Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace
da
Yazarina taje tasa kuyangi su shiryawa Attajiri
Abdul Nasir
abinci na musamman kuma ya gargadeta da
kada a dafa masa abincin da nama sai kifi.Koda
jin
wannan umarni sai Yazarina ta cika da mamaki
domin bata san dalilin dayasa aka bayar da
umarnin
ba amma sai ta kudurce a ranta cewar zata
tambayi
mahaifinta dalilin.
Nan take Abu Yazarina yaja Abdul Nasir suka tafi
izuwa
turakarsa suka zauna,ita kuwa
Yazarina ta tafi izuwa madafar gidan ta baiwa
kuyangi umarnin abinda zasu dafawa babban
bako
kamar yadda mahaifinta ya umarceta,daga na ta
wuce izuwa cikin turakarta taje ta kwanta domin
tayi
barci amma sai ta kasa.Ga abincinta na dare an
kawo an ajiye
amma ko kallonsa batayiba.Har dare
ya raba Yazarina bata rintsa ba.Koda taga tunani
ya
hanata bacci sai ta mike tsam daga kan gadonta
ta
fito izuwa cikin harabar gidan ta kama
tattaki.Koda
tazo zata gifta ta gaban turakar da aka sauki
bako
Abdul Nasir saita hangoshi a tsaye yana
nafila.Al'amarin dayai
matukar bata mamaki kenan
domin bata taba ganin irin wannan ibada dayake
yiba,bata ma san irin addinin da yake yiba.Kawai
sai
ta kura masa idanu har saida ya idar da nafilar
yayi
'yan addu'oinsa ya shafa.Koda ya mike tsaye da
nufin ya nade sallayarsa sai ya hango Yazarina a
tsaye acan
gefe daya ta zubo masa idanu.Al'amarin
dayai matukar girgiza shi kenan ya bashi
mamaki,kawai sai ya fito daga cikin dakin ya
taho
gareta ya dubeta yace,yake Yazarina lafiya kike
kai
kawo a gida cikin wannan dare haka?
Ga dukkan
alamun akwai wani abu da yaje damunki domin
na lura yanayin
da kike ciki a farkon zuwana
gidannan.Sa'adda Yazarina taji wannan tambaya
sai
ta sunkuyar da kanta kasa cikin alamun tsananin
damuwa sannan tace,yakai wannan attajiri kayi
sani
cewa hakika ina cikin damuwa matsananciya
wacce
ta hanani barci da sukuni.Nan take Yazarina ta
kwashe labarin
gasar aurenta da za'ayi gobe da safe
a fada tsakanin Yarima Lubainu da Yarima
Mangul.

ALLHAUSA NOVELSTV
kuma ta jaddada masa irin tsananin soyayyarta
ga
Yarima Lubainu.Koda jin wannan batu sai Attajiri
Abdul Nasir yakamu da tausayin Yazarina ya
dubeta
yace,yake 'yata ki kwantar da hankalinki zanyi
wata addu'a ta
musamman a daren nan domin na nemi
sanin sirrin abin dake cikin wannan gasa da
za'ayi
gobe da safen domin na sanar dake abinda
Yarima
Lubainu zaiyi don kare kansa daga sharrin abokin
hamaiyarsa.Saidai nifa da safen zan bar garin
nan
na wuce izuwa birnin Kisra don haka bazan sami
damar
halattar wannan gasa ba.Lallai da safe bayan
na gama kimtsawa sai kizo na sanar dake
wannan
sirri.Yayin da Yazarina taji wannan batu sai ta
kamu
da tsananin farin ciki tayi godiya ga Attajiri Abdul
Nasir sannan kuma ta dubeshi tace,ni kuwa ina
son
nayi maka wata tambaya in bazaka damu
ba.Abdul Nasir yayi
murmushi yace,ai matambayi baya laifi
domin yana neman ilmine,fadi abinda kikeso ki
sani
yake 'yata
.Yazarina tayi gyaran murya sannan
tace,dazu naga kanayin wata irin ibada wacce
ban
taba ganiba,shin ko zaka iya yi min bayani
akanta?
Koda jin wanann batu sai Attajiri Abduil Nasir
yayi murmushi
yace,Kiyi hakuri bai kamata nayi miki
wannan bayani ba ayanzu saboda wasu
dalilai,amma
bayan angama gasa zaki iya tambayar mahaifinki
wannan tambya da kika yi min,lallai zai baki
cikakkiyar amsa amma zaifi kyau ki bari sai
bayan an gama
wannan gasa ta neman aurenki.Saida safe
ina mai saurarin zuwanki kafin in tafi.
Koda gama
fadin hakan sai Attajiri Abdul Nasir ya juya ya
koma
izuwa cikin dakinsa ya rufo kofa.Itama Yazarina
sai
ta juya da sauri ta koma turakarta zuciyarta cike
da
farin cikin wannan bushara wacce Attajiri Abdul
Nasir
yayi mata domin ji take kamar ta sami cikakkiyar
nutsuwa da kwanciyar hankali.washe gari kuwa
da
sassafe fadar sarki Sailur ta cika ta batse da
jama'a,duk inda mutum ya hanga babu abinda zai
gani face kawunan bil'adama rututu.Abinda ya
daurewa jama'a
kai shine sarki Sailur da Yarima
Lubainu ne suka fara zuwa filin fadar tun kafin
jama'a su cika sannan sai ga Yarima Mangul Da
sarki Alkas sun shigo fadar,Yarima Mangul yayi
gagarumar shigar yaki ta jan sulke,hatta kufen
takobinsa,hular karfen da yasa da takalman
karfen dake
kafafunsa duk jajaye ne.Shi kuwa Yarima
Lubainu shigar fararen sulke yayi,farar takobi
gami
da farar garkuwa mai hoton zaki a jikinta.Koda
shigowar su Yarima Mangul cikin fadar sai
jama'a
suka kaure da shewa da tafi.Maroka kuwa suka
kama kirari,makada da masu busa suka kama
aikinsu.
Acan gidan Attajiri Abu Yazarina kuwa
hankalin Yazarina a DUGUNZUMe yake domin tun
da
Asuba tayi wanka ta kimtsa ta tafi kofar dakin
bako
Abdul Nasir domin taji sakamakon abinda ya gani
wansa yayi alkawarin sanar da ita amma sai ta
iske
dakin a kulle yana barci bai farka ba.Nan fa
hankalinta ya kara
dugunzuma ainun ta kama kai
kawo a kofar dakin zuciyarta na bugawa da karfi
saboda tana tsoron kada Yarima Lubainu da
Yarima
Mangul su fara gasar kafin ta isa can filin
fadar.Tana
cikin wannan haline Abu Yazarina ya fito daga
cikin
tasa turakar cikin shirin tafiya fada.Koda yaga
Yazarina a tsaye
a kofar dakin bako Abdul Nasir sai
ya cika da mamaki yace,me kike yi anan alhalin
ana
jiranmu acan fada kinsani cewa saboda ke ake
yin
taron yau.Cikin yanayin damuwa Yazarina ta
dubeshi
tace,yaka Abbana ina da alkawari mai girma da
wannan bako naka.Yace zai bani wani taimako
akan masoyina
Yarima Lubainu.Koda jin haka Sai Abu
Yazarina ya girgiza kai cikin alamun damuwa
yace,ai
kuwa mun makara,na sani cewa Abdul Nasir baya
barci da dare yana yawan ibadarsa,yanzu ne
yake
samun damar yin bacci bai kamata mu tasheshi
ba.Gama fadin haka keda wuya sai sukaji an turo
kofar dakin
bako Abdul Nasir.Cikin matukar farin
ciki
Yazarina ta ruga izuwa bakin kofar ta tari Abdul
Nasir,kafin ta budi baki tuni Abdul Nasir ya tari
numfashinta yana mai cewa maza ki ruga izuwa
fada
ki gayawa Yarima Lubainu cewa kada ya kuskura
ya baiwa
Yarima Mangul Hannunsa su gaisa.Kafin
Abdul Nasir ya gama rufe bakinsa tuni Yazarina
ta
juya da gudu ta nufi inda bargar dawaki
take.Koda
sauraron bawan dake kula da bargar batayi ba ta
shiga ciki ta kwanto doki guda da hannunta.Ba
tare
da ta tsaya dauwara dokin siddi ba tayi tsalle ta
haye kansa
sannan ta zabureshi da gudu ta fice
daga cikin gidan.Nan dai Abdul Nasir ya yiwa
Abu
Yazarina bankwana ya tafi sannan shima Abu
Yazarina ya tafi izuwa fadar cikin sauri.A can
fada
kuwa bayan maroka da makada sunyi
hayaniyarsu
tsawon dan lokaci sai aka kirawo Yarima Lubainu
da Yarima
Mangul suka shigo cikin tsakiyar filin fadar
suka tsaya suna masu fuskantar juna.
Alkalin gasar
ya dubesu yace,sai ku fara gaisawa bisa ka'idar
kowace irin gasa ka akeyi a birnin nan.
Adaidai
wannan lokaci ne Yazarina ta shigo filin fadar a
sukwane bisa dokin kuma a sannanne fadar ta
sake rudewa da
hayaniya da shewar mutane bisa ganin
jaruman biyu sun tsaya a tsakiyar filin sun
fuskanci
juna.Koda Yazarina ta hango Yarima Mangul ya
durfafi Yarima Lubainu yana mika masa hannu
zasu
gaisa sai ta kama kwalawa Lubainu kira domin ta
hanashi gaisawa da Mangul,amma saboda iface
ifacen daya
kaure a filin ko kadan Lubainu bai jio
kiran nataba.Tana isowa daf da kofar filin gasar
ne
ta hango gaisawar Yarima Lubainu da Yarima
Mangul.Nan take ta kamu da tsananin bakin ciki
har
hawaye ya zubo mata.Cikin sanyi jiki da karayar
zuciya ta sauko daga kan dokin nata ta tsaya cak
ruke da
linzamin dokin nata ta zuba ido izuwa cikin
filin gasar domin taga yadda gumurzun zai
kasance.Sarki Sailur da Sarki Alkas nacan sama
bisa wani gini mai tudu inda aka ajiye kujeru na
alfarma na sarakai da attajirai.
Ai kuwa saiga Attajiri
Abu Yazarina ma ya iso yazo ya zauna a kusa da
su Sarki
Sailur suka gaisa.Kwatsam sai akaji an buga
tambarin fara gasa nan fa filin yayi tsit tamkar
babu
abu mai rai a wajen,baka jin sautin komai face
sautin iskar dake kadawa.A lokacinne Jaruman
Biyu
suka zare takubbansu suka fara zagaya juna
kowannansu ya fara nazarin dan'uwansa.Daga
can sai suka
fara ja da baya baya kamar bazasuyi
yakinba,kuma sai suka rugo da gudu suka
kacame
da AZABABBEN YAKI,ya zama cewa suna kaiwa
junansu SARA DA SUKA cikin tsananin ZAFIN
NAMA,JURIYA DA BAJINTA.Nan fadar ta sake
rudewa
da sowa kowa nayiwa gwaninsa jinjina.Ita kuwa
Yazarina saita
fashe da kuka taci gaba da kallon
gumurzun a haka tamkar an tilasta ta da yin
kallon.Saida jaruman biyu suka shafe rabin sa'a
suna bakin gumurzu amma dayansu bai sami
nasarar koda lakutar dayan ba domin fadan ya
nuna
cewar karfinsu da kwarewarsu a iya yaki tazo
daya.Bisa dole
su biyun suka ja da baya suka yi
cirko cirko suna haki da kallon juna tamkar
zakaru.Bayan yan dakiku kowannansu ya gama
nazarin irin salon fadan da zai sauya sai suka
sake
rugowa da gudu izuwa kan juna.Koda ya rage
saura
baifi taku uku ba su hadu sai kowannansu ya
daka tsalle sama
cikin shammace yakai hari.Cikin sa'a
kuwa Yarima Mangul ya yanki Lubainu a damtsen
hannunsa na hagu,shi kuma Lubainu ya sami
nasarar yankarsa a cinyar dama.Duk su biyun
suka
kwalla ihu sakamakon jin tsananin zafi da zugi
kuma
suka rikito kasa a galabaice a lokacin da jini yayi
tsartuwa
daga cikin jikinsu,amma saboda juriya da
jarumtaka sai ko wannan su ya tsaya akan
kafafunsa.Kamar hadin baki sai ko wannansu ya
cire
kyallan daya daura a goshinsa ya daure rauninsa
don tsaida jini.Saida suka sake zagaya juna sau
uku
sannan suka kacame da sabin azababben yaki
cikin tsananin
fushi da kunar rai.Wannan karon dai sai
yaki nasu ya zamo abin tsoro domin sun sauya
salo
sosai sun hada da tsalle tsalle a sama da kasa
gami
da kaiwa juna sara da suka da hannu da kafa.Ai
kuwa sai kowannansu ya fara raina kansa domin
na
take suka fara hadawa juna jini da majina.Kuma
kafin cikar
wata rabin sa'ar sun sake yankar juna
sau biyar biyar.Nanfa jiri ya fara dibarsi suka
kama
layi,amma saboda naci da taurin kai basu fasa ci
gaba da yakinba.Nanfa jikin sarki Sailur dana
Sarki
Alkas yayi sanyi kuma hankalinsu ya dugunzuma
ainun domin babu wanda yake da tabbacin cewar
dansa zai
sami nasara.Ana cikin hakane Yarima
Mangul ya shammaci Yarima Lubainu ya danki
kasa
ya watsa masa a ido.Kafin Lubainu ya mitstsike
idon
nasa tuni Mangul ya soka masa takobi a gefen
ciki.Lubainu yayi ihu kuma yayi sauri ya rike
takobinsa da hannunsa a lokacin da Mangul ke
kokarin danna
takobin ta nutse a cikin ta faso ta
baya.Cikin tsananin Jarumtaka Lubainu yasa
hannunsa na hagu ya gabzawa Mangul naushi a
fuska.Saboda karfin naushin saida Mangul yayi
katantanwa sau uku a tsaye sannan ya zube kasa
a
mutukar galabaice.
A sannan ne Yarima Lubainu ya zare takobin
daga cikinsa ya
yanke jiki ya fadi kasa
magashiyan.
Koda Yazarina taga abinda ya faru ga
Lubainu sai ta kurma ihu ta sulale kasa
sumammiya.Ai kuwa Attajiri Abu Yazarina bai san
sa'adda ya mike tsaye ba ya ruga izuwa inda
Yazarina take ya kama yi mata firfita don ta
farfado.A wannan
lokaci Lubainu ya baje kasa yana dafe da
raunin cikin nasa wanda jini ke bulbulowa daga
cikinsa,jikinsa na tsuma kuma idanunsa na
lumshewa.Kawai Sai Yarima Mangul ya mike
tsaye
yana mai kyalkyala daritar mugunta da farincikin
domin ya tabbatar dacewar ya gama samun
nasara a wannan
gasa.Mangul yazo kan Yarima Lubainu ya
tsaya ya tofa masa yawu a fuska yace,burina ya
cika
akanka.Yanzu zan karasa kashe ka kuma na auri
masoyiyar taka.Gata can ta suma saboda ganin
nasarar dana samu akanka.Ko domin na cusa
mata
bakin cikina har abada saina karasa
kasheka.Koda jin wannan
batu sai Lubainu yaji zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone.Duk irin tsananin
ciwon
da yakeji a cikin nasa sai yaji kamar an zare
masa
shi saboda fishi.Koda Mangul ya dago takobinsa
sama da nufin ya datse masa kai sai ya mirgina
can
gefe daya cikin zafin nama,takobin Mangul ya
karci kasa.Ai
kuwa sai fadar ta rude da shewa.
Sarki Sailur
kuwa baisan sa'adda kwallar farin ciki tazo masa
ba.Kafin Mangul ya juyo ya sake kawo masa
wani
harin tuni Lubainu ya suri tasa takobin ya daka
tsalle
sama ya sare hannun Mangul mai ruke da
takobi.Take hannun ya gutsure ya fadi can gefe
daya.Mangul
ya kwarara uban ihu a lokacin da jini
ya kama feshi daga cikin dungulmin hannun
nasa,kawai saiya sulalae kasa sumamme.Shima
Yarima Lubainu sai jiri ya sake dibarsa shima ya
zube kasan sumamme.Nan take dakaru suka
rugo
da gudu izuwa kansu,aka daukesu aka shigar
dasu izuwa cikin
gidan sarautar aka kirawo lokitici suka
dukufa a kansu.A wannan lokacin gardama ta
sarke
a tsakanin Alkalan wannan gasa akan tantance
wanda ya lashe gasar tsakanin Yarima Lubainu
da
Yarima Mangul.A karshe dai aka tabbatar da
cewar
Yarima Lubainu ne ya lashe wannan
gasa.Lokacin da likitoci
suka sami nasarar ceto rayuwar Yarima
Lubainu da ta Yarima Mangul sai duk su biyun
suka
farfado lokaci guda,sukayi arba da iyayensu
tsaye a
kansu wato Sarki Sailur da Sarki Alkas.Koda
Yarima
Mangul yaga bashi da hannu daya saiya fashe da
kukan bakin ciki ya kurma ihu sannan ya dubi
Lubainu
yace,Yakai abokin hamayya ta ka cuce ni da
baka kashe ni ba,ka mayar dani masaki alhalin na
tabbatar da cewa kai za'a bawa zakaran wannan
gasa.Koda jin wannan batu sai Yaruma Lubainu
ya
bushe da dariya kuma ya murtuke fuskab
yace,nikam burina ya gama cika tunda yanzu
nine na zami
angon Yazarina.Kafin Lubainu ya gama rufe
bakinsa
tuni Yarima Mangul ya bushe da mahaukaciyar
dariya.Al'amarin da yai mutukar baiwa Yarima
Lubainu Dasu Sarki Alkas mamaki kenan.
Mangul
yacigada kyakyata dariyar kamar bazai daina ba
har izuwa
lokaci mai tsawo,daga can kuma sai ya hade
fuska ya dubi Lubainu yace,hakika ka lashe
wannan
gasa kuma zaka auri Yazarina amma ka sani
cewa
har abada baza ka taba tarayya da itaba,domin
yanzu
dakai da 'ya mace duk daya ne,ka tashi daga
matsayin 'da namiji.
A dazu kafin mu fara gasar nan na baka hannuna
mun gaisa,a
wannan gaisawa da
mukayi na goga maka wani sihiri wanda shikenan
ka
zama mara amfani.Wannan asiri danayu maka
duk
duniya babu mai iya karyashi domin kuwa neman
maganinsa daidai yake da neman jaki mai kaho
ko kuma
mutum ya tafi farautar Ajalinsa.
Koda Mangul
yazo nan a zancensa sai ya sake bushewa da
dariyar mugunta. Like and cmmntALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 5
Koda Mangul yazo nan a zancensa sai ya sake
bushewa da dariyar mugunta.
A"amarin daya
DUGUNZUMA hankalin Yarima Mangul da sarki
Sailur kenan.Cikin bakinciki da takaici Sarki Alkas
ya
dubi Yarima Mangul ya daka masa tsawa
yace,kaiconka ya kai dana,hakika kaci amanar
abokantakar
dake tsakaninmu da sarki Sailur domin
babu maganar sihiri a cikin wannan gasa.Hakika
baka yiwa Lubainu adalci ba,ka sani cewa ba
karamin adalci Sarki Sailur yayi maka ba daya
shirya
muku wannan gasa saboda kada ni na zargeshi
da
rashin kyautata maka bisa zabin zuciyarka.To ka
sani cewa
wannan cin amana dakayi babu hukuncin
da ka dace shi face na goge matsayinka na 'da a
zahiri da badini,kuma indai ina numfashi a doron
kasa bazaka hau karagar mulkina ba.Koda gama
fadin haka sai hawaye ya zubowa sarki Alkas ya
juya ya fice daga cikin dakin yana mai tsananin
bakinciki.Shi kuwa sarki Sailur sai ya sa ka
dauke
Yarima Lubainu aka kaishi can turakarsa sannan
ya
tura aka gaiyato babban Bokan kasar wanda ake
kira
Shalkar Ibini Madusa ya zaiyana masa abinda
Yarima Mangul
yace yayiwa Yarima Lubainu.Nan take
boka shalkar yayi bincike ya tabbatar da faruwar
hakan kuma ya sanar da sarki cewa babu yadda
za'ayi Yarima Lubainu ya sami lafiyarsa ta
cikkakken
'da namiji face yaje Kogon Bahar Imfal ya tsinko
dam itaciya da ake bukata,sannan ya baiyana
masa irin
matakan da zaibi na nemo sassan wannan Allon
Sihiri guda uku wanda dole sai an karanta
bayanin
dake jikinsa sannan za'a iya izuwa Kogon Bahar
Imfal.Koda Boka Shalkar yazo nan a jawabinsa
sai
Sarki Sailur ya fashe da kukan bakin ciki yana
mai
cewa ai kuwa indai haka ne wanann cuta batada
magani
kenan tunda ban ga ta yadda za'a iya samo
wannan maganin ba.
Lokacin da Yarima Lubainu yaga
mahaifinsa ya fashe da kuka yana wanann jawabi
sai
ya yunkura cikin matukar karfin hali yace,ya kai
Abbana shin ka manta ne cewar ka taba gaya
min cewa
dukkan CUTA tanada MAGANINTA?
Nikam ban
taba cire rai da samun wannan magani ba,don
haka
yanzu bayan na gama jinyar wannan ciwo nawa
zanyi shiri na bazama cikin duniya neman
wannan
magani don haka baza'a daura aurena ba da
Yazarina har sai na samo wannan magani.
CUTA DA MAGANI ko yaushe suna tare da juna
saidai rashin
sani.
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa sarki
Sailur ya jinjina kai yana mai dafa kafadar
Lubainu
yace,da kyau 'dana ina alfahari dakai saboda
baka
karaya bisa duk abinda baka sa a
gabanka,saboda
haka na amince wannan shawara daka yanke.
washe gari da safe sarki Alkas ya dauki dansa
Yarima
Mangul wanda ya zama nakasasshe mai hannu
daya
suka tafi izuwa nasu birnin.
Al-amarin Yazarina kuwa
lokacin data farfado taji cewar Lubainu bai mutu
ba
saita kamu da tsananin farin ciki ta mike zumbur
ta
ruga izuwa cikin gidan sarautar ta wuce kai tsaye
izuwa cikin
turakar Yarima Lubainu.Tana shiga ta
iske Yarima zaune akan gadonsa likita na bashi
magani a kofi yana sha.Yazarina ta karasa cikin
farin
ciki ta zauna a gefen gadon daf dashi ta dubeshi
cikin murmushi tana mai ajiyar zuciya tace,ya kai
masoyina inda ka tafi ka barni da nima bakin
cikin rashinka ne
zai kashe ni.Koda jun haka sai Yarima
Lubainu yayi murmushi ya sallami Likitan sannan
ya
zaiyana mata duk abinda ya faru a filin gasar tun
daga lokacin da ta fadi ta suma kawo izuwa
sa'adda
boka Shalkar ya tabbatarwa da Sarki Sailur asirin
da
aka yiwa Lubainu bisa cutar data sameshi da
kuma yadda za'a
samo maganinta.Koda jin wannan labari
sai Yazarina ta dora hannayenta aka ta kurma
uban
ihu kuma ta fashe da matsanancin kuka domin
tasan
cewa murna ta koma ciki,kuma idan Yarima
Lubainu
ya tafi neman wannan maganin abu ne mayuwaci
ya
dawo gida a raye.Koda Yarima Lubainu yaga
Yazarina ta fashe
da wannan kuka sai ya shiga
rarrashinta yana mai kwantar mata da hankali
gami da nuna mata cewa lallai idan ya tafi
neman
wannan magani sai ya sameshi.Da Kyar da sidin
goshi Lubainu ya samo kan Yazarina ta daina
kuka
amma sai tace da shi lallai bazai yi wannan
tafiya ba sai an
daura aurensu duk da cewar ya sami wannan
lalura domin burinta shine mutuwa ta rabasu
tana
dauke da igiyar aurensa.koda Lubainu yaga ran
Yazarina zai baci ainun idan bai amince da
bukatarta
ba kuma zata iya shiga cikin matsanancindamu
wa
sai ya amince da hakan.Saida Yarima Lubainu ya
shafe wata
shida a kwance yana jinyar wannan
rauni
na cikinsa sanann ya warke sumul.A ranar
dayazo
zaiyi bankwana da Yazarina sai da suka shafe
sa'a
daya a tsaye rungume da juna suna kuka.Daga
karshe ne Yazarina ta janye jikinta daga cikin
nasa suka
fuskanci juna suna masu zubar da hawaye
tace,yakai mijina kayi sani cewa daga yau bani
da
sauran sukuni da kwanciyar hankali a
rayuwata.Komai dandanon abinci daci zaiyi a
bakina
komai kyan sutura bazata burgeni ba har sai
gaka
ka dawo gareni a raye koda kuwa baka sami
nasarar
samo maganin daka tafi nemowa ba.Na yarda na
zauna dakai a cikin halin da kake ciki har izuwa
karshen rayuwa ta.
Koda Yarima Lubainu yaji wannan
batu daga bakin Yazarina sai yaji tausayinta ya
kamashi ainun bai san sa'adda ya rungumeta ba
suka dada
kankame juna suna masu fashewa da
sabon kuka.
Da kyar ya janye jikinsa daga cikin nata
ya juya mata baya ya nufi inda dokinsa yake.Sai
kawai yaga Sarki Sailur tsaye kusa da dokin nasa
ya kura masa idanu kawai idanunsa sun kada
sunyi
jawur.
Nan take Yarima Lubainu ya ruga izuwa ga sarki
Sailur suka
rungume juna.
Tsawon 'yan dakiku
suna manne sannan sarki Sailur ya janye jikinsa
daga cikin nasa ya fuskanceshi yace,Ya kai dana
guzurin kudi kona abinci dazan baka bashi ne
abinda
zai taimake ba a cikin wannan tafiya da zakayi
har ka kai ga
samun nasara.Yanzu zan baka babban guzuri
wanda aminina Abdul Nasir Ibini Hamza ya
bani,kuma ya shawarceni dana dinga amfani da
shi
a duk sa'adda tafiya ta kamani.Tabbas na jarraba
amfani da wannan guzuri har sau uku kuma ya
fidda
ni daga cikin mugayen masifun da suka
gagareni,wanann
guzuri dai ba komai bane
face,
GASKIYA,
AMANA da cika ALKAWARI.
Tabbas
idan ka ruke wadannan abubuwa guda uku babu
wata masifa da zata taso ta afka masa.Babu irin
tsautsayin da bazaka shallake shiba kuma duk
abinda kasa a gabanka sai ka sami nasararsa.
Lokacin da Sarki Sailur yazo nan a zancesa
sai Yarima Lubainu ya kamu da tsananin mamaki
yace yakai Abbana kayi sani cewa Yazarina ta
bani
Labarin amininka Abdul Nasir da abinda ya gaya
mata akan asirin da Yarima Mangul yayi
mini,kuma
akwai tambayar datayi masa yace kaine wanda
zaka bata
amsar wannan tambaya.Na duskanci cewar ka
aminta dashi dari bisa dari,amma kuma gashi ba
addininmu daya ba.To menene dalilin da yasa
baka
karbi addininsa ba?
Koda jin wannnan batu sai Sarki
Sailur ya murmushi yace,yakai dana kayi sani
cewa
komai da lokacinsa,tabbas na yarda da Abdul
Nasir kuma na
yarda da addininsa har cikin zuciyata
amma ina jiran lokacin da zan karbeshi Koda
gama
fadin haka sai Sarki Sailur ya juya ya nufi cikin
gidan
sarautar yana mai zub da hawaye ba tare daya
sake
waigowa ba har ya kule.
Nan take Yarima Lubainu ya
kama dokinsa ya hau ya nufi kofar fita daga cikin
gidan
sarautar.
Ita kuwa Yazarina sai ta bishi da kallo
kawai tana kuka.Lubainu bai sake dubanta ba
don
kada zuciyarsa ta karaya har ya bace ma ta da
gani..
Wannan shine asalin yadda Yarima Lubainu ya
baro kasar su ya taho izuwa nan birnin Rauhul
Rauhul domin neman maganin cutar da Yarima
Mangul yayi
masa asiri.Lokacin da Yarima Lubainu
yazo daidai nan a tunanin zucin abubuwan da
suka
faru ga rayuwarsa a baya sai hankalinsa ya sake
dugunzuma ainun,musamman daya tuno da
maganganun da sarauniya Akisatul Sauwara ta
gaya
masa bisa irin tsananin tashin hankalin dake
cikon daha
wannan Allon Sihiri dake hannun mutane uku
don karanta bayanin dake cikinsa sannan a tafi
neman abokan tafiya kogin Bahar Imfal har
mutum
uku kuma aketa ta cikin wadannan mugayen
dazuzzuka guda uku.Nan take Yarima Lubainu
yaji
zuciyarsa tasake karaya fiye da ko yaushe.Ya
fara tunanin
cewa ya kamata ya hakura da wannan
bukata tasa kawai ya tafi izuwa wani bigiren
dabam
na duniya inda zai karasa sauran rayuwarsa ya
kuma hakura da masoyiyar tasa.Amma da ya
tuno
da guzurin da sarki Sailur ya bashi sai kuma yaji
guiwarsa ta kara karfi akan tafiyarsa.
Haka dai ya wanzu yana mai ta sake saken zuci
har barci ya
sace
shi bai sani baALLON SIHIRI
Littafi na daya(1)
Part 6
Al'amarin sarauniya Akisatul Sauwara kuwa
lokacin
data shiga cikin gidan sarautar ta isa turakarta
sai ta
kasa zaune ko tsaye ta kama kaikawo a cikin
turakar tana tunani da zancen zuci.Koda taga
hakan
ba zai fissheta ba sai ta tura aka kirawo tsohuwa
Dulaiba.Tsohuwa Dulaiba ta kasance mahaifiyar
kakan
mahaifin sarauniya Akisatul Sauwara,don
haka
a fadin birnin Rauhul Bagadar babu mai yawan
shekarunta,domin shekarunta sun kai dari da
sittin,amma kuma Allah ya bata lafiya,idanunta
garau
tana gani sosai,hakoranta duka suna nan reras
daya bai fadi
ba,kuma tana iya jure tafiyar yini guda ba
tare da gajiya ba.Tsohuwa Dulaiba tana da kaifin
basira gami da hangen nesa,don haka duk
sarakunan da akayi a birnin Rauhul Bagadar basu
da wani abokin shawara sama da ita,kuma bata
taba
bayar da shawara akabi akayi nadama ba.Lokacin
da
sarauniya Akisatul Sauwara ta kadaita da
tsohuwa
Dulaiba a cikin turakarta sai ta kwashe labarin
duk
abinda ya faru tsakaninta da Yarima Lubainu ta
zayyane mata,kuma ta nemi shawararta bisa
abinda
ya kamata tayi.Koda jin wannan batu sai
tsohuwa Dulaiba ta
kyalkyale da dariya.Al'amarin dayai
mutukar baiwa Akisatul Sauwara namaki kenan
ta
dubeta cikin mamaki tace,yake Dulaiba ina dalilin
wannan dariya taki?Koda Dulaiba taji wannan
tambaya sai ta nutsu tace,ki karbi wannan bako
hannu biyu,kiyi masa duk abinda yake so,domin a
sanadinsa
ne zamu cika burin da kakanninki suka
kasa cikawa tun kafin a haifeni ni kaina.Ki sani
cewa
wannan barin Allon sihiri dake cikin gidan tarihin
garin nan wanda aka sanya shi a cikin kwalba ya
zamana cewa duk duniya ke kadaice zaki iya fito
da
shi to duk ranar da aka samo ragowar barinka
biyun aka
hadashi aka dora allon akan gunkin dake
tsakiyar fadarki sai Birninmu ya sami daukaka da
arzikin da babu wata kasa dazata kaishi kuma
har
abada baza a cimu da yaki ba har sai mun
mallake
gaba dayan kasashen duniya sun dawo karkashin
mulkinmu.Wannan shine burin da iyayenki da
kakannink suka
kasa cikawa amma yanzu ke kin
sami babbar dama ta cika wannan buri.Abinda
zakiyi
shine ki dauko wannan Allon Sihiri amma kada ki
damkawa Yarima Lubainu a hannunsa.Ki boyeshi
a
tare dake dare da rana kuma ki bishi kuyi wannan
tafiya tare har izuwa sauran kasashen biyu inda
za'a sami
ragowar barikan Allon biyu.Da zarar an samo
su saiki shammaci Lubainu ki kwashe Allunan ki
bace.Na san cewa ke gagarumar jaruma ce kuma
mayakiya mai tarin sirrikan tsafi don haka ko
gaba
da gaba zakiyi dashi sai kin sami nasarar
hallakashi.Idan ya tambayeki dalilin dayasa kike
son ki bishi
kuyi tafiyar tare kice dashi saboda a
rayuwarki babu abinda kike so sama da
tafiya.Koda
tsohuwa Dulaiba tazo nan a zancenta sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara ta gamu da tsananin farin ciki
kuma ta sami nutsuwa gami da kwanciyar
hankali.
washe gari kuwa da safe sai sarauniya Akisatul
Sauwara ta tura
aka zo da Yarima Lubainu
har cikin turakarya in ya riske a kishingide bisa
wata
doguwar kujera ta alfarma tana shan ruwan inibi
a
cikin wani kofin zinare.A wannan lokacin tana
sanye
da wata jar riga mai shara shara wacce take
bayyana
dukkan surar jikinta.Koda Yarima Lubainu yayi
arba da Akisatul
Sauwara cikin wannan hali sai zuciyarsa
ta buga da karfi,yayi sauri ya sunkui da kansa
kas.Ba komai ne yasa shi hakan ba face gani
yayi
kamar masoyiyarsa ce Yazarina zaune a wajen
saboda komai irin na surar jikin Akisatul Sauwara
yazo iri daya sak dana Yazarina tamkar Hassana
da Hussaina
suke.
Kawai a kamannin fuska ne suka
bambanta.Tabbas Sarauniya Akisatul Sauwara ta
cika kyakkyawar mace abin kwatance,To wai
shin
mene ne abinda ya hana wannan kyakyawar
sarauniya yin aure alhalin tana cikin kuruciyarta
don
baza takai shekara ashirin ba a duniya?Wannan
itace tambayar
da Yarima Lubainu ya yiwa kansa kuma ya
kasa bada amsarta.Lokacin da Sarauniya Akisatul
Sauwara taga Yarima Lubainu yayi saurin kawar
da
idanunsa ga barin kallonta ya sunkui da kansa
sai ta
kyalkyale da dariya sannan ta dago hannunta
guda
tana mai yiwa gaba daya kuyangin dake dakin
inkiya
dasu fita su basu wuri.Nan take kuyangin suka
cika
umarni.
Fitarsu ke da wuya sai Akisatul Sauwara ta
dauki wata abaya irin tasu ta saraunta ta yafa a
jikinta,wato ta suturce tsiraicinta sannan ta
dauko
tambula na ruwan inibi gami da wani kofin zinare
tazo daf da
inda Lubainu ke tsaye ta kusanceshi
ainun yadda har suna iya jin numfashin
juna,sannan
ta zuba masa ruwan inibin a kofin ta mika
masa.Ba
tare da tsoron komai ba Lubainu ya karbi kofin
ya
kurba.A sannan ne ta kama hannunsa taja shi
izuwa
kan waccan doguwar kujera suka zauna tare ta
dubeshi
fuskarta cike da annuri da murmushi
tace,yakai wannan 'dan Sarki kayi sani cewa kai
ne
da namiji na farko wanda ya taba shigowa har
nan
cikin turakata yasha ruwan inibina,kuma har
hannuna mai daraja ya taba nasa.Ka sani cewa
ba
komai ne yasa ka sami wannan matsayi ba face
saboda kazo
min da babban al'amari wanda na dade
ina jiransa a rayuwata.Kafin nayi maka wani
cikakken bayani ina son ka sanar dani sirrin da
yasa
kazo kasata neman barin Allon Sihiri ni kuma
nayi
maka alkawarin zan dauko maka Allon Sihirin
dake
hannuna amma bisa sharadi guda biyu.Sharadi
na farko shine
tafiyar da zakayi tare dani za'a tafi har a
gama hada Allon Sihirin uku.Sharadi na biyu
kuma
shine zan ajiye nawa allon a hannuna bazan baka
ba
har sai bayan an samo ragowar barikan
biyu.Nasan
zakayi mamaki bisa dalilin dayasa na kafa maka
wadannan sharuddai to ka sani ba wani dalili
bane face kawai
ni a rayuwata babu abinda nake so sama
da
yin tafiya domin naga abubuwan al'ajabi,kuma
nayi
gami da mugayen dabbobi da tsuntsaye don na
gano iyakar jarumtaka da sadaukantaka ta.
Lokacin
da Akisatul Sauwara tazo nan a jawabinta sai
Yarima Lubainu
yayi shiru yana tunanin da
mamaki,kawai har izuwa tsawon yan dakiku,daga
can sai yayi ajiyar zuciya yace shike nan na
amince
da wadannan sharudai naki.Nan take Yarima
Lubainu ya kwashe labarin rayuwarsa kaf ya
zaiyane
mata ba tare da ya boye komai ba.Ai kuwa yana
gama bata
labarin jikinta yayi sanyi don har saida
idanunta suka ciko da kwallah.Nan take taji
zuciyarta ta kama wasi wasi akan cewar bai
kamata
ta yaudari Yarima Lubainu ba ta gudu da Allon
Sihiri
bayan sun hadashi.Zaifi kyau ta rakashi har
izuwa
kogin Bahar Imfal in yaso bayan bukatarsa ta
biya sai ta dawo
gida da Allon Sihirin ta cika nata
burin.Wata zuciyar kuma sai tace da ita,idan
kikayi
haka kinyi babban kuskure tunda baki da
tabbacin
zaki iya wucewa lafiya kuma a raye ta cikin
wadannan mugayen dazuzzuka guda uku kafin a
isa kogin Bahar Imfal.Kawai sai Sarauniya
Akisatul
Sauwara ta dago kai ta dubi Yarima Lubainu
cikin
alamun tausayawa tace,ka kwantar da hankalinka
yakai Lubainu,hakika na tausaya maka mutuka
bisa
kaddarar daka tsinci kanka a

1 Comments On ALLON SIHIRI 1 TO 9
avatar
abdulazeez

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment