Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauran lokaci hakan yayi masu dadi suka samu front seat suka zauna suka fara karatunsu Zulaihat na nuna ma Zubaida inda bata gane ba suna cikin karatun suka ji ance.

"Aminci Allah ya tabbata a gareki Gimbiyata keda twin dinki." Kusan a tare suka waiga suna sauke idonsu a kanshi,duk da basu san sunanshi ba. amman ba zasu manta fuskar ba kuwa,tsuke fuska Zulaihat tayi tana maida kanta bisa book din gabanta dan ita sosai ya tsoratata ta tsani rashin tunani da hankali kamar yazo wajen wanda basu sallah. da zaizo masu babu ko sallama,Zubaida ce ta danyi murmushi tana cewa.

"Wa'alaikumus sallam." Dan dafe kanshi yayi yana cewa.."afuwan yanmata nazo banyi sallama ba a gafarceni kaina a kasa Sarauniya Assalama Alaikum."again Murmushi Zubaida tayi mashi tana cewa.."wa'laikumus sallam."itama Zulaihat sai da ta ansa sallamar amman a hankali samu waje yayi gefenta ya zauna yana daukar book din gabanta,dagowa tayi tana kallon shi cikin tsuke fuska tace.

"Maiye haka bawan Allah?bansan haka nidai ka bani littafina." Yanda tayi maganar cikin nuna ranta ya b'aci hakan ba karamin kyau yayi mata ba,shima kwabe fuska yayi yana cewa.."ni kuma inason haka Myluv." Mika mashi hannu tayi cikin tsare fuska daman hannun yasha kunshi sai daukar ido yake masha Allah...kafe hannun da kallo yayi yana sauke numfashi sannan yace.."ni ba sunana bawan Allah ba Sunana Alkhamis." Tabe baki tayi tana cewa.."wannan bai damaini ba nidai kawai kaban littafina shine abunda na sani."

Dariya ya fashe da ita yana cewa.."aikuwa kenan ba zaki taba ansar book dinki ba,tunda sunan mijinki bai damaiki ba." Batasan sanda ta wulla mashi harara ba,wai miji ita hauka take ta aureshi ai sam baiyi mata ba mutumin da ya cika tsokana babu kamun Kai kamar dai ba mutum ba,dan girgiza kai tayi tana jin d'aci har kasan zuciyarta.yana bata mata lokaci ga akwai inda take bukatar dubawa kafin mutane su fara taruwa a fara noise gashi kuma yana neman rushe mata budget sai ta tashi tsaye tana cewa.

"Kaga Malan ni ba wasa nike maka ba,bansan haka akan mai zaka daukeman abun karatu kuma nace ka bani ka tsaya yi man wasa haba mana." Dan karamin bakinta ya tsurama ido.ji yake kamar ya turmusheta ya shanye bakin tas yaga bakin tsiwar kauda abun yayi a ranshi yana cewa.. "Babe kina son na baki littafinki ko."? Gani tayi rainin wayau da hankali ya shigo sai ta mai da kallonta wajen Zubaida tana cewa.." Sis kina dai gani ko?kice mashi ya bani book dina ki nuna mashi gaskya bansan irin wannan dan bakomai ake man ba."

Zubaida tasan halin Zulaihat tasan ita batasan wasa shiyasa ba'a cika yinshi da ita ba.koda a cikin family tana da hakuri kuma tana da saurin kullewa ,shi kuma Alkhamis ta lura yana da son raha da wasa duk da wanann shine kallo na biyu da tayi mashi tunda randa ya daukosu daga fabjamb sai kuma yau ,amman ta lura da yana da son ayi raha sosai halinshi yayi mata dan ita batasan mutun mai fadin rai da fisfisgewa kamar wani sarki murmushi tayi tana cewa

"Alkhamis please ka bata mana tunda har ta gaya maka bataso." Cikin dariya yace ma Zubaida.."Aa Sis rabu da ita da gaske nike ba zan bata ba har sai ta fadi sunana kamar yanda kema kika fada."...."Aa please ka bata dai kaga ba dadi anayi ma mutun abunda baiso.tunda tace bata so ba sai ka bari ba."?..."Nidai gaskiya sis kisa ido kawai kiyi kallo kiga ya wasan zai kaya dan nidai ba zan bayar ba sai anfadi sunana."...ganin da gaske yake ba zai bada yasa Zubaida ta mai da kallonta wajen Zulaihat da ta cika tayi fam jira kawai take a tabata ta fashe,murmushi tayi tana kallon Alkhamis ta girgiza mashi kai tana nuna mashi da ya bata.amman sai nuna baifa badawa ba tare da tayi abunda yace ba,dole tasa Zubaida cewa.

"Sis kice mana ya baki komai ya wuce." Tashi tayi tana share hawayen fuskarta tace.."bazance ba Sis shin ana dole ne? Kuma dole ya bani littafina tunda bashi bane ya sayarman shi ba.". Mai da kallonta wajen Alkhamis tayi tana cewa.."Bawan Allah tun cikin mutuncinka da arzikinka ka bani littafina karda nayi maka abunda ba zakaji dadi ba.kuma kaga kaine ka jani kawai ka bani littafina. "

Nifa ba zan bada Queen har sai kince Alkhamis Myluv kina cewa haka shikenan littafinki yazo hannunki partner. " ya ida maganar yana nuna mata zuciyarshi gami da yin sing din luv,rintse idonta tayi cikin jin haushi da takaicin abunda yayi mata yanzun tace.."tunda dai kaki ka bada ta arziki to zan ansheshi koda tsiya kuwa." Gira ya d'aga mata yana cewa.. "Bissmillah idan zakiyi."

"Haka kace ko."?..." Kwarai kuwa haka nace Queen." Tsalle tayi tana kaima littafi wauta yayi sama dashi yana dariya ita kuwa ranta yayi nisa a b'aci .tasama ranta da tsiya bada arziki ba zata anshi littafin,shi kuma Alkhamis hanyar da tabi dan ansar littafin tayi mashi dadi daman hakan yake son ta kasance shiyasa yayi mata hakan,dan yana son ya kare mata kallo sosai da sosai yana son yaga yanda zatayi tsalle har nonuwanta suna nasu tsallen yasan ko bakomai ya rage zafin da yake ji akan yarinyar.

Sosai take tsalle tana kaima littafi farmaki yana sake yin sama dashi ita kuma bata fasa ba...tunda ya shigo idonshi sukayi kwalli da wannan drama ta Alkhamis da Zulaihat ga yan class sun natsu suna kallonsu sai dariya ake masu take yaji ranshi ya b'aci take yaji wani abu yazo ya tokare mashi k'ahon zuciya har juya mashi yake ga zafi yana mashi ,wani tsalle da tayi sai da nonuwanta suka girgiza sosai fiye da sauran tsallen da ta fara. wani ihu mazan class din suka rushe dashi ,rintse idonshi yayi yana budewa ya buga masu wata uwar tsawa yace..

*Kuyi Manage da wannan banjin dadi sosai*


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

#Love
#Najeeb
#Zulaihat
#AK
#BEAUTER
#Comment
#Share
#Pls

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*


*PAGE 51-60*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ


"Every body keep Quite,I said silence." Yanda ya buga tsawar..cikin harzigi ya ida hirgita Zulaihat dan bata san sanda ta fada jikin Alkhamis ba tana makalkaleshi tight tana mai rushewa da kuka,shi kuma Alkhamis k'ara gyara mata kwanciya yayi a kirjinshi yana shafa bayanta ya daura bakinshi a kunnanta a hankali yake cewa.

"Myluv are you ok.?"Kara shigewa tayi sai kirma take tana kuka,wani irin takukin bakin ciki da zafi ya taso ya tokare Dr Najib ko gabanshi baya ganin tsaban kishi da masifa. bai san taku nawa yayi ba sai dai ya ganshi gabansu da karfi ya fisgo Zulaihat daga jikin Alkhamis yana daura mata mari wani marin ya kara aza mata zai kara daura mata na uku Alkhamis ya rike hannunshi yana mashi kallon kai waye?kuma baka isa ba.

Bai san sanda zuciya ta d'ibeshi ba shima ya daura mashi wawan mari dan shi da Alkhamis sai da yaga tartsatsin wuta tsabar azaba kafin ya dawo dai dai ya kara daura mashi wani sai huci yake kamar wani yunwataicen zakin da yayi shekara bai samu abinci ba...cikin jin zafi da azaba Alkhamis ya cacimi kwalar Dr Najib aikuwa nai fada ya kaure a tsakaninsu daman Dr yana sama shima haka Alkhamis din amman duk da Alkhamis yana saman dokin zuciya bai samu nasara a wajen Dr Najib ba,dan Dr Najib ya fishi nesa ba kusa ba,dan yafishi tsawo harda karfin ma.

Ihun da lecture hall din ya dauka yayi attraction din mutanen waje tun daga students har lecturers kuwa. duk wanda ya shigo yaga abunda ke faruwa sai tsoro da tausayin Alkhamis ya kamashi tabbas wannan ko waye bako ne a cikin school din bai kuma san waye *DR NAJIB H ABDULLAHI* da bai yi gigin cewa zai had'a jiki dashi ba wai suyi dambe,koda Dr Moha ya shigo yaga abunda ke faruwa bai tsaya ba ya kira police yace kar wanda ya raba su,su bari masu rabawa suna kan hanya za suzo su raba su.

Ita kuwa Zulaihat tunda ta duke kasa babu abunda take sai kuka gashi daman bata son hayaniya da tashin hankali ko kadan ga kuma zafin marin da Dr yayi tunda tana iya yin kuka a zahiri har ta koma yin na zuci. dan muryarta ta dushashe sannu a hankali ta fara ganin mutane biyu biyu sai luuuuu ta ida faduwa kasa sumaimiya ba tare da kowa ya lura da halin da take ciki ba hankalin kowa yana wajen su Dr Najib.

Suna cikin ba juna kashi sai ga yan sanda sun iso take Dr Moha yaba yan sanda damar kama Alkhamis yace su tafi dashi yazo ya tada masu hankalin makaranta kuma yana fada da malamin makaranta ,aikuwa yan sanda sukayi cak a kan shi suka saka mashi aunka suka tisa keyarshi gaba sai station.

Cikin tsarewa da kamewa irin tashi yace.."duk wanda yasan ba nan bane venue din lecture dinshi just get out,idan kuma nan ne venue dinka get a sit." Yanda Dr Moha yayi maganar ba wasa yasa students suka kama fita daya bayan daya kowa mamaki fal a zuciyarshi mai ya hada wannan fadan? Da tambayar da suka tafi kenan,su kuma yan class zuciyar fal da tambayar mai hakan ke nufi? Dr Najib ya bugi saurayin Zulaihat dan yayi hunging dinta ko dan yana kishi akan abunda ya tadda anayi idan yana kishi hakan na nufin yana son Zulaihat kenan? Suma da wannan tambayar suka samu waje suka zaune sai a lokacin Zubaida ta hango Zulaihat yashe a kasa kamar gawa.

Ihu ta kurma tana yin kanta nan hankalin kowa ya koma a wajen duk da ba wanda yayi kokarin tashi daga inda yake amman ido ya koma kansu girgizata Zubaida tayi tana cewa.. "Sis wake up dan Allah ki tashi karki yi man haka karki tafi ki tafi ki barni Sis wayyo Allah ni Zubaida na bani na Shiga ukku na lalace." Rintse idonshi Dr Najib yayi yana maida kanshi gefe duk da zuciyarshi na jin zafin akan abunda tayi. amman sai da gabanshi ya fadi da yaganta yashe sosai yake jin dama shi yake kukan da Zubaida keyi ko yaji sausauci idan ta mutu ta barshi ba zai iya rayuwa ba, dan bai iya rayuwa da ko wace y'a mace idan ba da ita ba itace yake so kuma yake kauna, shi Dr Moha sai a lokacin ya lura da ita dan kallon Najib yayi yana girgiza kai sannan yasa mata suka.kamata aka sakata a mota sai Zubaida da ta biyo ba inda sukayi ma tsinke sai asibiti.

Duk da yana cikin yanayin damuwa hakan bai hana ya tara yan class ba yayi masu gal da masifa ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba,kowa kuwa ya shiga taitayinshi inda suke ganin suma basu kyauta ba da suka tsaya kallon wanann drama ba tare da sun hana ba. duk da wasu da dama tare suka shigo suka taddasu ba kowa yasan asalin abunda ya hada su ba.cikin takaici ya cigaba da cewa.

"Ba ita wannan yarinyar ba ko wacece na tadda tana wanann rashin tarbiyar dole ne na hukuntata a matsayina na malaminta,dan haka ya zama dole ku mata ku tsare mutuncinku kuma ku kama kanku a matsayinku na mata. kunga dai yarda daku da iyayenku sukayi shiyasa har suka turoku wajen nan ,karku biyema zamani da son zuciya ku dawo kuna aikin da na sani and shi namiji komai yayi adone ake cewa sai dai ni ban yarda da wanann maganar ba ,saboda idan shi ba'ayi mashi gori ba watan watarana sai anyi ma yaranshi idan ya haifesu gaba,kuma dai ance abunda kayi ma wani sai anyi ma naka."

Sai da yayi masu tas.ya kuma hada da wa'azi a fuska ya nuna baisan wacece Zulaihat ba a yanayin yanda yayi bayanin ko sunanta bai ma sani ba hakan ya wankeshi daga zargin da students suke mashi na son yarinyar yake ,wasu daga cikin yanmatan class din kuwa hankalinsu ne ya kwanta da kuma natsuwa da ta samaisu sabida son da suke mashi.

Bai fasa yin lecture din ba sai da yayi covering din da yace zaiyi yana gamawa ya kuma ce test zaiyi nan take.ba snap test ba normal test take hankalin Wanda basuyi karatu ba ya tashi nan yan kananun maganganu ya fara tashi a hankali a cikin hall din.

Basu ida sakankancewa da lamarin ba sai da suka ga malamai suna shigowa ana akace su fidda bags dinsu nan ma suka yarda da gaske dai Test zaiyi without notice,kowa natsuwa yayi bayan ya tadaji pen din shi dan yace pen kawai yake bukatar gani a gaban mutun sai da akayi parking din duk wasu papers sannann ya raba question dan full in the blank ne zaiyi masu questions 20 ne over 40 each question yana carry din two mark kuma 15min ya ba test din.

Yanda ya bada question din ba wanda yayi kokarin d'iga ma peper din shi ink saboda tsaurin da question din yayi masu wasu ma cewa suke baiyi masu ba...ga kuma tsaron da ake yi sai kace exams ake ba test kanaji kana gani baka da damar tambayar na kusa dakai. sai dai ido wasu hawaye suka fara wasu kuwa ganin ba sauki sai a wajen Allah reg number dinsu kawai suka saka sunayin submit,time na cika yace.

"Pen off."

Take suka kama ajiye pen dinsu daman ba sanin ansar suka yi ba,hana kowa motsawa yayi da kanshi da malaman da sukazo tayashi suka bi road by road suka kama ansa har suka gama kowa ya kama gabanshi ansar pepers din yayi yana godiya ya wuce office ya ajiye su ya tafi office din DEAN na faculty din koda yaje suka zauna gaisawa suka fara yi sannan yace.

"Dr Najib dalilin da yasa na kiraka inason sanin wai ya akayi maiya faru da har kai fada da wani saurayin dalibarka anzo har office an gayaman.ba mutun daya ba kuma biyu ba ance har Dr Moha ya mik'a yaron a wajen police."

Murmushi yayi yana cewa.."Sir ai nasa su da suka rugo suka gaya maka abunda suka gaya maka ya wadatar."girgiza kai Dean yayi yana cewa.."Dr inason ka sani kai kana da mahinmmanci a faculty din nan kaii ba a iya faculty ba duka school din nan kana da mahinmanci nasan kai kasan da haka,kaga dan sunzo sun gaya man shurutunsu ba zance ba zan sauraresu ba,zan jisu amman dole naji daga bakinka dani nasan ruwa baya tsami banza."

Murmushi yayi yana gyara zama ya gaya Dean Iya abunda yasani komai bai boye mashi ba..shima kanshi Dean sai da yaji ranshi ya b'aci cikin rashin jindadi yace.."A gaskiya wanann yarinyar bata kyauta ba Sam bata da tarbiya dan haka zamu kira iyayenta mu zauna dasu muji shin su suka koya mata wasa da maza ko kuwa."?

Rintse idonshi yayi yana girgiza kai yace.."ina neman alfarmar karda a sako iyaye a cikin wanann maganar." Shima Dean girgiza kan yake yana cewa.."saka iyayen shine dai dai Dr dan susan halin da ya'r su take ciki sai suka saka mata ido sosai akan tarbiyarta,barin kuma sai naga kamar b'arnane dan nasan iyayenta basu san ila ma tana da saurayi ba ko kuma basu san suna tare da shi ba."

Numfashi ya sauke yana cewa.."hakane kuma ni yanzun zanje asibitin naga halin da yarinyar take ciki." Mik'a mashi hannu Dean yayi yana cewa..Allah ya kara maka girma Dr." Murmushi kawai Dr yayi ya fito sai da ya biya office dinshi ya dauko question peper biyu sannan ya wuce.

★★★

Ta farfado daga sumar da ta tayi ta wucin gadi.sai dai tak'i tace komai sai hawaye kawai da ke kwarara a fuskarta,Dr Moha tunda ta farfad'o yace ta rufe masu baki karda ya sake jin tarin kukanta yana tambayarta maiyafaru da har akayi fad'a kasa magana tayi sai ma kukan zuci da take tunda ya hanata na baiyane...wata irin tsanar Alkhamis ce tazo ta baibaye zuciyarta da gangar jikinta har cikin ranta take jin bata sonshi bata son mai sonshi,ita kanta kunyar kanta take ji akan abunda ta aikata har ji take anya zata iya kallo yan class dinsu?da wani ido zata kalle su ma?balle Dr Najib kuma Allah kadai yasan irin hukuncin da zai mata.

Shi dai Dr Moha maida hankalinshi yayi a wajen Zubaida tana gaya mashi tun daga farkon haduwarsu har kawowa yau da abu da ya faru yaji ba dadi sosai ya kuma yi ma Zubaida fada sosai akan ba motar kowa ake shiga ba a wannan zamanin suna iya shiga motar yan iska ko kuma motar masu sace mutane aje a yankasu a banza kuma su suka kai kansu.

Share hawayenta itama Zubaida tayi tana cewa.."wallahi wallahi Sir daman mun bari tun ranar da Umma tayi mana fada ,daman bamu taba shiga ba sai a kanshi kuma sabida naga dare yayi shiyasa da bamu shiga ba wallahi."

"Is better dai Zubaida ya kama ta dai ku daina din har abada.yanzun duniyar nan tazo karshe mutanen cikinta ba gaskiya ne da su ba.kadan ne masu gaskiyar ,ai da sai ku kira Najib da kuka rasa abun hawa ku gaya mashi kuna waje kaza yazo ya daukeku na tabbata zaizo."

Dan zaro ido Zubaida tayi tana girgiza kai tace.."Sir ai bamu da Number Dr ,kuskurene mun aikata ba zamu sake ba in shaa Allah." Shuru yayi yana kallon Zulaihat yanda ta maida kanta k'asa tana aikin share hawaye. sai yau ya yarda da maganar Najib da yace mashi ita kukane abokinta bata da aiki sai kuka, kauda kanshi yayi yana kallon time kiran likita yayi yazo ya duba drip din da ya saka maka dan so yake yaje gida,daman exams question ya kawo ma exams officer shi ya shigo dashi school din ya tadda wanann tashin hankalin....koda likita yazo ya kara dubata cire mata yayi yana dan rubutu saman wata peper kallon Moha yayi yace.

"Moha gaskiya yarinyar nan tana bukatar hutu sosai stress yayi mata yawa dan jininta gab yake da ya hau." Zaro ido Moha yayi yana cewa.."hawan jini Dr."d'aga mashi kai yayi yana cewa.."yes of course."Dr Moha ya bude baki zaiyi magana kenan Dr Najib ya shigo yana cewa.."aikuwa yanzun ta fara hawan jini da irin wannan halin nata to gab take da kamuwa da ciwon zuciya ma." Su duka da kallo suka bishi banda Zulaihat da ta maida kanta gefe tana share hawayenta tana mamakin irin tsanar da Dr Najib yayi mata.ashe ta wuce duk tunaninta wata irin tsana ce wannann? da har yake mata fatan ciwon zuciya? Sosai tajin zafin kalamanshi har cikin ranta wannan wata irin jarabace?a hankali tace.."in shaa Allah kai ne zaka kamu da ciwon zuciyar kafin ni,I hate you."

Duk da baiji abunda take cewa ba ,Amman yana kallon bakinta na motsawa kwafa yayi yana aiyana Iya rashin mutuncin da zai aikata ma yarinyar.dan wani irin haushinta yake ji har baisan ganinta da ya ganta sai ya hangota lafe a jikin katon banza.dan karamin tsaki yayi yana ba Zubaida question gami da wulla mata harara ansa tayi tana yin kasa da kanta maida kallonshi wajen Zulaihat yayi yana jan dogon tsaki gami da cilla mata harara yace.

"Zaki tashi ki ansa ko kuwa sai nayi ball dake.?"

Turo baki tayi gaba ta tashi zaune hawaye na bin fuskarta bayan hannu tasa ta share hawayen,jefa mata question din yayi yana kallon time yace..." 15min remain." Kallon juna akayi tsakanin Zubaida da Zulaihat tsawa ya buga masu yace.."lokaci na cika zan ansa ku tsaya bata man lokaci." Hawaye ne suka fara zubo mata tana duba question din a hankali ta kalleshi tace.

" Pen."

Tsaki yayi a karo na ba adadi yace.."ina naki."?gauda kai gefe tayi bata ce komai ba sai ajiye peper din da tayi shima baice komai ba ya maida kallonshi wajen Zubaida da take ansa question din..girgiza kai Dr Moha yayi yana mik'a mata pen ansa tayi tasa reg number dinta ta fara answering question din cikin natsuwa nunawa tayi kamar bata san da zaman nashi ba a wajen. sai answer question din ta kawai take tanayi tana share hawayen fuskarta kafin yace time yayi ta mik'a mashi pepers tana komawa tayi kwanciyarta tana lumshe ido,kallon peper yake yana kallonta sai kuma ya danyi murmushin gefen baki.

Itama Zubaida bashi tata tayi tana yin kasa da kanta ansa yayi yana dubawa again dan murmushin yayi yana kallon Dr Moha yace..."mu tafi gida ko."?

"Aa bari Dr yazo ko sai mu saukesu sai mu wuce police ko."? Tabe baki yayi yana cewa.." Aa ba yau ba barshi suyi mashi hankali sanann." Murmushi kawai Moha yayi baice komai ba dan baya bukatar maganar tayi tsawo a gabansu karda yayi tabokara,wayarshi tayi ring ya fiddo ya dauka baice komai sai can yace.."OK shikenan Sir." Ya zare wayar daga kunnanshi yana kallon Zulaihat yace.

"Makaranta na bukatar ganinki keda iyayenki a senate gobe da misilin karfe goma na safe."

Gaba yayi yana barin room din bai tsaya jiran abunda zatace ba da kallo tabi bayanshi tana mai rushewa da kuka,haka itama Zubaidar kuka take tabi bayanshi Moha ne ya tsaya taimaka mata suka
fito sai kuka take.

Tsaye take gabanshi tana cewa. "Sir dan Allah ka taimakemu mun shiga ukku karda iyaye su shigo a wannan maganar wallahi har abada ba zata sake ba,kuma d...d'aga ma Zubaida hannu yayi yana cewa.." Lokacin da take wasa da katon banza kin hanata?baki hanata ba sai ma dariya kika koma gefe kinayi.abun da suke dai dai ne yayi maki kyau. to yanda baki hana aikata barnaba ki sani ba zaki hana makaranta aikata gyara ba maza b'aceman da gani."

Juyawa Zubaida tayi tana share hawayenta zuciyarta cinkushe da bakin ciki tabbas gaskiya ya gaya mata ,amman mai yakawo iyaye a cikin wannan maganar?tabbas ta tabbata yau mai rabasu da Umma sai Allah ta ina zasu fara bata wannan labarin marar dadin saurare? ,kamar wanda kwai ya fashe ma a cikin ciki ta bude motar Dr Moha ta shiga gidan baya maida marfin motar yayi yana mata key suka dauki hanya,shuru motar tayi ba abunda ke tashi sai ajiyar zuciyarsu sosai tausayinsu ya kama Moha.

Har kofar gida ya kai su yana kallon Zulaihat yace.."kuje ku cema Umma idan ba damuwa ina son magana da ita."kamar daman jira take ta rushe mashi da kuka tana cewa.."na bani Sir wallahi kasheni zatayi dan Allah ka rufaman asiri wallahi mun tuba ba zamu kara ba." Rintse idonshi yayi yana budewa cike da tausayinsu yace..."Zulaihat

Please Login or Register in order to submit comment