Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su yan biyu. Amma a lokacin da su ka gama sakandire sai su ka samu rabuwar ra'ayi. Ita Zainab ta sauya darasin karantunta ta wuce kai tsaye ga fannin koyon bada kariya ga al'uma, wato lauya. To amma wani abin mamaki dan sha'awa ga kawayen biyu, wannan rabuwar ra'ayi ba ta shafi kawance da son junansu ba. Duk da haka sai su ka ci gaba da ziyartar juna akai-akai, har kawo yanzu da kowannen su ya gama karatunsa kuma ya ke cin moriyar karatun. Haduwar wadannan kawaye ta na zama abin sha'awa, don da kyar su ke iya rabuwa saboda son juna. Yau ma tun karfe goma na safe Hannatun ta zo, kuma kamar yadda ta saba sai karfe biyar ko fiye da haka ta ke barin gidan. Shi ya sa yanzu da direba Lukman ya zo ya yi mu su sallama su ka ji kamar ya shiga rayuwarsu, don duk sa'ar da su ka hadu ba sa kaunar wani abu ya katse mu su hirarsu. Suka daubi kofar shigowa falon bayan sun amsa sallamar. Lukman ya daga labule ya shigo. Mamaki ne ya fi rinjayar komai a fuskar Zainab bayan ta gane Lukman ne ya dauko yaran daga makaranta. Shi ma alamun mamaki sun bayyana a fuskarsa sai dai shi nasa bai yi tasiri ba saboda sanin cewa dole ne ko wane ne zai yi mamaki musamman ma idan ka yi la'akari da cewa ba shi ne ya kai yaran makaranta da safe ba, kai hasali ma bai zo gidan ba tun safe. Bai samu damar magana ba har Zainab ta ce, "Lukman daga ina?" Tambayar ba ta ba shi mamaki ba. "Daga makaranta na ke na je na dauko su ne." ya amsa kai tsaye bayan ya tsuguna. Mamakin ta ne ya karu. Ta dubi Hannatu da zummar ta yi magana, amma kafin ta yi sai ta riga ta da cewa, "Lafiya na ga ki na mamaki don ya je ya dauko su daga makaranta, ba aikinsa ba ne?" "Aikinsa ne, amma..." "Amma me?" Hannatu ta katse ta. "Amma gani na yi cewa ba shi ya kai su ba, kuma ma bai zo gidan ba yau kwata-kwata!" Zainab ta amsa lokaci guda kuma ta mayar da duban ta ga Lukman din. Hannatu ba ta fahimci abin da ta ke nufi ba, don haka ba ta sake yin magana ba, maimakon hakan ma sai ta ci gaba da sauraron su. "Lukman me ya sa yau ba ka zo ba?" Tambayar ta so ta rikita shi, amma koda ya tuno da gargadi da kuma kudin da Hajiya Rukayya ta ba shi sai ya ji ya dan nutsu. "Ba ni da Lafiya Hajiya...mu..mura ce ke damu na Hajiya..dauriya ce kawai irin tawa ta sa na fi...fito." ya amsa a marairaice murya na rawai. Nan da nan alamun mamakin su ka yi kaura da ga fuskar Zainab yayin da na tausayi su ka maye gurbin, jin abin da Lukman ya ce. Ta girgiza kai cikin tausayi sannan murya a tausashe ta ce, "Allah ya saukake Lukman, sannu ka ji?" "Amin." Ya amsa lokaci guda kuma ya shafi kudin da ke aljihunsa wanda Hajiya Rukayya ta ba shi, a cikin zuciyarsa ya ce, "Yanzu har na yi aikin Naira dubu? Kai lallai wannan auki da sauki ya ke, da a ce zan rika samun irin sa tsawon wata shida ai da na bar aiki na koma ni ma na kwanta na dinga yi wa kudin cin kadan har su kare, na san dai kafin lokacin zan yi kaurin wuya da kumatu da kuma tumbi kamar na mai gidana." *** Sabanin kowace tana da Alhaji Basiru ya saba dawowa gida karfe shida na yamma, yau sai ga shi ya dawo tun karfe hudu, meyiwa hakan na da alaka da shirye-shiryen tafiyar da zai yi zuwa kasar Ingila. Kuma kamar yadda ya saba dawowa shi kadai, yau su uku ne, shi da kaninsa wanda su ke uwa daya uba daya da ke da zama a garin Katsina mai suna Alhaji Sambo da kuma wani abokin harkarsa kuma amininsa Alhaji Gali. Aminan biyu su ka samu a falon (Zainab da Hannatu) har zuwa yanzu su na zaune su na hira. "Sannun ku da zuwa." Zainab da Hannatu su ka fada lokaci guda cikin sakin fuska da walwala, bayan sun amsa sallamar magidantan uku. Doguwar gaisuwa su ka yi kafin daga bisani falon ya yi shiru. Alhaji Sambo shi ya kau da shirun da tambayar Zainab. "Hajiya Zainab amarya, ina uwargidan ne?" Ga ta nan tafe." Muryar Hajiya Rukayya ta ratso falon kamar daga sama, wanda hakan ne ya ja hankalinsu zuwa kofar shigowa falon daidai lokacin da ta dago labulen falon ta shigo. "Yar halak! Yanzun ann na ke tambayar ki." Alhaji Sambo ya ci gaba ya na duban ta cikin fara'a. "Ni ma ai ina jin ka, shi ya sa na amsa ma." Ta ce ta na yin wani dan asirtaccen murmushi, kamar ba ta so. "Ai daman na dauka kin fita ne ba tare da kin tambaye ni ba na dau mataki idan kin dawo." Ya kuma cewa cikin dariyar tasa, sai dai wannan karon ba shi kadai ba, kusan dukkannin su babu wanda bai dara ba, idan ka dauke ita Hajiya Rukayya da ta turbune fuska. Wannan wani wasa ne da Alhaji Sambo ya saba yi wa Hajiya Rukayya, wasan da ake wa lakabi da na kanin miji. Hajiya Rukayya ta samu daya daga cikin jerin kujerun da ke gewaye da falon ta zauna, sannan su ka gaisa cikin fara'a da sakin fuska. Ko shakka babu sakin fuskarta na da alaka da ganin bakin biyu, don kuwa idan da akwai abin da ya fi wuta zafi, zuciyar Hajiya Rukayya ta fi shi zafi a wannan rana ganin cewa duk abin da ta shirya akan Mujahid ya dawo daga makaranta lafiya. Ranta ya kuma kuna sa'ar da ta ji muryar Maigidanta ta ratsa dodon kunnenta da cewa, "Hajiya na zama mu ka zo yi ba abinci kawai mu ka zo ci kafin mu wuce, kin san karfe biyar jirginmu zai tashi." Duk da cewa muryarsa a kwancw ya yi maganar hakan bai hana jin kamar ta ce masa ba za ta kawo ba domin gani ta ke, raini ne a ce ta tashi ta kawo abinci bayan ga Zainab da ke matsayin kanwarta. Haka dai ta daure ta danne fushinta, ta tashi ta nufi kicin ta nakunkuni, shi ma kuma wannan duk ganin idanun bakin ne. Kamar wadanda ke jiran fitar ta, yaran uku su ka shigo falon a guje, Mujahid a gaba, Hauwa'u da Sailuba biye da shi. Turus! Hauwa'u da Sailuba su ka ja su ka tsaya kamar wadanda aka kira sunansu daga baya, wannan kuwa ya biyo bayan ganin mahaifinsu da su ka yi babu zato babu tsammani. Shi kuwa Mujahid bai tsaya ba har sai da ya dangana da mahaifin nasu, ya fada kan cinyarsa ya na dariya. "Kai, ua ya lafiya? Mene ne kuke bin sa a guje haka?" Alhaji Sambo ya fada. "Ba shi ne ya ce wai ya girme mu ba." Hauwa'u ta amsa da wata shagwababbiyar murya. Gaba daya su ka bushe da dariya. "To, mene ne don ya ce ya girme ku? Banda abin ku wa ya ke son girma?" A wannan karon Barista Hannatu ce ta yi maganar cikin ragowar dariyae da su ke yi. "To, ai karya ya ke yi...mun fa girme shi Wallahi." Sailuba ce ta fada ita ma cikin shagwaba ta na hararar Mujahid din. "To, ai shi kenan. Ku yi hakuri kun girme shi." Alhaji Basiru ya ce ya na shafa kan Mujahid da har yanzu ke kwance kan cinyarsa. Ya ci gaba, "Zan yi tafiya amma idan zan dawo karami kawai zan sayo wa kayan dadi, kun yar..." "E, na yarda ni ne karami, ni za a sayo wa" Mujahid ya katse shi ya na tafa hannu. "A'a, mu ba mu yarda ba" Su ma su ka fada. Da wannan kace-nacen su ka cika falon. "To, ku dakata, ya isa haka." ya dakatar da su "Kowa za a sayo masa...da me da me ku ke so?" "Ni ne zan fara Baba." Mujahid ya yi sauri ya fada bayan ya yi zumbur ya mike daga kwanciyar da ya yi. "To fadi." Ya ba shi izini da gaggawa don gudun kar su Hauwa'u su ce ba su yarda ba. Yanzu kusan falon ya yi shiru kowa yana sauraron abin da mujahid din zai ce ya na so. "Ina son a sayo min jirgi da mota, uhm...uhm da Bindiga da kuma kambos..." Gaba daya su ka kuma tintsire wa da dariya. "Babbar magana." Alhaji Basiru yace "mujahid sakon naka babba ne." ya juya ga su Hauwa'u, "Ku kuma fa me za a sayo mu ku?" Sailuba ce ta fara cewa, "Ni Dan kunne da Sarka da kwabashu (Cover Shoe) na ke so." Ba ta samu sabani da Hauwa'u ba, domin ita ma abin da ta lissafo kenan, sai dai karin abu guda akan na Sailubar, shi ne Alewa mai zaki, wanda kuma lokaci guda shi ne abin da ya tuna wa Mujahid alewarsa ra safe da Hajiya Rukayya ta saya mu su a makaranta. Nan da nan ya tuna, bai samu damar shanye tasa ba wancan lokacin saboda shiga aji da ya yi ya tarar ana karatu malaminsu ya hana shi sha, ya ce ya sa a aljihu. Allah da ikonsa kuma ya manta da ita sai yanzu da sakon Hauwa'u ya tuna masa. "Lah! Baba ni ma ina da Alewata wadda Momi babba ta ba ni da safe a makaranta." Bai saurare shi ba don a lokacin hankalinsa ya tafi ga Barista Hannatu da ta ce za ta tafi gida. "Tun yanzu za ki tafi Hannatu?" Alhaji Basiru ya ce ya na duban ta, "Ba za ki bari sai an jima ba?" Ta yi dariya lokacin da ta ke yunkurin mike wa, "Babu komai Alhaji, ai na dan jima anan, sai dai kuma an kwana bi..." Mujahid ne ya katse ta da kukan da ya soma ganin ba a saurari abin da ya ke fada ba. "Kai! Wai mene ne haka?" Alhaji Basiru ya tambaye shi da tsawa. "Alewata za a dauko min." ya amsa cikin kuka. "Ta na ina?" Bukata daga Alhaji Basiru. "Ta na cikin aljihun wandon makarantana." ya amsa ya na murtsuke idanu bayan ya tsagaita da kukan. "Zainab don Allah je ki dauko masa kar yua dame mu." Umarni daga Alhaji Basiru. Zainab ta mike, "Ina zuwa Hannatu, idan ban dauko masa alewar nan ba ba zai bar mutane su ji kumai ba." Cikin sauri ta shige dakin nata da ke manne jikin falon don gudun kar ta bata wa Hannatu lokaci. Jim kadan ta fito alewar rike a hannunta. To amma wani abin mamaki wanda ita kanta ta rasa sanin dalilinsa shi ne, tun daga lokacin da ta mike da zummar dauko Alewar sai ta ji zuciyarta ta na bugawa kamar za ta faso kirjinta ta fito, kuma har zuwa yanzu da ta shigo falon gaban nata bai daina faduwa ba. Tun kafin ta isa gare shi, Mujahid ya tafi da sauri ya karbi alewar, sannan ya koma wajen mahaifin nasa. "Baba ka ga alewar!" ya ce ya na nuna masa. "Na gani Mujahid, amma za ka sanwa su Hauwa'u ko?" Ya girgiza kai, "Ba zan ba su ba." "Kannan naka?" A wannan karon aminin Alhaji Basirun ne ya yi magana, wato Alhaji Gali. "Ni dai ba kannena ba ne." Mujahid ya ce ya na kumbura baki. "To shi kenan rabu da shi, idan na je na dawo ba zan kawo masa jirgi da mota ba." Cewar Alhaji Basiru. Alhaji Basiru mutum ne mai son hada kan 'yayansa a koda yaushe. Shi ya sa idan daya daga cikin su ya zo da wani abu matukar sauran ba su da shi, to sai ya ba su. A yanzu ma haka ce ta kansance don sai da ya lallabi Mujahid ya ba shi alewar. "Yauwa Mujahid, ka ga idan na je na dawo sai na sayo ma wata." yace bayan ya karbi alewar. "Bari na raba mu ku ko?" Mujahid da fuskarsa ke a turbune ya gyada kai cikin rashin son rai. Alhaji Basiru ya bare alewar sannan ya sa hakori ya fasa ta gida uku. "Fara zaba Mujahid." Ya ce bayan ya zube ta a tafin hannunsa. Mujahid ya dubi kason alewar cikin rainuwa da ruwan ido, ya sa hannu ya dauki daya. A hankali sai kuka ya kufce masa. Ba wani abu ne ya sa shi kukan ba, sai dariyar da Hauwa'u da Sailubar su ka shiga yi masa bayan sun dauki nasu kason. Ya dube su daidai lokacin da su ka sa alewar a baki su na yi masa gwalo. Da tsananin fushi ya dubi tasa alewar sai ya fashe da kuka, a lokaci guda kuma ya yi jifa da ita kai tsaye ya fice daga falon a guje ya nufi inda Hajiya Rukayya ta ke (Kitchen). Barista Hannatu ta mike, "Lallai Mujahid akwai rigima..Ni zan tafi." Zainab ma ta mike. "To, Hannatu a sauka lafiya, sai an kwana biyu ko?" Alhaji Basiru ya mike. "A gaida gida." Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka ambata. Momi...momi, Baba..ya kwace mini Alewa...ta". Wannan shi ne abin da Mujahid ya rika ambata cikin kukan nasa har ya isa gare ta. Ba ta fahimci abin da ya ke nufi ba saboda haka ne ma ta daka masa tsawa gami da kai masa hannu da zummar mangare shi. Maimakon damuwa da abin da ta yi masa sai ya ci gaba da cewa cikin kukan nasa, baya ya dan matsa baya, "Ba Baba ba ne ya kwace min...A...Alewata da ki..ka ba ni a makaranta...ya ba su Hau...Hauwa'u.." Sai yanzu ta fahimci abin da ya ke fada, ta kuma gane. A firgice ta saki kwanon abincin da ke rike a hannunta, abincin ya tarwatse a farfajiyar dakin girkin. "Kar ku sha alewar nan ba ta da kyau...kar ku sha alewar nan ba ta da kyau...kar ku sha!" Wannan shi ne abin da ke fita daga bakinta cikin daga murya da kuruwa, kuma shi ne abin da ya katse sallamar da kawayen biyu ke yi (Zainab da Barista Hannatu) Wadanda ke tsaye a bakin kofar falon. Cikin kin jinin rabuwa da juna kamar yadda su ka saba. Tafiyar ruwa ta so ta yi da su ba don sun ba ta hanya ba. Shakka babu ta tsorata su ganin shigarta falon kamar kibiya. To, amma duk wannan mai sauki ne, tsoron nasu ya fi bayyana karara lokacin da su ka rufa mata baya zuwa cikin falon su ka iske, Sailuba da Hauwa'u da Alhaji Basiru kwance a kasa su na murkususu! Turus su ka yi su dukansu sa'ar da kwayar idanunsu ta nuna mu su mummunan abin da ke faruwa a falon, abin da ya haifar da wasu irin alamu na rikitarwa da kaduwa lokaci guda a fuskokinsu, musamman ma Hajiya Rukayya da abin ya yi ma ta yawa, ga 'yaya ga miji, su na ta faman juye-juye da kakarin neman taimako. A ka ta dora hannuwanta biyu ta kwalla wani irin ihu mai garwaye da kuka. Lokaci guda ta nufe su, ta dire gwaiwoyinta biyu akan kilishin da ke shimfide a falon, ta tallafo kan Sailuba, ta girgiza ta, kana da sauri ta mayar da ita ta tallafo Hauwa'u ta girgiza, a yanzu sun daina motsi, jikinsu ya saki kamar matattu. Take ta kuma kurma wani uban ihu cure da wani kuka mai tsuma zuciya. "Wayyo Allahna... 'yan biyu sun mutu." Wannan ya sa Zainab ita ma da ke tsaye tare da kawarta cikin rashin sanin abin yi ta isa ga Hajiya Rukayya da ke kokarin faduwa ta dafe ta. Ba ta da abin fada shi ya sa ta kasa cewa komai, a lokaci guda kuma hawaye ya fara tsattsafowa daga idanunta ganin yara biyu da ke kwance ko motsa wa ba sa yi, bugu da kari ga mijinta na juye-juye cikin wani irin nishi na ban tausayi. Dabara ce ta fado ma ta, shi ya sa ita ma Barista Hannatu duk da cewa ta nacikin rikita ta motsa zuwa inda Zainab ke rike da Hajiya Rukayya. Ta duka da sauri ta tallafi Hajiya Rukayyar, "Sake ta Zainb, je ki kira likitanku a waya mana." Ba ta yi gardama ba kawai sai ta sakarwa Hannatu ita, ta nufi kan wayar sadarwar da ke ajiye kan matsakaicin teburin da ke durkushe can gefe guda. cikin hanzari ta soma lallatsa lambobin da su ne ta san za su sada ta da likita Idris. "Hello!" Ta ambata tun kafin ta gama daidaita zaman wayar a kunnenta. "Likita ne." Ta ci gaba. "Don Allah ka yi maza-maza ka zo." Ta juya kallonta ga maigidanta Alhaji Basiru jin ya ja wani dogon numfashi. "Likita ka yi sauri don Allah, alhaji ne da 'yan biyu su ka kamu..." Aka katse ta daga can bangaren ta hanyar ajiye wayar da likitan ya yi. Ita ma ta ajiye, maimakon ta dawo gare su sai ta nufi dakinta a guje, meyiwa akwai abin da ta tuno. Da sauri-sauri, gudu-gudu Zainab ta kuma shigowa falon hannunta na dama rike da 'yar karamar na'urar da likitoci ke rataya wa a wuya. Wajen maigidanta ta fara nufa. Da gaggawa ta balle maballen wuyan rigarsa ta dora na'urar a kirjinsa bayan ta sakala a kunnuwanta. To, a daidai lokacin ne Likita Idris ya shigo falon da sauri, hannunsa rike da irin karamar jakar nan tasu ta likitoci. Mamaki ne shi ma ya fara bayyana a fuskarsa ganin abin da bai yi tsammani ba, Alhaji Basiru kwance ya na nannauyan nishi. "Subhanallahi." Ya ce. Har ya nufi Alhajin amma ganin Zainab na yin iya bakin kokarinta, ya sa ya sauya nufin nasa ya nufi su Sailuba da ko motsi ba sa yi. Koda Hajiyya Rukayya ta kyalla idanu ta ga Likita sai ta yi zumbur ta kwace daga hannun Hannatu, ta mike ta tare shi ta nacewa, "Likita don Allah taimake ni, wadannan 'yayan sun mutu...wayyooo!" kukan ya hana ta ci gaba. Cikin hanzari Likita ya dire yar jakarsa a kasa, shi ma dai da yar na'urar da ke rataye a wuyansa ya soma. Falon ya yi tsit sai nishin kukan Hajiya Rukayya sakamakon zubawa Zainab da likita Idris idanu da aka yi akan gwaje-gwajen da su ke yi. Jim kadan likita Idris ya nisa, kana ya cira kai ya dubi su Alhaji Sambo da ke cikin wani mugun ya nayi, "Wannan ya na da kyau mu tafi da su asibiti da gaggawa domin..." "To, mu je mana likita?" Kusan mutum uku ne su ka katse shi (Ahaji Sambo da Alhaji Gali da Hajiya Rukayya). Ba su bata lokaci ba bayan umarnin likitan. Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka tallafi Alhaji Basiru a kafadarsu, su ka nufi waje da shi. Shi kuwa likita Idris ya sungumi Hauwa'u, Barista Hannatu ta sabi Sailuba Hajiya Rukayya ta sabi jakar likita ita da Zainab su ka dafa mu su baya har zuwa 'yar farfajiyar da aka 'kirkira don ajiyar motoci. Suna isa asibiti su ka zarce bangaren da ke da alhakin bayar da tallafin gaggawa A&E (Accident and Emergency). Sun amsa sunansu, domin ba tare da jinkiri ba su ka fara aiwatar da tallafin nasu na gaggawa akan Alhaji Basiru da 'yan biyu. Bayan wasu 'yan gwaje-gwaje sai wata kakkaurar likita fara, gajera, mai yalwar kumatu ta bayar da umarnin a shigar da su wani daki. Amma a duk cikin tawagar da su ka taho babu wanda aka bari ya shiga. Hakan ne ya sa su ka koma gefe su ka yi cirko-cirko su na jiran sakamako. A CAN GIDA *** Bayan fitar su da a kalla rabin sa'a Baraka ta isa gidan a kudurinta na jin sakamakon abin da su ka kulla. A bude ta samu babbar kofar shiga gidan, wanda hakan ne ya sa ta kunna kai ciki ba tare da jinkiri ba. Ta ja ta tsaya ganin mujahid na ta rusa kuka, mai gadi Bukar na ta rarrashin sa. Ga mamakinta sai ta ji gabanta ya yi mummunar faduwa. Ta taka a hankali ta isa gare su. "Assalamu alaikum." Ta ce a sanyaye. "Wa'alaikis salam". Maigadi Bukar ya amsa, ya cira kai ya dube ta. "Sannu Baba." Ta kuma cewa a sanyaye. "Yauwa ke ma Sannu." ya maida hankalinsa gare ta saboda sassauta kukan da Mujahid ya yi. Ta yi murmushin karfin hali, "Lafiya dai ya ke kuka?" ya dubi Mujahid din da ke zaune kusa da shi akan dogon bencin, "E to! Ba lafiya ba." "Mene ne ya faru?" Ta bukata wannan karon a 'kagauce. "Yan uwansa ne da kuma Alhaji ba su da lafiya." "Su wa kenan?" Ta dafe kirji. "Yan biyu mana, Hauwa'u da Sailuba." Gabanta ya kara faduwa, "Me ya same su?" "Abin da ban sani ba kenan. Ni ma ina zaune a nan na ga an fito da su za a kai su asibiti." Ba ta ga ta jira ba, akwai bukatar ta san dalili. Ta matsa ta dafa kan Mujahid, ta rankwafa, "Mujahid me ya same su?" Cikin ragowar shisshikar kukan da ya ke yi ya ce, "Ba...alewa ta su ka kwace min...ba, shi ne..." Ta saki kansa da sauri wanda hakan ne ya hana shi karasawa. Alamun razana su ka bayyana a fuskarta, take ta ji cikinta ya juya gami da bayar da wani amo kululululuuu, sai kuma ta ji kamar ta saki gudawa, cikin ta yan maza ta ce, "Yanzu su na asibitin?" "Eh". Maigadi Bukar ya amsa ma ta kai tsaye. "Wanne kenan?" Ta kuma bukata. "Ai ina jin ba za su wuce asibitin nan na dogon gida ba" "Har Hajiya Raukayyar?" "Dukan su!" Ba ta sake komawa ta kansu ba ta juya, "Sai an jimanku." Ta nufi babbar kofar da sauri da sauri kamar za ta fadi. Idan ka dubi saurin da ta ke yi sai ka rantse da Allah asibitin ta nufa. Ko kusa ba haka ba ne, ita Allah-Allah ta ke yi ta isa gidan da ta sauka domin tattare kayanta ta nufi tashar mota, don tuni ta kudurce ta kuma gaskata kwanan Kano a yau ya gagare ta, yau a kauyensu za ta kwana. To sai dai abin da ba ta sani ba shi ne; Ko da birnin Sin za ta koma bincike zai tuso keyarta zuwa Kano. *** Sa'a guda su ka share su na zaune su na jira amma shiru ba labari, hakan ne ya kara jefa zulumi a zukatansu, musamman Hajiya Rukayya da ta riga ta san makasudin faruwar abin da kuma irin hadarinsa. Duk ta rude ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta yi nan, ta yi can, ta na yi ta na sumbatu. Abu guda ta ke nanatawa. "Oooh! Wayyo Allahna, yau na shiga uku na lalace...shi kenan mutuwa za su yi. Wayyo ni kaina. Baraka ya haka?" duk da cewa a rikice ta ke yin maganar, babban abin mamaki da tambaya cikin abin da ta ke ambata, me ya sa ta ke cewa shi kenan sun mutu? Kuma wace ce Baraka? Wadannan tambayoyi guda biyu su na yin matukar tasiri a zukatan, Alhaji Sambo, Alhaji Gali da kuma Barista Hannatu, sai kuma yan tsirarun mutanen da ke zaune a wajen su na cikin jiran na su majinyatan da su ka kawo. A cikin wannan hali ne kofar dakin ta bude, likitoci guda biyu su ka fito. Likita Idris ne da wannan kakkaurar Likitar wadda ke amsa Dokta Safina A. Bashir. Cikin hanzari da kaguwa dukan su su ka tunkari likitocin don jin halin da ake ciki. "Ya ya likita...ya aka yi?" "Ya ya su ke?" "A wane hali su ke?" "Me ya faru da su?" Ba za ka iya tantance wadanda su ka furta wadannan kalamai ba a cikin su, da ya ke kusan a tare su ka furta. Bai ba su amsa ba sai kawai wani farin kyalle da ya zaro daga aljihunsa ya tsane gumin da ke tsattsafo wa daga goshinsa. Alama kawai ya yi mu su da hannu su biyo shi. Su ka bi shi kuwa duuu kamar kura har zuwa ofishinsa. Kai

Please Login or Register in order to submit comment