Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tsaki tayi tana cewa.."matsalarku ce daga ke har shi,daman duk ke kika ja mana fad'a a wajen Umma maiyasa kika ansar masa kudi."?kwabe fuska Zubaida tayi tana turo baki gaba tace.. "Haba Sis kinfa san halin Dr Najib ba sai angaya maki ba,so kike naita yi mashi gardama har yayi man fad'a ko."? Harararta tayi tana cewa.." Sai mai idan yayi maki fad'a?nace dai ai ba kasheki zaiyi ba ko?sai ki ajiye kudin gefe in mun koma gida kiba Umma ta kira shi waya yazo ya anshi tsiyarshi ni wallahi ko kudin bani son gani ma."

Saka kudin tayi a jikka tana cewa.."yanda kikace ai haka za'ayi Sis."tabe baki tayi tana kallon Zubaida tace.."niko Sis nace wasu kalar bak'i zamu har haka da Umma tace ayi kunshi da kitso?nifa abun ya daure man kai tun dazun." Gyara zamanta Zubaida tayi tana cewa.."nima wallahi Sis abun akwai ban mamaki tunda bata tab'a yi mana haka ba.ko suwaye wannan bak'in? Dagani suna da fahinmanci a wajen Umma gaskiya. "

"Gaskiya kam har na kosa ayi mana ko mun koma mu k'ara gyara gidan mu samu wani abu mu girka masu." Cewar Zulaihat haka suka kama tautauna abunda ya dace su girka ma bak'in Umma...ba tare da bata lokaci ba aka fara yi masu gyaran kai sai kuma gyaran farce aka tsintsara masu kunshinsu mai kyau da tsari dan har yafi wanda ya goge kyau da tsaruwa ,yau ba wani gyaran jiki akayi masu ba dan duka yaushe akayi masu wata daya kenan,fuska dai wata a cikin ma'aikatan wajen ta matsa sai da aka gyara fuskar sai daukar ido take koda suka fito suka fahincin zasu samu matsalar abun hawa sai suka kira mai naped din da yake kaisu school suka gaya mashi inda suke yazo ya dauke su.

Koda suka kirashi sai da ya kira Dr Najib ya gaya mashi izinin daukosu ya bashi sannan ya kashe wayar yana kallon Moha yace.."Angama masu amman Zulaihat ta hana Zubaida kira sai dai suka kira mai naped." Dariya Dr Moha yayi yana girgiza kai yace.."Zulaihat rigimar duniya Najib zaka sha fama da rigimar Zulaihat gaskiya." Murmushi kawai yayi yana tura hannunshi cikin gyarairar sumar kanshi yace.. "Rabu da ita duk zan iya mata,kawai dai ta shigo hannu." Dariya Moha yayi yana cewa..da kamar yaushe zamuje zancen."? Agogonshi ya kalla yace.."after ish'i ai yayi ko."? D'aga kai yayi yana game dinshi dan Moha ba daga baya ba wajen game.

★★★

Koda suka koma gida sai da suka shiga room din Umma suka nuna mata kumshin da gyaran gashin da akayi masu tasa albarka tace sai su shiga kitchen su dafama bak'in abinci sai da suka yi sallah sannan suka nufi kitchen...koda suka shiga sai da sukayi shawarar abunda zasu girka masu da yake suna da garin masa na kamfanin *MASALINA* daukoshi kawai sukayi suka yi hadin masar sannan suka fara nadin samosa da spring roll sosai suka hada masu kayan lakumashe da na motsa baki suka hada masu juices da milkshake, sallar mangariba sukayi sannan suka fito suka fara gyara tsakar gida Zulaihat tayu shara yi tas .Zubaida tayi mopping suka gyara parlon tas suka kunna tureren wuta bayan sun kunne tsintsiyar kamshi sun kuma fashe ko ina da room freshener.

Room din su suka koma suka fara shirin wanka Zubaida ta fara shiga sannan Zulaihat kafin ta fito Umma ta shigo ta kawo masu wani laces ash mai ratsin black sai wani turare mai saukin kudi amman yanada dadin kamshi ta ajiye masu tace suyi kwaliya mai kyau da kallo suka bi Umma fuskarsu ciki tab da mamakin Umma suyi kwaliya? Wannan wasu irin bak'ine haka masu kayan mamaki tunda suka dawo Umma take shirya ma zuwansu kallon juna sukayi kanan suka d'aga kayan sabbi ne kuma style din yayi masu kyau sosai zura doguwar rigar sukayi suka zauna sai da suka yi sallar ish'i sannan suka fara shiryawa poder suka shafa dan har da jan baki suka shafa kuma yayi masu kyau sosai ya kara fiddo masu da haskensu da kuma kwarjininsu.

Cikin natsuwa suka k'arasa shiryawa suka wuce room din Umma da kallo ta bisu fuskarta shimfide da murmushi tace.."masha Allah yan biyu kyautar Allah kunyi kyau sosai Allah yayi ma rayuwarku albarka." A tare sukayi dariya sai Zulaihat ta cinno baki gaba tana cewa.."Ayya Umma ki daina had'ani da ita kinsan fa na girmaita." Dariya Umma tayi tana cewa."Mamana uwar yanson girma duk da kin girmaita ai baki fita girman jiki ba sai dai tsawo ko.?" Dire kafafu ta fara tana cewa.."nidai nidai Umma naji duk da haka dai." Dukansu dariya suka saka Umma na cewa.."shikenan na daina Mamana uwata ta kaina." Dariya tayi tana rufe fuskarta Zubaida ce tace.."wai ni Umma wasu irin bak'ine zakiyi haka har yanzun basu zo ba ko dai kwana zasuyi."?girgiza kai Umma tayi tana cewa.."ko d'aya ba kwana zasuyi ba yanzun haka suna kan hanya ina jin sun kusa k'arasowa ma."

"Amman Umma yan nan cikin garin kano ne kenan."? Cewar Zulaihat nan ma d'aga mata kai Umma tayi tana cewa.." Kwarai kuwa yan asalin nan kano ne amman iyayensu suna zaune a abuja aiki ya kaisu su kuma suna zaune anan kano suma aiki ya kawo su." Har ta bude baki zatayi magana wayar Umma ta fara ringing dole tayi shuru tana had'iye maganarta.

Daukar wayar Umma tayi tana murmushi tana kallonsu sannan tace.."ok shikenan bari azo a shigo daku." Murmushi tayi bayan ta saurari abunda akace daga d'ayan bangaren ta ajiye wayar tana kallon Zubaida tace.."maza tashi kije ki shigo dasu suna kofar gida." Cikin jindadi Zubaida ta tashi ta daukar hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofar gida cikin doki tana son ganin su waye wannan bak'in masu daraja a wajen Umma.

Ita kuwa Zulaihat taso ace ita Umma ta aika dan shigowa dasu dan taga su waye itama dai kam,amman ai zasu shigo zata gansu tasan dai ko su waye to suna da mahinmanci a wajen Ummarsu kam..koda Zubaida ta fita bata lura da motar su Dr ba da yake sun kashe motar kuma basu kunna fitilar motar ba gefe da gefenta ta waiga bataga kowa ba har zata juya suka danna mata horn sai anan ta maida hankalinta a wajen...Sam bata ganesu ba da yake kullun cikin chanza mota suke kamar wasu gwannati har bakin motar taje tana dan yin nocking a hankali gami da sallama lumshe Dr Moha yayi yana jin sonta na fisgarshi kumshinta yayi mashi kyau sosai ,zuge glass din yayi yana cewa.."sannunki dai yan mata." Wani ja da baya tayi tana kallonsu sai kuma tayi murmushi tana cewa.."Laaa Sir wai da kune bak'in da Umma zatayi."? Murmushi yayi yana bude motar ya fito yace.."Kwarai kuwa mune gashi har mun iso kodai mu koma ba'a murna da ganinmu.?"Cikin wasa yayi mata tambayar girgiza kai tayi tana cewa.." Wai rufamana asiri ku shigo sannunku da zuwa."

Murmushi sukayi sannan sukayi gaba tana baya har suka shiga,har cikin parlo ta saukesu tana sake yi masu sannu da zuwa sannan ta shiga cikin bedroom din Umma zaune ta tadda Zulaihat sai labari suke da Umma samun waje tayi ta zauna tana cewa.."Umma ashe su Dr ne bak'in naki.?" Murmushi Umma tayi tace.."ba zama zakiyi tambaya ba tunda idonki ya gane maki ke Mamana tashi kuje ku kai masu abun motsa baki."

Kalllon Zubaida tayi ta kalli Umma tace.."Umma wasu su Dr din.!?"yanda tayi tambayar cike da al'ajabi da mamaki girgiza kai Umma tayi tana cewa.. "Zaku tashi kuje kun bar mutane zaune ko ni naje da kai na.?" Tashi sukayi suna nufar parlon da sallama suka fito ji tayi zuciyarta tana tsalle kamar zata fado kasa tsabar takaici mai hakan ke nufi? Wani zuminci suke sun kullawa mai karfi haka?dakyal ta ida isowa cikin parlon tana mai kallon Dr Moha tace.." Sir sannuku da zuwa barkanku da dare."

Murmushi Dr Moha yayi yana cewa.." Yauwa Zulaihat barkanmu dai ya gida ya kuma dare."murmushi itama ta sakar mashi tana cewa.."lafiya lau Alhamdulillah."gaba tayi tana fita daga parlon ta wuce kitchen tadda Zubaida tayi tana jera abunda suka girka a babban tire jingina tayi jikin bango tana cewa.

"Sis nifa duk kaina ya daure ban gane komai ba ina cikin duhu sosai daman sune zasuzo Umma ta sakamu kitso,kunshi,har da sabbin kaya.?"Itama Zubaida furzar da numfashi tayi tana cewa.." Sis nima nan a cikin duhun nike nayi nayi na gano ma'anar wannan hidimar na kasa kinga dauki muje mu kai masu karda Umma tayi fad'a kuma."

Gyade kai tayi tana daukar tire din abincin ita kuma Zubaida ta dauko su jug da cup da duk abunda suka tanada suka kai masu,suna ajiyewa Zulaihat ta tashi ta shigewarta room din Umma tana cinno baki gaba,kallonta Umma tayi tana cewa.

"Mamana ba dai kanwarki ba kika baro da aikin zuba masu abincin." Tabe fuska tayi tana cewa."Umma ai nasa munyi mai wuyar tunda mun girka kuma mun kai masu ko.?" Dakuwa Umma tayi mata tana cewa.."gidanku Mamana naci gidanku yau ga rashin tunani da wayau ace har kanwarki ta fiki iya karrama bako?zaki tashi kije kiyi abunda ya dace ko sai na sab'a maki.?"

Tashi tayi tana cewa..."yi hakuri Umma ba zan sake ba." Tsaki Umma tayi tana cewa.."da dai ya fiye maki." Fitowa tayi fuska a turnuk'e babu fara'a sai tura baki take gaba haka ta iso ta tsuguna tana wurgama Zubaida harara tace."mai kike zuba masu.?"Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."brown rice din ko Sis." Tabe baki tayi tana daukar plate ta zuba ta saka salad da duk abunda ake zubawa ta tura a gaban Dr Najib tana tsiyaya carrot juice din ta mik'a mashi.

Tunda ta dawo yake kallonta duk wani movement nata akan idonshi take yinshi shi dariya take ba shi sai wani ifizi take dan anzo gidansu..a cikin zuciyarshi yayi tsaki yana cewa.."yarinya kenan duk kiyi ki gama na kusa yin maganin wannan sabuwar rashin kunyar da kike tak'ama da ita." Murmushi kawai yayi idan ya tuna saura tik'i kadan ta shigo hannunshi duk da yana sonta amman hakan ba zai hana ya koya mata hankali ba ,dan ya lura wata sabuwar balaga take rudarta.

Kafeta da ido yayi yana aika mata da wani kallo wanda yasa take ta shiga taitayinta tana sauke kanta k'asa wani sabon tsoronshi ya shigeta take har sai da fuskarta da kwayar idonta suka nuna haka..saboda wasu kwallah suka taro sukayi kwance a saman kwayar idon nata dakyal ta samu ta hanasu zubowa,kin ansa yayi ya kuma ki daina kallonta k'asa tayi da kanta a hankali tace.."Sir ga juice. " dan karamin tsaki yaja wanda sai da ya maido da hankalin Moha wajenshi da yake aunama cikin shi daddar brown rice din da ta gaji da dadi da kuma tsokokin naman kazar turawa,had'a ido sukayi da shi yana girgiza mashi kai itama Zubaida sai da ta sake shiga taitayinta dan tsam ta tashi zata bar wajen Moha ya dakatar da ita yana cewa.." Yi zamanki ki karasa aikin lada." Murmushi tayi tana koma wa ta zauna.

A hankali ta sake cewa cikin muryar kuka.."Sir." D'agowa yayi again yana cewa.." Ai nasa shima ai wullo man zakiyi." K'asa tayi da kanta tana cewa.."Sorry Sir." Nan ma baice komai ba sai ya dauki juice din ya dan kurba yayi mashi dadi kam sosai da sosai sai da yasha kusan half sannan ya dauki plate din ya fara ci ba laifi yaci da yawa kam.kuma duk abunda suka girka sai da suka ci dai dai misali...bayan sun gama Umma ta fito kamar jira Umma na fitowa suka tashi suka bar masu parlon sai da suka gaisa sosai suka kara magana da Umma sannan ta tashi taje ta kira su tace su koma zasuyi magana mai mahinmanci da su Dr har Umma ta juya ta dawo tana ce ma Zulaihat.. "Mamana dan Allah idan kinje ki samu bulala ki zanesu karshen fushi da kumbura fuska kenan."

Cikin b'acin rai Umma tayi maganar tana fitowa ta bar masu dakin da kallo suka bita Zubaida ce tace.."Sis gaskiya koni banji dadin abunda kikayi ma Dr ba ,haba ai ko ba komai kin daga mashi tunda gidanku yazo ko.?" Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa."bakiji yanda nike ji bane shiyasa ko kadan ban san ganin fuskarshi kuma wata magana ce zamuyi dasu kuma bayan gaisuwar da mukayi.?"

"Duk da baki son ganin fuskarshi ki saki fuskarki ko dan Dr Moha da Umma mana da kuma ni kaina and maganar da zamuyi nima ban sani ba idan munje munji koma maiye ne ko.?"

Daga mata kai tayi tana yin gaba itama tana bin bayan ta da sallama suka shiga parlon.wannan karan fuskarta a sake take ba kamar dazun ba sake gaidasu sukayi a karo na biyu sai sukayi shurun dan basu san mai zasu ce masu ba,bama kamar Dr Najib da komai nashi ya kwance mashi baisan mai zaice ba dan wannan shine karo na farko a rayuwarshi da ya fara zuwa wajen mace,bai san mai zaice ba bai san ya akeyi ba kallon Moha yayi yana langwabe kai murmushi Moha yayi dan yasan waye Najib bai taba soyayya ba sai akan Zulaihat in fact common charting baiyi da mace dan duk basu gabanshi gwara shi yana dan taba soyayya a online ba laifi dan gyaran murya yayi ya fara cewa.

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*


*PAGE 81-90*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ


"Zulaihatu. " maida kallonshi wajen Zubaida yayi yace."Zubaida." Yanda ya kira sunayen nasu babu wasa a ciki yasa suka natsu suna ansawa a tare,murmushi yayi yana gyara zamanshi yanda zai ga reaction din kowa ce a cikin su idan ya fadi abunda ke cikin zuciyarshi...cigaba da cewa yayi.."ina son ku natsu ka bani aron hankalinku dan magana zani mai mahinmanci a garemu daga mu har ku." Numfashin bakin shi ya furzar yana daukar ruwa ya dan surb'a kadan ya ajiye ya cigaba da cewa."bama kamar ke Zulaihat inason ki natsu ki saurareni da kyau akan duk abunda zan gaya maki fatan kin gane.?"d'aga mashi kai tayi tana wasa da yatsun hannunta,ba abunda gabanta yake sai faduwa danma tana inallilahi wannan wace irin magana ce haka? Wanda take da mahinmanci irin haka? Kamar saukar aradu haka taji dirar maganar Dr Moha a cikin dodon kunnanta yana cewa.

"Daman munzo ne mu gaya maku muna sonku,ma'ana muna son aurenku muyi rayuwa ta *DA'IMAN ABADAN* ,Najib yana son ki Zulaihat ni kuma Allah ya daura man son Zubaida sonku muke ba da wasa ba,kuma ba zuwa makayi ba mu tsaya muta b'ata ma juna lokaci shiyasa kafin muzo anan sai da Umma tasan komai ta kuma yarje mamu tace ta bamu ku sai dai muzo mu gaya maku dan mu sasanta mu fahimcin juna."

Dafe kanta tayi da hannayenta duka biyun tana jin dumm waje bangaren kan, dan wani irin juya mata parlon yake komai ya rikice mata bata ganin shi da kyau sai dai double komai ya koma mata upsize down.bata fahimtar komai bata gane mai sukeyi, dakyal ta fisgo kuka tana cewa.."Impossible." Sai ta tashi ta fice daga parlon gaba d'aya tana koma wa room dinsu bisa gado ta fad'a tana mai ida rushewa da kuka tana cewa..."har abada in shaa Allah ba zamu taba had'a inuwa d'aya da kai ba,ban sonka na tsaneka nasan kaima ba sona kake ba so kake ka aureni ka ida kasheni da bak'in halinka."

Ko motsawa baiyi ba duk abunda ta gama da impossible din da tace ta bar masu parlon duk bai nuna yasan tanayi ba. ko da kuwa fuskarshi ta nuna bai bari ba,duk da har can k'asan zuciyarshi yaji zafin abunda yarinyar tayi mashi,mai take nufi?impossible! Impossible!mean ba zata aureshi ba kenan? Haka take nufi Najib zuciyarshi ta bashi ansa ,tabbas da sake dan sanda yaga gawar soja.

Cikin sanyi jiki da nuna rashin jindadin abunda tayi Moha ya kalli Zubaida,itama k'asa tayi da kanta tana jin kamar ta nitse wajen dan kunya abu biyu ya taro ya hau kanta ga wannan magana ta Dr Moha da yayi ta kamar saukar aradu babu zato babu tsanmani ga kuma nuna rashin amicewa da Zulaihat tayi a take tun kan aje ko ina. rasa bakin magana tayi sai sunna kai da take yi kamar wanda ta saci hatsin ma'auna,tashi Dr Moha yayi yana kallonta yace.

"Mundai gaya maku abunda ke rainmu a kan ku ina fata a anshemu hannu biyu ayi maraba damu." Murmushi kawai tayi tana wasa da yatsunta dan ta kasa cewa komai shima murmushi yayi yana cewa.."alright I understand zamu baku time dan kuyi shawara and gobe zamu tafi abuja danyi hutun season."

"Allah ya kiyaye ya kaiku lafiya." Har cikin rainshi Dr Moha yaji dadin addu'arta ,shima Dr Najib kallonta yayi yana cewa.."Amin Zubaida and idan kin shiga room ki cema Zulaihat ta kula da kanta ban yarda ta kula kowa ba sannan bance taje ko ina ba har sai da izinin Umma." Cikin mamaki take kallonshi da saurarenshi shida ba'a ce ana sonshi ba har ya fara kwafa doka,gaskiya karfin halinshi yana bata mamaki kam sosai.da to ta bishi sai da ta rakasu a bakin motar su bayan sun yi ma Umma sallama suna tada motar tana koma wa gida tana shiga ta nufi room dinsu bata ciki sai kawai ta zarce room din Umma tasan can ta koma.

Tana shiga ta samu waje ta zauna gefen Zulaihat da take kuka tana cewa.."Umma dan Allah ki rufaman asiri ki sake man wani zab'in ,dan Allah Umma ki duba Allah ki dubi girman Allah karda ki daura man aure da Dr Najib wallahi kashe ni zai yi ba sona yake ba mugune." Kuka take sosai tana durkushe gaban Umma tana magiya cikin takaicinci da kayan hushinta Umma ta kalleta tace."kin tai bata idan ya aure ki kasheki zaiyi.?"Da sauri ta d'aga kanta tana cewa.."eh Allah Umma dan nasan waye Najib ba imani ne da shi ba,sannan kowa yasan a faculty ba mutunci gareshi ba idan karya nayi mashi ga Sis nan ki tambayeta."

Girgiza kai Umma tayi tana cewa.."ba tambayar da zanyi ma Zubaida dan naga ansar da nike bukata a fuskarta."dan gyara zama Umma tayi tana cewa."Mamana." D'agowa tayi fuskarta cike tab da kwallah sai jera ajiyar zuciya take Umma bata damu da rashin ansawarta ba ta cigaba da cewa.."kinsan dai ina son ki ko?kinsan har abada ba zan taba zab'a maki abunda zai cutar dake ba ko?kinsan akan ki ba abunda ba zan iya sadaukarwar ba ko?in har ke zaki kasance cikin farinciki ba tare da kinyi kukan maraici ba." Dan shuru Umma tayi tana jawota jikinta ta kwantar da ita bisa cinyarta ta cigaba da cewa.

"Alkwari Na daukarma Yaya Aminu akan ki Mamana nayi alkwarin baki kulawa da ilimi mai inganci sannan kuma zai aurar da ake ga mutun nagartaice mai ilimin addini da na zamani wanda ya san mutuncinki yake kuma kaunarki da kishinki wanda zai saki farinciki na har *ABADAN* ya rayuwa dake da dadi ba dadi yaji ba zai iya yin nisa dake ba koda na second goma ne,ya kasance kullun kina zaune a zuciyarshi ba dare ba rana wanda zaji mutuwa ce kawai zata rabaku dan itama dan dole ce."

Hawaye Umma ta share dan duk randa ta tuna da dan uwanta mai sonta da kaunarta sai ta zubda kwalla,ta cigaba da cewa.." Duk wannan kulawar da jindadin da na lissafo ba wani namiji da zai yi maki koda rabinta ne sai Najibullahi, Najibullahi yaron kirki ne yana da kunya da tarbiya ga ilimi ga kuma kishi,yana son ki sosai kuma yana kishinki akanki ba abunda ba zai aikata ko kin manta akan sonki yayi dambe a gaban students din shi,kishin abunda Alkhamis yayi maki yasa ya tsaya tsayin daka sai da ya kwashi kashinshi a hannu.yayi wannan duk dan yana sonki da bai son ki da bai yi ba."

Cikin muryar kuka tace.."Amman Umma kullun cikin yaman fad'a yake baya man kirki ko kadan dan Allah Umma ki taimaka."girgiza kai Umma tayi tana cewa.."Naji Mamana amman abunda nike so dake ki bashi lokaci idan har bai kwanta maki a rai ba sai asan yanda za'ayi." Murmushi tayi tana kara lefewa jikin Umma tana share hawaye da bayan hannunta, ita san ba lokaci ba komai zata bashi ba zata taba sonshi ba har abada ,ba zasu taba zama inuwa d'aya ba dan jininsu ma bai hadu ba sam,Murmushi ta sake saki dan tasan yanda Umma take sonta ba zata taba yi mata auren dole ba...itama Zubaida Umma tambayeta ya tana son Dr Moha ko itama bata sonshi,sunkuyar da kanta k'asa tayi tana cewa.."A'a Umma ina sonshi." Murmushi Umma tayi tana cewa.."Alhamdulillah Allah ya albarkaci rayuwarku." Amin suka ansa sai da suka kara yin fira a wajen Umma sannan suka wuce room dinsu.

★★★

Koda suka koma gida basu wani tsaya neman abinci ba ruwa suka watsa da yake garin ana zafi sosai sannan suka dawo parlo dan fara marking din exams,Moha fahimta yayi idan har baiyi ma Najib maganar Zulaihat ba to miskillancinshi ba zai barshi shi yayi ba.duk da yana jin zafi a zuciyarshi, yasan waye Najib wajen yar'banzar zuciya wanda ya rasa a ina yayi gadonta dan gyaran murya yayi yana cewa.."Najib ya kamata fa ka sake tako,dan ga dukan alamu Madam fah zata bamu matsala sosai." Murmushin gefen baki yayi yana duba exams dinta yace.."ni nagama da wannan babin ai,matsalar daya ce ace bata san matsayinta a wajena ba. tunda ta sani ai shikenan ta yarda ayi ta dadin rai ko akashin haka duk ya rage damuwarta ba tawa ba."

Tsaki Moha yayi yana cewa.."wallahi kaji matsalarka sai ana gaya maka gaskiya ka kak'i fahimta nace maka karka biye ma dokin zuciya azo ayi ba da kai ba,amman na rasa maiyasa kake haka ita yanzun taitali da lailashi take bukata a wajenka har ta soka."

Cikin tsawa yace.."ba zan lailasheta ba idan har sai na lailasheta zata aureni sai dai ta mutu,kuma wallahi nine nan mijinta bata isa ta auri wani d'a namiji ba ina raye a doran k'asa karyarta tasha banban da ta soni da karta soni nidai abu daya na sani shine sai ta *AURENI DOLE* kuma muyi rayuwa ta aure har *DA'IMAN ABADAN*."

Dafa shi Moha yayi yana saukowa daga dokin fushin da ya hau yasan waye Najib dole ya dunga sausauta harshe wajen yi mashi magana karda maganar shi ta kara

Please Login or Register in order to submit comment