Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fandau dan basu san zancen ba.

Hadim tace "shikenan yanzu suma za aje ace musu yarannan bani na haife suba ko.?
Nabil yace "zasu sani dan tafiyar da Inna danja za aje.
Shiru Hadim tayi ita arayuwan ta bata son taji ance yaran nan ba ita ta haife su ba saide yazatayi d'an wani baya amsa sunan wani suma kansu yaran watara sai sunsani gawani mutuwar sonda take musu yanzu har Akkaram tarike bata son Nabil yayi maganan sama dan karya ce zai maidawa Fandau tunda yanzu kusan sati bai sha nono ba ai anyaye shi kawai wata 7 amma har yafara takawa
Katse mata tunanin yayi da cewa "me shawaran naki.?
tace "akan tsaren zaman da zamuyi ne ni aganina bai kamata ace muntafi duk ba yaka mata atafi da dayar mu tayi wata 6 sannan idan aka dawo akoma da daya yafi dan kishin dawani zanman rashi jituwa ko Wacce za ta dinga jinta kamar ita daya ce nakega hakan yafi ai.
Shiru yayi yana tunanin bazai iya barin Fandau ya jeyayi har wata 6 ba amma afile yace "kema kinsan hakan bazai yuwuba dan ina komawa zan sa su Fuj school tunda suna da baki kinga bazai yuwu adinga yawo dasu ba.
Hadim tace"sai su zauna awajin ta nima idan inacan suna wajena kaga hakan ba wani *dama* aka bata na kula da yaran ta ita ma nima kaga idan ina can zan hada harda Akkam da wanda zamu samu gaba na rike hakan zaisa yaran mu su tashi kansu ahade.
Yace "wanan shawaran naki yayi yanzu dawa za afara zuwa.?
Hadim tace da ita yadace kufara zuwa.

"yanzu my one kinyar da natafi na barki har tsawon wata 6?
"My star to yazan yi kaima kakira abin da yafaru damu da kaddara ne.
Shikan dadi yaji na zai fara zuwa da Fandau afile kuma yadinga gayawa Hadim kalaman so anan kichen din ta hada musu break yace wai ina su Fujna wllh inaga su Ashuwa ne fuka fita dasu Akkam yana bacci bari na dauko sa.
tafita shiku ma yace "haka kawai sun ma yarmin da yara gantalalu bari nakoma dasu jibi su samu nusuwa suma da sauri Hadim ta dawo tace Haba ai ba yanzu za a ta fimin da yara ba zai zan tafi inyaso sai nabar su asasu a school din amma bayanzu ba.
"Shikenan my one ai yanda kikace shi za acigaba dayi Modun ki bai taba kaucewa shawaran kiba ai cikin shawaran ki nake."
dariya tayi tare da ficewa shima yaci gaba da cin abincin sa yana tunanin ko me Fandau takeyi yanzu har Hadim tashigo da Akkam a hannun ta
Tameka masa yace "yaron nan fa dake yake kama k'auri sukaji suna waigawa sukaga girkin Fandau ne yakama da wuta Hadim ta kashe gas din
Tace "yakamata kuma ka koma wajen matar kafa.

Yace "ita me yahana tazo ta cigaba da abinda takeyi.
Haka de har Hadim tace zata je tayi wanka shima mekewa yayi muje nima kimin dan naga alama kwana 2 kin maidani maraya.
"a a rufamin asiri kaje ta maka duk da nasan da aiki agaban ka.

Yace "umm to shikenan de amma kiyi shirin tarbata yau fa.

"Aida naba ka 1week ina son bata damar da mamu bata ba tana budurwa akkin tashi sai kayi kwanaki 7 a wajenta.

"To ai kince tare zamu tafi da ita kinga dole nazo muyi na bankwana.
'a a wllh nayafe.
"yace nagode wa ALLAH da yaza bamin ke amatsayin uwar gida me adalci.

Itade sun guman Akkrama tayi ta haye a bin ta

Tana zaune tana shan tea ya shigo da wayan ahannun ta tana chatin da kawayen da yan uwanda dan yanzu Faridan Amjad ta zama babban amini yar ta
Cikin murmushi ya karasa inda take ya zauna yace "Mata dama ba bacci kika koma ba shine baki fito kinbani break ba sai my one ta tausaya ta bani Gaskiya my one tana da kirki wata da kwana da miji ita da ciyar mata.

"ai kaima kace my one tuda take daya awajen ka kaga ita ya dace ta maka komai musamman wanda ka kwana da ita yarinya ce me ta isa tayi maka da zaka sa ran zata baka breakfast.
Shide yarasa mezaice mata sai binda tada kallo yake dan yanda take kurban tea yana son yagane yanda fuskan ta yake ciji damu wace ko rashin sa amma yakasa tan tancewa
"Inason yin wanka mata fita zanyi.
Tace "ok.
"To kitashi kuje kimin wankan.

Da gowa tayi tana kallon sa tace "kabari sai na gurma yanzu ban isa yiwa babba kamar kaba kaje lantar kin gida ta maka ai mekyu da mekyu ta dace.
Cikin shan kunu yace "idan na fashin ceki kina son gayamin magana ne saboda reni yana son shiga tsa kanimu ko.?

Tace"A a yi hakuri ba reni tsakanin mu zan kiyaye gaba afuwa.
Tsaki yayi ya shige yana cewa girmana kikaga zaki iyayin fin haka ma.
Fandau cikin ta kaice ta ke bin kofan da kallo wato wannan shine hakurin da akecewa tayi ko amma meyasa zai mata haka dan yana son matar shibai gamata yana kusheta gaban taba
Har yafito yagama komai da yasa kayan tana kallon ta gefen ido ko kallon inda take baiyi ba saida yakusa fita yajuyo yace "kishiyar gobe zamuje damasak ziyara.
yana gama cewa haka yafita ita ko tace wannan kaine nade taburman kuyar ai

Tana nan ajaune sai bayan la asar yan matan gidan suka shigo mata yanzu kam tana dan sakewa dasu dan tana cin dariyan su dan basu boye mata Gulman ta da sukayi ba sudin ga gwada tafiyan ta da maganan ta agaban ta tun tana dauka raini ne yanzu ta gane tsabagen sangar tane irin na yan hutu sakalcin su yana bata dariya gashi dama duk kannen sane abokan wasan tane
Gana tace wai Aunty kirki meyasa bakya son zama a man parlor ne mutafi mu mar Hajiya Aunty ita kad'ai a parlour suka tadda Hadim acikin yara suna ta bata surutu FUJJI ce tazo da gudu Oyoyo Aunty kirki ta fada mata sai kuma Fandau ta kasa yi mata wasan take mata nada Fuj tace "baki d'agani ba bance miki nice FUJJI kiba.
"Sorry Fujin mum kinga yanzu kinyi nauyi bazan iya d'agaki ba saide kije mum ta dagaki.
Zun buro baki tayi
Tace "Aunty kirki bata da karfi ai su uncle Grem da mum da Abulna suna d'agani.
Su Maaf ko ball sukeyi sai Akkaam a cintar Hadim ta na bashi abincin sa
Fandau tace "Hajiya Aunty Allah yanzu karfi da yaji kunyaye min d'a kun hana nagan shi.
"tayi dariya tace "aikan gwara da na yaye din da yanda kuke barin kanku da yinwa shima haka zaku barmin shi shiba da amarcin ba a masa shoron wunwa yaude nasa azuma muku kayan abinci a part din ko zaku safa dan karna je ansamo min wani baby a masa shoron yinwa.
Duk dariya sukayi tare da jijinawa Hadim Falmata tayi shewa tace "se hajiyarmu ana cikin haka Basheu yashigo dan gidan Zannah kusan sa an Fandau ne gaishe su yayi tareda dan k'ada key din hannun sa yanayiwa BilAL wasa
Hadim tace "gashi ban gane kama kuma nasan tunda masu gadi suka bar kashigo to sunga na gidane.
Kafin yayi magana Fandau tace "kaninane.
Cikin fara a Hadim tace "Ayyya wllh ban gane ba kinsan yaran Baban ne masha Allah bazan gane ba sai ahankali shiyasa yanzu zan juri zuwa gidan dan nasan yan uwana zauna mana dan uwa.
Basheu ya zauna yana cewa wllh kuwa munada yawa.

Hadim tace "ai kunkai 30 amma ko.?
Basheu yace "wllh mu maza ma 26 ne sai mata 18 idan aka had'a kinga mu 44 daidai.
Hadim tace "Masha ALLAH toni ma yanzu nashiga ciki kaga munza ma 45 kenan.
Dariya yayi yace "hakane Aunty amma fa wanan da tace muku ni kanin tane to ni wanta ne itace yar raini amma su Hassana da su Hafsa yaya suke cemin.
Fandau tace "su Hafsa kace kaje ka tambaya duk nafiku. Hadim tace kinfishi tunda gaki da aure.

Basheu yace "saide tace hakan.
Hadim tace "ya sunan ka.? yace" MUSTAPA amma ana kirana da Basheu.
Hadim tace "Ayyya dan uwa zanje fa ayi family meeting dani dariya sukayi
Basheu yace "nifa da bak'o nazo Yariman Niger yana waje.
Fandau tace YaAfwan meyasa bai shigo ba.
Yasmin tace wai wannan tsadedden guy najiya.?
Ashuwa tace"wllh shine. " Zahra tace "wai wannan mejin kan.
Kafin su sake magana har sun shiko sosai suka kaisa da Fandau da Hadim tace "amma kanin Shateema ne ko.?
"eh inji Fandau ana Afwan yace "zamu wuce.
Fandau ta tashi rakashi saida suka fita yace "sister wllh batun yarinyar na da gaske nake naga baki dauki abin da serious ba.
Fandau tace "nagane Wacce kake nufi Jidda ce amma naji suna cewa tana da saurayi Aliyu amma bari na bata magana kashiga parlour bak'i zan turota.
Afwan yace" *Hauwa Jidda*
Sunan yayi kice mata waccen Aliyu ba na Gaskiyan bane ga *Aliyu Harda*
[3/13, 4:22 PM] BATUL ADAM JATTKO: Gata na Gaskiya nan.
Fandau tana shiga tace "Aunty waifa yayana yanace yana son kizama surukar sa gashi can parlour bak'i yana jiran Jidooo.
Gana tace"wai dan Allah da gaske.
Fandau tace "hakane ai duk basu san sanda suka fadawa Jidda ba suna mata murna amma ta daure fuskan taki cewa komai kuma bata tashin ba Hadim tace kitashi kidan gyara kije mana.
Jidda tace ai aunty da gaske kike naje nayaudare Aliyu kenan Hadim tace "haba jida wannan fa saurayine Aliyu yana da mata kin ko san halin *Yana* matar sa Allah kullum muna miki adua Allah yaza ba miki mafi alkairi gashiko Allah yakawo miki Dr Afwan wanda a India zai ajiyeki ai daga nan suka mata cah har ta tashi ta tafi

Nabil sai dare yashigo suna zaune a parlour su Fuj suka masa Oyoyo zama yayi yana biyewa shimen yaran Yace My one mezan cine.?
Hadim tace "Ummul Akkaam ki saukowa da dan sarauta naki abin kinsan idan sarauta yamosa maya hawa dining.
Fandau dan kar Hadim ta gane wani abu tameke ta dauko su yasmin ko dama suna gaishe shi suka wuce d'aki
Saida ta zuba masa tajuyo ta kalli Hadim tace "Aunty ni zan shiga ciki.
Hadim tace " to aida can din kika kaimasa nima tashi zanyi yanzu
Fandau de kowaigowa batayi ba ta haye da tafiyan na daukan hankali Nabil ajiyan zuciya yayi afili
Hadim tace" yawwa my star naga alert fa shine nace muraba da yar uwata ko? Nabil yace " a a kibar kayan ita ma za a bude mata nata account din kuma za abiyata kudin kamar yanda ake biyanki
millions 40 duk wata ita ma haka munyi da oga da na bude mata ma da anyi da ita.
"Allah my star shiyasa na keson Chelsea suna sonka dayawa matan Amjad Fa dayan suke r'abawa.
"ai Ajd kikace nida shi wayafi bautawa club.
Hakade sukayi ta fira
Hadim tace to katayani da d'akan yaran mu shiga ko dan bacci nake ji nima
Yana zaune tafito awanka dan shiyayi tana fitowa tace "wai dama baka tafi ba.
Yace "ina."
" tace wajen Mata mana.
Dariya yayi yace "to natafi.
Yafita ta kaita sallaman nashi yabata mamaki ga kuma kishi haka ta kwanda ko shafe shafen batayi ba

Da sallama yashiga amma da alama tana bacci hawa yayi tare da rungume ta yace "mata kinji yanda nayi missing naki ne wuni daya kamar shikara.

Da saurin Fandau ta meke zaune dayake wutan akashi yake ta nuna kamar bata gane ba cikin yanayin tsoro tace "Subahanallashi waye.?

Yaja bedside lame yace "yace wakike tsammanin zai tsalleke duk security gidannan ya shigo miki har bedroom.?

Tace "saikai kaikuma banyi tsammanin kaba saboda ai garin naji dadi shine gari banyi tsammanin zakazo garin da ba abinda aka isa amaka ba.?

Dariya yayi yace "mata ki min afuwa nayi kuskure da bansan ta ina zan fara baki Hakuri ba nasan kinsan masayin ki awajena basai nayi zaman gaya miki ba saide kitake dan kibani wahala ki manta da komai hakan bazai sake faruwa ba kinji Mata nasan ke me Hakuri ce.

"kaji nace kamin lefine ai abinda yake cikin zuciyar ka kafa d'a hakan yamin nima ina shirin komawa gidan iyayena kuma zan koma idan na girma na samu abinda zan baka sai nazo.?
"Mata amma nace kiyi hakuri ai.
"bazan hakura ba.

"yanzu yakike son ayi.?
,"inaso katashi ka tafi inda kake jin d'adi.

Mekewa yayi yace "wannan me saukine amfanin mata 2 kenan wata idan ta kunta ta maka wata ta faranta maka.
Saida yaje bakin kofan fita tace "kasan kafison matar kani kuma kadage saina koma?
Yace "sosai ina son matata ko na taba cemiki bana sonta ne.?

"toni na hakura ka mayar ni gida awai.

"Kina da k'afa ai koni na dauko ki ai gani nayi an kawoki.
"to shiyasa kake wulakan tani kenan.?
"kai sorry Mata kar my one tarufemin kofa gwara naje.
Yana gama fadan haka yafude kofan yafice abinsa

Kuka Fandau takeyi sosai tace da kafa nafa yace kena yana tufi mana tafi ai ko dasafe sai natafi
Wani zuciyar yace mata kin manta gidanku ba a yaji daganan taci kukan ta ta gaji tukun ta sauko tafara jera nafila dan kwana 2 nacin sa yasa bata samun yin nafila da yazame mata jiki kawai sai ta tsinci kanta da adua Allah ya sasanta tsaka ninta da mijinta
Shiko abude yatarar da da bedroom din Hadim sosai sukayi da Hadim kafin ta barshi dan ita ta kafe sai yaceka kwanakin da tayi alkawari shikuma yace bai dace ba tunda ita Fandau da ita za ayi tafiya
Yayi kokari sosai wajen nunawa Hadim tana ransa dan yanuna bata kauna zalla
Washe gari tun asuba Baban sa yakirashi yace "tafiyan safe zasuyi tunda yace bazasu kwana ba ya gayawa Hadim ta shirya yara dan ita duk gandan ko kichen bata shiga amma ita take kula da harkan yaranta bata yarda wani yamusu ba bata son ko t'abasu masu aiki suyi ko su Jidda ne suka musu wanka sai tace kaza bayi bata sake musu Nabil yagama shiryawa tace "kagayawa Ummul Kaam ta shiya dawuri kuwa.?

Yajuyo ya kalleta yace "ina naganta kije ke kigaya mata.?
Hadim tace "baza kaje kugaisa ba.
"idan tafito ma zaisa kawai.
Azaune akan sallaya tana karatun Qu ani Hadim ta samu Fandau tazauna Fandau ta kai aya tarufe Qua nin tana murmushi tace "Hajiya Aunty antashi lfy.
Hadim tace "Eh kefa

"lafiya lau.
"Masha ALLAH.
"ki gama shiryawa yanzu zamu tafi.
"ina zamu Aunty.
"Zamuje Damasak garin su megida.

Agidan su Nabil aka hadu inna matazo ba abinda kake gani sai jeren motoci haka suka shiga garin Nabil yana da taren masoya wanda idan yaje ko da yan uwa baya samun ganawa saide yan uwa idan yana meduguri suzo su Hadim anbi dangi Inna duk inda akaje saita bada labarin abinda yafaru itako Hadim harda kukan aboye bayan sunzo duk agidan Inna suka sauka saicen dare suka watse kowa yayi gidan sa yau Nabil ko mukwanan lafiyan baije yayiwa Fandau dinba ita ma Hadim agajiye take bata masa zancen ma dagari yawaye jirgin safe zasubi Hadim ta gama yiwa Nabil shiri sa tace "my star yanaji shiru Fandau bata fitoba gashi lokaci yakusa yana daure igiyar takalmin sa yace ki dubota mana.
Hadim tace "kai baza kajeba nifa na fashinci jiya ma har muka tafi banga kunyi magana ba bayan mun dawo haka meyake faruwa kaman bakwa jituwa.

"tabe baki yayi yace "nide ban ma kulata ba balle na mata nefi.

"bangane baka kulata ba inko hakane da lefin kenan Mamman katuna kayiwa Zannah alkawarin gina adalci a tsakanin mu.

"kigaya min mena mata na rashi adalci shikaran jiya naje na mata saida safe jiya da tafito lokacin tafiyan mu meyaka mata tamin data ganni tun ba d'aki daya muka tashi ba amma kinga ba ta gaidani ba to yazan mata ko ke haka kikemin kikoya mata yanda ake tattalin miji.

"To zan bincika dan nide nasan kanwata me biyayya ce inaga kamata wani lefinne kuma idan na bincika naga da lefin ka nima zan shiga yajin aiki.
Tana gama fad'a tafice awance tasamu Fandau

,"ai baki shirya ba kina kwance.?
Cikin turo baki Fandau tace Aunty yau ma wani wajen za asake fita.?
"Hadim tace "kina tufin bakinsan yaune tafiyan kuba.
"Aunty wane tafiyan kuma.?

"London zaku tafi.
Gaban Fandau ne yafadi wani irin zama zamuyi da wadannan bayin ALLAH yanzu tafiya har wani k'asan bani da matsayin da zaigaya min saide matar sa tazo ta gayamin kuma sai asanda za ayi tafiya shiyasa jiya muka dinga bin yan uwan sa ashi sallama yakeyi nikuma da nakeda yan uwan birjik tunda nazo inda banda gidan YaMuna ba inda naje.
Hadim tace "kinyi shiru time yatafi fa me dame zaki dauka na tayaki shiri.
"wai Aunty to yanzu banyi sallama da kowa ba kuma su YaZaha baza suji dadi ba wllh nide anya za ayi tafiyan nan dani kuwa.
Hadim ta zauna abakin gadon ta dafa Fandau tace" Sister to yaza ayi tafiyan ne ya matso ki musu waya kibasu hakuri nima duk zan bi gidajen su amadin ki in basu hakuri.
Fandau fadawa jikin Hadim yayi tace Aunty bansan mezan cemiki ba yanda kika dauki dangina ashe wai Basheu da Abor mota kika siya musu wllh bakiji godiyar da jiya sukeyi ba Aunty ki nada baiwar kirki wanda ba kowace macce ALLAH yabawa ba.
"yanzu Fandau dan
nayiwa yaran Baba Zannah abu har sai anamin godiya wllh baku daukeni yanda na dauke kuba sam.
"Aunty kirkinki kawai na fad'a Allah de yabarmu tare.
"Ameen nacewa Basheu din yamin les na sauran Wanda basu da mota ya turomin .
Fandau kam rasa bakin magana tayi

sai Hadim din dince ta tashi shiya mata kayan bata musa mata ba dan wani kiman ta take gani Hadim acikin whadrrop din Fandau taci karo wasu magun guna wanda da gani tasan na matane Tajiyo ta kalli Fandau tace kai yar uwa haka kike harka kin bar yayar taki a kasa nima ki daurani network bana ta kwasa ta zubawa jakan da take shiya kayan Fandau
Fandau sun kuyar da kanta tayi cikin kunya Hadim ta zo kusa da ita ta zauna tace "yar uwa da gaske nake dan Allah Mama ce ha hada miki wannan kayan wllh ina bukatan su danni bani koda kawaye anan narenasu sai turawa maganin bature yana k'a idodi kashinan yajanyo min matsala shine nake son yin amfani da namu na nan.
Fandau ta sauke ajiyar zuciya tace "wasu Mama ce ta had'amin wasu kuma YaMuna ce kisamesu.
"ok zan samesu amma sai kun kusa zuwa."
"ah Aunty ba dake zamu tafi ba.
"Eh nafison nabaku *DAMAR* ku kud'an ci amarci daga ke sai shi zaku tafi ko Akkam ba dashi za ajeba dan Gaskiya na shiga hakkin ki daga farkon auren ku shiyasa nace inason yanzu na gyara kurena.
Nabil ya shigo yace My one ya akayi kinsan time yayi kika zauna haka Hadim ta kama hannun Fandau ko wanka batayi basu ka tafita a airport Hadim ta rungumo Nabil shima yaji tausayinta yana goge mata hawaye yace "My one kawai mutafi abin mu Hadim sakin sa tayi ta karbi Akkaam ahannun Fandau tarike hannun Maaf da BilAL tasa su ta sake jan Fuj ta shige mota ta bawa drive umarnin yaja suka Bar wajen ita ko har akusa rufe jirgi Fandau bata da niyar shiga shiko ma dan girman kan yakasa mata magana yana so saita shiga ya shiga kawai sai yazo yakama hannun ta Ascort din shi suka dauki ja kansu suka shige dama shi ajirgi wajen zaman sa na musamman ne har nan yajata ya kuma kulle wayen ya dauki glass ya maka a fuska yaja laptop dinshi ya kunna bai sake ko kallon inda ta keba har 12 narana a gogon 9ja yanuna bai kulata ba bai bude wajen ba balle ma aikatan su zo suyin maganan abinci ko bacci ta kasa saboda yunwa can taga yazuge jaka ya dauko takeaway yabude wani kamshin taji tasan dambun kazane ya sake sa hannun ya dauko wani karamin flask tare da ciro cup yazuba coffee yana ci yana kurban coffee bai ko kalle inda takeba yace "idan zaki ci kici mana kinwani zubamin ido sai kinsa na kwaru.
Abin ya bata mamaki me yake nufi shifa yamata lefi kuma yafita daukan zafi ita ma hankalin ta ta maida kan wayan ta wayan sane yayi kara ya dauka tanajin muryar ta gane Mama ce tace "Nabil haka kuma zamuyi da kai ashi dama matar kake nema kwana 2 ko awaya.
"haba Hajiya Mama yaza kimin wanan fassara wllh ban samu zama bane shekaran jiya wani ma aika cinmu ne bashi da lafiya sai da naga yatashi k'asan su nasamu nusuwa jiya kuma mukaje Damasak kinga yanzu ma muna cikin jirgi zamu koma.
"zaku koma shine bako sallama da an kawo min ko Dauda da Hajara ai.
"Mama ai su suna gida dan bada My one muka zama ba nida Ummul kaam ne.
"Ayya yanzu ina ita Fandau din.?
Yajuya yakalli Fandau shi take kallo amma sai yace "Mama tana bacci ne.
"to ALLAH ya sauke ku lafiya.
Fandau ba karamin haushi taji ba ga idan awayan tane ko takira ba zai shiga ba tunda suna sama dan nashin ma international ni yasa kuma dasafe ma bata da kudi awaya dan ita tunda taje da dan kudin da Habiba ta sa mata take amfani a wayan da ya k'are ko bata da ko asi
Har kusan 3 na yamma yanwa yana cinta shiko yayi bacci yasa tayi sanda ta dauki guntun naman daya bari ta fara ci ita da take son tadan taba yanda bazai gane ba amma sai jinta tayi yace "kuma sai Kinga makerin *kwanon*
[3/13, 5:57 PM] BATUL ADAM JATTKO: Itade dan kunya tarasa mezata ce shikuma ya mayar da kansa ya rufe idon sa
Basu jitun ba har suka zauka sai yau Fandau ta ga matsayin Nabil a London yanda akazo taran sa

Angama shirya musu komai na abinci ita ko dama yinwa take ji gardawan duna fita ta na hawa kan dining shikuma ya haye sama da taga ma tashiga d'akinta nada tashiga bata gansa ciki ba tayi wanka tashiga rama sallolinta tana idarwa ko adua ba ta tsaya yiba ta bi lafiyan godo dan ita amma abin mamaki bata ga Nabil ba har wahegari saida daji yunwa ta shiga kichen dinta akwai komai saide ta jin bakinta take bata sha awan komai sai kawai ta daura ruwan tea tayi hadin kauri tasha tashiga taci wani uban makeup ga ta tsuke cikin kananan kaya tafito man parlor tana tafiyan ta na daukan hankali a falon ko tasamu Nabil yana waya "haba my one kema kinsan duk inda bake dushune haskena idan ankawo yaran ki kirani zamuyi video call dasu tana lafiya a a kikira awayan ta mana.
Hadim tace " ai bata kirani ba bani da no. nata tasa sim ne.?
Yace"ban sani ba.
"to dan Allah kabata wayan zamuyi magana.

"yace girman kine My one yi miki abinda kika so kinci sa ako gata nan.

Me kawa Fandau wayan yayi ranta ab'ace ba abin da take tunawa sai _My one inda bake duhune_
Ahaka har ta k'arasa ta karbi wayan
tace "Allah ya demaki Auntyna yakike ya yaran.?
"lafiya sister kun sauka nafiya.?
"Eh Aunty.
"ya baki nemeni ba na tambayi My star baki sa sim bane yace bai sani ba nace bangane bai sani ba yace na tambaye ki yanzu zaman da na fuskan kunayi kuka cigaba dayiko.
Fandau shiru dayi danme zata moyewa Hadim ai bayan ita Hadim har matsalan da tasamu ta gaya mata komai ai gwara ita ma tadauki Hadim ayanda ta dauketa kawai sai tace "Aunty toni yazan masa shine fa yadena min magana.?
"kin masa wani lefine.?

"nide bansani ba.
"to kinsan abinda nakeso dake ki samesa ki tambaye sa idan da lefin da kika masa kibashi hakuri Nabil yana da saukin kai amma gawan da baisan halin saba bazai gane ba kuma duk girman lefi idan kika bashi hakuri yana da saurin yafiya kuma kinga ni zaman mu dashi mutane suna ga kaman na mallake shi magana ta kawai yake amfani dashi to wllh kawai sanin halin sane kinga idan yamin lefi koda zan shikara ina fushi wllh banza zaiyi dani saima yafini dauka zafi saide ni na koma nabashi hakuri kije kibashi hakuri zan sake gaya miki sauran halayin nasa idan

Please Login or Register in order to submit comment