Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna kallon ta sun kunyar da kai tayi kasa Habiba ce takula da Fandau bata fitoba ta zagayo ta bude ta jawo hannun ta
Tace "Aunty ina tsoro.
"tun agida nagaya miki karkiji tsoro tsoro me?
"Aunty haduwar muda Mama Aunty inajin kunyar ta kuma ina tsoron Baba Aunty kisa amedani gida bazan iya shiga ba.
Fisgota habiba tayi ta fito da kita "kinga aiko ke zajija hankalin jama a kanki wanda idan wucewa zakiyi dom dom bazasu ganeki ba kiyi adua kawai haka suka fara takawa har get na biyu wada anan baban parlour Zannah yake nan mutanen suke ta duruwa akofan ma saida ta tsaya tare da kyankyame hannun Habiba janta Habiba tayi ta shiga da ita

*wai wai koni*
*B Jattko saida nayi kamar zan sanbada da gudu ganin taron maza da mata awannan makeken d'akin taron*

Habiba ta ja hannun ta Fandau kanta ararufe har suka samu waje suka zauna wayanda suka zo tare ne kawai suka gane itace amma duk basu ga fuskanta ba
Bayan Malam Dauda ya bude taro da adua
Zannah yayi kyaran muryar yace "to Nabil gaka ga BilAL Maina da kakawomin karan matar ka tana wajen sa.
"eh Malam tana wajen sa
Malam ya Kalli BilAL yace" Bilali ya akayi haka ina kataba jin ana aure kan aure kuzaku fara kaida abokinka?
BilAL cikin nusuwar yafara magana "Gafarta agabana Nabil ya tsara muku yanda ya auri Fandau ba akasannan ba kuma tana da ciki aka zubar da cikin to meye hadita danawa wanda gayanda akayi auren ya bawa Malam labarin auren Fandau na gaskiya wanda Malam Dauda ma yakara da cewa shine maya daura auren.
Zannah yace "to wandan abu da rikitarwa to inaga ba yarinya daya bace wacece tawa Fandau din aciki? Dasauri BilAL yace" tawa itace Fandau dinka dan yanzu haka neman aurenta nazo.
Malam yace "Masha ALLAH to kai Nabil kayi adua ALLAH ya baiya na maka taka Fandau din kaji ba ita bace
Nabil yace "itace Wllh itace.....
Baban sa yadaka masa tsawa yace "kama yarda mutane sha shawu ne irinka bayani da kamana da wanda BilAL yayi ba daya bane zaka kafe akan matar kace.
"Baba itace yazama dole nafadi gaskiya koda duk duniya za su tsinemin ne akan inaji ina gani arabani da matata
Ni newan da BilAL ya bada labari yanzu duk abinda na gaya muku wancen lokacin ba gaskiya bane shiryawa nayi dan na rufe nawa lefin ga Sani shine sheda na kuma shiya karbomin auren awajen Malam Dauda amma kuya femin.
Yana gama fadan haka ya fashi da kuka
Zannah kansa Afirgice yake kallon Nabil dan abin yabashi mamaki yajuya ya kalli Malam Dauda yace"Malam kasheda wanan Sani shiyaje da Fandau aka daura auren?
Malam Dauda yace "shine kuma ni dama Mutari yaga yamin nasani saide munbari ne kawai ya fadi kayansa kuma gashi ya fada.
Zannah yace "yanzu ina ita Fatiman Dr yanuna masa Fandau
Malam yace "ta matso kusa kanta asunkuye tafara ja dabaya dan tsoro Nabil ana nuna ta yameke a razane zaiyi inda take Baban sa yace "koma ka zauna.
Yakoma yana binta dawani irin kalllo yana so yaga fuskanta amma arufe Yana son ya gaskanta Fateeman sace meyasa wanan ranan tazomin da haka naci burin ahuwar mu dake zannuna miki matsayin ki agaban kowa amma Baba yahana.
Malam yace "Habiba matso da ita.
Haka Habiba tameke ta daga Fandau har gaban zannah hanunta yakama yace "tabbas wanan itace tawa Fatiman Fatima Muhammad Nabil shine mijinki?
Gyad'a kai Fandau tayi
shiru Malam yayi duk wanda yasan shi yasan ransa amutu kar mace yake da kuma mamaki da kunyar kunsan shikansa yayi karya wanda zai iya cewa shine karyar sa ta fari aduniya dawane ido zai kalli matansa da yaran sa dayamu su karya yayiwa Fandau Aure da bako yana daga kansa yaci karo da matan sa sunzuba masa ido har yaran sa maza manya rasa mezai ce yayi ya sunkuyar dakai cikin damuwa Baban Nabil ya fukanci haka yameke ya karasa wajen Zannah yazube guiwowunsa cikin tsananin bacin rai yafara magana
"kaicona kaicona Malam karene ni kamaye min gorbin uba asanda narasa nawa uban amma gashi yau nina haifi dan da yasaka b'acin rai wanda banta ba ganin sa acikin fuskanka ba atsawon rayuwata daka ina nema almarman ka zan yankewa Nabil hukunci agaban ka dan Allah kabani DAMATA na hukunta shi kar kace komai lefin sa babbane
Kai Nabil wandan auren naka na zanba cikin aminci kai tsaye bazance haramcecen aure bane amma ba abi yanda shari atace ba baka nemi kauren ta hanun waliyen ta ba bayan tana dashi koni waliyin auren Fandau ne amma ban sheda ba dan haka ba ka can canci zama da itaba tunda bakasan yanda ake neman aure ba shikan sa auren ka nafari kana England na dauki matar na gaimaka shiyasa baka san yanda ake neman aure ba ayanzu nake son karubutawa Fatima ta kardan sakin ta kai ba mijinta bane yarinya me daraja kamar ta ba matar ma karyaci maha inci irinka bane
Wanda hattta iyayen sa basu fi karfin ya musu karya ba yameke yaje ya ciro fefa acikin littafin Malam ya karasa inda Nabil yake ya meka masa tareda biro yace ina son karubutawa Fatima saki.

Girgiza kai Nabil ya shiga shi
"yace wllh da wanan hannun nawa bazan iya rubutu saki ga Fati ba.
"idan baka saketa amasayi na nawaliyin ta ba zaka saketa matsayayina nani ne uban ka bisa umarni idan baka sake taba kadena amsa sunan d'ana kuma ta take anan zan tsine maka.
"Baba kaji tausayina wllh mutuwa zanyi idan nasake rasata.
"ai idan da zaka mutun da yafi komai sauki da anrage iri dan gaba bansan irin yaudaran da za kuyiwa a wani wajen ba kuje kusake wannan zanban nakuba musamman yanzu ta matar taka take juya.
Nabil zaka saketa ko kazabi tsinuwa
Ni *Habubakar Ibrahim damasak* nat.......
"zan saketa kar ka tsine min Baba.
"to zaketa
Yakarba yabara rubutu duk awani karkace saboda hannun sada dayake mugun rawa

Afirgice Fandau ta bude fuskan ta ta fara magana cikin kuka da firgice

"Baba kar kasa yasakeni kar kamayarni karamar bazawara wllh inason mijina
Nabil da dakawa yayi yatsaya kalonta cikin kuka
Tsawa Baba yadaka masa yace kazabi...

Rubutun yafara amma fa wahaye duk yajika fefan sai yankewa yake yaru buta
_ni Muhammad Nabil nasaki matata Fatima Muhammad bisa umarni mahaifina amma batanin komai ba ALLAH kayafemin_

Yajefar da biron yakifa kansa a kujera
Baba ya dauka ya karanta afili
kowa tsaida yaji ba dadi
*dama haka saki yake yana da korjine wanda ko makiyin ka akayiwa sai kaji badadi*

itako Fandau jirine yafara ibanta Habiba tayi saurin zaunar da ita

Baban Nabil yace "kwantar da hankalin ki Fatima ki godewa ALLAH agobe ba yau ba zan daura miki aure tunda ba wani idda akanki dan da ciki kika fita tunda kika haifu baku haduba bakida wani iddan sa
Kai BilAL kanason Fatima?
BilAL yace "Eh Baba badan kar ayi aure marar tushe ba da anan zan aura maka ita amma kaje gobe kaso da waliyan ka.
"nagode Baba.

Afirgice Nabil yajiyo atsawace yace "
Wllh wllh duk wanda ya aurin matata yafara irga kansa cikin wanda zasu yi gado da makara aranan ga Fatima naga uban daya isa ya daura auren ta ina raye. Yasake kifa kansa yafara rusa kuka kamar yaru ba necewa shine Shiddams mutumin yafi SHEHU da gomna acikin garin meduguri adon mutane
Baban bai ceko maiba azagin da Nabil yayi dan yasan halin d'an nasa idan ransa yabaki zai iya bude baki yazageshi ma

Malam yayi Gyaran murya zai cewani abu Baba ya tashi yakara sa inda yake cikin kunne sa yarada masa wani abuda duk bacin randa Malam yake ciki saida yamurmusa
Daganan Malam yarufe da adua ya sallama kowa Akkam yanawajen Ummi har zasu fita

Malam Dauda yace" ina mesunsn nawa ita ko Fandau kuka take sosai Habiba tayi bangaren Mama da ita su BaGaji ansamu abin fada sai kira suke duniya abin tsoro abin magana irin wanan agidan Malam mama de shigewa tayi bata kulasu ba Hadim kam dama batazo ba
Baban Nabil shima bangaren Mama yashiga Fandau yaja gefe sunjima sannan yafito yatafi Fandau ta rungume Mama sai kuka suke har dare matan gidan suna shiga suna fita har zance yafara yaduwa gari itako Fandau burinta taga Bagana dayaran ta kawai

Shiko Nabil kinfita yayi agidan yasa Zannah agaba yana kuka har 10 dare shima Malam dannewa kawai yake amma jiyake kamar yayi kukan dan bai san hanyar da zaiyin ya gyara kuskure karyar da yayi ba dan bai zaci abin zai zoda hakaba amma ya danne nasa yake lellashin Nabil amma ina kamar kara masa suke sai zaje zaje yake ganin idan ya matsa shidin ma Nabil gaya masa magana zayi yasa Malam yafita wajen Abokin sa akaramin parlour sunfita sun barshi
Sai wajen 11 Malam yashigo ganin baiga tafiyan Nabil ba yace "Nabil yau kenan agidannan za ka kwanan?

"Eh wllh namai da matata sakin umarni nayi kuma na mayar zanga wanda ya isa yazo yafitamin da mata tunda na mayar ta Malam ka tekamin kar na rasata.

" a a Nabil wanan rigimane tsakanin kada mahaifin ka kana gani yahanani magana yace nabashi DAMAR sa amatsayin sana ma mahaifinka kaga dolo nabashi damar ko yanzu haka ma maganan daurin aure yake agobe karfe 8 nasafe Nabil tayi yayi yafada jikin Malam yanawani irin fitar da nunfashi saida Malam ya tsorata yace kaga tashi tashi kashiga ciki kasame ta idan tace kai tafiso akan BilAL sai insan yanda zanyi injuya abin bana son kasake danuwa irinna wancen lokacin kasha wahala kaji.
Nabil yace" tana ina?

"Tana wajen uwarta.
Nabil yameke da sauri zaifita.

Malam yace "ina zuwa kuma?
"Malam wajenta.
Dariya yabawa Malam yace"amma saida safe ko?
Aiko waigen Malam baiyi ba yafice

Mama kam yau ba bacci ita da Fandau fira kawai ake ayi kuka ayi dariya tayi mutukar mamakin yanda Nabil yake kula da Mama suna cikin haka sukaji anata dukan kofan falo da karfi kamar za aballe duk suka sorata itada Fandau saida ta zo kofan Mama tace "waye?
Yace "Mama kibude nine.
Mama tace "lafiya Nabil yace" kibude.
Mama takalli Fandau alaman ta shiga ciki tunkafin ta karasa fudewa ya fado ciki yayi falon yazube agaman mama yana kuka yana mata magiya yagaya mata yanda sukayi da malam
Mama tace"tunda yabaka dama ka shiga tana ciki.
Da sauri yayi hanyar dakin da akace Fandau take
Amma me yana shiga yatsaya jin wani irin dariya Fandau takeyi awaya

Haba my BilAL kasan fa aurenmu na gaggawa ne
Amma nide nafison koda bayan daurin aurene ayi dan events wanda zai nuna munyi auren SO dakuma yanci
Nima na dandani irin abin da yan gatan amare sukeji
dariya ta sake fashewa dashi
tace kamar ya gobe iyanzu muna manne kana nufin daga an daura aure zaka rabani da
Mamata kenan nima zanso ace gobe iyanzu muna manne.........
Wani irin mari taji yasauka afuskan ta wanda saida ganin ta yadauke na wucen gadi duk da tasan yana wajen bata zata zai tabata ba aiko bol yadingayi da kita mama da take falo taji marin da gudu ta shigo taga Nabil yana ball da Fandau wanda gaba daya hankalin sa baya jikin sa tako ina dukan ta yake Mama kasa kwatar ta tayi gashi da zafi safi yake dukanta aiko da gudu Mama tayi wajen ganin yana neman hallaka mata yar tafita tana kururuwa neman

akawo agaji
Shiko Nabil tunkarfin sa yake makarta yana surutai
"aiko gawar ki bai isa yagani ba zan kashiki in yaso nima akashine kin huta.....

*Tofa shikenan kurunkus Nabil kafutar dani*

*B JATTKO*
DAMATA

NA

BATUL ADAM JATTKO

🌈Kainuwa writers Asso🤝🏻

45
*M*atan gidan kowa da yaran su sunfito jin yan da Mama take niman temako ta san su mata ba abinda suka isa dan haka bata tsaya cemusu komai ba ta wuce part din Malam tana shiga yana sama dan haka tadinga zan bada masa kira
"Sayinnan kafito zai kasheta."
yana karatu a parlourn sama yaji kiran Mama da abinda take cewa ai da sauri ya fito yana tambayan ta
Tana gaya masa ya fara taka stareas da sauri
Yayi ban garen Mama har yanzu Nabil dukan yakeyi duk ta gala baita

"kaiiiii wani tsawo Malam ya doka masa

Yana ganin Malam yabar dukan yayi wajen Malam din dafe da kirji yana wani layi kamar dan ganye amma sai ya kasa karasa wa inda Malam yake dan jiri yana iban sa kuma duhu yake kani
Lun ya zube awajen
Dasauri Malam ya karasa inda yake yana kiran sunan sa ya dagashi ya daura kansa acinyar sa

Nabil ya kama hannun Malam ya fara magana cikin tsarkewar murya yace "Malam Fandau ta yarda da auren BilAL taci amana na bata sona na rasata na....
Bai karasa ba yanemi nunfashin sa ya rasa jijiga shi Malam yafara
Bagaji tace "lah meta masa Malam yasuma fa ko?

Jin wannan yasa mama ta saki Fandau tayi inda Nabil yake
Ita ma Fandau afir gice ta juyo aiko da gasken taga Nabil ba alaman numfashi Mama ce tayi yunkurin tauko ruwa a fridge ita ko Fandau tana ganin haka ta meke duk da kafanta yana mata wani irin zugi amma sai da ta meke da gudu ta karasa inda Nabil yake acinyan Malam hannun sa ta daga sai taga ya koma kamar ba rai wani kara ta kwalla daidai ta zuba masa ruwanda Mama tayi hakan yayi daidai da farfa dowan sa amma bai bude idon jin yanda Fandau take kuka
Dan ALLAH ka tashi Abu Fuji wasa nake maka wllh ne ban taba waya da BilAL ba bansan shiba sai dazunnan
Baban kane yace....

Dasauri Malam ya doka mata tsawa Kiyiwa mutane shiru yadubi Ba Alta yace daukomin wayata
Fandau ta koma gefe itama goshita akumbure gashi ko ina ciwo yake mata musamman hannun ta da take jin kamar ya targa d'ata
Mama tace" kai Sayinna dama mesunan ka yananan da wanan bakar zuciyar tasa wai meyasa duk masu sunanka suke hakane nekam Shateema da yaban shawara ban bari yasa maka mesuna ba dan shima Tajudin da gani irin halin masu sunanka yayi.
Shiko Malam yana kallon Nabil yasan ya farfado
Itako Fandau sai kuka take amma bana ciwon da take jiba
Ahaka
Ba Alta ta kawo wayan ta durkusa tameka masa
Kiran sojojin da suke tsaron kofan sa yayi dan lokacin doka yayi dole sai su zasu kai shi hospital
Su hudu ne suka shigo suka dauki Nabil zasu fita dashi itama Fandau ta meke zata bisu cikin tsawa Malam yace "ina zaki kuma tace" zan bisu yace"zauba." bude ido Nabil yayi cikin da shewar murya yace "kusaukeni a hankali suka sauke shi amma yana dubawa yaga duk matan Malam suna d'kin shiko arayuwan sa basu masa ba sam kuma bazai iyace komai agaban suba yadaga ya Kalli Malam yace "Malam inason ganinku kaida Mama
Malam ya Kalli matan da sojojin tunkafin yayi magana sojojin suka fice suma matan suna zunbure zun buren baki suka fita dan de basu isa su furta wani abu agaban Malam bane
Nabil ya Kalli Mama yace "Mama dan ALLAH kiyi Hakuri nasan ban kyuta ba na shigo har d'akin ki na dakar miki yarinya bayan banwake lefina nada ba na daura wani nikai na tsani hallina dan nasan zai iya sawa ha hanani
( *Hasken rayuwa ta Aisha sada* ,)
Amma Mama nasan Fandau bata san irin sonda nake mata bane bata san yanda na mutu akanta bane da ko na mutu ba zatayi sha awan cewa za ta auri wani ba yanzu lefin da nayi wa Fandau har yakai ta shukun tani da haka ina raye agabana take waya dawani kigaya mata inhar nine mijinta to ta kiyaye abin da zai tuzurani haka wllh wataran saide akwashi gawata
Tashi yayi ahankali yakara sa inda take ya zube guwoyinsa yakamo hannun ta yace "Fatina meyasa kika gujeni meyasa tun a chatting da mukeyi baki baiya namin ganki ba shiya sa kike cewa kina gujemin nadama duk sanda nagane kewacece baki san rashinki barazana ne na rasa rayuwa ta agareni ba
Kiyi magana mana ya matsa hannunta wada yake mata ciwonne kuwa wani kara ta kwallah cikin
Dama Malam da Mama sun fice tunda dama bakinta ne duk basu ga fitan suba

"me yasa kika boyemin kanki Fatina?
Zubura baki tayi ta janye hannun ta cikin tasa nata ta daura hannnun cikin tafin hannun ta dayan tafara juya kai
"Ayyya mata nine ko ya sake jawo hannun ta fizge har hannun ya kumbura yazubawa hannun ido yana gani yasan tar gadene kunsan dan ball baiwani dauki targade abakin komai ba dan she tunyana yaro ya iya gyaran targade idan yayi da kansa yake gyara kayansa ko idan acinkin abokan sa wani yayi yana gyarawa
Fakon idon ta yayi yaja hannun nata k'ara tasa jawota yayi jikinsa cikin dabara ya hadeta sosai da jikin sa yanda zata saki jikinta yana mata wani wasanni har ya fara gyara mata hannun ita ko Fandau jinta aduniyar da tajima tana nema yasa tayi lamo saida taji zafinyayi zafi ta fara jan hannunta tana kuka da yaga kukan nata zaiyi karfi kawai saiya hade bakinsu waje daya amma yana jan hannun wani kara tasa alokacin da yatsan ya fada ya gyaru kenan sake hade bakinsu yayi yanawani irin fitar da nunfashi itama haka sai da yayi facale da kayan jikinta da dafi zafi yake aika mata sakonne yazame mata tamkar wani mayunwacin zaki saida taga yakusa isa babban fada duk da itama ba abinda take so irin abin amma ta daure tameke da karfi ta fusge ta tunkuda shi tameke
Daga kansa yayi yana kallon ta idonsa yayi jajir cikin wani irin muryan da yake janyoshi cancikin makogoro yace "me haka Fatina?
itako sai kare jikinta take tana jada baya da rarafe ya karasa inda take zai kamota ta matsa
"yace mehaka?
"kai kai zan tambaya mehaka zakazo har cikin dakin uwata kanemi kayi lalata dani bayan kasakeni kaban dinbin jama a
"Mata na mayar da kefa wllh karkimin haka kar.

" karka renamin hankali mana kana nufin Fandau din dane daka yaudara ka aura
a gaban din bin mutane ubanda ya haifeka yace bani da iddan ka tun dana haifu bamu haduba dan haka bawani maidani da kayi.

"kiyarda indaura miki iddan yanzu wllh dole su hakura subarmu."

"Lalle Nabil duk dama nagane jikina kake so fiye da komai wllh banzaci abin har yakai haka ba karasa inda zaka nemi jikina sai dakin uwata."

"wllh bakiyi karya ba inason jikinki kuma ko aina zan iya neman sa tunda ina son komai naki inaso.
Cikin karaji tace "dama nasan jikina kakeso ai duk sanda jikina yadena baka sha awa zaka dena yayina ne kawai nikuma yanzu kadena moran jikina dan......
Cikin muryar tausayi yace" karki min haka wllh bazan iya daukan wannan horan ba idan baki amince dani ba wllh nakai gejin komai zai iya faruwa dani yana maganan yana dafa maransa
Tana ganin gasansa jitashi gaban ta yayi mugun faduwa da sauri ta dauki riganta ta sa shiko yanda ta sunkuya ta dauki rigan ne idon sa akan dukkan halitun jikinta da yafi so maranshi yasake dafewa maransa da yakeji kamar zai kashi shi ya kwata yana birgima dafe da maran "yanzu mata bazaki ji tausayi naba itako tama gasa juyowa dan ita tsoron sama takeji
Ayanda yake
Karasa wa tayi gaban gadon ta dauki Akkaram da yake bacci ta tayi hanyan waje saida take bakin k'ofan fita tajuyo ta kalle shi yana nan inda yake yana ta juyi

Tace "shikenan tunda bazaka fita mana ad'aki ba nina bar maka.
"dan Allah karki fita wllh zan iya shiga kowane irin hali idan na rasaki.
Kiduba halinda nake ciki."

"Wllh bazanji tausayinka ba nagaya maka kadena samuna da araha."

"wllh ke bame arahabace idan kinason duk abinda na balla ka aduniya zanbaki kibiyamin bukata yafi."

Abinda nake so dayane awajen kuma ka tabbarar minda bazan samu ba shine kace kana sona."

"idan ana magana kidena kawo banun so Fandau sonki yayiwa bakina girma da na furtashi idan kuma kinaso nafurta ne _INASONKI INA SONKI_ ."
"Taya zanyar da kai bayan kai din makarya cine mayaudari kayaudare ni kamin karya har gaban iyayena kace nabi wata saudia bana sonjin son naka dan bansa meshi asanda nake soba taya zanyar da da kai bayan nasan kai waye ne afannin yausara.

"Wallashi yanda nake sonki ban tabajin ina yiwa wani abuso kamarki ba kiyar da dani ki bani DAMA ki karbi sona zaki sameni mai amana akaru na 2."

"a a Rike abinka dan banyar da dashi ba."

dukan kirjinsa yayi da karfi Wayyo zuciya bazakayi magana ba kafito kanuna mata son nata da yake dankare atare dakai baka da amfani inde bazaka yi magana ba kafito zuciya Fatina shiyasa nace miki sonki abaki bazai faduba.
Zatafita mamakinta kawai sai taji fashiwan kukan Nabil tana juyowa taga kuka yake wuiwui yana dukan kansa da kirjin sa rasa ma yazata yi tayi dan bazata iya fita ta barshi acikin wannan haliba dan tayi mugun tausayin sa gashi idan ta tuna gargadin Dr da Baban Nabil sai taji idan ta amince dashi yanzu ba ta kyuta ba amma sai wani zukiya yace idan yamutu wa akayiwa asara dama ba anacewa tsakanin macce da miji sai ALLAH ba kawai saita fara takawa ahankali har kinda yake shiko kukan yake cigaba da rusawa
Karasawa tayi ta zauna ta daura Akkam aciyar ta sannan ta dago habar Nabil idon sa yayi ja da fuskan sa
tace "ka dena dukan kirjin ka haka mekake sone.
"kenake so much.
"To aigani gaban ga"
Kawai sai ya jawota zan hade bakinsu tayi saurin girgiza kanta
Tace "tokaga abinda yake tabarar min da jikina kawai kake sha awa kenan
yace "komai naki inaso nide nasan inason komai naki."
Ganin bazai yuwuba saida lallami yasa tayi da baran gwara ta lallaba shin
"to kaga yanzu bai kamata muyi wani abu adakin Mama ba kabari da safen asan yanda za ayi."

Dasauri yace "to mufita agidan.

"a a Abu Fuj baka tsoron yanda mutanen gidan zasu fassara ni yanzu ma tun dazu nakasa fita a part din Mama amma haka ma ban tsira ba har na ake biyoni da bakaken magan ganu sai ma gobe idan yaransu da suke aure sunzo zanji sauran."

"kigayanin suwaye suka gayamiki magana?
Wllh bazan bar duk me kunta ta mikiba. "
Tace"a a kar kaga lefisu ni cime babban lefi ai abinma yazomin cikin sauki banzata zaizo da haka ba."

"to yanzu yakike sonnayi."

"Kajen dasafen kadawo."

Kamar wani yaro haka ta dinga lallamin sa dakyar ta tasamu ya yarda zai tafi amma saida yadan rage zafi

Yana rugume da Akkam suka fito falo yace "wllh duk harda lefin Dr wanan yaron cemin yayi wai dansa ne shiyasa nake son ki gayamin gaskiya ya akayi kika gamu da su dashi shegen BG din."
" duk gobe zakaji.
A parlour ma daker suka rabu dazuman shikam anan sai kwana dan yajima da sallama escort dinsa ba inda zaijen sai anyita ta kare
Ita ko Fandau tana samu yana fita tarufo kofan tana cewa zaka gane kurinka tunda nasanu *DAMATA Bazan bari DAMAR* ta kufce min ba saina rama duk abin da kayimin amma har ta kwanta kalmo minsa na soyyyya daya furta mata ne yake mata yawo akunne gakuma kamshin turaren sa da tajima tana mafarkin sa ajikinta wani k'aran dadi tayi da tatuna wataran ko tace nanda dan kankani lokaci zata amarce juyi tadingayi tana murmushi

shima anasa

ban garin hakane kwana yayi yana juyin dan ALLAH ALLAH yake gari yawaye abashi matar sa banda suranta ba abinda yake bijiro masa
Sai asuba yasa mu bacci bayan yadado daga sallah falon da ya kwanan yakoma yakwata akan kujera saiko yasamu bacin ya kwashishi cikin mafarkin me dadi

Washe gari Fandau bayan anyi sallan asuba ta durkusa ta gaida Mama tace "Mama inason naje gidan Bagana Mama ta kalleta taganta da shijab har katsa kibari ita ma zata zo anjima kad'an zaki ganta idan kikaje sauran yan uwanki idan suka zo bazasu ji dadi ba.
"Mama idan

Please Login or Register in order to submit comment