Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunzurashi yasan kuma magana d'aya yake a rayuwarshi kaifi d'aya ne,cewa yayi.

"Amman Najib sai naga kamar hakan bai dace ba,aure soyayya yana da dadi ana gina rayuwa Cikin so da kaunar juna ana gina gidan da bai rushewa ayi rayuwa ta *DA'IMAN* a cikin gidan har *ABADAN* kuwa shin ba za ka so kayi irin rayuwar ba a gidanka kai da Zulaihat."? Dafe kanshi yayi yana furzar da iska mai zafi a bakinshi yace.." Moha ba zaka fahimceni ba kaima,yarinyar ce ta cika zafin kai da yawa baka ga abunda tayi ba dazun?Impossible tace fah Moha, shiyasa nima nike nuna mata na fita iya hauka ita nata haukan karami ne Moha idan banyi mata ta mahaukaci ba to ina ji ina gani zata zama mallakar wani ba ni ba.Moha understand me please Zulaihat ba kamar Zubaida bace mai saukin kai ,Zulaihat tana da zafin kai da shirme wanda kuka ya zama abokin firarta yanzun haka kukan take tana can tana yinshi gangar jiki da zuciya sun jiman haka,dan haka inason ka fahimceni ba zan zuba ido ba ina kallon ta jaman asara."(koba asara ba Najeeb🙄,Anya kuwa Najeeb ya dauko hanyar billewa?uhmmm mudai namu ado👁️ warrr😂)

Shuru Moha yayi yana nazarin maganarshi ,shi dai bai fahimci komai ba sai kawai ya bishi da ya fahimta Allah yasa su dace da Amin ya ansa ya koma ya cigaba da marking scrip dinshi dan baya son yaje dasu gida nan yake son ya gama yana bukatar hutu yana bukatar space yaji da matsalar da ake damun zuciyarshi akan son yarinyar da ya lura baya gabanta bata sonshi a hankali ya furta..."zaki soni ne watarana ki kaunaceni ki taitalani ki riritani kamar kwai sannan kuma kiyi kishina kamar zaki mutu soon I'll promised to you." duk da Moha yaji abunda yace sai ya nuna baiji ba hankalinshi ma baya wajen yana ga marking din da yake shima.

★★★

Sai da ta gama kukanta sannan taje toilet ta wanke fuskarta ta fito ta kwanta..data ta bude ta shiga whatsapp tayi kallon status sannan ta maida ma wanda ta gadama reply ta kyale wanda batayi niya ba,sako ya shigo na wata number tsaki tayi tana yin delate ko tsayawa karantawa batayi ba ,cigaba da hidimarta tayi da wata course mate dinsu Rukayya tayi mata magana nan ta tsaya suna gaisawa sake shigowa message din yayi tsaki tayi tana shiga cikin sakon ta fara karantawa.

_Maza kashe datar nan ki kwanta tun kafin ranki ya b'aci_

Dogan tsaki tayi tana cewa.."aikuwa da nayi niyar sauka amman yanzun na fasa sai naga yanda zakayi ubana." Groups ta shiga ta kama karanta messages har da su saurarar voice,hakan kuwa ya rage mata nauyin da take ji a zuciyarta dan wasu voice din idan ta saurara dariya yake ba wani kuma takaici sai dariya take abunta dan yanda akeyin drama a group dinsu na schools idan taji anan sai ta koma a group dinsu na secondary nan ma taji dramar da ake kwasa tasha dariyarta...sake turo mata wani sakon yayi ta share sai da messages din yayi kusan 20min sannan ta shiga ta karantawa.

_karki yarda na sake yi maki magana akan ki kashe datar nan ranki sai ya b'aci sosai dan har gida zan zo maki shashasha._

tsaki ta kuma ja tana tura mashi emoji irin wannan *🤷🏻‍♀️* ma'ana so what,ta cigaba da hidimarta sake mata magana yayi yana cewa.

_wannan shine magana ta karshe da zan maki dan Allah karda ki kashe datar._ tana karantawa sai ta kashe datar tana goge number duka ta koma tayi kwanciyarta tana sakin tsaki sai masifa take ita d'aya kamar sabon kaimu.

Tsaki yayi yana wurgar da wayar yace.."ai da baki sauka ba,da sai na nuna maki ke k'aramar marar kunya ce stupid." Cigaba da marking din shi yayi yana sak'awa da k'ancewa yanda zai gyara ma yarinyar zama,tabbas raini yana kokarin shigowa amman zaiyi maganinta sai ya saita mata brain dinta da kuma hankalinta gami da natsuwa.

Taitara kayan yayi ya ture yana yin addua ya kwanta dan komai ya fice mashi a rai rintse idonshi yayi yana cewa.."zanyi maganinki sai nayi maganin rashin kunyar taki."

*BAYAN SATI BIYU*

"Sannu da hutawa Umma." Dagowa Umma tayi tana kallonsu sai kuma ta girgiza kai tana kallon Zulaihat shafa addua tayi tana cewa.."Mamana." Dago da kanta tayi tana Kallon Umma dan murmushi tayi tana wasa da zoben hannunta tace.

"Naam Umma." Matso da ita jikinta Umma tayi sosai tana kwantar da kanta bisa cinyarta cikin muryar lailashi ta fara cewa.."duk akan maganar Najib ne kika rame haka kika shiga damuwa."? Da sauri ta dago kanta daga bisa Umma tana girgiza kai kasa magana tayi ga kuma kunyar Umma da ta baibayeta ta rasa dalilin da yasa ta kasa yarda da auren Najib duk da tasan har abada Umma ba zata taba yi mata zabin tumin dare ba,murmushi Umma tayi tana cewa.

"Karda ki boye man komai Mamana.idan har kin san baki son Najeeb ba zan maki dole ba kam.duk da dai inason ki aureshi saboda natsuwarshi da kuma hankalinshi da tarbiyarshi dan Najeeb yaron kirki ne ba abun gudu bane kuma raina na bani zan rike man ke amana ba zai barki kiyi kukan maraici ba.koda kuwa bayan rai nane shiyasa nayi maki sha'awar aurenshi ba dan komai ba." Murmushi tayi tana share hawayenta ta kama hannun Umma tana cewa.."Umma tuni na yarda da batun auren Dr tun randa kikayi man maganar na yarda fatana Allah ya bamu zaman lafiya ya kauda fitina." Sosai kalaman Zulaihat sukayi ma Umma dadi dan har sai da fuskar Umma ta nuna hakan tana cewa.."Allah yayi maku albarka baki dayanku yasa farinciki mai daurewa a rayuwarku yaran Albarka." Da Amin suka ansa su dukansu Umma maida kallonta wajen Zubaida tayi tana cewa.."ke kuma ya batun Muhammadu banji kince komai ba ko baki sonshi.?" murmushi tayi tana sunnan da kanta kasa wai ita kunya dan kasa magana tayi sai dai ruwan murmushi da Umma take zaggawa,itama Umma Murmushin tayi tana mai cigaba da saka masu albarka daga nan suka shiga firarsu ta yau da gobe.

★★★

Tafiya tayi riba cikin ikon Allah su Dr Najeeb sun sauka birnin taraiyya Abuja daga airport Khaleed kaninsu yazo daukarsu cikin murnar da dokin ganinsu suka tarbi juna,sannan suka kama hanyar zuwa estate dinsu lifecamp da yake nan suke zaune koda suka iso wani irin fareren gida na gani da fada dan tsayawa a fadi tsaren gidan sai a kwana ba'a gama ba.(gidan novel kenan lol🤪) Dan babban gidane mai dauke da shashe har guda hudu kuma duka ginin irin daya ne sai BQ da ke gefe wanda gateman dinsu yake zaune da iyalanshi.

Daga gefen gidan kuma wani dan garden ne wanda yaji kayan lambu sosai a cikin irin su kankana da su cabbage carrot da green beans pineapple da apple dadai sauransu duk akwai a cikin,daga wani bangaren kuma pool ne babba wanda ya Kara ma gidan kyau sosai ga su dawisu an baza a gidan sai shawagi suke banda su biri da su Zaki and tiger da aka sa a cikin keji ana basu kulawa ta musaman.

Koda suka fito cikin motar direct part din tsakiya suka dosa su dukansu da sallama a bakinsu suka shiga...wata farar dattuwace zaune a cikin parlorn tasha white glasses da suka kara fito mata da kyaunta duk da tsufa ya kamata amman da yake Jindadi da kwanciyar hankali sun boye tsufan nata dan ba zakace tsofuwar ta kai shekara 70 ba a duniya dan jikinta tsam yake idan ka kalleta sai kace bata wuce shekara 50 ba zuwa ta 60.

Zaune take tana kallon. yar aikinta na zaune gefenta tana mika mata apple tana ci wata kuma tana gefe tana goge mata lailen da aka sa mata,da yake Hajja ba daga ba baya ba wajen kunshi dan bata barin hannunta fari fas ba kunshi kulle cikin kunshe hannun take da ya goge tana sa a maida mata wani,wannan al'adarta ce haka ta daura matan yaran nata a kai har da jikokinta basu rabuwa da kunshi kuma bata son asa ko wani irin laile idan ba na hausa ba,sai dai yanmatan su takan barsu su saka black idan za'ayi masu na zane amman mudun jan laile za'ayi da to lalen hausa ne za'ayi using dashi. tun suna mita har sun daina sunzo sun saba dan kuwa ba yanda zasuyi da ita.daman ko zasuyi complain din bama suyi a gabanta sai dai bayan idonta dan mudun akace za'ayi a gabanta to ranar sai sunyi da nasani dan Hajja ba daga baya ba wajen fada.

Koda suka shigo Moha ne ya matsa wajen Hajja yana kwantar da kanshi bisa cinyarta yace.."missing you tsohuwa mai ran karfe,nayi missing din masifarki."Ture kanshi tayi daga bisa cinyarta tana cewa.."Uwarkace Missing kaji ko Moha?ban hanaka yi man wannan yaren yahudancin naku ba?bari Ubanka Kabiru ya dawo sai naci ubanshi a gabanka kazo godaidai dakai kana hayeman kafa dan kaga tafi taka lafiya."

"Ai kinji ke matsalarki wallahi ba mutun ya dawo gida ba yazo ya kuma hadu da wanann masifar taki ke aikinki kenan ga kuma zagi mai ya shigo da Abbu ciki daga cewa nayi kewarki shikenan sai ki hau zagina ba ko sannu da zuwa haka zan aureki kina zagina na fasa na barma Najib daman shine daidai ke."

Kama baki Hajja tayi tana tafa hannu tana rushewa da kuka tana cewa.."shikenan duniya tazo karshe to dan Ubanka ba dani kake ba da uwarka Zainab kake kaji ko,da uwarka kake ba dani ba yo daman ni mai zanyi dakai jiki duk ya mutu nasan koni nan na fika karfi kuma bari ubanka yazo zaizo ya samaini dole yau sai ya nuna maka matsayina a gidan dan Ubanka."

Kuka take bilhakki da gaske harda fashe majina tana cewa yau sai Kabiru yazo ko Hamisu yayi mata tsakani da Moha shi kuma ya sata a gaba sai dariya yake mata yana Kara tun zurata dan idan da sabo ya saba da wannan halin nata.tsaki mai tsawo Dr Najeeb yaja yana tashi ya bar masu part din baki daya saboda wannan halin nata shiyasa bai cika shigowa wajenta ba. ita sam bata san arziki ba ta cika ballo matsala daga wanann sai wanann aikinta kenan shi kuma Moha da yake irinta ne ya kama biye mata yana janta.

Sakake Hajja tayi tana bin kofa da kallo kamar ba ita bace mai kuka ba,ta kusa minti biyu tana kallon kofa kafin tayi kwafah tana cewa..."kaima Uwarka Murjanatu kayi ma tsaki dan Ubanka Hamisu mai mugun halin tsiya. ba gwara kowan kowa ba da kowan dawa ba,zaka dawo ka samainine mutumin banza mutumin wofi ace kullum mutun fuskarshi babu annuri babu fara'a." Kwafah ta sake yi tana kallon Moha tace.."Moha mijina tashi kaje kaci abinci kaji na ma yafe maka yaron kirki karda ka yarda ka biyo halin wancan ja'irin mai mugun halin tsiya mai hali irin na uwarshi anya kuwa wannan yaron ba masanjanshi akayi Hamisu ba a wajen haihuwarshi."? Yanda tayi tambayar with so serious ya ba Moha dariya sai da yayi mai isarshi sannan yace.."nima ina tunanin haka gaskiya Hajja,amman ni na fasa matar dake na barma Najib shine dai dai ke ai."

"Yo tsoranshi nike ne aka ce maka.ni nasan maganinshi bari dai iyayen naku su dawo aure za'ayi maku can kuje ku karata duk iskancin mutun yaje mace ta laddatar dashi,kuma ba zaku sake komawa kano da sunan aiki ba idan zaku tsaya kuyi aiki a wajen iyayenku ku tsaya idan kuma ba zaku tsaya ba can damuwarku dan nagaji da wannan yawon naku kan iska baku kano baku Abuja ku ga Yan Boko duk sai nayi maganinku daga ku har su Hamisu dan na lura sune suke daure maku har kuke wanann yawon kamar wasu engineer."

Shidai Moha baice mata komai ba dan ya lura yau yan rigimar ne a kanta dan haka sai ya kama bakinshi yayi shuru yaje ya zuba white rice with peppersoup ya zauna yaci ya koshi sannan ya tashi ya wuce part dinsu koda ya shiga bai shiga room din Najeeb ba nashi ya shiga ya watsa ruwan ya kwanta dan ya huta kafin su Mom su dawo daga wajen aiki.

Shiko Najeeb bayan ya fito daga part din Hajja sai tsaki yake dan shi baisan halin tsohuwar shiyasa kullun cikin fada suke ,ita ta cika fada da zagi shi kuma sam baisan zagi dan bai hada iyayenshi da kowa ba amman ita idan ta tashi sai ta kira sunan Uban mutun sai ta zaga dan kawai ita ta haifi mutun sai kuma ta kama zaginshi shi. bayason haka,sake wani tsakin yayi yana fadawa toilet wanka yayi ya fito ya shirya cikin tree queter ya fito.kitchen din part dinsu ya shiga ya dafa indomie ya hada tea ya dawo cikin bedroom dan yunwa yake ji kuma su Ammi basu nan suna office balle yaje wajensu yaci abinci ya kuma je wajen tsohuwarcan ta cika mutane da hayaniya ko dan sannu da zuwan nan babu ma.

Koda ya kama cin abincin maida plate din kitchen yayi ya wanke da kanshi dan Najeeb ba daga baya ba wajen tsaffa.daman part dinsu babu masu aiki da ankawo masu sai da yayi yanda yayi yasa suka daina zuwa dan yace basuso su iya yi da kansu sai da rain Mom ya baci akan hakan dan bata ga dalilin da zaice zasuyi aiki da kansu ba.bayan ga yan aiki cike da gida duk yanda ta nuna mashi rashin amincewarta akan bukatarshi sai ya kai maganar sama dan Hajja ya gayamawa kuma ta mora mashi baya.shiyasa ko wane part akwai masu aiki kusan biyar zuwa sama amman banda nasu dan kowa shi yake gyara bedroom dinshi parlorn kuma roster ce idan wannan yayi yau gobe wannan zaiyi daman su uku ne kawai maza a gidan.yana bukatar hutawa shiyasa bai kira Zulaihat ba sai dai ya kira Umma ya sanar mata da sun sauka lafiya sannan ya maida wayarshi silent ya kwanta kafin anjima ya shiga part din su Mom ya gaidosu idan sun dawo daga wajen aiki.

★★★

Koda suka shigo room dinsu shiga toilet tayi dan yin wanka,sai da tayi kukanta mai isarta sannan ta fara wanka sosai take jin zuciyarta tana mata zafi idan ta tuna wai Dr Najeeb shine zai zama mijinta nan da wani lokaci idan yazo.taya zata zaune da wanda baisonta?taya zata iya zama da wanda tafi tsana a duniyar nan?shine fa mutumin da yake sakata kuka kullun shine mutumin da yake son yaga bayanta ta kowace hanya,tasan ba dan komai yace zai aureta ba sai dan ya musguna mata ya wulakanta ta shine cikar burinshi anan duniya ganinta a kasa,share hawayenta tayi tana girgiza kanta tace.."Ina ba zan yarda ba zan nuna mashi wannan ba Zulaihat da ya sani da ba ce mai raunin zuciya,zan nuna maka da da yanzun ba daya ba Najeeb zan aureka amman ka sani sai kayi nadamar aurena da kanka zaka sakeni dan zan nuna maka ni ba kwanwar lasa bace dan ada ka takani yanda kaso amman banda yanzun zan lasa maka takobi mamaki." (Gaskiya ne Zulaihat har kin fara bani tsoro fah 🤣)


Share hawayenta tayi tana ida wanke jikinta ta fito ta shirya cikin halfgawn pink mai masifar kyau ta kuma Kara mata kyau abunka da farar fata,wayarta ta dauka ta kunna data ta shiga whatsapp dan gaisawa da course mate dinta...tana cikin chatting sai ga notice din Najeeb ya shigo tsaki tayi tana kauda kanta daga message din nashi ta cigaba da chatting dinta sake shigowa wani yayi nan ma again tsaki tayi shiga cikin message din nashi dan ganin da mai yazo. Karantawa tayi tana sakin wani dogon tsaki ta rubuta dan short note ta tura mashi tana turo baki gaba kamar yana gabanta...sai da tayi 5min da turo mashi sannan ya shiga dan ganin ansar da ta bashi fara karantawa yayi kamar haka.


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508315 for call or whatsapp

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_

Na
_YAR'MUTAN KANKIA_

_MANAZARTA WRITERS_

*BOOK ONE*


*PAGE 91-100*

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*NO EDITING❌*

_Ba damuwarka bace hawana online please malan I beg ka fita daga harkata_

kurama sakon nata ido yayi yana kallo.ya kuma maimaita karanta sakon nata yafi sau ba adadi,maimakon yaji haushin sakon nata sai yaji ya tsinci kanshi a cikin farinciki ya nemi fushi ya rasa.kalma Malan ka fita daga harkata shine yafi bashi dariya ma,wai ya fita daga harkarta bayan kuma yanzun ya fara shiga harkar tata tunda dai ko tana so ko bata so shine dai zai zama mijin nata,yana cikin sake kallon sakon nata Moha ya shigo yana cewa.."ka tashi mu shiga cikin gida kasan su Mom sun dawo." Kallon Moha yayi kamar ba zai magana ba sai kuma yace.."Ina sane so nike sai su Dad sun shigo sannan dan akwai maganar da nike son nayi dasu."

"Wace magana kenan."?

Cewar Moha yana ajiye wayar hannunshi dan daman gama wayarshi kenan Zubaida ya shigo room din,dan tabe baki yayi yana ajiye wayar tashi yace.."maganar wanann yarinyar mana." Murmushi Moha yayi yana cewa.."Broth wace yarinyar kuma." Harararshi yayi yana cewa.."ban sani ba please Moha wace yarinyar zan maka magana idan ba wanann marar kunyar yarinyar ba Zulaihat?dole nayi maganinta sai na koya mata hankali."

Fuuuu ya tashi ya shige toilet sai daure fuska yake,shi Moha murmushi yayi yana dage kafadunshi ya cigaba da wayarshi da Zubaida cikin so da kaunar juna,Koda Najib ya fito daga wanka direct gaban mirror ya nufa ya fara shiryawa kamar mace dan lotion din da yake using dasu wata macen ma bata dasu dan sun kusa kai biyar banda cream kuma ko wane sai ya shafa da yake bai tara suma kasunbace kawai da gemu ya gyarasu ya shafa masu mai da yake using dasu.wardrobe yaje ya fiddo wani white yadi mai kyau da tamsi ya saka yasaka hula white da takalmi hadda agogonshi apple ce white mai kyau ya saka ya fashe jikanshi da turaruka masu kyau da tsada ya dauki wayoyinshi ya kalli Moha yace.

"Zaka iya tasowa mu tafi."

Murmushi yayi yana cewa.."Babe byee zamu shiga cikin gida love you muaahhhh." Murmushi Zubaida tayi tana ajiye wayar tana kallon Zulaihat tace.."Sis fatan kinyi ma Dr Najeeb ya gajiyar hanya ko."?tsaki tayi tana girgiza kai tace.."Banyi ba kuma ba zanyi ba,Kinga Sis pls ki daina yi man maganarshi dan bansan ji sam."

"Amman Sis a gaskiya baki kyauta ba kaso mai sonka fa." Tsaki tayi tana cewa.."ce maki yayi yana sona?yaushe yayi dake sona yake?tom bari kiji na lura kema ya sanyenki kamar yanda ya sanye Umma da kalaman banza da wofi irin nashi.Najeeb ba sona yake ba kamar yanda nima bansonshi kawai zai aureni ne saboda wata muguwar manufa tashi nima kuma na shirya bi dashi da yanda yazo haka zan ansheshi."

Dafata Zubaida tayi tana cewa.."wallahi Sis Dr Najeeb yana sonki yana balain sonki so sosai ma tun kafin ya furta maki nasan da haka,kin manta number da ke maki text a da HA shin kin taba zaunawa kiyi tunanin waye HA kuwa Sis."?

"Bazanyi ba.ya kamata ki sani Sis banda lokacin tsayawa tunanin waye wani HA.ina hama da karatu ban damu da nasan waye shi ba dan ba matsala ta bace."murmushi Zubaida tayi tana cewa.."wai Sis yaushe kika zama haka?kamar ba ke ba." Turo baki kawai tayi bata sake cewa komai ba sai goge hawaye da ta kamayi dan zuciyarta zafi take mata sosai idan aka anbaci Najeeb a gabanta.(nidai nace Zulaihat ayi dai a sannu fah ahtoh lol🥂)


★★★

Ko wane part sun shiga sun gaida iyayen nasu sannan suka wuce part din Hajja dan sunsan a can ne zasu tadda su Dad a wajen Hajja dan acen suke firar dare.duk ranar duniya da sallama dauke a bakinsu suka shiga zaka samu waje a kasan carpet suka zauna suka mika gaisuwa a wajen su Abbu sannan suka kalli Hajja Najeeb ya fara gaisheta ,tsaki Hajja tayi tana cewa."Dan Ubanka ba zan ansa ba,ka gama yi man tsakin dazun shine yanzun dan kaga su Hamisu shine zaka wani gaisheni kamar na kirki?daman zama.jiranka nike wallahi yau sai naci ubanka Hamisu gashi nan zaune a gabana." Fashewa tayi da kuka tana face mijina ta nuna Dady ta cigaba da cewa.."Kai Hamisu kayi ma danka magana idan kuma ba haka ni zan tashi na bar maku gidanku na koma asalina daman Ina zaman zamana a wudil kuka daukoni kuka maidoni nan.dan kawai yaranku su ringa yi man rashin kunya da tabbata bayan ni na haifeku da ban haifeku ba ai ba zaku haifesu ba."

Matsawa kusa da Hajja Alhaji Hamisu da Alhaji Kabir sukayi a tare suka dafata suna cewa.."Hajja dan Allah kiyi hakuri." Dan shuru sukayi sannan Alhaji Hamisu ya cigaba da cewa."Hajja in shaa Allah daga yau hakan ba zai sake faruwa ba,kuma bake zaki bar gida ba dan wannan gidan kece ma mai iko dashi dan duk abuda muka mallaka a duniya naki ne dan Allah Hajja kiyi hakuri ki daina kukan nan."

Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa."A'a Hamisu ni nagaji da wannan wulakanci daga wannan sai wannan. nidai gidanku kawai zan bar maku dan haka gobe sanmako zanyi sai wudil." Girgiza kai Alhaji Kabir yayi yana cewa.."Dan girman Allah Hajja kiyi hakuri hakan ba zai sake faruwa ba."share hawayenta tayi tana cewa." Sai dai kam cikinmu ku zabi daya ni ko yaranku." Murmushi Dad yayi yana share mata hawayenta yace.."ke muka zaba Hajja yanzun ya kike so ayi."?

"Aure nike so ayi masu su bamu waje suje can su karata su da matansu mu mun huta da wannan fadin rai."

"To Hajja yanda kika ce haka za'ayi ai,amman anya suna da matan a kasa ma kuwa."?tsaki Hajja tayi tana tashi tsaya ta kama kuhu tana cewa."ai wallahi ko basu da yanmata sai anyi ma wannan gwardawan aure. sun bar mana gida zanje wudil da kaina na sama masu mata."

Cikin kwantar da murya Abbu yace."to Hajja zauna ayi maganar fahimata. tunda ga yaran nan aji ta bakinsu idan basu da wanda zasu aure sai aje wudil din a sama masu matan." Zama tayi tana hura hanci tana cewa.."wannan kuma can matsalarku ce dan ni na gama magana ta aure dai ba fashi." Girgiza kai kawai Dad yayi dan idan da sabo to sun saba da rigimar Hajja,gyaran murya yayi yana kallon su Najeeb yace.

"Har sau nawa zamu gaya maku ku daina yi ma mahaifiyarmu rashin kunya?to bari kuji shine farko da na karshen akan yin haka ku.

Please Login or Register in order to submit comment