Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki Lubainu kuma tasake
murtuke fuskarta tace.
Ai ba'a sanin maci tuwo Sai miya takare!
Idan har kana ganin zaka iya samun nasara
akaina da karfin takobinta saika jarraba!!.
A India babu kasa Anan ake gardamar kokawa!!!
GA FILI GA MAI DOKI Mu zuba mugani!!!
Tana gama fadin haka tasa hannu ta zare
takobinta, Al'amarin dayayi matukar girgiza
dakarun sarki Lubainu kenan suka kamu da
tsananin mamaki kuma suka tausayawa wannan
jarumar domin inda tsan tsananin iya yakin sarki
Lubainu da batayi wannan ganaganciba duk da
cewa sums basusan iya NATA yakinba.
Koda yake makaho bayacewa ayi wasan jifa
saiyaga hoge, Amma kuma ai bakin rijiya bawajen
wasan makaho bane!!!
Koda sarki Lubainu yaga irin dakewar wannan
jarumar budurwa harms ta rigashi zare takobi Sai
ya sake cika da mamakinta, kuma yaji ta Dada
burgeshi Ainun,domin yanason mace mai zuciyar
maza wacce yakeganin itace kadai zata iya
dacewa da shi ,
Nan take sarki Lubainu ya sake ja da baya kamar
taku biyar sannan yatsaya tsaf yazare tasa
takobin yanamai bude hannayensa suka kurawa
juna idanu shida ita har izuwa wani Dan lokaci.
Kamar hadin Baku Sai duk su biyun suka Togo da
gudu izuwa kan junansu sunamasu kartan kasa
da takubbansu kaida gani kasan cewa idanu
akayiwa wannan haduwar komai zai iya faruwa.
Muhadu gobe in Allah yakaim


.
ALLON SIHIRI
Littafi na shida (6)
Part F
Koda yarage saura taku uku su hadu Sai suka
daka tsalle sama suka kaiwa jujansu mugun hari.
Shidai sarki Lubainu a wuya ya kaimata saran da
nufin ya tsizge mata kai, ita kuma Sai takaimasa
Sara a kafada da nufin ta zaftaremasa hannunsa
na hagu.
Cikin zafin nama kowannensu yakaucewa harin
da aka kawomasa Amma Sai wani abun Al'ajabi
yafaru a lokacin da suka duro a kasa a bayan
junansu a tare.
Abunda ya faru shine, sakaomakon da saran da
sarki Lubainu yakaiwa jarumar wuya ko shafar
jikinta baiyiba Amma Sai kaifin takofinsa ya
tumke wani Jan kyalle da ta daure gashin kanta
da shi, ya tsargeshi gida biyu ya fado kasa.
Ita kuwa kwalar rigar da ke jikinsa ta yanke ta
yanke tafadi kasa.
Ita dai wannan rigar ta sarki Lubainu mai
muguwar tsada domin ta zallar rigar Alhariri
akayita gami da zaren danyen zinare, musamman
yasa akaje birnin farisa aka dinkota.
Koda sarki Lubainu yaga An lalata masa wannan
Riga mai Daraja Sai ranshi ya baci Ainun.
Itama jarumar dataga An yanke mata wannan
Jan kyalle nata Sai tajuyo a fusace Ainun.
Ashe wannan kyalle shine matsayinta na
sarauniyar mafarauta a cikin gabilarsu.
Cikin tsananin bakin zafin nama sarki Lubainu da
wannan jarumar suka juyo a cikin fushi Sai suka
juyo izuwa kan junansu suka ruguntsume da
sabon masifeffen yaki yazamana cewa suna
kaiwa junansu mugayen harehare.
Nan fa karar haduwar takubbansu yacika dajin
gaba daya, motsinsu da hare harensu ya haifar
da tashin kura, kuma ya dugunzuma hankalin duk
wani Abu dayake kusa. Domin hatta yaran sarki
Lubainu Sai suka rinka ja da baya, wani
lokacimma har buya sukeyi a bayan bishiyoyi kar
tsautsayi ya hausu,Dan wata 'Yar karamar
bishiya ma sarki Lubainu da jarumar Sara daya
sukeyi mata ta fadi kasa,a lokacin da suke
kaucewa harin junansu.
Nanfa dajin gaba daya ya hautsine, tsuntsaye ma
dake kan bishiyoyi babu shiri suka farayin yijira
dole suna sauya sheka.
Wannan tashin hankalin ne gami da karafkakiyar
yakuba na sarki Lubainu da jarumar ne yakai
izuwa kunnen 'yan uwan jarumar dake can gefe
nesa kadan awani bangare a dajin, inda suke
yada sansani.
Adadin wadannan Ayari yakai na mutum dubu
uku da sittin da biyu, kuma dukkajinsu suna
karkashin wani mutum ne ma'abocin kwarjini da
kamala gami da kira Da SADAUKANTAKA Amma
girma yafara kamashi, domin ya haura shekara
sittin a duniya, Ana kiransa da suna ZAHAR BIN
AUDASI.
Sadauki zahar shine mahaifin waccer yarinyar da
take fafatawa da sarki Lubainu.
Koda sadauki zahar yajuyo karar takuban 'yarsa
saiya zabura yafito ya fito da sauri daga cikin
tantinsa ya dubi gaba dayan dakarunsa wadanda
suka kasance maza da mata, kuma dukkaninsu
acikin shigar yaki suke irinta mafarauta yace, Ga
Sarauniyarmu can tana gunurzu, kuzo muje mukai
mata dauki tunda bamusan Adadin mutanen da
take yaki dasuba, kunsani cewa 'yata daga nesa
da sarki Lubainu yaga wannan gagarumar
jarumtaka da jarumar tayi kuma ya kare mata
kallo yaga irin tsananin kyawun da Allah yayi
mata Sai yasake dimaucewa kuma nan take
akaron farko a rayuwarsa yaji yakamu da
tsananin son 'YA MACE!!
Lokacin da wannan jarumar taga sarki Lubainu ya
kura mata idanu kuma ta kare masa kallo taga
yanayin shigarsa Sai tagane cewa mai mulki ne
Dom haka Sai ta turbine fuska tacigaba da
kallonsa kawai har ya iso daf da ita.
Dazuwansa Sai ya dubeta a fusace ya daka mata
tsawa yace, yake wannan bakuwar mafarauciya
wacece ke har da zaki shigu jejin kasata kiyi
farauta ba tare da izininaba?
Ina sauran 'yan uwanki suke wadan sukamin
mummunar barna haka kuka kwashe mana duk
Amfanin cikin dazuzzukanmu??
Kisani cewa tunda na kamaki dolene Ku
dawomana da dukkanin abunda kuka kwashe
kokuma Ku biya da rayukanku tunda kun karya
doka.
Hatta wannan damisa da kika kashe yanzu
dolene ki bani ita.
Koda sarki Lubainu yazo nan a zancensa Sai
kyakkyawar jarumar ta kyalkyale da dariya, lokaci
guda kuma ta turbune fuskarta tace, Ai isace
takesawa akarya dokar sarki!
Munan daka gammu babu bangaren da bamuje ba
a duniya munyi FARAUTA, Kuma kasa ko birni ko
Alkaryar da muka zuwa muka nemi izinin wani
Wanda mukashiga yankinsa"".
Koda gama fadin haka Sai jarumar ta sunkuya
tadau wannan damisar ta saba ta kafadarta
taruga inda 'yan uwanta suke, kawai Sai sarki
Lubainu ya daka tsalle sama dagakan dokinsa ya
shallaketa, sarki Lubainu yana gana Ayyana
hakan a ransa saiyaja da baya yadaina yakar
jarumar kamar zaiyi saran da Amma saiya
shammaci jarumar yaruga da gudu izuwa inda
damisar take.
Koda ganin haka Sai ita jarumar ta falfala da
wannan azabebben gudu nata tabi bayansa,
saigashi har tashi sama takeyi saboda tsananin
gudun, Amma duk da hakan dakyar ta riski sarki
Lubainu sukayi kafada da kafada, ahaka sukaci
gaba da kaiwa junansu naushi domin akai daya
kasa Amma abun yaki yiwuwa.
Koda sukaga saura baifi taku biyarba su isa inda
damisar take.Sai duk su biyun suka daka tsalle
suka kaiwa damisar cafka da Hannu daya.
Bisa rashin sa'a Sai sarki Lubainu ya damki
wuyan damisar, ita kuma Sai ta cafko kafadar
damisar.
Koda kowannensu ya yaja iya karfinsa Sai
damisar ta rabe gida biyu duk su biyun suka fadi
rike da tsagin damisar.
Kawai Sai yaran sarki Lubainu suka farayimusu
tafi sakamakon ganin gagarumar jarumtakar da
sukayi.
A daidai wannan lokaci ne zugar su sadauki
zahar ta karaso wajen a guje bisa dawakai
sukayiwa su sarki Lubainu KAWANYA.
Koda jarumar taga mahaifinta shima yaganta
kwance a kas rike da tsagin damisa kuma Ga jini
a hancinta da bakinta kuma yana diga Sai ya
dubi dakarunsa yamusu inkiya.
Take tadarun suka zaro kibiyoyi suka tana suka
ta6e zasu sakarwa sarki Lubainu da yaransa
harbi, Amma Sai jarumar tayi sauri yace ae
ba'abokin gaba bane, wannan shine sarkin
wannan birni da muke ciki"".
Koda jin haka Sai sadauki zahar ya dubeta a
fusace yace, idan ba abikin gaba ba to menene
yasa ya yakeki harya lalata naman farautarki?""
Koda jin wannan tambaya Sai tayi murmushi
tace, "' saboda munyi masa babbar barna mun
kore duk dabbobi da tsuntsayen dake cikin
dazuzzukan birninsa..
Yanada gaskia akan wannan Al'amari duk da
cewa shi daji na Allah ne bana kowa ba..yakai
Abbana abunda nakeso dakai shine, mu biya
wannan sarki duk abunda ya bukata dangane da
wannan barnan da muka masa, Amma ayau
dinnan nakeso mubar yankin kasar nan tasa mu
kara gaba.
Banason muyi yaki da wannan sarkin domin shine
jarumi na farko dana taba ganin iyada jarumtaka
irin taka"".. Koda jin wannan batu Sai mamaki
Yakama sadauki zahar da sauran jama'arsa.
Shi kuwa sarki Lubainu Sai hankalinsa ya dugun
Zuma Ainun bisa jin ayau su jarumar sukeson
subar kasarsa Alhalin ayanzu ma jiyake kamar
bazai iyayin rayuwa ba in baya ganin wannan
kyakkyawar sura tata. Nan take sarki Lubainu
yashiga tunanin dabarar da zaiyi ya hana
wadannan mafarauta barin kasarsa.
Ita kanta jarumar ta gano abinda ke cikin ran
sarki Lubainu domin ta lura da irin kallon da
yakeyimata run farkon haduwarsu kuma itama
jarumtakarsa ya burgeta.
To Amma Sai ta tambayi kanta a cikin zuciyarta
tace,
MEYASA WANNAN SARKI YA YAKENI DA
DUKKANIN KARFINSA DA NUFIN YA HALLAKANI
IDAN HAR WANNAN KALLO DAYAKE YININI NA
KAUNANE? WATA KILA DARAJARSA DA KIMARSA
AWAJEN YARANSA KOKUMA DOMIN YA JARRABI
JARUMTAKARSA AKAN TAWA""..
Shi kuwa sadauki zahar Sai ya sake doban 'Yar
tasa yace, yake SUHAILAT, Nawa ne adadin kudin
da wannan sarki yakeso mu biyashi bisa wannan
barna da mukayimasa?
Koda jin wannan magana Sai jaruma suhailat ta
dubi sarki Lubainu tace, Ai waka abakin mai ita
tafi dadi, don haka Sai yayi mana bayani da
bakinsa muji.
Koda jin wannan batu Sai sarki Lubainu ya kara
fadawa kogin tunani.
Abu na farko dayayi shine,ya karewa wadannan
mafarauta kallo domin yaga ya Arzikinsu saboda
yasamusu kudi mai yawa wadda baza su iya biya
ba.
Amma Sai wata zuciyar tace dashi, Aisu kudi
basuda kama, kuma bisbisa ganin yadda
wadannan mutane sukeyin wannan gagarumar
farauta, Akwai alamun zasu iya Tara makudan
kudaden da ba'a zato"".
Koda jaruma suhaikat taga sarki Lubainu yayi
shiru Sai ta matso kusa da shi ta katsenmar
tunani tace Malam kana bata mana lokaci mu
mata fiyane ba mazauna ba!
Bamu gaba zama akowane gariba sama da
tsawon kwana bakwai ba Sai a wannan gari
naka"".
Koda jin wannan tambaya Sai sarki Lubainu yayi
murmushi yace, Ai wannan babbar barns da
kukayimin baza Ku iya biyanta da kudi ba domin
ni mawadacine na kudi, harma sunyi mini yawan
da babu abunda zanyi dasu. Idan kunaso Ku
biyani saidai mu shirya wata Gasa ta jarumta
tsakanin zakurkuran mayakanku mutum Ashirin
da nawa, kuma kullum mutum biyu ne kacal
zasuyi wannan gasar.
Abunda ake bukata a gasar kawai shine, akai
mutum kasa ba tare ta an illatashiba, idan
jama'atane suka lashe wannan gasa to dole Ku
zauna a birnina tsawon wadansu kwanaki Ashirin
din kunayimin Aikin bauta a cikin gidan sarautata.
Idan kuma kune muka lashe gasar a cikin kwana
ashirin din to shikenan kun biyani barnar da
kukayinin saikuyi tafiyarku"".
Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar da
jaruma suhailat Sai suka dubi junansu kawai Sai
sukayi shiru suna tunani.
Suma jama'ar tasu Sai suka kama kus kus suna
tattauna Al'amarin a cikin fargaba da damuwa.
Muhadu gobe in Allah yakaimu muji yadda
wannan Al'amari zai kasance
ALLON SIHIRI
Littafi na shida 6
Part G
Koda ganin haka Sai sadauki zahar Yakama
hanjun jaruma suhailat ya jata gefe daya ya
dubeta yace, ni Abunda na lura dashi shine,
wannan sarki bayason tafiyar mu kuma laifin da
muka masa mashine a gabansaba kece
matsalarsa.
Ga dukkan Alamu yafada irin tarkon da sauran
sarakai dayawa suka fada akanki"".
Sa'adda jaruma suhailat taji wannan batu Sai tayi
ajiyar zuciya cikin alamun damuwa tace, yakai
Abbana indai hakane kuwa bamuda wani zabi
Wanda yafi muyi wannan gasa, domin idanma
mukace zamu gudu nida kai ne kadai zamu iya
gudun da barlza acimmana ba, yazamuyi da
sauran jama'armu zamu barsu ne akamasu
Amatsayin bayi? Duk da cewar bamusan irin
jarumtakar dakarunsaba dolene muma a
bangarenmu muma mu ware namu jaruman
wadanda muka yarda dasu kuma dole ne muma
mushiga cikin gasar domin karawa namu jaruman
karfin gwuiwa"".
Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar ya
jinjina kai yace, "" tabbas bamuda wata mafita da
tahuce wannan"".
Koda gama fadin haka Sai sadauki zahar ya
matsa kusa da sarki Lubainu yadubeshi yace, ""
mun yadda zamuyi wannan gasa ta kwana
Ashirin a birninka, Amma bisa shatadi guda!!
Sharadin kuwa shine, cimmu da shammu da
masaukinmu yana hannunka Atsawon wannan
kwanaki dakuma tsaron lafiyarmu dakuma
rayukanmu tunda mu munfi kwarewa rayuwar daji
yanzu kuma kai kanaso muzauna a birninka tare
da jama'arka.
Idan rayuwar daya daga cikinmu ta tabu ko
lafiyarsa to zaka biya diyya mai darajar gaske,
shin ka Amince da wannan sharadin??"".
Lokacin da sarki Lubainu yaji wannan batu Sai
zuciyarsa takamu da farin ciki tayi fari kal, kawai
Sai yadubi sadauki zahar yace, "" Nima na
Amince da duk wannan sharadin naku "".
Batare da wani bata lokaci ba sarki Lubainu da
dakarunsa shida suka wuce gaba da dakarun su
wannan tawagar su sadauki zahar suka rufa
masa baya aka nufi cikin BIRNIN ISTAMBUL.
Duk bayan kamar dakika goma Sai sarki Lubainu
ya dubi jaruma suhailat.
Koda taga kallon yayi yawa Sai ta dauko wani
shudin rawani ta rufawa kanta yazamana cewa
idanuntane kadai ake gani.
Koda ganin haka Sai sadauki zahar ya bushe da
dariya yace, dakyau 'yata kinyi maganin ido
domin shi ido gubane!
Ina mai shawartarki da kija ajinki awajen wannan
sarki da dukkan jama'arsa, kuma ki kula da kanki
don inatsaron wadannan mutane suyi wani Abu
Wanda zai cutar da mu"",
Koda jin wannan batu Sai jaruma suhailat tayi
murmushi tace, " kwantar da hankalinka yakai
Abbana, kayi sani Babu abunda zai samu
dayanmu a wannan gari, lafiya lau zamu gama
abummu acikinsu mutafi"..
Lokacin da sarki Lubainu ya iso gidan sarautar
akaganshi da wannan bakin mafarauta Sai aka
cika da tsananin mamaki,
Dafarko Sai dakarun suka taso danufin su tsare
bakin masarautar domin su azatonsu kama
sarkinsu Akayi, Amma Sai sarki ya musu inkiya
suka koma suka tsaitsaya a inda suke.
Nana take aka bude kofar masarautan take suka
kunnakai ciki.
Da zuwansu Sai akaga sarki Lubainu duk ya rude
yanata haba haba da wadannan bakin mafarauta,
domin da kansa yayi musu jagora izuwa
masaukinsu, kuma masauki mai Daraja yakaisu
inda ba'a saukar kananan mutane, daga manyan
sarakai Sai shahararrun Attajirai.
Nan take sarki Lubainu yabada umarnin
Ashiryawa bakinsa abinci mai Daraja.
Nana da nan kuwa akacika babban falon da aka
kaisu da kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri
birjik! Wadanda ma sunyi musu yawa, baza su iya
karar da su ba, duk da cewa adadinsu yahaura
dubu uku.
Dakin barcin da aka baiwa jaruma suhailat kuwa,
koda matar sarki ce iya abunda za'a shirya mata
Keenan acikin dakin,
Dakin yana hade da makewayi acikinsa. Shikansa
makewayin katone kuma bahon wankansama na
zallan lu'u lu'u ne.
Gadon da ke dakin kuwa Lumsheshene mai tarin
shimfidu masu taushin gaske.
Abinka da wadanda basusan komai ba Sai
rayuwar daji, kuma basu da dakujan kwana Sai
bukkoki da kogunan duwatsu da tanti, duk Sai
suka zama cikakkun 'YAN KAUYE, don haka Sai
suka kasa Amfani da kayan kyale kyalen cikin
dakinnasu dole aka kawo kuyangi suka koyar
dasu.
Bayan jaruma suhailat taci abinci ta koshi Sai
kuyangi uku su ka kamata suka shigar da ita
kewaye domin suyi mata wanka.
Koda suka kwabe mata kayan jikinta suka yi
mata tum6ur! Sai suka rude suka dimauce
sakamakon kyawun da dirin da Allah yabata
dakuma kyawun da Allah yayiwa fatar jikinta
dakuma laushi, domin ko a TARIHI basu tabajin
An wassafa mace mai irin kyawun jikintaba.
Hakadai kuyangin suka shigar da jaruma suhailat
cikin bahon wankan suka shiga yi mata wanka
hannunsu na kyarma, jikinsu nata makyarkyata
saboda tsananin Al'ajabi.
Bayan Angama yiwa jaruma suhailat wankan aka
shafeta da mai dakuma turare Sai aka je Aka
kwantar da ita bisa wannan lumsheshshen gadon.
Koda taji laushin gadon kuma ta duba kayan
kawan dake cikin dakin Sai fuskarta ta fadada da
murmushi da Annuri gami da kurawa rufin dakin
idanu tana mai cewa acikin ranta.
WAI SHIN YAUSHENE NIDA MAHAIFINA DA
JAMA'ARMU ZAMUSAMU NUTSUWA DA DAULA
IRIN WANNAN?
A IYA RAYUWAR DA NA TASO NA RAYU ACIKIN
DAJI, YAKA MATA ACE YANZU NE ZAN HUTA
NASAMU MIJIN DA ZAN AURA UBAN 'YA'YANA.
BANIDA BURIN DAYAWUCE IDAN NAYI AURE
NASAMU DA KO 'YA WACCE ZATA GADONI A
JARUMTAKA DA KYAU, KUMA TACI GABA DA
SHUGABANTAR KABILARMU!""
Koda jaruma suhailat tazo nan a zancen zucinta
Sai hawaye ya zubo mata, saboda bataga ranar
da wannan buri nata zaizo ba saboda
amatsayinta na shugabar kabilarsu kafin abaya
tashugabancin saida tayi rantsuwa akan har
abada bazata taba nisantar jama'arsuba kuma
zata ci gaba da shugabantarsu izuwa tafiye tafiye
donyin farauta akowane bangare na duniya har
izuwa karshen rayuwarta.haka Sai suhailat taci
gaba dayin wannan tunani har bacci yasaceta
bata sani ba.
AL'AMARIN Sarki Lubainu kuwa, tunda yaga
Anbaiwa su suhailat masauki da abinci mai kyau
Sai yatafi izuwa turakarsa cikin tsananin farinciki.
A wannan ranadai saida gaba dayan fadawansa
da hafiman gidan sarautar sukasan cewa lallai
yana cikin farinciki, domin saida halayensa suka
sauya nan take,
Kawai Sai Yakama yiwa mutane kyauta taban
mamaki da bazato, sannan ya 'yanta bayi tamkar
yasamu waraka daga lalurar da ta addabi
rayuwarsa.
Kai awannan ranadai sarki Lubainu kasa bacci
yayi domin duk sa'inda ya runtse idanunsa domin
yayi baccin saidai yaga fuskar jaruma suhailat na
yi nasa murmushi. Atakaice Sai yadda sarki
Lubainu yaga rana haka yaga dare a wannan
ranar.
Ita kuwa jaruma suhailat baccinta tayi ta more
hadda munshari.
Koda ta farka da safe saitaji zuciyarta na faman
bugawa alamar cewa Akwai wani Abu dake shirin
faruwa marar dadi agareta kokuma Ga jama'arta.
Koda gama aiyana hakan acikin zuciyarta Sai
hankalinta ya zugunzuma ainun.
Bisa wannan daliline ta dauko madubin tsafinta
ta shafashi da hannun hagu tashiga bincike.
Nan take taga duk abunda yafaru Ga sarki
Lubainu agaba dayan rayuwarsa da matsalar da
ta Addabi rayuwar harda baccin da yakasayi
sakamokon kamuwa da sonta da begenta.
Koda ganin wannan Abu Sai nan take taji takamu
da tsananin tausayin sarki Lubainu akaron farko
dataji sonsa yadan digu cikin zuciyarta. Jaruma
suhailat taci gaba da bincike akan rayuwarta da
sarki Lubainu, Aikuwa Sai taga wani babban abin
tashin hankali Wanda indai tana Raye da sarki
Lubainu Sai ya faru.
Ba komai ne wadannan abunba face mugayen
yake yake Wanda za'ayi miliyoyin rayuka da
dukiya dakuma tsananin wahala ta gaban
kwatance.
Koda ganin haka Sai jaruma suhailat ta Aiyana
aranta cewa bazata taba baiwa sarki Lubainu
fuskar da zasuyi soyayya ba. Abunda zatayi
kokarin yi shine, ta tabbatar da cewa itada
jarumansu sun sami nasara acikin wannan gasa
da sarki Lubainu ya shirya.
Bayan jaruma suhailat ta gama yanke wannan
hukunci ne Sai ta mike da sauri taje tayi wanka
da kanta domin wannan karon kuyangin basuzoba
tunda sun koya mata yadda akeyin wankan.
Koda tafito daga kewayenta tashiga dakin barcin
domin tasanya tufafinta na fita farauta Sai tayi
Arba da wasu tufafi masu kyawun gaske irin nasu
na mata visa kan gadon nata wata kuyangan
sarki na tsaye agefe daya.
Koda kuyangar taga jaruma suhailat tashigo
dakin saita zube kasa gabanta tayi gaisuwa
sannan ta dago kanta ta dubeta tace, ya
shugabata sarki ne ya turoni nasa miki wannan
tufafi saboda ya gaiyaceku izuwa fadarsa keda
mahaifinki, koma Akwai manyan bakin sarakuna
da sukazo halattan wani biki da akasabayi a
wannan gari namu arana irinta yau"".
Koda jin wannan batu Sai jaruma tadubi wannan
kuyanga da'alamun mamaki tace, Wane irin biki
ne wannan haka?"
Kuyangar tace, gasa ne na Raye Raye da kade
kade gami da wake wake.
Wanda duk yalashe gasar sarakuna nabashi
kyaututtuka wani ma Sai yasamu sarkin dazai
bashi kwangila ta daukemasa kewa har izuwa
karshen rayuwarsa yana biyanshi Albashi mai
tsoka." Koda jin wannan batu Sai suhailat takamu
da murna saboda a rayuwarta tanson kallon
abubuwan nishadi irin haka.
Batare da wata matsalaba ta Amince akasanya
mata wannan Riga mai Daraja akayimata kwalliya
ta gani afada.
Koda kuyangar takaita gaban madubi suka tsaya
takalli kanta Sai tacika da tsananin mamaki, da
farko razana tadanyi taja da baga don zato tayi
wata Al'jana ce me kamarta a jikin madubin.
Saida ta shafa hannunta ajikin madubin sannan
ta tabbatar hotonta ne ajikin madubin ba Al'jana
ba. Cikin murmushi suhailat tadubi kuyangar tace,
"Kaini masaukin mahaifina", Nan take kuyangar
tahuce gaba jaruma suhailat na biye da ita.
MUHADU A LITTAFI NA GABA WATO NA BAKWAI
(7) DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN
KASAITACCEN LABARI.
DAGA MAI DEBE MUKE KEWA A KULLUM A KO
YAUSHE. KING OF ADVENTURE STORY.
ABDUL'AZEZ SANI MADAKIN GINI.
NI NAKU HAR KULLUM KHAMIS IDRIS
MUHAMMAD NAKE CEWA MUGANA A GABA NAN
BADA JIMAWABA INSHA ALLAHAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
[1/23, 00:53] +234 808 677 7945: ALLON SIHIRI Littafi na bakwai 7 Part A Duk Inda Suka Wuce
Dakaru, Bayi, Barori Da Kuyangi Kamar Babu Mai Rai Acikinsu Sbd DuksuYazaunaKamar Gunki
Suna Masu Quramusu Idanu, Bakomaine Ya Haddasa Hakanba Face Ganin Tsananin Kyawun
Jaruma Suhailat, Gashi Kuma Wannan Riga Datasaka Ba Qaramin Kyawu Tayi Mataba, Da
Shigarsu Cikin Dakin Sai Suhailat Tasake Cika Da Mamaki, Ba Komaine Ya Haddasa Hakanba
Face Ganin Mahaifinta Sadauki Zahar Zaune Akan Kujera Cikin Tufafi Na Alfarma Tamkar Wani
BASARAKE, Koda Sadauki Zahar Ya Hango Suhailat Acikin Wannan Kyakyawan Shiga Wace
Taqara Fito Da Tsananin Kyawunta Da Kwarjininta Sai Ya Miqe Tsaye Cikin Matuqar Farin Ciki Ya
Tareta Suka Rungume Juna Sannan Ya Janye Jikinsa Daga Cikin Nata Ya Dubeta Cikin Alamu
Matuqar Damuwa Yace, Yake 'yata Shin Kinada Lbrn Cewa Inda Zamuje Yanzu Taro Ne Na
Sarakai Da Manyan Masu Fada"aji, Jaruma Suhailat Ta Gyada Kai Tace Nasani Ya Abbana,
Kuma Ka Kwantar Da Hankalinka Babu Wani Sarki Ko Attajiri Wanda Ya Isa Ya Mallakeni Da
Qarfin Arziqinsa, Na San Wannan Ce Damuwarka, Kodajin Hak Sai Sadauki Zahar Yayi Murmushi
Yace Wannan Gsky Ne Yake 'yata, To Amma Wane Mataki Zaki Dauka Don Kaucewa Hakan?
Kisani Cewa Dazarar Sarakan Sun Ganki Zasu Dimauce Kuma Sufara Tunanin Hanyoyin
Dazasubi Su Mallakeki Ta Kowanni Hali, Jaruma Suhailat Tasake Yin Murmushi Akaro Na2 Tace
Kada Kadamu Yakai Abbana Domin Tuni Nadauki Mataki Akan Hakan, Kai Dai Kawai Kazuba Ido
Kaga Abinda Zaifaru, Gama Fadin Hakan Keda Wuya Saiga Wani Hadimi Ya Shigo Cikin Turakar
Da Sauri Ya Dubesu Yace, Sarkine Yaturoni Nayi Muku Jagora Izuwa Fada, Batare Da Bata Lkc
Ba Jarumu Suhailat Da Sadauki Zahar Sukabi Bayan Wannan Hadimi Suka Nufi Fadar, Filin
Fadar Yacika Ya Batse Da Bil'adama Duk Inda Mutum Yahanga Babu Abinda Zaigani Face
Kawunan Mutane Rututu! An Kange Tsakiyar Filin Dawata Katangar Qarfe, Makada, Mawaqa Da
'yan Rawa Sunjeru A Gefe Sahu Sahu Acan Sama Bisa Wani Gini Mai Tsawo Wanda Ke Dauke
Da Matattakala Sarakai Ne A Zazzaune An Shirya Kayan Ciye Ciye Da Shaye Shaye Agabansu,
Tuni A Wannan Lkc Anfara Gabatarda Sauran Jama'a Kuwa Sai Idanunsu Sakakafe Bakunansu
Suka Wangame Sbd Kallon Kyakkyawar Surar Dake Wucewa Ta Cikin Tsakiyar Fadar Wato
JARUMA SUHAILAT Tarada Muqarrabanta Nan Take Sarki Lubainu Da Dakkannin Sarakuna
Dake Kewaye Dashi Suka Mimmiqe Tsaye Dao Tarbar Jaruma Suhailat Da Tawagarta, Sudai
Sarakan Sunyi Zaton Cewa Suhailat Wata Shahararriyar Sarauniyace Daga Wani Bangare Na
Duniya, Donhaka Basusan Sa'adda Sukakama Risinawa Ba A Gareta Suna Gaisheta, Shikansa
Sadauki Zahar Anzata Cewa Sarkine Sbd Kwarjininsa Da Yanayin Shigar Dayayi Irinta Manyan
Sarakai Ce, Cikin Hanzari Sarki Lubainu Yatarbi Jaruma Suhailat Da Mahaifin Sadauki Zahar
Yarakasu Harzuwa Inda Aka Tanadarmusu Suka Zauna Sannan Shima Yakoma Gaban
Karagarsa Yatsaya Ya Fuskanci Jama'a, Nanfa Fadar Tayi Tsit! Kamar Mutuwa Tagifta Aka
Zubawa Sarki Lubainu Idanu Ana Sauraronsa Aji Bayanin Dazaiyi, Sarki Lubainu Yayi Gyaran
Murya Sannan Yace Yaku Manyan Baqi Da Dukkanin Jama'a Dake Wannan Wurin, Ina Yimuku
Barka Daxuwa Wannan Babban Taro Wanda Mukasabayi Aduk Shekara Awannan Birninamu Mai
Albarka Na Istambul, Bayan Haka Inamaiyiwa Jama'a Busharada Cewa Wannan Tarona
Banatarone Nadabam,kumanamusamman Wandabamutabayin Kamarsaba Sabodawannankaron
Munada Wadansu Bakinamusamman Masu Dumbinbaiwada Darajakamar Yaddakukaga
Shigowarsu Akarshe Izuwacikinwannantaro.Wannanmanyanbaki Sunzoda Zakwakuran Sadaukai
Kuma Jarumaihar Gudaashirin Wadandazasu Yigasar Karfindantseda Dakarunbirnina,inamaiyiwa
Jama,a Albishirdacewa Nimainacikin Jarumandazasuyi Wannan Gasarjarumtaka;kodasarki
Lubainuyazo Nan Azancensa,saimutanesukarude.Dashewa,gami-datafi.Sabodasun,san.Irin
Tsananin JARUMTAKARSA Da Sadaukantakarsa Don Hakasuna Son Kallon GUMUZUR,
Al'amarin Jaruma Sahailat Da Mahaifinta Sadauki Zahar Kuwa Koda Sukaji Cewar Sarki Lubainu
Mazai Shiga Wannan GASAR JARUMTAKA, Daza Ayi Sai Sukakamu Datsananin Mamaki Kuma
Tsoro Yadarsu Acikin Zukatansu Domin Basu Taba Zaton Cewa Hakan Zatafaruba, Cikin Kaduwa
Jaruma Suhailat Tadubi Zahar Cikin Qaramar Murya A Daidai Kunnensa Tace Yakai Abbana
Yanzu Meye Abinyi? Idan Harmuka Bari Saski Lubainu Yashiga Wannan Gasa Muza A Cinye,
Sadauki Zahar Yanumfasa Yace Maganarki Dutsece Donhaka Ina Ganin Cewa Nima Zanshiga
Gasar Sbd Natareshi, Jaruma Suhailat Ta Girgiza Kai Tace A'a Bazaka Tareshiba Nice Dai Dai
Dashi Domin KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA Yadda Yake Taqama Da Quruciya
Daqarfi Nima Haka Nake Taqamadasu Kaikuwa Shekarunka Sunfara Nisa, Zai Iya Amfani Da
Wannan Dama Yayi Saurin Galabaitar Dakai Donhaka Kawai Kabarni Dashi, Sarki Lubainu Yaci
Gabada Bayani Yana Mecewa Yaku Jama'a Yanzu Batare Da Bata Lkb Ba Ina Kira Ga
Wadannan Manyan Baqi Namu Dasu Fitoda Jaruman Gasarsu Guda Ashirin Su Gabatardasu A
Tsakiyar Filh Sannan Muma Mu Gabatar Da Namu, Bayan Nan Za'ayi GASAR JARUMTAKA
Guda Daya Jal! Awannan Rana Sannan A Cigaba Da GASAR NISHADI Koda Gama Fadin Hakan
Sai Sarki Lubainu Yakoma Kan KARAGAR MULKINSA Yazauna. Muhadu gobe in Allah yakaimu.
Naku khamis idris Muhammad
[1/23, 00:53] +234 808 677 7945: e
ALLON SIHIRI Littafi na Bakwai 7 Part B A Sannan Ne Sadauki Zahar Da Jaruma Suhailat
Sukamiqe Tsaye Suka Kira Jama'arsu Suka Koma Gefe Daya Acikin Filin Fadar Sunaware
Sadaukan Dazasuyi Wannan Gasa, Bayan Sungama Ware JARUMAI Goma Sha

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment