Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka haifi Zulaihat wani kuncin ya rage daga cikin zuciyata kusan kaso 50 daga cikin 100 sunan ban haifi Zulaihat bane kawai,amman komai nike ma yarinyar wajena take wuni bacci ke maidata a wajen uwarta ,haka muka kama rayuwa an haifi Zulaihat da wata shidda Allah yayi ma mahaifiyarmu rasuwa..,an kwanta da ita lafiya aka wayi gari bata nan nayi kuka har na gode Allah daga karshe dai na saka ma kaina dangana ba uwa ba uba bani da kowa sai Yaya Aminu shima haka bai da kowa sai ni ,sai muka hade kanmu muka zama tsinstiya madaurinki daya.

Zainab matar Yaya Aminu lafiya tak'i yau ciwo gobe ciwo haka dai aka tafi asibiti gwajin farko da akayi mata aka gano da tana dauke da wani cikin nan ma munyi murna.ni lokacin har na cire rai da haihuwa dan nafi shekara uku ko b'atan wata ban sake yi ba,da yake cikin yana bata wahala yasa na dawo da Zulaihat wajena muka cigaba da zamanmu.

Duk ina ankare da wulakancin da ake man a gidanMustpha ban nuna nadamu ba,ina dai rayuwa ta na baima Allah lamarina.fahimta da akayi ba zan tamka ba sai aka fara zalintar Zulaihat yarinyar da ko magana bata damu da yinta ba kominta silent yake.bata da fitina ko kadan sai dai idan suka zalunceta ta koma gefe tayi kuka,tun ina kauda kai har na kasa ina magana,idan kuma nayi magana ko na rama mata sai ace dan bansan zafin haihuwa ba shiyasa. na kanyi kuka na gode Allah.

Ganin zaman lafiya na neman gagarata na maida Zulaihat gidansu wajen iyayenta sai dai naje masu wuni ko suma suzo man da yake cikin Zainab ya dan tasa zai kai wata shidda zuwa bakwai.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi sai dai hakuri har cikin Zainab ya isa haihuwa nan haihuwa tayi gardama har sai da aka yankata aka fiddo d'a namiji sai dai uwa babu lafiya... Binciken likitoci aka gano tana dauke da cencer mahaifa sai da aka cireta sannan lafiya ta samu aka dawo gida yaro yaci suna Hamza.

Muna kiran Hamza da suna Daddy ,Daddy yarone mai shiga rai ga kyau da Allah ya wadatashi dashi ,bai da rigimar banza sabanin Mamana da kullun take cikin kukan banza sai ya zama Daddy ne babba itace karama dan idan tana kukan shi yake lailashinta duk da ko magana bai ida iyawa ba a lokacin.bai wuce shekara daya a ta biyu yake ita kuma Zulaihat tana da shekara uku tana neman shiga ta hudu ma.

Watarana ina zaune kawai na shirya na tafi gidan Yaya Aminu dan inason ganin su Mamana. koda naje gidan Mamana na tadda tasa uwar a gaba sai kuka take anyi anyi tayi shuru taki har Zainab tasaka mata ido. tana ta hidimarta shi kuma Daddy yana kwance yana bacci,tambayarta nayi tun yaushe yake baccin?tace man zaiyi awa biyu yana gama shan sweet ya kwanta nace baccin ya isa haka ya kama ta a tadashi.

Ashe rai yayi halinshi ba jijigawar da bamuyi mashi ba cikin rudewa uwar ta dauke shi tayi waje dashi tana watsa mashi ruwa nan ma bai motsa ba haka muka hakura muka kira babbanshi muka gaya mashi halin da ake ciki akazo aka kai shi gidanshi na gaiskiya.

Jamamin mutuwar yaron ya jefeni bani da aiki sai ciwo ganin ba sauki sai wajen Allah na tafi asibiti anan ake gayaman ina da ciki har na tsawon wata takwas nayi murna harda kuka kuwa...koda na gayama Mustapha shima yayi murna dan farincikinshi har bai boyu ba haka na karasa rainon cikina Daddy nada wata biyu da rasuwa na haifi y'ata mace mai kama dani a asibiti na haifeta koda muka dawo gida yarinya taci suna *ZUBAIDA* sunan kakar Mustapha kenan.

Haka nida Mustapha muka cigaba da rainon Zubaida duk da yaiyenta su Abdul suna zaluntarta sai dai na kauda ido dan basan fitina da tashin hankali sam, da Zubaida ta girma ta kai shekara hudu a duniya sai ta fara rama fada da kanta dan bata kyale duk wanda ya tabata lokacin Zulaihat tana da shekara shidda a duniya,amman Zubaida ke rama mata fada dan ita Zulaihat sam bata san rigima da tashin hankali ,duk da Zulaihat ta girmi Zubaida amman komai tare ake masu dan Zubaida tana da garin jiki tsawone bata dashi sosai kamar Zulaihat, hatta makaranta tare Yaya Aminu ya sakasu komai tare yake masu nima idan na samu kudi inayi masu dinki iri daya da dai abunda baifi karfina ba dan ina Sana'a kuma ina samu Alhamdulillahi.

Bayan wasu shekaru a lokacin Zubaida na da shekara takwas itama kuma Zulaihat tana da shekara goma tafiya ta kama Yaya Aminu zaije sokoto interview din wani aiki har sun shirya suka biyo ta gidana yi man sallama. Zulaihat na ganin Zubaida sai tace bata binsu tana wajena ba yanda ba'ayi da ita ba.ta bisu taki harda kukan ta. ba dan sunso ba suka barta suka tafi ita kuma ta cigaba da wasanta da Zubaida daman wasan ta gani ya dauke mata hankali taki bin iyayen nata sokoto..cikin dare muna zaune sai karatu nike koya masu aka kira wayata sai naga number Yaya Aminu daman na kirasu har sau biyu basu dauka ina dauka nace nayi fushi inata kira ba'a dauka ba sai akace man bashi bane hatsarin mota sukayi yanzun haka suna teaching hospital sokoto dan haka ana bukatar ganinmu gobe duk yanda naso a gaya man a wani hali suke anki andai ce suna lafiya na dai zo.

Haka na kama kuka Mustapha harda Jamila sun kewayeni sai hakuri suke bani tun da asuba muka dauki hanyar sokoto dani da Mustapha da Zulaihat muka barma Jamila Zubaida koda muka isa asibiti muka kira waya a emergency akace muzo muna zuwa na tadda Yayana cikin halin rai ko mutuwa nan na fasa ihu ina na bani na lalace Yaya dan Allah karda ka mutu ka barni kasan bani da kowa kaine uwata Yaya kaine ubana

Kallona Yaya Aminu yayi ya maida kallonshi wajen Zulaihat hawaye na zubowa a fuskarshi a hankali yace mutuwa rigar kowa ce Hafsat duk mai rai sai ya mutu ya bar duniya ita duniya gidan arone ga amanar Zulaihat nan na bar maki ki tuna bata da kowa sai ke da Zubaida... Wani sabon kukan na fashe dashi ina cewa in shaa Allah zaka tashi ka cigaba da rainon Zulaihat har ka aurar da ita kai da aunty Zainab... Girgiza man kai yayi yace ..Hafsat ai tuni Zainab rai yayi halinshi nima ta Allah nike jira karda ki yada zumuncin Allah Hafsat ki rike Zulaihat da amana kamar yanda zaki rike Zubaida ki sakata tayi ilimi mai zurfi wanda al'umma zasuyi alfahari da ita ina fatan aurene kawai zai rabaku....daga ni har Zulaihat din kuka muke da yake yarinyar a lokacin tasan maiye mutuwa dan tana da shekara goma a duniya kuka nike ina rike da hannunshi itama Zulaihat tana rike da gudun hannunshi ta daura kanta saman gadon da yake kwance tana kuka...muna cikin haka Allah ya anshi abunshi nan sabon tashin hankali ya barke dan suma na dunga yi a asibitin sai da nasha ledar ruwa biyar sannan Mustapha ya bada kudi aka bamu gawarsu Yaya Aminu da matarshi Zainab muka jiyo dasu kano.

Bayan rasuwarsu da wata biyar Mustapha yace shi sam bai yarda da zaman Zulaihat a gidanshi ba sai dai na kaita jigawa wajen dangin uwarta amman bata zaman mashi gida...ba yanda banyi dashi ba akan ya barta ta zauna ba sai yayi mata komai ba ni zanyi mata komai amman yace sai fa ta bar mashi gida..ganin da gaske Mustapha yake sai nima nace ban yarda ba...banga wanda ya isa ya rabani da marainiyar Allah ba nan akaita fada nidai na tsaya akan bakata sai Mustapha yace na zab'a zaman aure dashi ko kuma zama da Zulaihat? Ni kuma nace zama da Zulaihat anan ne yayi man saki biyu na kwashe kayana na dawo nan gidan da zama wato gidan Yaya Aminu na kwashe kayan matarshi na saida na sama Zulaihat kudin a account kudin suna nan ajiye ko biyar ban taba ba ,ban kuma bar mashi Zubaida ba da ita na taho muka cigaba da rayuwarmu ina sana'ata ba abunda ban masu har kawo yau kunji dalilin rabuwata da mijina.

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*


*PAGE 71-80*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

So da tausayinta suka k'ara dirar mashi a cikin zuciyarshi gami da wata zaizafar kaunarta wanda baki ba zai musalta ta ta ba,furzar da iskan bakinshi yayi yana share zufar da ta keto mashi a fuska dan k'ara matsawa yayi kusa da Umma yana maida kanshi k'asa yace.."Umma dan Allah ki bani auren Zulaihat zan riketa amana zan zamai mata bango. zan sata farinciki in shaa Allah ba zan taba barinta tayi kukan maraici ba." Ya ida maganar kanshi k'asa shi kadai yasan yanda yake jin tausayinta da sonta jin labarinsu ya k'ara mashi wata kaunarta mai girma mai wuyar fassarawa.

Girgiza mashi kai Umma tayi tana share hawayenta tace.. "Najibullahi duk da a yau na fara saninku na yarda da tarbiyarku kuma na dauke ku a matsayin yarana. har shiyasa na shigo daku cikin gidan nan,sai dai maganar gaskiya ba zan boye maka ba yanda nike jin son Zulaihatu a zuciyata ko Zubaida da na dauki cikinta na haihota banma shi.dan ita Zulaihatu abun tausayice bata da uwa bata da uba sai ni.nice uwarta nice ubanta dan haka bazanso na aurar da ita idan zatayi maraici ba."

"Umma na fahimceki amman wallahi Umma zan riketa zan kula da ita zan bata kulawa ta har abada,Umma zan rayuwa da ita har *DA'IMAN ABADAN* nayi maki wannan alkwarin Umma." Dan shuru Umma tayi tana tunani can tace.."naji amman karatunta fah Najib? Kaga dai wasiyar da Yaya Aminu ya barman na sata tayi karatu mai zurfi." D'aga kai yayi yana cewa.."Umma zata cigaba da karatunta a gidana idan har tana son cigaba ma tayi master. Umma zan barta dan nima ina bukatar hakan tunda tana da kokari kinga bai kamata a tauyeta ba." Har a zuciyata Umma ta amince da Dr Najib kuma tana fatan lamarin ya tabbata duba da natsuwarshi da hankalinshi da kuma haiba da daitako tana ma Zulaihat fatan samunshi a matsayin miji, ta tabbata zai kula da ita zai bata kulawa kamar tsoka d'aya a miya ,bata da guri da fata da taga ta aurar da yaranta ga mazaje na gari masu nagarta da tausayi da amana,Murmushi tayi tana cewa.."sai kaje ka nemi so a wajen Mamana dan ba zan mata dole ba." Kasa kawai yayi da kanshi baice komai ba dan shi kunyar Umma yake ji,shima Dr Moha tambaya yayi shima a bashi dama ya nemi Zubaida numfashi Umma tayi tana cewa.

"Wannan kuma ba humurina bane Muhammadu.sai dai kaje wajen Mustapha, amman zan maka alfarmar ku fara fahimtar juna da ita sai na turaka wajen shi." Shima godiya sukayi mata sannan suka tashi dan tafiya,koda suka fito basu tadda kowa a tsakar gida ba suna cikin room din su.

Ba haka Dr Najib yaso ba ,yaso yaga Zulaihat koda sau daya ne ji yayi kamar ya kirata waya ta fito sai kuma yana jin nauyin Umma ba yanda ya iya haka ya hakura suka shiga motar. ji yayi bai iya koda driving nan ya mikama Moha key yana komawa wajen mai zaman banza ,ansar key din yayi ya tada motar suka tafi dan rage karar radio yayi yana cewa.."A gaskiya Zulaihat ta bani tausayi baiwar Allah.dan Allah Najib ka sauke girman kan nan naka ka kula da yarinyar nan. karda kace zaka nuna mata gadara azo ayi ba da kai ba naga hausawa na cewa durkusawa wada ba gadarcewa bace."

"Hakane ai kasan yanda nike sonta ba zan taba bari wani abu ya cutar da ita ba,amman na lura kanta rawa yake zan bita a yanda tazo man ne idan da hankali tazo welcome sai muyi soyayyarmu idan kuma da hauka tazo nan ma normal sai na nuna mata na fita iya hauka." Dariya Moha yayi yana cewa.."idan kuma tace bata sonka fah.?" Waigowa yayi yana kallonshi sai kawai yayi murmushi baice komai ba,shima Moha murmushin yayi bai sake cewa komai ba.

★★★

Kallon Zubaida tayi tana tabe baki tace.."dan ma baki ga yanda yake ma Umma biyaiya ba sai ki rantse kice bashi bane Dr Najib marar mutunci da tausayi ba, ita kuma Umma sai wani nuna jindadi take dan kawai bata san baida hali ba shiyasa ni wallahi bansan ko ganinshi gashi ya wani yi mana zaune a gida sai kace gidansu."ita dai Zubaida dariya tayi tana cewa.."Sis wallahi ki rage wannan abun ba abu bane mai kyau and ya kama ta dai ki rage wannan tsanar da kike mashi ina guje maki karda ta juye ta koma so fa." Dafe kirji tayi tana turo baki gami da matso yan kananun kwalla tace.."amman wallahi Sis kin gama dani kin cuceni haba Sis mai nayi maki mai zafi haka? Da zaki hadani da Dr Najib ko masoya na rasa ai wallahi ba zan iya soyayya dashi ba balle aure koda shine autan maza kuwa."

Yanda take maganar har cikin zuciyarta take fitowa wata irin tsana take ma Najib yanda bai sonta itama bataji zata iya son shi ba,dariya ta kama yi tana cewa.. "Kedai ki bar cika baki wallahi ni soyayyarku dariya ma take bani Allah ko." Tashi tayi tana kaima Zubaida bugu tana cewa.."wallahi Sis ki fito idona na kulle.ban san haka ban san wulakanci ni ba kawarki bace na lura kin rainani a gidan,amman tunda ni bakijin magana ta bari naje na fadawa Umma sai ta shiga tsakanina dake.."

Rikota Zubaida tayi tana yin kallar tausayi tace.."na tuba ba zan k'ara ba Aunty ki yafeman. karki hadani da Umma daman tana cikin wannan fushin kuma ki k'ara daura man wani ba zan sake ba amaryar Dr." Pillow ta wurga mata tana tashi ta bar mata dakin ,parlon Umma ta shiga tayi kwaciyarta bisa three seater tana karatu dan ta lura idan ta biyema Zubaida sai ta bange a banza bata karanta komai ba gashi Monday zasu fara exams.

Tunda abun ya faru su Zulaihat basu sake shiga school ba suna gida suna karantunsu basu aikin komai dan Umma ta dauke masu tace suyi karatun ita zataji da aikin gidan,da sunso yi mata gardama amman ta nuna ita haka take bukata kuma take so sai suka saka mata ido kawai suka cigaba da karatunsu idan suka samu sarari su dan kama mata koda girki ne.

Yau zasu fara exams tun asuba basu tsaya siririta ba da wuri sukayi komai suka fita kuma cikin ikon Allah suna fita suka samu mai naped tsaye a kofar gidansu koda suka tambayeshi tafiya zaiyi? yace masu eh,suka shiga suka gaya mashi inda zai kai su koda ya kaisu. da zuka bashi kudi yace a'a an bashi kudin tuni daukarsu ce kawai nashi sunyi mamaki sauri suke shiyasa basu tsaya tambayarshi waye ya sakashi wannan aikin ba suka shiga exmas hall zuciyarsu fal da mamaki.

★★★

Alkhamis yasha wuya a hannun yan sanda dan mugun bugu sukayi mashi,gashi makaranta ta hana a bada bellin dinshi ba yanda iyayenshi basuyi ba da sunzo wajen Dean affairs sai yace masu sai dai sunje wajen Dr Najib shine kawai zaice ayi belling dinshi ayi .dan shi yayi ma rashin kunya a matsayinshi na malami ,haka iyayen Alkhamis suka kama zarya basu wajen Najib basu police Najib ya kulle ido yaki cewa komai koda sunzo sai dai yace su tafi gida za'a sakeshi haka ya kama yi masu.

Yau Alkhamis satinshi biyu a wajen police duk sun chanza mashi kamanni sun koya mashi tarbiya koda Dr Najib yazo sai ya kama yi mashi kuka yana cewa ya tuba yasa a sakeshi ba zai sake ba,sab'anin da.da yake auna mashi zagi yana cewa idan har ya fito sai yayi ma Zulaihat abunda har su mutu ba zasu manta dashi ba.haka yake cewa a duk lokacin da Dr yazo police din.

Murmushi Dr Najib yayi da aka fiddo mashi Alkhamis ya durkusa a gabanshi sai kuka yake yana mashi magiya akan ya tuba ba zai sake ba. ya bar shi haka ya hukuntu ,kallonshi Dr Najib yayi yana ce ma D.P.O.."Oga ni har yanzun ban yarda da tuban yaron nan ba,dan haka kawai a mai dashi a cigaba da koya mashi hankali kawai gaskiya."

Rike mashi kafafu Alkhamis yayi yana kuka yana cewa.."dan Allah ka rufaman asiri ka duba Allah ka dubi girman Allah kayi hakuri wallahi ba zan sake ba har abada ni inda take ma wallahi ba zan sake kallo ba. unguwarsu ma ba zan sake zuwa ba." Cire hannunshi Dr Najib yayi d'aga jikinshi yana kallon D.P.O yace.."har yanzun dai ina kan bakana ban yarda dashi ba tunda dai kaima shedane akan furuncin da ya dunga yi akan dilabata,karda a sakeshi yaje yayi mata wani abun kamar yanda yake fadi."

Gyaran murya D.P.O yayi yana kallon Alkhamis yace.."Kwarai kuwa da bakinka kace zakayi mata abunda har a mutu ba za'a manta ba,Kaga kenan furuncinka sun kunshi abubuwa da yawa irin su fyade da bugun mutuwa kai harda ma kissan kai duk suna ciki tunda jam'i kayi."

"Wallahi Aa ku rufaman asiri daman fadi kawai nike amman ba har zuciya ba dan Allah Yallabai ka gafarceni wallahi nayi maka alkwarin unguwarsu ma na daina zuwa." Girgiza kai D.P.O yayi yana cewa.."wannan maganar ai bata kyalewa bace Alkhamis kayi furuci ai,dan haka cell zamu maidaka case dinka za'a kai shi a kotun sulhu gaka ga iyayenka ga iyayen yarinyar da kuma wasu d'aga cikin dalliban makaranta har da yan unguwarku da yan unguwarsu da kuma mu da alkhali anyi komai a rubuce shedu susa hannu sannan zaka bar wajen nan."

Ba kukan da Alkhamis baiyi ba amman a banza haka aka sake mai dashi D.P.O yasa aka rubuta takardu aka aika duk inda ya fada,washe gari kuma duk sun hallata bayan kowa ya zauna alkhali ya shigo aka karanto case aka kuma fadi furuncin da yayi akan yarinyar take alkhali yayi rubuta a takarda ya d'ago yaba maba takarda ya fara karantawa kamar haka..

_Ni Alkhamis Amadu nace zanyi ma Zulaihat Aminu abunda har ta mutu ba zata mantaba,dan haka na yarda duk abunda ya samu Zulaihat Aminu nine kuma na yarda da hukuncin da hukuma zata zarta a kaina mutane ku shedda._

Alkhamis cewa yayi ya yarda ya saka hannu aka ba kowa ya saka hannu akayi printing din takardar aka ba kowa tashi sannan akayi belling din Alkhamis har kasa ya duga yana ma Najib godiya dan shi kadai yasan wahalar da yasha a wajen yan sanda.

★★★

Tunda suka fara exams kullun da sun fito suke tadda mai naped a kofar gida shigewarsu suke dan idan sunce basu shiga to watarana kuwa zasu iya yin missing din exams dan unguwarsu akwai wahalar samun abun hawa..kuma sun tambayi mai naped wa ya turoshi sai yace wasu ne shi bai san sunansu ba,sun dai bashi kudi sunce ya ringa kaisu school daga ranar basu sake tambayarshi ba suka cigaba da hidimarsu.

Course din Dr Najib shine last peper dinsu a 200 level kuma cikin ikon Allah sun samu intervel har na kwana ukku,dukufa sukayi kan karatun dan ko dan aikin da suke fitowa suna taya Umma dainawa sukayi da Umma tace duk karatun ne ya hanasu motsi har haka? Ce mata sukayi eh ai course din Dr Najib ne course din yana da wahala gashi kuma malamin da ya dauki course din shima ba sauki gareshi ba.dan har yafi course din zafi ma,sosai Umma ta kama yi masu dariya wai yafi course din zafi kenan zafi biyu ya hade masu a waje daya.

Ana gobe zasuyi course din kusan kwana sukayi zaune sai wajen 3:30 suka kwanta shima Dr Moha ne ya kira Zubaida yace idan karatu suke su ajiyeshi hakanan su kwanta karda suje filin exams din kuma su manta abunda suka kwana suna karantawa.

Godiya tayi mashi da shawarar da ya basu ta kashe wayar tana kallon Zulaihat da keta karatu tana gengadi tace su kwanta inji Dr Moha aikuwa ko gardama ba tayi ba ta kwanta daman ta gaji ga ciwon kai,koda suka tashi da asuba suna sallah suka cigaba da karatunsu sai wajen Tara suka fito tsakar gida danyi wanka. suna fitowa suka shirya abinci suka ci bayan sun gama suka cigaba da karatunsu da yake sai 12 suke da exmas din.goma nayi suka kira mai naped dinsu yace ai yana kofar gidansu tuni har zasu tashi Umma ta fito tana cewa.."idan kun fito ku biya wajen gyaran kai da kunshi ayi maku dan gobe zakuyi bak'i." Da to suka ansa bayan sun anshi kudin da ta basu suka wuce zuwa 11 suna cikin makaranta samun waje sukayi suna cigaba da karatunsu har 12 ta kusa suka je venue suka zauna.

Alhamdulillahi dadin karatu kenan,yanda wasu ke kukan tayi zafi wasu kuma murmushi suke suna cewa tayi dadi sosai wasu kuma tsaka-tsakiya batayi zafi ba batayi dadi ba sosai, koda suka dauki bags dinsu suka kama hanya dan samun abun hawa su wuce wajen gyara Dr Najib ya parking gabansu kallonsu yayi yana cewa.

"kullun ai sai nace ku shigo kuke shigowa ko.?"
Zubaida ce ta bude ta shiga tana cewa.."sorry sir." Itama Zulaihat shiga tayi amman batace komai ba tada motar yayi yana cewa.."ya Exmas din." Nan ma Zubaida ta bashi ansa da Alhamdulillah amman mutuniyar bace komai ba sai ma maida hankalinta waje da tayi tana kallon mutane shima watsi yayi da ita ya cigaba da driving dinshi Zubaida ce ta gaya masu inda zasu har bakin wajen ya kaisu yana ba Zubaida kudi su kara amman taki ansa sai da yayi mata Jan ido ta ansa yace idan sun gama suka rasa abun hawa ta kira Moha sai azo a daukesu da to ta ansa tayi godiya suka shiga....Da kallo ya bisu yana murmushi wai shi Zulaihat take ma haka zaiyi maganinta ne soon ta dai shigo hannunshi.

*Ayyya Dr Najeeb kafa fiye complain fah🤔,ba Kai ka koya mata irin halin ba lol😂*

Koda suka shiga ciki tarba suka samu ta mutuncin kamar dai ko da yaushe sun tadda ana ma wasu amare gyaran jiki sai suka samu waje suka zaune,Zubaida ce ta lissafa kudin da ya basu d'agowa tayi tana kallon Zulaihat tace.."Sis 15k ce ya bada."

Please Login or Register in order to submit comment