Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan gagarumin al'amari ne, ko na ce gagarumin sakaci ne da ya bar baya da kura, wanda kuma kacokan zai iya sauya dukkan sakamakon da jami'an su ka samu, domin kuwa wadda su ka bari din ita ce ta farko da ya dace a ce an gana da ita kuma ma abin tambaya ne a ce wai matar da ta rasa yayanta biyu ta sami damar barci. Don haka ina kira ga shari'a da ta shata layi a karkashin wannan babban kuskure don gudun kar a yi tsallen-badake a cikin wannan shari'a. Na gode." Ta koma ta zauna. A wannan karon ma sai da mai shari'a ya tsawatar saboda hayaniya da ta sopma karfi. Bayan an sarara ne mai shari'a ya dubi Garba ganin bai taso ba. "Garba ko shaidun sun kare ne?" Ya mike "A'a ba su kare ba, yallabai. Yanzu zan gabatar da shaida ta gaba wadda koken ta ne mu ke dubawa a yanzu, kuma matar da a ka ci amanarta wato Hajiya Rukayya." Hajiya Rukayyar ta fito ta hau mumbari. Garba ya dube ta, "Hajiya Zan so na ji ko lokacin faruwar wannan al'amari, ki na cikin falon?" T girgiza kai "Ba na ciki" "To ke me ki ka sani kenan dangane da al'amarin?" "Ranka ya dade, ni ban san komai ba, kawai dai ina cikin dakin girki sai na ga dan wajen amaryar tawa ya zo ya na sanar da ni cewa wai ga..." Shisshikar kuka ce ta hana ta karasawa. "Sannu Hajiya Ki yi hakuri...kar ki yi kuka." Garba ya shiga ba ta hakuri. Bayan ta sassauta, sai ya juya ya koma ya zauna. Hannatu ta mike, "Da farko in jajenta miki wannan rashi, Hajiya Allah ya ji kansu." "Amin." Ta amsa da kyar. "Hajiya sa'ar da aka sanar da ke cewa ga abin da ke faruwa, abin nufi lokacin da Mujahid ya kai miki kara cewa an kwace masa alewarsa. Me ya sa ki ka nufo falon a rikice?" Fuskarta ce ta sauya lokaci guda. Ba ta yi tsammanin wannan ta nacikin tambayar da za a yi mata ba. Shiru ta yi na yan dakiku. "Ba ki ce komai ba...ko kin taho ki kwatarwa Mujahid din alewar ne..." "Eh...e...ha...ka ne.." Ta ce cikin in ina ta nagyada kai, gami da kifkifta idanu. Hannatu ta yi murmushi, "To kuma me ya sa ki ka taho ki na ambatar cewa kar su sha wannan alewa ba ta da kyau?" Yanzu ma shiru ta yi cikin rarraba idanu. Tsawon dakiku goma ba ta yi magana ba, hakan ne ya jawo hayaninya a cikin kotun. Hayaniyar da jama'ar ke yi ta nuna mamakinsu ga faruwar wannan al'amari. Bayan kotun ta yi shiru ta hanyar tsawatarwa daga mai shari'a Mukhtar, sai Garba ya mike jiki a sanyaye. "Ya mai shari'a ba zan taba amincewa da wannan soki-burutsun tambayioyi ba. Sannan ina kira ga shari'a da ta bada umarnin a sassautawa wannan mata domin a halin yanzu ta na fama da tunanin makokin yayanta don gudun kar a tilasta ta ta amsa abin da ba ta yi ba." ya koma ya zauna. Mai shari'a ya dube shi, "Kotu ba za ta iya amsa wannan kira naka ba domin kuwa ya nayin mai amsar tambayar, ya nayi ne da ke da rufa-rufa a ciki, saboda haka akwai bukatar a kwalkwaleshi tas domin ketare zalunci a cikin wannan shari'a." Ya juya ga Hannatu ya ba ta umarnin ta ci gaba. Hannatu ta kuma murmushi bayan ta dubi Hajiya "Hajiya ba ki fadi dalilin da ya sa ki ka ambaci waccan kalmar ba, ko daman kin san da alewar?" "A'a...ban...san..da ita ba...kawai dai..." Ta kasa karasawa, ta juya kallonta ga Barista Garba da tuni kansa ya fara daukar zafi. "Kawai me?" Hannatu ta dawo da hankalinta gare ta. Yanzu duk idanun da ke kotun kallon ta su ke cikin mamaki. "Hajiya ya kamata ki amsa wannan tambaya domin ki na batawa shari'a lokaci". Mai shari'a Mukhtar ne ya fada. Ta yi ajiyar zuciya "Saboda alewar ba saya aka yi ba." Idanun da yawa daga cikin mutanen ne su ka kara girma don mamaki. "kamar ya ya ba saya aka yi ba, mu na so ki fayya ce ma na. "Ba...ba ni ce na sa..ya ba.. Wata...kawata...ce Baraka...ko da ya ke na saya mu...musu alewa a makaranta...uhn...uhn..." Ta kasa ci gaba. Hayaniya ta kaure a kotun kamar kasuwa, wasu har mikewa su ka yi don mamaki. Bayan an tsawatar Barista Hannatu ta dubi Hajiaya Rukayya ta ce, "Hajiya, yanzu dai ya tabbata ke ce ki ka samar da wannan alewa kenan?" Ba ta yi magana ba. Hannatu ta juya ga alkali, "Ya mai shari'a kamar yadda na sanar tun a farko, cewa wannan shari'a tabbatattun shaida ne kadai ke da muhimmanci wajen gano gaskiyar wannan al'amari, to wannan haka ya ke, domin kuwa idan mu ka duba a yanzu bisa wannan tabbatarwa da wannan mata ta yi da bakin..." "Ba zan taba amincewa da wannan ba." Garba ya mike, "Ya mai shri'a babu wata hujja a yanzu da za ta tabbatar da a bin da Hannatu ta ke shirin fada domin kuwa tun farko sai da na ja hankalin shari'a a kan ta tsawatar da a sassauta wajen yiwa wannan mata tsauraran tambayoyi don gudun kar a tilasta ta fadi abin da ba ta yi ba, kamar yadda a ka yi mata yanzu. Sannan daga karshe ina rokon shari'a da ta daga gabatar da wannan kara saboda dalilanmu na son binciko wasu kwararan hujjojin da za su tabbatar da gaskiyarmu, kuma kafin lokacin wannan baiwar Allah ta dan huce." Mai shari'a ya dubi Hannatu da ke ta faman murmushi ya ce, "Mene ne ra'ayinki dangane da rokonsa, ki na da ja?" "E, to ranka ya dade tun da har an samu tsaiko da dalilin gazawa daga abokin karawar tawa, zan iya amincewa, amma akwai wata alfarma da na ke bukata shari'a ta yi min. Lallai ya zama wajibi shari'a ta nemo wannan mata Baraka da Hajiya Rukayya ta ambata ta hanyar tuhumar ita Hajiyar, don kuwa ba yanzu ba ne ta fara ambatar sunanta, ta soma ambatar sunan matar ne tun sa'ar da su ke a asibiti, saboda haka babu ko tantama nemo matar gagarumin abu ne da ya ke da matukar amfani." Mai shari'a ya dukar da kansa ya yi yan rubuce- rubuce, kana ya dago, "Mun ji wannan kira naki Hannatu kuma lallai za mu aikata. Sannan mun daga wannan zama zuwa ranar Alhamis ashirin da hudu kennan ga wannan watan, a matsayin ranar da za mu ci gaba da sauraron wannan shari'a. Da wannan kotun ta tashi. 'yan sanda su ka kuma tusa keyar Zainab zuwa cikin bakar motar su ka tafi da ita, yayin da dokacin jama'ar da su ka sami sauyin ra'ayi daga zargin na zainab su ka bi motar da kallo suna cewa, "Allah Sarki, baiwar Allah, Allah ya kubutar da ke." *** Kashe gari da safe Hannatu ta nufi makarantar "Sasif da burin samun dan saurayi mai shagon sayar da kayan tsotse-tsotse, Habu mai shago. Tafiyar tata kuwa ta yi nasara, domin lokacin da ta isa makarantar dan saurayin na zaune cikin sa rai da ganin wanda zai zo ya yi masa ciniki, don haka ta na tsayawa a karamar motarta kirar Toyota Starlet, ya zubawa motar idanu. Lokacin da Hannatu ta kashe motar ta turo kofar ta fito, sai ya yi wata nannauyar ajiyar zuciya, kana ya ce, "Kai, ka ga wata tsaleliya, tsada! Allah ya yi halitta a nan. Tsantsari!" Amma ko da ya fuskanci ta nufo shi sai ya yi sauri ya dauke kansa daga kallon ta a kokarina na kare mutuncinsa, don ba zai taba mantawa ba, akwai wata yarinya kyakkyawa da ya taba kallo ta tambaye shi "Mene ne ya ke kallon ta?" "Assalamu alaika." Hannatu ta yi masa sallama sa'ar da ta isa gare shi. "Wa'alaikis salam!" Habu mai kanti ya dawo da hankalinsa gare ta, "Sannu da zuwa." "Yauwa sannun ka, ya gari?" "lafiya sumul, ya hutu?" Ta yi yar dariya, "Malam, hutu ai sai ku." "Hajiya wane mu?" "Ba sunana Hajiya ba, sunana Hannatu." Yayi dariya "Ai idan na ce Hajiya ban yi laifi ba." Su ka yi yar dariya su dukansu. "Malam don Allah wata bukata ce ta..." "Ba sunana Malam ba, sunana Habu mai kanti kuma ki na iya kirana da "Harka". Ta yi murmushi "To Habu mai kanti kuma Harka, ina da bukatar yin wata magana da kai." "Ni?" Ya bukata cikin mamaki. "Kwarai, kai" "To Bismillah, wace magana ce?" "Dan samar mana abin zama mana?" Ta ce ta na duban sa. Ya waiga "Ga wani benci can mu karasa gare shi." Ya nuna wani benci da ke ajiye can gefen gindin wata bishiya. Su ka nufi bencin fuskar dan saurayin cike da mamaki. A lokaci guda kuma zuciyarsa na ta saka masa cewa. "Lallai ka yi sa'a ka sami kyakkyawa, idan ta ce ta na son ka kar ka kuskura ka yi sanya don auren irin wadannan na da ribobi. Ka ga na farko dai ko ba komai fuskarta da kirar jikinta ta shiga taro ce. Na biyu kuma daga duk inda ta fito yar mai abin hannunsa ce, ka ga shi kenan ka sami auren jari." Bayan sun isa ga bencin sun zauna sai Hannatu ta shiga gabatar ma sa da kanta, sannan daga baya sai ta shiga tambayarsa, "Habu don Allah ko za ka iya tuna adadin mutanen da su ka zo sayayya kantinka daga makon da ya wuce zuwa yau din nan? Misali daga ranar Litinin sha biyu ga watan sha biyun nan har zuwa yau?" "Eh...gaskiya ba zan iya tunawa ba, amma da ya ke ina rubuta duk abin da na sayar ba mamaki na gane." "To idan ka rubuta abin da ka sayar kana rubuta sunan wanda ka sayarwa ne?" "A'a" "To, ya za a yi ka gane?" "Wani lokaci idan na dauko littafin ina dubawa, zuciyata na kokarin tuna min kamannin mutumin da ya yi sayayyar, in dai ba lokaci guda mutane daban-daban su ka zo ba." Taq gyada kai "To yanzu za ka iya dauko littafin kenan?" "Me zai hana." Ya mike ya nufi kantin nasa. Ta bi shi da kallo har sa'ar da ya shiga cikin kantin ya dauko littafin, da sauri ya kuma nufowa wajenta, "Kin ga littafin." Ya mika ma ta bayan ya zauna. Ta kuma mayar ma sa, "To bude ka duba mana, a ranar sha biyu ga wannan watan su wane ne su ka zo su ka yi sayayya?" Ya karba ya fara budewa. Da ya zo shafin ya tsaya, "Kin ga mutum biyar ne kawai su ka yi siyayyar a ranar, da ya ke ban jima ba na rufe saboda tafiya da zan yi a ranar." Ta dan leka ta dubi littafin, "To za ka iya tuna mutanen?" "Da wa-da wa kenan?" Ta bukata a kagauce. "Kin ga dai wannan Naira hamsin din malami ne a nan makarantar, malam Ibrahim Mu'azzam ya sayi sabulu guda biyu GIV, wannan kuma Naira dari da Naira sha biyar din wata mata ce da ta kawo yara cikin wata mota Lexus, ta sayawa yaran alewa da biskit, wanan su ne kawai zan iya tunawa." Hannatu ta dube shi ido da ido, "Matar da ka ce ta zo da yara ya ya take?" "Su uku ne, mata biyu namiji daya. Abin da ya sa na tuna hakan, bana mantawa, biskit uku ta saya alewa biyu har na tuna ma ta cewa alewa uku ya kamata ta saya amma sai ta ce dai biyu zan kawo ma ta. To bayan na kawo ne da ta raba alewar yaron namijin bai samu ba, har zai yi ma ta kuka sai ta bude yar jakarta ta dauko ma sa wata alewar." Hannatu ta nisa bayan ya ida. Shakka babu yanzu ta sami abin da take so kuma ta nada tabbacin Hajiya Rukayya ce, saura da me? Ta dube shi "Habu za ka iya tuna kalar biskit din da alewar da ta saya?" "Sosai, ai ga sunan a rubuce, alewar "NANY" ce, shi kuma biskit din "Shortcake' ne". Ta gyada kai "Na gode, Habu yanzu saura taimakon da na ce za ka yi min." ya dube ta, "Fadi ina jin ki." "So na ke dan Allah ranar Alhamis ka halarci kotu dan bada wadannan shaidu domin..." Ya daga ma ta hannu. "Wace kotu ce?" "Arewa majistiri" Ya yi dariya, "Kin ce da ke za a tsaya ko?" "Kwarai kuwa." "To kar ki damu, idan Allah ya so zan zo to sai dai ni ma da bukatata gare ki bayan kammala shari'ar." Ya ce ya na dariya. Ta kalle shi, bayan ta mike tsaye "Mece ce bukatar taka?" "Wallahi kaunarki nake yi, yar kyakkyawa." Zuciyarsa ce ta fada. Amma a fili sai ya ce, "Ki dai bari sai ranar." "To Allah ya kai mu," Ta ce. Ya taka ma ta, su na hira har gindin motarta. Ta bude ta shiga, ta tashe ta, ta tuka ta bar makarantar cikin murna da ganin cewa kawarta za ta kubuta daga zargin da a ke yi ma ta. Shi kuwa dan saurayi Habu mai kanti ya bi motar da kallo yana ta murna ya sami budurwa kyakkyawa. ZAMAN KOTU NA BIYU A yau ma kotin ta arewa tak ta ke taf da jama'a, kusan ta fi zamanta na farko ma cika. Meyiwa hakan na da alaka da bazuwar da shari'ar ta yi ta hanyar mutanen da su ka halarci zamanta a karo na farko. Lokacin da lauyoyin su ka shigo kotun sai jama'a su ka shiga nuna su wasu da zunde, musamman ma Barista Hannatu da su ke ganin ta nuna bajinta a zaman farko. Kafin Barista Hannatu ta zauna sai da ta dubi jama'ar, ta dubi bangaren da Zainab ta ke ta yi ma ta murmushi ita ma Zainab da ke dauke cikin sarka ta mayar mata da murmushin da kyar, kana Hannatu ta zauna. Zamanta ke da wuya sai ta hango cikin jama'ar ana dago ma ta hannu, ko da ta lura da kyau sai ta ga ashe Habu mai kanti ne. Ta daga masa hannu ita ma cikin fara'a don ta yi matukar jin dadin ganin sa. Shi kuma ganin ta dago masa hannu sai ya yi ajiyar zuciya kana ya ce, cikin zuciyarsa. "Kai, Allah fa ya yi hallita a nan. Ni idan wannan tsaleliyar za ta amince ta aure ni, ai zan iya amincewa a tsire min idanuwana duka na daina ganin komai, tunda ina tare da kyakkyawa karshen kyau." Da misalin karfe goma da yan dakiku mai shari'a Mukhtar Kano ya shigo cikin dakin shari'ar. Kamar yadda ya ke, jama'a duk su ka mike cikin girmamawa. Bayan mai shari'a ya yi rankwafawar da ya saba cikin girmama jama'ar, sai suma su ka rankwafa a girmame, ya zauna kan kujerarsa kana kowa ya zauna. Kotun ta yi tsit. Bayan kotun ta samu nutsuwa, mai gabatar da shari'a Furoskito Nura Salihu ya mike hannunsa rike da takardu. "Yau ranar Alhamis ashirin da uku ga watan sha biyu, ita ce ranar da Shari'a ta ajiye don ci gaba da sauraron wannan kara, wadda ake tuhumar Zainab Ilyas amaryar Alhaji Basiru da yiwa yayan kishiyarta kisan gilla". Ya rankwafa girmamawa ka na ya kuma tsawatarwar da mai shari'a Mukhtar Kano ya yi, sai ya dubi Hannatu, "Kafin mu mika damar ci gaba da gabatar da shaidu ga Barista Garba ko ki na da wani abin da za ki ce?" Hannatu ta girgiza kai "Babu Yallabai. Sai dai ina so na yi tambaya ga shari'a ko ta samo wannan mata, Baraka?" Mai shari'a ya gyada kai "Kwarai an samo ta, shi kenan?" Ya bukata. "Ranka ya dade, shi kenan." Hannatu ta ce Mai shari'a ya dubi Garba "Bismillah". Garba ya mike, "Zan so na yi amfani da wannan dama, na yi kira ga shari'a kafin na ci gaba da gabatar da kwararan shaidun nawa. Babu shakka ya dace akwai kuma soyuwar a ce shari'a ta gane cewa, ba kowane dan Adam ne ke iya magana ko amsa tambaya cikin jama'a ba ba tare da ya yi rawar baki ba. Don haka ina kira ga shari'a da kar ta yi la'akari da gaza amsa tambayar da shaidun da zan gabatar za su.." "Ina da ja!" Hannatu ta mike "Ya zama wajibi na kalubalanci wannan sharhi da Garba ya yi. Ya mai shari'a babu yadda za a yi gumi ya karyowa mai gaskiya a cikin ruwa. Abin da nake nufi shi ne, ba zai taba yiwuwa a ce mutumin da ke da gaskiya ya gaza amsa tambayar da za a yi ma sa ko ya yi rawar baki yayin amsa tambaya ba, matukar ba haka halittarsa ta ke ba. "Don haka ina kira ga shari'a da ta yi watsi da wannan kira don babu wata fa'ida a cikinsa." Ta koma ta zauna. Garba ya yi murmushin karfin hali, "Shaida na farko da nake so na gabatar a yau shi ne direban gidan Alhaji Basirun, wato Lukman." Lukman ya fito ya hau mumbarin shaida. Garba ya dube shi "Lukman kai ne direban gidan Alhaji Basiru ko?" "Haka ne." Ya amsa. "Kai yara da dauko su ne kawai aikinka a gidan?" Ya gyada kai "Haka ne." "A ranar litinin sha biyu ga wata kai ka dauko yara daga makaranta?" "Eh, ni ne." "Shin ko ka ga wani abu a tare da yaran sa'ar da ka je daukop su a makarantar, abin nufi na dangane da ci ko sha?" "A'a." Ya girgiza kai. "Kuma ba su fada maka cewa akwai makamancin wannan abu tare da su ba, har sa'ar da ka kai su gida?" Ya girgiza kai, "Ba su fada ba." Garba ya yi ma sa godiya ya koma nya zauna. Hannatu ta mike "Lukman zan so na san wanda ya kai wannan yaran makaranta a wannan rana". Sai da ya dan jinkirta kadan, kafin ya ce wace Hajiya kenan?" "Hajiya ce." "Hajiya Rukayya." "Daman ita ta ke kai su?" "A'a... " ya girgiza kai, "Ni ne ke kai su". "To, menene ya sa ta kai su a wannan rana?" "Saboda bani da lafiya." Ya amsa kai tsaye. "To, ba ka da lafiya, wa ya je ya dauko su da rana?" "Ni...ne?" "Hakan na nufin ka samu sauki kenan?" "Eh." ya amsa da kyar gami da gyada kai. "Dangane da gurbin kwanan motocin gidan zan so na ji, dukkansu su na kwana gida ne ko akwai ma su kwana a wajenka?" "A'a, duk a gidan su ke kwana, babu mai kwana a wajena." Sai bayan ya amsa ne ya gane cewa ya yi kuskure, domin irin tambayar da ta yi ma sa ya kasa amsawa, ita ta ke shirin yi ma sa yanzu. "To, idan haka ne me ya sa a wannan rana ka tafi da mota gida? Ko daman ka san za ka yi rashin lafiya, kuma da rana za ka samu sauki?" Lukman ya hadiyi yawu da kyar, "Motar ta kwana wajena ne saboda..." ya yi shiru ya na kifkkifta idanu, kamar kwado. "Saboda me?" Hannatu ta dawo da hankalisa gare ta. Ya na rawar baki ya ce, "Saboda Hajiya ce ta ce na tafi da ita." "Wace Hajiyar?" "Hajiya Rukayya." Ba shi da zabi ya zama wajibi ya fada. Idanun Hajiya Rukayya su ka dada girma, ta dafe krji, alamun fargaba da mamaki. Ta mike tsaye "Wace Hajiyar, Ni?" Ta ambata cikin karaji, wanda hakan shi ya ja hankulan daukacin mutanen dake kotun zuwa gare ta. Ta juya kallonta ga mai shari'a. Ta soma rantse- rantse, "Alkali! Na rantse da Allah...wallahi karya ya ke yi min. Ni ban fada ma sa ya ta..." Buga gudamar da mai shari'a Mukhtar ya yi ne ta katse ta, tare da guna-gunin da jama'a su ka soma. "Zauna Hajiya!" Mai shari'a ya yi ma ta tsawa, "Kar ki kuma magana in dai ba tambayar ki a ka yi ba. Idan ba haka ba za ki fuskanci fushin shari'a." Ya gargade ta. Jama'a su ka kuma mayar da hankalinsu ga Hannatu da Lukman don jin mafadar wannan abu da ya soma ba su mamaki, ganin mai shari'a ya umarce ta da ta ci gaba da yin tambayoyinta. "Saki jikin ka malam Lukman, ko za ka sanar da mu dalilin da ya sa a wannan rana ita Hajiyar ta ce ka tafi da motar gida?" Ya girgiza kai, "A'a, wallahi ni ma ban san dalili ba. Ni ma na yi matukar mamaki,tunda tun da na soma tuki a gidan hakan ba ta taba faruwa ba." Da alama ya amsa kiran na Hannatu, na ya saki jikinsa tunda yanzu murya ba ta rawa. Kuma ko washe gari ba ka tambaye ta ba?" Ya girgiza kai, "Gaskiya ban tambaye ta ba saboda..." Ya yi shiru. "Saboda me?" "Saboda ta ba ni kudi. A yanzu ya kudiri aniyar fadar gaskiya, don haka ba ya fargabar duk abin da zai biyo baya. Mamaki ne ya kara bayyana a fuskokin jama'ar, kana hayaniya ta biyo baya. Mai shari'a ya tsawatar. Bayan an yi shiru, Hannatu ta ci gaba, "Kenan ya tabbata a wannan lokaci akwai abin da ta ke kullawa, wanda daga bisani shi ya yi sanadiyar ya yanta ko?" "Kin ga saurara Hannatu." Garba ya katse ta a fusace, "Ya mai shari'a ba zan taba amincewa da irin wannan tursasawa ba. Don kuwa ta nakokarin wanda ta ke yi wa tambayar ya tabbatar ma ta da abin da bai sani ba. Lallai wannan ya kauce layin da mu ke kai, ya dace a tsawatar ma ta." Mai shari'a ya tsawatar ga Hannatu. Ta yi godiya, sannan ta koma wajen zamanta, fuskarta cike da annuri, musamman ma ganin yadda ta fuskanci kan yan kallo ya fara wayewa. Garba ya ce, "Zan gabatar da shaida na gaba kuma na karshe, wanda kuma nake matukar fatan ganin cewa daga kansa kotu za ta fahimci gaskiya, ta kuma yanke hukunci ga wannan mata mara amana. Wannan mutum shi ne mai gadin gidan Alhajin." Duk da cewa jikinsa a sanyaye ya ke yanzu, a muryarsa ya na kokari domin ba ta sanyaya ba. Maigadi Bukar ya hau mumbarin shaida. Garba ya dube shi, "Malam Bukar mene ne aikinka a wannan gida?" "Gadi nake yi." Ya amsa kai tsaye. "Kullum kai ne a bakin kofar kenan?" "E, kwarai." "A ranar da wannan al'amari ya faru ko ka ga Hajiya Rukayya ta fita da mota, abin nufi ta tafi kai yara makaranta?" Ya girgiza kai "Gaskiya ban gani ba...ai bama ita ce ke kai yara makarantata ba." Garba ya gyada kai "Na gode." ya juya ga mai shari'a" (Matsala akasamu anan wacca badan itaba datini nagama littafin,amma saidai nanemi afuwa dan batawarwaru bakidayaba) "Abu na farko da za mu lura da shi shi ne, hana Lukman direba zuwa kai yaran makaranta da kuma mallaka masa mota ta kwana a hannunsa da zummar idan rana ta yi ya je ya dauko yaran, bugu da kari da kudin da ta ba shi. "Abu na biyu kuma hikimar aiken maigadi don kar ya ga sa'ar da ta fita zuwa kai yara makaranta. Abu na karshe, alewa biyu da ta saya wajen Habu mai kanti, a maimakon uku wanda hakan ya nuna kiri-kiri ta tanadi waccan muguwar alewa kamar yadda shi Habu ya ce ya ga ma sa'ar da ta dauko alewar daga jakarta. Kuma idan mu ka lura da bawon wannan alewa mai guba ya bambanta da wadda Hajiyar ta saya." Hannatu ta gabatar da bawon alewar ga mai shari'a kowa ya tabbatar ba iri daya ba ne da wanda Hajiya Rukayya ta saya a wajen Habu. Bayan an tabbatar ta ci gaba, "Daga karshe ina kira ga shari'a da ta kula da wadannan dalilai da su ka kama Hajiya Rukayya da yunkurin kashe dan kishiyarta wanda daga bisani reshe ya juye da mujiya." Hannatu ta koma ta zauna. Bayan yan rubuce-rubuce da mai shari'a ya yi sai ya juya kallonsa ga Barista Garba. "Ko kana da abin cewa?" Ya girgiza kai a sanyaye, "Babu ranka ya dade." Har yanzu akwai guna-gunin jama'a. Hannatu ta mike, "Ya mai shari'a zan so shari'a ta ba ni

Please Login or Register in order to submit comment