Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mama sai kinjine
Kai mama ba komai fa."
Fandau tace " mama kuma yace" yes
Tace "kabani ita mugai
Yace bayan wanda kumayi ai kun gaisa canza murya nayi dan nasan idan mama taji muryar ki zata gane haka kema idan kikaji nata zakiyi kuka ki fallashe mu
Aiko bai karasa ba tasa wani uban kukan da ya rikita Nabil
Yanzu dama da mama muka gaisa ban sani ba naki maganan kirki dan sake bani ita wllh banan yiba yace "a a
Sai watarana kuma
Haka tasha kukanta shikuma sai aikin lallahinta yake

Washe gari suna zaune a parlour akasa tana wance a cinyar sa yafara wayan nasa najaraba da hadim wanda sai suceye awa guda sai kace abin ibada yawan rabin firan akan fujjirat ne wai sai yaji muryar ta sai kashe ita kuma anyi anyi taki dariya
Ita kuma Fandau yakamo mata gallery a daya wayan tana aikin kallon pic din baby da mama idan tazo nashida Hadim ta tabe baki duk da suna mugun kyau da dacewa zugo iya Nabil take ta kallo
Yana sani da abin da take yakashe wayan
Yace"yanaji kiba tsaki ko kina jin haushin inayiwa matata kalaman soyayya."

"Ni ba haka ba waya nakeson ka koyamin."

Yace"kamar yaya inkoya miki waya wani irin koyawa?

Inkoyi shiga ko ina kozan kamo hoto basai ka kamomin ba amma kai naga alaman idan zakayi amfa dashi agabana sai kayi yanda bazan koyaba."
Yace"kikoyi imin bincike ko."

Tace "nibawani bincike dazanyi
Bazakice zaki kira mama ba
Tace"wllh kokai kace yanzu inbai yana kaina ga mama wllh ALLAH bazan baiyana ba komai yana da lokaci inaso nafito da shirina yanda zan bawa kowa mamaki,
.shiru yayi yana tattara kalaman ta yaji taci kakiramin Sani mugaisa
"Naki wai mekuke shiryawa da Sanin ne kwana kadan sai kice nakirashi kuma baza kuyi, maganan agabana ba sai kinfita gefe."
Tace"yanzu ko agaban kaza ayi."
Yace "bayau ba

Zreky yau zaije siyaya meda me kike son kari asiyo miki."
tace "ummm abubuwan dayawa kuma sai yazo natuna kaga dana iya rubutun da sai narubuta ai dama nace kakoyamin kak'i."

Yace"nima awajen rubutu katon jakine ko a class har karatun ma ne abinda nabudi idon dashi tsalle tsalle koba haka kike cewa ba".
Taso ace yakoya mata rubutu
Amma tunda dana hada bak'in
Me zai hana tana jagolgola rubutun dakan tama tana rubutun koda hausa ma to mema zan rubuta aiko tarishin ratuwan ta idan tace zata rubuta kafin ta gama ta gama kwarewa darubutu

Tace" to inason cemasa ya tsiyo min biro da takar da ma tafadi duk abubuwan da take bukata

Haka sukayi wanan zaman cikin soyayya sowajen 3 hadim tana saranan zuwa yana cemata tabari sai gobe sai data gaji tace"ita sai tazo ya kyaleta

"Yanzu da gaske yau zata zo dan ALLAH kasan yada zakayi kahana zuwan
yace "wllh bahali nayi nayi nakasa
Amma ai zandinga fakewa da baby ina shigowa ai."

*Bayan wata* 4

Fandau tashiga watan haifuwa yau ko gobe amma ko min rashin ima in mutum idan yaga Fandau awanan lokacin zai tausaya mata ita kanta hadim mugun tausayin ta take dan gaba daya kaman nin ta ya janja fuskan tada kafafuwan sun kumbura sosai gawani irin girma da cikin yayi nunfashin ta kansa awani sama sama takeyin sa magana idan tafara da kyar take karasawa kwanciyar ma gagaran ta yake ko tsakar dare ne saide ta tashi tayi ta yasho kullum bakin ta yaya aunty kuji tausayin kukai ne aciremin cikin nan wllh ayanda nakeji cikin nan kaine zai
Nabil yace "my one mukai ta acire banason ta mutu."
Bazata mutuba
Wani lokacin haka Nabil zai rungume ta yayi ta lallashita
Jiyake inama ajikin sa cikin yake da da sauki ina ma shi doctor ne da yatemaka mata
Ana haka yau ta tashi dawani matsanan cin ciwon mara wanda sunsan na nakuda ne ita da Nabil amma banda Hadim da taketa faman cewa juyine dan ita adaukan ta cikin wata 8 ne

Gayakama yau ne zuwan inna ZAINABU wanda tace zata zo idan hadim tasauka sai su hada sukoma tare suna cuku cukun zunan inda wana sai dare zata sauka itada Kamal da Grema
kawai sai Fandau tashi da Wannan hali
Tajiga ta sosai
A zuciyar sa yace '
amma hadim sai tayi duk abinda zatayi awanan karan sai yakaita hospital

Dagota yayi cak zaiyin hanyan waje da ita Hadim tarike shi" ina zaka kaita?

"Hospital yabata dan bazan barta agida tawahala irin wacen ba dan wan da alama yafi wancen ko agoyon cikin wannan yafi wahala

"kana nufin haifuwa zatayin nagayan ma juyine kata ba ganin an yin haifuwa wata 8
Yace "saketa mutafi nace miki haifuwa ne
Cikin karaji tace "inko haihuwa ne cikin nan banaka bane

*Nace ummm Hadim zauna nan*

*fans ankusa fa Inna takusa sauka ga fandau ba lfy*
DAMATA



NA



BATUL ADAM JATTKO


34

Ai Hadim tana ganin dagaske Nabil kaitan,zaiyi sai tayi sauri tarigashi fita parlour karshe wanda zai fitarka a part din Fandau taje da saurin kafin Nabil yakaraso tacanja securityn kofan saida yazo yanasa no akofa yace ba daidai bane yajuyo yakalle ta yace "come an open
Tace "my star kashiga hankali ka mana yazaka rushe mana shirinmu da muka sha wahala, akai
Yanzu kana fita da ita asirin mu yatonu ko awajen ma aikatan gidan nane,
Nikuma nayin yaya da wanan tarin summan danatara aciki

Ahankali yasauke Fandau dayaga tanawani irin mika
Zaije wajen Hadim dan bai tabajin arayuwa ya tsani ganinta irin yauba dan jiyake idan yayi nasaran dankan ta sai yaga tadena nunfashi
Amma yana sauke ta fandau din tayi saurin rikeshi
tace" Muhammad inawannan wasikan da nabaka a haifuwan Fujjirat to dan Allah shinakeson kakaiwa mama idan ALLAH yasa na mutum kayafemin abin da namaka badaidai ba."
"mata mazaki mutuba jikina yana bani tare zamu rayu zaki haifamin yara dayawa...
Hadim "tace dame kakirata mata fakace?
Nabil baisan metake cewa ba danshi burinsa yakwace daga hannun Fandau ita kuma ta kenkemeshi da dukkan karfinta shikuma yakasa fizgewa dan lallaba ta yake dan gani yake kokamata yayi zataji zafi shine yaki kwace jikinsa da karfi

Take kenkeme shi Fandau tayi tana cije baki saiwani gumine yake keton mata
Tana salati cikin wani irin sauti take salati
Nabil yajuya yakalli Hadim yace" Halima idan baki zokin budemin kofannan ba wllh zammiki abunda baki taba sammanin wani mazai miki ba balle ne idan matata tamutu wllh kema saide ajera kabarin ku ai Hadim cikin wani irin kishi da hargagi takaraso inda yake tana nunashi Nabil nizaka kashi akan wata dani nayin silal haduwan ku zaka kira wata macce da matar ka ayu.......
Aibata karasa ba jin kukan jariri cikin sauri takara sa ta sugunnan tazaro jaririn da Fandau take shirin dannewa dan sabar wani sabon ciwon dataji wanda yafi nada yarfa hannuwa ta fara tanacewa yaya yazanyi da ciwon nanne
Nabil gaba daya yagama gigita yarasa yazaiyin
Hadim ko tana zaro dan tazare ido kai my star wllh Namiji ne ALLAH Namiji ne fari mekamar mu har yafimu kyu wllh ban daba ganin jariri me hancin saba
Ina shi Nabil ta Fandau yake
Wani irin nishi Fandau tasakeyi saiga wani katon jaririn yafado ai Hadim dasaurin taje tasake daga wancen ma tace kai yan biyu duka maza ALLAH mungode maka
Fandau tasauke wani nan nauyen ajiyan zuciya
Tayi lamo ajikin Nabil da yakasa kowane irin yunkuri tsaba gen murna da farin ciki bai san yana mutuwan son yara maza ba sai yanzu da yasamu shiko mezai yiwa Fandau arayuwa yabiyata yazai da wannan farin cikin da tasashi kawai sai yakwantar da Fandau ya matsa jefe yayi sujjada yana meka godiyar saga ALLAH nawan nan baiwa da yamasa cikin watanni 10 yamasa kyutan yara 3 idan ba shiba wazai masa wanan kyuta sai rafkawa ALLAH kirari yake yama banta yanda jikinsa yake abace sai da yadago yaji Fandau tanacewa dan ALLAH yaya ka daukesu sudena kuka
Sai asannan yajuya yaga ba Hadim a wajen da sauri yakarasa inda yaran suke amma sai yarasa yanda saiyin dasu dan cibiyan su ba ayanke take ba baisan yazaiyi yadauke suba sai wusilni ya suke a kan tyles yace" mata yazan musu sai ita Fandau dince tayinkura ta tashi zaune ta matsa kusa dasu tayi Bismillah ta daga dayan ta dorawa cinyan Nabil dayan ma tasake daurashi daya gefen jinyan nasa taso ta dauki dayan amma take ganin idan tayin nesa dasu zasu iya jin ciwo dan duk ajikin mabiyi daya cibiryar su yake
Ta kalli Nabil tace "kamusu adua mana."
Yace"bari namusu kiran sallah ko."
Fandau sai kallon yaran da suke cikin jinin take yaran shuwa sak ashuwan ma dama su Nabil nasu kyun daban ne'

Dagudu Hadim ta shigo hannun ta dauke da almakashi da zare dama iyasu ne agidan dan ma aikatan gidan suna ban garen su wana tsakanin suma da katanga zasu shigode da zasafe suyin shara sukoma sai kuma masu abin idan suna son abu sumusu waya dan Hadim cikin ma, basosai ta kesa tsunman basai taji za ashigo,

Jikin ta harrawa yake ita tamanta da batun wani watan cikin bai cika ba murna kawai take tanason ya kawayenta da family s
Zasuji aceta haifi twins kuma duk maza farare
takara sa inda suke ta tazauna dabas ta kama dayan ta yanke masa cibiyan ta kulle tayankewa dayan ma
Tana daura almakashi daga Fandau har Nabil rintse idon su sukayi dan jisu ke kamar yaran zasuji ciwo
Awanan karon ma Nabil neyayiwa Fandau komai suna futowa sukaga ba Hadim ba jaririn
Itako Hadim awannan bata goga jini ajikin ta ba dan tasan ba megani
Amma tana kaiwa yaran part dinsu takira wata acikin ma aikatan tace" tazota haifu matar da godu tazo dayake bature ba hankali bata gawani alamun rashin haifuwa ba atattare da Hadim saima santin yaran da taketayin
Hadim tace tanazuwa tajire mata yaran part din Fandau tanufa yayin daidai dafitowan su
Tace" my star ALLAH de yasa baka wanke kayan ba?
Nabil baiko kalli inda takeba yaje yace"Fandau yayane mezaki ci
tace "kafara bani tea sai kafani abinci to yace" yayi hanyan kitchen ita kuma tadan jingina da fukar godon yanzu kam ba abinda takeji jinta take sakayau ta kalle Hadim da tayi hanyan bathroom tace "aunty."
Hadim tajuyo takalleta tace"yayane? Fandau tace "dama danaga yaran biyune shine nanemi alfarman ko zaku bar bin daya nima narike."
Kallon ta Hadim tayi ashake tace "ina miki wasane ko kindauka zan lalabaki irin yanda Nabil yakeyi har zaki dubi sabar idona kice mubaki danmu daya ko goma kika haifa alokaci daya bazamu iya baki koda hoton daya ba balle d'a
Naga kinaji dawani fallin rashin kunya sa anki daya yanzu zaki bar gidan nan dan yanzu zankira doc yamiki allura Sani zai zo jibi kuwuce

Zama yayi dashir yana bata tea din abaki kuma yasa ayin mada pepper chicken nama kala kala hadim tazo da kayan da fandau ta haifu acikin wani baho
Yadaga yakalle ta yace"ina zaki dawanan kayan kuma?
Murmushi tayi tace "part dinmu mana ai karin sheda ne awajen inna ZAINABU dan bar mata zanyi tawake da kan ta idan tazo."
Tabe baki Nabil yayi yajuya yaciga ba da abin da yakeyin
Ita kuma tafice sabar murna yau kishin ma tamanta dashi

Sai aka hada komai yaje yakarbo yabaje mata a gaban ta dahuwan saide kowanne idan ta taba saitaji lami hakan tasamu naman dawusu taci sosai sai da Hadim ta dameshi da kira akan yazo gashinan doctor Muktar da habiba dasu Amjad Da usman duk har sunkara so
Koda ya tashi zai fita Fandau rike masa hannu tayi tafara kuka sosai
Zama yayi "yace mata ya akayi ne?
Cikin kuka tace"shikenan idan kafita wata kila bazan sake ganin ka inacikin hankali naba ko?

Yace"saboda me?
Tace "yanzu tace min yanzu zata turo amin alluran jibi muwuce da Sani idan yazo gobe."

Wannan fadan tane kinga yau yayar babana zatazo yanzu haka saura awani kadan su sauka kuma idan tazo tare zamu wuce da ida ko wajen jibe amma sai tazo dinde kinga ba muda wani lokacin cewa za akira doctor ko
Ki kwantar da hankalin ki idan na kaisu zan dawo ko suna bazan tsaya ayin dani ba zan daukeki muwuce Saudia ai namiki alkawari dama idan mudawo tukun sai musan yanda za ayi shiru tayi
Shikuma yafita

Tun kafin yakarasa shiga yakejin shewan mutane maza da mata turawan da fakaken fata yana shigowa abokan sa duk sukayi kansa ban da doc Muktar da kollon inda yake baiyi ba gaisawa sukayi duk suka tayashi murna yana a gurguje ya tsaya suka gaisa yawuce bedroom kai tsaye toilet yawuce ya sakarwa kansa shower yana wankan yana tunanin mezai yiwa fandau arayuwa kai kome nabata banbiya taba'
Daya fito haka yasamu Zahran Amjad da habiba suna goge jikin yaran da man zainu Hadim an hakimce akan godo sai amsan waya take ba kakkautawa
Da dare tunkafin zaukan Inna Nabil da abokan sa da securities dinshi sukaje taran ta Nabil yana hangota da gudu yaje ya fada mata sai kuma yafashe da kuka abin yabawa kannen sa Kamal da Grema mamaki yau Nabil da kuka meya sameshi Inna tadan zamoshi tasake kallon fukansa

tace" Modu lfy usman ne yayi saurin cewa Inna lfy lau sai alkairi akwai albishir sai Munje gida tukun
Haka suka karasa gidan
Inna direct inda su Hadim suke akayin da ita tana shiga habiba tameka mata jariri Inna tace"meye dan waye
habiba tace"inna kibude kigani mana Inna tabude tace"aiwanan Modu ne jaririn sa karde kucemin Halima ta haifu dasauri zahra ta meka mata dayan ma idon Inna kamar yafado take kallon yara takasa cewa komai kawai sai Halima Halima take kira Hadim ta sunkurar da kai wai ita irin kunyan nan
Inna ta Kalli Nabil tace" modu dole kayi kuka sai itama kawai ta fashe da kukan ta zauna kujera tahada yaran tana daga hannun tana godewa Allah tace" kubani abukar a waya nagaya masa."

Dariya sukayi sukace ai kowa yaji dama kune dakuke hanya bakuji ba sai dare sosai kowa yawatse ina tana shiga toilet tace karo da kayan jini a baho tace"aikin banza duk wanan taron kawayen naki ko kayan jinin ba asamu mai wankewa ba yau naji rashin hankalin irinna afuno yo ko hannu zaka sa awanke ai kawanke balle dagawa ka jefawa injin yawanke haka tazuba kayan a engine tas tagama tukun ta fito tana fadan da Hadim tace" basu shiga nan din bane basu gani ba nikuma dazun idan natashi sai indin gajin jiri shine nabari namanta."
Inna tace"dama yaushe zaki iya shiyasa fa dawatan haifuwan yakama nace bazan zauna ba zanzo kuke cewa wani karna zo
Shiko Nabil daga rakiyan abokai dakin Fandau yafada amma Baccci take yasameta dakani nagaji yane dakuma ramukon Baccci dan shi bcc inkaci bashin sa sai kabiya tsayawa yayin yazuba mata ido kunburin na fuskan ta yananan ajiyan zuciya ya sauke afili yace"yar albarka kenan yafito
Yayi saman karshi inda su Kamal suke suma suna shirin kwanciya yasamesu dan haka suna kara gaisawa yafita
Daya dakin na gefen su har ya kwanta kuma ya tashin ya canja security yayi part din Fandau har yanzu Baccci take dan haka yakwata agefenta yarungumo ta
Da asuba yatashi yayi alwala yafita masallacin gefen gidan sa wanda su basufi 4 suke sallahn asuba saboda karancin musulmai a wajen hakan ma 2 sai sunyin tafiya sosai amma idan na ranane akwai wanda suke zuwa awani anguwan suyin jam i yau de yasan su Kamal sunzu
Tare ko suka fita

Da daren yayi Hadim saida tarena kanta dan Fujjirat kuka saita sha nono idan aka bada madara bata so gaba ruwan nonon twins sunzuge idan Inna tace''hakan ma bata hadim harda kukan ta dan wani irin ja fujjirat take wai zata zuko ruwa ana cikin haka sai dayan yatashi shima kukan neman abincin yake ga doc Muktar agaban Inna yace kada a kuskura abawa jaririn nan madara kowane irine idan ba nono ba har zuwa wata 6 sannan adaura su kan madaran da yadace tasan idan tace zata basu madara Inna bazata bari ba daya nonon Inna tafita tasa jaririn aiko da karfi yaja saida tasaki kara inna tace" ai dama yanzu sai kin daure dama tsosan namiji yafi zafi kekuma naga alama kinada tsoron tsosa Hadim cikin yarfa hannu tace"inna to ayaye fujjirat mana."
Inna tace" a a bayan zuba sai tacika shekara tukun kafin nan adage da koya mata cin abinci amma yanzu lokaci daya idan akacire ta zata sha wahala ana haka dayan ma yatashi shima da kuka Hadim tace"wayyyo nashiga ukku
Inna tace" karki damu nazo da garin kunun kanwa zan miki kisha yana gudano daruwan nono haka Hadim suka kwana ana kwantar da daya daya zai tashi bakin nonon ta yayi jajajir kamar ataba jini yafita sai faman gyangyadi take azaune ai koya nonon yazame abakin su zasu sawani uban kuka har asuba Inna ta tashi tayin sallah ita kuma Hadim Allah yasota awanan karon tana rashin sallah sai abin yazo mata adaidai har pants dinta tacire ta jefar a toilet dan Inna tasake gaskanta ta haka inna da ta shiga alwala tagani tadauka tawanke tana cewa Allah sarki ai wanan jaraban tsosan yaran ma zaisa ta taman ta garashin bacci
Hadim tana zaune ido yamata hulu hulu kowa yaganta sai yatausaya mata ba medauka ba ita ta haifu ba dan yanda tayin kaya kayan Nabil ma daya shigo saida yayi mugun tausaya mata daya tambayeta meyasame ta tafashe da kuka tace "kai bakaje kana Baccin kaba nina kasa yara sai kuka suke min sorry dama reno akwai wahala Allah zai baki lada

Fandau tana kulada jikinta yanda yakamata dan tanada wayo sosai ruwan zafi sosai take shiga kamar nawancen karan amma awancen nafari tafi jin zafi kodan wannan din bawani girmane dayaran ba
Washe garima haka Hadim tasha azaba har yafi najiya itan kaganta har tafara rama sosai
Aranan sukayin shirin tafiya dan yan gida sun matsu suga wanan twins dan wasu ma harcewa suke zasuzo shine Inna tace to atafi dama ita tace ta gaji saita huta


Nabil da zasu tafi yana ta kallon saman fandau amma bai shiga ba yasan idan yashiga zata masa kuka jiya de yabata waya yace "zaina kiranta dashi amma kafin yabata saidaya settings din wayan number sane kadaya zai shiga


A meduguri fadin murnan da family din nan sukayin bata lokacine misaltashi kowa yagani yace kamar kara katsaga da ubansu Iya ko kishiyar ummi haka tace har zafin irin na Nabil ne dan yanda suke wusulniya shima haka yayi yasha faduwa amannun mutane idan yabank'are shiyasa kakar sa tasamasa shitta
Kwana 3 Nabil yace zainafi Hadim tace "haba katsaya mana suna jibi ne yace "tafiyan nefa yakama dole sai naje" wane abune da bazai yuwu kayishi online ba kace dole sai kaje ko uzurin can din yafi kanunawa Duniya murnar kyutan da ALLAH yamaka."

Ai kyutan da ALLAH yamin basai nanunawa Duniya ba wanan tsakanina dashine dan bawani ne yasa yabani ba nema bani nasa yabani ba,
Ana miki maganan meeting ne gameda companyn mu kina wani zance
"Amma ai general manager yana nan basufiye neman kaba."
"Waine meyasa kikafiye son jan zancene bayan hakan bazai sana fasa ba."
" zuba masa idon Hadim tayi meyake damun Nabil ne yanzu badama tayi masa kyara ko shawara bazai dauka ba wanda da kome tace daidaine awajen sa nunfasawa tayi tace tom "amma da Sani zakutafi ko?

"yayi me?
"yatawo dawanan yarinyar munyin da doctor agadys ta samo alluran sai kusame ta kawai amata yazo da ita ."
"A a Sani nabashi aikin company nan yakusa kammaluwa amma naga anfara mun wasa da al amuran shine nacirin ahannun Sandan da Bunu nabawa Grema da Sani jiya naje har an sa suna sunan yayi fujjirat Muhammad akasa baro baro
"amma kai kace susa natan ko?
"Yees ninace."
Hadim batasan dalili ba kawai sai taji ba dadi ai kwara yabari asunan sa nada dayake sawa *shidmas*
Kasa hakuri tayin tace kawai sai kasa sunanta bayan da sunan ka kake amfa ni dashi kumama ga maza nan sai asa na macce bayan na gaba ma bakasan abinda zamu samu ba ni kacireni sawun mata masu haifuwa ne."

Saida yakare mata kallo yace "baki ji ance ko dukane karbi nafari ba ai duk wani da dazan samu bayan uwata yake dan hakama jiya nasiyi file zan gina mata company nata na kanta akudinta da kungiya ta bata dan jiya ankawo min korafin duk girman meduguri bamuda company man abinci atake na bada umarnin memo inda yadace yayi kuma muje dan har ansiyi filin yanzu za afara aikin( *Fujjirat groundnut oil* )
Ai Hadim ido ta zaro dole ta batar da Fandau karma watarana tane mi tada mata hankalidole tayin abinda yaran nan zasu zama permanent
Awajen ta
Tanacikin wannan tunanin sanda tajin fujjirat tana tamata kwaranci wai tana mata bye kafin tabude baki har Nabil yafita parlor gagida acike ba daman magana ga tanason taji towane shawara yayanke akan yariyar nan ita kam ayanzu tanaganin alluran mantau yayiwa Fandau kadan ga ita bata san bin malamai ba yazatayi tana jitana gani Nabil yayi sallama dasu ummi yafita,

Yara sunci sunan bilal da kuma Habubakar baban nabil dan haka suna kiran su bilal da maaruf suma ansha shagalin suna

*YAU FANDAU A KASAN SAUDIA*

Amma ita kira take ita bata gane ba saita ganta ak'aba
Nabil yace"a a sai kin samu tsarki dan kiji dadin ibadan ki muzauna a Riyadh kawai kafin kisamu tsarki
Ai ko ko awanan zaman Nabil yana rage zafi da Fandau ga yana kula da magugun ta yakar bomata awajen mama Kafin yabar garin
Ba inda yake fita kullum suna makale da juna koda zaije gaida sarkin Saudiya zuwan bazata yayi musu saboda yan jarida shikuma yanason zuwa da Fandau tare sukaje Fandau de jinta take kamar aduniyar mafarki bai san dalili ba idan abokan sa na larabawa suka zo aidashi faya shayin nuna fandau amasayin matar sa sukuma basa ganewa tunda tana cikin shijab d nikaf wani wani company yakaita na gyaran jikin ta mata sun yiwa Fandau aiki sosai fadin yanza Fandau takoma bata lokacine sosai sunfito mata da colour chocolate dinta sunada kwana 10 a Riyadh Fandau ta samu tsarki lokacin tanada kwana 18 da haifuwa ai ranan Nabil bai hakura ba dayake dama amatse yake saida yahana ta saket
Washe gari dasafe bayan sungama break yaja kujeran sa gaban ta yace"Fatima
Saida Fandau taji wani yar ajikinta" dama kasan sunana?
Murmushi yayi yace"bansan sunanki ba zanmiki passport din fitawani kasan."
Ai sunan ki narike shitun sanda kika furta minshi Fatima amma anakiran ki Fandau kokin manta ranan acikin shid hotel lokacin kina me allon ki
Dariya tayi tace "yanzu ma aini me allo ce wazai ki karatun allo yafi zama akwakwalwa."
Yace "Fatima shigowan ki rayuwata kin shigomin da abubuwa dayawa cikin na alkairi kinbani farin ciki maran misaltuwa arayuwa wanda bawani nunfashina dazai wuce batare da yawuce da tunanin kiba kowane irin bacin rai yasamemi ke nake sawa arai naji kin yayemin
saide wani babban matsala idan natuna rabuwa zamuyin dan koyau Hadim tasa kafar ta cikin London zaman ki yakare agidana wanda nikuma shine babban tashin hankalina."

Fandau tace" kana sona ne?
Zuba mata ido yayi yace "ai wani son baki bazai iya furtashi ba idanu da ganganjiki kawai kenunawa."
Tace" kenan baka sona ko?
Batarai yayi yace" karki kara tambaya na batun so
Yanzu abinda yake gaban muyafishi mushin manci
Kuka tasa tace ai dama nasani bazaka taba sonaba shine Sani yace" wai zakasoni
"audama munafircin da kuke kulawa kenan keda Sanin ko
Tace" shikenan za amin alluran ko?
Yace"bar wannan nifa mafita nake nema kin kasa nusuwa kigani nufina
Yanzu me mafita bazan iya rabuwa dake ba sannan bazan iya kai kaina gaban malam amatsayin wada ya dauke masa yar ba dama badan malam bane baban ki dasai nace zain iya yin hakan amma

Please Login or Register in order to submit comment