Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ma Ammie gardama tayi sai tashi da tayi batace komai ba ta shiga bedroom din ta sauya kayan jikinta tayi tasa abaya kamar yanda Ammie ta umirceta harda saka hula ta kulle gashinta sannan ta fito,da kallo Ammie ta bita tana cewa.

"Masha Allah My Daughter kinyi kyau sosai bari naje na shigo da Dad ko."? Nan ma batace komai ba sai ma daga mata kai da tayi tana binta da kallo wacece ita koma wacece tayi mata matarta daga gani tana da daddatako. da sallama suka shigo ita da Dad ansa Sallamar tayi tana mai kallon Dad dan yayi mata kama da wanda ta sani sai dai ta manta ina ta taba ganin fuskar sannu da zuwa tayi masu tana mai tashi ta shiga kitchen ruwa da fruit ta kawo ta ajiye masu,da kanta ta zuba masu ruwan ta basu sannan ta yanka masu watermelon da pineapple da apple ta kuma ajiye masu ,godiya sukayi mata bayan sun gama shan ruwan sanann Dad ya fara magana.

"Sunana Alhaji Nurandeen Abu-kadir jigawa,wannan kuma matata ce sunanta Umma Salma Abubakar ko ke zamu iya sanin sunanki."!?

Murmushi tayi tana cewa.." Ur welcome." Dan shuru tayi kuma sai tace.."Am Hauwa'u Abdullahi Jibirin." Kallon Kallon akayi da Ammie da Dad ajiyar zuciya Ammie ta sauke cikin mamakin jin tana da sunan hausawa amman basu kawoma ransu yar Nigeria bace duk da Beauter bakace amman bakinta bai kama da na yan Nigeria ,murmushi Ammie tayi tana cewa.

"Masha Allah Hauwa,Allah yayi ma rayuwar ki albarka ko wace kasa kike sanann maiye religiou dinki."

Har cikin ranta haka Beauter taji dadin yanda Ammie ta saka mata albarka dan rabon da taji Kalmar ma har ta manta ji tayi hawaye suna son zubo mata tasa bayan hannu ta gogesu tana mai hana su zubowa tace cikin murmushi.

"Nigeria and am a Muslim." Kasa boye mamakinta Ammie tayi a wannan karan dan sai da fuskarta ta nuna haka kuma ta hango damuwa a saman fuskar Beauter kuma taga sanda take goge hawayen da suka zubo mata,to maiyasata kuka? Kuma maiyasata karaya har haka?tabbas da wata a k'asa a taitare da yarinyar nan,ruwa ta dauka tasha tana cewa.

"Ashe kasarmu daya ma Hauwa,Allah yayi maki albarka ya kareki daga sherin zamani kinji My Daughter." Daga kai tayi tana murmushi tace.."Amin Amin Mom thank for prying. " dan shuru suka dauka na dan lokaci sannan Dad ya cigaba da cewa.

"Hauwa'u daman munzo ne akan danmu." Dasauri ta daga kanta tana kallon Dad shima Dad din murmushi yayi mata yana d'aga mata kai ya cigaba da cewa.."kwarai kuwa munzo akan danmu ,Abu-Kadir Nurandeen wato A-kadir yazo yace mana yana sonki kuma yana son ya aureki amman kinki ki kulashi balle ki bashi hadin kan da yake bukata a tare dake wato aure. shine mukazo da kanmu mu rokeki alfarma dan Allah Hauwa'u ki taimaka ki auri A-kadir yana sonki muma kanmu iyayenshi munason ki dawo cikinmu ,mu zama family daya."

Tashi tayi tana girgiza kai tana mai rushewa da kuka,maiyasa kukazo mata da wannan alfarmar bayan kallo daya tayi masu taji ta samu iyaye wanda itama zasu ringa saka mata albarka,amman maiyasa? maiyasa? ba zata iyaba .ba zata iya jin zata sake soyayya ba ,ba zataji zata iya sake kallon d'a namiji ta gaya mashi kalaman soyayya ba.dukawa tayi a gabansu tana girgiza masu kai cikin yanayin tausayi da tausayin kanta tace.

"Kunzo man da abunda ba zan taba iyawa ba,dan Allah ku fahimceni Ku kuma yi man uzuri ,da ace zani iya da na anshi wanann alfarmar taku dan gani daya nayi maku naji inasonku kuma nasamu iyaye naso ace wata alfarmace ba wannan ba. da nayi maku ita ba tare da bata lokaci ba.dan kunyi man abunda na dade ba'ayi man ba,wato saman albarka da kuma yi man addua abunda yake da tsadar samu a wajena. dan rabon da a saman albarka ko ayi man adduar shekarun basu fado amman maiyasa kuka tambayen abunda ban iyawa."?

Tashi Ammie tayi ta dafa Beauter tana share mata hawayen fuskarta cikin nuna kulawa da damuwa tace.." Munji maganarki Hauwa kuma mun fahimceki amman kina da Wanda kike so ko."?

Da bayan hannun ta share hawayenta tana girgiza kaii tace.."ko daya Mom bani da wanda nike so,asali ma na tsani soyayya kuma bani yinta." Kallon Dad Ammie tayi tana auna maganar Beauter ta tsani soyayya mai akayi mata mai zafi haka a soyayya har tayi mata wannan tsana mai muni haka? Har zatayi magana Dad ya rigata yana cewa.

"Karki damu Hauwa'u mun fahimceki fatan zaki cire komai ki cire mun taba yi maki wata magana ta ki so danmu,ina son ki cigaba da yi mana kallon iyaye ko zamu samu wannan alfarmar."?...daga kai tayi tana cewa.." Amman Dad sai..."zamu samu wannan alfarmar eh ko Aa Hauwa."?Ammie ta katseta ta sake maimaita mata tambayar Dad,murmushi kawai Beauter tayi tana fadawa jikin Ammie ta rungumeta itama Ammie rungumeta tayi tana cewa.

"Allah yayi maki albarka Hauwa yayi ma rayuwar ki albarka Hauwa ya kareki da kariyarshi. mungode da wannan karancin da kikayi mana." Sakin Ammie tayi tana kallonta tana mai mamaki karanci irin na matar daga ita har mijinta yanzun taki yarda da soyayyar dansu amman hakan baisa sun nuna mata fushinsu ba sai ma kauna da suke nuna mata.hakan kuwa yayi mata dadi sosai har ta sake dasu suka danyi labari da exchanged content suka bata address dinsu sannan suka wuto gida.

Koda suka koma gida sai da sukayi wanka suka huta sannann suka kira A-kadir sai da suka yi dinner sannan Dad ya kalleshi yace.

"My son." Dago kanshi yayi yana kallon Dad sanann yace.."Naam Dad." Shafa gefen fuskar shi Dad yayi yana cewa.."munje gidan yarinyar da kake magana kuma mun ganta munyi magana da ita sunanta Hauwa'u Abdullahi Jibir yar asalin Nigeria ce,yarinyar tana da saukin kai amman idan akaje mata da saukin kai kuwa,munyi mata maganar soyayyarka ta nuna mata bata da interest akan soyayya,da farko naji haushi sosai sai na lura da wani abu a wajen yarinyar."

Kallon Dad yayi cikin damuwa yana cewa.."Dad mai ka lura dashi a wajen JIDDAH?Dad inasonta ina son na rayu da ita *DA'IMAN ABADAN* Dad please help me."

"Lura da son da kake mata yasa nayi control din zuciyata har na gano da akwai rauni a cikin zuciyarta wanda har yanzun yaki ya warke. kuma rauni a hanyar soyayya akayi mata shi. shiyasa ta tsani soyayya ta kuma ki kara ba so dama a karo na biyu,Son yanzun ta zama yar gida zamu cigaba da janyota a jiki har mu samu ta gaya mana abunda yasa ta daina soyayya ta nan ne kawai zaka samaita,amman idan har kace zaka nuna mata iko da isa ba zaka taba samunta ba balle har ku rayu *DA'IMAN ABADAN*."

Shuru yayi yana kallon Dad ruwa ya dauka yasha yana cewa.."Dad maiye solution."?dariya Dad yayi yana cewa solution daya ne shine ka fita a harkarta ma'ana kabar mata maganar soyayya ka koma nuna mata ta zama yar'uwarka kawai kana janta a jiki a haka zaka dasha mata tausayinka a zuciyarta zakasha mamaki and nasan waye kai sai dai zan kara tuna maka duk inda ka samu kanka kaji tsoron Allah."haka suka gama maganarsu suka wuce room dan kwantawa.

*NIGERIA🥀*

Koda ya koma gida wanka yayi ya shirya ya shiga kitchen ruwan tea kawai ya dafa sai ya dauko shawarma daya ya fara ci.time ya duba yaga har tara ta wuce na dare murmushi yayi yana kallon Dr Moha da yake ta danna waya yana murmushi, girgiza kai Dr Najib yayi yana daukar shima wayar tashi data ya bude ya shiga whatsapp ya dan yi replying din messages din da suke important a wajen shi. sannan ya koma IG nan ma yaga post din da suke da mahimcin a wajenshi sai da ya gama sannan ya kashe datar yana maida cup da plate din da yayi using dasu kitchen yana dawowa an she wayar hannun Dr Moha yayi yana tsaki yace.

"Aikin kenan danna waya ko gajia bakayi Moha kuma baka tsoron ko ciwon ido ko."? Harararshi Dr Moha yayi yana cewa.." Nidai Malan kaban wayata sai mutun yana jin dadi kazo ka tsinke mashi haba man."

Tsaki yayi yana cilla wayar a aljihu yana cewa.."ank'i a bada wayar haba Moha ni kana ban mamaki wani lokacin wallahi akan mai zaka bata lokacinka a wajen aikin banza."

Tashi Moha yayi yana cewa.. "Kasan Allah sai kaban wayata ashe aikin banza.soyayyarce aikin banza?idan aikin banza ce kai kakeyinta."? Wurga mashi wayar yayi yana tsaki yace.." Ni nace maka ina soyayya ai ko."?daukar wayarshi yayi yana cewa.. "Sai kace kana soyayya zamu yarda ai kasan dai ni ba karamin yaro bane ,wallahi Najib ina baka shawara tun wuri kace ma Zulaihat kana sonta idan ba haka ba sai dai kaji anyi bada kai ba." Tsaki kawai yayi yana kwanciyarshi baice ma Moha komai ba sai ma yan rubutu da yayi da wayarshi yana turawa ya kashe wayar switchoff yayi addua ya kwanta kallonshi Moha yayi yana murmushi yace.

"Naga yanda wannan soyayya zata yuyu kullun sai zafin tura mata massage kana tsuke mata fuska haka kake son yarinya ta soka baka da sense kuwa Najib."

★★★

Karatunsu kawai suke sune basu fara shirin kwanciya ba sai wajen 2 na dare shima Zubaida tace gaskiya a kwanta dare yayi daukar wayarta tayi dan ta maidata switchoff nan taga message kamar ba zata karanta ba sai kuma ta bude dan karantawa. yarda wayar tayi bisa gado tana ja da baya baya kallonta Zubaida tayi tana daukar wayar ta fara karantawa kamar haka..


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp
*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_


*BOOK ONE*


*PAGE 21-30*


https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ


_"Gimbiyar mata karatun ya isa haka mana a ajiye a kwanta fatan kiyi addu'a kafin ki kwanta Luv daga masoyinki H A_

"HA."? Cewar Zubaida tana kallon Zulaihat cikin mamaki da alajabi ta sake cewa.." Sis waye HA."? Zufar fuskarta ta share tana cewa.."I don't know." Kwanciyarta tayi tana rufe jikinta duka dan ita bacci take ji bata son tayi late sam shiyasa bata ba maganar mahinmanci ba,ita dai tasan bata da case da wani HA yayi ya gama koma waye shi ita ba sonshi zatayi ba abunda ta sani kenan.

Girgiza kai Zubaida tayi gami da tsura mata ido tana mamaki waye wannan da yake son shigowa rayuwar Zulaihat waye shi?wannan wani irin sone haka? ya sunan wannan son? wani suna ya dace dashi? boyeyyen so? ko kuma matsoracin masoyi mai tsoron baiyana kanshi? furzar da iskan bakinta tayi tana mai yin addua ta tofesu ta kwanta.

*Washe gari*

Tun bayan da sukayi sallar asuba ita Zulaihat bata koma baccin safe ba dan tasan da matsala idan har ta biye ma Zubaida ta koma baccin safe tsab zasu makara gashi Dr Najib ne garesu early morning, dan haka tana gama azkar ta fada toilet wanka tayo ta zura doguwar rigar material ko mai bata tsaya shafawa ba ta fita ta fada kitchen. doya ta fere dan yamball taji tana bukatar ci bata tsaya bata lokaci ba ta hada kayan hadi da komai doyar na haduwa ta murzeta ta zuba kayan hadi sanann tayi shape din ball din, ta fasa kwai ta fara soyawa tana gamawa ta juye a cooler sanann ta dafa masu tea da yaji kayan hadi da kayan kamshi a parlo ta jerasu sannann ta wuce room dinsu a lokacin 7:30 gashi 9:00 suke da lecture din.

Turus tayi tana zabga ma Zubaida harara da ke kwance tana baccinta hankali kwace sai kace ba lecture gareta ba nine. gashi tasan daga gidansu zuwa makara sai sun kusa 30-40min kafin su isa idan suka tadda goslow ma sai ya kaisu 50-1hour ma,kallon time ta sake yi taga har 7:40 tayi take taji ranta yayi kololuwa wajen b'aci ,ita kullun a rayuwarta ba mai jamata yin late sai Zubaida ai tana sane da wanda zaiyi masu lecture kuma tasan halinshi ba sai an tsaya fada mata ba.

Tsaki tayi tana buga mata bugu mai zafi ma kuwa, sake daura mata wani tayi firgigi Zubaida ta tashi tana kwabe fuska tana cewa.."wayyo Allah Sis mai nayi maki."?tana mai kokarin sake komawa,fisge devut din Zulaihat tayi tana cewa..."haba Sis dan Allah har 8 ta kusa fah kuma kasan dai matsalar da muke samu kafin ma mu samu naped aiki ne balle kuma mu isa a school din. shi kanshi aiki ne kuma one hour tayi mana kadan shine zaki kama bacci haba mana Sis. "

Ta ida maganar tana share hawaye zaro ido waje Zubaida tayi da ta duba time sam ta manta da su na da nine. lecture din Dr Najib da bata koma baccin ba,dirkowa tayi bisa bed din tana nufi toilet ko ta kan Zulaihat bata sake bi ba...itama bata sake bin ta kanta ba gyara gadon tayi sannan ta zaune bisa stool ta shafa mai sai poder da lipstick sannan ta yafa gyalenta da dauki bag din ta ta fito parlo ta zaune. ta fara zuba yamball din sanann ta hada tea time ta sake kallo take taji sun kusa zama sorry dan har 8:05.

Tashi kawai tayi ta shiga kitchen ta dauko flake da foodflake ta zuba masu tea din da duk abunda ta girka masu as breakfast ta saka a basket sannan ta zauna zaman jiran Zubaida..fitowar Umma kenan ta gaisheta kallonta Umma tayi tana cewa.."Mamana har an shirya kenan."?daga kai kawai tayi tana wasa da zoben hannunta. murmushi kawai Umma tayi tana kallonta komai nata a raunane yake bata son shiga matsala tana kokarin ganin ta guje ma duk abunda zai sakata a damuwa a rayuwarta ,girgiza kai tayi tana cewa.

"Tashi yi tafiyarki idan bata fito ba,daga yau karda ki sake jiranta tunda ita bata san ciwon kanta." Girgiza kai tayi tana cewa."Aa Umma ai ta kusa fitowa shiryawa take."

Tsaki Umma tayi tana cewa.."mai ya hanata shiryawar kan lokaci kamar yanda ke kika shirya?na lura sam Zubaida bata damu da karatunta ba.dan haka daga yau karda ki kuskura na sake kamaki kina zaman jiranta. da kinga zaki makara kiyi tafiyarki kinji dai ko."?cikin fada Umma tayi maganar d'aga kanta kawai tayi tana mai sake kallon time 8:12 ,hawaye ne taji suna son zubo mata sharewa tayi da bayan hannun tana dai zaune zaman jiran Zubaida, da dankwali a hannu Zubaida ta fito tana cewa.

"Am so sorry Sis ,tashi mu tafi." Ajiyar zuciya ta sauke tana daukar basket din tace.."Umma mun tafi."A dawo lafiya Allah yayi maku albarka." Da Amin suka ansa suka tafi cikin sauri kamar zasu tashi sama tsabar sauri,cikin minti ukku suka iso bakin titi,suka fara kokarin tsada kake naped duk wanda suka tsada ba hanyarsu tabi ba....time ta duba taga 8:20 komawa gefen titi tayi ta zauna ta bugu uban tagumi tana share hawaye ,ita kuwa Zubaida tsaye take bakin titin tana ta aikin tsada neped amman har yanzun bata samu ba itama duba time tayi taga 8:30 saura 30min kenan ya shiga inalillahi ta kamayi a hankali. ta na tausayin kansu bama kamar Zulaihat da yasama ido a yanzun dan ta lura duk motsinta a kan idonshi ne.

★★★

Tsaki yayi yana kallon Moha yace mashi.. "Gaskiya nayi leting sosai da sosai kuma ban iya fita ban sha koda tea ba." Dagowa Moha yayi daga daure igiyar takalminshi yace.."sorry Najib ga tea can kasha to ka tafi kaga time yana ta tafiya." Tsaki ya kuma yi a karo na hudu yana fasa turarenshi masu kyau da tsada gyara sumar kanshi yayi ya daura rolex dinshi yana mai zura zobenshi a yatsarshi sannan ya fito daga bedroom din ,kitchen ya nufa ya hada tea mai kauri ya sha sanann ya dan leka yace ma Dr Moha.

"Broth am done ,sai ka shigo." ..."OK take care." Cikin motocin da suke fake a parking space ya je ya zabi motar da tayi mashi ya shiga. dan daman already duka motars din gidan duk safiyar duniya sai an wankesu dan bai cika maimata mota ba mudun zai shiga school to sai ya chanza ,da bissmillah yayi ma motar key ya dauki hanya cikin sauri dan tara saura minti talatin.

Tun daga nesa ya hangosu bakin titi,take yaji ranshi ya baci duba time ya sake yi yaga 8:35 tsaki yayi yana rage gudun motar tashi yana mamakin yanda yaran nan suke wasa da karatunsu .mai suka tsaya yi da har yanzun basu shiga school ba?tsaki ya kuma yi yana yin parking a gaban Zubaida zuge glass din yayi yana balla ma Zubaida wata uwar harara take tayi baya tana shan jinin jikinta,maida kallonshi yayi wajen Zulaihat da take zaune kasa tana kukan da ta saba.again tsaki ya kuma saki yana cewa.

"Ko ni zan fito na shigo daku."?girgiza kai Zubaida tayi tana tabo Zulaihat da bata san da zuwan na shi ba.tana can tana kuka ita daya tasan halin da take ciki,wurga mata harara ta yi cikin fushi take cewa.

" Dallah can malama ni ki kyaleni ki rabu dani naji da matsalar da ta damai ni na gaya maki."

Girgiza kai Dr yayi cike da mamaki ashe ta iya fada har haka?komai kyau yaka mata shi tsiwar da tayi ma Zubaida yanzun sai yaji daman ta dauwama a haka dan ba karamin kyau tayi mata ba.

Da hannu Zubaida ta nuna mata shi tana maiyin gaba ta barta da sauri ta tashi tana nufar motar dan zuciyarta har tafasa take tsabar takaici. tasan ta ta samaita yau kuwa Allah kadan yasan hukuncin da zai yanke mata,budewa tayi ta shiga da sallama bakinta cikin rawar murya,maida kanshi gefe yayi yana girgiza shi,sannan ya maido da kallonshi kanta yace.

"Wancan Basket din wa kika barma shi yaje ya dauko maki."? Girgiza kai tayi tana bude marfin motar ta fita ta dauko basket din tana bude baya ta dungurama Zubaida shi a cinya.ta koma ta zauna a mazauninta,tada motar yayi yana kallon Zubaida yace.

"Kema ta fara koya maki makara ko."?

Da sauri Zulaihat ta dago kai tana kallonshi sai ta maida kanta a cinyarta tana kuka a hankali a hankali. wai ta fara koya mata makara bayan duk makarar da suke Zubaida ce sanadi,itadai Zubaida kasa tayi da kanta batace komai ba cigaba da cewa yayi.." Wannann shine na karshe da zaki sake biye mata tana b'ata maki lokaci da kinga ta tsaya shirmanta ki tahowarki. ki kyaleta idan ba haka kema sai na hukuntaki fatan zaki kiyaye."?

A hankali tace.."in shaa Allah Sir." Daga nan basu sake magana ba sai wuta da yake ba mota daga gefen ido kuwa Zulaihat yake kallo tana bashi mamaki ,ita dai tayi kuka ko gajia da kukanma ba tayi,bata gudun ciwon kai sam.baice tayi shuru ba duk da yana jin radadin kukan nata har can cikin kasan zuciyarshi.daurewa kawai yake dan so yake yaga kafin 9:05 tayi yana cikin school cikin ikon Allah suka iso yaje wajen da yake parking yayi gami da kashe motar ,kallonta yayi yana mai bata ruwa yace.

"maza wanke fuskar nan tas."

Ansa tayi tana bude marfin ruwan ta wanke fuskar handkerchief ya mika mata nan ma ansa tayi ta goge fuskar,kallonta yayi yana cewa.."kukan ya isa haka maza tafi lecture hall." Daga mashi kai tayi nan ma tana daukar bag dinta ta fita gaba tayi ko ta gode batace ba,murmhshi yayi yana girgiza kai sannan shima ya fito sai da ya fara shiga office dinshi ya ajiye laptop dinshi da abunda ya dace sanann ya nufo lecture hall dan bada darasi.

Tunda ta shigo bata kalli inda Zubaida take ba dan ta kai ta karshe sosai.duk makarar da sukeyi ita ke janyo masu,amman saboda ya tsaneta ko ya fara binciker cikinsu wacece taja makarar amman saboda shi mugune bai iya hukunci ba ya daura laifi a kanta. kwafa tayi tana mai fiddo joting da pen ba ta wani dade da zama ba ya shigo as Usual fuskar nan a murtuke kamar wanda aka kashe ma dan fari,sauke ajiyar zuciya tayi tana mai gyara zamanta dan so take ta gujema duk wani laifi dan ta lura nemanta yake da sheri. (Lol Team Zulaihat Kun fara koya mata rashin ta ido fa,kuma dai kunsan Dr Najeeb baya daukar wurgi😂)

Cikin kamaiwarshi da natsuwarshi da kwarjininshi da kuma haiibarshi da miskillancinshi da ya kara mashi girma a idanun students din nashi ya fara yi masu bayanin abunda ya tarasu bakajin motsi komai sai gudun fan da ke tashi a cikin hall sai kuma kaukausar muryarshi da ta kaurayen hall din baki daya ,lecture ta dauko dadi dan babu wanda bai ganewa sabida ya iya koyawa iya koyawa. tafiya tayi tafiya dan har ya kusa kaiwa inda yake son ya kai ya fara jefo masu question,hall daukar tsuwar waya yayi, wayar Zulaihat ce ake kira da sauri ta datse ta tana mai data meeting, gami da rufe bakinta tana zaro idanu waje ,baki daya hall din sai da kowa yasha jinin jikinshi ana mamaki wani mai tsautsayin ne ya manta bai maida wayarshi silent ba ,bayan kuma kowane yasan role din Dr Najib bai son ana shigar mai lecture da waya na ring(general), jikin kowa lagwas yayi masu waigawa nayi dan gani wane ko wacece wannan, ita kuma ta dukar da kanta kasa tana jiran hukuncin da ya dace da ita wato get out,gyaran murya yayi take attention ya koma wajenshi kowa ya shiga taitayinshi dan karamin tsaki yayi ya cigaba da abunda yake questions yayi masu ana bashi ansa sanann yasa akayi mashi questions shima ya bada ansa,hada koman shi yayi yana kallon Captain ya kama gabanshi, captain ne ya hau step yace.

"Dr Najib yace wanda aka kira waya yana cikin lecture karda ya rigashi zuwa office din shi."

Rintse idonta tayi tana budewa da sukayi jajajir kwallah ne kwance cikin idon kiris suke jira su fara anbaliya,share kwallah tayi tana tashi ta yafe size bag dinta ta fito da sauri Zubaida ta biyo bayanta tana cewa.

"Sis ya akayi kika manta baki maida wayarki off ba."?

Kallon Zubaida tayi tana share hawaye tace.." Sis mantuwa ce kawai,nasa na saka off bari naje nidai na bani da nasan zan hadu da wannan mutumin a makarantar nan wallahi da ba zanyi karatun ba."

Rufe bakinta Zubaida tayi tana cewa.."laaa Sis ki daina cewa haka pls kije kiji mai zai ce maki kizo muci abinci kinsan bamuyi break ba and pls ki share hawayen nan mana."

Juyawa kawai tayi bata ce mata komai ba dan ita bata hawaye take ba. balle wata yunwa ta wanann azzalimin take tana tafiya tana kuka kamar wata karamar yarinya.bata damu da kallon da mutane keyi mata ba,ita kadai tasan yanda takeji bata son tana shiga case dinshi. amman kamar baki kullun cikin yi mashi laifi take a hankali ta bude baki cikin rawar murya tace.

"Wannan ne karshe in shaa Allah am tire na gaji na gaji sosai." Da hannu ta rufe bakinta tana mai share kwallan da suke zarya a saman fuskarta a bakin office dinshi ta tsaya tana kare ma kofar office din kallo,wannan shine zuwanta na biyu a wannan wajen kuma zai zama karshe da yarda Allah.

Matsawa tayi gefe tana mai da kanta kasa, zuciyarta da sauri da sauri take bugawa sakamakon kamshin turarenshi da ya kawo mata ziyara.duk da bata daga kanta ba amman jikinta ya bata yana kusa da ita,lumshe idonta tayi tana budewa a hankali gami da maida kallonta wajen office din,budewa taga yayi ya shiga sauke ajiyar Zuciyata tayi tana mai daura hannunta a door din office din tayi nocking,shuru baice komai ba sake wani nocking din tayi nan ma dai bai ce komai.sai da tayi sau ukku ana hudun ne yace.

"Come in."

Da sallama ta shigo cikin office din tana mai tsayawa gefe a hankali cikin natsuwar da ta zamai mata jiki tace.."Sir gani." Dan dagowa yayi ya kalleta sannan ya ajiye pen din hannunshi.nuna mata kujera yayi da hannu,bata tsaya bata lokaci ba taja ta zauna tana sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zoben hannunta.

Kureta yayi da ido yana mai kare mata kallo ya kusa 5min yana kallonta sannan ya sauke numfashi yana cewa.

"Zulaihat."

Dago kanta tayi tana kallonshi a hankali tace."Naam Sir." Gyaran zamanshi yayi ya cigaba da cewa."maiye matsalarki?maike damunki?gayaman matsalar Zulaihat kinji."?cikin kwantar da murya da sakin fuska yayi mata maganar,ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai tace.

"Bakomai Sir.babu matsalar komai." Shima girgiza

Please Login or Register in order to submit comment