Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daga kai kawai yayi ya wuce room dinshi daman hutawar yake bukata sosai, dan yarinyar ta chaza mashi kwakwalwa sosai.


*NIGERIA🥀*

_Kano_

"Sis." Ajiye handout din hannunta tayi tana kallon Zubaida ba tare da tace mata komai ba,sanin ba magana zatayi ba yasa Zubaida ta cigaba da maganarta dan ta saba da halinta daman.

"Daman shawara zan baki." Dan shuru tayi tana cigaba da cewa.. "A gaskiya tsoranki yayi yawa haka saurin kukanki yayi yawa ya kamata tun wuri ki chanza dan yana kawo maki chikas fah." Dan karamin tsaki Zulaihat tayi tana cewa.

"Kin cika matsala gaskiya kam Sis,tom ni ya zanyi haka Allah yayo ni bani son tsawa bani son fada keni gaba daya bani son tashin hankali Sam bani son fitina wlh."

Dariya Zubaida tayi tana cewa.."kice kina da babban aiki a gabanki kuwa."

"Kamar ya kenan."?cewar Zulaihat tana kallon Zubaida.. "Eh mana taya zaki iya zama da Dr Najib kina da wannan dan banzan tsoro wahala zaki sha a wajenshi kuwa."

Tsaki kawai tayi bata sake cewa komaii ba ,ta maida hankalinta wajen karatunta dan ta lura bata lokacinta kawai zatayi idan ta tsaye biyema shashancin Zubaida, itama Zubaida dariya kawai tayi ta cigaba da karatunta dan gobe test din Dr Moha zasuyi early 8 ma kuwa.

Washe gari tun 6am su Zulaihat suka shriya suka kama hanyar school dan bata son abunda zai ja mata matsala da Dr Najib duk da ba test din shi zasuyi ba Amman ai Dr Moha close friend din shi ne dole kuwa ta kiyaye duk wasu dokoki da ya shimfida mata mundun tana son kanta da arziki kuwa,zuwa 7 suna cikin school,venue suka nemo suka samu waje suka zauna kara dubawa sukayi tans nuna ma Zubaida idan bata gane ba, sai ga Dr Moha ya shigo shi da wasu malamai da zasu taya shi invigilation din test din,dukansu ya fidda waje ya saka su saka layi sai ya kira mace ta shiga sannan namiji two seat per intable haka ya gama arranging dinsu sannan aka rubuta question aka bada umirnin farawa tsit haka hall din ya dauka dan tsautsaran tsoro aka dauka ko motsi mai karfi baya tashi a hall din. kuma kowa nashi yake babu damar tambaya balle har ka tambaya wani abunda ka sani shi zaka rubuta.

Shigowarshi kenan hall din cikin tsuke fuska as usual haka Dr Najib yake murmushi bayi yake ba. balle dariya miskiline na karshe haka Allah ya halliceshi kuma bai daukar raini daga wajen kowa dan a aganinshi bai raina ba tom ba zai yarda a raina shi ba,saman step din ya hau yana hangen kowa da kuma motsin kowa kara nastuwa student din sukayi fiye da da.wasu ma fara dabarbarcewa sukayi sakamakon shigowar tashi.

Ita kuwa Zully tunda ta d'ago kanta sau d'aya ta kalleshi ta maida kanta kan papper din ta.ta cigaba da answering questions duk da gabanta sai faduwa yake gami da karmar jiki ,dan jikinta ya bata ita yake kallo dan ajiye pen din hannunta tayi tana d'ago kanta carab idunuwansu suka sarke da juna da sauri ta maida kanta kasa gami da rintse idonunta fatfatfat haka zuciyarta take bugawa sai kace Wanda tayi tseren gudu.

Cikin takun nan nashi na kasaita yake saukowa daga kan step din yana bin round by round yana kuma duba pappers Wanda yaji za ya iya haka har yazo seat din da Zubaida take dauka yayi ya karanta full name dinta yana mai duba question din da tayi answering ajiye mata yayi yana mai karawa gaba. yana duba na sauran yana zuwa seat Zulaihat ya dan tsaya ya dauki paper dinta ya duba kallonta yayi yana cewa.

"Be fast."

A hankali yayi maganar kuma ba wanda yaga motsawar bakinshi,rintse ido tayi tana budewa gami da daga mashi kai,dan maganar tashi har cikin jinin jiki haka ta shigeta gaba yayi yana cewa..

"gud girl."

Ficewa yayi daga hall din yana mai wurgama Dr Moha harara dan ya lura da irin kallon da yake mashi yana mashi murmushin raini,bayan fitarshi da five minute aka fara ansa sanann suma suka kama gabansu.


Cafeteria suka nufa bayan sun fito daga test din sai da tasha ruwa mai sanyi one bottle sanann ta lumshe idonta ta bude tana sauke ajiyar zuciya sau ukku a jere tana cema Zubaida..

"Sis bakiji yanda zuciyata take tsale ba har yanzun bata daina ba."

Dariya Zubaida tayi tana dan kurbe lumun chivita dake gabanta tace.."farar kura mai ya saka maki tsalen zuciya har haka."? Harararta tayi tana cewa.."ban sani ba je ki nemo farar kura ta baki ansa,ki fa fita idona in kulle naga kina son rainani bayan kuma na girmaiki."

Dariya kawai Zubaida tayi tana cewa.."to Umma ki yafenman karda kiyi man baki na koma tafa ko hirji." Tsaki tayi tana tashi tace.."kinji da shi tashi mu tafi saura 20min karda ki ki ja mana masifa kinsan dai Dr Najib ne yanzun 12-2 ko."?itama tashi tayi tana. Cewa.."Ina sane Mrs Najib taya zan manta."

Wani dogon tsaki Zulaihat tayi tana fisger back bag din ta. ta goya ta kama gabanta,dan zuciyarta har tafasa take idan Zubaida na hadata da Dr Najib ita ta rasa ya zatayi mata ,ta ma rasa da wa zata hadata sai Dr Najib mutumin da jininsu bai hadu ba ,ita ko shi kadai ya rage a duniya ba zata taba aurenshi ba,balle ma tasan har abada ba zai taba sonta ba shima,dan ita ba kallarshi bace ,sosai take cikin fushi dan har fuskarta ta nuna.tana shigowa class ta samu front seat ta zaune tana mai kara tamke fuska dan ta kasa control din fushinta ji take kamar ta kurma ihu ta rasa mai tayi ma Zubaida take mata haka. amman dole yau tayi maganinta ta kawo karshen rainin nan na Zubaida.dole ta tuna mata tafa girmaita ta bata shekara a duniya zata tuna mata shekara daya ba kwana daya bane,jin shiru da class din ya dauka yasa ta fahimce da shigowarshi d'ago kanta tayi sai idonta ya sauka cikin nashi dan tsaye yake ya kafeta da ido,dauke idonta tayi tana goge hawayen da suka fito mata a saman fuska,girgiza kai kawai yayi,ya fara abunda ya tarasu amman rabin hankalinshi yana wajenta dan ya lura da bata cikin happy kamar ranta a bace yake ,mai yasa ta kuka?tambayar da yake ma kanshi kenan.take yaji komai ya fice mashi a rai shima sai ya tsince kan shi a situations din da take ciki,dakyal ya samu ya danyi masu abunda ya sawaka ya sallamaisu yana fita ko office dinshi bai koma ba direct motarshi ya nufa yana shiga yayi mata key ya kama gabanshi.

Suma suna fitowa suka fara traking dan babu abun hawa babu bus kuma babu naped Zubaida na kallonta take ta zubga mata uwar harara harda karamin tsaki, itama sai ta kama kanta. idan ta harareta sai ta rama suna cikin haka sukaji mota ta tsaya gabansu da sauri taja baya tana jan tsaki dan sauran kadan a take mata kafafu.itama Zubaida ja da baya tayi cikin masifa tace.

"Maiye haka?waye wannan yake kokarin kashemu k..makalewa maganar tayi tana fiddo ido waje gami da rufe bakinta da hannu,ita kuwa Zulaihat k'ara ja da baya tayi tana neman rugawa da gudu, lura da hakan da Dr Najib yayi ya buga mata tsawa yana cewa.

"kika kuskura kika motsa daga inda kike sai ranki ya b'aci stupid."

Cak ta tsaye tana dafe zuciyarta dake kokari fitowa kasa tsabar firgici da tsoro.haka ma Zubaida da take taji cikinta na juyawa babu abunda take bukata sama da ta ganta toilet dan zawo zawo taji tanaji take,tsaki ya buga yana cewa..


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp

Share
Comment

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_


*BOOK ONE*

*Wannan page din naki ne Pharteemarh kankia much luv🥰*


*PAGE 13&20*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

"Zaku shigo mu tafi ko sai na fito na balballaku."? Cikin tsawa ya ida maganar da sauri Zulaihat ta toshe kunnenta har rige rigen bude motor suke dan shiga da sauri Zubaida ta bude baya ta riga Zulaihat shiga tana lumshe idonta gami da sauke ajiyar zuciya. dan ta tsorota sosai da tsawa da ya daka masu,ita kuwa Zulaihat tsaye tayi bakin motor tana share hawaye ,kallonta yayi ya girgiza kai yana sakin karamin tsaki zuge glass din yayi yana wulla mata harara cikin masifa da tsare fuska yace..." Mudun na sake magana akan ki shigo wallahi ranki sai ya b'aci zaki shigo ko kuwa."?

Kuka ta fashe dashi tana balle murfin motor ta shiga gaban da bata bukatar shigar ko kulle marfin batayi ba ta daura kanta bisa cinya tana kukanta,tsaki yayi yana kulle motor da kan shi gami da bissmillah yayi ma mota key suka tafi shuru kake jin motar ba abunda ke tashi sai sautin kukan Zulaihat.

Har cikin kasan zuciyarshi haka yake jin saukar kukan nata,ji yake kamar ana yankar mashi naman jikinshi tsabar yanda yake jin rad'adin kukan a cikin jini da bargo,da karfi ya rintse idonshi yana kaima sitirarin motor duka gami da danna giyar motor ji kake k'iiiiiiii haka sound din ya fita, salati Zulaihat tayi tana fadawa jikinshi gami da makalkaleshi tana rushewa da wani sabon kuka,zuciyarta da sauri sauri take bugawa fat fat haka sautin bugawar zuciyar yake fitowa,rintse idonshi yayi yana sauraren yanda zuciyar tata take bugawa sai da ya bata kamar 5min sannan ya tureta daga jikinshi yana balla mata kallon banza natsuwa tayi tana kama bakinta da ke rawar kuka,tsaki yaja mai tsawo yana kallon ta fuskar nan babu annurin murmushi a saman yace.

"Na sake jin koda tarinki sai nayi ball dake ,na kasheki da maruka tunda baki da hankali har yanzun idoit." Rintse idonta tayi da karfi tana budesu gami da goge hawayen da suke zuba bisa fuskarta, tabbas taji ciwon zagin da yayi mata ta rasa mai tayi mashi har haka ya tsaneta?bata da ansa sai kawai ta kalle gefe tana sauke ajiyar zuciya gami da goge hawaye a zahiri tayi shuru kamar yanda ya bukata din,amman zuciyarta taki tayi shuru sai tafasa take tana zubda hawaye sake yi ma motar key yayi suka dauki hanya.bai sake kallon idan take ba har sai da ya iso har kofar gidansu yayi parking sannan ya kalleta.

Itama kallonshi take da idanuwanta da sukayi luhuluhu sun sha kuka, sai ta kara mashi kyau ma,ita kuwa mamaki ne fal a zuciyarta taya hakan ta faru?ya akayi yasan gidansu?fuskarta kasa boye mamakinta tayi sai dai kash tasan ko giyar wake tasha bata isa tayi mashi wannan tambayar ba.ai wasa ma waje gareshi ita a rayuwarta batason taga abunda zai hadasu koda na second d'aya ne.maganar Zubaida ce ta dawo daga ita daga duniyar tunanin da ta tafi...da sauri tabi Zubaida da kallo da har ta kusa shiga gida,sauke ajiyar zuciya tayi tana mai kokarin bude motar itama ta shiga gida, sai dai taji motar a lock take. waigowa tayi tana kallonshi hawayen dai basu daina zubowa ba,so take ta samu ta fita ta shiga gida ko ta samu yin kukanta yanda take so ko zataji sausaucin a zuciyarta.

Girgiza kai yayi gami da kafe ta idonunshi masu sata gigicewa da shiga taitaiyinta a take kuwa,kallonta yake kamar ya samu TV haka yake kallonta kuma yana mamakin yanda take maida kuka abokin hirarta ace ita bata da aiki sai na kuka,ko gajiya batayi idan bata gajiya ai ta rage kodan lafiyarta dan ai ciwon kai ba kanwar uwa bane balle tace,lumshe idonshi yayi yana budewa yace.

"Sannu da aiki."

Dan shuru yayi yana dauko mata wani farin handkerchief sai kamshi mai dadi yake, ya bata babu wasa a fuskarshi yace mata.."maza goge wannan sakarcin banzan a fuskarki tun ban karyaki anan ba."ansa tayi tana goge hawayen sai da ta gogesu tas sannan ta mik'a mashi tana maida kanta kasa dan a takure take sosai da sosai, ansa yayi yana dan sakin tsaki yace.."kuka kuma ba zan hanaki yi ba, idan kin shiga gida ki cigaba daga inda kika tsaya ni nasan abunda zan maki gobe a school fita ki ban waje."

D'aga kai kawai tayi tana ficewa cikin motar a natse ta nufi hanyar gida yana kallonta har sai da yaga shigewarta ya sauke ajiyar zuciya gami da sakin murmushi yana cewa."Myluv ba dai rigima ba."Murmushi ya kuma saki da ya hango zallar shagwabe da rigima da tsoro a tare da ita yana son halinta sosai ba kamar tsoronta yana tsaye mai a rai kuma yana sakashi a cikin nishadi mudun zai tuna. haka ya juya dan komawa gida.

Koda ta shigo cikin gida bata bi ta kan Zubaida ba gaida Umma kawai tayi ta shigewarta room din su ajiye back bag din ta tayi tana shigewa toilet ta watsa ruwa tana fitowa ko mai bata tsaya shafawa ba saboda zafin da akeyi kaya ta samu mararsa nauyi da ta kura ta saka ta nemi hula ta sakama kanta ta fito parlo zama tayi tana kallon Umma cikin langwabar da kai gefe tace.

"Umma mai aka girka mana."?

kallonta Umma tayi cikin sonta da tausayinta tace." Favorite dinki yar gidan Umma." Murmushi ya baiyana a fuskarta ta na cewa.. "Thank you Ummana Allah ya kara nisan kwana." Tashi tayi taje kitchen dan zubo shinkafa da wake da man kulli da yaji,a can ta tadda Zubaida tana neman spoon ko kallonta batayi ba, again ta wuce ta fara abunda ya kawota a kitchen din,dariya Zubaida tayi tana cewa.

"Sis har ya tafi kenan."? Ko kallonta batayi ba balle ta bata ansa ida zuba man tayi tana bin gefenta ta wuce tana sakin karamin tsaki dan har yanzun haushin Zubaida take ji har cikin ranta,koda ta fito zama tayi ta fara cin abincinta tana kallo a hankali ,itama Zubaida fitowa tayi tana zama kusa da ita tana cewa.." Allah dai ya ida nufi Sis,amman wallahi hadin ya bata color sosai." Ta ida maganar tana kanne mata ido,hawaye ne suka fara zubowa tana kallon Umma cikin muryar kuka tace.

"Umma kice mata ta fita a harkata ba ruwanta dani tunda dai ni ba sa'arta bace." Tana turo baki gaba ta ida maganar gami da share hawaye, dakuwa Umma tayi ma Zubaida ta na cewa."karki kuma tsokanarta daga yau." Maida kallonta tayi wajen Zulaihat tayi tana cewa.."kukan mai kuma zakiyi mana?ba nayi Mata magana ba."?kukan ta ida rushewa da shi tana cewa. "Umma baki ji abunda take ceman ba shiyasa nidai kawai ta daina ba na so nidai kawai." Tashi tayi tana bar masu parlon hararar Zubaida Umma tayi tana cewa.

"Har sau nawa zan ce maki ki daina janta tunda bata so kuma ba yayarki bace."?

Itama Zubaida jikinta shanyi yayi tana maida kanta kasa cikin rashin jindadi tace.." Yi hakuri Umma in shaa Allah daga yau na daina ba zan kuma ba."

"Da ya fiye maki sai kisan yanda zakiyi ki bata hakuri kinsan dai yar'uwarki marainiya ce bata da kowa sai mu maimakon ki sata farinciki sai ki dunga b'ata mata rai karki sake daga yau ki dunga tuna bata da uwa kuma bata da uba ke ya dace ki zama kamar uwarta dan haka karda na sake ganin irin haka daga yau."

"In sha Allah Umma." Tashi tayi ta nufi room din nasu kwance ta taddata tana aikin kuka, hawa tayi bisa bed din tana kwanto da kanta bisa cinyarta ta fara lailashinta sai da ta tabbatar da ta dawo normal har tana mata murmushi suka ji wayarta tayi notice ma'ana sako ya shigo a cikin ta Zubaida ce ta dauko tana cewa.

"Sis message ne fa ya shigo." Tashi tayi ta nufi hanyar toilet tana cewa.."share Sis nasan Mtn ne zasu isheni da shashancinsu." Ida shiga tayi tana wanke fuskarta ta fito tana kallon Zubaida da ta kurema wayar ido kamar tana kallon abunda ya bata tsoro a cikin wayar zama tayi tana cewa.."what wrong."? Sauke numfashi tayi tana mika mata wayar dan tsaki tayi tana ansar wayar dan son ganin abunda ta gano a wayar har ya sata mamaki kurama dan short message din tayi da ido tana kara maimata karantawa.

_barkinki sarauniyar kyau sarauniyar zuciyarta uwar y'ay'ana ki barman zuciyata haka ki taimaka man ki daina kukan nan hakanan dan yana konaman zuciya da gangar jiki Myluv_

Ajiye wayar tayi tana kallon Zubaida cikin nuna damuwa tace."Sis na bani waye wannan kodai aljanine."!?

A tsorace ta tayi mata maganar har tana yarfa hannayenta tana son sake rushewa da kukab,hakan da tayi ne ya ba Zubaida dariya dan bata san ta daria ba sai da tayi mai isarta ta kalli Zulaihat tace.

"Ko daya ba aljani bane mutune dan uwanki kamar kowa kawai dai sonki ne yayi mashi kamun da idan kina cikin farinciki jikinshi zai bashi idan kuma kina cikin bacin rai da damuwa haka ma jikinshi yana bashi."

Numfashi mai zafi ta furzar tana lumshe ido dan har hankalinta ya kwanta da Zubaida tace ba aljani bane kallonta tayi tace.."to waye shi Sis."

"Nima ban sani ba Sis ,sai dai ya dace ya baiyana kan shi ko wane idan ba haka ba yana ji yana gani zakiyi mashi nisa ki zama mallakin wani *DA'IMAN ABADAN* kuwa. kinga yayi dakon so a banza."

Ita dai Zulaihat batace komai ba sai ma kallon Zubaida da tayi tana cewa.. "Sis baki yi mamakin yanda Dr Najib ya san gidanmu ba,ni abun ya tsorata ni sosai."

Murmushi kawai Zubaida tayi tana cewa."nima nayi mamaki amman ba sosai ba.dan na lura ba da wasa zai shigo ba,abunda dai ya tsorata ni da ya kusa kashemu dazun kinsan Allah Sis nasa har na mutu ma kukanki ya maidoni na ga ashe da sauran ranmu."

Tsaki tayi tana cewa.."banson Dr Najib sam ko ganinshi bansan yi Sis, shi da yaso kashemu dan nayi kuka shine har da zagina yace man idoit naji haushi sosai wallahi." Girgiza kai Zubaida tayi tana cewa.."karda ki sake furta Kalmar tsana ga kowa ba ma a wajen Dr Najib ba Sis,sannan ki zama jaruma a duk inda kike ki rage wanann kukan naki dan ba zai anfaneki da komai ba,balle ma kina tare da Dr Najib dole ki chanza idan ba haka ba kuwa Sis zaki sha doka kala kala a wajen shi kinsan dai halinshi ba sai na gaya maki ba."

Tsaki ta Kuma ja tana daukar handout dan maganar ma baki daya ta fice mata a rai,itama Zubaida bata sake cewa komai ba ta dauki ta ta handout din ta cigaba da karatun itama.

*URKAINE🥀*

Shuru Alhaji Nurandeen yayi yana sauraren Matar tashi har sai da ta kai karshe sannan ya maida numfashi yana cewa.."ikon Allah kenan Yar Albarka. So kenan shi So ai nufin Allah ne kuma ba ruwanshi da kyau ko nasaba ,inba haka ba har akwai yarinyar da Myson zaice yana so tace bata sonshi,idan kyau ake bukata yana dashi haka kuma dukiya ko ni kaina bansan iya adadin dukiya taba balle shi kanshi A-kad'ir da yake neman na kanshi, da gobe zamu koma Nigeria dan nagama duk abunda ya kawoni dole tafiyar ta fasu dan samama gudun jinina farincikin dan haka kiraman shi naji ita yarinyar yar wace kasace ."

Murmushi Ammie tayi tana shafa gefen fuskar mijin nata kissing dinshi tayi tana tsotsar lips dinshi kadan gami da dan cizawa kashe mashi ido daya tayi tana cewa.."angama Oga na." Murmushi yayi yana shafa lips dinshi gami da binta da ido har ta bace ma ganinshi ajiyar zuciya ya sauke yana kallon iyalin nashi cikin tsantsan sonsu da kaunarsu ,suna isowa bisa cinyarshi A-kadir ya daura kanshi yana cewa..

"Welcome back Dad." Murmushi Dad yayi yana shafa kanshi yace..."thank you Son,naji wani labari maidadi kuma marar dadi wacece wannan yarinyar mai kuma tazo yi a wannan kasar karka boye mana komai mu iyayenka ne ka gayamana gaskiyar wacece ita yanda komai zaizo mana da sauki."

Dan shuru yayi yana tunanin ta ina zai fara taya zai gaya masu zaman kanta take a kasar nan taya zai gaya masu karuwanci take a kasarnan,kuma idan sukace mashi Ina suka hadu yace mai?ajera ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Dad yace.

"Dad ba kowa bace face mai zaman kanta a wannan kasar ba karatu ya kawota ba haka ma ba business ne ya shigo da ita wannan kasar ba,tazo ne zaman kanta tana abunda ta gadama shine kawai abunda na sani a tare da ita dan ko sunanta ban sani ba shine gaskiyar maganar Dad."

Ya ida maganar yana tsurama Dad din nashi ido dan yana son yaga yanda ya dauki maganar tashi,abun mamaki murmushi ya gani dauke saman fuskar Dad din, yana shafa gefen fuskar A-kadir din sai da ya gama murmushinshi ya maida kallonshi wajen Ammie da itama murmushin take dan ita bata da matsala abunda luv din ta yake so tana sonshi bata da damuwa da wani karuwancinta damuwarta Dad dinshi. daman tunda taga yana murmushi sai taji sanyi a ranta.

Gyaran murya Dad yayi yana cewa."idan har kana sonta my son zanyi yanda zanyi naga ita wannan yarinyar ta zama mallakinka *DA'IMAN ABADAN* zanyi wanann kokarin ku kasance cikin farinciki har karshen rayuwa ,Abu daya zakayi ka bani address din ta zamuje nida Ammie dinka danyin magana da ita yarinyar in shaa Allah." Murmushi yayi yana boye fuskarshi a jikin Dad dinshi yana mai kara jin son iyayen nashi yana shigarshi ,girgiza kai Dad yayi yana cewa.

"Dan nema ka gama jin kunyar ka bani address mu tafi dan ance da zafi zafi akan buga karfe."

Tashi yayi yana shigewarshi room dinshi sai murmushi yake. da ya shiga room din sannan ya tura mashi address din through SMS,bayan Dad ya gama karanta Address din yayi dariya yana cema Ammie.

"Yar'Albarka yarinyar ma a estate dina take zaune." Murmushi Ammie tayi tana cewa.."masha Allah komai yazo da sauki kenan wace estate din a ciki."

"Landscape Alley,tashi muje dan nasan waye Abu-Kadir shiyasa na yarda da ya auri yarinyar. duk da ban ganta ba amman ta ban tausayi a rayuwar da ta zabama kanta sai kiga mun shiga aljana ta hanyarta, dan cireta daga wannan kazamar rayuwar Allah yaga zuciyarmu Allah ya daura mu a kanta ya kuma bamu ladar."

Amin." Ammie tace tana yafa gyalen abayarta suka fito drive har ya taso Dad ya dakatar da shi yace ya hutar dashi da kanshi zaiyi driving din ,da bissmillah ya tada motar sai landscape Alley dai dai parking lot din gidanta sukayi parking din motarsu.sannan suka fito Ammie ce ta fara nocking tana kara karema estate din kallo dan tayi mata kyau tasan da estate din bata taba shigo taba sai yau ta dalilin beauter.

Beauter na zaune a parlo taji ana danna door bell ,banza tayi ta share ta cigaba da cin tupa din ta tana kallon zeeword,dan batayi da kowa zaizo ba kuma ita k'aidarta ce bata kula bakon da bata san da zuwanshi ba,tsaki tayi jin anki daina dannan bell din take ranta ya bata A-Kadir ne ya sake dawowa a karo na ukku kenan?cikin fushi ta tashi ta nufi door din dan karta mashi rashin M bata damu da kayan da ke a jikinta ba dan mini sikert ne iyakar cinya sai amless dakyal ta rufe cibiyar ta sai gashinta da ta baza a baya da yaji gyara,face din ta babu ko digon makeup amman duk da haka face din glowing take lips din ta pitch sai shek'i suke cikin fushi da bacin rai take cewa..

"Heyyyyy wai waye ne zai sakaman ciwon kai."? Ta ida maganar cikin tsiwa tana bude kofar idonta sauka yayi saman fuskar Ammie. da take tsaye fuskarta dauke da murmushi, take nauyin Ammie da kunyarta suka dirarma Beauter.itama murmushin tayi ma Ammie duk da bata santa ba. amman taji tanajin kunyarta sosai ma,dan weaving tayi mata tana cewa.." Welcome Ma please come in." Murmushi Ammie tayi tana shigowa tace.."Thank you My Daughter."

Juya kalma My Daughter Beauter tayi sai taji jikinta yayi sanyi sosai.take yanayinta ya sauya dan har Ammie sai da ta lura da hakan,sai sharewa tayi tana cewa.."Daughters zan iya zama."daga mata kai Beauter kawai tayi itama tana samun waje ta zauna tana kallon Ammie. da take son tambayarta wacece ita?daga ina kuma mai tazo yi a gidanta har take kiranta da sunan yarta?murmushi Ammie tayi tana cewa.

"Bani daya bace nazo da mijina yana waje yana jiran a bashi izinin shigowa ko zaki dan saka koda afteradress ce."? Kasa

Please Login or Register in order to submit comment