Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi masu set daya daga gado har kujeru da kuma kayan kitchen ba abunda bata sayar masu ba daga kan kayan electric har zuwa kayan ma'aikaci.

Baban Zubaida shima yayi kokari dan yayi ma Zubaida kayan daki komai set biyu sai yayi ma Zulaihat set daya itama ya ce gudunmuwarshi Shima. Wajen gara kuma da kore komai sai da Umma tayi dan tace zata kashe ko nawa ne wajen ganin ta fidda yaranta kunya dan ta lura da gidan da za'a kaisu zatayi dai dai kokarinta ba kuma zata cuta kanta ba.

Shirin tafiya jigawa suke dan Zulaihat zataje tayi ma dangin mahaifiyarta hutu Koda na wata daya ne ta kuma yi masu bankwana Zubaida zata rakata.Washe gari suka kama hanyar Jigawa haka suka tafi suka bar Umma cikin kewarta dan ji suke kamar su rushe da ihu dan Zulaihat sai da ta koka.

★★★

"Yaushe zamuje jigawa.?" Ajiye cup din hannunshi yayi yana cewa."ba rana gaskiya." Tsaki Najeeb yayi yana wurga ma Moha harara yace."idan kai baka zuwa ni zanje dan nayi kokari kusan one month banganta ba."

"Ai zuwan namu baida amfani Najeeb." Kamar ya kenan."? Kamar yanda kaji nace haba Najeeb kana ban mamaki sai kazo ka damu mutane da aje wajen yaran nan kuma idan anje sai ka kama.wani daure daure bama ka yi mata magana sai dai ita tayi maka.abun bakin cikin ma wanda yake ciman tuwo a kwarya idan tayi maka maganar sai ansawa tayi maka wuya sam baka kyautawa wallahi kana ma Zulaihat abunda ka gadama dan kawai kaga tana tsoranka. dan haka ba inda zani kana iya zuwa kai daya idan ta damaika."

Ok haka ma kace kenan.?yes haka nace ba zani ba Najeeb Allah ya tsare hanya amman jigawa kam ba dani ba." Fine tunda baka zuwa." Banza Moha yayi dashi ya cigaba da kallonshi dan shi wannan miskilancin banzan nashi haushi yake bashi. ace aita hama da mutun ya chanza hali ya kasa,da anyi magana sai yace haka Allah ya yi shi ai shikenan.

Shima Najeeb bai sake cewa komai ba sai ma lumshe idanunshi da yayi yana taune kasan lip din shi.hakan da yayi ya nuna bai ji dadi ba akan maganar da Moha din yayi mashi,Daman shi idan aka bata mashi rai abunda yake kenan har sai ya huce.tabe baki Moha yayi yana tashi ya bar mashi parlorn ya tafiyar shi part din Hajja ko drama ma sunyi zai fiye mashi akan wannan miskilancin na Najeeb Wanda bai ragama kowa ba.

Bayan fitar Moha ya dauko wayar shi ya lalubo number dinta har zai daina dialing sai ya fasa. yayi haka ya kusa sau goma yana fasa,dan tunani yake idan ya kirata yace mata mai?shi dai yasan yana sonta amman bai san ta wace hanya zaibi ya nuna mata hakan ba,bai san ya zaiyi ba. ya nuna mata daga ita babu wata ya nuna mata itace sarauniyar zuciyarshi itace sanyi idanunwanshi sanann baki daya itace rayuwarshi ya yarda tuni ba zai iya rayuwa ba idan babu ita . ba zai iya yin komai ba. ba tare da tana a kusa dashi ba.ya yarda zai iya yin komai a hakanta kuma zai zama bawa a kanta.zai mallaka mata komai nashi.zai bata ragamar rayuwarshi. itace shi itace itace itace har baisan ma taya zai kwatanta matsayinta a zuciyarshi ba.

Furzar da iskan bakinshi yayi yana tura hannunshi a cikin sumar kanshi yana mai kara lafewa a saman tower din da yake zaune dan murmushi yayi yana dafe zuciyarshi dan ba abunda zuciya take muradin gani da Ji sama da ita , zuciyarshi tana azabatarshi akan rashin ganinta da yayi. yana jin kamar yayi fiffike ya ganshi zaune a gabanta koda kuwa ba zasu ce ma juna komai ba kuwa.

Ganin zaman ba mai karewa bane ya taitara wayoyinshi ya wuce part din Hajja koda ya isa ciki ciki yayi sallama yana turmuke fuska dan yasan Hajja na da cikinshi jiranshi take.dan jiya ma da ya biye mata da sunyi tas dan kawai ya tashi ya bar mata part din.

Samun waje yayi ya zauna yana cewa.."barka da hutawa Hajja." Gyara farin glasses din ta tayi tana kallonshi da kyau sanann ta maida kanta gefe tana cewa.."Moha ni kam nace yaushe zaka hadani da kishiyata mu gaisa?ko har da nima rowarta ake mana.?" Dariya Moha yayi yana cewa.."ba dole nayi maki rowarta ba. tana sabon jini da ita kizo ki goga mata tsufa."

Kame baki tayi tana girgiza kai tace.."uwaka nace Moha dadina da kai ba'a abun arziki da kai sai ana maganar hankali ka sako halinku na faranci."...fashewa da dariya Moha yayi yana cewa.."ke dai kawai na harbo jirginki kishi ne kawai yake dawainiya dake.kuma dai banyi matar dake zuciyar Moha ta gimbiyar Zubaida ce."

Fari Hajja tayi da Ido tana tashi ta juyawa da gyara glass tace.."ai nasan nafi matar taka kalleni da kyau ,nima ai na daina yin mijin da kai mai zanyi da kai nida nike da Najeeb." sai a lokacin Najeeb yayi magana yana cewa.."habawa tsohuwar nan wato yaudarar kaina ta dawo kenan?tunda Moha ya sakeki shine kaka dawo wajena to bani so kije can ki koma wajen Moha dan ni kuwa na bar mashi sarauniyata ta isheni."

Kallon Moha Hajja tayi tana cewa.."Moha daman wanann miskilin banzan har soyayyya ya iya?ni Ina mamaki yanda Zulaihatu ta yarda da aurenka ma,ko mai yake ce mata idan yaje zance da har ta yarda da auren wannan murdadar mutumin oho."

Tashi yayi zaune yana cewa.."sai da kuma na kasa ba, kalaman da nike gaya mata special ne ba kowa mace take samunsu ba a wajen saurayinta kin dai ji."

"La'ilaha'ilailahu ni Aminatu yar Amadu naga ikon Allah da baida karshe
yanzun tsakani ga Allah in banda kaddara wace mai tsotsayin ce zata aureka?mai zata samu inba fadin rai ba da miskilancin banzan da wofi .Ina ce dai halinku daya shine tafiyar zata tayi nisa. Banza yayi da ita bai sake ce mata komai ba .da suka damaishi da surutu sai ya bar masu part din yaje wajen Ammi(mahaifiyar Moha) suna gaisawa yaci abinci ya shige bedroom yayi kwanciyar shi dan yau jinshi yake duk bai jin dadi kuma haka na dangane da rashin ganin ta ne yasan da hakan.

Baccin kasa zuwa yayi,daurewa yayi ya janyo wayarshi yayi dialing din wayarta har tayi callend bata dauka ba.lumshe idonshi yayi ya bude a saman screen din wayar wai shi Najeeb yake kiran mace waya tana kin dauka,mamaki fal a zuciyarshi. sai da ya kusa five minutes sanann ya kara trying din kiranta nan ma no answer yaji ba dadi dan yasan tana kusa kin dauka tayi saboda wulakanci da rashin kunya da kuma rainashi da tayi .

Kwafah yayi yana ajiye wayar yace.."soon zanyi maganin wannan rashin kunyar taki nayi maki alkwari Babe zan kama ki ne." Sake lumshe Ido yayi sai kuma ya saki murmushi yana sake daukar wayar yayi trying din number again sai da ta kusa zama miscall sanann ta dauka kuma tayi shuru bata ce komai ba,Shima a nashi bangaren kasa cewa komai yayi duk da yana da abun da yake son yace ,amman bakinshi ya kasa furtawa sai dai ajiyar zuciya da yake ta saukewa, sun kusa 10min a haka sannan ya numfasa yace.

"ya mutun gida?"Kamar wanda aka yi ma dole haka yayi maganar ita har dariya abun ya kusa bata daurewa tayi tana cewa."duk suna lafiya." Sauke ajiyar zuciya ya sake yi yana cewa."and you hope kina lafiya." Sai da ta mula sannan tace.."Alhmdulh."

Ok fine bye." Kashe wayar yayi yana jin sanyi a ranshi da ta kasance cikin koshin lafiya,itama a nata bangaren rike wayar tayi tana kallo zuciyarta cike mal da mamaki.dan tunda aka saka.masu ranar biki bai taba kiranta waya ba sai yau...kuma bai taba tambayar lafiyarta ba sai yau and bai taba nuna ya damu da ita ba sai yau hakan yayi mata dadi sosai bata san sanda ta kama sakin murmushi ba. sai da tayi mai isarta sannan ta ajiye wayar ta fito waje ta shige cikin mutum gida suka cigaba da hidimarsu amman kallo daya zakayi mata kasan yau fuskarta tana cikin farinciki da annashuwa marar musultuwa.

*BAYAN SATI UKU*

Yau su Zulaihat suka komo gida kano a inda suka tarar da Ummi ta tanadar masu da masu gyaran jiki jiran dawowarsu kawai ake dan a ranar da suka dawo a ranar aka fara dan bikin baifi saura wata daya ba,shiyasa shirin ya kankama kamar ba gobe. kuma ta tadda a kara mata set daya na kayan daki itama sun koma komai set hudu kamar yanda Zubaida take da,ranar sai da tayi kuka ta kuma yi ma iyayenta addua harda Umma ma,dan har inda aka ajiye kayan nasu Umma ta kaisu tace su duba suga abunda babu sai su fadi a sawo masu sosai suka duba ba abunda ba babu. dan wani abun ma basu taba ganinshi ba sai a wajen,haka suka gama duba komai sukayi ma Umma godiya suka rungumaita sai kuka suke itama daurewa tayi ta lailashesu.amman ita daya tasan yanda take ji akan rabuwa da yaran nata da suka kasance tamkar uwarta da ubanta dan bata ganin kowa sai su sune take gani taji dadi a ranta.bama kamar Zulaihat da take rage mata radadin rashin dan'uwa da kuma iyaye dan Zulaihat tana kama da mahaifiyarsu Umma kwabo da kwabo komai nata irin na mai sunanta take yi kadan ta dibo daga mahaifiyarta.

Tabbas komai lokaci ne mutuwa haihuwa da kuma aure ba zasu zo ma mutun ba har sai lokacin yayi ga shi lokacin rabuwa da yaranta yayi ba tare ta hango abun nan kusa ba ,dan ta sakankance akan sai sun kammala karatu sannan za'ayi masu aure to daman ance kana naka Allah na nashi haka daman abun yake.fatan ta Allah ya basu zaman lafiya ya kauda fitina ya kuma basu zuri'a daiyaba ta gari wanda zasuji tausayinsu su kuma taimakesu.

Dakyal Umma ta samu sukayi shuru dan sai da tayi masu jan ido sannan suka hakura da kukan suka share hawayensu, nan suka koma inda ake masu gyaran jiki aka cigaba da yi.

★★★

A bangaren su anguna ma ba a barsu a baya ba dan sun kammala komai lefe ne kawai bai iso ba shima masu hado lefen ne basu dawo ba amman sun kusa dawowa dan ingila akaje dan hado masu lefen.dan Hajja da kanta tace aje ko wace kasa a hado masu lefen na gani na fada sannan kuma a edu estate gidansu yake dan babban gidane mai dauke da shashe hudu kuma ko wane shashe yana da upstairs a sama akwai three bedroom ko wane bedroom akwai toilet sai kuma kasan ma two bedrooms ne sai kitchen da store haka ko wane part yake.

Najeeb yana da daya sai Moha sai kuma Khalled shima idan yayi auren nan zai kawo matar.dayan part din kuma na yaransu ne maza idan Allah ya kawosu sai BQ akwai garden sai pool gidan yayi kyau sosai so Masha Allah sai Wanda ya gani...haka rayuwa ta cigaba da tafiya ta ko wane bangare babu ko wace matsala dan sun fahimce juna tun daga kan amaryen har iyayen ma dan Umma tana iya shafe awa daya tana waya da Ammi ko kuma Mom dan kuwa idan ta fara da Hajja har sai ta kusa yin ciwon ciki dan dariya dan Hajja ta dunga janta fada kenan tana ce mata ai sun kusa anshe yanmatan ta su dawo wajensu haka zasu kama yin gwanin sha'awa.

*KYIV UKRAINE🥀*

Saukowa take daga upstairs so gently kallon daya zaka yi mata ka gane ta samu sauyi.sauyin ma ba dan kadan ba tun daga kan shigarta zuwa annurin fuska duk sun chanza daga yanda suke a baya...sauyin bakomai bane face haduwarta da su A.Kadir da kuma iyayenshi mutanen arziki.da suka yanjo ta a jiki suka maidata a matsayin yarsu duk da taki ta aminta da soyayyar dansu.

Amman hakan baisa sun watsar da ita ba ko kuma sunyi mata korin rayuwar da suka taddata a ciki a da,a'a sudai kullun fatansu daya ta ida dawowa daidai ta kuma koma ga mahaifarta kasarta ta haihuwa ta koma ga iyayenta su cigaba da rayuwarsu kamar da.duk da kuwa har yanzun basu tambayi abunda yayi sanadin barowarta a wajen iyayenta ba ko sau daya basu taba tambayarta ba. kuma basu da alamar tambayar tata rayuwarsu kawai suke,kamar daman sune iyayenta dan a yanzun har sunfi nuna mata kulawa akan tilon dansu da suke jin har cikin jininsu.

Murmushi tayi tana hade hannuwanta wajen daya tana cewa.."Sorry." Dagowa yayi yana harararta cikin wasa,sai kuma ya langwabar da kanshi gefe yana mai kureta da Ido,jin idanunshi na yawo a jikinta yasa ta turo baki tana mai rufe fuskarta da tafin hannunta,Shima murmushin yayi yana cewa.."ki bude fuskan mana,na ida kallon kyawkyawan budurwata kuma mata ta and wanann shine kawai hukuncinki na wasting time dina da kikayi bayan kinsan muna da wajen zuwa da yawa."

Dirdire kafafu ta fara yi tana cewa.."ba nace kayi hakuri ba,kuma ai ba laifi na bane bacci ne ya sace ni fa." Kureta da Ido kawai yayi yana tura hannunshi cikin kwantaiciyar lafiyaiyar sumar kanshi da tasha gyara,gyaran ma irin na larabawa dan daman sumar shi sak irin tasu ce. dan har yafi wani balaraben sumar kai har da kyau ma dan sunan kawai mahaifarshi tana a nigeria amman idan aka kalleshi ga wanda bai sanshi ba sai ace ba daga Nigeria ya fito ba. sai dai makka ko Madina dan ko a turkey ba za'a sanyashi ba dan ba irin kyaun yan kasar gareshi ba balle kuma India.

Shidai a rayuwarshi ba abunda yafi so da kauna a wajen mace saman da shagwabe.tana saurin tafiya da imaninshi yaji idan ba mace ba to sai rijiya.yana jin itace partner dinshi kuma zai rayu da ita har *ABADAN* yana jin haka a ranshi idan har akayi mashi shagwabe shiyasa yake son mace yar shagwabe ita kuma Beauter al'adarta kenan shagwabe dan har ta zaman mata jiki.dan bata sanin tana yin ta ma,wanann shagwabar tata tana bada gudumunwa sosai wajen sonta da yake.(yan'uwana mata ku daure ku koyi shagwabe idan baki iya ba,idan kuma kin iya ki zage damtse kina ma maigida har mararsa aure ku dunga yi ma saurayinki idan kuna waya.shagwabe na sa shakuwa da dankon soyayya a tsakanin masoya wallahi sai kin zama ta musaman especially kina dan turo baki gaba kina dirdira kafarki da yarfa hannu kina shirin sakin kukan so gwada wannan a wajen Oga Zaki Sha mamaki,amman fa karda a yarfa hannu fari tas ba ko dan kunshi fah warrr🙄,and yanmata kuma karda kuyi diredire a gaban saurayi ahtoh ki dai turo baki da yarfa hannu kodan yaga kunshinki ya kuma yaba infact Alhaji shagwaba duniya ce🥂)

Hura mashi iskan bakinta tayi tana cewa."mudai mu tafi kaga inajin yunwa."ta ida maganar tana turo baki,ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yanda ta cinno mashi dan karamin pitch lips dinta da sai ka rantse da Allah shafa masu pitch lipstick tayi amman ko daya haka Allah ya hallaci bakin,yi yayi kamar zai kamo bakin taja dan baya kadan tana mashi dariya, girgiza kai yayi yana nuna mata bakin yace.

"Wannan bakin ko?yana shigarman hanci da gudundune ya guje randa zai fatoshi."farrr tayi mashi Ido tana cewa.."sorry Oga." Dariya yayi yana kama hannunta suka fito baice komai ba ,kuma shigar tayi mata kyau sosai duk da tana da brown skin amman komai kyau yake.mata kamar ba ita ba tayi kyau tayi kyau har yajin kishin wani ya kalle mashi ita yaji yanda yake ji a kanta a yanzun haka,sai dai ko yace ta koma ta sake kaya wasu kayan yake son yace ta saka bayan wannan shigar ita ta koma yi tunda suka shigo rayuwarta tabar saka kananun kaya tana fita waje ba tare da ko ta saka hula ba.

Amman yanzun ko haka aka tsaya yasan sun samu lada tabar shigar kananun kaya.sannan yanzun abaya(after dress) kawai take sakawa kala kala different campany haka Ammie take sawo mata su itama idan ta fita shan iska tana sawowa balle uwa uba Kadir da kusan kullum.sai ya kawo mata su tun tana lissafa yawansu har tazo da ta daina saboda yawan sai kuma veils da caps masu kyau haka suke sawo mata suna bata dan kawai ta kulle gashinta.

Da kanshi ya bude mata front ta shiga sanann ya zagaya ya shiga suka wuce escape garden dan tana nan suke son farawa. aikuwa tunda suka shiga kallo ya dawo kansu dan kaf wajen babu na biyun su wajen kyau harda saka kaya masu tsada,sun dan zagaya sosai sunyi wasa sosai a wajen daga nan suke je Teaning coffee anan suka sha coffee haka dai suka kama yawan bude Ido duk da daman duk inda sukaje ba bakon su bane kawai dan suna son dan rage zaman gidan ne ba kamar Jidda(Beauter) da tafi sati bata leka koda da kofar gida ba.

Sun sha pictures dan duk inda sukaje sai sunyi picture sai kuma su kama gardama nafi kyau nafi kyau,bayan sun dawo gida suka zauna kallon pictures dinsu wani sukaje kanshi wanda sukayi Beauter ta daura kanta a kafadarshi shi kuma ya waigo yana kallonta sai murmushi suke su dukansu aka daukesu sai kuma wani da ta kwanto bisa bayanshi ta turo kanta a kafarshi tana kallon fuskarshi. shi kuma ya lakutar mata kumatu suna dariya nan ma gardama ta kurre a tsakaninsu nan ma Jidda ya fara kuka tana cewa.

"Allah nafika kyau haske ne kawai ka fini fah kuma ai yanda kake cewa baka shafa poder ba haka nima ai ban shafa komai ba,ba zuwa kayi ba kayi man zaune ina fitowa wanka na saka kaya kawai.na sauko." Yanda tayi maganar tana tura baki tana yarfa hannu sai yaji Ina yana son a cigaba da yin gardamar ma dan kukan kyau ma yake Kara mata kamar wata brown shuwa,daure fuska yayi yana yin zooming din pic din yace." Haba Babe duba fa ki gani jibi hancina jibi naki kamar ankife kunkuru a roba ko anan ai kinsan na fiki." Shafa hancin nata tayi tana mai kara volume din kukan shakiyancin da take tana cewa.."Allah ko aa kuma sai na kai kararka a wajen Ammiena kana ce ma hancina kamar yan rufe kunkuru kuma na b'ata da kai ma." Ta ida maganar tana juya mashi baya,maida dariyarshi cikin ciki yayi yana yin hunging dinta ta baya yana cewa."haba Myluv kina son yau kenan na kwana a asibiti ko."?tureshi tayi daga jikinta tana cewa.."yo ba kaine ba." Kama kunnenshi yayi yana dukawa yace."am sorry life na tuba ba zan sake ba nawane kamar kunkuru."

"Nidai nidai sai ka buga kanka sannan zan hakura idan kuma ba haka ba gobe ba zanyi break ba harda lunch da dinner ma." Kama baki yayi yana cewa.."haba partner rufaman asiri kina son yunwa ta kama man ke kenan."?banza tayi dashi girgiza kai yayi yana marin kanshi zai.kara ta rike hannun tana girgiza kai sai kuma ta duka itama tana hura mashi iskan bakinta a idan ya mara din har da guntun hawayenta,shi kuma hawayen yake goge.mata sun dade haka dakyal tace.."sorry na hakura amman ai bance kayi.marin da karfi ba ko."? Kissing dinta yayi yana tadata tsaye ya zaunar da ita saman sofa nan suka danyi labari ganin 1am tayi ya tashi dan tafiya gida.

★★★

*NIGERIA 🥀*

Yau ake kawo lefen su Zulaihat gidan cike yake da mutanen Umma yan ansar lefe su kuwa amare bama su gidan suna neighbor dinsu kwance suke a saman sofa sunyi jigum sun kurama tv Ido,a zahiri kallon tv suke amman a badiri sam hankalinsu ba anan yake ba bama kamar Zulaihat da tafi Zubaida jin fargabar auren.

Ba auren take ji ma tsoro ba dan daman ya zama dole tayi shi da lokaci yayi koda kuwa ba da Najeeb ba.zaman da zatayi da Najeeb shi take ma fargaba da tashin hankali bata san da wani irin hali zai ansheta ba da mutunci ko kuwa da wannan murdadar halin nashi wanda yake da wuyar sha'ani.

Hawaye ne suka ziraro ta share tana mai sauke ajiyar zuciya tana tsoron Allah tana tsoron zaman da zatayi da azzalumin mutum kamar Najeeb.mutumin da baisan darajarta ba yana mata kallon kasa kasa gashi bama nan kusa zasu zauna ba tafiya mai nisa har abuja...kawai daura hannun tayi a kai tana kuka kamar jira itama Zubaida ta barke nan suka hade waje daya suna aikin kuka cikin kuka Zubaida ke cewa.

"Dan Allah Sis ki yafeman komai nayi maki a zaman da mukayi ki yafeman Dan Allah." Nan ma kukan ya kara yin karfi dan ita Zulaihat kasa cewa komai tayi sai ma.kukan da ta volume,shigowar Aunty Nana gida ta tadda kukan da sukeyi tafa hannaye tayi tana salati tace.

"Ohni Nana mai zan gani haka ni kam Nana Aishatu amare har an fara kukan rabuwa da Umma tun yanzun." Idasa shigowa cikin parlorn tayi tana lailashensu da bada baki dakyal ta samu.sukayi shuru nan ta zauna tayi masu wa'azi sai da mangariba ta gabato sannan suka dawo gida lokacin da suka shigo gidan tsit yake ba kowa a gidan sai Umma duk kowa ya tafi gidanshi.

Zama sukayi suka gaida Umma sanann suka dauko abinci dan suci.dan kadan suka dan tsakura suka cire hannu.kallon abincin Umma tayi tana cewa."maza ku maida hannunwanku ku cinye abincin nan tun kafin ranku ya baci." Marairaice fuska sukayi a tare suna cewa."Ayya Umma wallahi mun koshi."murtuke fuska Umma tayi tana cewa."yaushe na fada kuna man gardama."? Girgiza kai sukayi suna mai janyo cooler din suka cigaba da tura abincin dan komai ya fice masu a rai ba dan basu san cin abincin ba kuma ba dan basu jin yunwa ba,hakanan sukaji cikinsu a tunkushe yake kuma bakinsu bai da testing ko kadan.

Sai da suka gama cin abincin sannan Umma tace su biyota,babu gardama suka mike suna bin bayanta har cikin bedroom nan tace.."ga lefenku nan ku kalli kokarin da yaran nan sukayi, Allah dai yayi masu albarka da ku baki d'aya ya baku zaman lafiya ni har tsoro wannan lefe ya bani Mamana har cewa nayi sunyi yawa a maida wasu amman fir iyayensu suka ki ansa,amman lefe akwati shabiyu ai yayi dashi ga mutun daya yawa." Dan murmushi Zulaihat tayi tana mai kare ma set 24 na akwati ido tabbas da gani an kashe kudi a wajen nan duk da bata bude ba akwatin kawai ta kalla tasan ba karamin akwati bane,dan kallon Umma tayi tana cewa."gaskiya kam Umma sunyi yawa ina laifin shida shida amman har sha biyu muyi ya dasu."

"Nima abunda na gani kenan ai shiyasa nace a maida na mutun daya a dauki na mutum daya sai a raba maku,amman suka ce ina sam basu san da haka ba,kuma ko tukuncin da ake badawa da aka basu kin ansa sukayi dakyal aka samu suka tafi da lemu." Cewar Umma daga lefen suke daya bayan daya suna kallo abun sha'awa da burgewa dan komai da ke cikin akwatim choice dinsu ne kamar sun tambayesu kasa boye farincikinsu sukayi itama Umma ta kama tayasu a haka har suka gama sannan suka kulle suka dawo parlor.

Nan fa Umma ta kallesu tace.."Zulaihat, Zubaida."a tare suka dago suka kalli Umma take idon Zulaihat ya fara tara kwalla daman kukan take son yi hakuri take tana kokarin maida shi dan bata son tadama Umma hankali a tare suka ansa suna mai maida kansu kasa,cigaba da cewa Umma tayi.

"Kunga dai yau saura kwana bakwai a daura maku aure ku zama matan aure nan gaba kadan ku zama iyaye wanda zasu bada tarbiya." Dan shuru tayi tana maida abunda ya taso mata ta maida hawayenta cikin wayau da dubara dan karda su gani su tada hankalinsu,cigaba da cewa tayi.

"Abunda zance anan shine Allah yayi maku albarka ya baku zaman lafiya mai daurewa har abada nasanku nasan halinku nasan kuma tarbiyar da na baku dan Allah Ina neman alfarma a wajenku dan Allah kuyi ma mazajenku biyaiya karda kuyi masu abunda zasuyi nadamar aurenku,sannan kuma kuyi ma iyayen mazajenku biyaiya suma harda kakarsu ku mutunta yan'uwansu karda naji kuma.karda na gani ku zauna da kowa lafiya da kuma zuciya d'aya tsakani ga Allah,yi nayi bari na bari shikenan anzauna lafiya,ku sani zamanku lafiya a gidan mazajenku shine zai sani farinciki shine zaisa na yarda da na baku tarbiya ta gari amman rashin zaman lafiya

Please Login or Register in order to submit comment