Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gyada kai, "To na ji kin ce ki na neman taimako, na mene ne?" Ta kura masa idanu, "Likita, idan dai har da yiwuwar hakan ina so ka ba ni sakamakon da ka samu na wannan guba a rubuce." Bai yi tsammanin shi ne taimakon da za ta nema ba. Ya yi murmushi, "Barista wannan ai mai sauki ne, bari na ga?" Ya jawo dan abin adana takardu da ke makale jikin teburinsa, ya dauko wani fayal kana ya mayar ya rufe, kai tsaye ya bude fayal din ya fara bincike. A hankali ya zaro wata takarda a ciki, ya yi dan nazarinta. "Barista wannan shi ne sakamakon." Ya mika ma ta. Ta sa hannu ta karba ita ma ta yi nazarinta. Ta cira kai ta dube shi, "Likita ya za a yi na samu kwafin wannan takarda?" "Kamar yaushe ki ke so?" "Ko yanzu ma." Ya nisa, "To za ki iya jira na na rubuta miki wata?" "Me zai hana?" Ya mika hannu ya karbi takardar, kana ya dauko wata takardar cikin gaggawa ya soma rubutawa. Bai dau lokaci mai tsawo ba ya kammala, ya mika ma ta. Ta karba, "Na gode likita." Bayan ta dan dudduba ta mike tsaye, "Ni zan tafi." Shi ma ya mike, "To barista, godiya na ke." "Ni ce da godiya." Ta ce ta na murmushi. Har ta kai ga bakin kofar ficewa daga ofishin sai ta juyo, ta dubi Likita Idris wanda tuni ya zauna, "Likita Alhaji Sambo da Alhaji Gali fa, ko su ke jinyar Alhajin?" Ya gyada kai, "Su ne, kuma su na nan don dazu na shiga wajen na gan su." Ta kama hannun kofar ta murda, "A daki na nawa su ke?" "Daki mai lamba na ashirin da daya." Ta gyada kai, "Na gode." kana ta bude kofar ta fice, ta nufi dakin da likitan ya sanar da ita da zummar ganawa da Alhazan biyu, mutane na uku cikin rukunan mutanen da ra ke son ganawa da su. Lokacin da ta isa ga dakin ta tura kofar ta shiga, su na zaune su uku, Alhaji Gali, Alhaji Sambo da Hajiya Rukayya, a kan kujera. Shi kuma Alhaji Basiru kwance ya na barci, robar karin ruwa makale a hannunsa. Salla ta yi mu su. Da kyar su ka amsa kamar an yi musu dole musamman ma Hajiya Rukayya da ke kallon Hannatun a wulakance. Ba ta damu da abin da su ka yi mata ba ko kadan, maimakon hakan ma sai ta ce, "Sannunku Hajiya! Ya me jikin?" "Jiki da sauki". Alhazan biyu ne su ka amsa, don ita Hajiya Rukayya ma dauke kanta ta yi gefe guda. Ta isa ga wata kujera daidai lokacin da take cewa, "Allah ya kara sauki." "Ameen." Su ka kuma amsawa. Ta zauna a hankali ita ma ta yi shiru kamar yadda su ka yi, tsawon dakiku talatin su na a haka. Can ta nisa ta dubi Alhazan "To! Ni zan koma, Allah ya ba shi lafiya." "Ameen". Su ka amsa. Ta mike a hankali ta kuma mayar da dubanta gare su, "Alhaji don Allah ina da bukatar tattaunawa da ku." kafin su yi magana. Hajiya Rukayya ta kalle ta da sauri, "Kamar ya ya ki na son ganin su su na zaman jinya? Idan wata magana ce ki yi anan mana." Ta yi murmushi, "Hajiya ba wani lokaci za a dauka ba. Ga ni na yi bai kamata mu yi a nan ba saboda mara lafiyar." Ta daka ma ta harara, "To ba za su..." "Ya isa Hajiya." Alhaji Gali ya dakatar da ita, "Bari mu je." ya taba Alhaji Sambo, "Tashi mu je." Su ka mike. Hannatu ta dubi Hajiya Rukayya, "To Hajiya sai an jima, Allah ya sauwake". Ta muguda baki, "Amin idan da gaske ki ke." Barista Hannatu ta juya su ka bi ta a baya zuwa waje. Wani dan benci su ka samu bayan sun fito farfajiyar asibitin. "Bismillah ga wajen zama!" Ta nuna musu dogon bencin. Bayan sun zazzauna, ta gabatar mu su da kanta a matsayin lauyar da za ta ba kawarta Zainab Kariya. Sun yi mamaki...ba su yi mamaki ba. Mamakin da su ka yi shi ne, ya za a yi Hannatu ta ba matar da a ka tabbatar da ita ta bayar da wannan guba kariya..ta wace hanya? Rashin mamakin kuwa shi ne. Dole ne ta yi hakan musamman da su ka duba cewa kawarta ce. "Ina so na yi muku wadansu Yan tambayoyi ne." Ta ci gaba bayan sun fahimci ko ita wace ce. "A game da me fa?" Alhaji Sambo ne ya bukata. "A game da abin da ya faru shekaran jiya, kasancewar ku na cikin falon abin ya faru." "To mece ce tambayarki?" Ya kuma cewa, a hasale ya ke maganar. Ta shafi goshinta "Alhaji a matsayinku na wadanda mu ka bari a falon, bayan fitar mu, ya a ka yi su Alhaji su ka kasance cikin halin da mu ka dawo mu ka riske su?" Alhaji Gali ya dube ta, "Su yaran kawai gani mu ka yi sun fadi, kuma Alhaji da farko cewa ya yi cikinsa ya na ciwo, kamar wasa shi ma sai ya fado daga kan kujera, duk kuma a kusan lokaci guda." "Daga nan kuma sai a ka yi ya ya?" Ta ce ta na kallon su ido cikin ido. "Daga nan sai mu ka jiyo Ihun Hajiya Rukayya, sannan kuma sai mu ka ga sun shigo falon." Barista Hannatu ta shafi kuncinta, "Don Allah ko za ku iya tuna abin da Hajiya Rukayyar ke ambata cikin ihun nata?" Shiru su ka yi na dan lokaci kana Alhaji Sambo ya ce, "Kwarai na tuna." "Me ta ke cewa?" "Cewa ta ke kar ku sha alewar nan, alewar ba ta da kyau." "Me ya sa ta ce hakan, daman ta san ba ta da kyau ne, ko kuwa?" Shiru su ka kuma yi su ma su na tunanin abin a zuciyarsu. "Haka ne fa! Ya aka yi ta san alewar ba ta da kyau." Zuciyar Alhaji Sambo ce ke juyayin abin. Lallai akwai alamar tambaya anan. Ganin sun yi shiru babu amsa, sai Hannatu ta ce, "To idan wannan ma ba komai ba ne, ko za ku iya tuna abin da Hajiyar ke fada cikin surutunta na jiya yayin da mu ke zaune muna jiran fitowar likita?" Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 4 Posted by ANaM Dorayi on 11:16 AM, 29-May-15 su na da yawa Hannatu wanne daga ciki?" "Ba ku ji ta naambatar Baraka cikin sambatunta ba?" "Lallai mun ji." su ka amsa a tare bayan sun tuna. "To wace ce Baraka da har Hajiya Rukayya ke cewa, Baraka ya haka?" Basu da amsa kuma shi ma lallai sun tabbatar abin tambaya ne. "Ba mu san ta ba Hannatu." Alhaji Sambo ya ce a sanyaye, yanzu kusan duk jikinsu ya yi sanyi kuma hakika su na son wadannan amsoshin, to sai dai duk wannan kafin su hada ido da Hajiya Rukayya ne, tuni za su manta. Barista Hannatu ta nisa, "To shi kenan na yi matukar godiya da wannan lokaci da ku ka ba ni, ni zan koma." Ta mike, su ma su ka yi godiya su ka koma ciki cike da raba daya biyu a zukatansu. Bayan ta bar asibitin, ba ta zame ko ina ba sai ofishinta na musamman da ke kan titin Gwarzo domin tattara abubuwan da ta samu, da ya ke sha biyun rana ta yi, idan ya so daga bisani idan yamma ta yi sai ta tafi ga mutun na karshe a cikin bincikenta, wanda ke sayar da kayan lashe- lashe a makarantar su Mujahid. Bayan an yi sallar La'asar ta bar ofishin ta nufi makarantar, sai dai ta yi matukar takaici da aka shaida ma ta saurayin Habu mai kanti ya yi tafiya, kuma ba zai dawo ba sai gobe. Haka ta hakura ta baro makarantar ba tare da ta sami komai ba. ZAMAN KOTU NA FARKO Arewa majistiri, Babbar kotu ce da ke da fadi da tsayin gaske. A bisa kiyasi kotun ta na daukar a kalla mutane dari da hamsin. Amma a yau take ta ke da yan kallo, haraba da wajen ta, babu masaka tsinke. Misalin karfe tara daidai babbar bakar motar yansandan (Irin wadda ake daukar yan fashi) ta shiga farfajiyar farko da aka tanada don ajiye motoci. Tsayawarta ke da wuya wasu dandazon jama'ar da su ka makara da shiga kotun su ka zubawa motar idanu. Bayan kashe ta, yan sandan dake ciki su ka fito da Zainab da ke daure da ankwa a hannu daga bayan motar, kai tsaye su ka shige da ita cikin kotun, da kyar da turereniya, saboda tasowa da jama'ar su ka yi cikin hargowa, wasu na la'antar ta da tsinuwa, wasu kuma na zagin ta gami da Allah wadai. Su kuwa lauyoyi tuni sun hallara a sababben dakinsu tun kafin isowar yan sandan. Rabin sa'a da zuwan yansandan mai shari'a Mukhtar kano ya iso, kai tsaye shima ya shige cikin dakin da aka kebe masa kafin shigowa dakin shari'a. Jim kadan lauyoyin su ka shigo cikin kotun, su ka zazzauna a kebabben wajensu. Barista Hannatu, lauyar da ta shigo dakin shari'ar yau don kare kawarta, fara ce kyakkyawar gaske, ta na sanye da irin bakaken kayansu da su ka yi matukar yi mata kyau. Ta na rike da takarda, farin gilashi dane a fuskarta. Sai dai kuma babu fara'a a tare da fuskar tata, meyiwa saboda ta san ita ce ke da karancin magoya baya a cikin kotun, musamman da ta yi la'akari da yadda aka rika sanar da shari'ar a kafafen yada labarai na cewa, ana zargin kawarta da laifin kashe yayan kishiyarta har da yunkurin kashe mijinta. Mintuna biyar su ka rage karfe goma ta cika, mai shari'ar ya shigo cikin dakin shari'ar. Wannan ya sa jama'ar dake dakin gaba daya su ka mike cikin mutuntawa. Mai shari'a ya dan rankwafa cikin girmamawa ga jama'ar, su ma su ka rankwafa cikin karamci kana ya zauna, su ma su ka zauna. A yanzu dakin shari'ar tsit ya ke kamar babu kowa, don son jama'a na jin me zai biyo baya. Koda aka tabbatar kowa ya nutsu, sai me karnto shari'ar Furoskito Nura Salihu ya gabatar da shari'ar da za a yi kamar haka: "A yau litinin ashirin ga watan goma sha biyu shekara ta dubu biyu da uku (20/12/2003) za mu saurari shari'ar Hajiya Zainab Iliyasu Umar a kan zargin da ake yi ma ta na kisan yayan kishiyarta guda biyu, wato Hajiya Rukayya da kuma yunkuri ko saka mijinta a halin kaka-ni-kayi, wanda har zuwa yanzu ya na kwance rai a hannun Allah." Bayan kammalawarsa sai hayaniya ta kunno kai tsakanin jama'ar kowa na fadr albarkacin bakinsa cikin tsana da kyamar Zainab. Idan ka dauke mahaifin Zainab, Malam Iliyasu Umar da Iyalansa, babu wanda ba ya surutu a dakin shari'ar. "Kamar yadda mai gabatarwa ya gabatar." Mai shari'a ya soma, bayan ya tsawatar an yi shiru, "Yanzu ba tare da bata lokaci ba, za mu saurari karar daga bakin jami'in tsaron da ya shigo da ita, wato Sufeto Habibu." Wani dogon Dan sanda ke zaune a gaba-gaba ya mike, hannunsa rike da wasu takardu, ya nufi mumbarin da masu amsa tambaya ke hawa, ya hau. Bayan an rantsar da shi, ya soma gabatar da karar cikin daga murya. "Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, da ya ba mu dama da ikon kammala wannan bincike, akan wannan mummunan laifi na aikata kisan kai, ta sigar yaudara, wanda Zainab Iliyas ta yi ga yayan kishiyarta Hajiya Rukayya. "Ya mai shari'a wannan al'amari ya faru ne a yammacin ranar lahadi sha biyu ga watan biyu na wannan shekarar. "Kamar yadda sakamakon bincike ya nuna akan wadda ake zargin (Zainab) ta samar da wata Alewa ne mai guba, da ita ce ta kai yaran ga mutuwa. "Hujjojin da ke hannunmu zuwa karshen wannan bincike namu, wadanda da su mu ka dogara wajen shigo da wannan kara su ne;- (Dan Allah kuyimin afuwa nangun ya yanke) "Zan fara da gabatarwa da shari'a kaina". Ta ci gaba, "Sunana Barista Hannatu, lauya mai zaman kanta. Na dauki wannan bangaren ne na ba wadda ake zargi kariya kasancewar har zuwa yanzu babu wata kwakkwarar hujja ta zahiri da ke nuna cewa, Zainab ita ta samar da wannan alewar. Sannan ina kira ga shari'a da ta yi duba da cewa, duk fa abin da a ka ce zargi a ke yi, bai tabbata ba kenan, akwai bukatar samun tabbaci tun kafin a shigo nan. Don haka ina fatan kotu ba za ta damu da duk wadannan abubuwa ba tunda an nuna ba a bincika an tabbatar ba. Idan kuwa haka ne akwai bukatar shari'a ta yi kyakkyawan duba ga ingantattun hujjojin da za a gabatar ma ta domin tserewa da gudun afkawa ga dorawa mara laifi, laifi. Na gode!" Ta koma ta zauna. Duk da cewa wannan jawabin nata kusan bai gamsar da kowa ba, da alama shi mai shari'a ya gamsu. Za ka gane haka ne ta hanyar gyada kai da ya yi, ya kuma duka ya yi yan rubuce-rubuce. A hankali ya dago ya dubi Barista Garba Shehu, "Shari'a ta baka dama ka fara gabatar da shaidunka yanzu." Garba ya mike ya fara takawa a hankali. "Da ya ke shari'a ta amince zan fara gabatar da mutane biyu a matsayin shaidar farko, amma daya bayan daya. Mutanen kuwa su ne, Alhaji Sambo kanin maigidan wadannan mata, uwa daya uba daya, da kuma Alhaji Gali babban aminin mijin wadannan mata. Amma da ya ke na ce daidai da dai-dai, za mu soma da kanin magidancin." Alhaji Sambo da ke sanye da manyan kaya (Malum-malum) ya mike ya nufi mumbarin shaida, ya shiga ya tsaya, aka rantsar da shi. Garba ya isa gare shi, "Ko za ka iya tabbatarwa da shari'a matsayinka ga Alhaji Basiru, mai gidan wadannan matan?" "Kwarai kuwa!" Ya ce ya na gyada kai. "To za mu so hakan." "Ni dai uwarmu daya, ubanmu daya." Ya fada a takaice. Garba ya gyada kai "Da kyau! Kasancewarka ka na daga cikin mutanen da su ka tsinci kansu cikin wannan falo yayin faruwar wannan al'amarin, ko za ka iya sanar da mu yadda abin ya faru?" "Tabbas zan iya". Ta ke ya zayyanewa kotu duk yadda a ka yi har zuwa sa'ar da su ka dunguma asibiti. Garba ya nisa cikin gamsuwa "muna godiya." Har ya yunkura da zummar sauka daga kan mumbarin shaidar sai ya ga mai shari'a ya juya ga Hannatu, "Ko ki na da bukatar tambaya?" Ta gyada kai kana ta mike, ta nufi mumbari. Bayan ta isa ta ce, "A matsayinka na wanda ya ke cikin falon abin ya faru ko za ka iya sanar da mu wanda Zainab ta dankawa wannan alewa sa'ar da ta shigo falon?" Ya gyada kai "Lallai kuwa". "To wane ne?" "Mujahid ta ba." "Mujahid dan wane ne?" Ta bukata. "Dan ta ne." ya amsa. "Kenan mutum zai iya daukar gubar mutuwa ya ba dan da ya haifa a cikinsa, musamman ma uwa da danta...?" "Malama saurara!" Garba ya mike, "Ya mai shari'a ina so kotu ta lura da cewa, wannan tambaya da aka shigar yanzu ta sauka daga kan asalin turbar da mu ke don kuwa me tambayar ta tambayi abin da ke cikin zuciya ne, kuma shi sanin gaibu sai dai Allah, Lallai ya dace a duba, wannan abin tsawatarwa ne." Mai shari'a Muktar Kano ya dubi Hannatu gami da tsawatar ma ta, da kar ta kuma irin wannan tambayar. "Na daina ranka ya dade." Hannatu ta ce kana ta kuma mayar da dubanta ga Alhaji Sambo. "Alhaji a lokacin da wannan al'amari ya faru an ce Hajiya Rukayya ta na waje, haka ne?" "A'a tana kicin dai." Ya gyara ma ta. Ta gyada kai "Ma'ana dai ba ta falon ko?" "Yaron nan mujahid ne ya fita da kukansa ya je ya sanar ma ta. Shi ne ta taho a guje." Ta gyada kai, "A lokacin ta taho ta namagana, ko za ka iya tuna abin da take fada...?" "Ya mai shari'a." Garba ya yi caraf ya cafe, "Kamar yadda na sanar yanzu, wajibi ne kotu ta dauki tsauraran matakai kan irin wadannan tambayoyin domin kauracewa afkawa rudani." Mai shari'a ya dubi Garba ya ce, "Ina so ka fahimta cewa, ba kowace irin tambaya ce ta sabawa doka ba, irin wannan tambayar akan hanya ta ke, don haka kai ma ka kiyaye." Barista Garba ya koma ya zauna cikin damuwa ganin mai shari'ar ya ba Hannatu damar ci gaba. Hannatu ta ci gaba, "To Alhaji za ka iya tuna abin da ta ke fada sa'ar da ta nufo falon?" Sai da ya yi dum na dan lokaci kana ya ce, "Na tuno." "Me ta ke cewa?" "Cewa ta ke, Alhaji kar ku sha alewar nan, alewar nan ba ta da kyau!" Hannatu ta juya ga mai shari'a, ta ce, "Ya mai shari'a lallai babu shakka ina so kotu ta lura ta gano wasu sirrika daga cikin maganar baiwar Allahn nan, don babu yadda za a yi kaza ta san hanyar rafi, abin nufi babu yadda za a yi Hajiya Rukayya da ba ta san komai a kan wannan alewa ba, ta yi wannan furuci. Na gode!" Ta koma wajen zamanta ta zauna. Garba ya mike "Shaida na gaba da za mu kira wo kamar yadda mu ka ce, shi ne aminin Alhaji Basiru wato Alhaji Gali." Alhaji Gali ya hau mumbarin shaidar, bayan Alhaji Sambo ya sauka. Garba ya isa gare shi. "Zan so kai ma ka sanar da shari'a matsayinka ga Alhaji Basiru, wato mai gidan wadannan matan." "Sunana Alhaji Gali." Ya soma da gabatar da sunansa. "Kuma ni babban amini ne ga Alhaji Basiru." "Ko kai ma ka na cikin wadanda su ka riski kawunansu a cikin wannan falop sa'ar da abin ya faru." Ya gyada kai "Hakika!" "To me za ka ce mana game da faruwar wannan abu?" Ya gyada kai, kana ya soma zayya na abin da ya faru. Ba su sami sabani ba, kusan abu guda su ka fada shi da Alhaji Sambo. Bayan ya kammala sai Garba ya yi masa wasu tambayoyi guda biyu, kamar haka. "Wato dai ya tabbata Zainab ta dauko wannan alewa kenan?" "Kuma a dakinta?" "Babu ko shakka!" "To madalla mun gode." Garba ya koma wajen zamansa ya zauna. Ganin ba ta taso ba ya sa mai shari'a Muktar Yakub ya juya gare ta "Ki na da tambaya ne?" Hannatu ta girgiza kai, "Babu yallabai!" Yar hayaniya aka yi kadan, me yiwa ta samo asali ne da tunanin mutanen na fara ganin gazawar Hannatun. Garba Ya mike, ya ce "Shaida na gaba da za mu gabatar wanda ya zama shi ne mutum na farko da ya halarci wannan gida bayan faruwar al'amarin shi ne Likita Idris, wanda kuma dama can likitan gidan ne." Likita Idris ya fito, dan kakkaura ne haka fari, mai sakakkiyar fuska. Garba ya ce, "Likita zan so ka warware min zare da abawa game da matsayinka a wannan gida, da kuma tsawon lokacin da ka dauka ka na yi musu aiki." Ya gyara murya, "Kamar dai yadda ya ke, a gaskiya ni likita ne na musamman a wannan gida, kuma tsawon shekaru goma kenan." Garba ya gyada kai "Da kyau! Wato duk abin da ya faru na game da rashin lafiya a gidan kai a ke nemo wa kenan?" "Haka ne." "To sa'ar da wannan abu ya faru aka gayyato ka, a ya ya ka riski abin?" Sai da ya yi dan jim kana ya ce, "Ni dai lokacin da na shiga falon yayin faruwar abin, na riski ita uwargidan wato Hajiya Rukayya durkushe gaban yayanta biyu, sai kuma Zainab, amaryar kenan, durkushe a gaban mijinta, Alhaji Sambo wato kanin Alhajin kenan da kuma aminin Alhajin wato Alhaji Gali tsaye a kanta. Ganin hakan ni sai na nufi gun Hajiya Rukayyar don ba ta tallafi." "To ita Zainab din me ta ke yi ga Alhajin?" "Ta nagwagwgada shi ne da irin abin gwajinmu na likitoci." "Hakan ya nuna ita ma likita ce kenan?" "Kwarai kuwa likita ce." Garba ya juya ga mai shari'a ya ce, "Ya mai shari'a idan har shari'a za ta tsaya ta fuskanci inda wadannan jawaban su ka sa gaba, lallai za mu ga cewa akwai wata makarkashiya cikin wannan al'amari wanda ya afku a ba-zato, wanda za mu ga kiri-kiri Zainab ba ta damu da yayan kishiyarta ba, ta mijinta ta ke, wanda wannan kadai ya isa ya sa a fahimci cewa akwai manufa ta son kisan gilla ga wadannan yara." Ya yi godiya ya koma ya zauna. Hannatu ta tako zuwa ga mumbarin da likita ke kai. Ta dube shi, "Likita ko za ka iya sanar da mu yadda aka yi ka sami labarin faruwar wannan al'amari?" "Eh! An sanar da ni ne ta waya." "Wane ne ya sanar da kai?" "Amarya ce". "Wace ce amarya?" "Zainab." "Wadda a ke zargi kenan?" "Eh!" ya amsa ta hanyar gyada kai. "Ita ce ta yi ma waya, ta ce da kai me?" "Ta ce don Allah na yi gaggawa na zo." Ta nisa kana ta juya ga mai shari'a, "Ya mai shari'a, idan mu ka yi la'akari da wannan za mu fahimci cewa, babu yadda za a yi matar da ta yi shirin aikata wannan abu da ake zarginta da shi yanzu, ta yi tunanin sanar da kafar da za ta bayar da taimakon gaggawa, don hakan na nuna cewa a na son ceto rayukan wadannan yara, musamman idan mu ka duba cewa ita ma likita ce zata iya ba mijinta shi kadai kariya, idan har zargin da a ke ya tabbata..." Tun kafin ta karasa hayaniya ta soma fitowa jifa- jifa, da alama jama'ar sun fahimci abin da Hannatun ta ke nufi, kuma har wasunsu ma sun fara shiga cikin tunanin abin. Bayan mai shari'a ya tsawatar sai aka yi shiru. Bayan saukar likita Idris daga kan mumbarin shaidar, sai Garba ya mike, sai dai mikewar tasa ta yanzu ba kamar ta baya ba. "Kafin na kira shaida na gaba ina so na yi amfani da wannan dama domin kira ga kotu da ta rika dubawa ta nakuma bijirewa irin wadannan sakarkarun tambayoyi da aka gabatar yanzu ko don tsafta ce wannan shari'a." Ya dan yi shiru kana ya ci gaba "Shaida na gaba da na ke son gabatarwa shi ne jami'in bincike a kan kisan kai, wanda kuma shi ne ya bi diddigin wannan al'amari, wato Sifeto Habibu Hudu Darazo." Sufeto Habibu ya mike ya shiga mumbarin shaida ya tsaya. Garba Ya dube shi, "A matsayinka na mutumin da wannan al'amari ke hannunka ta fuskar bincike, ko za ka iya sanar da shari'a sakamakon da kuka tattara?" Daki-daki Sifeto Habibu ya yi bayanin game da sakamakon bincikensu da kuma irin shaidun da su ka samu har zuwa lokacin da su ka miko karar ga kotu. Garba ya yi masa godiya, ya koma wajensa ya zauna. Hannatu ta mike ta nufi mumbari shaidar da Sifeton ke tsaye, "Sifeto zan so na san lokacin da ku ka isa gidan, abin nufi karfe nawa?" "Karfe takwas mu ka ce za mu isa gidan, amma saboda wani dan tsaiko da mu ka samu takwas din ta dan gota." "Yallabai kenan, saba lokacin bai sa kun samu matsala ba wajen ganawa da duk wanda ya dace, tunda watakila idan su ka ga lokacin ya gota za su iya fidda rai da zuwanku?" Sifeto ya yi murmushi, "Ba mu sami wannan matsalar ba, sai dai..." Ya dan yi shiru gami da dukar da kansa alamar tunani. "Sai dai me?" Hannatu ta bukata ganin shirun nasa na yunkurinsa tsawaita. Ya dube ta, "Sai dai uwar gida da ba mu sami damar ganawa da ita ba." "Uwargida? Hajiya Rukayya kenan?" "Eh, ita." Ya gyada kai. "To me ya hana damar ganawar da ita?" "Saboda ta yi barci lokacin..." "Barci?" Ta nanata cikin mamaki. Ba ita kadai ba ma kusan kowa a kotun sai da fuskarsa ta sauya, har da shi mai shari'ar. Ta juya ga mai shari'ar, "Ya mai shari'a lallai

Please Login or Register in order to submit comment