murmushinta lokacin da zuciyar tata ta ci gaba da jero ma ta abubuwan da ya kamata ta samu. "Kudi da neman yardar Alhaji, da kuma jiran zuwan Baraka" Yanzu su ne abubuwan da su ke gabanta Shakka babu ya zama dole ta nemi yardar Alhaji Basiru a wannan karon, ba wai don ta nashayin zai iya hana ta fita ba, a'a, saboda ta nason ta fita da mota da kanta don gudun kar asirinta ya tonu idan sun fita da direba. Ta riga ta san duk abin da take so Alhaji Basiru zai ba ta, ko don a zauna lafiya. Amma fa banda barin ta ta ja mota. Haka dabi'arsa ta ke, ba ya barin iyalansa su ja mota da kansu sai dai duk inda za su a kai su. A tunaninsa, abin kunya ne a ce mai kudi kamar sa ya bar matansa su na jan mota da kansu. Tunda kuwa ta san da haka, lallai akwai bukatar ta lallashe shi ta kowace irin hanya don ya bar ta ta fita ba tare da direba ba. Al'amarin kudi kuwa da sauki-sauki, don ta natunanin wadanda ke hannunta ma za su iya isar ta, duk da ya kamata ta nemi kari. Sai kuma jiran Baraka, wanda ya zama dole don ita ce idon garin. Ta kuma yin murmushi cikin madubin a karo na biyu, ta namai yabawa da kyakkyawan tunanin da ta yi. A hankali ta juya, ta bawa mudubin baya kana ta fara duban gefe da gefen dakin a tsanake kamar mai tsammanin ganin wani a dakin bayan ita. Ba wani abu ta ke tunani ba kawai ta na fasalta adadin yan gaisuwa da zaman makokin da dakin zai dauka ne. Lokacin da ta isa dakin Alhaji Basiru a kishingide ta same shi a kan doguwar kujerar da ke cikin kujerun da ke dakin. Sau biyu ta yi sallama amma bai dago ba balle ya amsa. Ba wai bai ji sallamar ba ne, amsawar ce kawai ta gagara saboda hankalinsa ya tafi duniyar tunani, kuma ba wani abu ya ke tunani ba da ya wuce matsaloli na rigingimun da ke faruwa a tsakanin iyalan nasa, da kuma hanyar da zai bi ya warware su. Wannan shi ne tunaninsa a kullum. Sai dai baya ga wannan, yau akwai wani, tunanin gayyatar da aka yi masa zuwa kasar ingila a game da harkokin kasuwancinsa, wanda shi ne dalilin zuwan turawan nan biyu wajen sa. Abinda ya fi tunani a yanzu shi ne, ya ya iyalansa za su kasance idan ya yi tafiyar da ya ke so ya yi a jibi. Ya na nan ma ya aka kare? Wannan shi ne ya sa a yanzu da Hajiya Rukayya ta shigo cikin dakin ya gaza amsa ma ta sallamar har sai da ta je kusa da shi ta dafa shi. Ya cira kansa a hankali ya dube ta. Bai ce komai ba ya kuma mayar da kan. "Alhaji lafiya kuwa?" Ta tambaya da alamun mamaki a fuskarta. Ya nisa, kana ya kuma cira kai ya dube ta, "E, to, lafiyar kenan." ya ce daidai lokacin da ya ke yunkurin sauyawa daga kishingidar zuwa zama. "Haba Alhaji, to mene ne abin yin dogon tunani irin wannan bayan ka ce lafiya?" Ta ce bayan ta samu waje ta zauna kusa da shi. "Dogo ne tunanin nawa? Ya bukata ya na sababben murmushinsa don gudun bacin ranta. Don tun bayan karin aurensa, duk lokacin da za su yi wata magana sai sun saba. "Dogo ne mana..sau nawa na yi sallama ba ka amsa ba?" Ta fada a marairaice. Mamaki ne ya fi bayyana a fuskarsa fiye da komai, don rabonsa da ya ji sassanyar muryarta tun kafin ya tuntube ta da maganar karin aurensa. Ya kuma yin murmushi "Ina jin ki, kawai dai na.." "Au! Ashe ka na ji na ma ka kyale ni? Ta katse shi da tambaya ta naharararsa, harara ta wasa. "Ba haka na ke nufi ba, ki bari na karasa mana." ya ce cikin murya mai cike da mamakin irin hirar da ke gudana tsakaninsu. Ya kura ma ta idanu cikin kokarinsa na gano wani abu tare da ita. Ta dukar da kai kasa bayan ta fahimci abin da ya ke nufi. A zahiri har a badini ba ta bukatar ya gane yaudarar da ta ke kokarin shirya masa, don ta samu damar fita da mota ba tare da direba ba. Sama da dakika talatin ba ta dago ba. Shi kuwa bai daina kallon ta ba, zuciyarsa sai dawurwura ta ke tsakanin yarda da rashin hakan, a dan abin da ya nazarta a tare da ita. "Ai kawai ka godewa Allah, da alama ya shirye ta ne ta zo ta nemi afuwa ga abin da ta yi maka a baya. Idan ba haka ba, me zai kawo ta dakinka da sassafe kuma har ta rika yi maka magana a tausashe?" Wani sashe na zuciyarsa ya ambata. "Kai haba, ina! Ba wani nan, kai dai kawai akwai wani abin daban." Wani sashen ya karyata na farko. To, ko ma mene ne dai a yanzu ya na bukatar ya sani, kuma lokaci ya yi da ya kamata ya yi amfani da wannan damar wajen shawo kanta don su samu zaman lafiya da amaryarta. "Hajiya ya na ga kin dukar da kai kasa kamar mai dinkin hula?" ya bukata cikin raha. "Dole na yi haka Alhaji tunda na zo takanas gare ka ka ce ka na ji na ka kyale ni." Ta amsa ta na duban sa, a wannan karon ta kara kwantar da muryarta fiye da baya. Ya kuma fadada murmushinsa na mamaki da jin dadin ganin irin damuwar da ta ke nunawa, wai don ya ce ya na jin sallamarta ya kyale. Take sai ya ji kamar duk duniya babu wanda ya fi shi jin dadi. Don a rayuwarsa babu abin da ya fi so irin ya ga ya na zaune kalau da iyalansa. "Ba ki fahimce ni ba. Cewa na yi na dan sha'afa cikin tunani ne...amma ai ina jin ki." "To, share ni ka yi kenan?" Ta sake bukata ta nayi mai fari da idanu. "A'a." ya ambata da sauri. "To mene ne?" Ta ce ta nadariya, a wannan karon sai da fararen hakoranta su ka bayyana a fili, wanda hakan shi ma ya sa shi darawa. "Yau kuma sai ina? Na ga kin yi kwalliya kamar wata sabuwar amarya." Ya sauya hirar bayan sun dakata da dariyar. Ta harare shi, "Wa ya sani ko amaryarce?" Ya yi mamakin abin da ta ce abin da bai taba tsammani zai zama amsar tambayarsa ba. Ya riga ya san idan da abu guda da ta tsana a rayuwarta bai wuce amaryarta Zainab ba. To, amma jin sabanin abin da ya yi tsammani sai ya yi sauri ya ce, "Ni dai na san wannan shiga ba banza ba, akwai wajen zuwa ko?" Ta langwabar da kai akan majinginar kujerar kana ta kuma fari da fararen idanunta, wadanda sau da yawa ta san fari da su kan yi tasiri wajen jan hankalinsa. Sannan da sababbiyar murayarta ta yaudara ta ce, "Alhaji, ina so na je unguwa ne idan an jima." "Har ina kenan?" Ya bukata bayan ya dauke kansa daga kallon ta zuwa sakalallen hotonsa da ke kafe jikin bango, jin abin da bai taba tsammanin shi ya kawo ta ba. Abin da ya riga ya sani ne, ta sha fita zuwa unguwa ba tare da saninsa ba. To, amma yanzu me ya sa ta zo tambayar sa. Sai dai bai bari

Please Login or Register in order to submit comment