Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ransa ya baci zai iyayin fin hakama dan haka tace "tashi katafi kafin ka rufe muda duka."

Cikin kuka Maman Hadim tace ni yaje ya karbo min jikata ya karbota kawai."

Har zai fita Ummi tace "kaje ka karbo Fujjirat."

Juyowa yayi ya kalli mama yace jikar ki ya wuce na jikin yarki idan ta sauka idan macce ta haifa inason asa mata Fatima idan kuma Namiji ne Abba inusa amma fa Fatiman da na fada kar ki dauka sunan kine tunda kema Fatime sunaki."

Girgiza kai Ummi tayi tace "bance kafita ba."

Yafice yana cewa danme baza ta barni da masifar da yarta ta jamin ba sai tazo tana min masifa
Wllh in Hadim batayi furcin ba to wllh Fatima ta baiyana kafin haifuwar ta kai ko ta baiyana inde bata cikin haiyacen ta sai tayi zaman gidan yari baki koyawa yarki yand....... Ummi ce ta katse mishi maganan da jifansa dawani cup na glass sannan ya karasa ficewa "Yaya dan ALLAH kiyi hakuri ke kanki sheda ce akan yanda halin Nabil yake tun yana yaro idan ransa yana bace ba a masa magana bake ba koni idan na matsa wllh abin ba zaiyi kyauba."
"hajara ke sai ya miki ki kyale shi amma banda ni. A zaburi Hjy Fatime ta mike har da gudun ta tafita wajen a daidai inda zai shiga parlour Iya ta same shi ta baya ta fincikoshi "kazo ka gaya min matsayin y'ata awajen ka kuma ko a kotu sai na karbi dukka jikokina."

A hankali Nabil yasa hannu ya kwace a hannu ta idon sa fes cikin nata sai kace a gaban abokin sa yake yace "matsayin yarki bata dawani matsayi a wajena sai dai idan ragowan sakinta kikeso zan iya bin umarnin ki a masayin ki na uwa a gareni in baki sakinta.

"Sai kuma batun yara kema kince jikoki, jika ko ba d'a bane ki bari me yaran tace a bata da bakin ta" Iya ce ta fito tana "Subahanalla Nabil ya haka" Ummi mari tafara zu bawa Nabil shiko Nabil nade hannunsa yayi a kirjin sa yana jin yanda Ummi take zuba masa marin, kanne sa dukka suka fito sai kuka suke dakyar Iya ta ja Ummi itako Mama zubewa tayi tana rinjin kuka
Nabil ficewa yayi ya fada mota driver yaja motocin security dinshi suka rufa masa baya suka fita cewa yayi airport zasuje dan shi gani yake kamar ABUJA ne zai bashi Fatin sa.

*GIDAN DR MUKTAR*
"Aunty yanzu jibin zamu tafi kenan?
"habiba tace insha ALLAH kirki ta Ghana zamu tashi saboda ke Dr ya sara tafiyan ta can dan a wanan kasan bazai ykwu mu tashi dake ba yanzu haka Ghanan ma a mota zamu tafi saboda Shiddams ya tsanata bincike."

"Aunty yanzu haka zankoma banje naga su mama ba."
"Toni Fandau ya zanyi ne nayi nayi dashi yaki, nace idan munje dake kisa nikaf har mufito a kallah de kinga mama zakiji dadi, amma sai cewa yayi ai baki damu da ita ba da baki barta ba, saide idan kezaki gaya masa kiji."

Fandau tace"ni kema kinsan ban isa ba jiya haka yace wa maimu me aiki kar ta karayin komai a gidan nan nice sabowar me aiki ni zanyi."

Dariya Habiba tayi tace"wai dan kikoyi hankali ne yace ko amma da nake tambayar sa yace yana sone kina dan mosa jikin ki kinga cikin ki ya shiga wata 6 dan kisamu sauki wajen nakuda."

Ko da zasu tafi kaduna barin Fandau sukayi da meimu suka tafi.

Shiko Nabil abubuwa ya kacabe masa ga yan kungiya sun matsa masa wata 2 bashi har sauran kun giyoyin sun fara kawo farmaki ana ta yadawa wai Shiddams yabar Chelsea fans dinsa da sauran mutane sun damesa a media ga zaryar hospital yake ma dan ba shida cikakkiyar lafiya kullum ciwon kai dana kirji yake fama dashi, kowane dr idan ya duba shi sai yace yasa wani abu ne a ransa wanda yafi karfin zuciyar sa idan bai cireba to yana barazana ga rayuwar sa aiko yan club din su sunajin haka suka zo tafiya dashi ayi jinyar sa acan yace a'a abu har ya kaishi ga kwanciya sosai.

*HADIM*

Ko makiyinta ya ganta cikin wannan hali zai tausaya mata "Mama yanzu Nabil din bazai zoba bayan ance yana garinnan Ummi yasani a blacklist bana samun sa mama kibari naje London din mana na same sa tunda kince yakoma."
Mama cewa Hadim tayi Nabil ya koma dan ta kwantar mata da hankali amma kullum zancen ta Nabil da kuma a karbo mata Fuj yanzu dai Ummi ta sa ankawo Fuj sai Nabil da take ta ambata wanda acikin asbitin daya ma suke akwance bata sani ba dan ita ma sosai take akwance kullum Dr suna cikin yimata nasiyar ta kwantar da hankalin ta saboda kwata kwata BP dinta baya sauka zai iya janyo matsala idan watannin haifuwan ta yayi idan zamu mata aiki dan.......
"aiki kuma?
inji Ummi da mama
Dr Hafeez yace ba na rubuta muku bayanan acikin katin da na baku ba amma kubini office na karamu ku bayani."

Ummi da Maman Hadim zaune gaban Dr Hafeez
Yace " yaka mata ku kula da halin da yariyar nan take ciki, yanayin cikin ya kamata a kula da ita sosai tunda ba haifuwa zata iyayi da kanta ba aiki za amata dan mun duba mugani kugunta bazata iya haifuwa ba sai de aciro to alluran da zamu mata idan lokacin yayi ba ayiwa me hawan jini dan zai iya barazana ga rayuwar ta ita kuma BP mai makon ya sauka kullum kara hawa yake....

Mama kaseshi tayi da cewa aikin banza rashin sanin aikin kune na kasannan yaza ace bazata iya haifuwa ba itada ta haifi yan biyu ma lafiya haifuwa na 3 ace kugunta bazai iya haifuwa ba."
Dr yace" hjy a kugun akwai wani kashi a kugun kowani mutum mace ko namiji to dana maza ta na bata akwai ban banci na maza babu tsagu na mata da tsagu yanda idan mace tazo haifuwa wannan kashin shi zai bude shine zakiji nishi yazowa mace a daidai budewan tsagun na kashin bazai koma yarufe ba harsai d'a ya fado zai rufe, to ita Halima wanan kashin ba tsagu anata dan haka zan iya ja da kowane likita akan bazata iya haifuwa fa."
Mama tsabar haushima kin magana tayi Ummi "tace Dr dena fada duk haifuwan ta da kanta take haifan su Dr Hafeez yace"hjy kina nufin wannan ta taba haifuwa?

Ummi tace "Wanne irin tambaya ne wanan Dr muna cemaka haihuwa na uku zatayi na 2 ma yan 2 ta haifa yariyar da ka gani a gefin ta tana bacce itace yarta ta fari"

Dr Hafeez yace "Hjy ni a bincike na wanan mahaifan bai taba daukan ciki ba sai wannan asali ma shikan sa mahaifan cike yake da matsaloli dayawa da farko yana iy.......
"dakata inji Ummi dan itama yafara bata haushi itako Mama fuuu ta fice Ummi ma mara mata baya tayi.

Dr yace "niko idan matar na ta haifu da kanta daga ranan zan bar ai kina dan bai min amfani ba."

Sude basu saya bashi amsa ba suka fice.

Suna fita wajen dakin da aka kwantar da Nabil sukace karo da su Jidda sai runjin kuka suke suna ambaton Ya Shid kar kamana haka wllh kaine gatanmu shi kawai suke mai maitawa Ummi ji tayi bata iya daga kafanta dan dama tabar Nabil cikin wani hali yana aman jini dasauri wani Dr yafito yace"wacece Ummi? Da sauri Kamal ya kamo hannun ta yace" gatanan ya farfado ne? ni nasan dama suma yayi ai
Nabil yana gani Ummi yayi wa Dr alaman ya cire masa roban jawo nufashin da yake hancin sa dan baya iya daga hannun sa Ummi tana karanta duk addu'an da yazo bakin ta takara sa inda take kamo hannun sa tayi dakyar ya bude bakin yace "ba'a ganta ba Ummi an nemeta an rasata bansan hanyan da zanbi na samota ba Hadim ta hallakamin ita naso ALLAH ya barni naga haifuwan Hadim na daukarwa Fatima fansa bakin cikina Ummi tasha cewa nace ina son ta amma ban taba furta mata ba ina ma zan ganta ko a mafarki da nace inason ta inason ta ba a dadi, Ummi zan barmiki wasiya idan ta baiyana kice ina sonta har na rasa raina akanta karki damu da yanda take na rashin hankalin ta kigaya mata nina sani ni da ita zuciyar mu ahade yake Ummi me na yiwa Hadim ta lalata rayuwa ta bayan ni namata duk yanda take so ita fatasa na auri yariyar dan.................



*Tofa Nabil Allah ya baka lfy amma kar ka tona asiri*😭😭😭

*Ya Hadim zasu kare da Dr Hafeez me tonan silili mai gani har hanji da gaske ne kashin kugunta irin na maza ne wato ba zai iya budewa ba idan tazo haifuwa wane irin matsaloline a mahaifarta*

*Ya Aisa maman Fandau taji da taji yanda rayuwa ya juya da yarta*


*B JATTKO*
hhh[8:27PM, 2/21/2018] πŸ˜„πŸ˜„SMILERπŸ˜„πŸ˜ƒπŸ˜€πŸ˜€: *DAMATA*





*NA*





*BATUL ADAM JATTKO*

*Phareedah umar sokon ki ya iso gareni kuma na gdy da kauna ki zanduba bukatun ku na insamu ina muku typing koda (2days ) ne*

*Haeeza Murtal*
Banman tadake ba
Dakeda duk kan masoyan damata

*ME ZOGALE*
*kema muna mugun tare*


*Gaskiya kina mutukar godiya agareku masoya ina mamakin yanda kuke nuna soyyyyan ga* ```DAMATA```
*Ina baku hakuri wanda suka min magana ban samu na amsa musu ba wllh abubuwa ne suka min yawa amma ina dare da masoyana aduk inda kuke karfin guiwan ku da addua anku yake kara karfafanin guiwa musamman JATTKO GROUP kuna sani nishadi wllh 🀣🀣🀣🀣ina tare daku*


( editing mzz daddy)


*40*


*K*asa k'arasawa yayi dan yanda dan tumfashin da yake ja yagagare shi yaja idonuwan sa suka kakkafe atake da sauri Dr yabayar masa oxygen ahankali nunfashin yafara sauka

Ummi kuka take sosai Kamal ya kamata yafita da ita yana kwantar mata da hankali

Wani sadeden gaye nagani shida familyn disa badan karnayi karyaba zan iya cewa wane Nabil akomai da sauri saurin yake takawa haryabar ss dinshi da family shi su Jidda suka meke kai Ya BilAL BilAL Maina kangeya kenan d'aga Ahj Maina kange millions wanda ya dauki dauyin karatun Nabil shine yake takawa har gaban su Ummi ya durkusa ya gaida su Kamal cikin girmamawa yamasa jagora har gaban gadonda Nabil yake kwance Bilal yasa abokin nasa agaba yana mamakin wai Nabil da mata suke tsoron tunkara yakoma haka akan macce

Yakalli Kamal yace kamal "kiramin Dr din ."
kamal yafita suka shigo da Dr tare
Bilal yace"Dr kuhada mana kwararun doctor wanda zasu ina control din matsalan sa acikin jiri har kukara sa England."

Dr yace ok sir yaushene tafiyan? yace "yanzu."

Kamal dadi yaji dan bayanda ba ayi da Nabil afita da shi amma yace shibawan da ya isa yasa shibarin Nigeria dan Fatin sa tanaciki sunrasa wacece Wata Fatin dansu har yanzu ba agaya musuba yanzu koyasan bai isa hana BilAL fita dashi ba

dasauri doc yafita

daidai da shigowan malam da Baban Nabil da Bunu dan gidan Malam
Addua malam yamasa yace Bunu da Baba su daga shi abashi rubutun Baba
Yace
"akkaramakalha da anbar rubutun nan tunda kace na dan ganane kar kuma wata rana matar sa ta baiyana yakita azo ana nadama."

Murmushi Malam yayi yace" Abukar abashi."

Bunu da kamal suka daga shi kuka Nabil yasa daker yabude bakin sa yace"Malam kar abani abinda zan manta Matata."

Matsawa Malam yayi inda yake yakama hannun sa yace"baza ka manta ta ba wannan na samun saukine acikin cunci ko bakaso Fatin naka ta sameka da lafiya ne?
" ina somana Malam
Yaushe zanganta?
"kakusa ganinta kasha rubutun komai zai zomaka da sauki."
ai dasauri
Yace"idan nasha za aganta?
Malam yace "insha ALLAH."

Ai da sauri ya daga kansa duk da bazai iya tashiba alaman abashi Bunu ne yakara masa roban abaki yadan sha sosai sai da yaji cikin sa yana murdawa yabari shiko kashi zai iya ci inde za asamu Fatin sa
Kamal ya kwantar masa kan a filo
Bilal ya durkusa ya gaida su Baba yace "Malam waifa BilAL soyake ya fitar da abokin nashi."
"ai ba lefi saide aikin da zan masa na kwana 3 addua idan angama sai su tafi."

Cikin kwantar da murya BilAL yace"gafurta sai atafi da kai ai inde badamuwa."

Malam yace "badamuwa zanso hakan saide gobe akwai meeting namu na hakimai wanda yazama dole na halarci taron da safene da yanma sai muwuce."
Baba yace "da yau da goben duk dayane ai."

Haka washe gari aka tarkata Nabil da har yafara samun sauki dallin aduar da ake masa aka fita da shi yan club din Chelsea su sunji dadin hakan su suka dauki nauyin komai

Maman Fandau danne watayi agaban su Malam amma hankalin ta bakaramin tashi yayi ba harya fi na sanda Fandau ta tafi tashi yanzu shikenan anmata alluran da ta banta da komai arayuwan ta bazan iya yafewa matar da ta dauketa ta kaita saudia dan ta nema mata kudiba ALLAH sarki Fatima na da taji labarin zan warke shine aka yaudare ta da dashi dama nasan yanda kike sona da kishina komai zaki iyayi akaina saide yarinta daya hana baki gane illar kina macce me karancin shikaru barin ki gida da hatsarine ba bakiyin tunani ba gashi har kin fada halinda kwara makantata so dubu amma nasan Halima bata san ke y'ata bane da bata gwada wanan zalincin akanki ba dan kina kishiyar ta
Koda ta gayawa Bagana haka bagana taci kukanta tace "mama wllh dawannan labari kwara ace ta mutu."

Mama tace "ina zaki hada dama ai mutuwa kowa zaman jiranta yake."

"mama ALLAH ya isa tsakanin muda Hadim."

Mama tace "kai dena fadan haka kiyafe mata dan nasan ba lefinta bane lefin mesunan Malam ne daya gaya mata yarmu ci danasan halin kirkin Halima da bazata mata ba."

"mama wllh da lefinta ai kishi ba hauka bane koma yar wacece yaka mata tayi hakane jiyan nan fa naje naduba ta baga yada taba ni tausayin ba bata da lafiya abin dausayi tunda nazo nakecewa abban Tajjudeen anty Hadim ta zama abin tausayi ashe ita ta jefa min yar uwa cikin wani hali ban sani ba sake fashiwa tayi da kuka tana cewa YaFandau ina zanganki."

Dakyar mama ta lallasheta
tace" keda kike hakin haifuwa yau ko gobe bai kamata kijefa kanki cikin damuwa ba shima Nabil din yana iya kokarin sa wajen nemanta
Mama ta dauki Tajuddin tace "dashi zan tafi dama an dauke Hajara."

Bagana tace "wllh Mama tunda muguwace kar ki kara rike mata yarinya."
Mama de har suka fito harabar gidan bata yiwa Bagana magana ba dan ita son Fujjirat ajinin ta yake har driver yaja suka fita suka bar Bagana da tisisin ciki

Nabil yasuki yafara samuwa yanzu har takawa yake da kafafuwan sa memakon da da kowanka yimasa ake yadena jin ciwon kirjin aman jini duk yadena sai kuma tunanin Fandau yananan dan duk baya ji kamar da
Malam da Baba har sun tafi sun barsu amma tunanin Fandau kam haryanzu yana fama dashi kullum yana makale da wayan sa yana ganin photon ta a status dinshi kam kullum kalaman soyayya yake daurawa instagram, tweeter dasaura media amma baya daura photon dan yasan yana kishin ta a status dinshi na whassapp kawai yake daurawa dan yasan bawan da zai gani dai wanda yayi saving dinshi shima da wata ta dauka da shijab a saudia yafi daurawa
Akullum Billah yana kwantar masa da hankali daza a sameta Dr MD da Habiba sunzo sunduba shi agidan bayan an sallame shi ko da suka zo saida Nabil yace "wai Habiba wanan yariyar haryanzu baki kara ganin mai kamarta ba wllh wanda nake sawa bincike duk basu san akin suba."

Habiba tace "kai YaShid kadamu da yariyar nan dayawa fa wai meye masayin ta awajen kane?

Nufasawa yayi
Yace to yau zakuji basayinta awajen na yagaya musu kamar yanda yakayawa su Ummi amma yace "saide fa sunce nabar zance sai sanda tafito kawai sai ace dama ni aka daurawa kunga lifin ita yariyar na bin matar saudia ya bata sannan lefin Hadim yabata abin da yasana fada maka innaso tunkafin ta fito anemo mata maganin da zata koma kamar da shiya sa nake ta meman wanan yar iskan Dr Adegas din bana samunta
Inason tambayar ta wane irin allura ta mata
Dr yace "Ai yanda kafada bawani magani da za asamu alikitance wanda zai dawota tunani kunriga kuncici yariyar kawai."

*Yafadi haka fal da haushi Shid wani irin makar yacine akan abinda yanacewa yanzu kenan zai rushe masa komai tunda gashi har ya ganar da iyayen sa cewa Fandau matar sace*

Nabil kamar yaro haka yace "wllh ban cuceta ba nide Hadim ce kuma wllh jiran ta haifu nake ta gane kureanta."

Dr da Habiba dan haushi kasa magan sukayi yanzu shikenan Nabil yaci
Bulus kenan ko sallama Dr bai saya yiwa Nabil ya fece


*Gidan Dr*

"yanzu yaci nasara yara kuma dunzama na Hadim kenan waishi Shiddams dinnan wane irin mutum ne komai nasa cikin ruwan sanyi yake zuwa dubi yanda yake tsara mana zance kamar gaske da irin wanan kalaman ya yaudari yariyarn fa kuma haryanzu ta na mugun sonsa ayanda da karance ta." cewar Habiba

Dr yace "ai dama nace miki shiddams shegene zai iya rusa kowane irin shiri akan abinda yake so,
Yayi kokarin ya fashim tar dasu yanda nasa lefin basai fito ba ko toni kuma na yi alkawarin insha ALLAH yarushe min *DAMATA* *DAYA* acikin ukkun amma biyun nima sai na cinasara sai ya karyata kansa da kansa ."

"haba Abban Nol yazaka rike matar aure ka fito da ita kawai ayita da kare wllh iyaye zasu yarda da ita abata yaran da aware karyar da yayi musamman idan bayanan da Dr Hafeez ya maka in Gaskiya ne kaga kowa zai yarda da da yaran tane su zauna suyin zaman auren su me amfani cigaba da rike matar wani kai kasan bazaka iya karawa da Shddams ba wllh."

"Bayanan Dr Gaskiya ne naduba sosa,
amma ai su Ummi basu yarda ba Dr yabari ne sai tazo haifuwa su gani maganan garawa da Shid kuma kowa yana da dama fa sai de inbai iya amfani dashiba zan baki mamakin cikin *DAMATA*."

Fandau kam ba asata makaranta ba amma ta gama wayewa duk inda za akira wayeyiya za asoko da ita yanzu kam ta iya turanci sosai ba abinda Habiba bata koya mata ba dan yanzu haka zaki iya sata sawun matakin yan secondary dan duk abinda habiba takoya mata dauka take idon ta yabude sosai

Cikin ta yacika wata 9 cif Aunty Habiba ta tafi dauko yara a makaran ta wayan habiban ne ahannun tana dan danne danen ta de sai ta shiga whassapp dinta pc din Hadim ta shiga amma tajima bata hauba pic din Fujjirat ne a dp tarike ball tana dariya tayi kyu

Ta tuce na Nabil shima Fuj ne saide nashi tana cikin taron jamaa duk yan mata ne kyuwawa wasu farare wasu bakake Fuj tana tsakinyan su sai da ta jawo taga ashe abinda suka sa agaba cake ne ansa happy Birthday to Hajara
2years
Amma me tana shiga status dinshi ta cikaro da nata pic din wanda tayi a harani akasan photon anrubuda
_yaushe zan ganki matata ido da gangan jikin suna bukatan ki baki yana son turta miki kalman da kika dade kina son ji_

Kifa kanta tayi a hannun kujera kenan Nabil bai manta da ita ba yana son ganinta fa yace da sauri da daga idon ta ta Kalli tafkeken photon dayake manne jikin bango tace nima ina sonka bansan yanda zanyi bane to idan kaganni me zaka gayanin min akwai wani kallma ta yarage baka gayamin ba kokana nufin zaka furtanin karman```SO```ne dan shi nadade ina nema awajen ka

goge hawayen nata tayi ta shiga ta rubutu masa _SLM_ amma sai da yajima yaturo amsan

_Waalaikumus salam Mamana ys Nol Nol,_

dama Nol sunan Nabil ne dashi shiyasa Nabil yake cewa Habiban mamana

Rasame zatace tayi dan hannuta sai rawa yaje cande ta daure ta mayar masa da reply

_lfy abu Fuj yasu Fuj ya kawata?_

_yace Fuj de lafiya amma jiya ta cika shekara 2 su Jidda sun mata happy shine suka turomin pic dinta kawar ki kam ban sani ba kunfi kusa_
_yazakace munfi kusa kai da matar_
Cewa yayi
_uummmmm_
Daganan bai sake cewa komai ba

Itama shiru tayi tana so tace yayi mata voice taji muryasa ta tuno ashe wayar matan mutane ne

Jira take yace wani abu amma taji shiru har shigowan yaran da hayani yanzu tayi saurin tayi delete din chet din

Hadim iya wahala tana sha har yanzu a asbitin renon cikin take tayi kaya kaya dama gatada uban tinbi ya hadu da cikin wata 7 wani irin ciwo mararta yake mata wanda duk doctor da ya auna sai yace matsala ta na cikin ma haifa
Mamar tace ni Hadim nagaji da yanda kowane likita sai yace da matsala acikin mahaifar ki bayan da kalau kike haifuwar ki kode wajen zamu fita."

Hadim dama dukda ciwon da yake damunta tana son ganin Nabil tace "eh mama muje kawai nake ga kamar sun fisu sanin aikinsu yanzu haka bawani matsala sai nasu na rashin kwarewa."

Nabil yayi shiru yana tunanin chat dinsu da Habiba yaji dadin sunan da takirashi dashi wato *Abu Fuj* dan shi Fandau dinsa cekawai take kiransa dawanan sunan ****

Yau Fandau ta tashe da nakuda Habiba takira Dr yana hospital din ta gaya asa nurse kawai yaturo da kayan kinsu yace sugaya masa duk abinda yabiyo baya Fandau taji dadin wanan haifuwar dan sun temaka mata sosai sanda kan d'a yafaso
Awanan karan ma namiji ta haifa mekama dasu maaruf sak yana duk wani kulawa itada jaririn ta sun samu kunsan de gidan doctor
Fandau tayi kyu tayi shar da ita dan tasan idan tana bawa Akkaram nono jitake kamar ta kaida shi cikin ta dan so sunan Malam Dauda Dr ya sawa yaron dan isa shine yace kar akira masa uba dawani suna sai Akkaram ko dawud to de Fandau tace gwara Akkaram din

Fandau tana son yaran har ta kasa ban bance wanda tafiso shida Fujjirat dan ita tana ganin twins kamar ba yaran taba takeji amma Fujjirat bata san iya sonda takewa yarinyar ba kullum pic dinta ne a fukan wayanta
***
Ranan da yakama suna duk da bakowa aka gayawa ba Fandau tayi makeup tayi kyu
Habiba tana shigo ta fara mata kirari
"kai kai cankaji wanan hawan girman fa yayi gimbiya y'aga Zannan barno hakimin Gargar mulki da sarauta bayeku a barno koda karfin rawani zamu karbo yaran mu kinyi kyu wanan idan Nabil yakanki ko zai ganeki?
Gaki dama da iya kasai ta wllh tun lokacin da nake zuwa gidan ku duk baki ta bamin magan ba nasan ke jinin sarautane ne kinfi sauran yan uwanki iya tsate gida

Murmushi tayi tace "Aunty foundation din kara hanci tasamin wllh duk na canza kama gawani gira data samin a ido Aunty ba kyu fa canza halita wanan abinda ta samin acikin ido ba abin da zaiyiwa idona ina tsoro."
"eh bawani abu kwaliya nefa kuma ba sallah zakiyi ba Abban Nol yace amiki zai turaro wani wanda ya kware a daukon photo da editing yamiki pic dan yayi amfani dawani *DAMAR* kinga ma kayan ma caccanzawa zakiyi."

Itade dan Dr ne bayanda zatayi amma da wannan kayan canza halittan bada itaba

Wani bature ne yamata photo wajen kala 10 harda wanda aka mata da English wears fadin kyun da tayi ta adin lokaci ne

Wahegari Habiba tace zata jen duba Hadim dan sun sauka ita da Ummi da Mamar ta asbitin dr suka sauka dan sun dauko Hadim agalabaice

"aunty da Fujjirat akazo?
" eh da ita man kinsan Hadim baza ta iya zama ba Fuj ba shiyasa nake tausayawa Hadim duk ranan da asirin zai tonu dan wllh abin tausayi ce inde za akwace Fuj da bata da lfyn nan fa a asbitin a bed daya suke kwanan ga shima uban ya

Please Login or Register in order to submit comment