Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye likita Idris ya wuce ga kujerarsa da ta sa wani madaidaicin teburin da ke dauke da tulin takardu. Alhaji Gali da Alhaji Sambo su ka zauna a kujerun biyu da ke gefe da gefen madaidaicin teburin. Barista Hannatu da Zainab da Hajiya Rukayya su ka zauna a kan wata kujerar laushi da ke ajiye gefe guda. Likita Safina kuwa wucwe wa ta yi kusa da likita Idris ta tsaya. Bai bari shiru ta ratsa tsakanin zaman nasu ba, likita Idris ya fara da cewa," ko da ya ke mun bar zane tun ran gini saboda dalilai na rikicewa, ma'ana ba mu tambaye ku abin da su ka ci ya kawo mu su wannan matsalar ba tun a lokacin da na isa gidan dazu. To, amma duk da haka zan so sanin hakan yanzu, me su ka ci haka?" Shiru ba wanda ya amsa tsawon dakiku goma, kowannensu na kokarin tuno abin da ya san sun ci, musamman ma Zainab da Barista Hannatu da su ka kasance a waje yayin Faruwar al'amarin. Amma ita fa Hajiya Rukayya ko shakka babu ta san abin da su ka sha. Ta san alewa su ka sha, to sai dai ita ma abin da ta ke tunani shi ne, shin wai maigidanta shima Alewar ya sha? Alhaji Sambo ne ya kawar da shirun wucin gadin da ya fara ratsa tsakaninsu, bayan ya tuno abin da a iya saninsa shi ne abin da ya gani sun sha a gabansa. "Am...likita ni dai Alewa ce kawai na ga sun sha. Amma fa shi Alhaji ban da shi domin shi kawai dai ya raba Alewar ne da hakorinsa." "Alewa?" Likita Idris ya maimaita cikin mamaki. "Eh, Alewa." Alhaji Sambo ya tabbatar. "Wacce irin Alewa?" "Alewa dai da ka sani". Likita Idris ya nisa, "To, tabbas wannan Alewar akwai wata guba a cikinta, gubar da ke saurin kashe Dan Adam. A ina aka samu wannan Alewa?" "A'a, mu dai ba mu sani ba, yaron nan mujahid ne da ya ce ya na da Alewa da aka saya masa a makaranta da safe. Ganin zai yi rikici sai Alhaji ya sa mahaifiyarsa ta je ta dauko masa...ka ji yadda aka samu Alewar? Dasss! Kirjin Hajiya Rukayya ya buga. Yau shi kenan asirinta ya tonu. Da wanne za ta ji? Rashin lafiyar 'yayanta da maigidanta ko fallasa. Nan da nan sai ya nayi na nadama ya fara kore na damuwar da ke fuskarta. "Wace ce ta dauko Alewar?" Likita ya bukata. "Ni ce Likita". Zainab ta amsa kai tsaye "A ina ki ka saya masa ita?" "A'a, ba ni na saya masa ba...ina jin Hajiya ce ta saya masa lokacin da ta kai su makaranta, tunda..." "Wacce Hajiya...Ni?!" Hajiya Rukayya ta yi zumbur ta mike tsaye gami da dafe kirji. Babu shakka yanzu ne ya kamata ta kare kanta domin idan wannan damar ta wuce ta, to fa babu wata da za ta yi amfani da ita don yiwa kanta garkuwa. "Sam! Ni ba ni ba shi wannan shegiyar Alewar ba." Ta ci gaba cikin tsagalgalewa, "Ki nemi wanda ya ba shi tun dare bai yi miki ba. Ni da ba na ma falon ki ka dauko..." "Kin ga saurara Hajiya, Zauna." A wannan karon likita Safina ce ta katse ta, kana ta ci gaba, "Shi dai wannan al'amari koma dai ya ya ke wannan alewar ce ta zama sanadiyar mutuwar yan biyu da kuma sa Alhaji cikin halin kaka-na-ka-yi, halin mutuwa ko yau ko gobe..." Maganar likita Safina ta katse ganin dukkansu sun mike a firgice. "La'ilaha illalLahu". Hajiya Rukayya ta fada cikin daga murya, "Wayyo Allah...na ga ta kaina yau." yanzu ne ya kamata ta yi amfani da abin da zuciyarta ta kitsa mata. Nan da nan ta juya cikin rufewar idanu ta cakumi wuyan Zainab, cikin kukan ta ci gaba da cewa, "Ke munafuka, wallahi yau sai kin sanar da ni inda ki ka samu wannan Alewar ki ka kashe min 'yaya na da mijina, sai kin fada min...sai kin fada min!" Ta na yi ta na jijjiga ta. Barista Hannatu da Likita Safina su ka zaburo su ka rike hannun Hajiya Rukayya da ta shake wuyan Zainab. Da gumi da sidin goshi su ka bambare hannun. "Ni wallahi yau ba zan yarda ba...wallahi ba zan taba yarda ba, shegiya, tsinanniya, da ma ki na jin haushin yayan nan..." Ta kuma fashewa da kuka. Likita Idris ya mike daga kan kujerarsa, "kin ga Safina, ku je waje da ita." ya yi Umarni. Likita Safina da Barista Hannatu su ka janye Hajiya Rukayya su ka fice daga ofishin su na bata hakuri. Zainab kuwa tuni jikinta ya yi likis tana tsaye dafe da wuyanta ta na wani irin dan tari, da alama shakar da Hajiya Rukayya ta yi mata ta kai matuka saboda idanunta sun kada sun yi jajur. Yanzu ofishin ya yi shiru kamar ruwa ya shanye su, meyiwa maganganun da Hajiya Rukayya ta yi ne sunyi tasiri a zukatansu Don kuwa tuni wasu daga cikinsu sun shiga zargin Zainab din a matsayin ita ta sa guba a cikin muguwar Alewar. Likita idris ya nisa cikin rashin sanin abinyi, Hakika shi ma yan surutan da Hajiya Rukayyar ta yi yasa zuciyarsa ta fi karkata ga darasin da ke nuni da cewa Zainab ce ta samar da wannan Alewa, kuma yana zargin tayi haka ne ga hajiya Rukayya domin ta hallaka ta da yayanta. Ya dubi Zainab a sanyaye yace "Hajiya Zainab". ya nuna mata gun zama. Zainab ta zauna a sanyaye hannunta rike da wuyanta. "Alhaji". Likita Sambo ya ambata ya na duban su Alhaji Sambo da su ke zaune cikin mutuwar jiki. Su ka cira kai a hankali su ka dube shi. Babu wanda ya samu amsawa. "Ko da ya ke". Likita ya ci gaba, "Zainab ku ya kamata na tambaya." Ta cira kai a hankali ta dube shi. "Tsakani da Allah Zainab a ina kika samu wannan Alewar. Ki daure ki sanar da mu sai mu je har gurin domin daukar mataki ga mai sayarwar. Ta yiwu ke ba ki san mai guba ba ce." Zainab ta sa mayafinta ta goge hawayen da ke faman bulbulowa daga idanunta. Abin gwanin ban tausayi, ta soma magana, "Likita, na rantse da Allah ba ni na saya masa wannan Alewar ba, hasali ma ni ban san da ita ba sai a lokacin da aka ce na dauko. Wallahi...walla..." kukan da ta soma ya ci karfinta ya hana ta karasawa. "Kin ga malama saurara, babu wani kukan munafurci da za ki yi mana, kawai ki sanar da mu inda ki ka samu wannan guda." Alhaji Sambo ya ce da ita a kufule kuma cikin tsawa, don tuni shi ya sakankance a zuciyarsa cewa ita ce ta samar da Alewar, idan ba haka ba ai Hajiya Rukayya ba za ta sayo abin da zai kashe ma ta ya ya ba. "Kawai abin da ya dace ki sanar da mu kenan amma ba rantse-rantse da kukan munafurci ba." Shi ma Alhaji Gali ya dora cikin fushi. Zainab ta ji kamar gini ya ruguzo ma ta a ka, jiri mai tsananin gaske ya afka ma ta sakamakon wadannan maganganun da ta ji daga bakin mutanen da ba ta taba tsammanin za su zarge ta ba. Nan da nan sai ta ji wata marainiyar murya daga can cikin Zuciyarta da ke iya sa mai sauraro kuka ta fara ambatar, "Wayyo Allahna, yau ya zan yi da kaina. Ubangiji ka kawo mini dauki cikin wannan al'amari." Likita Idris ya kuma nisawa. Yanzu kuma hankalinsa ya fara rabuwa tsakanin yarda da rashin ta da cewa Zainab ce ta samar da Alewar, a dan nazarin da ya yi wa fuskarta a yanzu. "Hajiya." Ya kuma kiran sunanta. Ta dago kai ta dubeshi, har yanzu ofishin juya ma ta ya ke yi. "Yanzu ke kin tabbatar ba ke ki ka samar da wannan Ale..." "Ka ga likita saurara! Ai sam babu bukatar ta tabbatar tunda na fuskanci ba ta da shirin fadar gaskiya. Mu da aka yi komai a gabanmu?" Alhaji Sambo ya katse shi kana a na huci ya ci gaba, "Ka rabu da ita kawai Likita, idan mu ta ki sanar da mu ai ta sanar da hukuma ko?" Ya mike tsaye, "Tashi mu je Alhaji Gali." Alhaji Gali ya mike. Har sun kai ga bakin kofar fita daga ofishin, Alhaji Sambo ya juyo, "Za mu je ga jami'an tsaro Likita, don Allah ku ba Alhaji Kyakkyawar kulawa, yanzu za mu dawo." *** Karfe Bakwai saura minti biyar su ka isa babbar Hedikwatar yan sanda kamar yadda agogon da ke like a gaban motar ya nunawa kwayoyin idanun magidantan biyu (Alhaji Sambo da Alhaji Gali) wadanda su ka zo don kawo karar Zainab a matsayin matar da ta aikata kisan kai. Bayan samar wa motar kyakkyawan matsuguni cikin yalwatacciyar harabar ginin Hedikwatar, su ka bude motar su ka fito, a lokaci guda su ka mayar da murafen su ka rufe. Kallo daya za ka yi wa fuskokinsu ka tabbatar akwai gagarumar matsala da ke damun su. Kamar kurame su ka dubi junansu ba tare da sun yi magana ba, su ka tunkari wata yar majalisa da wasu yan sanda biyar su ka kafa, su na hira, meyiwa su na yi wa juna murnar busharar da shugaban kasa ya yi mu su ne akan karin albashi. Sa'ar da su ka isa ga yan sandan su ka yi mu su sallama duk sai su ka juyo gami da amsawa. "Sannun ku." Cewar Alhaji Gali. "Yauwa, Alhaji ya gari?" Cewar biyu daga cikin yansandan. "Ma su gidana don Allah mu na neman ofishin bincike ne game da kisan kai." "Ofishin ASP Haladu kenan ko?" Daya daga cikin yansandan ya bukata ga yan uwansa. "Eh, nan ne." Yan sandan su ka tabbatar ma sa. "Ya na cikin gidan nan kuwa? Anya bai fita ba?" Dan sandan ya bukata bayan ya dubi fuskar agogon da ke daure a hannunsa, "Yanzu fa karfe bakwai saura minti uku." "Kai ya na nan bai fita ba, ba ga motarsa can ba." Daya daga cikin yan sandan ya amsawa dan uwansa bayan ya kai dubansa ga tsiraran motocin da su ka sage a harabar. "Eh, kwarai bai fita ba." Dan sandan ya amsa, "Ku zo mu je mu je na raka ku." ya ce da su Alhaji Gali. Ya juya su ka ki shi a baya, su ka ratsa ta tsakanin wasu yan furanni da aka jera gefe da gefen yar siririyar hanyar da za ta sada mutum da makeken benen. Daraf-Daraf su ka haye, su ka nufi wani lungu. A can kuryar lungun ofishin ya ke. Manne a bango jikin wani katako da ke saman kofar ofishin kadan, an rubuta cikin manyan haruffa "HOMICIDE" kasancewar a bude su ka same shi ba su yi jinkiri wajen kunna kai ciki ba. Faffadan ofis ne kuma ciki da falo. A zaune su ka iske wani Dan sanda mai mukamin sajen (Igiya Uku) ya sanya dan madaidaicin tebur a gaba ya na ta faman rubuce-rubuce. "Wa'alaikumus salam." sajen Sani ya amsa sallamar mutanen uku bayan ya cira kai daga rubutun zuwa duban su. "Ah! Auwal ya aka yi?" ya mika wa kofur Auwal hannu. (Dan sandan da ya rako su alhaji sambo) . Su ma su Alhaji Gali su ka mika masa Hannu, su ka gaisa. "Don Allah ko mai gida na ciki?" Cewar kofur Auwal. "Ya na nan" Sajen Sani ya amsa kai tsaye. "Yauwa, dama wadannan bayin Allah ne ke son ganinsa" sajen Sani ya dubi agogon da ke daure a hannunsa. "Kai karfe bakwai fa yanzu, kai ma ka san ganin maigida ba zai yi wuya a yanzu. Sa'a aka yi fa yau mu na son kawo karshen wani bincikenmu akan wani kes (Case) da za a shiga kotu gobe, idan banda haka ai karfe uku mu ke tashi" "Gaskiya da farko ni ma na dauka kun tashi" cewar kofur Auwal. Ya juya ga su Alhaji Gali "Alhaji Me zai hana gobe ku dawo da wuri ku gan shi, kun ga yanzu dare ya kawo kai.." "Don Allah yallabai a taimaka mana mu gana da shi yanzu, wani gagarumin al'amari ne..wata mata ce ta kashe yayan kishiyarta biyu da kuma jefa mijinta cikin gagarumin hadari. Don Allah a taimaka kar kafin goben ta gudu" Alhaji Sambo ya ce a sanyaye cikin muryar roko. Idannun yansandan ne su ka kara girma (alamun mamaki da tsoro) Hakika babban kes ne, ya kamata su bi diddiginsa. Sajen Sani ya rufe littafin da ya ke rubuta a ciki ya mike tsaye da gaggawa, "Ina zuwa" ya ce kana ya nufi kofar da ke like cikin ofishin nasa wadda kuma ita za ta sada shi da maigidan nasa ASP Haladu. Ya turo kofar ya rufe bayan ya shiga. Ya kame ga mutumin da ke zaune kan wata babbatar kujerar laushi, damfareren teburin da ke take da takardu durkushe a gabansa. "Sani ya ya?" ASP Haladu ya bukata. Ya saki jikinsa daga kamewar da ya yi, "Yallabai wasu ne dauke da wani muhimmin kes, su ke son ganin ka" "Yanzu abin da na ke so da ku." ya mayar da dubansa gare su, "Ku tashi maza ku koma asibitin, ku tattara kawunanku gaba daya ku hallara a gidan, don nan da karfe takwas zuwa tara za mu zo domin yin bincike." Ya dubi agogon da ke rataye jikin bangon ofishinsa, "Kun ga yanzu bakwai har da kwata." "To yallabai." su ka amsa kusan a tare." "Har fa gawar yaran mu ke so a mayar gidan. Ku yi maza don Allah." ya rufe littafin da ke gabansa. "An gama yallabai." Su ka kuma ambata, kana su ka nufi kofar fita. Su na fita ya janyo wayar sadarwar da ke dare a kan teburin ya soma laluban lambobi cikin sauri. *** Tunda Motar yansandan da ke dauke da yansanda hudu ta shiga faffadar unguwar, Sifeto Habibu da ke zaune a kujerar gaban motar ya ke ta rarraba idanu cikin fatan ganin lamabar da aka ba shi wadda aka ce ita ce lambar gidan Alhaji Basiru. Abinka da unguwar masu hannu da shuni, shiru babu motsin komai sai haushin karnuka da ke tashi lokaci-lokaci. "Tsaya mun zo gidan." ya ce ya na duban Direban bayan ganin lambar da maigidansa ASP Haladu ya ba shi sakale jikin kofar gidan da su ke kokarin giftawa. "No 20 B KNS." ya kuma ambatar lambar a fili, ya na duban wadda ya rubuta jikin wani dan littafi da ke rike a hannunsa, a lokaci guda kuma ya na duban wadda ke makale jikin kofar. Tabbas yanzu ya yarda gidan ne, don haka sai ya umarci Direban da ya gyara tsayuwar motar a gaba da gidan kadan. Ba gaba dayansu ne ba ne sanye da kayan aiki a jikinsu. Su ka mayar da murafen motar su ka rufe. Sifeto Habibu ya jagorance su har bakin makekiyar kofar. Sau daya kawai ya kwankwasa kofar, jim kadan sai su ka ga ta bude. Ba su yi mamakin hakan ba don sun san an san da zuwansu. Maigadi Bukar ne ya bude kofar. "Sannunku da zuwa." Ya ce da alamun mamaki a fuskarsa. Meyiwa saboda ganin su da ya yi ba yadda ya zata ba, cikin fararen kaya, "Ince dai ko kune jami'an tsaron". "Eh, mune Baba". Daya daga cikin su ya bashi amsa a takaice. "Bari nayi muku jagora zuwa ciki". "To, Baba." Sifeto Habibu ya amsa. Har maigadi Bukar ya shiga gaba da zummar su bi shi zuwa ciki, sai Sifeto Habibu ya ce, "Baba kafin mu shiga ciki ina so na yi ma wasu yan tambayoyi a matsayinka na maigadin wannan gida." Maigadi Bukar ya tsaya, "To, Dan nan, Allah ya sa na sani." Sifeto ya yi murmushi, "Ai sanannen abu ne a gare ka domin kuwa adadin shekarun da ka kwashe kana aiki a wannan gida na ke so mu sani." "E to! Ku san ni ne maigadi na farko tun gina gidan." "kusan ne, ko kuma kai ne?" Sifeto Habibu ya nemi tabbaci. "To, ni ne". "To Baba da ya ke kai ne maigadi tun farko, ko ka san wani abu game da Alhaji da matansa?" Shiru tsawon dakiku bai amsa ba, can ya nisa, "Yallabai ka san tsakanin miji da mata sai Allah, gaskiya ni kullum ina nan bakin kofa, zai yi wuya na san abin da ke gudana a ciki, sai dai kawai na san kirki da rashin kirkin kowacce a cikin matan. Idan shi ka tambaye ni zan iya fada ma. Tunda mai kyauta da mai rowa ma Allah Bai yi su daidai ba." Kusan dukansu sai da su ka yi murmushi. "Banda wannan Baba." Sifeto Habibu ya ce, "To, bayan kai akwai wani ma'aikaci a gidan?" "Eh, kwarai kuwa, akwai abokin aiki na amma shi ya jima da rasuwa, don yau..." ya cira kai sama alamar tunani, "Ina ga zai kai shekaru kamar bakwai da rasuwa." A wannan karon kusan ya ba duk yan sandan haushi, musamman Sifeto Habibu da shi ya ke tambayoyi. "Banda wanda ya rasu Baba. Bayan wannan ba wanda ya ke aiki a gidan ko da ba irin naka ba?" "Eh, lallai akwai Lukman, amma shi Direba ne." Sifeto ya gyada kai, "Ko ya na nan yanzu?" "A'ah ba ya nan, don shi rabonsa da gidan nan tun da rana da ya dauko yara daga makaranta, kuma shi da ma haka al'adarsa ta ke, idan ya kai yara makaranta ya koma da rana ya dauko su to aikinsa ya kare sai kuma gobe. Shi ya sa ko dazu ma da za a kai su Alhaji asibiti sai wata Bakuwar Hajiya Karama (Zainab ya ke nufi) da kuma kanin Alhaji ne su ka ja motocin" Sifeto Habibu ya nisa gami da gyada kai alamar gamsuwa, "Wato yanzu kai kana nufin shi Lukman ba ya nan abin ya faru?" "Sosai" In ji maigadi Bukar. "To Baba na ji kuma kawar Hajiya Karama, wace ce Hajiya Karama?" "Amaryar Alhaji Kenan" Ya amsa cikin dariya, "Ita a ke cewa Hajiya Karama, amma ni kadai na ke fada mata saboda la'akarina na ga cewa ita ta zo gidan daga baya" "To, ita wannan kawa ta Hajiya Karama ko.." "Ba fa sunanta Hajiya Karama ba, ni kadai na ke fada mata. Sunanta Zainab" Maigadi Bukar ya katse Sifeto Habibu. Sifeto Habibu ya yi dariya, "To, ita kawar ta Zainab ya sunanta?" "In ga?" Ya yi jim, "Sunanta Hannatu" "Kar dai ka gaji Baba, kasan aikin da mu ka zo yi kenan, ko za ka iya tuno tsawon lokacin da ita Hannatun ta dauka a cikin gidan, ma'ana tun yaushe ta zo, kuma yaushe ta fita?" "A'a dama ita al'adarta tunda na san ta, idan ta zo tun safe ba ta barin gidan nan sai yamma likis. To yau din ma ina zaune anan daidai lokacin da ta saba tafiya sai na ga sun fito gaba daya cikin halin rikita. To! Ka ji." Kusan gaba daya duk wanda ya kasance a falon yayin da al'amarin ya faru dazu, ya na cikin falon yanzu idan ka duke Barista Hannatu da kafin su Alhaji Sambo su koma asibitin ta tafi gida, sai kuma Hajiya Rukayya da ke can dakinta a kwance kasancewar ciwo da ta ce kanta na yi. Bayan yan gaishe-gaishe da jajantawa da yan sandan su ka yi ga mutanen da su ka iske a falon sai jagoran tafiyar, Sifeto Habaibu ya bukaci ganin gawarwakin su Hauwa'u. Ba tare da bata lokaci ba, Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka kai yan sandan wani daki da ke like cikin falon inda anan ne su ka shimfidar da gawarwakin. Lillibe da farin kyalle su ka iske su. Sifeto Habibu ya isa gare su ya duka a hankali ya yaye kyallen iya fuskokinsu. Idanunsu duk a rufe su ke. A hankali ya mayar ya rufe kana ya mike ya dubi jama'ar tasa. "Doctor Nasir." Ya kira sunan daya daga cikin su. "Na'am yallabai." wani dan dogo ya amsa. "Ina so ka yi mana kyakkyawan bincike akan wadannan." ya nuna gawarwakin, "Mu za mu koma falon." "An gama yallabai." ya ware daga cikin yan uwansa ya nufi gawarwakin, daidai lokacin da su Sifeto Habibu da sauran yan sandan su ka fice daga dakin zuwa falon. Har yanzu Zainab da ke zaune kan daya daga cikin kujerun falon na nan, ta zabga tagumi, hawaye sai kwaranya ya ke daga idanunta, danta Mujahid zaune kusa da ita, shi ma ya na kuka, meyiwa saboda ya ga ta nayi. Bayan sun kuma zama sai Sifeto Habibu ya dubi Alhaji Sambo, "Alhaji da ya ke kai ne kanin maigidan nan uwa daya uba daya, ko za ka iya sanar da mu iya adadin yan uwansa bayan kai?" ya girgiza kai, "Babu yallabai, mu biyu ne kawai a wajen iyayenmu." "To, su iyayen naku su na nan a raye?" "A'a, sun jima da rasuwa, don ni ban ma san su ba, tun ina karami su ka yi hadarin mota su ka rasu." Sifeto Habibu ya gyada kai, "To, bayan wannan ko ka san wani mutum da su ke muhimmiyar alaka da shi." "Su na da yawa, ga daya ma kusa da ni. Shi ne ma babba daga cikin aminansa." Ya nuna Alhaji Gali. Shi kuwa ya yi dan Murmushi. Sifeto ya kalle shi, "Alhaji kasancewarka aminin Alhaji fiye da kowa cikin aminansa, bai taba sanar da kai cewa akwai wani abu da ke damun sa ba, kafin wannan abin ya faru da shi?" ya girgiza kai, "Bai taba ba, sai dai kawai matsaloli na gida da ya ke yawan kawo min, ina nufin game da iyalansa." "Matansa kenan?" Bukata daga Sifeto Habibu. "Eh." Amsa daga Alhaji Gali. "Kamar wace irin matsala ya ke yawan kawo ma game da su?" "Rashin zaman Lafiya a tsakaninsu." "Kamar ya ya?" Sifeto ya bukata bayan ya ware hannuwa. Sai da ya yi gyaran murya domin bai yi tsammanin Sifeto zai nemi sanin irin matsalar ba. "Kamar yawan rikici da su ke..." "Na gane wannan." Sifeto Ya katse shi, "Game da me su ke yin rikicin?" Alhaji Gali ya dubi Zainab, "Kamar ita amarya da ta ke shan tsangwama da matsi daga uwar gidan..." "wato dai ka na so ka ce uwar gidan ce ke haifar da matsalar." "Eh, haka ne." Sifeto ya gyada kai bayan ya dubi dan sandan da ke ta faman rubuce-rubuce. Ya mayar da dubansa ga Zainab da har yanzu ke ta faman zubar da hawaye. Ba wani abu ne ya sa ta cikin wannan ya nayin ba sai sharrin da aka kulla mata, ita a rayuwar duniya ba abin da ta tsana irin a ce ta yi abin da ba ta yi ba. "Wannan wacce ce daga ciki?" Sifeto ya nuna Zainab. "Ita ce Zainab, amaryar kenan". Alhaji Sambo ya amsa. "Sannu amarya." sifeto Habibu ya ce da ita, "Ya mu ka kara ji da hakuri." "Hakuri sai Ma'aiki." Ta amsa da kyar cikin muryar kuka. "Hajiya, mu ma'aikata ne kamar yadad ki ka sani, mun zo ne domin warware wannan dambarwa musamman ma ga ke da ake zargi a matsayin matar da ta aikata kisan kai..." Zainab ta girgiza kai, "Wallahi Yallabai ba ni ba ce hasalima ni ban san da wata Alewa ba sai da aka umarce ni na dauko." Ta fashe da kuka. "Ya isa Hajiya." Sifeto Habibu ya dakatar da ita ganin kukan na kokarin tsawaita, "Ba kuka za ki yi ba. Abin da kawai na ke so ki gane shi ne, hukuma ba ta yankewa mai laifi hukunci har sai ta yi bincike ta tabbatar da laifinsa. To daga nan kuma sai ta hukunta shi daidai da abin da doka ta shimfida." ya tsagaita, kana ya ci gaba ganin ta sassauta da kukan, "Hajiya kin ce ba ki san da wannan Alewar ba a farko har sai lokacin da aka umarce ki da ki dauko ko? Ta gyada kai. "To, wane ne ya umarce ki ki dauko?" "Alhaji ne." "Alhaji? Maigidanku kenan?" "Eh." "To shi ya aka yi ya san da Alewar?" ta yi shiru na dan lokaci kana ta ce, "Shi ma bai san da ita

Please Login or Register in order to submit comment